Page 1

15.04.18

AyAU LAHADI LEADERSHIP Don Allah Da Kishin Qasa

JARIDAR HAUSA MAI FITOWA KULLUM TA FARKO A NIJERIYA Leadership A Yau

LeadershipAyau

15 Ga Afrilu, 2018 (28 Ga Rajab, 1439)

www.leadershipayau.com

No: 031

N150

An Kammala Mauludin Inyass A Kaduna Cikin Lumana Daga Abdulrazaq Yahuza Jere, , Abuja

Milyoyin al’ummar Musulmi, musamman ‘yan failar xariqar Tijjaniyya, sun kammala mauludin fitaccen shehun Musuluncin nan, Sheikh Ibrahim Inyass, cikin kwanciyar hankali da lumana. Katafaren filin da a ka gudanar da taron mauludin na Murtala Sikwaya da ke tsakiyar garin Kaduna ya cika maqil ba masaka tsinke, maza da mata, yara da manya kowa ya halarta.

Tun daga ranar Alhamis da ta gabata, qungiyar Majma’u Ahbabu Shaikh Ibrahim Inyass ta tarbi tawagar babban khalifan Inyass da su ka zo daga qasar Senigal a filin jiragen sama na Kaduna. babban khalifan bai samu damar zuwa ba, saboda nauyin jiki, inda ya wakilta tawaga mai qarfi a qarqashin Shehu Mahi Inyass. Cikin garin Kaduna ya cika ya batse saboda dandazon mahalarta mauludin a lunguna da saqo na garin waxanda suka riqa yin zikirori da rera yabon Shehu Ibrahim.

Da ya ke jawabi a bainar milyoyin mahalartan, Shaikh Muhammadul Makkiy Inyass, ya ce Shehu Ibrahim na kowa da kowa ne ba na wasu jama’a su kaxai ba. “Khalifan Shehu Babba, Shehu Tijjani Inyass ya so ya halarci nan tare da ku amma saboda nauyin jiki sai ya wakilta mu. Ya ce a gaishe ku, yana gode wa dukkan jama’ar Nijeriya. Shehu Ibrahim na kowa da kowa ne, idan mutum a matakin Musulunci yake Shehu nashi ne, idan a matakin Imani yake Shehu nashi ne, haka

nan idan a Ihsani yake Shehu Ibrahim nasa ne. Wannan haxuwa ta Allah babu irin ta a ko ina cikin duniya sai fa waxanda suka yi irin ta... Allah ya mayar da kowa gida lafiya”, ya bayyana. Shi ma da yake jawabin godiya, shugaban qaramin kwamitin shirya Mauludin, Alhaji Lawal Salihu Malami, ya gode wa duk waxanda suka taimaka walau da kuxi ko da jikinsu domin samun nasarar mauludin. An dai kammala taron Mauludin kafin Azahar, indajama’asukakamahanyarkomawagidajensu.

2019: Manyan Qalubale Bakwai Da Ke Gaban Buhari 5

Fatara Da Talauci Kashe-Kashe Da Satar Mutane Rikicin Cikin Gida Majalisar Dokoki Na Hannun Daman Buhari Farfaxowar PDP Vangaranci

Wane sashe na mahalarta Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass da a ka gudanar a garin Kaduna jiya Asabar, 14 ga Afrilu, 2018.

Mazan Jiya: Tunawa Da Xan Sanda A Azare Ya Yi Qarar Rasuwar Malam Aminu Kano Budurwa Don Ta Qi Auren Sa > Shafi naa 2

> Shafi na 2


2

leadershipayaulahadi@yahoo.com

A Yau LAHADI 15.04.2018

Mazan Jiya: Tunawa Da Rasuwar Malam Aminu Kano Daga Ado Musa

A ranar Talata mai zuwa 17 ga April, 2018, za a yi bikin tunawa da rasuwar Malam Aminu Kano,wanda ya ke gogaggen malamin makaranta ne kuma mashahurin xan siyasa, masanin al’amuran yau da kullum kana ga shi marubucin qagaggun labarai na hikayoyin kaifafa zukata. A yau dai Malam Aninu ya cika shekaru 35 da kwana huxu cif-cif ya na kwance a makwancinsa na kabari. Kafin rasuwar Malam Aminu a ranar Lahadi 17 ga April, 1983, an daxe a na furta cewa, ‘Malam ya rasu’, ba sau xaya ba, ba kuma sau biyu ba, illa dai a ce mutuwa ba ta cimmar ba sai da Allah ya kawo qarshen wa’adinsa, domin ko a 1982 lokacin da a ka taya shi murnar cika shekaru 62 da haihuwa a gidansa, sai da Malam ya yi tsokaci a kan masu yi ma sa qage da fatan mutuwa har ya kira su da suna ’yan tsegumi, kana ya qara da cewa, “da ana cewa wai na mutu, to ga shi na farfaxo, kuma yanzu zan yi magana.” Allah Akbar! Haqiqa Nijeriya ta yi rashin xan kishin qasa, wanda cike gurbi irin nasa ya na da matuqar wahala, domin Malam Aminu uba ne kuma mai matuqar kula da al’ummarsa da kuma ’yan siyasa, wanda a zahiri ya yi imani da tsari irin na adawa, wanda a cikin tsarin ya rayu har kuma ya koma ga Allah. Tun lokacin da Malam Aminu ya kammala karatunsa, abubuwa guda huxu ya so ya yi a rayuwarsa ta fuskar sana’ar zaman duniya, amma daga qarshe babu wanda ya samu, amma sai dai a ka ce ma sa, sai dai ya yi aikin koyarwa, shi kuma sam ba ya son sana’ar koyarwa, amma idan an duba za a ga cewa, a cikin aikin koyarwar ne Malam ya samu damar zama xan siyasa, ya kuma cimma duk wani burinsa da zai share wa talakan qasa hawaye a kan ya ga lallai ya samu ’yanci. A ta haka ya riqa ganawa da talakwa ya na faxa mu su yadda za su san ’yancinsu cikin hikima da dabaru, su kuma yi karatu domin a riqa damawa da su a sha’anin mulkin qasar. Don haka a qarshe dai Malam ya faxa siyasa gadan-gadan, kuma siyasar da bai tava tsammani zai shige ta ba, amma sai ga shi ya shige ta har ya rayu a cikinta, ya kuma koma ga Allah a cikinta. Malam Aminu ya shiga harkokin siyasa ba domin ya samu mulki ko-amutu-ko-a-yi-rai ba, a’a ya shiga domin ya cimma wasu buruka guda shida kamar haka: (1) Domin bin sahun ’yan kishin qasa masu gwagwarmaya da Turawa ’yan mulkin mallaka, domin samawa Nijeriya ’yancin kai. (2) Domin ganin Talaka ya samu ’yanci da sassauci game da biyan haraji da jangali, domin a na yi mu su kuxin goro wajen biyan haraji tsakaninsu da masu arziki. (3) Ya kuma koyawa talaka cewa, “a’a” ko “na qi” a lokacin da a ka umarce shi ya

yi noma a gandun sarki ba tare da an ba shi ko Kwabo ba. (4) Ya yi qoqarin a tsame hannun sarakuna gargajya game da sha’anin kula da iko a kan ’yan doka da kuma gidajen yari. (5) Malam Aminu shi ne mutun na farko a Arewa da ya matsa da cewa lalle sai an ba wa mata ’yanci a Arewa, kuma sai sun samu ’yancin jefa quri’a a lokacin zave da kuma ba su dama su shiga harkokin siyasa da sha’anin mulki a dama da su. (6) A bawa ’ya’yan talakawa dama su yi karatu kuma a bar su su riqe muqamai na siyasa da na sha’anin mulki. To, kuma idan kun duba za ku ga cewa, duk waxannan manufofi na Malam da ya yi ta qoqarin ya ga sun tabbata, to Allah ya cika ma sa burinsa, domin tun kafin Allah ya xauki rayuwarsa sai da ya ga cikar burin nashi. Duk wanda ya san Malam Aminu Kano, musamman ma dai waxanda su ka yi tarayya da shi a cikin shekaru fiye da 30 da ya yi ya na hidimar siyasa a qasar, to sun san tunaninsa idan garin Allah ya waye bai wuce abu xaya ba, wato yadda za a kyautatawa zaman jama’a, talakan qasa ya san masu shugabancinsa kuma su ma su san da zamansa da kuma sanin abin da ke damun sa. Ko 1979 abin da ya hanga kenan lokacin da ya ji ’ya’yan jam’iyar PRP su na ta qorafi da jin zafin cewa, jihohi guda biyu kacal su ka samu, wato Kano da Kaduna, a zaven da a ka yi, amma Malam ya ce, mu su, “a’a, ku yi haquri, Allah ba ya yin abin shi sai da dalili, domin wataqila Allah jarraba mu ya yi, ya gani, bari ya ba mu jihohi guda biyu a cikin 19 ko za mu iya kwatanta gaskiya da adalci, domin kada ya ba mu jihohin duka mu handame dukiyar al’umma.” Wannan kenan. Wataqila babu abinda ya fi tayar wa da Malam hankali a rayuwarsa ta duniya, illa yadda ya ke ganin sauran jama’ar qasar su ke xaukar ’yan Arewa cewa ba su san ciwon kansu ba, ba su da ilimin zamani, iyayensu al’majirai ne ko kuma makiyaya ko ma bayan sauran jama’ar qasar, musamman ma idan an kwatanta su da mutanen Kudu, waxanda su ka yi mu su fintinkau wajen ilimin boko. Haqiqa wanan shi ne dalilin da ya sanya Malam ba ya saurarawa ko rangwantawa duk wanda ya raina mu, musaman ma a lokacin da shugaban qasa Alhaji Shehu Shagari na wancan lokacin ya yi yunqurin zai dawo da hedikwatar qasar nan daga Lagos zuwa Abuja a 1982, a lokacin da ya ji irin muggan kalamai da su ka riqa furtawa daga bakunan waxanda ba sa so a taso. To, da a ka zo wannan fagen na qiyayya da cigaban Arewa, duk da Malam ya na jam’iyar adawa, to Malam ba ya shakkar a-yi-ta-ta-qare, domin kare martabar Arewa. Sau tari idan an zo irin wannan matsalar, to za ka ji ya na cewa, ba za a haxa kai da mu ta kowacce hanya a cuci wannan vangare na Arewa muddin mu na nunfashi. Wato a kullum irin tunanin

Malam kenan, shin yaya za a yi? Mu iya zama da junanmu, mu gane mai son mu da dalilin da ya ke son mu ko kuma qin mu da kuma ta yadda za mu zauna, domin mu ci amfanin zaman tare. A ta fuskar zaman jama’a da junanmu kuwa a kullum Malam ya na yawan yiwa al’ummar qasar nasiha a kan cewa su girmama kansu su da kansu, su kuma kyautatawa juna, kuma kyautatawar nan ya kan ce ba ta tsaya ga mutane ba kawai har ta kai ga dabbobi da tsuntsaye, domin ko a gidan Malam akwai wani kare mai suna Jaura. Bayani a kan wannan karen kuwa shi ne, Malam ya tava zuwa wata unguwa a cikin birnin Kano, domin yin ta’aziyya, a lokacin a na tsananin hunturu. Bayan ya kammala ta’aziyyar, a hanyarsa dawowa gida sai ya ci karo da wasu yara su na ta jagwalgwala wani xan kwikwiyo, ga shi a yatsine yunwa ta kassara shi, ga tsananin hunturu ya ratsa shi. Sai Malam ya sa a •Marigayi Malam Aminu Kano ka kori yaran ya kuma umarta da a sawo wa karen abinci. Bayan Malam ya koma matasan NEPU ya sa hukumomi da gida sai ya yi tunani cewa idan yau ya sarakuna su ka qara qaimi wajen ba shi abinci, to gobe kuma wa zai ba farautar su da tsanar su a kan haka da shi? Daga nan sai Malam ya ce, a je a yawa daga cikinsu a ka yiwa kisan gilla. xauko ma sa karen a kawo ma sa gida. Misali; irin kisan gilla da a ka yiwa To, haka tunanin Malam ya ke da kuma Malam Audu Angale ba tare da an kai tausayawarsa ga na baya har ga tsofaffi shi kotu ya kere kansa ba. A haka a ka da dabbobi. ya da gawarsa a kan titi da kuma wata Irin tausayin Malam da yafiya ya qara shari’ar da ta ja hankalin kowa a lokacin fitowa qarara, musamman ma a lokacin ta Malam Adamu Gaya wanda a ka zarge da a ka tava yiwa tawagar Malam shi a ka kuma gurfanar da shi a gaban kwantan vauna saura qiris a kashe shi kotu, saboda ya wuce ta qofar fadar a lokacin ya na kan hanyarsa ta zuwa hakimi sanye da takalmi a qafarsa. garin Rano, domin yin wata ta’aziyya. Saboda wannan irin zalunci da a ke To, ya zo daidai garin Bunkure, sai a yiwa mabiya Malam ya sa a kullum ya ka afkawa tawagar su Malam xin babu kan yiwa mahukunta qasar nasiha da zato babu tammani. To, da qyar dai ya cewa, Allah ne fa kaxai ya san waye Malam xin ya tsira da rayuwarsa. Bayan bawansa na kirki da na banza. ya isa garin na Rano sai Malam ya ce, a Don haka a daina zaluntar su, domin qyale su kawai; rashin imani ne irin na su ma ’yan adam ne kamar kowa. Don xan adam; shi kuwa xan adam Allah ma haka su ma a ba su da ma a ga hikimar ba ya iya ma sa. Allahu Akbar! Haka dai da ta ke tattare da su domin cigaban Malam ya ke da irin wannan tunani abin qasa, domin babu abi da Allah ba ya yabo da koyi. so kamar wulaqanta mutane domin Ko a lokacin da ya ke jagorantar mutuncin mutun kuwa shi ne babban jam’iyyar NEPU kafin a ba wa Nijeriya magana kowa a ba shi mutuncinsa. mulkin kai da kuma bayan ta samu Waxanda ba su san irin zaman da ’yancin kai, irin wannan halayyar tashi a ka yi tsakanin Malam Aminu Kano ne ya sa xaruruwan dubunnan talakawa da Sardaunan Sokoto Firimiyan jihar su ka ringa shiga NEPU, domin yin Arewa, Sir Ahmadu Bello (Allah ya ji tarayya da shi wajen gwagwarmaya qan sa), sun xauka cewa gaba a kai ta a kan zalunci da danniya da a ke yiwa ta yi a tsakaninsu, kuma a zahiri ba al’umma. haka abin ya ke ba, domin ko shi karanA dalilin haka xaruruwan ’yan NEPU kansa Malam Aminu ya sha nuna irin a ka riqa azabtarwa a yayin da wasu halayyarsa sun zo xaya da na Sardauna, aka garqame su a kurku, wasu kuwa wato wajen qoqarin riqe amanar jama’a tilasta mu su a ka yi su ka tafi gudun da shugabanci nagari da tsoron Allah. hijira a yayin da su ka bar iyalansu da Babban misali a nan shi ne maganar dukiyoyinsu, domin tsira da rayuwarsa. da ya yi game da su Sardauna da Tafawa Bayan da NEPU ta yi matuqar qarfi da Valewa a garin Bichi ranar 2 ga Disamba, tasiri da kuma karvuwa a cikin al’umma, 1982, inda ya ce, Sardauna da Tafawa sai hukumomi su ka fara daqile qarfin Valewa sun mutu sun bar gona xaya da yaxuwarta domin tsoron kada mulki ya gida xaya, sai kuma bashin banki da su suvuce mu su. Don haka sai a ka fara ka karva, don su yi noma. hana su takara ta kowacce kujera ta hanyar tsoratar da su da azabtar da su Za mu cigaba a makon gobe. da kuma bi ta hannun iyayensu, domin iyayensu su hana su yin takara. Ado Musa ya rubuto ne daga Unguwar Waqoqin zambo masu hikima da raza Qaura Goje a birnin Kano. Za a iya samun zuqata da a ka ringa rerawa a tsakanin sa a wannan lamba: 08069186916.


3

A Yau Lahadi 15 Ga Afrilu, 2018 (28 Ga Rajab, 1439)

ra’ayinmu

Sunayen Verayen Gwamnati: Share

Fagen Siyasar 2019

A

kwanakin baya ne babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya, PDP, ta bugi qirji ta qalubalanci jam’iyyar mai mulkin qasar, APC, da cewa, idan ta isa ta fitar da jerin sunayen verayen da su ka sace kuxaxen gwamnati, musamman a zamanin da ita PDP xin ke riqe da madafun ikon qasar. Ita kuwa APC ba ta yi qasa a gwiwa ba, sai ta biye wa PDP xin, ta fitar da jerin sunayen wasu ’yan siyasa da a ke tuhuma da laifukan sace-sacen kuxaxen gwamnati a lokacin da a ka damqa mu su amanar ’yan qasa. Tabbas jerin sunayen, waxanda ministan yaxa labarai Mista Lai Mohammed ya fitar a lokuta mabambanta, sunaye ne na ’yan siyasar da ke fuskantar qalubalen tuhuma a gaban kotuna dabandaban ko hukumomin yaqi da cin hanci da rashawa na qasar, ICPC da EFCC ko kuma hukumar kula da xa’ar ma’aikata ta Nijeriya. A wannan kam bau qarya, babu sharri, to amma fa yawancinsu har kawo yanzu gwamnatin ta APC ba ta iya yin nasarar kama su da laifi a gaban kotu ba, ballantana a hukunta su. Bugu da qari, babban abin lura shi ne babu ’yan APC ko qwaya xaya, waxanda a baya su ke gwamnatin PDP, amma su ka yi tsallen baxake su ka dawo APC xin ba, bayan da su ka raba hanya da tsohuwar gwamnatin ta APC. Abin nufi a nan shi ne, maimakon gwamnatin APC ta fitar fa jerin sunayen duk waxanda a ke zargi da sace dukiyar al’ummar qasa a lokacin na PDP ba tare da warewa ko la’akari da waxanda su ka fice daga PDP xin su ka dawo APC ba, a’a, sai gwamnatin ta fitar da zallar waxanda har yanzu su ke cikin PDP kaxai; sauran kuwa da alama sun sha kenan, domin ba sa cikin waxanda za a yiwa terere. Daga dukkan alamu, haqiqa wannan salon ba komai ba ne face tabbatuwar sharar fage ga siyasar 2019, lokacin da za a gudanar da manyan zavukan qasar. Ita kanta PDP ta yi tsaurin kai da yawa da ita fitowa ta murje idanunta a gaban ’yan Nijeriya har ta qalubalanci APC a kan ta idan ta isa ta fitar jerin sunayen waxanda ta ke zargi da kasancewa

manyan veraye a lokacin baya. Kada manta, dukkan varnar da ta faru a gwamnatin baya, ta faru ne fa a qarqashin gwamnatin PDP, wacce ita ce mulki qasar tun daga lokacin da Nijeriya ta dawo mulkin farar hula, bayan da soja ya miqa mulki ya koma bakin aikin da kundin tsarin mulki ya

tanadar ma sa na tsaron qasa. Shekaru 16 PDP ta yi ta na riqe da madafun iko tun daga 1999 har zuwa 2015, inda ta yi faxuwar baqar tasa a babban zaven shekarar, wanda wannan shi ne faxuwar zave irinsa na farko a tarihin siyasar qasar, domin a lokacin ne shugaban

EDITA Nasir S. Gwangwazo

MATAIMAKIN SHUGABA (NA MUSAMMAN) Christian Ochiama DARAKTAN SASHE Mubarak Umar

RUKUNIN KAMFANONIN LEADERSHIP SHUGABA Sam Nda-Isaiah

BABBAN MANAJAN DARAKTA Abdul Gombe BABBAN MANAJAN DARAKTAN KADARORI David Chinda MANYAN DARAKTOCIN KAMFANI Dele Fanimo Felicia Ogbonlaiye DARAKTAN KULA DA MA’AIKATA Solomon Nda-Isaiah DARAKTAN KULA DA KADARORIN KAMFANI Zipporah D. Tanko MANYAN MANAJOJI Ibrahim Halilu Femi Adekunle Ebriku John

manufarmu

LEADERSHIP A Yau jarida ce da ake bugawa a Abuja. Ta yi tsayuwar daka wajen tabbatar da shugabanci da wakilci nagari. Jaridar za ta ci gaba da kare muradun al’umma, ba kare ra’ayi da muradun mahukuntanta kaxai ba. Da waxannan qudirorin ne muke fatan jama’a za su xora mu kan Mizani. Haka kuma duk ra’ayoyin masu karatu da muke bugawa, ba manufar kamfanin LEADERSHIP ba ne, ra’ayin masu karatun ne. Sai dai, ba za mu tava mantawa da dalilin wanzuwarmu a doron qasa ba, wato: Don Allah Da Kishin Qasa!

qasa mai ci ya faxi a zavi yayin da ya ke yunqurin yin tazarce a karo na biyu. To, amma a zahirin gaskiya za a iya cewa, talakan Nijeriya ba fitar da jerin sunaye ya ke buqata ba; abinda ya fi buqata shi ne a hukunta waxanda su ka aikata laifukan a cikin shekaru ukun nan da APC ta amshe ragamar mulkin qasar, sannan kuma a dakatar da irin wannan ha’incin ya tsaya cak! Sai dai kuma wani abin takaici shi ne, ko a cikin gwamnatin ta APC an samu irin wannan matsalar, inda a ke zargin wasu manyan jami’an gwamnatin da aikata irin wannan mummunar xabi’a, amma kuma APC xin sai ta yi murqisisi ta qi saka sunayensu a jerin sunayen verayen na na lalitar gwamnatin. To, qarara hakan na nufin cewa, an shiga fagen wasan siyasar 2019 kenan, inda za a cigaba da musayar yawun da ya wuce haka a nan gaba. Ba zai zama abin mamaki ba, idan PDP ita ma ta fitar da nata jerin sunayen, wanda babu tantama za ta kwaye bayan ’yan APC ne, domin ta xauki fansa kan kwance ma ta zani a kasuwa da APC ke shirin aikatawa a yanzu da sunan fitar da jerin sunayen waxanda a ke zargi da aikata hali ko samartakar vera a gwamnatin Nijeriya. Wannan zai iya buxe qofar da ita kuma APC za ta iya mayar da martani ta hanyar sauya wani salon na siyasa, la’alla ma za ta iya yin barazanar kamawa da garqame wasu ’yan siyasar ta PDP, don rufe bakunansu, kamar yadda ita ma PDP xin ta yi aikata hakan a baya, inda ya riqa yin amfani da musamman EFCC wajen yunqurin hana wasu ’yan adawa takara, la’alla ko da sunans ne dai ya vaci ko kuma ta hana su sakat har zuwa lokacin gudanar da manyan zavukan, wanda a sannan kuma lokaci ya qure mu su na dawowa su gyara qimarsu a idanun masu kaxa quri’a. To, ko ma dai mene ne zai faru, a fili ta ke cewa, an gama share fagen siyasar 2019. Shi xan tsako mai rabon ganin baxi, ko a na muzuru ko a na shaho, sai ya gani!!!


4

A Yau LAHADI 15.04.2018

leadershipayaulahadi@yahoo.com

Xan Sanda A Azare Ya Yi Qarar Budurwa Don Ta Qi Auren Sa Daga Muazu Hardawa, Bauchi

Wani xan sanda da ke aiki a ofishin ’yan sanda na garin Azare da ke cikin jihar Bauchi ya rattava wata budurwa mai suna Hauwa Gixaxo a gaban kotu tare da mahaifanta, saboda ta qi amincewa ta aure shi, domin abin da ta kira barazanar cin zarafinta da na iyayenta da ’yan uwanta da ya fara yi tun kafin ya aure ta. Xan sandan mai suna Mustapha Ado ya yi qarar budurwarsa mai suna Hauwa Gixaxo Azare wacce takardar sammacin da a ka tura gare ta ke nuna a na tuhumarta da zamba cikin aminci da aikata manyan laifuka da a ke kira ‘criminal charge’ tare kuma da kauce wa gaskiya da cutar da wanda ya yi qara. Bayan haka shi ma mahaifinta mai suna Mohammed Gixaxo an tuhume shi da aikata zamba cikin aminci da kaucewa

gaskiya da kuma cuta. Yayin da mahaifiyar mai suna Habiba Gixaxo ita ma sammacin ta ya nuna a na tuhumar ta da cuta da zamba cikin aminci da kauce wa gaskiya, wanda ya ci karo da doka ta 125 da 176 da kuma doka ta 95 cikin kundin tsarin mulki. An fara sauraron qarar ranar Litinin da ta wuce a babbar kotun majistare ta biyu da ke garin Azare, inda a ka ba da umarnin a tsare waxanda a ke qara, wato budurwar da iyayenta, lokacin da su ka halarci kotun, amma daga baya alqalin ya duba irin cajin da a ka yi mu su akwai gyara a kai. Don haka ya bayar da umarnin a ba da belin su, inda ya ce a dawo ranar Litinin, don cigaba da sauraron qarar wacce ta xauki hankalin kafafen yaxa labarai su ka ziyarci garin na Azare, amma kuma su ka iske har an bayar da belin mutanen.

Cikin hirar wakilinmu da xaya daga cikin ’yan uwa da su ka tsaya wa budurwar da iyayenta mai suna Malam Abubakar Usman ya bayyana cewa, ya zamo wajibi su kawo mu su xauki, saboda ganin yadda xan sandan mai suna Mustapha Ado ya qudiri aniyar cin zarafin waxanda ya ke qarar, inda ya bayyana cewa, ya nemi Hauwa Gixaxo da aure, amma sai ta fahimci shi mutum ne mai wulaqanci, saboda akwai lokacin da ya zo har gidan iyayenta da ankwa a hannunsa ya riqa sanya wa hannun yayyenta da qannenta ya na kuncewa tare da barazanar cewa matuqar ba ta aure shi ba, duk sai ya yi dalilin da za a sa wa mutanen gidansu ankwa a xaure su a gidan yari. Ganin haka ne ya sa ta ce ba za ta aure shi ba, don ya fara noma da kisan yabanya. Yayin da shi kuma xan sanda Mustapha Ado ya ji haka sai ya lissafa ma ta kuxi kusan

Naira 200,000 da cewa wannan abin da ya kashe a kanta tun daga kuxin hira da wasu kyaututtuka da ya ba ta. Don haka dole ta biya shi. Cikin kuxin akwai na wanke kai da ya ba ta, don ta yi kitso kusan sau 11 da kuma kuxin kaya da ya haxa na aure ya kawo. Amma da a ka bayyana ma sa cewa, kayansa ya na nan kamar yadda ya kawo, ya karvi abinsa, sai ya ce, shi kuxi za a biya shi, don babu abin da zai yi da kaya, sai ko a biya shi jimlar kuxin da ya sayi kayan. Waxannan su ne kaxan daga cikin dalilan da suka sa ya yi qarar budurwar da iyayenta. Dukkan qoqarin da wakilinmu ya yi wajen neman Mustapha Ado a garin Azare, don jin ta bakinsa har ya bar garin bai samu yin tozali da shi ba. Don haka ya tuntuvi kakakin rundunar ’yan sanda ta jihar Bauchi, Malam Kamal Datti, don jin ta bakinsa game da

ko su na da labarin wannan qara da ma’aikacinsu ya yi, inda ya bayyana cewa, ba wani labari makamancin wannan da ya zo gabansa. Ya qara da cewa, a matsayin Mustapha Ado na mutum a cikin jama’a, idan wani ya tauye ma sa haqqi ya na da ikon neman hukuma ta bi ma sa kadi, amma kuma idan lamarin ya kasance da nufin cin zarafin wani, saboda shi xan sanda ne, idan sun ga an yi mu su abinda bai dace ba, matuqar lamarin ya zo gabansu, dole za su zuba ido, kuma su ma su na iya kai qara gaban kotu, don a bi mu su kadi idan har a ka yi wani hukunci da ba su aminta da shi ba lokacin shari’ar. Kamal Datti ya bayyana cewa, hukumar ’yan sanda ba za ta zuba ido wani mutum, don ya na taqamar ya na aiki tare da su, ya tauye haqqin wani mutum ko ya ci zarafinsa ba tare da doka ta yi aiki a kansa ba.

