Leadership A Yau Juma'a 6 Ga Afrilu 2018

Page 1

6.04.18

AyAU JUMA'A LEADERSHIP Don Allah Da Kishin Qasa

www.leadershipayau.com Leadership A Yau

JARIDAR HAUSA

LeadershipAyau

6 Ga Afrilu 2018 (19 Ga Rajab, 1439)

TA FARKO MAI FITOWA KULLUM A NIJERIYA

Bugu na: 030

N150

‘Ibo Masu Saida Magunguna Ne Silar Shaye-Shaye A Arewa’ Daga Abubakar Abba

Wani Malami a sashen sadarwar na Jami’ar Bayero da ke jihar Kano, Dakta Bala Muhammad ya soki Ibo a kan cewar su ne qashin bayan dillalan da suke safarar qwaya da ‘codeine’ zuwa Arewacin Nijeriya. Dakta Muhammad ya yi wannan

zargin ne a qasidar sa da ya gabatar a taron zaman lafiya da wayarwa da matasa Kano da Gidauniyar Hamisu Magaji ta shirya a gidan Mambayya a cikin jihar Kano. Taken qasidar tasa shi ne, “Xabi’ar Shaye-Shaye a Tsakanin Matasa da Aikata Laifuka da kuma Sha’anin Tasro.” Muhammad ya xora laifin qara

qazantar xabi’ar a Arewacin Nijeriya musamman a Jihar Kano a kan Ibo masu safarar kayan maye. Malamin ya kuma bayyana mamakin sa qarara, a kan yadda xabi’ar ta shayeshaye ba ta yi qamari a Kudu-MasoYamma na kamar yadda ta qazanta a Arewacin Nijeriya ba. >Ci gaba a shafi na 4

Ba-Ta-Kashi Da ’Yan Bindiga:

Zamfara Ta Numfasa, Kaduna Ta Motsa 5

An Kashe Mahara 21

Sun Kashe Basarake Da Mutum Biyar

Shugaba Buhari Ya Qalubalanci Malaman Addini Kan Haxin Kai Daga Abubakar Abba

Shugaban Qasa Muhammad Buhari ya bayyana cewar wasu muryoyi da ake yin su don wata manufa ta siyasa ko qabilanci suna furta kalaman vatanci, inda suke sukar gwamnantin sa da shi kansa a kan nuna banbancin addini. Shugaban Qasan ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawaunsa, Mista Femi Adesina ya fitar a fadar shugaban qasa jiya Alhamis a Abuja. Ya ce, sukar ba ta da wani tushe balle makama.

> Ci gaba a shafi na 4

Shugaban Qasa Muhammadu Buhari yayin da yake tarban Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara, Mai Martaba Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmad a ziyarar da ya kawo fadar Shugaban Qasan da ke Abuja, jiya Alhamis.

Bincike Ya Gano Raggwanci Alama Ce Ta Kaifin Basira > Shafi na 2 Kwalara Na Cigaba Da > Shafi na 2 Maharba Sun Bayyana Sirrinsu Kwantar Da Mutane A Yobe Na Yaqi Da Boko Haram > Shafi na 2


Turn static files into dynamic content formats.

Create a flipbook
Issuu converts static files into: digital portfolios, online yearbooks, online catalogs, digital photo albums and more. Sign up and create your flipbook.
Leadership A Yau Juma'a 6 Ga Afrilu 2018 by Leadership Newspapers Nigeria - Issuu