16.4.18
AyAU LEADERSHIP
Litinin
Don Allah Da Kishin Qasa
JARIDAR HAUSA MAI FITOWA KULLUM TA FARKO A NIJERIYA
www.leadershipayau.com Leadership A Yau
16 Ga Afrilu, 2018 (29 Ga Rajab, 1439)
LeadershipAyau
No: 124
N150
Lambar Yabo Ta ZIK: An Karrama Gwamna Masari A Legas Daga El-Zaharadeen Umar, Legas
Gidauniyar tsohon shugaban qasar Najeriya Dakta Nmandi Azikiwe ta shirya taron karrama wasu daga cikin fitattun mutane da suka bada gudunmawa a cigaban al’umma acikin shekarar 2017 ciki harada Gwamna Masari, bayan wani bincike da wata cibiya mai suna ‘’Public Policy Research And Analysis Center’’ da ke jihar Legas. Da man dai wannan cibiya ta saba
Babban Taro:
gudanar da lakca duk shekara domin bayyana wasu daga cikin halayyar marigayi Dakta Nmandi Azikiwe da kuma tunawa da wasu abubuwan da ya bari. Daga baya kuma cibiyar suka yi tunanin bullo da bada kyauta ta musamman ga wasu kevavun mutane da suka taka mahimmiyar rawa wajan cigaban al’umma. ita dai wannan karramawa da aka yi wa gwamna Aminu Bello Masari tare da wasu manyan mutane da suka bada gudunmawa
ta fannoni daban-daban ta biyo bayan wani bincike na musamman na wata cibiyar bincike da tsare-tsare da kuma yin fashin baki ta gudanar inda daga qarshe ta bayyana gwamna Masari a matsayin gwamnan da ya kawo canji a fannoni da dama da suka haxa da kawo cigaba a rayuwar jama’a da kuma samar da abubuwan more rayuwa ga mutanen jihar Katsina.
>Ci gaba a shafi na 4
•Gwamna Masari
Jam’iyyar APC Ta Kafa Kwamitin Gudanarwa 4
• Shugaban Qasa Muhammadu Buhari yayin da ya amshi baquncin Bola Ahmed Tinubu jiya a Birnin Landan
Jerin Mutanen Da Buhari Ke Abin Da Ya Sa Na Ke Sukar Buqata Don Takarar 2019 Gwamnatin Mijina –Aisha Buhari > Shafi na 18
> Shafi na 4