• Samarin Ahlul Faidhati a kan hanyar zuwa filin tarin Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass da aka gudanar ranar Asabar a Kaduna

’Yan Matan Chibok Sun Cika Shekara Huxu Da Sacewa Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja

Ranar 14 ga Afrilun 2014 rana ce wacce ta shiga tarihin Nijeriya da duniya bakixaya, domin a wannan rana ce ’yan qungiyar Boko

Haram su ka sace ’yan matan makarantar sakandare a garin Chibok guda 276. A jiya Asabar, 14 ga Afrilu, 2019, ne su ka shekara huxu cif da sacewa kenan. Iyaye, ’yan uwa da abokan

arzikin waxannan ’yan mata ba za su tava manta wa da wannan fargaba da su ka shiga ba shekaru huxu da su ka wuce, inda duniya ta xauka da kiraye-kirayen dawo da su.

Yanzu haka dai mafi yawan ’yan matan sun dawo, inda xan jarida mafi kusa da ’yan matan Chibok, Muhammad Salqida, ya bayyana cewa, saura 15 kacal a cikinsu, waxnda sun

riga sun zama ’yan qungiyar ta Boko Haram kuma ba su da niyyar dawowa gaban iyayensu. Salqida ya bayyana haka ne a jiya ta hanyar aike wa da saqon Tuwita.


Babban Labari 2019: Manyan Qalubale Bakwai A Yau LAHADI 15.04.2018

5

Da Ke Gaban Buhari

A ranar Litinin, 9 ga Afrilu, 2018, ne shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana wa taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyarsa ta APC cewa, zai nemi yin tazarce a karo na biyu. Wannan sanarwar da shugaban ya bayar ta kawo qarshen duk wani shakku da kokwanto kan yiwuwar tsayawar takarar tasa a babban zaven qasar da za a gudanar a shekara mai zuwa ta 2019. Don haka masu goyon bayansa sai su bazama share ma sa hanya, yayin da masu yunqurin hana shi zarcewa, su kuma sai su bazama wajen yi ma sa hayaqin ramin gafiya, don ya fice daga fadar shugabar qasar a 2019, sannan su shiga aikin jefa ma sa qayoyi da qaiqayi a kan hanyar tasa ta sake shiga fadar. A kan hakan, Editan LEADERSHIP A YAU LAHADI, NASIR S. GWANGWAZO, ya yi nazari kan wasu manyan qalubalen guda bakwai da ke gaban Shugaba Buhari a yunqurinsa na fatan yin tazarce: 1. Fatara Da Talauci Matsalar tsanantar quncin aljihu da tsadar rayuwa da talakan Nijeriya ke fama da ita tun bayan kafuwar gwamnatin APC a qarqashin jagorancin Shugaba Buhari, abu ne da zai yi matuqar tasiri wajen yaqin neman zave daga yanzu zuwa 2019. Tabbas ’yan adawa za su iya yin amfani da wannan fatara da talauci da mafi yawan ’yan qasar ke kuka da su wajen neman quri’arsu, don ganin sun qi yarda su sake kaxa wa APC quri’unsu. Don haka Buhari ya na buqatar ya yi wani abu kan hakan tun kafin lokaci ya qure ma sa. 2. Kashe-Kashe Da Satar Mutane Za a iya cewa, gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi rawar gani wajen kassara tasirin qungiyar Boko Haram, wacce ta fi addabar yankin Arewa maso Gabas kuma ta zamo barazana ga ilahirin tsaron qasa a lokacin gwamnatin baya ta PDP a qarqashin Goodluck Ebele Jonathan, to amma kashe-kashe da satar mutane da su ka yawaita tun bayan kafuwar gwamnatin APC a Nijeriya wani abu ne wanda zai iya raunana karsashi da kwarjinin Buhari a lokacin yaqin neman zave mai gabatowa. 3. Rikicin Cikin Gida Irin rigingimun cikin gida da a ke fama da su a cikin jam’iyyar APC, wani abu ne da ka iya tasiri wajen kawo cikas ga Shugaba Buhari a babban zaven 2019 mai qaratowa. A jihohi da dama a na fama da irin waxannan matsaloli, kamar Zamfara, Kano Kaduna, waxanda kuma abin damwar shi ne yanki ne wanda shugaban qasar ya fito, inda hakan ke nuni da cewa,

idan wasu su ka valle ma sa a can, to zai iya samun qarancin quri’a kenan a yankin da ya fi qarfi. Kada manta, ba a waxancan jihohi kaxai a ke yin irin wannan dambarwar ba. Baya ga wannan rigima kuma, ga rikicin da ke tsakanin jagoran jam’iyyar APC, Bola Tinubu da shugaban jam’iyyar na qasa, Cif Oyegun. Shi ma wannan riki na iya taka muhimmiyar rawa wajen kawo wa shugaban cikas. Sannan kuma ga takun saqar da ke faruwa tsakanin ita kanta gwamnatin APC xin da ’ya’yanta da ke shugabantar majalisun dokoki na qasa, wato Bukola Saraki da Yakubu Dogara. Su kansu zavukan fitar da gwani da APC za ta zo ta gudanar, don tsayar da waxanda za su yi ma ta takara a matakai dabandaban, wani abu ne wanda idan ba a yi taka-tsantsan ba, zai iya zama ya rura wutar fitina a cikinta, wacce ka iya zama qalubale ga nasarar Buhari a babban zaven 2019. 4. Majalisar Dokoki Ba shugabannin majalisar dokoki na qasa, Bukola Saraki da Yakubu Dogara, ne kawai matsalar Shugaba Muhammadu Buhari a zaven 2019 ba, a’a, hatta su kansu mafi rinjayen ’yan majalisar kama daga sanatoci zuwa wakilai waxanda ya kasance Buhari ba shi ikon sarrafa su yadda ya ke so a siyasance, ciki kuwa har da na jam’iyyarsa ta APC, wani abu wanda ka iya zame ma sa qalubale a 2019. Tun yanzu sun fara nuna ma sa, saboda ganin yadda su ka taru su ke son sauya jaddawalin zaven, inda su ke so a fara da nasu, sannan a yi na Buhari a qarshe. Da yawan manazarta su na zargin cewa, turin-je-ka-mutu su ke son yi ma sa.

• Shugaban Qasa Muhammadu Buhari

5. Na Hannun Daman Buhari A gaskiyar Allah yawancin na hannun dama da makusantan Shugaba Muhammadu Buhari da ke cikin gwamnatinsa ba su yi ma sa aikin da ya kamata a siyasance, musamman a matakai na unguwanni da mazavun da ke faxin qasar. Mafi rinjayensu a na zargin su da yin ‘qabalu’. Don haka ba ma sa so su riqa haxuwa da mabiya, sannan kuma ba sa yiwa shugaban aikin da ya kamata a kafafen yaxa labarai da sauran majalisu na sadarwa. Mafi yawansu ma a yanzu jira su ke shi shugaban ya zo ya yi mu su kamfen, maimakon su riqa taimaka ma sa yadda ya kamata, kasancewar a yanzu harkokin mulki sun yi ma sa yawa. Hatta mai xakinsa, Aisha Buhari, ta fito fili ta bayyana qorafinta kan hakan, amma har kawo yanzu babu wani abu da ya sauya. Wannan na iya zama babban qalubale a yunqurin Shugaba Buhari na yin tazarce a 2019, domin za a iya wayar gari mutane na valle wa daga tafiyar har a rasa ta inda za a bi a shawo kansu, domin na hannun damansa sun riga sun gama kai su bango. 6. Farfaxowar PDP Idan har jam’iyyar PDP ta daidaita sahunta kuma martabarta ta dawo a idanun talakawan Nijeriya, to tabbas ta na duk wata wacce za ta iya dawo wa kan karagar mulkin qasar bisa la’akari da yadda ’yan qasar ke jin-jiki a halin yanzu da APC ke mulki qarqashin

gwamnatin Shugaba Muhammdu Buhari. Masu iya magana su na cewa, xan hakkin da ka raina shi ke tsone ma ka idanu! Idan gwamnatin APC ta cigaba da raina halin da ’yan qasar ke ciki kuma ta cigaba da yin shakulaton vangaro da damuwarsu, tabbas Buhari zai iya shan mamaki a zaven 2019, idan a ka sake PDP ta farfaxo. 7. Vangaranci Kasancewar Nijeriya ta kasu zuwa yankuna daban-daban, waxanda kuma kowanne yanki ya na iya xaukar alqilba guda xaya da ya ke fifitawa a lokacin zaven qasa, wani abu ne wanda zai iya zama qalubale ga tazarcen Shugaba Muhammadu Buhari a 2019. A fili ta ke cewa, yankunan Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu ba su zavi Buhari a 2015 ba kuma daga dukkan alamu ba su da niyya zaven sa a 2019. Bugu da qari, duk da cewa, yankin Kudu maso Yamma sun zave shi a 2015, amma faxuwar jam’iyyarsa ta APC a jihar Ekiti lokacin da a ka gudanar da zaven gwamna, hakan ya na nuni da cewa, idan a ka yi sako-sako da yankin, to fa za su iya kwayewa shugaban baya a 2019. Don haka dole ne sai an yi kwanan zaune a kan yankin. Haka nan yankin Arewa ta Tsakiya ma abar fargaba ce, saboda ganin yadda matsalolin tsaro su ka fara saka manyan yankin su na tunzura jama’a a kan gwamnatin, kamar yadda a ka ji Janar T.Y Xanjuma da Gwamna Ortom na jihar Binuwe su na yi.


6 TALLA

A Yau Lahadi 15 Ga Afrilu, 2018 (28 Ga Rajab, 1439)


A Yau Lahadi 15 Ga Afrilu, 2018 (28 Ga Rajab, 1439)

Burinmu Shi Ne Mu Sauqaqa Muku

Ba a chaj in kuxin on ka cire d i j a h c a a B saqonnin watin waya kuxi daga ak na wasu banku

Da zaran an buxe asusu da mu, za a morewa rashin chaji idan mutum ya cire kuxi a akwatin wasu bankuna, haka kuma ba za a riqa cire kuxin saqonnin waya ba.

Domin cimma nasara a hada-hadar banki, ka yi mu’amala da bankin Sun Trust a Yau Ziyarci: www.suntrustng.com

TALLA 7


8 LABARAI

A Yau Lahadi 15 Ga Afrilu, 2018 (28 Ga Rajab, 1439)

Shekara Takwas Da Rasuwar Limamin Canji: Kishin Kano Ya Sa Rimi Naxa ’Yan Adawa A Gwamnatinsa –Muntari Ishak Daga Mustapha Ibrahim, Kano

Mai bawa gwamnan jihar Kano shawara kan samar da tsaftataccen ruwan sha kuma mai aqidar Santsi na Gidan Limamin Canji, Marigayi Alhaji Abubakar Rimi, wanda Allah ya yi wa rasuwa yau shekaru takwas da su ka wuce, wato 4 ga Afrilu, 2010, Hon Muntari Ishak Yakasai, tsohon shugaban qaramar hukumar Birnin Kano kuma tsohon shugaban qungiyar shugabannin qananan hukumomi (ALGON) na jihar ta Kano, ya bayyana Alhaji Marigayi Rimi a matsayin gwamnan da ya kawo wa jihar da qasa bakixaya cigaba. Hon Ishak Yakasai ya ce, saboda kishin Marigayi (Dr.) Abubakar Rimi ne ya sa bayan an zave shi a matsayin gwamna a 1979 an rantsar da shi, sai ya ce, an gama siyasa sai aiki kawai za a yiwa Kano ba tare da nuna bambancin siyasa, addini ko qabila ba, domin shi gwamna ne na al’ummar Kano bakixaya. Don haka ne da ya zo naxa kwamishinoni ya zavo wanda su ka cancanta su ka qware a jam’iyyarsa ta PRP har ma da

sauran jam’iyyu, waxanda su ka yaqe shi a lokacin yaqin neman zave, inda ya nuna cewa, babu ruwansa da adawarsu; duk wanda ya cancanta Rimi ya naxa shi domin cigaban Kano da qasa bakixaya, sai ya naxa shi, wanda wannan ya sanya ya bar tarihi abin koyi, wanda ba za a tava mantawa da shi ba. Don haka Hon Muntari Ishak ya bayyana gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin gwamnan da ya ke koyi da Marigayi Rimi ta hanyar yin ayyukan makarantu, hanyoyin sifiri, gadodji, asibitoci da dai sauran harkoki na buqasa ilimi, lafiya da kamantansu a cikin birni da yankunan karkara, kamar yadda marigayin ya yi na qirqiro abubuwa masu amfani tun lokacin Kano da Jigawa na haxe. Ya ce, “babu inda ba za ka ga aikin Marigayi Rimi ba, indai ka zaga Kano da Jigawa za ka gani, kamar yadda yanzu Gwamna Ganduje ya zo da harkar Lungu Qalqal Karkara Salama’alaikum.” Haka kuma Muntari Ishak ya bayyana qoqarin Gwamna Ganduje wajen samar da tsaftataccen ruwan sha a birni da

karkara, inda ya ce, tunda a ka ba shi wannan muqami na mai bada shawara ga gwamna, shi da kansa ya ziyarci wuraren tace ruwa kamar kogin watari, Challawa da Gwauran Dutse, inda kuma ya ke ba wa gwamnan shawara a kan abubuwan da ya kamata a harkar samar da ruwa kuma nan take ya ke bada umarni a yi “Ga shi nan yanzu kwalliya ta fara biyan kuxin sabulu; inda ba a samun ruwa a da, yanzu a na samu kuma bada daxewa ba matsalar ruwa da qarancinsa za ta zama tarihi,” a cewar Hon. Ishak Yakasai. Haka kuma dangane da mahawarar zaven shugabannin APC na jam’iyya ya ce, ra’ayin shugaban qasa Muhammadu Buhari a kan a yi zaven, ra’ayin Gwamna Ganduje ne kuma shi ne ra’ayinsu su da su ke tare da gwamnan a matsayinsa na jagoran APC na jahar Kano. Hausawa sun ce, waiwaye adon tafiya. Idan dai za a iya tunawa, a na yin taron tunawa da Marigayi Rimi duk shekara ne qarqashin jagorancin qungiyar tunawa da Marigayi Rimi, wacce Hon Alhaji Sani Qwalli ke jagoranta da goyan bayan

•Marigayi Abubakar Rimi

xaukacin masoya Rimi ’Yan Santsi na haqiqa kamar irinsu Umar Liman Xanfulani da irinsu

Gwamma ’Yarfulani da sauran masoyansa ke Kano da Qasa bakixaya.

Bikin Cikar Sarkin Ningi Shekara 40 Ba A Tava Ganin Kamarsa Ba –Yunusa Ningi Daga Mustapha Ibrahim, Kano

A kwanakin baya ne a ka gudanar da gagarumin bikin taya Mai martaba Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Mohammed Xanyaya, murnar cika shekaru 40 bisa karagar mulkin masarautar. Bikin wanda ya tara manyan sarakuna da qanana daga kowane sashe na qasar, ciki har da Sarkin Kano da Sarkin Musulmi da Alhaji Atiku Abubakar Wazirin Adamawa tsohon mataimakin shugaban qasa da sauran manyan baqi. A saboda haka ne xaya daga cikin yaran Mai martaba Sarkin na Ningi, Alhaji Yusuf Yunusa Xanyaya, ya kira taron manema labarai, inda ya bayyana godiyarsa ga dukkan

mutanen da su ka ziyarci garin na Ningi, domin halartar wannan bikin, sannan ya bayyana cewa, wannan shi ne karon farko da masarautar Ningi ta tara mutanen da ba a tava tara kamarsu ba a tarihin masarautar Ningi. Don haka ya yi fatan zumunci zai cigaba da wanzuwa tsakanin mutanen da su ka ziyarci garin da kuma masarautar, don a samu ciyar da yankin da mutanensa gaba. Alhaji Yusuf Yunusa, Xanburam Ningi, ya bayyana farin cikinsa a madadin dukkan mutanen masarautar Ningi ya qara da cewa, dukkan sarakuna 15 da a ka yi a masarautar Ningi, Sarki Yunusa Mohammed Xanyaya shi ne ya shekara 40 kan gadon sarauta kuma zaman

lafiya da ya ke yi da mutane ya kawo shi wannan lokaci, musamman ganin yadda jama’a su ka halarci wannan taro, bai tava ganin haka ba a Ningi, lamarin da ya bayyana cewa, a matsayin wani babban qalubale ne da zai yi wahala na ko wani sarki a ka naxa a ce an tara mutane kamar na wannan rana. Ya ja hankalin gwamnati kan inganta sarauta a qasar, don babu wanda ya isa ya goge sarauta, domin harka ce ta talakawa, saboda su ne ke kusa da mutane, kuma ba wani abu da za a yi ba tare da sarakuna ba. Ya ce, ko doka a ka kafa, idan ba an bi ta vangaren sarakuna ba, to ba abin da zai isa ga mutane, saboda hatta

mulkin siyasa idan ba an nemi taimakonsu ba, haqiqa babu yadda za a samu kafuwar gwamnati ingantacciya. Saboda haka ya nemi gwamnati da ta duba ta kuma samar da gurbin da ya dace ta sanya sarakuna a ciki, don su cigaba da bayar da irin tasu gudunmawar da ta dace, don a samu cigaban qasa da jama’arta. Alhaji Yunusa Ningi har wa yau ya ja hankalin gwamnatoci a Nijeriya da su riqa neman gudunmawar sarakunan gargajiya, domin a samu ingancin zaman lafiya ta hanyar neman shawararsu, ba sai abu ya kai ga lalacewa ba kafin a nemi tallafinsu ba. Don haka ya qara da cewa, dukkan matsalolin da a ke

fuskanta a Nijeriya, idan har an nemi shawarar sarakuna, dole a samu sassauci daga wasu masifun da ke faruwa. Kuma ya ja hankalin jama’a kan su cigaba da bayar da goyon baya ga hukuma wajen inganta tsaro da zaman lafiya tare da yin addu’ar samun zaman lafiya a wannan qasa. Don haka ya ja hankalin shugabanni kansu himmatu wajen ganin sun taimakawa matasa wajen basu ayyukan yi a ma’aikatu saboda an wayi gari akwai qarancin ma’aikata amma ba a xauka lamarin da ya bayyana cewa ya haifar da lalacewan gine ginen gwamnati, saboda yawancin ma’aikata sun rasu wasu kuma sun bar aiki amma ba a xauki wasu ba.

Abdulsamad Zai Gina Asibiti Mai Gadajen Kwanciya 220 A Kano •Ya Yaba Wa Gwamna Ganduje Da Sarki Sanusi

Daga Mustapha Ibrahim, Kano

Hamshaqin xan kasuwar nan na Afrika kuma haifaffen Kano, wato shugaban kamfani BUA da 9mobile, Alhaji Abdulsamadu Isiyaka Rabi`u, wanda ya yi fice wajen tallafawa tattalin arzikin Nijeriya da kuma al`umma bakixaya,

yanzu haka zai gina wani katafaren asibiti wanda ya qunshi dadajen kwanciya 220 a Kano, wanda kuma a ka qiyasta zai laqwame kuxi zambar Naira biliyan 7.5, inda faxin asibitin ya kai mita 15,000, kamar dai yadda rahotanni su ka tabbatar. Haka kuma a wani labarin daban, Alhaji

Abdulsamadu ya yabawa gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da masarautar Kano a qarqashin jagorancin Mai Martaba Malam Muhammadu Sunusi II a kan qoqarinsu na inganta harkar auratayya da kuma zamantakewar al’ummar Kano da ma Arewa bakixaya.

Ya faxi haka ne a cikin wata hira da ’yan jarida a xakin taro da ke titin Luggard Road a Kano kwanakin baya. Haka kuma ya shawarci al`umma a kan su zama masu ba da haxin kai a kan duk wani abu da shugabanni da masana su ka zo da shi, wanda zai inganta rayuwarsu bakixaya.

• Abdulsamad A Rabi’u


9

A Yau LAHADI 15.04.2018

Jiya Da Yau Adabi/Al’ada/Zamantakewa/Nishaxi

Nazari Kan Asalin Hausa (3) Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN 08060869978 .......................................................................

Da alama dai, magana mafi inganci bisa kwayoyin halittar Hausawa shi ne wanda wasu gungun masana suka gudanar akan Hausawa mazauna Sudan. Da fari, binciken ya nuna cewar kashi 40 na qwayoyin halittun Hausawa da ke zaune a Sudan sunyi dai-dai dana kabilun Sudan xin. (Hassan et al 2008) Akwai kuma makamancin binciken da ya nuna cewa qwayoyin halittar Hausawa ya nuna cewa su ‘yanuwan juna ne da wasu qabilu masu amfani da yaren Nilu mazauna Nigeria, Cameroon, Central Chad da kuma kudancin Sudan. (Toshkoff et al 2009). Binciken ya nuna cewar asalin yaren Hausa, da yarukan waxancan kabilu guda xaya ne saboda alakar yarukan da aka gani su na da shi da juna. Baqaqen fatar Chadi da na Kamaru duk a na tsammanin sun gangara yankin ne shekaru da dama da suka gabata daga daular Sudan. Su kuwa mazauna Sudan, duk da gaurayuwar qwayoyin halittun Larabawa da na sauran qabilu a tattare da su, an gamsu da cewa su jikokin tsoffin baqaqen fata ne na tsohuwar daular nan ta ‘Meroa’ da ta shahara a duniya wadda ta wanzu a Sudan xin. Ta haka, sai a ke hasashen cewa kakannin Hausawa da kakannin Sudawa da kakannin waxancan qabilu mazauna Cameroon da Chadi sun fito ne daga tsatson uba xaya, amma hijirar da ta riqa afkuwa tsakankanin mutanen da shi ne sanadiyar rarrabuwarsu ta yadda yanzu kowa ya yi nesa da kowa. Hasashen kuma na nuna cewar wannan rarrabuwa ta auku aqalla da shekaru dubu biyu baya zuwa sama, tayadda a iya wancan lokacin ne kowacce kabila tayi chakuduwa da sauran kabilu har kashi sittin na kwayoyin halittar su ya sauya, kashi arbain ne kadai zuwa yanzu bai jirwaya ba. Babbar hujjar hakan itace samuwar wasu kabilun daga jikin waxancan na ainihi, tayadda ansan ana xaukar tsawon lokaci kafin faruwar hakan. Sai kuma tsawon zamanin da daular bakaken fatar tayi a raye har kuma ta rushe. Kamar abinda Marubuci Morton H. Fried ya faxa

a littafinsa mai suna ‘The Notion of the Tribe’ cewar akwai kabilu na ainihi (primary tribe), akwai kuma kabilu samammu daga na ainihi (secondary tribe). Don haka idan har kabilun yahudawa guda goma sha biyu sun fita daga jikin Annabi Yakuba A.s (Israel), to muna iya cewa kabilar Annabi yakuba da yarensa shine kabila ta ainihi, samammun kabilun kuwa sune waxanda ‘ya’yansa sha biyu da jikikinsa suka xauka bayan rarrabuwarsu ga wajen zama Kuma ana iya samun kabilu sama da xaya mai amfani da yare xaya, amma dai anfi samun kowacce xlkabila da irin nata yaren gami da xabi’a wanda take samarwa kanta-da-kanta gwargwadon wurin zamanta da avin bukatarta da kuma abubuwa makusanta da take dasu. Sannan tana iya yiwuwa ma, kafin Hausa ta zama Hausa, sai da wasu kabilu suka firfita daga asalin kabilar ta ainihi. Tunda dai zamu gamsu cewa Hausa daga wata kabilar ta cire kanta. Kowa dai ya rike cewar Maguzawa sune asalin Hausawa, har ana kallon kalmar Hausa a matsayin bakuwa. Don haka yadda akayi hasashen alaka ta jini tsakanin kabilun maguzawa, Gwandara, Ngizzim da kuma Bole shima abin nazari ne wajen gane asalin uban jinsi wanda Hausawa suka fito daga gareshi, tunda masana sun nuna cewar kwayoyin halittu gami da yaruka duk sunyi kaman-ce-ceniya da juna. A Littafin tarihin Gwandara da Dr. Silvestri O. Ayihai ya wallafa mai suna ‘The History of Gwandara towns and villages’ ya nuna cewar sai da kabilar Gwandara ta jima tana zagaye-zagaye daga nan zuwa can, suna Farauta karkashin jagorancin shugabansu mai suna Dan Baba sannan suka riski wani waje mai suna Kupai sannan suka fara zama. Daga nan ne sannu a hankali suka samar da masarautar su gagaruma. Mu kuwa anan kasar Hausa, an samu labarin baka cewar asalin Gwandara Hausawa ne da suke zaune a kano, wai lokacin da Musulunci yazo sukace sam Gwanda (suyi) rawa da (suyi) Sallah, don haka suka bar kano zuwa wani wajen da zama. To idan ma wannan labarin na Gwanda-rawa-da sallah bai inganta

ba, wancan binciken na kwayoyin halitta ya isa ya nuna mana cewar zamani mai tsawo daya gabata kabilun biyu sun zauna da juna a matsayin yanuwan juna. Kabilar Ngezim kuwa ance sune asalin wadanda suka soma zama a tsohon birnin Ngazargamu na daular Kanem. Suma dai ance sun warwatsu a wannan yanki da Hausawa suka mamaye ayau, amma dai yankunan Yobe, Borno da Jigawa nan ne tsohon wurin zamansu. Haka ma kabilar Bole, wadda akace suma mafarauta ne waxanda suka mamaye yankunan Bauchi, Gombe, Yobe da kuma Jos. Zuwa yanzu ana ganin kamar sun saki al’adunsu da yarensu sun xauki na

Hausawa. Su kuwa maguzawa ance manoma ne, amma tana iya yiwuwa sun jarraba noma ne sukaga yagi farauta riba don haka suka yadda sana’ar kakannin nasu. To ai waxanda suka fara zama a dutsen dala na garin kano ma ance mafarauta ne.. Wai har taron shiga farauta ma akeyi a bakin dutsen lokaci zuwa lokaci, inda manyan mafarauta ke zuwa daga sassa mabanbanta.. Kenan farauta sana’ar kakannin waxannan alummomin ne baki xaya, don haka suka kasa sakinta, tayadda koda sun zauna a wani wuri na wani lokaci sun jarraba wani abin, da zarar sun tashi daga wurin kanta suke sake komawa.

