Leadership A Yau Lahadi 1 Ga Afrilu 2018

Page 1

01.04.18

AyAU LAHADI LEADERSHIP Don Allah Da Kishin Qasa

JARIDAR HAUSA MAI FITOWA KULLUM TA FARKO A NIJERIYA Leadership A Yau

LeadershipAyau

01 Ga Afrilu, 2018 (14 Ga Rajab, 1439)

www.leadershipayau.com

No: 029

N150

2019: Har Yanzu Ina Jiran Lokaci Kan Yiwuwar Takarar Shugaban Qasa –Bafarawa Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja

Tsohon gwamnan jahar Sokoto kuma jigo a jam’iyyar PDP a jahar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa ya baiyana har yanzu yana jiran dukkan abin da Allah yayi dangane da yiyuwar fitowarsa fili ya baiyana zai nemi tsayawa takarar shugabancin Najeriya. Alhaji Attahiru Bafarawa wanda ya shaidawa taron daruruwan matasa yan

kasuwa na gamayyar kungiyar yan kasuwa na jahar Sokoto da suka ziyarce sa a garin Sokoto. Bafarawa ya baiyana bai da wani zabi ko iko dangane da neman kowane mukami har sai ya samu wannan dammar daga irin tsarin da Allah ya hukunta akanshi. Ya bayyana a yanzu babu wani abin da ya rage da zai iya ceto kasarnan kamar dukufa ga addu’a don neman Allah Ya kawo karshen irin matsalolin da ake fuskanta, ganin cewar shugabanin

dake mulkin kasarnan sun kasa magancesu, tare da sakaci da watsi da lamarin hadin kai, zaman lafiya da ci gaban al’umma, inda aka koma son rai da danniya tare da rashin adalci. “Mafi dacewa garemu a wannan halin shine na a dukufa ga addu’oi tare da kiyaye hakkokin juna da tsare adalci bisa gaskiya don samun sauki da rangwame daga Allah. Mu tsaya mu roki Allah akan samun nasara ga abin da yafi alheri,

’Yan Boko Haram Ba Su Ci Zarafinmu Ba > Shafi na 4

5

–Xalibar Dapchi

Wakilin shugaban qasa kuma ministan ilimi Malam Adamu Adamu, Sarkin Ningi Alhaji Yunusa Xanyaya da Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubukar III a lokacin bikin murnar cikar Sarkin na Ningi shekara 40 a gadon sarauta da a gudanar a filin Xanyaya Square da ke kan Hanyar Kano a garin na Ningi ta jihar Bauchi jiya Asabar 31 ga Maris, 2018.

Kalaman T.Y Danjuma Na Da Cutar Kwalara Ta Kashe Tsoratarwa Da Ban Mamaki, In Ji Mutane Biyar Ta Kwantar > Shafi na 8 > Shafi naa 5 Fada Shugaban Qasa Da 70 A Yobe


2

leadershipayaulahadi@yahoo.com

A Yau LAHADI 01.04.2018

Martanin Sa’adatu Kankia: Ko Kwalliya Ta Biya Kudin Sabulu A Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya? Daga Rabiu Ali Indabawa

Wannan wani martani ne da fitacciyar marubuciyar nan, MALAMA SA’ADATU SAMINU KANKIA, ta rubuta bayan kammala Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya da aka gudanar a birnin Katsina daga ranakun 16 zuwa 18 ga Maris, 2018, kuma ta aiko wa LEADERSHIP A YAU LAHADI. Ta rubuta martanin ne ga qasidar da mu ka wallafa a makon jiya mai taken ‘Katsina 2018: Ko Kwalliya Ta Biya Kudin Sabulu A Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya?’ wanda Yazid Nasudan ya wallafa. Ga dai ainihin abinda wannan Fasihiya Kankia ke cewa a cikin martanin nata: Assalamu Alaikum wa rahmatullah wa barakatuhu! ’Yan uwana marubuta barkanmu da wannan lokaci. Da fatan bakinmu na nesa da na kusa sun koma gida lafiya. Allah ya saka da alkairi ya bada ladar zumunci. Haqiqa wannan taron wani abu ne mai xumbin tarihi da ba za a manta da shi ba a tarihin marubuta. Taro ne da aka sha fama da gwagwarmaya da qalubale iri-iri kafin a samun tabbatuwarshi. To, sai dai Alhamdulillah! an yi taro lafiya an tashi lafiya. Na karanta rubutun da Yazid Nasudan ya yi mai taken ‘Katsina 2018: Ko Kwalliya Ta Biya Kudin Sabulu A Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya?’. A cikin rahotansa ya faxi irin qalibalen da taron ya fuskanta, wanda a ciki ya ke cewa, ‘wani abun dubawa shi ne irin yadda taron ya yi shakulatin vangaro da jarumar da ta yi sanadiyar assasa taron tun farko, wato Fadila H. Aliyu Kurfi. Abin mamaki ne a ce ko a cikin takardar tsarin jadawalin taron sam babu sunanta kuma ko sau xaya taron bai ambaci sunanta ba. Tabbas wannan babban butulci ne da babu wani abunda ya ke haddasa shi idan ba hassada ba. Kodayake dai Hausawa su kan ce ba a sauya wa tuwo suna. Saboda haka ko an ambaci sunan Fadila H. Aliyu Kurfi ko ba a ambace ta ba, ko an ba ta wata kulawa ko ba a ba ta ba, babu wani mahaluki da ya isa ya sauya tarihin cewa ita xin dai ce ta yi sanadiyyar assasa wannan abin alheri da wasu su ke ta xagawa su na hura hanci da shi.’ Ko da ya ke Yazid ba marubuci ba ne kuma sanda mu ka fara tafiyar babu shi. A wannan karon Fadila ta kawo shi daga baya. Don haka ban san wannan

