29.3.18
AyAU Alhamis
LEADERSHIP Don Allah Da Kishin Qasa
JARIDAR HAUSA MAI FITOWA KULLUM TA FARKO A NIJERIYA
www.leadershipayau.com Leadership A Yau
29 Ga Maris, 2018 (11 Ga Rajab, 1439)
LeadershipAyau
No: 115
N150
Savanin DSS Da EFCC: Majalisa Ta Amshi Rahoto Daga Bello Hamza
Majalisar Dattijai ta amshi rahoton kwamitin da ta kafa domin bincikar taqaddamadar da ta auku tsakanin jami’an hukumar EFCC dana DSS ranar 21 ga watan Nuwamba 2017. Shugaban kwamitin Mista Francis Alimikhena ne ya miqa wa majalisar
rahoton a zaman ta na jiya Laraba. Sanata Fatima Rasaki ce ta bayyana amincewa da qudurin karvar rahoton. A watan Nuwamba na shekarar 2017 ne majalisar dattijai ta naxa kwamitin domin binciken rikicin daya varke tsakanin jami’an hukumar yaqi da cin hanci da rashawa EFCC
da hukumar leqen asiri ta qasa DSS a Abuja. Rikincin dai ya auku ne yayin da jami’an hukumar EFCC suka yi qoqarin cafke tsohon shugaban hukumar leqen asirin DSS Mista Ita Ekpeyong da kuma shugaban hukumar NIA Mista Ayodele Oke. “Jami’an Hukumar EFCC su je gidan
tsohon shugaban hukumar DSS xin ne Mista Ita Ekpeyong domin cafke shi sai jami’an hukumar DSS suka hana su aiwatar da kamun”. Mista Alimikhena, ya bayyana wa manema labarai cewa, a halin yanzu dai an miqa wa majalisar rahoton, sai majalisa ta tattauna kafin ya iya cewa komai a kan rahoton.
An Kashe Sama Da Mutum 20 A Zamfara 4
Daga hagu zuwa dama: Ministan Sadarwa, AbdurRaheem Adebayo Shittu; Ministan Tsaro, Mansur Xan Ali tare da Ministar Harkokin Mata, Aisha Alhasan yayin taron majalisar Zartaswa wanda aka gudanar jiya a fadar Shugaban Qasa dake Abuja
Abubuwa 12 Da Buhari Makiyaya: Jihar Kwara Ya Shelanta A Taron APC Ta Haramta Kiwon Dare > Shafi na 2
> Shafi na 5