Arewa HipHop Zaman Lafiya Mu Ke Buqata Don Samun Cigaba A Arewa Hiphop –Sardaunan Sauti Shafi na 22

K ANNY WOOD

Kannywood A Zamanin Afaka… Shafi na 16

Kaucin Kaba

Sarqaqqiya (3) Shafi na 20


A Yau LAHADI 15.04.2018

10

Wa’azin Kirista

Tare Da Fasto Yohanna Y.D. Buru 0806 871 8181 yyohanna@gmail.com

Wa’azin Kirista: Yesu Ne Mai Ceto “Za ta haifi xa; kuma za ka kira sunansa da Yesu; domin shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.” Wurin Karatu: Matta 1:21. Duk mai zunubi ya na da buqatar mai ceto, ko kuwa kowane mai zunubi na da buqatar ceto. Littafi mai tsarki ya qara tabbatar ma na da cewa, dukkan bil adama tun daga Annabi Adamu da Hauwa’u sun yi zunubi ta wurin qarya ko qetare iyakokin Ubangiji Allah (Farawa 3). Littafin mai tsarki ya cigaba da bayyana ma na yadda zunubi ya cigaba da bazuwa a rayuwar mutum tun asalinsa. Littafin Mai tsarki na cewa, “Ubangiji kuma ya ji qamshi mai daxi, Ubangiji kuwa ya ce cikin zuciyarsa, ba ni qara la’anta qasa sabili da mutum; gama tunanin zuciyar mutum mugunta ne tun daga quruciyarsa; ba kuwa za ni sake bugun duniya mai-rai daidai, yadda na rigaya na yi.” (Farawa 8:21). Bisa ga littafin mai tsarki ga abin ya ke cewa, “Gama tunanin zuciyar mutum mugunta ne tun daga quruciyarsa.” To ashe, mutum ba ma ya yi zunubi ba ne, amma ya ma gaji yin zunubi ne daga kakaninsa, Adamu da Hauwa’u. Abin tambaya a nan shi ne, wane ne ya koya wa matashi yin zunubi tun daga quruciya, idan dai ba gado ya yi ba? Idan kuwa mutum ya gaji zunubi ne daga assalinsa, to ashe mutum ko bil adama na da buqatar mai ceto, domin ceton sa. Littafin mai tsarki ta qara ma na da wani tabbaci a kan zunubi da cewa:“Ga shi cikin mugunta aka siffanta ni; cikin zunubi kuma uwata ta xauki cikina.” (Zabura 51:5). Jama’a idan kuwa “cikin zunubi kuma uwata ta xauki cikina,” to ashe, asalin mutum shi mai zunubi ne ko kuwa ya gaje ta ne tun daga xaukar cikinsa. Kuma littafin mai tsarki ya qara tabbatar ma na da cewa , “cikin mugunta a ka siffanta ni.” Amma littafin Mai tsarki ta tabbatar ma na da cewa, an siffanta

Adamu da Hauwa’u a cikin adalci da tsarki. Haka ne Allah ya siffanta Adamu da Hauwa’u, amma bayan da su ka yi zunubi ne, shi ne mugunta ta shigo a duniya har ta kai ga yadda mutum ya fara gadon zunubi ko mugunta daga iyayensa. Annabi Irimiya shi ma ya qara tabbatar ma na da matsayin mutum game da zuciyarsa. Irimiya na cewa, “zuciya ta fi komai rikici, Ciwuka gare ta qwarai irin ta fidda zuciya. Wa zai san ta? Ni ubangiji mai bimbinin zunciya ne; Ina gwada ciki, domin na saka wa kowane mutum bisa ga aikinsa, bisa ga yanayin aikinsa.” (Irimiya 17:9 – 10). To, ga wani tabbaci da Annabi Irimiya ya ba mu bisa ga matsayi rikicin zuciyar bil adama. Irimiya na cewa; “zuciya ta fi komai rikici.” Litaffin Farawa 8:21 ya kuma tabbatar ma na da cewa, wannan zuciyar mutum fa na cike da tunanin mugunta run daga quruciyarsa. Sai kuma Sarki Dauda a cikin Zabura 51:5 ya na cewa, “cikin mugunta ne a ka siffanta ni.” A kuma “cikin zunubi kuma uwata ta xauki cikina.” To tunda ga shi ba mu da ja da littafin mai tsarki, domin kalmar Allah ce, saboda haka dole ne mu yarda da maganarsa, kamar yadda Manzo Bulus ya ruwaito ma na a cikin littafin mai tsarki Romawa 3:23 da cewa, “da shi ke dukkan mutane sun yi zunubi sun kasa kuma ga darajar Allah.” Wannan ita ce qololuwar maganar a kan mutum da zunubi, domin wannan ayar ta qara tabbatar ma na da cewa, dukkan bil adama ne su ka yi zunubi har sun kasa ga darajar ubangiji Allah. To, ashe babu mamaki da ubangiji Allah mai jin qai da rahama Ya “... aiko xan cikin duniya ba domin ya yi ma duniya shari’a ba; amma domin duniya ta tsira ta wurinsa.” (Yohanna 3:17). To, ashe akwai mafita kuma mafitar na daga wurin Allah Ubangiji mai jin qai da rahama ga bil adama ta wurin Yesu Almasihu mai

ceton duniya, kamar yadda wannan aya ta tabbatar ma na. Littafin mai tsarki; Matta 1:21, wato wurin da mu ka xauki karatunmu ya zamar ma na asalin tabbacin da cewa, Yesu shi ne mai ceton duniya. A kuma cikin littafin mai tsarki; Yohanna 3:16, Allah ya tabbatar ma na ta wurin Yesu Almashihu da cewa, ‘Allah Ubangiji ya aiki Yesu Almashihu domin duk wanda ya bada gaskiya gare shi ba zai lallace ba, amma zai sami rai na har abada.’ A cikin Littafin Mai tsarki, Ayukan Manzani 4:12 an qara tabbatar ma na da cewa, ta wurin sunan Yesu ne kaxai da ceto ke samuwa. Mala’ikan ubangiji ya tabbatar ma na a cikin

littafin Matta1:21. A cikin Tsohon Alqawari, Allah Ubangiji ya bada annabce–annabce game da zuwan Yesu Almasihu a matsayin mai ceto kuma dukkan annabcin sun cika a kan shi Yesu Almashihu zai bayyana. Kuma shi ne kaxai ya cika dukkan annabcin har ya gamsar da mutanen da yin imani da shi a duniya cewa, Yesu Almasihu shi ne mai ceton duniya. Wato dukkan wanda ya bada gaskiya a gare shi ba zai lalace ba, amma zai sami tsira, wato rai na har a bada. Allah ya ba mu fahimar maganar Allah, wato maganar ceto domin mu gaskanta a cikin sunan Yesu domin mu sami ceto na har abada. Amin summa amin.


A Yau

11

Lahadi 15 Ga Afrilu, 2018 (28 Ga Rajab, 1439)

KA SAN JIKINKA

Tare da Mustapha Ibrahim Abdullahi 08037183735 musteeibr10@yahoo.com

Tsokar Jikin Mutum (3) Satikan da suka wuce, na xanyi bayani akan tsokokin da suke a sassa daban daban a jikin mutum. A mafi yawan bayanan da nayi, ban tavo tsokar naman dake bayan mutum ba; kuma nayi nazari na fuskanci yin bayanin su ko yaya yake, akwai qaruwa a ciki. Tsokar baya an kasa ta gida biyu: kashi na farko sune na waje, waxanda suka taso daga qahon qashin baya zuwa wuya, da hannaye. Kaso na biyu ya qunshi tsokoki da suke shimfixe a gadon baya. Asalin su ya taso ne tun daga qugu har ya zuwaa tushen wuya da kai. Waxannan tsokoki Aikin su shine daidaita tsayuwa kyam, wanda bature yake kira “posture”. Bugu da qari, suna taimaka wajen tallafawa motsawar qashin baya. Rauni ko ciwo kan shafi waxannan tsokoki a sakamakon xaukar abubuwa masu nayi ta hanyar da bata dace ba. Za ku iya gujewa yiwa waxannan tsokoki rauni ta hanyar tsugunawa yayin xaukar Abu mai nauyi sosai. za’a a iya sunkuyawa a xauki abu a qasa, amma an gaano cewa; durkusawa ko tsugunawa yafi kubuta daga samun waccan matsalar Kaso na biyu na tsokar baya wanda ya qunshi tsokokin da suke shimfixe a gadon bayan an sake kasa shi gida uku: na farko akwai tsokoki na samasama, akwai na tsakaiya, akwai kuma na can ciki. Waxanda suke a samasaman guda biyu ne: Na farko, yawansu ya kai bakwai kuma sun taso ne daga qahon qashin baya (spinous processes) na wuya gua bakwai. Na biyu kuwa, sun taaso ne daga qahon qasusuwan baya na vangaren wuya guda 7, sun qare a fika-fikan qasuwan baya na vangaren wuyan dai( Kamar yadda zamu gani nan gaba, mafi yawan qasusuwan baya suna da fikafikai, qaho, jiki, da kuma tushe). A ma’ana, aikin da sukeyi shi ne kula da motsawar qasusuwan baya zuwa ga gefen hagu ko dama. •Sai Kuma Waxanda Su Ke A Tsakiya A na kiran su da “erector spinae”, wato masu miqar da qashin baya. Sun taaso ne daga qashin baya da yake a tsakanin qugu guda biyu da

kuma qashin baya da yake wajen xuwawu, sai sukayi sama domin su xafe a jiki qasusuwan haqarqari daga baya( qashin haqarqari kamar kwando yake; akwai a gaba, akwai a baaya. Na qarshe, wato na can ciki suma aiki iri xaya suke yi da waxancan dda na fada. Suna taimakawa wajen miqar da qashin baya, juya shi gefe da gefe, da kuma tanqwara shi yayi sunkuyo. Idan na ce qashin baya, ba wai qashi xaya nake nufi ba, a’a. Ina nufi nufin qasusuwan da suka fara tun daga bayan wuya har ya zuwa qarshe. A dabbobi masu jela, qasusuwan

dake jelar har zuwa qashin baya da wuya da zaku bi asalin su. A dunqule, tsokar naman dake bayan mu, tana taaka muhimmiyar rawa wajen abubuwa da daama kamar zama, tafiya, daukar abu mai nauyi, kwanciya da tashi, tsugunawa, yunquri, da sauran su. Kuma dai waxannan tsokoki na baya suna tabbatar da qasusuwan haqarqari a mazaunin su, da hana su gocewa, da kuma tallafa musu wajen daidaito bisa tsari mai kyau. Shin ko kunsan akwai tsoka guda shida da suke kula da

jujjuyawar iadnun mu? Akwai mai riqe idanu daga sama domin kar su sako-sako suyo qasa ko suyi gefe, Akwai mai tokare ido daga qasa domin kar ya dinga yin can sama ko yayi gefe. Haka kuma ragowar guda huxun sune kamar haka: xaya tana juya ido gefen hagu, xaya tana juya shi gefen dama, xaya tana jan ido qasa idan mutum yana so ya kalli qasa, xayar kuma tana xaga ido sama idan mutum yana so ya kalli sama. Akwai kuma tsokar da ta ke rufe idanu. Ita ma ta sama da ta qasa. Idan mun zo bayani a kan ido, zan faxaxa idan Mai Duka Ya so.


12 TALLA

A Yau Lahadi 15 Ga Afrilu, 2018 (28 Ga Rajab, 1439)


A Yau

Lahadi 15 Ga Afrilu, 2018 (28 Ga Rajab, 1439)

TALLA

Gaba dai! Gaba dai “Super Eagles”

Bankin Zenith na taya ‘yan qwallon Nijeriya “Super Eagles”, murna sakamakon nasarar da suka samu ta kai wa gasar Cin Kofin Duniya wanda za a gudanar a qasar Rasha.

13


14

Sirrin Iyayen Giji…

A Yau LAHADI 15.02.2018 Tare da UMMA SULAIMAN SHU’AIBU ‘Yan Awaki (Aunty Baby)

Anty Baby matar aure ce. Don haka mata zalla (banda maza) za ku iya tura ma ta da tambayoyi ta hanyar imel ko lamba wayar kamar haka: auntybaby790@gmail.com 08028586967

Ya Zan Yi Idan Mijina Ba Ya Iya Biya Min Buqata? ’Yan uwana mata barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan fili namu mai matuqar farin jinni, wato SIRRIN IYAYEN GIJI… a jaridarku ta LEADERSHIP A YAU LAHADI. Kamar yadda ku ka sani, shi wannan shiri a na yin shi ne, don matan aure zalla, domin ba su shawarwari ta kowane vangare na rayuwarsu ta yadda za su samu su gyara zamantakewarsu da mazajensu da mu’amalarsu ta vangaren girki, tsafta, gyaran gida da gyaran jiki, irin abubuwan da su ka kamata mu mata mu dinga ci domin qarin ni’imarmu da gamsuwar mazajenmu da ma duk wani abu da ya shafi rayuwar ’ya mace. Da fatan za ku dinga bibiya ta a cikin wannan shafi. Gurin da na yi kuskure, sai na ce Ina neman afuwar ubangiji da afuwarku, domin ajizanci irin na xan adamtaka, gurin kuma da na yi daidai sai na ce Allah Ya haxa mu a ladan bakixaya. A wannan makon zan amsa tambayoyin da wasu daga cikin masu karatu su ka aiko ne. Bismillah: Tambaya: Assalamu alaikum. Anty Baby, tambayata a nan ita ce, ni mijina ba ya biya min buqata a shimfixa. Ma’ana; ta wajen jima’I; mu na fara saduwa idan ya samu biyan buqatar kansa shikenan sai ya xaga ni ko da kuwa ban ji daxi ba. Ba ruwansa da sha’awar da zan kasance a ciki kuma ba ruwansa da damuwar da zan yi. Shi kansa kawai ya sani. Haka ma gobe idan ya zo zai kuma yi. Abin nan ya na matuqar damu na har na ji na fara tsanar sa a raina. Meye shawararki, Anty Baby? Amsa: ’Yar uwa ya na daga ilimin da ya kamata a dinga sanar da mutanen da su ka mallaki hankalin kansu shi ne ilimin jima’i a Musulunci. Manzon Allah (saw) ya ce, kada xayanku ya afka wa matarsa, kamar yadda jaki ya ke afkawa jaka. Idan xayanku zai je wa iyalinsa, ya kamata ya aika xan aike, wato ya kamata a ce kafin ya kwanta da matarsa su gabatar da duk wani wasa da zai motsa musu sha’awa, domin samun gamsuwar su kansu ma’auratan. Sannan idan mutum ya sadu da matarsa, bai kamata ya yi gaggawar fitar da gabansa daga cikin matucinta ba har sai wannan matar ta sami gamsuwa daga gare shi, saboda wata matar ba ta samun gamsuwa a daidai lokacin da shi mijin ya sami gansuwa, har sai ya jira ita ma matar ta sami tata gamsuwar.

Wani mutumin ba ruwansa; da zarar ya sami gamsuwa da matarsa koda a iya wasan da su ke yi ne, to fa shi ya gama, ba ruwansa da ita. Shi ba abinsa ya yi ma sa zafi. Kun ga wannan shi ne qarshen rashin adalci. Wata matar kuma ta na da doguwar sha’awa, saboda haka, idan mijinta bai yi wasa da ita ba, sannnn bai jira ta samu gamsuwa daga gare shi ba, to maniyyin da ya ke jikinta ba zai sauko ya haxu da nasa ba, sai dai ya tsaya ma ta a mararta. Daga nan kuma sai ciwon mara, sai ciwon ciki, sai ciwon kai, sai warin gaba. Daga nan sai mace ta dinga tsintar kanta da rashun kuzari da rashin walwala. Ta rasa abin da ya ke yi ma ta daxi, kuma wannan ke sa mace ta dinga jin haushin mijin da tsanar mijin. Sai ka ga mace ba ta girmama miji yadda ya kamata. A rasa dalili. Nan kuwa rashin ba ta haqqinta a shimfixa ne ya jawo ma sa. Sannan ya kamata mu sani cewar mata kala-kala ne kamar yadda maza su ke kala-kala. Akwai mai qarfin sha’awa, wacce idan ba ta sami daidai ita ba, akwai damuwa. Sai dai ka ga auren ya na kai kawo. Qarshe dai sai an rabu hankalinta zai kwanta. Ba yin ta ba ne; haka Allah Ya yi ta. Haka su ma mazan, wani idan ya sami wata matar, da kanta za ta gudu. A-yi-a-yi ta dawo, ba za ta dawo ba, amma wata ta na qoqari ta sanar da ’yan gidansu cewar ya fi qarfinta. Shawara ga mata da mazan

da ba sa iya biya wa junan buqata; su sani ba sai ta kai su ga rabuwa ba. Idan ka san ba ka da juriyar da za ka iya biya wa matar ka buqata a shimfixa ba, to ka dinga wasanni da ita sosai kafin ka shige ta, kuma ka tabbatar ka gane guraren da idan ka tattava ma ta ta ke jin daxi sosai yadda kafin ku zo saduwa ka gama tayar ma ta da sha’awarta, ta fara jin daxi sosai. Ka ga ka na shigar ta, kafin ka biya buqatarka, ta gama jin daxinta. Za ka ji ta sharkaf; komai ya yi daidai. Shawara ta biyu; ka kasance mai neman maganin qarin qarfin mazakuta da xarin kuzari yadda matar taka za ta ji ka gagau. Uwar gida idan mijinki ya na fama da rashin qarfin mazakuta ko ba ya biya miki buqatarki a shimfixa sai ki yi ma sa wannan haxin, ki samu: Baqin gagai Jan gagai Namijin goro Tsintsiyar maza Tatarixa ’Ya’yan Dabino Citta mai yatsu Masoro Barkono A haxe, a dake su a tankaxe luqwui a dinga zuba ma sa a farfesu ko gasashshen nama ya na ci ko ki tafasa ma sa ki sa zuma ya dinga sha kamar shayi. Tambaya: Anty Baby, mene ne maganin warin baki da yadda zan magance shi? Amsa: A abubuwan da ke janyo warin baki akwai rashin wanke baki bayan an ci abinci, domin a yadda a ke so, duk sa’adda mutum ya ci abinci da dare ne ko rana a na buqatar ya wanke bakinsa. Babu shakka duk yadda bakin mutum ya ke da tsafta, to idan ya ci abinci ya bar bakin tsawon awa guda bai wanke ba, to fa qwayoyin cuta ne za su taru, don su cinye guntun abincin ciki. Idan sun gama kuma su fara cin haqora. Daga nan sai bakin mutum ya riqa wari. Sannan da yawa daga cikin mutane sun xauka wanke baki sai an tashi daga barci ne kawai, tunda a lokacin ne ake jin bakin ba daxi. To, bincike ya nuna wanke baki da dare kafin kwanciya ya fi amfani fiye da wankewa da safe.

Shawarar da zan ba ki a nan ita ce, ki nemi man kanumfari ka riqa wanke baki da shi sau uku a rana, haka ma duk lokacin da ki ka ci abinci ki nemi ruwa ki wanke bakinki, sannan ki nemi citta ki riqa tauna ta a lokacin da za ki yi barci tsawon kwana bakwai. Haka kuma ki nemi gawayi ki dandaqa shi, ki haxa shi da gishiri ki riqa wanke baki da shi ko sau biyu a rana. Sannan shi kansa gawayin a na tauna shi da haqori a tsotse ruwansa, don ya na maganin warin baki. Haka a na zuba xanyen wake guda uku a abi a tauna a tsotse ruwan a zubar da tuqar. Hakan ya na maganin warin baki. Bayan nan ki nemi Apple Sider Venger ki riqa shan cokali uku a lokacin da za ki yi bacci. Haka a na watsa kanumfari guda uku ko sama da haka a baki a dinga tsotsa. Ya na kawar da warin baki kuma ya na saka qamshin jiki. In sha Allahu idan ka bi waxannan hanyoyi za ka samu waraka da yardar Allah. ’Yan uwana mata, baki ya na taka rawa wajen mu’amalar soyayya a wajen mijinki; kar ki bari mijinki ya zo zai sumbace ki ya ji bakinki ya yi ba daxi. Ki kasan ce mai kula da bakinki yadda duk sanda angonki ya so ku haxa baki, domin ku ji daxin rayuwa; ya ji daddaxan qamshi na fitowa daga bakinki. Amman idan ki ka bari ya ji banki ya na wari, za ki fita daga ransa. Take sha’awarsa za ta xauke daga kanki, kuma zai ji ya fara tsanar ki. Bari na bar ku haka, sai wani makon idan Allah ya kai mu


A Yau

15

Lahadi 15 Ga Afrilu, 2018 (28 Ga Rajab, 1439)

SHARHIN FINAFINAI

Tare Da: Saddiqa Habib Abba 09097438402 habibsaddiqa@gmail.com

Sharhin Fim Xin ‘Ranar Aurena’ Suna: Ranar Aurena Tsara labari: Yakubu M Kumo Furodusa: Abdul Amart Bada Umarni: Ali Gumzak Kamfani: Abnur Entertainment Jarumai: Ali Nuhu, Adam M Adam, Isa I Isa, Mustapha Musty, Asiya Ahmad, Garzali Miko, Asma’u Sani, Salisu Chali, da Babangida Jalingo. Sharhi: Saddiqa Habib Abba A farkon fim xin an nuna taron bikin Nasir (Ali Nuhu) da Jamila (Asiya Ahmad) a na rawa a na waqa a na gwangwajewa, ango ya na yin waqa da kansa, abokansa su na ta ya shi rawa. Bayan nan an nuna Nasir a gidansa ya tare tare da amaryarsa a daren ranar angoncin, an nuna ya hawo wa kan bene gurin da xakin amaryarsa ya ke ya shiga ya umarce ta da su sauko qasa, domin ta raka shi sallamar abokansa, sannan ta taya shi yi mu su godiya, saboda hidimar biki da su ka sha. Jamila ba ta yi ko musu ba ta tashi ta bi angon nata su ka fito. Sun zo matattakalar bene su na saukowa sai Nasir ya yi tuntuve ya faxi. Jamila ta qwalla kururuwa; abokan su ka ji su ka taho a guje. Su na zuwa su ka tarar Nasir tuntuni ma ya riga ya sume. Su ka xauke shi ranga-ranga su ka ta fi asibiti. Su na zuwa likita ya yi gwaje-gwajensa ya tabbatar mu su da cewar qashin bayansa ya sami matsala. Sakamakon haka daga qugunsa zuwa qasa ya daina aiki. Jamila tare da abokan Nasir suka shiga cikin tashin hankali su ka xauko shi su ka dawo da shi gida. Jamila ta fara jinyar sa tare da qaninta, Habib. Duk abinda ya ke so shi su ke yi ma sa. Ba su tava gazawa ba har tsahon shekara guda, kuma a tsahon shekara gudar nan Jamila ta na fita aiki, domin a yadda a ka nuna tun kafin su yi aure da Nasir ta ke yin aikin. To, wannan aikin da ta ke fita sai Nasir ya fara zargin ta a kan ko ta na kula wani a waje sakamakon shi ba wani amfani ya ke yi ma ta ba tunda ba shi da lafiya. Nasir ya fara canja ma ta ya na ta yi ma ta qananan abubuwa, ta na shanyewa har sai da wataran maigidan Jamila a gurin aiki, wato darata xin kamfaninsu, ya gan ta a hanya za ta tafi gida, ya rage ma ta hanya ya kai ta gida. Daga nan ya shiga cikin gidanta, domin ya duba mijinta. Su na shiga sai Nasir ya qara tabbatar da zargin sa a kan cewa, ta na kula wani. Ya qare mu su ta tas! har ya sake ta. Tun lokacin da Nasir ya saki Jamila rayuwarsa ta faxa cikin garari. Ba shi da mai kulawa da shi, mahaifiyarsa ta kawo ma sa qannensa, mace da namiji, domin su dinga kulawa da shi, amma dukkaninsu su ka gaza; ba sa yi ma sa abinda ya ke so a kuma lokacin

da ya ke so, savanin yadda Jamila da qaninta, Habib, su ke kulawa da shi a baya. Har sai da ta kai mahaifiyarsa ta gaji ta zo ta xauke shi ta mai da shi gidanta ta na cigaba da kulawa da shi. A lokacin Nasir ya fara nadamar rabuwa da Jamila. Ita kuwa Jamila duk da sun rabu, amma ta na cigaba da bibiyar lamarinsa. Ta je gurin likitansa ta tambaye shi ko zai iya yiwuwa a yi ma sa aiki lafiyarsa ta dawo? Likitan ya ce ma ta, a na yi, amma sai a qasar waje. Jamila ta tafi ta je ta sayar da gidanta na gado da wasu kadarorinta ta haxa ta ba wa abokan Nasir Naira milyan 30 su ka fita da Nasir qasar waje a ka yi ma sa aiki ya sami lafiyarsa ba tare ya san wane ne ya biya ba. Sai bayan sun dawo su ke faxa ma sa. A nan ya qara nadamar abinda ya yi ma ta, sannan ya tafi gidansu a kan amai da aurensu. Sai mahaifiyarta fafur ta qi amincewa. Ya tura abokansa, ta qi amincewa, Ya tura mahaifiyarsa, ta qi amincewa, domin mahaifiyar Jamila ta ce ‘yarta ba za ta koma ba tunda ya yi mata mummunan zargi na zina. A haka har mahaifiyar Jamila ta aurar da ita ga wani a cikin zawarawanta. Nasir ya qara shiga cikin matsananciyar damuwa. A ranar da Jamila ta tare da mijinta saboda halin da ta ke ciki na tunanin Nasir ya zama na babu abinda ta ke yi sai kuka. Mijinta ya na ganin haka ya tabbatar cewa zuciyar Jamila ba ta tare da shi. Hakan ta sa a daren ya sauwaqe ma ta. Bayan ta dawo gida, da safe mahaifiyarta ta ci ma ta mutunci ta kuma tabbatar ma ta cewar ba za ta koma gidan Nasir ba. Sai daga baya Habib ya je ya sami Nasir ya ba shi shawara a kan akwai wani kawunsu a Zariya; mahaifiyarta ta na jin maganarsa sosai, idan ya same shi, za ta amince ko da a waya ya yi ma ta magana. Ba da vacin lokaci ba Nasir da Habib su ka xauki hanyar Zaria su ka je su ka sami Kawu. Nasir ya ba shi haquri sosai a kan abinda ya faru. A take Kawu ya kira wo mahaifiyar Jamila a waya ya ba ta umarni, kuma ta amince ba da vacin lokaci ba. Kawu ya kirawo wasu abokan arzikinsa a ka maida auren Nasir da Jamila. Nasir da Habib su ka kama hanya su ka dawo gida, amma har a lokacin mahaifiyar Jamila ta na fushi da Nasir; ba ta goyon bayan komawarta; dole kawai a ka yi ma ta. Sai daga baya Nasir ya ba ta haquri sosai, sannan ta yarda kuma ta haqura ta saka mu su albarka, Nasir ya xauki matarsa su ka ta fi. Abubuwan Birgewa: 1- Waqar fim xin ta yi daxi sosai kuma ta nishaxantar da masu kallo.