maganar da ya faxa mene ne hujjarsa ko a ina ya ji ko waye ya ba shi labari ba. Sai dai wani abu da na ke so duk wani marubuci ya sani shi ne tabbas Fadila ta yi qoqari matuqa wajen buxe Gidan Marubutan Hausa tare da tattaro marubuta a duk inda su ke ta haxa mu a cikin gidan. Tabbas ta yi qoqari kuma ta cancanci a kira ta ‘jaruma!’ To, sai dai Ina so kowa ya sani cewa, Ni Sa’adatu Saminu Kankia ni ce na fara kawo shawara akan mu ma mu fara yin taron Ranar Marubutan Hausa Ta Duniya a Gidan Marubuta na WhatsApp, saboda na je ofis xin Aminu Ala na same su su na shirye-shiryen Ranar Mawaqa a Bauchi. A cikin waxanda aka yi maganar akwai Zainab wouwo, Sister Iyami, Sadiya Garba Yakasai, Comd Zailani, Teemah Zaria da wasu da ba zan iya kawo su ba. Amma a cikin waxanda na lissafa da yawansu su na cikin wannan tafiyar ta Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya da mu ka kammala, kuma na yi imanin su na sane da haka •Marubuciya Kankia kuma za su iya bada shaida shawarar da mu ka yi, sannan a kan hakan idan an tuntuve ne ta goyi baya. Daga nan muka su. Kuma a halin yanzu Ina haxu muka bada shawara akan tuntuvar wasunmu da ba su cewa, Ado Ahmed Gidan Dabino canja waya ba su koma su xauko ya jagoranci tafiyar. maganar duk da ta yi nisa, An sha fama da shi kafin ya amma Ina sa ran za a iya samun amince, saboda ya ce, harkar ta kowa ya gani. An daxe ana bi marubuta ba ta da daxi. A na ta ‘inbox’ ana cewa ‘yaya na qarshe muka sha kanshi ya bari ake ci da gumina? Don me yarda zai shige mana gaba. Daga ba zan fito na yi magana ba?’ nan ne aka fara shawarar ta yaya A lokacin da mu ka yi wannan za a fara? Sai ya bada shawara maganar, Fadila ma ba ta akan cewa a yi zama na gemu‘online’, sai da ta zo ta tarar da da-gemu, kuma nan take mu ka

tsaida ranar da za a fara zama a ofis xinshi a Kano. Aka fara tunanin abinda za a ci, idon an haxu, wanda ni xin dai daga Kankia na dafa abinci na haxa komai. Zainab Wowo ta taso daga Dutsinma ta zo muka tafi Kanon, yayin da Kabiru Assada ya bada 10,000 aka sayi lemu da ruwan da aka sha a wajen zaman ganawar. Kuma cikin ikon Allah aka tsaida matsaya akan shirya Taron Ranar Marubuta Hausa

Ta Duniya Karo na Farko. Abinda ya sanya na kawo wannan tarihin shine, saboda waxanda suka tarbi tafiyar a hanya, ba tare da su mota ta tashi ba tara su kayi suka hau, to gwanda a saka maganar a muhallinta. Kuma Ina kira ga masana da manazarta da su binciki wannan magana su gani. Da wannan ne na ke yi ma kowa bankwana. Allah ya tabbatar ma na da alkairinsa, amin.

• Wasu daga cikin jiga-jigan Taron Ranar Marubuta Ta Duniya karo na biyu da aka gudanar a Katsina a watan Maris, 2018


3

A Yau Lahadi 1 Ga Afrilu, 2018 (14 Ga Rajab, 1439)

ra’ayinmu

Naxin Sarki Sanusi II: Ganduje Ya Yi Farar Dabara

A

watan da ya gabata ne gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya naxa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, don ya jagoranci wani babban kwamitin bayar da shawara kan samar wa da jihar hanyoyin zuba hannun jari, wato Kano Investment Advisory Committee, wamda a ke yiwa laqabi da KanInvest. An xora wa kwamitin alhakin duba dabarun da za a iya yin amfani da su ne wajen ganin an samar wa da jihar yadda tattalin arzikinta zai sake qarfafa ne. A lokacin da gwamnan ya ke jawabi kan batun kafa kwamitin, ya bayyana cewa, an kafa shi ne domin a ci moriyar gogewa da qwarewar sarkin ya ke da ita a fannin sha’anin tattalin arziki, musamman a matsayinsa na tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya. Tabbas wannan ba qaramar farar dabara ba ce da Gwamna Ganduje ya yi, domin kuwa ba wai kawai muqamin gwamnan babban banki da Sarki Sanusi II ya riqe ba, qwarewarsa a harkar ceto tattalin arziki daga durqushewa ita ce babbar damar da za a samu daga gare shi bisa la’akari da yadda tattalin arzikin jihohin qasar ke tangal-tangal, domin a tsawon shekarun da Mai Martaba Sarki ya shafe ya na aikin banki ya tabbatar wa da duniya cewa, ya na iya tserar da duk wani tattalin arziki da ya ke tangal-tangal kuma ya miqe ya tsaya da qafarsa kyam! A fili ta ke cewa, an ga yadda Sarki Sanusi II ya taimaki bankin UBA a lokacin da ya ke aiki tare da shi, musamman yadda ya jagoranci sashen kula da ‘Risk Management’ na bankin. Yawancin tsofaffin bankunan qasar a wancan lokacin sun kusa durqushewa, saboda zuwan sababbin bankuna da kuma juyawar yanayin tattalin arziki zuwa tsari na zamani, to amma da taimakon Malam Sanusi Lamixo Sanusi (sunansa sarkin a wancan lokacin), sai bankin na UBA ya miqe da qafafunsa. Hakan bankin First Bank ya gani ya yi farar dabara irinta Ganduje ya xauke Sanusin kuma a qarshe ya naxa shi a matsayin shugabansa. A fili ta ke cewa, tun daga lokacin da Sanusi Lamixon ya jagoranci

