4.4.18
AyAU LEADERSHIP
Laraba
Don Allah Da Kishin Qasa
JARIDAR HAUSA TA FARKO MAI FITOWA KULLUM A NIJERIYA
www.leadershipayau.com Leadership A Yau
4 Ga Afrilu, 2018 (17 Ga Rajab, 1439)
LeadershipAyau
No: 118
N150
Hatsabibi: Yadda Aka Yi Musayar Maitangaran Da Matan Dapchi Daga Umar A. Hunkuyi
Bayanai sun bayyana kan yadda Jami’an tsaro na SSS, suka yi musayar fursuna da vangaren Boko Haram, na al-Barnawi, bisa sharaxin a sakan masu wani babban kwamanda na su, Hussaini Maitangaran, su kuma su saki yara
mata, ‘yan makarantar Dapchi. LEADERSHIP A Yau, ta kawo rahoton kama Maitangaran xin da Jami’an tsaron na SSS, suka shelanta a cikin wani bayani da suka fitar ranar 9 ga watan Satumba 2017, wanda aka ce shi ya kitsa harin bamabaman da aka kai a Kano.
A wata maqala da Ann Mcgregor, wata qwararra a fannin sha’anin tsaro na duniya ta fitar, a shafin ta na yanar gizo mai suna, News Plus Views, ta yi qarin haske kan yadda wasu ‘yan Nijeriya da abokanan hulxan su na waje, suke cin qazamar riba kan kuxaxen musayar da suke shiryawa ana yi
da ‘yan ta’addan. “Tun a shekarar 2009 ne gwamnatin ta Swiss ta mayar da kan ta wata ‘yar baruwanmu ta musamman, wacce take shiga tsakani a rigingimu da yawa da ake yi a qasashen Afrika.
>Ci gaba a shafi na 2
• Maitangaran
Taron Gwamnonin APC Da Buhari:
An Gaza Cimma Matsaya Kan Wa’adin Oyegun 4
• Daga hagu zuwa dama: Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar; Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje; Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, tare da Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu, jiya a wurin taron da qungiyar Gwamnonin APC suka yi da Shugaban Qasa Muhammadu Buhari a fadarsa dake Abuja (Hoto: REMI AKUNLEYAN)
Budurwa Ta Kashe Sanata Xansadau Ya Buqaci A Kanta A Jigawa Sa Dokar Ta Vaci A Zamfara > Shafi na 4
> Shafi na 10