2- Jaruman fim xin sun yi qoqari sosai gurin isar da saqon, musamman Asiya a matsayinta na sabuwar jaruma. 3- Daraktan ya yi qoqari gurin gudanar da aikin fim xin. Kurakurai: 1- A cikin fim xin ba a nuna cewar Nasir mawaqi ba ne kuma a cikin tsarin biki wanda su ke faruwa a qasar Hausa ango ba ya zama mawaqi a gurin bikinsa ko da mawaqin ne; abokansa mawaqa su ne za su yi ma sa kara tunda shi ango ne, amma sai ga shi Nasir shi ne mawaqi a gurin bikinsa, amaryarsa tana can kujerar amarya ta na zaune, gurin ango kuwa babu kowa, saboda ya na can filin rawa ya na waqarsa. Wannan abin babu tsari a ciki. Idan so a ke yi lallai sai an yi waqar, za a iya saka wani ya zo a matsayin mawaqi ya hau kan waqar, idan ta dace da lafazan. 2- Akwai gurin da Nasir ya kirawo Jamila su na magana a kan maganar komawarta gidansa, an ji Nasir ya ce, ‘abinda ya sa na kirawo ki, wani waje saboda mu yi magana’, amma mai kallo ya ga ne gurin da Nasir ya kirawo ta ai ba wani waje ba ne, kamar yadda Nasir ya faxa; cikin gidansu ne, amma yadda Nasir ya nuna kamar wani wajen su ka fita daban. 3- Akwai gurin da Nasir ya zo ya na yi wa mahaifiyar Jamila magiya a kan ya na so ta bari matarsa ta koma gidansa, amma sai mai kallo ya ga Nasir a tsaye ya na nuna ta da hannu a matsayinta na surukarsa, sannan ma shi da ya zo roqon ta, ai a tsarin biyyaya da tarbiyya Nasir durqusawa zai yi tunda an nuna shi mutumin kirki ne. Hakan bai kamata ba. 4- Shin Nasir ba shi da wani xan uwan mahaifi ko mahaifiya babba namiji, wanda zai shigo lamarin

aurensa ne? Tunda harka ce ta aure, ai maza yakamata a gani a ciki, ba mata ba, a al’adar Bahaushe, amma sai a ka ga Nasir daga shi sai mahaifiyarsa sai abokai su ne su ke taka rawar ganinsu. 5- Lokacin da a ka ji Kawu ya buga wa mahaifiyar Jamila waya a kan maganar komawarta, sai a ka ji Kawu ya faxa ma ta cewar, ga Nasir kuka ya ke yi tunda ya zo, don a yanzu ma haka kuka ya ke yi, amma mai kallo bai ga Nasir ya na kuka ba a lokacin; idonsa qamas ya ke. A matsayin yadda a ka nuna Kawu a fim xin babban mutum ne tsoho kuma mai faxar gaskiya, bai kamata a ji ya faxi wannan maganar wadda ba haka ta ke ba, wato qarya. 6- Shigar da Jamila ta ke yi ta na fita ba ta kamata ba a matsayinta na matar aure, domin mayafin da ta ke sakawa ma ba shi da bambanci da na budurwa a qasar Hausa. 7- Lokacin da Nasir ya zo tafiya da Jamila bayan an mai da aurensu, sai a ka ji Jamilar ta fito falo ta faxa wa Nasir har a lokacin ummanta fushi ta ke yi, sai a ka ga Nasir ya danna kai ya shiga cikin xakin ummar, domin ya ba ta haquri. A matsayin Nasir na siriki bai kamata a ce ya danna kai xakin kwanan sirikarsa ba, ba tare da wani iso ba, saboda bai san a halin da zai riske ta ba kuma ya kamata a ce akwai alkunya a tsakaninsu har lokacin. Hakan bai kamata ba. Qarqarewa: Fim xin Ranar Aurena ya faxakar kuma ya yi kyau, amma akwai abubuwan da ya kamata a buxa wa mai kallo, sannan kuma fim xin ya yi kama sosai da fitaccen tsohon fim xin Aisha da a ka yi a can shekarun baya ba tare da an sanar da mai kallo cewa shi a ka sake kwaikwaya ba.


16

17

A Yau Lahadi 15 Ga Afrilu, 2018 (28 Ga Rajab, 1439)

KANNYWOOD

Kannywood A Zamanin Afaka… Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja

Naxa Babban Sakataren hukumar tace finafinai ta jihar Kano, Isma’il Na’abba Afakallah, da gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi ya na da dogon tarihi, domin an yi naxin ne ba don cancanta ba, illa don wasu dalilai na siyasa da nufin kyautata masu sana’ar shirin fim a jihar ta Kano. To, amma daga dukkan alamu babban daraktan bai fahimci hikimar da Gwamna Ganduje ya yi ta naxa shi ba, idan a ka yi la’akari da yadda a kullum ya ke raba gari da mafi yawan ’yan fim. Idan dai za a iya tunawa, masu sana’ar shirin fim a jihar sun sha mummunan qalubale da azabtarwa a zamanin tsohuwar gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau lokacin da a ka naxa Abubakar Abdlkarim Rabo a matsayin shugaban hukumar ta tace finafinai ta Kano bayan vullar bidiyon baxala na Hiyana. Irin salon mulkin da Rabo ya gudanar a kujerar shugabancin hukumar ya buxe wagegiyar varaka tsakanin gwamnatin da masu sana’ar, inda shi kansa Afakallah ya na xaya daga cikin waxanda su ka yi ta faman gwagwarmayar qalubalantar salon mulkin na Rabo. To, amma fa kafin zuwan Rabo tabbas gwamnatin Shekarau ta dama da ’yan fim kuma ta taimake su ta hanyoyi da dama. A taqaice ma dai, har kawo yanzu ba a yi wata gwamnati a jihar Kano da ta zuba jarin kuxi a cikin masana’antar Kannywood kamar gwamnatin Shekarau ba,

•Afaka

domin ko a vangaren hukumar A Daidaita Sahu da duk mako sai hukumar ta xauki nauyin shirya fim guda xaya, wanda a ke nuna wa a gidan talabijin, don wayar da kan jama’a, kuma ’yan fim a ke bai wa kwangilar shirya waxannan finafinai. Hakan ya farfaxo da tattalin arzikin masana’antar ya qara ma ta yalwa da walwala. Baya ga wannan kuma, masu sana’ar da dama sun amfana da kwangiloli ko rancen kuxi, don havaka sana’ar. To, amma duk da wannan kyakkyawar alaqa ta taimakon juna da a ke akwai a tsakanin ’yan fim da waccan tsohuwar gwamnati, yayin da Rabo ya fara kama su ya na xaurewa, ya na quntata mu su, sai dangantakar ta yi tsami. Hakan ya bai wa babbar jam’iyyar adawa a jihar lokacin wancan zamani, wato PDP, qarqashin jagorancin Injiya Rabiu Musa Kwankwaso fara zawarcin ’yan fim, domin taya PDP xin yaqin neman zave tare da yi mu su romon bakan cewa, za a kyautata mu su a ba su ’yancinsu, sannan a daina tsangwamar su a jihar matuqar sun taya ’yan adawar yaqin kafa gwamnati. Wannan ya sanya mafi yawan ’yan fim su ka fara yin tururuwa su na mara wa Kwankwaso da tawagarsa baya, saboda neman ’yanci kansu daga mulkin Rabo. Daga nan ’yan fim su ka fara yin waqoqi na sukar gwamnatin da kuma yabon ’yan adawa. A lokacin da wannan dangantaka ta fara yin tsami, gwamnatin Shekarau ba ta iya fahimtar irin illar da Rabo ya yi ma ta ba har sai da zave ya qarato, lokaci ya riga ya qure ma ta. Daga nan wasu daga cikin gwamnatin su ka fara farautar quri’ar ’yan fim a na rarrashin su a kan su zo a sake tafiya tare a na yi mu su romon bakan ba za a sake ba. To, amma idanun mafi yawan ’yan fim ya riga ya rufe, ba za su sake gaskata gwamnatin Shekarau ba, domin a ganinsu ya na ji ya na gani a ke kama su a na xaure su. A haka a ka tafi zaven 2011; Allah Ya amsa bakin ’ya fim, gwamnatin Shekarau ta faxi, a ka sake kafa ta Kwankwaso. Babbar hikimar da Kwankwaso ya yi a dawowarsa mulki karo na biyu shi ne, qin yarda a xauki ’yan fim a matsayin vatattu ko ’yan iska. Qarewa ma umarni ya bayar cewa, su je duk inda su ke so su gudanar da sana’arsu, ciki kuwa har da sabuwar unguwar da ya gina ta rukunin gidan Kwankwasiyya, saboda a cewarsa, fim ma sana’a ce mai muhimmanci. Sannan kuma Gwamna Kwankwaso ya hana malamai yawan aibata ’yan fim da kallon su a matsayin kishiyoyinsu a jihar. Sa’innan a zamaninsa, gwamnatin ba ta xauki mataki na matsin lamba ta hanyar yawan kamawa da xaure masu sana’ar ba. Sai a ka fito da dabara ta jan kunne, idan an yi kuskure tare da yin afuwa. Wannan ya taimaka matuqa gaya wajen rage matsalolin da ke cikin finafainai, domin duk wanda a ka xaga wa qafa, ya kan ji daxi kuma ya kiyaye gaba. Haka a ka yi har zuwa qarshen gwamnatin Kwankwaso, inda a ka zauna da lafiya da ’yan fim ba tare da samun baxala ko rigingim

masu zafi a tsakani ba. Wannan ne dalilin da ya sanya mafi yawan ’yan Kannywood su ka yiwa Kwankwaso kara su ka zavi Ganduje bayan jam’iyyarsa ta tsayar da shi takarar gwamna a matsayinsa na mataimakin Kwankwaso a lokacin. Lokacin da Ganduje ya kafa gwamnati, sai ya yi niyyar kyautata wa masu sana’ar fim fiye da yadda Kwankwaso ya yi tunda da ma a yaqin neman zaven sa ya yi alqawarin cewa, xorawa zai yi daga inda Kwankwaso ya tsaya. Tabbas Gwamna Ganduje ya cika wannan alqawari, domin sai ya xauki kujerar hukumar sukutum ya damqa wa ’yan fim, inda ya xauki xaya daga cikin, wato Afaka, ya naxa shi a matsayin babban sakataren hukumare, wato shugabanta kenan a gwamnatance kuma a gwari-gwari. Haqiqa ba za a ce Afaka bai yi qoqari ba ko kuma bai taka wata rawar gani a hukumar ba ga ’yan fim, to amma salon mulkin Rabo da hukumar tasa ta xauko a qarqashinsa ya na kawo rauni ga hikimar da ta sanya gwamnatin Ganduje ta naxa shi. Misali a nan shi ne, a zamanin Afaka ne a ka buxe ofisoshin hukumar a dukkan qananan hukumomi 44 da ke jihar da nufin bunqasa kasuwancin fim, to amma a zamani nasa ne kasuwar fim ta yi durqushewar da ba ta tava yin makamanciyarta ba, saboda hukumar ta hana yawancin manyan ’yan kasuwar fim sakat, waxanda su ne su ke raba kuxaxe ga furodusoshin da su ke fita su xauki finafinan da a ke kai wa kasuwar. Ga wanda ya san ta kan kasuwancin fim a Kano, zai iya gaya ma ka cewa, wannan dalili kaxai ya isa ya hana a amfana da ofisoshin na qananan hukumomi 44 da a ka sa gwamnati ta kashe maqudan kuxi ta buxe, ta saya mu su baburan aiki, sannan a ka xira wa gwamnatin nauyin biyan su albashi ba gaira babu dalili. Wannan kenan. A zamanin Afaka ne a ka haxe yawancin qungiyoyin fim waje guda a qarqashin uwar qungiyarsu ta MOPPAN da nufin kawo ingantaccen tsari mai xorewa a masana’antar, amma a zamaninsa ne kuma hukumar ta ke farautar shugabannin qungiyoyin a wajen ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro da nufin a kama su a xaure. Ko a makon jiya sai da Afaka ya kai shugabannin qungiyar MOPPAN da na furodusoshi gaban hedikwatar rundunar ’yan sanda ta jihar ya na tuhumar su. Shin mene ne

amfanin aikin da a ka shafe shekaru a na yi na haxe kan qungiyoyin, idan har ba za a bar shugabanninsu su yi aikinsu ba? Wani cigaba da Afaka zai iya yin iqirarin ya kawo shi ne, na shirya semina ta mutum 450, don bunqasa ilimin masu sana’ar da samar mu su da qwarewa. Kuma haqiqa gwamnatin Ganduje ta yi rawar gani, saboda yadda ta fitar maqudan kuxi wajen xaukar nauyin wannan semina. To, amma babban abin takaici shi ne mafi rinjayen waxanda su ka amfana da semina xin ba ainihin ’yan Kannywood ba ne, saboda tsarin da a ka bi wajen xaukar mahalarta semina xin ta hanyar intanet ne. Kowa ya na da damar ya buxe intanet ya latsa ya cike fom ya tura a xauke shi, maimakon a kira qungiyoyin ’yan fim a nemi su bayar da sunayen ma’aikatan da masana’antar za ta fi amfana idan sun kammala semina xin. Wannan dalilim ya sanya a cikin mutane 450 xin nan da su ka halarta, a na jin cewa, ba su kai rabi ba waxanda su ke yin sana’ar fim. Sauran kawai sun halarci semina xin ne sun tafi ba tare da za su iya gwada abinda su ka koya ba. Wannan ba qaramar asara ba ce ga Kannywood kuma ba qaramar asarar kuxi a ka saka gwamnati ta yi ba. A zamanin Afaka ne kuma kullum idan an tashi hira da shi a kafafen yaxa labarai ya ke cewa, yaqi hukumarsa ta ke yi da baxala da munanan xabi’u a cikin finafinan Hausa. To, amma babban abin kunyar shi ne a zamaninsa ne ma’aurata su ka fara koyi da finafinan Hausa su na kashe junansu, kamar yadda shi da kansa ya furta a wata wasiqa da ya tava aike wa shugabannin qungiyoyin masu shirin fim. A lokacin Kwankwaso, wanda ba a yin irin wannan iqirari na vatanci ga ’yan fim ba, ba a tava samun Hausawa su na koyi da finafinan Hausa su ka kashe kawunansu ba, sai a lokacin Afaka ‘sarkin yaqi da baxala’! Daga dukkan alamu dai Afaka bai gane cewa, Ganduje ya naxa shi ne domin ya kyautata wa masu sana’ar shirin fim ba, domin gwamna ya na ganin sun cancanci a saka mu su, amma ba wai don Afaka ya gyara wani abu a tattare da su ba, saboda tare da taimakonsu a ka kafa gwamnatin. To, lallai haqiqa wanda duk a ka kafa abu da shi kuwa, ai don an yarda da nagartarsa ne kenan!

Za mu cigaba insha Allahu!

A zamanin Afaka ne kuma kullum idan an tashi hira da shi a kafafen yaxa labarai ya ke cewa, yaqi hukumarsa ta ke yi da baxala da munanan xabi’u a cikin finafinan Hausa. To, amma babban abin kunyar shi ne a zamaninsa ne ma’aurata su ka fara koyi da finafinan Hausa su na kashe junansu, kamar yadda shi da kansa ya furta a wata wasiqa da ya tava aike wa shugabannin qungiyoyin masu shirin fim •Afaka


18

A Yau Lahadi 15 Ga Afrilu, 2018 (28 Ga Rajab, 1439)

HAYAQI...

Tare da Mu’azu Harxawa 08062333065 hardawamuazu@mail.com

Rukunin Mutane 10 Da Za Su Bijirewa Sake Zaben Buhari A 2019 Sanin kowa ne akwai mutane da dama da suka taimaka wajen zavar shugaban qasa Muhammadu Buhari a shekara ta 2015, kuma duk sun yi wannan zave ne da nufin rayuwar su ta inganta, amma sai aka wayi gari wahalhalu sun shiga cikin rayuwar mutane yadda ake ganin a zave mai zuwa yawanci waxannan mutane ba za su sake zaven gwamnatin APC ba musamman idan har aka ce ta sake tsayar da shugaban qasa Buhari a matsayin xan takarar shugaban qasa. Duk da cewa qaunar Buhari a jinin mutane take amma da dama sun saduda saboda a yanzu an bayyana cewa ya yi alqawurra sun fi xari biyu amma bakwai kacal ya iya cikawa, bayan kuma kowane mabiyin addini ya san cewa alkawari abin tambaya ne tun daga duniya har zuwa lahira. Don haka na zaqulo rukunin mutane goma da na ke ganin a baya sun zavi Buhari amma a zave na gaba 2019 yawanci ba za su kuma maimaita zavar sa ba saboda ganin yadda mutane basu amfana da samun ingancin rayuwa da walwala ba, sai fatara da yunwa da tsadar kaya da talauci da rashin tallafi ko jin qai da sauran matsalolin da suka shafi rashin aikin yi, don haka ga mutane goma da nazari kan su: Rukuni na farko na magoya bayan APC da suka rabu kashi da dama sune a kan gaba wajen gwagwarmayar kawo shugaba Muhammadu Buhari ta hanyar canji dole da yin zaven a kasa a tsare a raka ajira a faxa, sun yi gwagwarmaya ta hanyar tura kuxin kamfen na sayen katin Buhari da yin roqon Allah da tayar da jijjiyar wuya da bijirewa ‘yan PDP masu mulki a wancan lokacin ko da tsiya ko da arziki har sai da haqar su ta cimma ruwa. Amma bayan wannan qoqari wasu a halin yanzu an mayar da su gefe ba a yi da su sun zama ‘yan kallo, musamman ko bugawa shugabannin da suka zava waya suka yi basa xagawa wasu sun rufe layin su wasu kuma ko zuwa mazavunsu basa yi. Waxanda suka samu muqaman siyasa kuma cewa suke yi su ba ‘yan siyasa ba ne, don haka waxanda suka yi wannan gwagwarmaya sun tashi bawan bawan karatun xan kama, don haka a bana zai yi wahala su sake yin irin waccan shahada, sun koma gefe sun zama ‘yan kallo suna jiran lokacin zave ya dawo su da iyalan su xauki fansa. Irin waxannan mutane sun haxa manya da qanana’yan siyasa irin su Injiniya Buba Galadima da su Naja’atu Mohammed da su Alhaji Atiku Abubakar wanda ya koma PDP kuma akwai irinsa masu yawa da sun yi xawainiya wajen xora Buhari a kan mulki amma yanzu sun zamo ‘yan adawa da

suke jiran xaukar fansa nan gaba, duk da cewa sun jima da Buhari suna ziyartar sa ba dare ba rana suna buga masa waya ana nuna masa goyon baya yanzu ya zamo labara kamar almara. Kuma akwai yiwuwar da zarar an fara kamfen idan magoya bayan PDP suka haxa kan su da wasu jam’iyyun adawa suka fito da kuxi tunda duk barazanar cewa su varayi ne da ake musu, har yanzu akwai masu kuxi kuma suna kyauta ta fitar hankali fiye da ‘yan APC, don haka za su jawo mutane da dama saboda sanin kowa ne duk wanda ke yin siyasa baya jiran ladansa a lahira ya fi son ya gani tun yana duniya. Saboda suma masu cewa wasu varayi akwai alamun idan sun sauka suma za a tallata tasu satar ta fi ta mutanen PDP musamman ganin yadda su basa iya kyauta, alhali shi xan Nijeriya ko sata za ka yi ka bashi ba ruwansa shi sanyi ya ke son ji a rayuwa. Saboda talauci ya baibaye xan Nijeriyai ga tunanin ya yi adawa maras amfani kuma lokacin da zai amfana ya zo amma an nuna masa bai yi komai ba sai cin zarafi da jona masa talauci da fatara da yunwa da tsadar abinci da magani da kuxin makarantar yara da sauran wahalhalun rayuwa. Rukuni na biyu sune shugabannin addinin kirista da musulmi waxanda a 2015 sun yi ta kamfe a gidajen su har da wuraren ibada, wasu har sun samu savani da magoya bayan su. Wasu kuma shugabannin PDP na lokacin har kujerun zuwa makka da Jerusalem sun basu da su tare da magoya bayan su don su je su roqawa gwamnatin PDP Allah ta samu nasara. Amma an wayi gari yawanci sun yi ta roqon Allah da ya kawo canji saboda ganin halin da aka shiga na rashin tsaro a wancan lokacin don haka, ko ni a gabana na sha ganin waxanda ke xawafi a qasa mai tsarki ta Makka suna cewa Allah ya ba Buhari mulki duk da cewa alamu na nuna PDP ta tura su, amma an wayi gari yanzu ko kujerar zuwa Abuja ba wanda ke basu wasu sun kasance basu da farcen susa wasu hatta abinci da za su ci babu. Bayan haka kuma hatta ginin masallatai ko cocin da suke ibada an fara cewa za su fara biyan haraji wa gwamnati, bayan haka kuma wasu limaman sun dogara da xan abin da gwamnatin PDP ke ba su na alawus ko domin yin addu’ah wa qasa, amma wannan gwamnati ta Buhari ta ce ba ruwanta, gwamnoni duk sun soke irin wannan taimako. Alamu na nuna wannan gwamnati bata damu da addu’ar su ba alhali lokacin da suke neman mulkin duk sai da suka yi ta bin masallatai da cocin suna neman goyon baya da taimakon addu’ah

•Shugaban Qasa Muhammadu Buhari inda limaman da mabiya suka yi hangen dala ba shiga birni ba da nufin idan gwamnatin Buhari ta kafu za su samu ingancin rayuwa da walwalar addini fiye da tunanin kowa, amma sai wahalar kullum qara nunkuwa ke yi saboda hatta masu ibada a irin waxannan wurare suma samun su ya koma baya wasu sun tsiyace. Akwai misalin da zan iya bayarwa na wani limamin masallaci da ya riqa kamfe wa Buhari a xaya daga kasuwannin cikin garin Bauchi, har ya riqa samun matsala da magoya baya domin yadda ya halasta kamfe kan munbari, amma an wayi gari Allah ya jarrabe shi da karyewar jari a wannan lokaci saboda dama yana samun ciniki da kwangila daga mutanen gwamnatin PDP da ta gabata ne yanzu kuma babu. An wayi gari wata rana za a tsai da sallah ya tsaya zai yi limanci jiri ya xauke shi, zai faxi aka riqe shi ya zauna da aka tambaye shi ya ce yunwa yake ji don kwana biyu bai xora girki a gidansa ba saboda jarinsa ya qare, nan take aka nemi taimako a masallacin aka haxa masa naira dubu 21 aka sayi abinci aka kai gidansa aka bashi sauran canjin ya zuba a aljihu ya murmure na xan lokaci. Rukuni na uku sune “Yan shi’ah almajiran Sheikh Ibrahim Elzakzaky, waxanda kowa ya san suna da yawa a Nijeriya a baya basa zave amma lokacin zaven Buhari ganin yadda wasu manyan ‘yan siyasa suka riqa zuwa markazin su da ke Zariya don yin kamfen, lamarin ya sa sun sassuta ra’ayi wasu sun zavi gwamnatin Buhari da nufin rayuwar su za ta

inganta su samu rangwame kan matsalar da suka fiskanta na faxa da gwamnati a baya musamman ganin yadda lokacin PDP ne a gwamnatin Goodluck Jonathan aka kashe musu mutane sama da talatin ciki har da yaran Elzakzaky guda uku, don haka suma suka himmatu suka ba Muhammadu Buhari goyon baya. Kwasham bayan hawan gwamnatin ba da jimawa ba sai aka samu akasi shugaban sojan Nijeriya Janar Burtai zai wuce ta garin Zariya a daidai lokacin da suke bikin da suka saba na gangami daga ko’ina har aka samu savani suka tare wa soja hanya har ta kai ga sun buxe wuta sun kashe sama da mutane 20 nan take duk magoya bayan Elzakzaky. Madadin hukunci ya tsaya kan waxanda suka jawo fitinar sai ya zarce ga dukkan magoya baya waxanda duk inda aka gan su kan hanyar su ta zuwa Zariya sai a buxe musu wuta ko a kama su kamar yadda aka kashe mataimakin Elzakzaky wato Sheikh Mahmud Turi kan hanyar Kano zuwa Zariya. Ba a tsaya nan ba aka yi dirar mikiya a markazin Husainiyya da ke Zariya soja suka buxe wuta suka kashe mutane sama da dubu, cikin har da yaran Malam guda uku da ke karatu a qasashen waje, shima Ibrahim Elzakzaky da matarsa Zinatu aka raunatu su, aka kuma musu kaca kaca aka tsare su har yau kusan shekaru uku kenan. Hatta markazin aka ruguza aka mai da wajen fili kabjurburan iyayen sa da ke wannan wuri an ce sai da aka tone, aka rusa gidan da masallacin wasu magoya baya an ce da ran su aka yi ta tura su a cikin

Ci gaba daga shafi na

19


19

A Yau Lahadi 15 Ga Afrilu, 2018 (28 Ga Rajab, 1439)

Rukunin Mutane 10 Da Za Su Bijirewa Sake Zaben Buhari A 2019 Ci gaba daga shafi na