First Bank zuwa yanzu a na kallon bankin a matsayin xaya daga cikin waxanda su ka fi kowanne tsaya wa da qafafunsu a faxin Afrika, ba ma Nijeriya kaxai ba. Masana tattalin arzikin da harkar banki su na danganta hakan ne da qwazo da qwarewar Sarki Sanusin. Babu shakka abinda tsohon

shugaban qasa, Marigayi Umaru Musa Yar’Adua, ya hasaso kenan ya naxa shi a matsayin gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) duk kuwa da kasancewar an kai ma sa sunayen waxanda su ka fi Sanusin daxewa a aikin banki, irin su Alhaji Umar Abdulmutallab. Wannan naxin da Yar’Adua ya

EDITA Nasir S. Gwangwazo

MATAIMAKIN SHUGABA (NA MUSAMMAN) Christian Ochiama DARAKTAN SASHE Mubarak Umar

RUKUNIN KAMFANONIN LEADERSHIP SHUGABA Sam Nda-Isaiah

BABBAN MANAJAN DARAKTA Abdul Gombe BABBAN MANAJAN DARAKTAN KADARORI David Chinda MANYAN DARAKTOCIN KAMFANI Dele Fanimo Felicia Ogbonlaiye DARAKTAN KULA DA MA’AIKATA Solomon Nda-Isaiah DARAKTAN KULA DA KADARORIN KAMFANI Zipporah D. Tanko MANYAN MANAJOJI Ibrahim Halilu Femi Adekunle Ebriku John

manufarmu

LEADERSHIP A Yau jarida ce da ake bugawa a Abuja. Ta yi tsayuwar daka wajen tabbatar da shugabanci da wakilci nagari. Jaridar za ta ci gaba da kare muradun al’umma, ba kare ra’ayi da muradun mahukuntanta kaxai ba. Da waxannan qudirorin ne muke fatan jama’a za su xora mu kan Mizani. Haka kuma duk ra’ayoyin masu karatu da muke bugawa, ba manufar kamfanin LEADERSHIP ba ne, ra’ayin masu karatun ne. Sai dai, ba za mu tava mantawa da dalilin wanzuwarmu a doron qasa ba, wato: Don Allah Da Kishin Qasa!

yiwa Sanusi haqiqa ya kawo alheri mai tarin yawa, domin shi ne ya zo da sababbin manufofi, waxanda a yanzu ba ma kawai tattalin arzikin qasa ba, hatta sha’anin tsaro ya sake havaka, saboda tsarin sa Sanusi ya zo da shi a harkar bankunan qasar na tafi-da-gidanka, wato tsarin ‘cashless’. A yanzu duk inda za ka je ba sai ka xauki kuxi a hannu ka na fargabar ’yan fashi ba, kawai ta wayarka za ka tura wa mutum. Idan har gwamnatin jihar Kano ta bai wa kwamitin Sarki Sanusi II damar yin aiki yadda ya kamata, tabbas a kwai yiwuwar nan gaba kaxan jihar za ta bunqasa fiye da yawancin jihohin qasar, musamman irin su Lagos da su ka yi nisa a dogaro da kai. To, da ma da yawan mutane su na ganin cewa, naxa Sanusin a matsayin sarki tamkar tauye Nijeriya ne, domin wasu gani su ke kamata ya yi a ce shi ne shugaban qasar, amma kasancewarsa ba zai ba wa ’yan qasar damar cin moriyarsa yadda ya kamata ba. To, aqalla da irin wannan dama da masu riqe da madafun ikon qasar za su riqa bai wa mutane irin su Sanusi II, za a iya amfana da qwarewar tasu. Don haka za a iya cewa, shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ne ya fi dacewa da ya aikata irin wannan farar dabara da Gwamna Ganduje na jihar Kano ya yi, domin bakixayan ’yan Nijeriya su cigaba da cin moriyar qwararru irin su Sanusi II, waxanda hatta qasashen duniya da hukumomi na duniya, kamar Bankin Duniya, su ka yarda da qwarewarsu da cancantarsu wajen riqe muqamai. Babban abin farin ciki a nan ga jihar Kano shi ne, yadda sarkin ya nuna ya amshi abin hannu bibbiyu, ya na mai cewa, “za mu sauke alhakin da a ka xora ma na mu na masu ji a jikinmu cewa tamkar kanmu ne. Mu na masu yaba wa gwamna bisa irin wannan qirqira mai cike da farar dabara da ya yi.” Ashe kenan waxannan kalamai sun nuna cewa, a shirye sarkin ya ke da ya amshi duk wani aiki wanda zai iya taimaka wa al’ummar qasa, duk kuwa da cewa, akwai rawani a kansa! Ganduje ya yi farar dabara. Qalubale gare ka Shugaba Buhari wajen zaqulo irin su Sarki!