18

wuta, lamarin da ko wa mai bautar gunki bai dace a ce gwamnati ta yi wannan hukunci ba tare da an kai mutum kotu ba balle musulmi. Kuma abin mamaki Buhari yana Kaduna wajen taron mawaqa da suka taimaka masa yaqin neman zave amma bai tsawatar an kama mai laifi an gabatar a gaban kotu ba, duk da cewa sai da aka yi kusan kwana giyu ana gewaye da su a cikin gaidan ana tankiya. Daga baya sun garzaya zuwa kotu don neman hakkin su kuma Alkalai sun tabbatar cewa an yi kuskure kan abin da aka musu don haka a saki waxanda aka tsare da malam Ibrahim da matarsa Zinatu a kuma biya su diyya a gina musu inda aka rushe, amma gwamnati ta qi bin umarnin kotu. Duk da irin iqirarin da ‘yan aware na Ibo su Namandi Kanu ke yi na fita daga Nijeriya da wagaza haxin kan qasa a gwagwarmayar neman qasar Biafra, amma gwamnati ta kama su kuma an bayar da belinsu harma sun fice sun bar qasar. Kuma na san cewa ko rantsuwa mutum ya yi ba zai yi kaffara ba ‘yan shi’ar da suka zavi Buhari saboda kishi sun fi mutanen Biafra yawa da magoya bayan Kanu yawa. Sanin kowane waxannan mutane almajirai ne duk da cewa suna da banbancin aqida da mutanen Nijeriya Ahlissunnah, amma kowa ya san ba a musu adalci ba, kuma a kullum suna ta roqon Allah don ganin bayan wannan gwamnati saboda haka zancen su sake zavar Buhari ba ya ajandar su, waxanda basa zave daga cikin su yanzu sun himmatu suna ta karvar katin zave bayan miyagun addu’o’in da suke na ganin an samu rugujewar gwamnatin ta kowane hali, kuma kowa ya sani Allah na amsar addu’ar wanda aka zalunta tun daga duniya kafin a je lahira. Rukunin mutane na huxu sune ‘yan adawa masu sassaucin ra’ayi waxanda suka yi wake wake a lokacin zave a sama su zavi Buhari a zaven gwamna da ’yan majalisu sun zavi magoya bayan su, amma suma basu sha da daxi ba saboda waxanda ke cikin APC suma kuka suke yi basu qoshi ba balle su da suka yi anti party muhajirun da nufin rayuwar su ta inganta, amma yanzu matsaloli sun dabaibaye su wasun su har sun bar siyasar sun koma gefe sun gyara guri’un su suna jiran lokacin zave 2019 su xauki fansa. Rukuni na biyar sune ma’aikatan da suka rasa aikin su ta hanyar kora ko ragewa ko tantancewa ko ganin sun yi yawa ko ba a buqatar su a bakin aiki ko ta hanyar kora da hali su ajiye su kama gaban su da sauran nau’o’in ma’aikata da a halin yanzu suka rasa farcen susa. Bayan haka wasu kuma sun yi ritaya tun lokacin PDP ana biyan su hakkokin su suna jira a zo kan su yanzu kuma an wayi gari a jihohi da qananan hukumomi gwamnoni sun kame kuxin sun qi biyan su hakkokin su, yayin da hatta albashin da suke biya gani suke yi alfarma ce har suna sanya shi cikin nasarorin ayyuka da suka samu. Wasu kuma kamfanoni suke aiki da bankuna amma tsari irin

na jari hujja ya sa an sallame su da nufin ana neman sabbin jini ne. Wasu kamfanonin kuma sun karye saboda hauhawar farashin dala ko bashin banki ya tarnaqe su. Wasu kuma yawan neman kuxin haraji daga hukumomi dabam dabam ya sa sun rufe kamfanonin bayan haka ga uwa uba rashin ciniki saboda qarancin kuxi a hannun mutane, suma irin waxannan mutane na san ba za su sake zavar wannan gwamnati ba kuma suna jiran lokacin zave su xauki fansa ta bijirewa zavar APC. Rukunin mutane na shida sune mazauna kan iyakokin Nijeriya inda ake da boda sama da dubu biyu amma rubutatta sune sama da xari bakwai, kuma kowa ya sani duk wanda ke zaune kan iyaka ko ta Amurka ce abincin sa na wurin ko ta hanyar yin fito ko ta hanyar saye da sayarwa, da kuma yin sumoga ta halartacciyar hanya ko haramtacciya. Tun daga zuwan wannan gwamnati ta rufe kan iyaka an daina walwala ba tare da tunani ko tsara yadda za a tallafi mutanen da ke kan iyaka ba, saboda kar rashi ko talauci ya kai su ga shiga miyagun hanyoyi na ta’addanci don neman abin da za su ci. Madadin a tsara rufe kan iyakar Nijeriya a qarqashin wani shiri na shekaru da za a yi don tabbatar da manufofin, sai aka kawo su kwatsam aka rufe, don haka mazauna kan iyaka musamman matasa wasu sun kama faxa da kwastam wasu kuma sun koma aikata laifu kamar su fashi da makami da garkuwa da mutane da sauran muggan laifuka. Iyayen su da iyalan su kuma suna gani rufe iyakar ya haddasa wannan matsala don haka sun gyara guri’un su duk suna jiran lokacin zave su ramawa kura aniyarta. Rukunin mutane na bakwai sun haxa da ‘yan kasuwar da suka karye a cikin garuruwa manya da qanana waxanda ke ganin qarancin kuxi ya haifar da rashin ciniki yadda tun suna cin riba sun koma cin uwar kuxi har sun koma cin dukiyar iyayen gida da abokan hulxa wasu har sun kai ga sun rufe shagunan sun koma xauke yadda za ka ga mai jarin milyan goma ya sayar da shago bayan ya qare ya koma bulaguro ko yaro ga wani abokin hulxa don ya samu yadda zai ciyar da iyalan sa, duk irin waxannan suna jiran lokacin zave su xauki fansa wajen ganin kowa ya tuna bara bai ji daxin bana ba. Rukunin mutane na takwas sune ‘yan sumoga da a baya ke tafiya da kuxin mota xaya ko biyu zuwa Kwatano su sayo mota su shigo da ita su biya kwastan su nemi abinci, yanzu an rufe shigo da motocin ta kan iyaka sai ta ruwa lamarin da ya sa ‘yan kudu suke walwala amma ‘yan arewa suka koma wahala. Waxannan mutane sun haxa da masu sayo motocin da masu gyara ko fanalbitin ko fenti ko yin fito ko kiliyarans da makamantan su. A yanzu duk sun koma ‘yan kallo yadda gidan sayar da motocin da a baya za ka samu mota xari yanzu daqar ka samu talatin tsoffi, don haka duk masu ci ta wannan hanya basa tare da wannan gwamnati musamman ganin ‘yan arewan sune suka zavi

gwamnatin ba mutanen legas ko Kalaba ko Potakwal ba. An wayi gari mutanen da ke shigo da motoci ta ruwa an ninka kuxin fito da gwamnati ke caji don haka sumoga ta qaru a kan iyaka ta arewa kullum faxa ake yi da jami’an tsaro da kwastam. Haka suma jami’an basa jin daxin irin artabun da ake yi saboda suma uwa ce ta haife su kullum rasa rayukan su suke yi a sanadiyyar xauki ba daxi da ‘yan sumoga saboda rashin iya tsara yadda lamarin zai tafi har mutane su saba an abko da wannan manufa ta rufe kan iyaka ce lokaci guda don haka mutane da dama sun faxa cikin wahala da rashin sanin tudun dafawa suma yanzu sun shirya tsaf don qin zavar wannan gwamnati lokacin zave mai zuwa. Rukunin mutane na tara sune ‘yan kudanci masu qaunar zaman lafiya daganin an samu sauyi a Nijeriya don ingancin rayuwa amma sai suka ga akasin haka, yadda an wayi gari kamar yadda xan uwa ke tallafa wa xan uwa a arewa a kudancin Nijeriya lamarin da kamar wuya ba kowa ke yin hakan ba. Don haka yanzu wahala ta musu yawa, musamman ganin yawanci dama basu yi Buhari ba sai qalilan albarkacin su Rotimi Amaechi da Bola Tinubu da Obasanjo da irin su Rochas Okorocha da su Adam Oshiemole da makamantan su. Yanzu kuma yawanci an raba gari da wasun su wasu kuma ana tafiya tare da su amma tafiyar babu daxi inda suke qorafin sun kashe kuxi don Buhari amma an wayi gari wasu basu samu komai ba in baicin waxanda suke jikin gwamnati ake tafiya da su. Sanin kowane ‘yan kudu dama basu yi Buhari sosai ba an tattaro masu sassaucin ra’ayi ne, saboda hatta Lagos da ake da kusan mutane milyan uku da aka tantance guri’un su dakyar Buhari ya samu guri’a dubu xari shida daga Lagos, don haka a bana yadda suka ji a jikin su talauci ya rungume su harkoki basu garawa yadda suke so da wahala ace sun sake zaven Buhari a 2019 ko da kuwa zai sanya kuros a wuyan sa ya rataya littafin injila yana shiga coci don yin kamfen zai yi wahala ya samu guri’un rabin waxanda suka zave shi a shekarar 2015 . “Yan arewan da ke fama da rikicin makiyaya da manoma da garkuwa da mutane da sauran gyauron boko haram sune gatar Buhari a siyasance ko a zamantakewa balle kuma a fannin addini da kabila duk an wayi gari yawanci ba a ci moriyar canjin ba. Rukunin mutane na goma sune matasa da suka kasa suka tsare suka raka suka jira da tunanin idan gwamnati ta kafu kakar su ta yanke saqa za su samu abin yi za su yi walwala, amma sai aka wayi gari duk inda ka je ofishin jami’an tsaro ko kotu ba wanda za ka samu cikin wahala sai matashi saboda basu da abin yi kuma basu da haquri da talauci don haka nema suke yi su rayu ta kowane hali kuma cikin jin daxi. Lamarin da ya sa zukatan su suka gurvata yayin da wasu vata gari ke amfani da su wajen yin

•Shugaban Qasa Muhammadu Buhari ta’addanci. Wasu kuma da suka yi karatu sun rasa aikin yi yadda an kai matsayin da kusan milyan biyu ke gama NYSC a duk shekara amma ba wani shiri na basu aiki sai N-power wanda har yau bamu tava ganin xan minister ko gwamna ya cika N-powar ba sai aiki a manyan ma’aikatu ko fita qasashen waje. Wani abin takaici kuma shine yadda babban mutum da ke cikin gwamnati da ya motsa sai ya razana matasa da cewa kar su yi karatu da tunanin za a basu aiki don haka su dogara da kan su wajen sana’a. An wayi gari sun koma kan sana’ar tura kurar sayar da kaya ba ciniki suna kasa kaya a bakin hanya ba ciniki, idan sun xauka a kan su suna yawo ‘yan ruwa ruwa na gwamnati sun kame su a zuba kayan a mota su tafi da su duk ciniki da suka yi a kwace haka kayan da kyar za su ceci kan su su kuvuta, anya wannan qasa ana son gaskiya? Wallahi idan amarya bata hau doke ba bai kamata a xora mata dutsen niqa bag ammo ba. Kuma waxannan matasa za su ci gaba da zuba ido suna kallon dukiya na gilmayya a tsakanin wasu mutane qalilan da iyalan su masu mulkin alhali matasan sune suka yi gwagwarmayar kawo wannan gwamnati, daga qarshe ta zamo kura da shan bugu gardi da amshe kuxi. To an ce kowa ya tuna bara bai ji daxin bana ba bayan haka kuma kowa yayi na gari don kansa, talakawa suna nan suna jiran masu jiniya su koma qauyukan su domin neman goyon bayan jama’a don su sake zavar APC, saboda tun daga yanzu sun ga yadda idan sun je taron biki ko xaurin aure a ke bin su da ihu an ace varayi, lamarin ba daxi mutane har sun zamo basa tsoron gwamnati ko masu mulki, waxamda le cewa suna son APC kuma su na yi ne da nufin ko za su samu wani abu, amma idan tafiya ta qare suka ji wayam za su sake layine su bi siyasar masu zub da ruwa don a taka danshi da fatar Allah ya kawo mana mafita cikin wannan lamari yasa a yi zaven a gama lafiya.


20

A Yau

Kaucin Kaba Sha Nema Sarqaqqiya (3) Ga wanda ya yi katarin bibiyarmu tun daga makonni kusan goma da su ka gabata, na tabbata yana iya fahimtar ashe dai gagarumin aiki ne ibadar da yake yi. Ta zama wuri guda da wani mutum irinsa, amma kuma wanda a kusan komai na rayuwa sun sha bamban! Abu mafi rikitarwa kuma shi ne, kai ba ka san cewa bambancin naku ya kai haka ba. Don haka kana tsammanin ya mu’amalance ka da yadda kake mu’amulantarsa. Tafiyarmu daga Iyayen Giji na xaya har zuwa Mai Gida Kan Gida na huxu, babban burinmu kawai zaqulo wasu muhimman muhallai da mu ka sha bamban da juna, musamman a fannin xabi’u. yayin da daga Sarqaqqiya na xaya kuma mu ka fara qarin bayani game da wuraren da bambancin xabi’un yawanci yakan bayuwa ga haddasa rigima a cikin gidajenmu. Wanda ba mamaki wannan ya zama cikamakin wannan gavar. Ba kuma wai don abubuwan ambata a fannin sun tiqe ba. Sai don wataqila zai fi kyau a ce muna tafe muna tattava vangarorin da dama, domin abin ya fi amfanar mutane da dama. Alabasshi idan hali ya yi wani lokaci mu qara waiwayar gavvan. A wannan karo ma akwai abin da ya kamata a ce mu xan duba a gurguje kafin yi wa batun fitar shantun qadangare kamar haka: Maza Su Kan Shiga Kogo, Mata Kuma Su Yawaita Magana. Wani muhimmin fanni kuma da maza da mata suka sha bambam a cikinsa, shi ne yadda sukan fuskanci yanayin vacinrai, ko tashin hankali. Yayin da shi namiji yake samun sauqi idan ya warware matsalarsa, ita kuma mace tana samun sauqi ne idan ta tattauna game da matsalarta. Idan ba mu san yadda abokan zamanmu ke tunkarar matsalolinsu ba, babu abin da zai hana rikici ya ywaita a tsakaninmu. Misali: Murja da Isma’il kowannensu ya dawo gida cikin damuwa, saboda matsalarsa da ya ci karo da ita a waje. Isma’il ya zauna yana karatun jarida, cikin tsammanin ko Allah zai sa ya manta da raxaxin matsalarsa. Ita kuma Murja ta zo ta zauna tana ba shi labarin tata matsalar, da nufin ko idan suka tattauna za ta sami sauqin nata raxaxin damuwar. Don haka, sai Isma’il ya fara jin haushi, cewa Murja ta cika surutu. Domin shi babu abin da

yake buqata a lokacin kamar yin shiru. Yayin da ita kuma Murja wadda babbar buqtarta a tattauna matsalarta, ita ma ta fusata, tana jin haushin an qi a kula ta, ba a damu da matsala ko damuwar da take ciki ba! Irin wannan matsala abu ne da yake faruwa acikin kusan kowanne gida. Kuma warware irin wannan matsalar, ba wai yana da dangantaka ne da qarfin son da ma’aurata suke yi wa junansu ba. Yana da dangantaka ne kawai da yadda suka fahimci bambancin dake tsakanin maza da mata. Idan har Isma’il bai fahimci cewa, mata suna yin magana ne don samun sauqi daga irin tasu matsalar ba. Har abada abin da kawai zai yi ta tunani shi ne, Murja ta cika surutu. Don haka yayin da yake son samun nutsuwa sai ma ya qi shigowa gidan, ya sami wani wurin shaqatawa mai qarancin hayaniya ya yi zamansa. Wataqila sai ta yi barci ya dawo gidan. Kamar haka ne kuma idan ita ma ba ta fahimci cewa maza suna buqatar su yi shiru yayin da suke cikin matsala ba, za ta xauka kawai cewa Isma’il ba ya son magana da ita. Don haka ita ma sai ta ci gaba da ‘yan kumburekumburenta duk lokacin da ya shigo gidan. Wannan yana xaya daga abubuwan da suke sa wasu matan marasa haquri samun wani xan’uwa ko aboki a waje, wanda za su riqa tattauna matsalarsu da shi, da nufin samun wanda zai saurare su, su ji sauqin damuwarsu. Wanda kuma hakan zai iya zama buxe hanyar kowace irin varna. Yanayin Da Mata Su Kan Tsinci Kansu

Yayin Da Mazansu Su Ka Shiga Kogo Yayin da namiji yake cikin tsananin damuwa, bai isa ya iya samun damar ba wa matarsa cikakkiyar kulawar da take buqata ba. Mata sukan tsinci kansu cikin wani mawuyacin hali a irin wannan lokacin. Domin sau da dama, shi ba ma zai faxa mata halin da yake ciki ba, balle ta san cewa yana cikin wani yanayi da ba zai sami damar ba ta waccan kulawar ba. Amma yayin da ya zo ya yi shiru kawai, za ta iya yarda cewa lallai wataqila yana cikin damuwa, amma kuma duk da haka ba za ta dena zargi ko jin haushin cewa ya qi kula ta ba. Idan ba ai sa’a ba sai ka ji ita ma ta kufula: “Mutum kawai sai ya je an vato mar rai a can waje ya zo gina ya ishi mutane da kumburekumbure!” A mafi yawan lokaci, mata ba sa fahimtar yanayin da maza sukan kasance yayin da suke cikin damuwa. Tsammaninsu shi ne, namiji ya zauna ya bayyana musu dukkan matsalolin da yake ciki, kamar yadda sukan yi. Yayin da ya qi yin hakan kuma sai ya zama abin zargi, cewa “Idan ba ka gaya min matsalarka ba kuwa wa za ka gaya wa?” Tsammaninta shi ma yana da wani amini da yake zuwa su tattauna abin da ya dame shi da shi, kamar yadda ita ma take da qawar da suke tattauna tata. Amma shi a wurinsa ya fita waje ya yi wani abin da zai xauke mar hankali ya fi mar wannan tattaunawar. Yanayin Da Maza Sukan Tsinci Kansu Yayin Da Mata Su Ke Magana Yayin da mace ta shiga cikin

Lahadi 15 Ga Afrilu, 2018 (28 Ga Rajab, 1439)

Tare Da Hamza Dawaki 08034753238, hamzadawaki@gmail.com

yanayin damuwa ta fara magana don ganin ta sami sauqin abin da ke damun ta. Shi kuma mijinta sai ya fara damuwa, yana ganin ai wannan qorafe-qorafen da take yi, ba komai ba ne face qoqarin jingina dukkan wani laifin shiga damuwarta a kansa. Bai san cewa tana yin maganganun ne da nufin ta sami sauqin matsalolin dake addabar ta ba. Bai fahimci cewa da zai yi shiru ya nuna ya fahimci abin da take nufi ba, ko da bai buxe ba ki ya ce ta yi haquri ba, da sai ta sauko. Maza suna yin qorafi ne kawai saboda abubuwa guda biyu. Ko dai qoqarin bayyanar da laifi ga wani, ko kuma neman shawara. Shi ya sa duk lokacin da mace ta yi qorafi sai su zata xayan biyun ne. Idan mace ta yi magananu cikin fushi yayin da take bayyana matsalolinta, sai mijinta ya zaci ta na qoqarin xora masa laifi ne. Idan kuma ta yi maganar a sannu, cikin nutsuwa, sai ya xauka neman shawara take yi. Idan Namiji Ya Qi Yin Magana Wani abu da ya ke yi wa mata wahalar fahimta shi ne yadda wataran namiji zai yi shiru, su yi ta magana ba tare da ya tanka ba, domin mata ba su san cewa yayin da namiji ya shiga cikin kogo ba ya son jin magana balle kuma shi ya yi. A tunaninsa yin shirun shi ya fi sauqi a kan duk wata magana da za ta fito daga bakinsa. Abinda shi kuma bai sani ba, a duniyar mata a na yi wa mutum shiru ne kawai idan ba shi da wani muhimmanci a rayuwarka. Ko shakka babu dai, sanin yadda xabi’unmu su ke ya na da matuqar muhimmani wurin kyautata zamantakewarmu.


21

A Yau Lahadi 15 Ga Afrilu, 2018 (28 Ga Rajab, 1439) Tare Da Bilkisu Yusif Ali – 08054137080– bilkisuyusuf64@gmail.com

Daga Na Gaba... Madakin Kano Bello Kano: Gwarzonmu Na Mako An haifi Marigayi Madakin Kano Bello a shekarar 1907 a cikin unguwar Yola da ke tsakiyar birnin Kano. Ya fara karatunsa na elemantare a shekarar 1918 a makarantar Shahuci lokacin makarantar su suka zama xalibai na farko. A shekarar 1921 Marigayi Madakin Kano Bello ya zama shi ne xalibi na farko daga Kano da ya sami gurbin karatu a makarantar horar malamai da ke da ke Katsina. A 1945 ya zama xalibi na farko da ya fita jami’a a qasar London, don yin don yin difloma a tsangayar ilimi da al’adun Afrika.( school of oriental and African studies). A shekarar 1927 Madakin Kano Bello ya fara aiki a matsayin malamin makaranta a makarantar Midil da ke Kano, inda a qarshe har ya zama mataimakin hedimasta a lokacin Alhaji Abubakar Muhammad Gixaxo ya na hedimasta. A shekarar 1932 Madakin Kano Alhaji Bello ya zama an naxa shi hedimasta. Ya riqe wannan matsayi har zuwa shekarar 1945 lokacin da ya tafi Ingila. A shekarar 1946 bayan ya dawo daga Ingila sai a ka yi ma sa jami’i a vangaren ilimi (Education officer, E.O). An xora ma sa alhakin kula da harkar ilimi a masarautar Kano wanda cibiyar jakadanci ta Birtaniya ta wakilta shi (British Council), inda ya zama kansila na farko a jihaår Kano. A shekarar 1947 lokacin da a ka qirqiri Majalisar Dokoki a Najeriya wacce ke Legas, sai jihar Kano ta tura Madaki Bello, don ya wakilce ta. A shekarar 1951 wannan Majalisar Dokokin an samar da wakilcinta a jihohi uku na Nijeriya, sai a ka naxa shi ya zama minista na ayyuka a na jihohin Arewa. Daga baya a shekarar 1952 aka sauya shi zuwa ministan raya karkara da cigaban al’umma. A ranar Talata 23 ga Afrilu, 1952, Sarkin Kano Abdullahi Bayaro ya naxa Bello sarautar Xan Amar hakimin Dawakin Tofa, inda ya shafe shekara shida a kan wannan kujera. A shekarar 1959 likafar Malam Bello

•Madakin Kano, Marigayi Bello Kano

ta kuma cigaba, inda Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya naxa shi matsayin Makaman Kano, amma zai cigaba da zama a matsayin hakimin Dawakin Tofa. Sarkin Kano Marigayi Alhaji Ado Bayaro shi ya qara ciyar da Malam Bello gaba, inda ya gaji mahaifinsa Madakin Kano Shehu. An yi wannan naxin sarautar ne a shekarar 1984, inda ya zama shi ne na 12 a jerin Madaki da a ka a masarautar ta Kano kuma shi ne Babban Xan Majalisar Sarki. Madaki Bello ya shafe shekara uku ya na taimakon Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayaro wajen shugabantar majalisar Sarki. Jami’ar Bayaro ta karrama makaman Kano Bello da digirin girmamawa a vangaren shari’a. An yi bikin ne qarqashin gwamnan Kano na wancan lokaci, Kanar Idris Garba. Lahadi huxu ga Afrilu a shekarar 1987 Allah ya amshi rayuwar Madakin Kano Bello wanda ya shafe shekara 60 ya na bautawa jiharsa da cigabanta. Allah ya jikansa da gafara, amin. Madakin Kano ya bayar da gagarumar gudummawar da tarihi ba zai tava mantawa da shi ba. Don tunawa da shi gwamnati ta sanya sunansa a titin Bello Road, sannan

•Madakin Kano, Marigayi Bello Kano

a qofar shiga makarantar kwalejin Rumfa an sa sunansa. Marigayi Madakin Kano Bello ya rasu ya bar matan aure biyu da qwaraqwarai guda biyu da ’ya’ya 25. Matansa akwai Hajiya Amina, wacce qanwa ce ga tsohon gwamnan Kano, Marigayi Audu Baqo, sai kuma Fulani Maryam, wacce ’ya ce ga Sarkin Kano Muhammad Sunusi I; shaqiqiya ga Ciroman Kano mahaifin Sarkin Kano na yanzu Mai martaba Sarkin Kano na yanzu, Muhammadu Sunusi II. Halayyar Marigayi Madakin Kano Bello Marigayi Madakin Kano ya na daga cikin abin da ya mayar da shi xabi’a a gurinsa shi ne dubiyar marasa lafiya. Kullum sai ya je duba maras lafiya. Haka ta’aziyya ma. Ya qi jinin rashin gaskiya ba ya shiri da duk wanda ya fahimci ba shi da gaskiya. Don haka ma shi halayyarsa ita ce gaskiya da tsayawa kan ta kuma mutum ne kaifi-xaya ba ya cewa, a’a, ya dawo ya ce, ‘eh’. Sannan ya washi sava alqawari da yaudara. Idan ka nemi alfarma ko wani abu, idan har ka cancanta, nan take zai amsa ma ka, amma idan

•Madakin Kano, Marigayi Bello Kano

har ya san ba ka cancanta ba ko kuma ba zai yiwu ba, nan take zai ce ma ka ba zai yi wu ba. Mutum ne da komai zai yi ya na yi ne a tsanake; ba ya gaggawa. Wannan ne ma ta sa ake kiran sa da Mikiya Mai Hangen Nesa. Mun sami qarin bayani wajen ’yar Marigayi Madakin Kano Bello, Hajiya Fulani Ruqayya ( Balaraba) Bello mai xakin Alhaji Abbas Gandi, sakataren kuxi na jam’iyyar APC da ke jihar Sokoto.


A Yau LAHADI

22

15.4.2018

Arewa HipHop

Tare da UMAR MUHSIN CIROMA ‘Smartkid993@gmail.com Instagram: Smartkid.skd_official 08104314052

Zaman Lafiya Mu Ke Buqata Don Samun Cigaba A Arewa Hiphop –Sardaunan Sauti

Fasihin mawaqi USMAN SHU’AIBU, wanda a ka fi sani da Sardaunan Sautin Arewa, ya yi maganganu masu matuqar mahimmanci dangane da abubuwan da ke faruwa yanzu a duniyar mawaqan Hiphop na Arewa, ya kuma ba wa ’yan uwansa mawaqa shawara da su haxa kai, don samun cigaba a waqoqinsu. Ya bayyana hakan ne a hirar da su ka yi da wakilin LEADERSHIP A YAU LAHADI, UMAR MUHSIN CIROMA. Ga yadda hirar ta kasance: To, da farko dai masu karatunmu za su so su san taqaitaccen tarihin rayuwarka? To, ni dai sunana Usman Shu’aibu kuma da Usman nake amfani a waqa, amma wasu su na kira na da Usman Abun Kallo ko Sardaunan Sautin Arewa, kuma ni haifaffen garin Minna ne ta jihar Niger kuma a can na girman na yi karatun firamari da sakandire. Daga nan ne na tafi qasar Malaysia, don karatun digiri. Hakan ne ya sa yanzu kodayaushe Ina can.

ba a san ni a matsayin mawaqi ba, to da damansu idan na yi ma su magana, sai su dinga yi min yawo da hankali kan cewa za su yi, amma sai ka ji su shiru, saboda su na ganin kai me za ka iya yi? Ba su xauki abin da ma’ana ba. Irin waxannan abubuwan su na xaya daga cikin qalubalen da mutun zai dinga fuskanta.

To, me ya ja hankalinka ka tsunduma harkar waqa? Da na ke can vangaren mu Hausawa mu na da yawa, kuma ba Igbo kaxai ba ne da Yarabawa, amma kuma ba a san mu na waqa ba, bayan kuma mu Hausawa mu na da basirar waqoqi sosai. So, sai na fara, na kira furodusana Ozee, ya kira min Mognito da Dj-Ab na sa su a waqata ta farko. Wacce na fara yi ta farko ita ce, Abun Kallo. Mu na zuwa guraren shaqatawa mu na bada waqoqin a qasashen waje a sa a gurin, don dai a san mu sosai.