4

A Yau LAHADI 01.04.2018

leadershipayaulahadi@yahoo.com

Compol Gombe Ya Karrama Wani Jajirtaccen Xan Sanda A Jihar Daga El-mansur Abubakar, Gombe A ranar Alhamis xin da ta gabata ne Kwamishina yan sanda na jihar Gombe Msita Shina Tairu Olukolu, ya karrama wani dan sanda mai mukamin Kofur mai suna Yohanna Musa, da yake ofishin yanki na fadar Gombe wato Gombe Division saboda kwazon da ya yi har ya kama wani gagararren Barawon Babura. Shi dai Kofur Yohanna Musa mai inkiya da Big Time, dan sanda ne dan asalin jihar Adamawa wanda yake aiki tukuru wajen ganin ya kama duk wani gagararren barawon Babur da Mota a Gombe wanda saboda sunan da ya yi hatta yan kalare idan suka ji sunan Big Time ba sa zama inda a yan makonni da suka gabata ya kama wani shahararren Barawon Babura da yake sace Baburan mutane a bankuna mai suna Ibrahim Umar. Bayan karramawar da Kwamishinan Yan sanda ya yiwa Kofur Yohanna Musa, Leadership A Yau Lahadi ta samu zantawa da shi dan jin irin kwazon da ya yi har ya samu lambar yabo da kuma tukuici na ladan aiki daga Kwamishinan Yan sanda na Gombe. Kofur Yohanna Musa, yace a shekarar da ta gabata ne ya sa kansa

wani aiki wanda ba sa sashi aka yi ba amma duka a cikin aikin dan sanda ne inda ya mayar da hankali wajen ganin ya tsarkake jihar Gombe dama arewa maso gabas da sauran jihohi daga ta’addancin kananan barayi da suka addabi jama’a da sace sace na Babura da motoci har ma da masu kwace jakakkunan Mata. Ya ce, aikin da yasa kan nasa shi ne a duk lokacin da aka kawo kara da ta shafi sata a ofishin su na yanki na Gombe sai ya bi diddigi har karshe wajen ganin an kamo barayin nan kuma an hukunta su. A cewar Big Time, a makonni biyu zuwa uku da suka gabata wani Matashi mai suna Alhaji Yakubu Da’u Babawo, ya kai rahoto ofishin su kan cewa an sace masa babur a bakin bankin Jaiz shi ne shi kuma a kashin kansa yaje kotu ta ba shi takardar izini ta Court Order da zai je bankuna dan samu bayanan da kamarar bankunan take dauka. Shi ne ya ce, a lokacin da yaje bankin Jaiz din ya gabatar da kansa bankin ya ba shi hadin kai inda suka ba shi hotunan da suka dauka anan ne yaga hoton shi Ibrahim Umar da ya kware wajen satar Babura a bankin wanda kusan ma duk wani barawon babur a Gombe shi ne ubangidan sa. Kofur Yohanna ya ce, da bayanan bankin ya yi amfani har ya gano gidan

barawon yaje ya same shi ya kama shi duk ba tare da sanin manyan sa ba har shi wannan Barawon ya yi masa alkawarin cewa ya rufa masa asiri zai bashi kudi naira dubu dari biyu yace baya so ya kara cewa ya fadi ko nawa yake so zai ba shi Yohanna yace shi aiki yake ba kudin sa yake so duk da ma duk wannan aiki da yake yi da kudin aljihunsa yake. A nan ne Kofur Yohanna Musa, ya kara bayyana cewa da barawon yaga ba zai bar shi ba sai yace masa ya yarda zai bashi gidan da yake ciki suje a canja takardu shi zai bar gari nan ma Yohanna yace ba ya bukata sanda ya kai shi helkwatar yan sanda bangaren jami’an CID. Irin wannan jajircewa da Yohanna Musa, ya yi tayi har ya kai ga cafke wannan shugaban Barayin ne yasa Kwamishinan yan sandan jihar Mista Shina Tairu Olukolu, ya karrama shi ya ba shi takardar yabo da tukuici na yan kudade dan karfafa masa guiwa. Ganin yadda aka karrama shi Kofur Yohanna ya ce, yanzu ne ma zai kara zage damtse dan yaki da irin wadannan barayi da suka addabi mutanen Gombe kuma tunda akan gaskiya yake aiki baya jin wani azzalumi zai iya illata shi tunda da zuciya daya yake aiki kuma Allah yana tare da shi. Bayan wannan barawo, dan sandan

• Kwamishinan ’yan sanda na jihar Gombe, Shina Tairu Olokolu, ya ke miqa takardar karramawa ga Kofur Yohanna Musa

yace ba sau daya ba ba sau biyu ba yabi barayin Motoci da Babura har jihohin Adamawa da Jos da Taraba da Yobe ya kamo su ya dawo dasu Gombe an hukunta su. Kofur Yohanna, ya yi amfani da wannan damar ya yi godiya ta musammam ga maigidansa wanda shi ne DPO na Gombe Umar Kabir Faruq, (Singam) na yadda yake ba shi shawari da kuma taimako wajen gudanar da wannan ayyuka nasa inda yace da ba dan da yarda sa da kuma shawarin sa ba da ba zai iya ba.

Daga na sai ya nemi al’ummar jihar Gombe da su sa shi cikin addu’a domin ya lashi takwabi sai ya kawo karshen wadannan barayi har ma da wasu yan ta’adda a Gombe duk da kasancewar sa qaramin dan sanda amma aiki ba daga karami ko babba yake ba zuciya ne da sa kai. Sannan sai ya godewa shi kan sa Kwamishinan yan sanda bisa wannan karamci da ya yi masa a gaban dubban yan sanda yan uwan sa inda ya yi fatan bayan wannan karamci a kara masa girma.

2019: Har Yanzu Ina Jiran Lokaci Kan Yiwuwar Takarar Shugaban Qasa Ci Gaba Daga Shafin Farko

ba wai abin da muke so ba; ganin mun kasance wadanda suka wuce iyakokinsa da dogara da wani abin da ba zai kai mu ga gaci ba. Ba shakka mu na fuskantar kalubale mai yawa, sakamakon sakacin da mun kayi da watsi da bin hanyoyin magance

wadanan matsaloli, tun basu kai haka ba. Yanzu lamarin yafi karfinmu, sai mu koma ga Allah don neman yardarsa da gafara tare da neman sauki akan wannan masifar wadda muke ciki da wadda take gabanmu” Inji Bafarawa. Ya roki matasan yan kasuwar dasu kara azama ga tsayawa akan neman hakkinsu

ta hanyar bunkasa kasuwanci da hulda ta gari da al’umma don ciyar da jahar Sokoto da kasa baki daya. Ya kuma nuna godiyarsa dangane da sha’awar da suka nuna da soyyayar da suke yi masa, tare da basu tabbacin kofarsa da zama bude ga bayar da shawara ko taimakawa ga ci gaban jahar baki daya.

Tun da farko a jawabinsa, shugaban gamayyar Kungiyar Matasan Yan kasuwa ta jahar Sokoto, Alhaji Bello Abubakar ya nuna godiyarsa da jijjina ga tsohon gwamna Attahiru Bafarawa saboda irin gudumuwar da ya bayar ga ci gaban jahar Sokoto mussaman a fannin kasuwanci, siyasa da ci gaban al’umma.

Alhaji Abubakar ya nemi tsohon gwamna Bafarawa da ya fito ya amsa kiran jama’a ga tsayawa takarar neman shugabancin Najeriya, don ganin kusan mafi rinjayen masu neman wannan mukami a yanzu basu kai ga irin kwarewarsa da kwazonsa ga samar da ci gaban da al’umma da kasa baki daya ba.

Babu Bashi Tsakanin Tambuwal Da Manoman Shinkafa Na Jihar Sokoto –Qungiyar RIFAN Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja

Gwamnan jahar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya zarce duk sauran gwamnonin jihohin Nijeriya da muke dasu a yanzu wajen bayar da muhimmin tallafi ga manoman shinkafa bisa kyautatawa da karfin guiwa a cikin dukkan gwamnonin Nijeriya. Wannan ya sanya manoman shinkafa a jihar Sokoto basu da wani bashi ko karafi garesa dangane da tsarin da yake bi wajen ganin sun amfana ga ayyukan bunkasa noman abinci da samar da inganttacen tsari garesu. Shugaban Kungiyar Manoman Shinkafa ta kasa, RIFAN bangaren yankin karamar hukumar mulkin Gwadabawa a jihar Sokoto, Alhaji Musa Lumu Gwadabawa

ya baiyana haka a garin Sokoto jim kadan da kamala taron masu ruwa da tsaki ga bunkasa hanyoyin noma kayan abinci da noman shinkafa na jihar Sokoto. Alhaji Musa Lumu wanda har ila yau yana cikin manyan manoman alkama da rogo a kwamtin kasa ya baiyana irin tallafi na kwarin guiwa wanda gwamna Tambuwal ya bayar ga manoma a jihar Sokoto ya kara taimaka musu da muhimmin karin karfi wajen ganin an bunkasa noma, mussaman irin na shinkafa, abin da a zahiri yayi banbanci da sauran irin ababen dake faruwa a wasu jihohin kasarnan. Ya baiyana cewar ko kadan basu da wani korafi daga kulawa da akeyi musu da dimbin gudumuwar gwamnatin jihar Sokoto na samar da takin zamani da iraruwa kyauta ga manoman

shinkafa kari da sauran tallafi da gwamna Tambuwal yayi ga manoman shinkafa. Haka ma an samar musu da injunan ban ruwa har guda dubu biyar aka sayar musu akan farashi mai rahusa na naira dubu goma, sabanin naira dubu arba’in da ake sayarwa a kasuwani. Wannan tallafin da mai girma gwamna Tambuwal ya bayar ga manomanmu, inda har manoma kusan dubu hamsin yanzu haka suke cin moriyar wannan tallafi a kananan hukumomin mulki 23 na jihar Sokoto; ni kaina an bani daruruwa na rarraba ma yankin Gwadabawa don bunkasa noman shinkafa, hakan kuma ya taimaka matuka, inji Musa Lumu.. “Hakika mun kara samun karfin guiwa fiye da sauran lokuta na gwamnatocin da suka gabata, mussaman idan anyi la’akari da

yadda ya hana ayi amna coge ko kara farashi ga kayyakin da ake tallafawa manoma a wannan zamani. Za mu ci gaba da baiwa gwamna Tambuwal da gwamnatinsa goyon baya tare da fatan alheri dangane da kokarin bunkasa aikin noma a dukkan yankunanmu don ciyar da kasa gaba baki daya” Inji Musa Lumu Alhaji Musa Lumu wanda kuma tsohon shugaban karamar hukumar mulkin Gwadabawa ne ya nemi kyakyawan hadin kai da goyon baya ga al’ummar jihar Sokoto dake fatan ci gabanta akan kudurorin gwamna Aminu Waziri Tambuwal na bunkasa nomad a kyautata ma manoma. Haka ma ya nemi Gwamna Tambuwal da ya kara himma ga ayyukan bunkasa aikin gona tare da samar da sabbabin dubaru

na ciyar da manoma gaba, mussaman noman alkama da na rogo wadanda zasu kawo Karin arziki da ci gaba ga jihar da kasa baki daya.