Yaya yanayin ma’amalarka da sauran mawaqan Hiphop na Arewa? Eh, gaskiya yanzu kam a Arewa na shaqu da wasu kamar su Xdough_Abokina da Morel da su NT4 da dai sauransu. Kusan in ce ma dukkansu mu na mutunci da su kuma abu na haxa mu.

Daga lokacin da ka fara waqa zuwa yanzu ka na da waqoqi kamar nawa? Na sako waqoqi guda biyu; Abun Kallo tare da Ozee Dj-Ab da Magneto, sai kuma na sako Disco tare da shi Ozee da NT4. Ina da waqoqi yanzu a qasa kamar guda tara, amma Ina qoqarin na sake su ne a EP xina na kwanan nan da zan saka “Arewa Check Over” cikin shekarar nan. A ciki na sa kusan duka manya mawaqa na Arewa, don na xaga sunansu a qasashen waje. Waqarka da ka yi Abun Kallo ta samu karvuwa a duniya, musamman a nan Arewa. Ko za mu iya sanin wane irin darussan waqar ke koyarwa? Eh, to ita waqar Abun Kallo ta na nuna wa mutane ko’ina ka ke ko ya ka ke, ka kan ji da kanka, don a cikin waqar za ka ji a na cewa, “we no like rigima, dala mu ke nema.” Magana a ke yi kan yadda za ka cigaba a rayuwa kuma ka zama mai ba wa kanka qarfin gwiwa. Wane irin qalubale ka fuskanta daga lokacin da ka fara waqa kawo yanzu? To, shi da ma harka irin wannan a rayuwar nan bakixaya idan ba ka fuskanci matsaloli irin wannan ba, ba za ka san ina ka dosa ba. Qalubalen da za ka fuskanta su za su sa ka dinga gyara kurakuranka. Wasu lokutan za ka yi waqa, tun kafin ka fitar idan ka samu na kusa da kai, zai ba ka shawarar ba ta yi ba. Sai kuma na biyu, kamar Abun Kallo, waqar da na yi ta farko, ba sai na faxi suna ba, akwai artist xin da na so na sa da dama, amma lokacin kawai an san ni ne a matsayin ‘promoter’

Ka na aiki ne qarqashin wata qungiya ko kuma ka na da qungiyarka mai zaman kanta? Eh, Ina da qungiyar kaina ne; a na kiran ta Exposure Movement. Kamar kamfani ne ya kasu daban-daban; akwai vangaren mawaqa da su irinsu textile da dai sauransu. Don haka ni ne shugaba a vangaren waqa, kuma babban matsugunninmu ya na can Dubai. Shin harkar waqa ne ya mai da kai Malaysia da zama? Ni karatu ne ya kai ni can, amma daga yanayin rayuwar da na ke ciki, tun kafin na koma can ni mutum ne ma sha’awar sauraron waqoqi da dama. Don haka ko da na je can a na fita guraren shaqatawa za mu ga a na ji da Yarabawa, Igbo da dai sauransu, shi ne na ke tunani na ce, to mu me ya sa Hausawa ba za a ji da mu ba? Kawai ni ma na fara waqa, na yi magana da mutanen Exposure Movement, na yi mu su bayani dai da sauransu. Sai su ka ce sun ware min vangaren nishaxi na jagoranta, haka dai. To, ya ka ke qoqari gurin haxa waqa da karatu? To, ai duka abubuwan guda biyu kowanne da lokaci yinsa. Ka ga ita waqa ba abu ba ce da za ka zauna kullun koda yaushe ka yi ta ba. Waqa ko a rana xaya za ka iya haxa waqa. Ni nawa kawai na yi wa mawaqi magana, sannan na yi wa furodusa magana cewa, ga abinda na ke so. Idan a ka haxa mun bit sai na tura wa mawaqi ya xora murya a kai. Ba sai an haxu ba, don ka ga kamar Abun Kallo mun yi waqa tare da DJ Ab, amma har yau ba mu haxu ba. Ka ga dai yadda abin ya ke. Ita waqa ba ma dole sai kun haxu a ke yinta ba, amma wasu lokutan ya na da kyau ku haxu, don shawara da juna.

Ci gaba a shafi na

23


23

A Yau Lahadi 15 Ga Afrilu, 2018 (28 Ga Rajab, 1439)

‘Zaman Lafiya Mu Ke Buqata Don Samun Cigaba A Arewa Hiphop’ Ci gaba daga shafi na

22

Waxanne irin nasarori ka samu daga lokacin da ka fara waqa kawo yanzu? Eh, an samu nasarori sosai, don da na fara sako Abun Kallo a itune ma kaxai na samu kamar Dalla 700 waxanda su ka sayi waqar a yanar gizo, kuma an samu a YNS sosai. Ka ga an kira ni wasanni da dama kamar su Dubai da dai sauran gurare, kuma biya na a ke yi, ba kyauta na ke yi ba, kuma da ma abinda mu ke so kenan a san ka a duniya ko’ina, ba wai na Nijeriya kaxai ba, kuma mu na kan samun abinda a ke so. Mu na kuma cigaba da nuna wa duniya cewa, akwai mawaqa a Arewa masu basira sosai. To, da ka ce YNS, ban sani ko ka na da wata mu’amala da su sosai ko kai ma ka na aiki ne qarqashinsu? A’a, na dai san Dj Ab kuma Ina ga a Arewa ba wanda bai san Dj Ab ba, sannan kuma Ina ga a “Yaran North Side” na san Jigsaw kuma Ina jin waqoqinsu, sannan mu abinda mu ke so, waxanda a ka fara sani Arewa a san su a sauran gurare. Saboda haka ne ya sa na yi wa Ozee kan magana yadda za a yi mu saka Ab a Abun Kallo, sai Ozee ya yi wa Dj Ab magana, sai ya hau waqan Abun Kallo, amma kuma da ma idan na ji waqar mutum, na ji ta yi, na kan nemi mutum na ce ya zo mu yi aiki da sauransu. A cikin manya mawaqan da mu ke da su da wa da wa ku ka tava yin waqa tare? To, a Arewa dai Ina da aiki yanzu da su Morell. Sauran ba zan iya kira ba, amma dai na Morell xin shi ne sabuwar waqar da zan saka kwanan nan, amma dai Ina da waqoqi da manya mawaqa da yawa. Aqalla yanzu ka je gurare kamar nawa wasanni? Eh to, na yi a Dubai kuma ya kamata mu yi a Sudan Karmako Festival da su ka yi a Disambar nan, amma ban samu zuwa ba saboda na yi yarjejeniya da wasu, kuma a nan Nijeriya mun yi a nan Nasarawa Keffi, mun yi a Minna mun yi a Kano, sai kuma Kaduna dai an kawo yarjejeniyar amma bai yi aiki, amma dai har zuwa yanzu a na kawo ma na gayyata kuma idan mu ka sasanta da mutane mu na zuwa.

Ka san ko wane mawaqi ko k u m a mutum da ya shahara a duniya ya na fama da

qalubale a shafukan sada zumunta. Ya ka ke qoqarin ka ga ka faranta wa masoyanka a shafukan sada zumunta? Ai ni da ma mutum ne mai son al’umma. Don haka ka ga Ina da abokai ta ko’ina. A Arewan ma Ina yawo sosai Ina zuwa garuruwa na san mutanen garin na ga halin garin ya ke. Ka san shi shafukan sada zumunta ya na saka ka kusa da masoyanka ba. Dole sai an dinga waya kullum ba, amma kuma hira da sauransu, kuma ni ban da xaga kai haka da sauransu ko ya mutum ya ke mu na mutunci, saboda babu wanda ya san gobe. Ka san a na cewa duka artist su na da xaga kai. To, ba haka ba ne sai ka zo kusa da mutum za ka gane halinsa. To, daga nan zuwa shekaru biyu masu zuwa wane irin dutse ka ke wa Arewa sha’awar ta taka? Eh, da yardar Allah nan da shekara xaya ko biyu sai an fara kai mawaqanmu da ’yan wasan Hausa bakixaya wasanni irin su Amerika da sauran manya qasashe wasa, don yanzu kam Arewa an fara sanin mu ta ko’ina, don da ma ba mu xaukar abinda mahimmanci ba ne,

amma kuma yanzu idan ka lura, ko sauran ’yan Kudun ma nan Arewa su ke zuwa wasanni. Saboda

haka ka ga yanzu mu ma an fara sha’awar jan mu a jiki. Don haka nan da shekara biyu an san mu ta ko’ina insha Allah. Bincike ya nuna cewa akwai matsaloli da ku ke samu tsakaninku manya Arewa Hiphop. Ya ka ke kallon lamarin? Ya na xaya daga cikin ajannda na cewa na ga na janyo duka mawaqa mun haxa kai, don gaskiya ba mu da haxin kai kuma shi ne babban matsalarmu. Kuma ka ga yadda ’yan Kudu su ka fi mu kenan. Don haka ka ga ni abinda na ke yi za ka ga na kawo mawaqa xaya biyu haka mu yi waqa tare, kuma ka san yawan yin aiki tare na kawo kusanci da juna. Amma matsala ai dole a fuskance ta. Ni dai shawarata ita ce, mu cigaba da haquri da juna. Da ma ai dole wani zai fi wani. Wacce irin shawara za ka ba wa matasa masu ra’ayin fara waqar Hiphop? Ka san waqa ba a yi ma ta hanzari. Abua ce da ta ke buqatar natsuwa. Sai ka zauna ka ga a wane vangare ka fi qwarewa. Ka ga kamar ni ban yin waqa cikakke ni kaxai. Na kan kawo mawaqa ne mu yi aikin tare. Ka

ga ni Sardauna ne. Don haka ne zan sa murya ne kawai a waqa a ji muryata. Da an ji kawai an san wanda ya yi waqar. Shikenan, sai sauran mawaqan su xora nasu kalmomin. Ba wai ban iya waqa ba ne ya sa ban yi, a’a, na zavi inda zai fi daidai da ni ne kawai. Amma sai ka ga mutum dare xaya kawai ya bushi iska ya ce, ya zama ‘rapper’ kuma alhalin ba ka iya rapping xin ba. Ka ga kenan ya na kashe wa kansa kasuwa. Ita waqa aba ce wacce sai ka na da baiwarta za ka iya, kuma sai ka nemi shugaba da manya a harkar waxanda ka san sun daxe su na harkar. Wacce i r i n shawara za ka ba wa sauran abokan harkarku na waqa? Abinda mu ke buqata shi ne zaman lafiya. Mu daina jin haushin juna, mu dinga taimakon juna. Ka san da dama abinda ke faruwa kenan; da zarar mutum ya kai wani guri, sai ya ga shi fa shikenan ya daina taimakon kowa. To, don Allah mu dinga taimakon juna, don cigabanmu bakixaya. Wacce mota ka fi so kuma wacce kalar kaya ka fi sha’awar sawa, sannan wane irin abinci ka fi so? Kodayake ban cika hawa mota na ke yi a Nijeriya ba, gaskiya ni masoyin Toyota ne, kaya kuma gaskiya na fi son mai launin ruwan qasa, sannan abinci kuma na fi son sakwara. Duk da dai ni ba gwari ba ne, ni Banufe ne, sannan kuma Ina son tuwan shinkafa. Daga qarshe me za ka ce wa masoyanka? A cigaba da ba mu goyon baya, saboda a san da mu daga Arewa. Kun ga idan mu ka samu karvuwa daga gida ’yan waje ma za su mara ma na baya. Kun san mu mutane ne kamar kowa. Don haka duk inda mu ka yi kuskure a dinga ba mu shawara mu gyara ko da ta shafukan sada zumunta ne, za ku iya samu na a Intagram: mrusman1, Snapchat: Usman_shu’aibu, Twitter: Usman_shu’aibu. To, na gode.


24

ADABI A YAU

A Yau LAHADI 15.04.2018 Tare da Adamu Yusif Indabo 07038339244 ay1indabo@gmail.com

Tsohuwar Taska: Littafin ‘In Da So Da Kauna’ Daga Ado Abubakar Bala

Littafin ‘In Da So Da Qauna’ na Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, an fara wallafa shi a shekarar 1991, wato a yanzu ya na da shekaru 27 da haihuwa kenan. Labarin In Da So Da Kauna labari ne na soyayya a tsakanin Sumayya da Muhammad. Sumayya yarinya ce kyakkyawa `yar gidan masu hannu da shuni. An yi soyayya irin ta zamanin da, inda Sumayya ta rubuta wa Muhammad wasika a kan irin son da take yi masa, amma da farko Muhammad ya ki, saboda yana ganin sun sha bambam ta fuskar aji, ma`ana ita Sumayya ta fito daga gidan masu arziki, a yayin da shi kuma Muhammad ya fito daga gidan talakawa. Manyan taurarin wannan labarin sun hada da: Muhammad, Sumayya, Abdulkadir, Naja`atu, Saratu, Hajiya-Mai-Idon-Cin-Naira. Farkon harkallar wannan labarin ta faro ne daga inda Sumayya ta hadu da Abdulkadir. A wurin wani biki ne, Sumayya ta hadu da Abdulkadir, saurayi dan gidan masu hannu da shuni. Abdulkadir ya fada cikin soyayyar Sumayya, amma ta ki ba shi hadin kai. A gefe guda kuma ga kakar Sumayya nan Hajiya-Mai-Idon-CinNaira, ta kallafa ranta a kan Abdulkadir, saboda tana ganin shi ne ya fi dacewa da ya auri Sumayya a maimakon Muhammad. Daga nan ta shiga neman magani a wurin bokaye domin ta raba Sumayya da Muhammad. Idan da za a lissafa manyan labarun soyayya na Hausa guda goma wanda ba za a ta6a daina yayinsu ba, to lallai littafin In Da So Da Kauna zai shigo cikin jerin na daya zuwa na uku. Zan iya kwatanta littafin In Da So Da Kauna da littafin soyayya na Ingilishi mai suna Pride and Prejudice na Hausa, saboda tsananin kar6uwarsa. Wannan littafi na In Da So Da Kauna ya yi tasiri sosai a fagen adabin Hausa, ya zaburar da wasu makaranta na wancan lokacin ta yadda har suka rikide suka koma marubutan kansu, sannan ya samu kar6uwa sosai ta hanyar yaduwa a sassan duniya daban–daban. An fasara wannnan littafin zuwa harshen Ingilishi da

sunan The Soul of my Heart. Cikin littafin na IN DA SO DA KAUNA akwai baitukan soyayya da Muhammad ya yi wa Sumayya: 1- Bismil ilahi jallah ya sarki gwani roqo na ke a gare ka sarkin mulki. 2- Karan basira har hazaqa rabbana , domin na waqe sahiba mai kirki. 3- Allah dado tsira ga Ahmadu sayyadi, alay sahabbai tabi’ai ba burki. 4- Waqa ta soyayya na ke so zana yi, a gare ki lallai don na nuna halinki. 5- Tauraruwata ya ki gani sarauniya , ni ne masoyin naki mai qaunarki. 6- Sumayya girman sonki birnin zuciya, ya zarce ma in bayyana shi da baki. 7- Kogi na qauna na shige na dulmiye, na cusa kaina

can cikin qaunarki. 8- Ko da ana jifa da harbi zan shiga , raina yana matsayin a fansar naki. 9- Amma akwai makiya da ke yin hassada, burin su kullum kadda in aure ki. 10- Suka su ke kullum suna zargi kwarai, Allah yasa su gane aikin kirki. 11- Sun ce da ni talakan da ba shi da ko dari, kuma banda halin ma da zan aure ki. 12- Sun manta Allah ne ya ke yin arziqi , in yai nufin ya azurta mamman naki. Ga duk wani ko wata mai sha`awar karanta tsofaffin littattafan Hausa, to ya kamata a nemi littafin In Da So Da Kauna a karanta. A gaida babban yaya, Ado Ahmad Gidan Dabino, MON. Allah ya ja kwana.

•Ado Gidan Dabino, MON


RAHOTANNI

A Yau Lahadi 15 Ga Afrilu, 2018 (28 Ga Rajab, 1439)

25

Shin Taron Ranar Marubuta Hausa Na Duniya Ya Bar Baya Da Qura? Daga Ibrahim Garba Nayaya

Kamar yadda aka sani wannan rana, muhimmiyar rana ce gare mu, domin a wannan rana marubuta na Hausa, har ma da manazarta da makaranta daga sassan duniya su na dafifi, domin halartar wurin wannan taro tun shekarar da aka fara, wato 2016, wanda mu ka yi a Kano. Dukkanin wanda ya halarci taron, to wajibi ne a kansa ya shaidi irin abubuwan da ya amfana da su. Daga ciki; sada-zumunta tsakanin juna, kwankwaxar ilimi dabandaban a fannoni na adabi daga bakunan manya-manyan malaman jami’o’i da kwalejojin wannan qasa, har ma da wanin wannan. Misali; abin da ya shafi xab’i da tallata littattafai a kafofin soshiyal mediya. Baya ga waxannan, akan yi bajekolin littattafai sabbi da tsoffi, wanda hakan zai bai wa mutum mallakar waxanda ya ji labarinsu a zamunnan baya. Xoriya a kan wannan, akan samu kyakkyawar alaqa da fahimta tsakanin masu mulki da marubuta. Wannan ke bai wa masu mulki damar fahimtar amfani da muhimmancin marubuci. A wannan shekara, kamar yadda mu ka gani, mun gudanar da wannan taro a jihar Katsina, inda tun kafin wannan taro ake naxa kwamitoci daban-daban, domin gudanar da taron cikin jin daxi da kwanciyar hankali. Sai dai a wannan shekarar an xan samu matsalolin da ba a rasa ba, wanda na ke tunanin virvishinsu ya faro ne tun kafin rana taron. Amma samuwar waxannan matsaloli ba zai rushe qoqarin wasu cikin kwamitin shirya wannan taro ba, domin sun yi rawar gani sosai wanda har wasu ke hasashen inda waxannan mutane sun janye hannayensu, to da fa an samu matsala tun farko, ko ma da taron ya gagara. Xauki misalin Bilkisu Yusuf Ali, a ranar farko ba ta bar wajen taron ba sai da ta ga an kai kowa makwancinsa. Ina kyautata zaton ni da Al’amin Daurawa ne mutane na qarshe da sai wajen qarfe 1:00 da wani abu na dare aka kai mu. To, idan ba dan ita ba, wa zai kai mu? Kafin na zo an nuna duk wanda ya zo zai yi rajista, sannan a haxa shi da wanda zai kai shi masauki, kuma a ba shi abinci. Da zuwana na fi awa xaya Ina neman masu yin rajista, amma ban samu ba. Ba maganar rajista, balle abinci, balle masauki. Lokacin da na zo, a duk ’yan kwamiti, idan ban da

Bilkisu, Fadila, Abdulrahman, Xanborno, Fatimiyya, Kankia da Daurawa, sai wasu masu motoci, babu wanda na gani bayan su. Na dai ji wasu na rawa a cikin xakin taron. Afuwan; hatta shi kan shi shugaban kwamitin taron neman shi aka yi aka rasa, kuma an yi ta kiran wayarsa, amma ba ta shiga. Sannan an samu wasu matsaloli a batun ajandar rana ta biyu ma, an samu sauyesauye, domin tun a farko aka yi latti, sannan aka riqa shigo da abubuwan da babu su, ko kuma aka riqa qara mu su lokaci. Misali, masu waqa kwata-kwata mintuna 20 ne a ajandar, amma fa an sha kixa da waqa kusan ya ninka na waxannan mintuna. Idan ka dawo kan karanta labari, wannan ba zai zama illa ba, domin taron da ma na masu bayar da labarin ne. Don haka, ni a fahimtata, karanta labarai na da muhimmanci a gaban manya, wanda mun bar zaman safe da cewar za a yi da yamma, da yamma ba a yi ba, da dare kuma sai abin ya koma wani abu daban. A lokacin dan da Nasir Wada (mai gabatarwa a taron) ya yarda da laifinsa, da na san an wuce wurin! Idan da Shugaba Na’auwa ya kwantar da hankulan waxanda su ka fusata, da magana mai daxi, wallahi da komai ya wuce. To, amma duk ba a yi haka ba; kowa sai qara tabbatar da maganarsa ya ke. Qarshe ita ma Sa’adatu Kankia ta zo da nata faxan, wanda ba haka yakamata ba. Idan mu ka koma kan maganar Farfesa Malumfashi Ibrahim, ai ya fayyace ma na qirqira da kuma yadda marubuci ke qirqirar labari, wanda mafi yawa gaskiya ne; ko dai ya faru da shi ko ga waninsa, amma sai a qara wani abu wanda bai faru ba, qila ma ya shamakance tunani da hankali domin tabbatar da wani abu. Kenan kuskure ne babba a kira masu son karanta wannan labari da maqaryata. Matsalolin wurin kwana kuwa, ban tsammanin akwai wannan, sai dai tabbas an yi jinkiri wajen kai mutane masauki. Ni idan ka xauki misali; a hotel aka ba mu xaki, Maikuxi Hotel, kuma wuri ne mai kyau, wanda dole ne mu cigaba da ganin qoqarin Hajiya Bilkisu Yusuf Ali, kamar yadda na faxa a baya, ba ta bar wurin taro ba sai da ta tabbatar an kai kowa masaukinsa. Sai dai batun da wasu ke cewa, idan mutum na da kishi ko da kansa zai nemi masauki da abinci. Qwarai haka ne, amma domin me ake yin rajistar? Shin ba don abinci da masauki da satifiket ba ne? Ni Ina ganin

•Wasu daga cikin fitattun marubuta a lokacin Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya da a ka gudanar a Katsina

•Wasu daga cikin fitattun marubuta a lokacin Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya da a ka gudanar a Katsina

bai ma dace a kawo wannan maganar ba kwata-kwata. Ni a shawarata Ina ganin tun yanzu yakamata a fara zama domin yin wani tsari na cigaba da wannan taro a duk shekara. Ni a karan-kaina Ina da shawarwarin da na ke kyautata zaton idan an bi su, to wannan taro zai xore insha Allah. Daga cikin shawarwarin nawa kuwa, Ina ganin zai fi kyau a kafa wata dunqulalliyar qungiya ta marubuta Hausa ta qasa, wadda za ta xinke dukkanin qungiyoyin da ake da su. A qarqashin inuwarta, sai a riqa shirya Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya kenan. A tsarin da za a bi, sai a riqa canja shugabanni duk bayan wasu ’yan shekaru, sawa’un biyu ko uku. Sannan a riqa sanya tarukan a mabambanta jihohi. Duk jihar da za a je, sai a riqa kafa ‘Local Organization Committee’ a tsakanin ’yan jihar, sannan a samar da tsari na kwamitocin shirya wannan taro duk shekara. Har wa yau, a samu wani sarki cikin sarakunanmu masu martaba ya kasance shi ne uban

wannan qungiya ta qasa, kuma duk jihar da za a je yin wannan taro, to ya kasance gwamnatin jihar ce ke da alhakin bayar da aqalla kaso sittin na gudumawar wannan taro. Sannan a ware wasu ranaku a duk shekara waxanda a cikinsu ne za a riqa gudanar da wannan taro. Misali, a sanya kwanakin Good Friday zuwa Ester Monday ko wasu ranakun da aka san za a samu wata babbar makaranta da xalibanta sun tafi hutu, kuma hutun ya kasance na qasa ne gabaxaya. Sannan kuma taron ya kasance ya na da manufofi da tsarin karantar da marubuta da bi da matakai nasu dabandaban. Hatta waxanda ke ganin sun wallafa littattafai da dama. Na tabbata idan aka yi haka, to za a samu komai ya gudana kamar yadda ake so. Da fatan Allah Ya taimake mu, Ya haxe kawunan marubuta cikin gaskiya da amana, amin. Nayaya shi ne shugaban qungiyar Nguru Writers’ Association of Nigeriaa (NWAN) daga jihar Yobe.


26

A Yau Lahadi 15 Ga Afrilu, 2018 (28 Ga Rajab, 1439)

Tare da Fadila H. Aliyu Kurfi fadilapeady@gmail.com tweeter @FadilaKurfi

RIGAR ’YANCI Da Zan Zama Shugabar Nijeriya Sai Na Hana Alfarma –Maryam Turau

An fi sanin MALAMA MARYAM NUHU TURAU a fagen rubutun littattafan Hausa, amma kasancewar ta mai lura da al’amuran yau da kullum a qasa, musamman siyasar Nijeriya, Turau ta na da damuwa kan yadda alfarma wajen tafiyar da Nijeriya ke hana ruwa gudu da kuma yadda ’yan siyasa ke amfani da matasa wajen tayar da zaune-tsaye a lokacin zave. Ga dai yadda tattaunawarta da wakiliyar LEADERSHIP A YAU LAHADI, FADILA H. ALIYU KURFI, ta kasance: Ko za mu iya jin taqaitaccen tarihinki? Sunana Maryam Nuhu Turau. An haife ni a Katsina a cikin unguwar Rafindaxi. Na yi firamare a Rafindaxi Model Primary School, wacce a ka maida Waziri Zayyana Science Model Primary School a yanzu. Na je sakandare a makaranyar ’yan mata ta WTC na yi qaramar sakandare daga xaya zuwa uku, sannan na koma Unity Girls College (exchange school) na ida SS 1-3. Na yi NCE a FCE Katsina na karanta Primary Education Hausa. A vangaren addini kuma na fara tun Ina ’yar sheka huxu a makaranyar allo sai da na yi sauka ta ta farko sannan a ka saka ni Islamiyya. Mene ne asalin fara rubucerubucenki, sannan kuma ya zuwa yanzu littafi nawa ki ka fitar? Asalin fara rubuce-rubucena ya samu asali daga karatun littafin irinsu Magana Jari Ce da a ke ba ni Ina karantawa lokacin Ina makarantar firamare kasancewa ta wadda na fi kowa iya karatun Hausa a ajinmu. Ya zuwa yanzu na rubuta littattafai da dama, amma biyu ne kawai su ka shiga kasuwa. Me ya ja ra’ayinki har ki ka fara rubutu? Zan iya cewa yawan karatun littattafai ya sa na fara sha’awar rubutawa har Allah ya ban ikon zama marubuciya. Wane hasashe za ki yi game da siyasar Nijeriya da makomarta? A da siyasar Nijeriya siyasa abar qyama ce, domin a wancan lokacin a na tsara zave a kuma aikata shi ba bisa qa’ida ba. Xan takara zai iya yin komai, ciki har da kisa, don ya ci zave. To, alhamdulillahi, yanzu an samu cigaba sosai a siyasar Nijeriya, wanda idan har a ka xore a haka qasar nan za ta iya kaiwa wani matakin da za a riqa koyi da ita. Me ki ka fahimta bambanci tsakanin siyasar ra’ayi da siyasar neman muqami? Siyasar ra’ayi siyasa ce da a ke yi domin kawo cigaban qasa. A kan nuna kishi da jajircewa, domin a kawo gyara da kuma cigaba. Duk mai irin wannan siyasar ba ya neman dole sai shi ne zai zama mai muqami ba, sai dai ya ga ta ina za a yi gyara, ta ina za a samu cigaba da duk wani abin alkhairi. Ita kuwa siyasar neman muqami siyasa ce da a ke yi kawai

don cikar buri; siyasa ta handama da babakere, siyasa ce ta son kai, rashin kishi da rashin taimakon talakkawa, siyasa ce ta wargaza qasa da kashe ’yan qasa. Mutum zai yi duk abinda zai yi ya xare mulki ya kama madafun iko ya karqame su a hannunshi. Komai zai yi, zai yi ne, don ra’ayin kanshi, ba ruwanshi da gyaran qasa bare talakkawan da ke tsugune qarqashinsa. Meye makomar matasa a mahangarki game da siyasar qasar? Babu masu ban takaici a siyasar qasar nan sai matasanmu da ba su san kansu ba har yanzu. Wai yaushe matasanmu za su farka su dawo cikin hayyacinsu ne? Yaushe matasanmu za su bar zama karnukan farautar ’yan siyasa? Har idan matasanmu ba su dawo hayyacinsu su ka bar bangar siyasa ba, ba za su rasa makoma mai kyau ba. Matasa na da matuqar mahimmanci sosai kuma za su iya taka kyakkyawar rawa a harkar siyasa, amma idan har ba jagaliyar siyasa a ka jefa su ba. ’Yan siyasarmu su bar vata rayuwar matasanmu, su riqa taimaka ma su wajen samun ingantaccen ilimi, don su ma su zama wasu a gobe. Shin ko manyan Nijeriya na yin wani yunquri, domin tallafa wa matasa ko kuwa dai su na tayar da mota ne ta baxe su da qura? Tam! Babu wani qoqari da manyan qasar nan ke yi, don inganta rayuwar matasan da su ka taimaka ma su har su ka xare kujerun mulki. To, wai ma

• Maryam Turau ina matasan su ka gan su? Wani ma daga ranar da ya ci zave ya tattara iyalinsa su ka haura Abuja, ka gama ganin shi ko muryarshi ka gama ji sai dai idan ka dace wata rana ka gan shi a talabijin ko ka ji muryarshi a gidan rediyo a na hira da shi. Da matasanmu za su gane, su bar wahala da kashe junansu a kan ’yan siyasa. Wacce gudunmuwa matasa za su iya bayarwa wajen cigaban siyasa ko dimukradiyyar kanta, idan damar hakan ta samu gare su? Ba don kar a ce na cika baki ba, da sai na ce, matasa na iya canza Nijeriya idan har su ka samu taimako a ka inganta rayuwarsu da ilimi, kasancewar su su ne qashin bayan al’umma kuma su ne ma su jini a jika da a ke hangen kamar yanzu su ka fara rayuwa. Da za su samu dama, tabbas da an sha mamaki. Ko a qasar Katsina mata na shiga a dama da su a siyasance ko kuwa su ma su na komawa baya su naxe hannu su zama ’yan kallo ne? Har yanzu kan mata a Katsina bai ida waye ba sosai ta fannin siyasa ba. Qalilan ne ke fitowa. Su ma za ki ga ba neman wani muqami su ke fitowa ba, sai dai su raka yarima a sha daxin kixa. Mu na fatan nan gaba kaxan mata su fara fitowa a na gogawa da su.