• Shugaban RIFAN, Alhaji Musa Lumu Gwadabawa


Babban Labari A Yau LAHADI 01.04.2018

5

’Yan Boko Haram Ba Su Ci Zarafinmu Ba –Fatima Xalibar Dapchi

LEADERSHIP A YAU LAHADI ta sami zarafin ganawa da xaya daga cikin ’yan matan garin Dapchi na jihar Yobe, FATIMA ADAMU, waxanda ’yan Boko Haram su ka sace a makarantar kwana makonnin baya, amma su ka dawo da su a makon jiya bayan cimma shiga tsakani da gwamnatin tarayyar Nijeriya a wani irin yanayi mai xaure kai. “A gaskiya mun ga tashin hankali. Mun shiga ruxami ba xan kaxan ba. Sai mu ka fauwala al’amarin ga Allah. Mun gode Allah da ya nufa a ka dawo ma na da ’ya’yanmu. Abin ya na da xaure kai, domin a gaskiya irin wannan xin kam abu ne da ba mu tava ganin irinsa ba kuma ba mu yi tsammaninsa ba; a ce ’yan Boko Haram sun zo sun sace ’yan mata kuma a qarshe su dawo da su, ba su doki kowa ba, ba su zagi kowa ba, har a na gaggaisawa da su. Shi ya sa wasu su ke ganin kamar akwai wata qullalliya ta ’yan siyasa a ciki,” in ji Malam Inusa Tela, xaya daga cikin iyayen xaliban da a ka sace xin. A ganawarta da wakilin LEADERSHIP A YAU LAHADI, HARUNA AKARADA, ya yi da ita, xaya daga cikin ’yan matan mai suna Fatima ta ce, ’yan Boko Haram xin ba su ci zarafinsu ba. Ga yadda hirar ta kasance: Za mu so ki faxa mana sunanki. Sunana Fatima Adamu. Ajinki nawa? SS1. Me za ki iya tunawa ranar da waxancan mutanen su ka zo su ka tafi da ku? Tara mu su ka yi a jikin makarantar tamu su ka ce, mu shigo mota xaya bayan xaya. Su ka ce ma na taimakonmu za su yi; wai a na kashe mutane a gari. Da su ka ga ba mu da niyyar shiga, sai su ka ce, ‘mu na iya kashe ku mu yi tafiyarmu’. Sai mu ka shiga xaya bayan xaya. Mu na tafiya ne a ka tsaya a ka sauqe waxanda su ka mutu a cikin namu. Daga nan ne mu ka shiga ruwa mu ka cigaba da tafiya. Mutum nawa ne su ka mutu a cikin naku? Mutum biyar. Ina su ka ajiye su? A’a, wallahi ban san wajen ba. Binne su a ka yi? Eh, binne su a ka yi. An yi masu sallah? A’a. Kun san su waxanda su ka mutu xin? ’Yan uwanmu ne xalibai.

Kun kai nawa waxanda a ka tafi da ku? Mu 110 ne ko 107 su ka tafi da mu. Bayan an sake ku, ina kuma a ka kai ’yan SS3 da su ke jarrabawa? Garin Guru a ka kai su. Me su ke faxa maku lokacin da ku ke hannunsu? Su na yi ma na wani wa’azi ne; wai a kan a na shari’a ba da Qur’ani ba da sauransu. Wai su sai an daina shari’a da ‘constitution’, an koma yi da Qur’ani. Wai sai sun yaqi wannan. Su ka ce kuma wai a bar karatun boko; wai boko ba shi da kyau, shi ya sa. Su wai ba sun xauko mu ba ne don su cutar da mu; kawai wai don saboda mu bar boko ne. To kun tava roqon su cewa, don Allah su sake ku su mayar da ku gidajen iyayenku? Eh. To, me su ka ce maku? Sai su ka ce, wai za su mayar da mu hannun iyayenmu. Za su maido da mu saboda mu ’ya’yan masu sallah ne. Su ka ce, wai su da ma ba sun kamo mu don su riqe mu ba ne; saboda wai akwai ’yan uwansu a hannun wannan gwamnatin ne. Su ka ce wai saboda a sakar masu ’yan uwansu ne su ka xauko mu, mu ma.

Ba su yi maku waxansu abubuwa na cin zarafi ba ko zagi ko tozartawa? A’a, ba su yi ma na ba. Guntun ’yan uwanmu su sun bazu a cikin jeji su ka gudu su ka ce su za su dawo gari. Su ne da a ka kamo su a ka yi masu bulala. Waxansu an yi mu su bulala 50, wasu 30, wani 20. Haka a ka yi mu su. Matan? Eh. Su nawa ne su ka gudu? Sun kai su 20. Sun xauka ba nisa kenan? Da su ka gudu sun haye ruwa guda xaya, xaya ruwan ne da su ka shiga su ka gagara hayewa, sai su ka zauna. Shi ne ruwan da mu ka shiga tun da Isha’i sai da Asuba mu ka sauka. A nan ne su ka zo su ka dawo da su. Da a ka dawo da ku Dapchi, an kai ku Abuja. Me za ki iya tunawa kun yi a Abuja? A Abuja mu dai da mu ka je an kai mu asibiti an gwargwada mu, an ce idan ka na jin wani abu ya na damun ka, ka faf-faxa. Duk a ka yi ma na ‘test’ a ka ba mu magunguna. Shi ne kawai. Da ku ka gana da shugaban qasa, me ya faxa mu ku? Eh, mun gana da shi; ya ce ma na

• Fatima Adamu

kar a bar makaranta. Ya ce a koma makaranta. Akwai wani taimako da su ka yi mu ku su gwamnati, bayan magunguna da a ka ba ku? Eh, an ba mu hijabai, an ba mu kayan kwalliya da sabulai da man shafawa da su ‘brush’ da makilin da turmin zani da kayayyaki dai. To, mun gode qwarai da gaske. Mu ma mun gode.

Kalaman T.Y Danjuma Na Da Tsoratarwa Da Ban Mamaki, In Ji Fada Shugaban Qasa Daga Khalid Idris Doya, Abuja

Fadar shugaban qasar Nijeriya ta misalta kalaman da tsohon Ministan tsaro, Janar Theophilus Xanjuma, na cewar ‘yan Nijeriya su fito su baiwa kawukansu kariya daga masu kisan jama’a, a matsayin kalamai masu xumbin ban mamaki da kuma tsoratarwa. Idan za a iya tunawa, shi dai tsohon Ministan tsaron, TY Danjuma ya bayyana hakan ne a kwanan nan a lokacin da

ke gabatar da jawabi a jami’ar Taraba, inda ya ke bayyana wa ’yan Nijeriya cewar su fa tashi tsaye domin kare kawukansu daga makasa, har ma ya ce rundunar sojin qasar nan ba ta shirya ko yunqurin kare su daga makasa ba. A jawabin da fadar shugaban qasar ta fitar mai xauke da sanya hanun babban mai tallafa wa shugaban Nijeriya kan hulxa da ’yan jarida, Malam Garba Shehu ya ce, masu aikata aikin ashsha na ta’addanci za su yi amfani da waxannan kalamai na TY wajen lalata

wa jama’ar da ba-su ji-ba-ba-su-gani ba. Har-ila-yau kuma, ya jinjina wa dakarun sojojin Nijeriya a bisa qoqarin da suke yi na kiyaye doka da kuma oda a faxin Nijeriya. Mai magana da yawun shugaban qasar, ya bayyana cewar babu fa wata qasa da ta isa ta samu nasara a sa’ilin tana faxa da sojojinta. Ya bayyana cewar gwamnatin tarayya tana fata na gari a wajen ‘yan qasa da cewar ba za su tava rungumar hanyar da ka iya jawo wa qasar barazana ta fuskacin tsaronta ba.

Garba Shehu ya bayyana cewar sun ji matuqar mamaki da takaicin kalmomin da TY Danjuma ya bayyana a kan hidimar tsaron qasa, yana mai qira ga sojojin Nijeriya da su ci gaba da qoqarinsu na wanzar da zaman lafiya da ci gaban qasa a kowani bigire. Ya kuma sha alwashin cewar gwamnatin tarayya ba za ta zura ido wasu na neman kawo wa tsaron qasa barazana ba; don haka ya nemi masu munanan manufa da su gaggauta canzawa domin wanzar da zaman lafiya a faxin qasar nan.


68 TALLA TALLA

A Yau Lahadi 1 Ga Afrilu, 2018 (14 Ga Rajab, 1439) A Yau Laraba 28 Ga Maris, 2018 (10 Ga Rajab, 1439)


A Yau Lahadi 1 Ga Afrilu, 2018 (14 Ga Rajab, 1439)

Burinmu Shi Ne Mu Sauqaqa Muku

Ba a chaj in kuxin on ka cire d i j a h c a a B saqonnin watin waya kuxi daga ak na wasu banku

Da zaran an buxe asusu da mu, za a morewa rashin chaji idan mutum ya cire kuxi a akwatin wasu bankuna, haka kuma ba za a riqa cire kuxin saqonnin waya ba.

Domin cimma nasara a hada-hadar banki, ka yi mu’amala da bankin Sun Trust a Yau Ziyarci: www.suntrustng.com

TALLA 7


8 LABARAI

A Yau Lahadi 1 Ga Afrilu, 2018 (14 Ga Rajab, 1439)

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Qarawa Jami’anta 766 Girma A Kebbi Daga Umar Faruk, Birnin-kebbi

Rundunar ‘Tan sanda ta qasa reshen jihar kebbi ta gudanar da bukin Karin girma ga jami’anta 766 a rundunar ta jihar kebbi a jiya a Birnin-kebbi. Taron bukin an gudanar da shine a hedkwatar rundunar ta ‘yan sand da ke a Birnin-kebbi a jiya. Da yake gabatar da jawabinsa kafin soma bukin na karin girma ga jami’anta rundunar, kwamishina mai kula da rundunar ta jihar kebbi Alhaji Ibrahim M. Kabiru ya bayyana cewa a cikin kuduran insifeto janar na qasa Ibrahim Kpotun Idris shine ya tabbatar da walwala da jindadin jami’an rundunar ta ‘yan sandan qasar nan da kuma biyan su albashi a cikin lokaci, saboda haka ya karima jami’in rundunar jihar kebbi 766 girma Kama tun da ga makamin insifeto har zuwa ga Marar mukami a

rundunar kawai ta jihar kebbi. Jami’an da suka samu Karin girman sun had da masu mukamin sajan zuwa insifeto jami’i 181 da kuma kofurori zuwa mukamin sajan 585 duk a rundunar ta jihar kebbi. Kwamishinan rundunar CP Ibrahim Kabiru ya ci gaba da cewa “karin girman anyi shine domin a karama jami’an ‘yan sanda kwarin gwiwa kan gudanar da aiki xansan a qasar nan”. Hakazalika ya yi amfani da wannan dama domin nuna jindadinsa da kuma godiyarsa ga jama’ar jihar kebbi kan irin taimako da kuma goyun baya da suke bayar wa wurin bada bayanan sirri ga jami’an • A lokacin da ake yi wa wasu jami’an ‘yan sanda qarin girma a Kebbi rundunar ta ‘yan sandan jihar, domin bisa ga bayanan jaha zaman lafiya da kuma xansanda a qasar nan da kuma gudanar da ayyukkaansu da a ke bayar wa ta hakan harakar tsaro”. Daga nan kwamishinan ya kamar yadda dokar aikin ne aka samu nasarori ga rundunar, inda jihar kebbi ja kunnuwa jami’an rundunar xansanda ya tanadar. Taron bukin karin girman ta zama xaya daga cikin da su ci gaba da zama jakadu jahohin da sukafi kowace na gari a cikin aiki gidan ya samu halartar dukkan DPO

DPO da mataimakansa masu Kula da qananan hukumomi guda 21 da ke akwai a jihar ta kebbi da kuma sauran wasu manyan ‘yan sanda da ke a rundunar ta jihar kebbi.