• Maryam Turau

Da za ki yi mulki a Nijeriya, wane abu ne za ki fara yunqurin gyarawa? Alfarma ce farkon abinda ke ci min tuwo a qwarya. A Nijeriya ne za ka ga

wanda bai cancanta ba ya riqe wani muqami, saboda ya na da alfarma, amma ga wanda ya cancanta ba za a ba shi ba, saboda bai da kowa. Don haka na ke adawa, baqar adawa! da alfarma. Sai cin hanci. Wannan na san ba ni kaxai ba, duk wani mai kishi zai yi fatan ganin qarshen numfashin cin hanci da rawa. Sai inganta rayuwar matasanmu. Ina mai mafarkin ganin rayuwar matasanmu ta inganta ta hanyar da za su zamo shugabanni nagari a gobe, sannan ilimi. Zan gyara harkar ilimi ta yadda zai zamo ingantacce. Kowa ya sani a Nijeriya mu na da albarkatun qasa da shugabanni ba su damuwa da su. Zan yi qoqari gyara waxannan albarkatun har sai ya zamo mu na gogayya da manyan qasashen da su ka cigaba da yardar Allah. Wane kira za ki yi ga shugabannin duniya kan yadda su ka xauki siyasa ko mulki tamkar gado? Wannan halin nazari da dogon buri a kan kujerar mulki ya kamata shugabanninmu su farka. Shugabanci ba mulkin sarauta ba ne, wanda za ka ce idan ka hau ba ka sauka har sai ka mutu a kai. Ya kamata idan ka yi wa’adinka ya cika ka sauka wani shi ma ya gwada irin nashi qoqarin. Daga qarshe wacce shawara za ki ba wa matasa? Shawarar da zan ba su ita ce, don Allah su san kansu, su taimaki rayuwarsu su ingantata ta, su bar bangar siyasa, su nemi sana’ar da za su dogara da kansu. Ina yi wa matasanmu fatan alkhairi. Na gode; ni ce maryamturau@gmail.com.


RAHOTANNI

A Yau Lahadi 15 Ga Afrilu, 2018 (28 Ga Rajab, 1439)

27

Gobara Ta Lashe Matsugunin Falani A Kebbi Daga Umar Faruk, Birnin-kebbi

A jiya ne gobara ta lashe matsugunin falanin da ke garin bawada a karkashin gudumar kambaza qaramar hukumar mulkin Gwandu a jihar kebbi a jiya. Watar gobarar ta tashi ne da misalain karfe 1 na daren jiya sanadiyar iskan guguwa daya tashi a cikin dare da tunanin cewa za’ayi ruwan Sama a ruggar ta Fulanin na garin bawada da ke cikin yakin kambaza a hukumar Gwandu a jihar ta kebbi. Hakazalika bukokin uku da kuma dukiyoyinsu da zasu kai kimani miliyan xaya da kuma xaruruwa sun halaka sanadiyar gobarar da ta tashi a cikin dare a ruggar ta falanin a jiya. Da ya ke bayyana yadda tashin gobarar ya auku a ruggar ta Fulanin garin bawada a jihar ta kebbi, Malam Umaru Ja’eh yace” wannan gobarar ta tashine da misalin karfe xaya na dare bayan muna barci sai muka gan hayaki ya tashi a cikin bukokin mu gudu

uku bayan tashin guguwa inda muke tsammanin cewa ruwan sama ne sai sauko”. Ganin cewa ba ruwan sama bane sai na nemi xauken jama’ar da ke kusa da mu domin kashe watar. Har ila yau ya ce, “kafin mu samu ruwan da zamu kashe watar ta lashe dukiyoyin kayan mu da ke kimanin Naira Miliyan Xaya da wasu xaruruwa a cikin bukokin uku a ruggar ta fulanin garin bawada.” Hakazalika Umar Ja’eh yace “ rashin bamu da ma’aikatan kashin gobara yasa mun samu asarar kayan mu da kuma bukokin mu”. Bugu da kari yace “ babu asarar rayuwa ta mutanen ko ta dabbobi sai dai asarar kayan mu da kuma bukokin uku. Daga karshe yayi kira ga gwamantin jihar kebbi da kuma hukumar da abin ya shafa domin taimaka muna da gudumawa na tallafi kan asarar da mukayi ta dukiyoyinmu na Kaya da kuma matsugunin.

•Bayan gobara ta cinye rugar Fulani a Kebbi

Tijjani Baba Gamawa Ya Nemi A Inganta Rayuwar Talaka A Hukunta Masu Laifi A Nijeriya Daga Muazu Hardawa, Bauchi

An bayyana rashin inganta rayuwar talaka ta hanyar samar musu da walwala a fannoni dabam dabam na rayuwa a matsayin wata hanya da za ta cigaba da haifar da matsaloli a Nijeriya, musamman ganin yadda ake cigaba kama waxanda ke haddasa fitina a Nijeriya ba tare da ana hukunta masu laifi ba. Tsohon mai ba gwamna shawara na musamman a Jihar Bauchi Air Kwamanda Ahmed Tijjani Baba Gamawa mai ritaya shine ya bayyana haka cikin hirarsa da wakilin mu a Bauchi, inda ya qara da cewa abin takaici ne yadda a kullum ake samun tashe tashen hankula a Nijeriya da kuma aikata laifuka ta hanyar mu’amala da manyan makamai, amma har zuwa wannan lokaci lamurran qara ta’azzara su ke yi madadin a samu daqile su, don a samu ci gaban zaman lafiya da walwalar jama’a a Nijeriya. Air Kwamanda Ahmed Tijjani Baba Gamawa mai ritaya ya ce abubuwan da ke faruwa a Nijeriya ba su da daxi kuma kowa yasan abin da ke faruwa dole ya nuna damuwa, duk da cewa gwamnati na

iya qoqarinta dole ta yi wa mutane adalci ta riqe gaskiya a riqe amana a tabbatar kowa ya riqe gaskiya kuma mutanen qasa da shugabanni dole a faxawa juna gaskiya a fuskanci gaskiya don a samu ci gaban lamurra. Ya ce abubuwa da dama sun faru kamar wasa musamman game da harqar da ta shafi tsaro, amma an wayi gari lamurra na nuna kamar za su fi qarfin gwamnati, don haka ya zamo wajibi a tashi tsaye a magance irin lamurran da ke faruwa don a samu ci gaban zaman lafiya, ta hanyar neman shawarar masana don yin abin da ya dace saboda a daina • Tijjani Gamawa zubar da jinin bayin Allah. Ya ce abin mamaki ne wuta a ba shi haquri. Amma idan na tashi nan na tashi can dole aka wayi gari mutane na mutane su marawa gwamnati haifar da husuma tare da baya kowa ya yi qoqarinsa a ba kashe mutane a kowane wuri jami’an tsaro bayanai game da ba tare da an hukunta masu abubuwan da ke faruwa cikin laifi ba to dole za a ci gaba da al’umma don ba za su iya yin samun matsaloli a qasar nan komai su kaxai ba dole sai da rashin daidaito ko yafewa sarakuna da mutane kowa ya juna tsakanin kabilu da aka ba da gudummowar sa kafin a jima ana zaune tare. cimma nasara. Don haka ya bayyana cewa Ya ganin irin halin da matuqar ana son qasa ta ake ciki game da yadda a ka zauna lafiya dole shugabanni tozarta wassu al’ummomi su tsaya su jajirce wajen ganin wasu aka raba su da rayukan an hukunta mutane da suke su, gwamnati dole ta hukunta haifar da fitintinu a qasar nan mai laifi kuma wanda aka don su zamo misali ga duk cutar a mayar masa hakkinsa wanda ke da nufin yin abin

da ya kauce wa dola, don gobe wani ba zai yi nufin aikata laifi ba. Don haka ya ce dole shugabanni su jajirce su yiwa mutane adalci, kuma duk da qoqarin da gwamnati ke yi dole a tashi kan matasa a tabbatar sun samu abin yi don lamarin akwai barazana yadda matasa ke zaune babu ayyukan yi basu san tudun dafawa ba. Baba Gamawa ya qara da cewa ya zamo wajebi a yiwa qasa addu’ah don samun zaman lafiya da cigaba mai albarka, haka kuma ya nemi a hukunta masu laifi a duk inda

suke don a xauki darasi daga waxanda aka kama da laifi kuma aka bayyana laifukan su aka tura su kotu ta musu hukunci. Amma idan mutum ya yi laifi ana kallo aka kyale shi ba tare da an hukunta shi ba to wasu za su bi suma su ci gaba da haifar da matsala saboda sun san idan suna da farcen suka duk varnar da suka yi ba wani mummunan hukunci da za su fiskanta. Ahmed Tijjani Baba Gamawa ya qara da cewa abubuwan da ke faruwa a qasar nan basu da daxi don haka dole a lura wajen ganin masu mulki sun daina tozarta mutane tare da kawar da masu gaskiya idan suna son a zauna lafiya. Idan kuma ba haka ba akwai lokacin da zai zo talakawa za su yanke hukunci wajen qin zavar duk wanda ya qi musu adalci da jagoranci na gari wajen nuna gaskiya da yin aikin da ya dace don ci gaban jama’a. Saboda haka ya zamo wajibi shugabanni su fahimci cewa mutane suna cikin wahala kuma dole a duba halin da suke ciki don a inganta rayuwar su saboda suma mutane ne ba bayi ba kuma suna da buqatar rayuwa cikin walwala da ’yanci kamar kowa.


28 RAHOTANNI

A Yau Lahadi 15 Ga Afrilu, 2018 (28 Ga Rajab, 1439)

Hukumar Shige Da Fice Ta Damqe Baqin Haure 67 A Mashigin Neja Daga Abdulrazaq Yahuza Jere, Abuja A qoqarinta na tabbatar da tsaron kan iyaka domin hana haramtattun baqi silalowa cikin qasar nan, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Qasa (NIS), ta damqe baqin haure 67 ‘Yan Nijer. Dakarun hukumar na musamman masu sintiri a kan iyakar Nijeriya da Nijer suka damqe baqin hauren ta mashigin Jihar Neja. Sanarwar da jami’in yaxa labaran hukumar ta NIS, DCI Sunday James ya raba wa manema labaru, ta nunar da cewa Babbar Jami’ar Hukumar reshen Jihar Neja, Misis Hornby ta bayyana waxanda aka cafken. Sanarwar ta ce nasarar da aka samu ta damqe baqin hauren ta biyo bayan taron da shugaban hukumar, Muhammad

Babandede, ya yi da shugabannin manyan shiyyoyi da jihohi da kuma sassan hukumar na kan iyakoki, filayen jirgin sama da kan iyakoki na ruwa ne inda ya hore su su qara matsa qaimi a bakin aikinsu domin tabbatar da cewa ba a bar duk wanda ba Xan Nijeriya ba ya jefa quri’a ko tsayawa takarar zave kamar yadda yake qunshe a tsarin mulkin qasa. Har ila yau, nasarar ba za ta rasa nasaba da sabon yunqurin shugaban hukumar ba na tabbatar da shigar da al’ummomin da ke kan iyakokin qasa cikin sha’anin tsaron kan iyaka inda shugabannin al’ummomin ke taimaka wa jami’an hukumar da bayanai. Damqe baqin hauren ‘Yan Nijer 67 a kan mashigin Jihar Neja alama ce ta sabon yunqurin

na Muhammad Babandede ya fara haifar da xa mai ido. Sanarwar ta ce tuni aka xauki bayanan baqin hauren kuma za a tasa qeyarsu zuwa qasarsu. Shugaban hukumar, Muhammad Babandede ya buqaci sauran shugabannin sassan hukumar su yi koyi da shugabar reshen Jihar Neja, CIS Hornby da jami’an sintirin kan iyakoki waxanda suke aiki tuquru tare da qara qaimi bayan Kwanturola Janar xin ya ba su sababbin motocin sintiri a kwanan baya. Idan za a iya tunawa dai, a kwanan baya Hukumar Shige da Ficen ta yi qawance da Hukumar Zave ta Qasa (INEC) domin tabbatar da cewa babu wani baqo daga waje da aka bari ya kaxa quri’a a zaven 2019 da ke tafe idan Allah ya kai mu.

•Muhammad Babandede Shugaban Hukumar Shige Da Fice na qasa

Santurakin Ningi Ya Roqi Sarakuna Su Lura Da Halayen Mutane Kafin Su Ba Su Sarauta Daga Muazu Hardawa, Bauchi An shawaarci sarakunan gargajiya a Nijeriya da su riqa lura da mutuncin mutanen da suke naxawa a sarautar gargajiya tare da duba irin halayen waxannan mutane ba yin la’akari da abin da suka mallaka ba inda ya ce hakan zai taimaka wajen kare martabar gidajen sarauta da sarakunan gargajiya. Santurakin Ningi Hakimin Gwam Alhaji Zakari Isa Liman shi ne ya yi wannan jan hankali cikin hirar sa da wakilinmu a lokacin bikin taya mai martaba Sarkin Ningi Alhaji Yunusa Mohammed Xanyaya murnar cika shekaru 40 bisa karagar mulki wanda aka gudanar a garin Ningi kwanakin baya. Alhaji Zakari Isa Liman Santurakin Ningi ya bayyana cewa mai martaba sarkin Ningi ba ya wasa da mutuncin talakawansa kuma yana taimaka musu fiye da yadda ake zato shi yasa mutane suka himmatu wajen ganin sun nuna farin cikin su a yayin wannan biki. Ya qare da cewa kyautatawa mutane da basu mutunci da walwala da mutuntawa da samar da wadatar arziqi shi ne zai kawo ci gaban mutane. Don haka ya buqaci gwamnati ta vullowa mutane hanyoyi da za su ci su sha don a magance damuwar da ake ciki a wannan lokaci saboda a samu ingancin zaman lafiya. Zakari Isa ya ja hankalin matasa kan su sani suma mutane ne masu ’yanci ba masu bauta ba, don haka su kasance suna walwala cikin al’umma ta hanyar neman abin kan su tare da nisantar biyewa mutanen da suke da wadata ko mulki

waxanda ke jefa su cikin wahala ko bautar da su suna yin rashin mutunci a cikin al’umma. Don haka ya gargaxi matasa su kasance masu neman abin kan su ta hanyoyin da suka dace, su daina biye ’yan siyasa ko miyagun mutane suna amfani da wajen aikata varna ko cin zarafin mutane.

Har wa yau ya shawarci sarkuna da su ci gaba da kare mutuncin gidajen sarauta ta hanyar xaukan sarauta a matsayin baiwa ce daga Allah su nisanci kwaxayi su xauka Allah da ya basu sarauta shi ne zai buxe musu hanyar arziqi don su riqe kan su da talakawan su. Don haka qara da cewa su

nisanci rungumar mutane daga ko’ina saboda suna da wadata ko mulki ana basu sarauta ta ko wace hanya domin neman abin hannun su alhali ba a san irin qudindinen da suka yi suka tara abin duniyar ba, ta yiwu ta hanyar satar dukiyar gwamnati ko ta mutane da sauran munanan hanyoyi da miyagun

mutane ke bi a wannan lokaci don tara dukiya. Don haka ya buqaci sarakunan gargajiya da su fahimci cewa ba mai karya sarakuna sai Allah duk mulkin mutum, don haka su nisanci biyewa ‘yan siyasa wajen yin abin da bai dace ba don a kare martabar gidajen sarautar gargajiya.

A Na Zargin Majalisun Dokoki Kan Rashin Baiwa Qananan Hukumomi Gashin Kansu –Diggi Daga Umar Faruk, Birnin-kebbi A jiya ne shugaban qaramar hukumar mulki ta kalgo Alhaji Umar Namashaya Diggi ya zargin 'yan majalisun dokoki na taraiya da kuma na jahohin qasar nan kan rashin baiwa qaranan hukumomin qasar nan gashin kansu. Shugaban qaramar hukumar ta kalgo da Kwamitin a jihar kebbi ya bayyana hakan ne yayin wata zantawa da yayi da wakilin LEADERSHIP A Yau lahadi a ofishinsa da ke a sakatariyar hukumar ta kalgo a jiya . Ya cigaba da cewa, “su tuna cewa zaven su akayi domin suyiwa talakawa abin da suke so ba abin da su 'yan majalisun keso ba". Domin jama'ar da suka zaven su na bukatar aba qaranan hukumomin qasar nan incin cin gashin kansu amma sai gashi sun ki amincewa da kudurran da jama'a suka gabatar gaban majalisun biyu na taraiya da kuma na jahohin, wannan abin yaba jama'a mamaki sosai. Har ilayau yace " rashin baiwa qananan hukumomi gashin kansu yasa qananan hukumomi basu iya ayyuka ga jama'arsu da suke mulki kuma anwayi gari shugaban

qaramar hukumar mulki a qasar nan baya iya yi aikin hanya koda na kilo mita xaya ne ko kuma wata matsala tasamu jama'ar da yake mulki baya iya kai musu wata gudunmuwa saboda basu da wani cikakken ikon ga kuxaxensu na asusun hukumominsu sai dai kawai ya rubutawa gwamnatin jihar wanda sai randa taga dama ta bada umurni sainan a iyakai tallafi ga jama'ar da suke mulki wanda hakan ya savawa dokar da ta bada damaryin qarnanan hukumomin qasar nan ". Saboda dokar qasa da ta qananan hukumomi dai ta basu dama ga cin gashin kansu da kuma cikaken ikon ga kuxaxensu na asusun kowace qaramar hukumar qasar nan". Hakazalika ya ce, "jama'arsu su daina zargin Gwamnonin qasar nan ko shugaban qasa kan rashin baiwa qananan hukumomi 'yancin cin gashin kansu suga laifin wakilansu na taraiya kama tun daga sanatoci, 'yan majalisar taraiya da kuma na jahohin qasar nan domin abin da sukayi na hanawa qananan hukumomi gashin kansu baqa ramin lalata tsarin siyasi bane kuma karya doka, saboda hakan su tuna cewa sune keyi doka don haka mikesa su bazasu bi doka ba. Ya

•Shugaban qaramar hukumar Kalgo, Umar Namashaya Diggi kuma ce a jihar Kebbi yana jin cewa wasu mutane na zargin Gwamnatin Abubakar Atiku Bagudu kan rashin baiwa qananan hukumonin jihar gashin kansu tausu daina zarginsa saga laifin wakilansu na taraiya da kuma na jiharsu da suka zava domin su wakilcesu a majalisoshin. Domin kungiyar ma'akatan qananan hukumomin qasar nan da kuma sauran kungiyar masu zankansu sun

gabatar da kudurin neman baiwa wa qananan hukumomin qasar nan gashin kansu. Amma sukasa aiwatar da hakan, saboda haka wannan ba dimokaradiya bane. Kuma su sani cewa hakkin jama'a na kansu. Bugu da kari yace dokar qasar nan tace matakin gwamnatin uku ke akwai kama daga gwamnatin taraiya, gwamnatin jihar da kuma ta qananan hukumomi amma yanzu 'yan majalisu sun kashe gwamnatin qananan hukumomi a qasar nan. Saboda haka jama'a su sani cewa gwamnatin biyu kawai a akwai a qasar nan. Domin qananan hukumomin yanzu a qasar man suna ne kawai a baiyane amma a zahirance babusu domin an savawa dokar data bada dama yin qananan hukumomi a qasar Nijeriya kuma idon ba'a gyara wannan matsala ba siyasar shekara ta 2019 na da haxarin gaske. Daga nan yayi Kari ga gwamantin da kuma hukumomin da abin yashafa da su shigo cikin wannan matsala da qananan hukumomin qasar nan ke fustanta domin magance matsalar. Ya kuma cewa jama'a su canza duk wakilin da su ka zava, amma ba su yin aikin da aka zave su a kai.


Wasanni

A Yau Lahadi 15 Ga Afrilu, 2018 (28 Ga Rajab, 1439)

29

Tare da Abba Ibrahim Wada Leadership Ayau@yahoo.com

Anya Akwai Qungiyar Da Za Ta Iya Taka Wa Real Madrid Birki A Gasar Zakarun Turai? Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Qungiyar qwallon qafa ta Real Madrid tana neman lashe kofin zakarun turai sau uku a jere kuma na 13 a tarihi a wannan shekarar bayan da qungiyar takai wasan kusa dana qarshe bayan ta doke qungiyar Juventus a wasan da suka fafata a baya. Duk da cewa nasarar da Real Madrid tasamu akan qungiyar qwallon qafa ta Juventus tana cike da qalubale da cece kuce bayan da masu kallon qwallon qafa na duniya musamman masu adawa da qungiyar suka bayyana cewa alqalin wasan dayayi alqalancin wasan Real Madrid da Juventus ya nuna son zuciya ta hanyar bawa Real Madrid bugun fanareti. Real Madrid dai tana neman lashe wannan gasar karo na uku a jere sai dai abune mai wahala duba da irin qungiyoyin da suka rage a gasar kawo yanzu da suka haxa da Bayern Munchen da Roma da kuma qungiyar Liverpool ta qasar ingila. A ranar Juma’a ne hukumar qwallon qafa ta nahiyar turai taraba jadawalin yadda ragowar qungiyoyin huxun da suka rage zasu fafata inda aka haxa Real Madrid da Bayern Munchen sai kuma Roma wadda tayi waje da Barcelona zata fafata da qungiyar Liverpool wadda itama tayi waje da Manchester City a gasar. Sai dai ko yaya wasannin za su kasance? Bayern Munchen Da Real Madrid Qungiyoyin Real Madrid da Bayern Munchen sun haxu sau 24 a tarihi a gasar zakarun turai inda Real Madrid ta lashe wasanni 11 itama Bayern Munchen ta samu damar lashe wasanni 11 sannan aka buga canjaras sau biyu. Sai dai a haduwar da akayi Real Madrid ta zura qwallaye 37 yayinda itama Bayern Munchen ta zura qwallaye 36 a duka wasannin da qungiyoyin suka buga a tarihi. Qungiyar qwallon qafa ta Real Madrid tafi kowacce qungiya yawan lashe gasar bayan data lashe sau 12 a tarihi sannan kuma qungiyar ta lashe guda uku cikin shekaru huxu sai kuma Bayern Munchen wadda take neman lashe kofin karo na shida a tarihi rabon da qungiyar ta lashe gasar tun shekarar 2013 lokacin da qungiyar ta doke qungiyar Borussia Dortmund ta qasar Jamus. A cikin haxuwar da qungiyoyin sukayi sau 24 a tarihi qungiyar qungiyoyin biyu sun haxu sau shida a wasan kusa dana qarshe inda Bayern Munchen ta samu nasara a haxuwa 4 Real Madrid tasamu nasara a haxuwa 2 sai kuma a wasan kusa dana kusa dana qarshe inda suka haxu sau biyu

kuma Real Madrid ce duk tasamu nasara a haxuwar tasu. Qungiyoyin sun kuma haxu sau biyu a zageye na biyu wato wasan falan xaya inda Real Madrid ta samu nasara sau xaya itama Bayern Munchen tasamu nasara sau xaya sai kuma haxuwarsu acikin rukuni-rukuni na gasar inda Real Madrid tasha kashi a wasa farko daci 4-2 sai kuma wasa na biyu Bayern Munchen xin tasake samun nasara daci 4-1. Kusan za mu iya cewa duka qungiyoyin sunyi qoqari idan muka duba yanayin haxuwarsu da kuma yadda kowacce qungiya ta zura qwallaye a ragar yan uwarta, sai dai sun tava haxuwa a wasan sada zumunta inda Real Madrid tasamu nasara daci 1-0 ta hannun xan wasa Danilo wanda yanzu yake buga wasa a Manchester City. Qungiyar qwallon qafa ta Bayern Munchen dai bata fara gasar wannan kakar cikin nasara ba inda sai da takai har ta kori mai koyar da yan wasan qungiyar, Carlos Ancelotti, xan qasar Italiya amma daga baya kuma qungiyar ta farfaxo inda har takoma ta xaya akan teburin gasar Bundes Liga kuma tuni qungiyar har ta lashe kofin na wannan shekarar. Sai dai Real Madrid ma abin haka yake itama bata fara buga gasar ta laliga da qafar dama ba kuma kawo yanzu qungiyar tana mataki na uku akan teburin gasar bayan da Barcelona take kan gaba da maki 16 tsakaninta da Real Madrid Mai koyar da ’yan wasan qungiyar Real Madrid, Zinedine Zidane yana fuskantar qalubale a wannan kakar na lashe kowanne irin kofi sakamakon gasar zakarun turai ce kawai gasar data rage masa bayan da Barcelona tayi musu nisa sannan kuma anyi waje da qungiyar a gasar cin kofin Copa Del Rey.

Hakan ya sa Zidane ya ke cikin matsin lamba daga vangaren magoya baya da kuma shugabannin qungiyar na ganin ya lashe gasar cin kofin zakarun turai domin ya tsira da aikinsa. Real Madrid dai zatayi iya qoqarinta don ganin ta samu nasara a gasar domin lashewa amma kuma abune mai wahala ganin yadda ita qungiyar ta Bayern Munchen zata lashi takobin ramuwar cin da Real Madrid xin tayi mata a shekarar data gabata. Xan wasa Cristiano Ronaldo dai shine yafi kowanne xan wasa zura qwallo a raga a gasar ta wannan shekarar sannan kuma kawo yanzu ya buga wasanni 11 a jere yana zura qwallo a raga. Qungiyar qwallon qafa ta Bayern Munchen dai ta buga wasanni 20 a wasanni daban daban batare da an samu nasara akanta ba a gida sannan kuma qungiyar tana yawan zura qwallo a raga musamman idan tana buga wasa a gida. Za a buga wasan farko ne a filin wasa na Allianz Arena dake birnin Munich a ranar 27 ga watan nan na Aprilu sannan kuma wasana biyu zaizo ranar 3 ga watan Mayun wata mai kamawa. Liverpool Da AS Roma A karo na farko xan wasa Muhammad Salah zai koma birnin Rome domin fuskantar tsohuwar qungiyarsa ta Roma wadda ya bari watanni takwas da suka gabata zuwa Liverpool akan kuxi fam miliyan 36. Qungiyar qwallon qafa ta Roma ce abin kallo a wannan haxuwar da akayi bayan data doke qungiyar Barcelona a wasan kusa dana kusa dana qarshe da suka fafata a kwanakin baya wasan da yaja hankalin yan kallo a duniya. A wasan farko da suka buga Roma

ce tayi rashin nasara daci 4-1 yayinda wasa na biyu kuma Roma tasamu nasara daci 3-0 wasan da yabawa yan kallo mamaki ganin yadda Roma tayiwa Barcelona dukan tsiya. Ita ma qungiyar qwallon qafa ta Liverpool ta doke Manchester City ne daci 3-0 da kuma 2-1 gida da waje kenan duk da cewa Manchester City ce take kan gaba a gasar firimiya kuma kusan za’a iya cewa ta lashe gasar ta wannan kakar. A shekarar 1984 qungiyar qwallon qafa ta Liverpool ta doke Roma a wasan qarshe na gasar ta zakarun turai a wasan da aka fafata a filin wasan na Roma inda Liverpool ta lashe wasan 4-2 bayan bugun fanareti, tun da farko dai wasan 1-1 aka buga. Gaba xaya qungiyoyin sun haxu sau biyar inda Liverpool tasamu nasara a wasanni biyu Roma tasamu nasarar wasa xaya sannan aka buga canjaras a wasanni biyu. Masana dai suna ganin cewa qungiyar qwallon qafa ta Liverpool cezata samu nasara a wasanni biyun da zasu fafata sai dai kuma idan aka kalli yadda Roma tayi waje da Barcelona a gasar za’a iya cewa itama kanta Roma zata iya bawa Liverpool matsala. Itama dai qungiyar qwallon qafa ta Real Madrid ana ganin zata samu nasara akan Bayern Munchen a haxuwar da zasuyi biyo bayan a yan shekarun nan qungiyar Real Madrid tana yawan samun nasara akan qungiyar Bayern Munchen. Real Madrid ta lashe gasar zakarun turai guda uku cikin shekaru huxu wanda hakan yake nufin qungiyar ta mamaye qwallon qafar nahiyar turai a yan shekarun nan kuma wannanne karo na uku a jere kenan idan har qungiyar ta sake lashewa. Shin akwai qungiyar da zata iya takawa Real Madrid birki a cikin qungiyoyin da suka rage a gasar?


30 WASANNI

A Yau Lahadi 15 Ga Afrilu, 2018 (28 Ga Rajab, 1439)

Xan Cristiano Ronaldo Na Son Ya Gaji Mahaifinsa

Cristiano Ronaldo dai ya kasance dodon raga a rayuwarsa ta tamaula bayan da yake yawan zura qwallaye a raga musamman a yan shekarun nan da shekaru suke sake yawa akansa. Xan wasan na Portugal mai shekara 33 yana cin qwallaye 50 duk kaka a Real Madrid a cikin shekara tara da ya shafe a kulob xin, qwazon da wani bai taba yi ba. A yayin da a yanzu ake ganin Ronaldo ya kai qarshen ganiyarsa, mutane sun fara tunanin yadda duniyar tamaula za ta kasance ba tare da xan wasan ba ba. Ko yaya qwallon qafa za ta kasance ba tare da xaya daga cikin ‘yan wasan da ba a taba ganin irinsu ba? To sai dai da alama xan wasan da ya lashe kyautar gwarzon duniya har sau biyar yana qoqarin ganin ya samu wanda zai gaje shi ta hanyar dansa, Cristiano karami. Duka shekarunsa bakwai, amma

matashin Ronaldon ya fara nuna alamun qwarewa da qwazo kuma idan aka yi la’akari da cewa yana samun horo ne na musamman daga mahaifinsa, to ba abin mamaki ba ne. Kuma ko a yanzu Cristiano karami ya nuna yana samun qwarewar da sannu a hankali za ta iya yin daidai da ta mahaifinsa. Cristiano Ronaldo qarami yana da wasu halaye da qwazo da fasaha irin na mahaifinsa domin yana motsa jiki da horo sosai, Kuma ya kanyi hakan tare da mahaifinsa. Ronaldo gwani ne a bugun fanareti a qwallon qafa, inda ya ci qwallo 100 a shekarun rayuwarsa a tamaula, don haka shi ne ya dace ya horar da xansa dabaru da koyon cin qwallo a raga. Ronaldo ya shaida wa dansa cewa “Idan ka gaza cin kwallo, sai ka kara kwazo,” a yayin da yake koya ma sa

dabarun cin fenareti. Karamin Ronaldon ya varar da fanareti biyu daga cikin uku da ya buga a gaban mahaifinsa. Bayan cin qwallo kuma, qaramin Ronaldo ya kwaikwayi yadda ake murnar cin kwallo a raga a kullum dai ‘yan wasan qwallon qafa suna nuna qimarsu ko a bayan fili, inda ake ganin suna saka tufafi masu tsada da motoci masu tsada. Tuni Cristiano karami ya san dadin zama a cikin mota mai tsada da ta kai fam miliyan 2.15 kuma a kallum yana son yin hoto da mahaifinsa tare da sanin muhimmancin sanya tufafi masu tsada Yanzu qalubalen da ke gaban Cristiano qarami kafin ya kamo mahafinsa, shi ne lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar tare da girke mutummutuminsa kamar yadda aka karrama mahaifinsa.

De Bruyn Da Salah Da Harry Kane na Kokawar Lashe Gwarzon Gasar Firimiya Hukumar qwallon qafar qasar ingila ta fitar da jadawalin sunayen yan wasan da zasu kara domin lashe kyautar gwarzon xan wasan firimiya na bana wato xan wasan dayafi kowanne xan wasa qoqari. Xan wasa Kevin De Bruyn yana cikin yan wasa uku da aka zava a qungiyar Manchester City bayan xan wasa Lorey Sane da kuma David Silva sai kuma Harry Kane na qungiyar qwallon qafa ta Tottenham xan qasar ingila wanda shine xan wasa na biyu acikin yan wasan da sukafi zura qwallaye a raga. Muhammad Salah, wanda yafi kowanne xan wasa zura qwallo a raga yana ciki sai kuma mai tsaron ragar qungiyar qwallon qafa ta Manchester United wato David De Gea wanda ya buga wasanni 16 batare da an zura masa qwallo a raga ba.

De Bruyn dai ya zura qwallaye 7 a raga sannan kuma ya taimaka anci qwallaye 12 sai Muhammad Salah wanda kawo yanzu ya zura qwallaye 29 kawo yanzu sannan kuma ya taimaka aka zura qwallaye tara. Harry Kane, wanda ya lashe kyautar xan wasan dayafi zura qwallaye a raga shekaru biyu a jere da suka gabata shima yana ciki inda

kawo yanzu yanada qwallaye 25 sannan kuma ya taimaka an zura qwallaye biyu. Lorey Sane kuma ya zura qwallaye 9 ne kawo yanzu sannan kuma ya taimaka an zura qwallaye 12 sai kuma takwaransa na Manchester City, David Silva, wanda yaci qwallaye 8 sannan kuma ya taimaka akaci qwallo 11.

Yakamata Qasar Morocco Ta Karvi Baquncin Gasar Cin Kofin Duniya, In Ji Carlos

Tsohon xan wasan qwallon qafar Brazil Roberto Carlos na goyan bayan takarar Morocco ga shirya gasar cin kofin qwallon qafar Duniya na shekarar ta 2026 bayan dayace qasar ta cancanta da karvar gasar. Carlos ya bayyana hakane a wata ziyara daya kai qasar ta Morocco bayan daya jagoranci wani kwamiti na hukumar qwallon qafa ta duniya akan yadda za’a bunqasa qwallon qafa a tsakanin matasa batare da faxace-faxace ba. Tsohon xan wasan yace abune mai wahala a samu wata qasa a nahiyar Africa da tayi irin shirin da qasar Morocco tayi kuma ko a qasashen nahiyar turai sai an bincika sosai kafin asamu qasar da zata goga da Morocco. Ya kuma yabawa hukumar qwallon qafata qasar bisa qoqarinta na ganin matasan qasar suna bada gudunmawa sosai akan wasan qwallon qafa inda yace nan gaba kaxan qasar zata zamo zakaran gwajin dafi a qwallon qafa a duniya. A qarshe kuma yayi kira ga hukumar qwallon qafa ta duniya data duba irin shirin da qasar Morocco tayi wajen zavar qasar da zata karvi baquncin gasar inda yace Morocco ta haxa duk abinda ake buqata don amincewa da ita. Qasar Morocco da ta shiga sahun qasashen Colombia da Sweden da sipaniya wajen neman samun damar xaukar nauyin gasar cin kofin duniya da za’a yi a shekara ta 2026.


WASANNI 31

A Yau Lahadi 15 Ga Afrilu, 2018 (28 Ga Rajab, 1439)

Zan Yi Farin Ciki Idan Nijeriya Ta Tafi Da Ni Gasar Cin Kofin Duniya –Junior Lakosa Xan wasan gaba na qungiyar qwallon qafa ta kano Pillars, Junior Lakosa, wanda kawo yanzu yafi kowanne xan wasa zura qwallo a raga a gasar firimiyar Najeriya da qwallaye 14 yace zaiyi farin ciki sosai idan Super Eagles ta Najeriya ta gayyace shi zuwa gasar cin kofin duniya a qasar Rasha. Lakosa ya bayyana hakane a hirarsa da manema labarai inda yace zaiyi alfahari idan yasamu wannan damar ta wakiltar qasar nan a gasar da babu kamarta a duniya kuma yana fatan hakan. Ya cigaba da cewa abin alfahari ne ace yabuga wasa da shahararrun yan wasan Super Eagles xin kuma idan har an gayyace shi zai bada gudunmawar

data dace domin ganin qasar ta samu abinda yakamata. A tsakiyar kakar wasan data gabata ne dai xan wasa Lakosa yakoma Kano Pillars daga qungiyar First Bank dake jihar Legas inda acikin wasannin daya buga a iya lokacin ya zura qwallaye biyar. Ya qara da cewa gogewa da inda yakamata ace xan wasan gaba yana zuwa da kuma taimakon yan wasan qungiyar Kano Pillars ne yasa yake samun nasarar zura qwallo a raga a wannan kakar sannan ya qara da cewa yan wasan qungiyar sun bashi dama kuma suna taimaka masa sosai kuma yana aiki tuquru domin ganin ya bunqasa wasanninsa.

Mancheser City Ta Fara Zawarcin Isco Rahotanni daga qasar ingila sun bayyana cewa qungiyar qwallon qafata Manchester City ta cigaba da zawarcin xan wasan gaba na qungiyar qwallon qafa ta Real Madrid, Isco domin siyan xan wasan idan kakar wasa ta qare. Xan wasan dai yana cigaba da samun matsalar lokacin buga wasanni akai-akai sakamakon mai koyar da yan wasan qungiyar yafi amfani da yan wasan qungiyar na gaba wadanda sukafi shahara wato Bale da Ronaldo da Benzema. Hakan ne ya sa xan wasan yafara tunanin barin qungiyar domin samun qungiyar da zata bashi wasanni da yawa inda tuni Manchester City daman ta tava neman xan wasan a kakar wasan data gabata ta sake komawa Mai koyar da yan wasan qungiyar Manchester City, Pep Guardiola, yana son siyan dan wasanne domin ya maye gurbin dan wasa David Silva, wanda shima xan qasar Sipaniya ne kuma ya shafe kusan shekaru 8 a qungiyar ta Manchester City. Har ila yau wasu rahotanni sun bayyana cewa Manchester City ta shirya bayar da xan wasanta, Sergio Aguiro ga qungiyar Real Madrid

domin ta karvi Isco sannan ta cikawa Madrid xin kuxin da zata buqata. A na tunanin qungiyar Real Madrid zata rabu da xan wasan sakamakon shirin da qungiyar take dashi nayin garanbawul a yan wasanta wanda ake tunanin har da Isco a yan wasan da ake tunanin zasu raba gari da qungiyar. Isco dai kawo yanzu ya bugawa Real Madrid wasanni 239 sannan ya zura qwallaye 30 sannan kuma ya taimaka an zura qwallaye 55 tun daga lokacin da yakoma qungiyar daga qungiyar Malaga dake qasar ta Sipaniya.

Yakamata Ozil Ya Taimaka Wa Arsenal Ta Lashe Manyan Kofuna –Garry Neville Tsohon xan wasan qungiyar qwallon qafa ta Manchester United kuma mai sharhi akan wasanni a qasar ingila, Gary Neville, ya bayyana cewa sakamakon sake sabon kwantaragi da xan wasa Mesut Ozil yayi a qungiyar Arsenal a yanzu lokaci yayi da zai taimakawa qungiyar ta lashe manyan kofuna. Tun a farkon kakar wannan shekarar ne dai ake ta rade-radin cewa dan wasa Ozil da Alexis Sanches zasu bar qungiyar sakamakon qin amincewa da sabon kwantaragin da qungiyar tayi musu tayi, sai dai Sanches shi tuni yakoma Manchester United yayinda Ozil yaci gaba da zama a Arsenal xin bayan ya amince da sabuwar yarjejeniyar da suka qulla. Gary Neville yace, yanzu lokaci yayi da Ozil zai nunawa duniya cewa babban xan wasane kuma qwararre ta hanyar jagorantar Arsenal ta lashe babbar gasa kamar Firimiya ko kuma gasar cin kofin Europa da qungiyar take bugawa a wannan kakar. Ya cigaba da cewa yanzu qungiyar ta Arsenal tanada manyan yan wasan gaba wadanda zasu bawa kowacce qungiya wahala ba kawai a qasar ingila ba har a nahiyar turai saboda haka akwai buqatar qungiyar ta lashe wani kofi babba. Ya ce ya zama dole Arsenal xin ta

Casemiro Ba Na Sayarwa Ba Ne Qungiyar qwallon qafa ta Real Madrid ta bayyana cewa xan wasanta, Casemiro, xan qasar Brazil ba na siyarwa ba ne sakamakon raxeraxin da ake na cewa qungiyoyin qwallon qafa na Paris Saint German da Manchester City su na zawarcin xan wasan. Casemiro, mai shekaru 25 a duniya, ya na xaya daga cikin yan wasan da mai koyar da yan wasan

qungiyar Zinedine Zidane yakeso sosai kuma tuni yashiga cikin yan wasa sha xayan farko na qungiyar a duk wasan da qungiyar zata buga. Qungiyar qwallon qafa ta PSG dai tanason siyan xan wasan wanda take ganin shine zai iya maye mata gurbin Thiaggo Motta wanda shekarunsa suka kusa qarewa a qungiyar. Yayin da itama Manchester City take son xaukar xan wasan

domin maye gurbin Fernandinho gashi kuma qungiyar zata rabu da Yaya Taure wanda zai bar qungiyar a qarshen kakar da take qoqarin qarewa. Kamar yadda rahotanni suka bayyana, tuni PSG ta ware kuxi, fam miliyan 50 domin taya xan wasan wanda yazura qwallo a wasan qarshe nacin kofin zakarun turai da qungiyarsa ta lallasa juventus daci

lashe kofin Europa da yanzu takai matakin wasan kusa dana qarshe sannan kuma yakamata su sake shiri domin fuskantar kakar wasa mai zuwa. Ya qara da cewa rashin Alexis Sanches a qungiyar ba qaramar matsala bace domin babba ne kuma qwararren xan wasa amma tunda har Ozil yaci gaba da zama yakamata qungiyar ta dawo cikin manyan qungiyoyi hudu na gasar firimiya sannan kuma su koma matsayin da aka san qungiyar a baya. Kawo yanzu dai Arsenal tana mataki na 6 a gasar firimiya sai dai takai matakin wasan kusa dana qarshe a gasar Europa inda zata kece raini da qungiyar Atletico Madrid ta qasar sipaniya a qarshen wannan watan. 4-1 a qasar Wales a watan Mayun daya gabata. Ita ma qungiyar qwallon qafa ta Manchester City tana zawarcin xan wasan wanda take ganin zai kai fam miliyan 60 Xan wasan yazura qwallaye 15 cikin wasanni 131 daya bugawa qungiyar kuma yana bugawa qasar sa ta Brazil wasa a yan kwanakin nan. Sai dai kuma wani rahoton yana cewa xan wasan bashi da niyyar barin Real Madrid a daidai wannan lokaci da tauraruwarsa take haskawa.


15.04.18

AyAU LAHADI LEADERSHIP Don Allah Da Kishin Qasa

www.leadershipayau.com Leadership A Yau

JARIDAR HAUSA MAI FITOWA KULLUM TA FARKO A NIJERIYA

LeadershipAyau

No: 031

N150

15 Ga Maris, 2018 (28 Ga Rajab, 1439)

WASANNI

Anya Akwai Qungiyar Da Za Ta Iya Taka Wa Real Madrid Birki A > Shafi na 29 Gasar Zakarun Turai?

Mahanga UFUK DIALOGUE: Gudumawarta Wajen tare da

Musa Muhammad

Samar Da Zaman Lafiya Da Fahimta 08148507210 mahawayi2013@gmail.com

S

aboda muhimmancin abubuwan da suka shafi zaman lafiya da fahimtar juna, ya sa a yau ma na sake kawo maku wannan bayani na irin da gudumawar da gidauniyar UFUK DIALOGUE ke bayarwa, wajen musamman vangaren samar da zaman lafiya da fahimtar juna, inda muke tavo irin gudumawar da take bayarwa a wannan fanni, ta hanyoyin gudanar da taruka. Na kuma bayyana mana cewa wannan gidauniya tana gudanar da ayyuka da dama a wannan qasa, ciki kuwa har da gudanar da tarukan samar da fahimtar juna a tsakanin jama’a, inda ake tattara mutane masu mabambantan ra’ayoyi ana musayar ra’ayi domin amfanin juna wajen samar da fahimtar juna da zaman lafiya. A makonnin da suka gabata na bayyana cewa a wasu kwanaki can, UFUK DIALOGUE ta gudanar da irin wannan taro a garuruwan Abuja, Legos da Kaduna, inda suka samu haxin gwiwa da wasu Hukumomin qasar nan wajen gudanar da tarukan. Kamar yadda na kawo a makon da ya gabata, akwai IPCR, ECOWAS, NDA, NCWS, Ma’aikatar yaxa labarai da al’adu, ma’aikatar matasa da wasanni da kuma jaridar DAILY TRUST. Za mu xan maimaita wasu bayanai kaxan don amfanin waxanda ba su samu ganin jaridarmu da ta gabata ba, wanda kuma yana da matuqar muhimmanci a ji waxannan bayanai. Ga wanda bai san wannan qungiya ba, a taqaice za mu iya cewa ita Gidauniyar UFUK DIALOGUE ta Sasantawa ce a tsakanin addinai da al’adu, wacce wasu mutanen qasar Turkiyya, almajiran Shaihin Malamin nan, Fethullah Gulen suka qirqiro a qasar nan. Manufa da ayyukansu, ne shirya dandali da tarukkan sasantawa da qaunar juna da yafiya da cuxanyar juna a tsakanin mabambantan addinai da ala’adu domin samun ci gaba mai xorewa. Gidauniyar ta UFUK DIALOGUE ta shirya taron shekarar 2018 ne, mai taken Soyayya Da Haquri Da Juna, watau love and tolerance, wanda shi ne na huxu a jerin sahun tarrurkan da ta ke shirya, wanda n ace sun gudanar a Abuja Legas da Kaduna. A Kaduna, taron ya gudana ne

• Shugaban Gidauniyar UFUK DIALOGUE, Mista Kamil Kemani a a Gidan Hassa Usman Katsina da ke Kan hanyar Kawo a Kaduna, inda mahalarta taron sun tattaro kowane sashe na al’umma ,kama daga Malaman addinan Musulunci da Kiristanci da ‘yan kasuwa da jami’an tsaro da jama’an gwamnati da xalibai da ‘yan jarida da Sarakunan gargajiya da sauransu. A Jawabinsa na maraba da baqi, Shugaban Gidauniyar ta UFUK DIALOGUE, Mista Kamil Kemanci ya bayyana Gidauniyar a taqaice da kuma ayyukanta tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 2011 a qasar nan. Mista Kemanci ya ce tarurruka irin waxannan ba abin wasa ba ne, idan aka yi la’akari da irin yadda rashin jituwa da tashe-tashen hakula, ko rikice-rikice ke faruwa a ciikin al’ummar duniya, ba ma na Nijeriya kaxai ba. Ya kuma bayyana fahimta da aqidun Shaihun Malaminsu Fethullah Gulen, wanda ya qaurace wa duniya yana bautar Allah da kuma koyar da zaman lafiya da ilmi a cikin al’umma. Da yake magana a wajen taron, Gwamna jihar Kaduna, Malam Nasiru El-rufai, wanda mataimakinsa, Barnabas Bala Bantex ya wakilta, ya jawo hankalin ‘yan Najriya akan muhimmancin zaman lafiya da kawar da bambancebambancen da ke tsakaninsu, inda ya yi magana mai tsawo akan rikcin

Fulani da makiyaya. Ya ce tilas ne a cire maganar addini da qabilanci a wannan rikicin, a kalle shi ta fuskar tattalin arzikin qasa, da kuma gano mafita, wacce za ta amfani Fulanin da sauran al’ummar qasar nan. “Tun ina xan majalisar tarayya na tava kawo wannan batun na rikicin makiyaya da manoma, amma sai sauran ‘yan majalisun ba su dabi batun da wani muhimmanci ba, sai ga shi abin da ba a son shi ne yake faruwa a halin yanzu,” in ji Mataimakin Gwamnan. Ya qara da cewa, “abin takaici ne wasu sun sanya maganar addini da qabilanci a al’amarin, maimakon a kalle shi ta fuskantar matsalar tattalin arzikin qasa.” A nasa jawabin, mai magana na farko, Sakataren qungiyarJama’atu Nasril Islam, Dokta Khalid Abubakar ya ce idan ana son a samu zaman lafiya sai an samu soyayyar juna da haquri da juna mai xorewa a cikin al’umma. Ya kawo koyarwar Fethullah Gulen, inda ya ce soyayyar wani babban al’amari ce a zamantakewar xan adama, sannan tausayi da rahma da yafiya da kuma juriya da juna. Dokta Khalid ya ce sasantawa ita ce a cire ganin girman kai da amince wa gaskiya ta bayyana, ba tare da son zuciya ba, inda ya kawo ayoyin Alqurani mai tsarki domin ya tabbatar da hujjojinsa. Daga nan

ya kawo rabe-rabe da tsattsauran aqidoji da illolinsu a cikin al’umma, da kuma hanyoyin da za a bi domin magance su gaba xaya. Hanyoyin, in ji shi, sun haxa gano al’ummun da talauci ya yi wa kanta ko waxanda aka zalunta suna son su yi ramuwar gayya, samar da Malamai masu hikimar magana da iya jawo hankali waxanda za su lallami al’ummar da ka iya faxawa cikin tsattsauran ra’ayi ko waxanda aka zalunta da samar da jagoranci na adalci da gaskiya ba tare da nuna bambanci ba. A muqalar da ya gabatar a wurin taron, Dokta A.O. Yahaya na sashen Akawu na Jami’ar Horos da Sojoji ta qasa, NDA Kaduna mai suna ‘Yadda za a magance tsauraran ra’ayoyi a cikin al’umma,’ ya haqiqance cewa, iyali su ne qashin bayan magance tsauraran ra’ayoyi a cikin al’umma, inda ya kawo misalai da dama domin ya tabbatar da iqirarinsa. Muna fata za a samu irin waxannan qungiyoyi, ko gidauniyoyi, waxanda za su shiga gaba wajen ganin al’umma ta samu fahimtar juna a tsakaninsu, musamman ta nahyar shira tarurrukan qara wa juna sani da kusan tar juna, kamar irin wannan da UFUK ke gabatarwa. Domin a haqiqanin gaskya irin wannnan abu, ana ganinsa kamar ba komai, zai iya bayar da gagarumar gudumawa wajen samar da fahimtar juna a tsakanin jama’a, domin sai da fahimtar juna ne ake samun cikakken zaman lafiya.

Babba Da Jaka Matan Chibok 15 Kacal Suka Rage Cikin 113

-Salkida

Lamarin dai da ban tsoro...

Ana shiryawa da buga LEADERSHIP A Yau a kamfanin LEADERSHIP GROUP LIMITED, lamba 27, kan Titin Ibrahim Tahir, a Gundumar Utako, Abuja. Tarho: 09-2345055; Fax: 09-2345360. P. O. Box 9514, Garki II, Abuja. Ofishin mu a Legas: 34/36 Titin Adegbola, Anifowose, daidai Oba Akran, Ikeja. Tarho: 01-8963459. Shafinmu: leadershipayau.ng, E-mel: leadershipayaulahadi@yahoo.com ko Edita: +2348032875238

Leadership A Yau Lahadi 15 Ga Afrilu 2018  

Leadership a yau lahadi 15 ga afrilu 2018

Leadership A Yau Lahadi 15 Ga Afrilu 2018  

Leadership a yau lahadi 15 ga afrilu 2018

Advertisement