Kwalara Ta Kashe Mutane Biyar Ta Kwantar Da 70 A Yobe Daga Muhammad Maitela, Damaturu

Varkewar cutar Kwalara, wato amai da gudawa, a Gashuwa, cibiyar qaramar hukumar Bade da ke jihar Yobe, ya kwantar da mutane sama da 70, yayin da kuma sama da mutum biyar suka rasa rayukan su, ta dalilin cutar. Bayanai daga jami’an kiwon lafiya a qaramar hukumar, sun bayyana cewa tun a farkon wannan makon aka gano vullar cutar kwalarar (ranar talata). Dakta Muhammad Bello Kawuwa, shi ne kwamishina a ma’aikatar kiwon lafiya a jihar Yobe, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa, tuni

ma’aikatar lafiyar ta xauki matakin tura ma’aitanan ko-ta-kwana. “Tun bayan yadda muka samu labarin varkewar cutar kwalarar (amai da gudawa) muka xauki qwaqwwaran matakan shawo kan mtsalar, ta hanyar tura kwamitin qwararru na ko-ta-kwana domin bin diddigin musababbin lamarin da matakan xauka domin daqile kwalarar. Sannan kuma gwamnatin jihar Yobe ta xauki nauyin bayar da magunguna ga waxanda suka kamu da cutar”. Dakta Kawuwa ya sake bayyana cewa, “kawowa yanzu ba zan iya tabbatar maka adadin waxanda

suka rasu ba, saboda muna sauraron rahoton kwamitin. Kuma da zarar mun tattara bayanan zamu sanar daku”. Inji Kwamishinan Haka zalika kuma, Yerima Girki shi ne mataimakin kodinata (Coordinator) a ma’aikatar kula da kiwon lafiya, a matakin farko (Primary Healthcare) a qaramar hukumar Bade (Gashuwa), kuma ya tabbatar wa wakilin mu a jihar Yobe, wannan batun, tare da qarin hasken cewa, jami’an kiwon lafiya a matakin farkon suka xaukar matakan shawo kan cutar. “Matsalar amai da gudunawar ta fi shafar unguwannin Katuzu,

Sabon Gari da unguwar Sarkin Hausawa dake nan cikin garin Gashuwa, cibiyar qaramar hukumar Bade. Kuma mun zagaya waxannan shiyoyi guda uku tare da faxakar da jama’a dangane da wannan cutar ta kwalara. Kuma a cikin asibiti, inda aka kwantar da waxanda suka kamu da cutar, shima akwai ingantattun matakan hana yaxuwar matsalar”. “Mun ankarar da jama’a kan cewa su kula da tsabtace muhallin su, kuma a kula da tsabtar abincin da ake ci. Haka kuma mun gaya musu kan cewa su xauki matakin kai rahoton duk wasu alamun da suka gani dangane da cutar, zuwa ga

cibiyoyin kiwon lafiya, cikin gaggawa. Sannan kuma mun rarraba magungunan riga-kafin cutar, domin daqile yaxuwar matsalar “. Inji Yeriman. Malam Hassan Gadaka, shi ne babban jami’in tattara bayanai a babbar asibitin Gashuwa, (General Hospital) ya tabbatar wa Leadership A Yau cewa, “kawowa yanzu, cutar amai da gudawar ta kwantar da mutane 70, kuma mutum biyar daga wannan adadin sun rasu a asibitin- banda wasu da suka rasu a gari. Kuma mun sallami wasu daga asibitin, kuma yanzu haka akwai mutane 35 waxanda ake ci gaba da kula dasu”.

Kotu Ta Yanke Wa Wani Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya A Bayelsa Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Babban kotun tarayya da ke da matsuguni a Yenagoa ta jihar Bayelsa a qarqashin mai shari’a Justice Emmanuel Ogola ta yanke wa wani matashi mai shekaru 38 haihuwa wato Diepreye Sunday Olayo kisa ta hanyar ratayewa. Diepreye Sunday Olayo, wanda ake zarginsa da kasancewa cikin qungiyoyin asiri daban-daban, shine ya

yi sanadin mutuwar wani mai suna Being Ilebiri, wanda aka kashe tun a ranar 6 na watan Disamban 2011, a hanyar RBIs da ke kan titin Mechanic a garin Amarata, ta Yenagoa, da ke jihar. Mai shigar da qara a gaban kotun, Andrew Seweniowor Arthur, ya gabatar wa kotun shaidunsa da kuma bayanan da suke tabbatar da cewar Olayo shine ya kashe Ilebiri a wannan ranar da suke zargin.

Gabanin alqalin ya yanke hukuncin, Justice Emmanuel Ogola ya shawarci vangarori biyun da cewar suna da zavin jewa babban kotu ta gaba da nasa idan basu amince da hukuncinsa da ya zai yanke ba. Alqalin ya ce a bisa samun shaidu da kuma gamsuwa da shaidun da suke tabbatar da wanda ake zargi ya yi kisan ne ya sanya kotun ta yanke masa hukuncin kisa “A bisa haka,

bayan samun shaidu da kuma hujjoji da suka tabbatar da wanda ake zargi ya yi kisan kai. A dalilin haka, ba za mu tsaya wahalar da kanmu ba, za mu yi aikinmu yadda ya dace. A don haka, na yanke wa wanda ake zargi hukuncin mutuwa a sakamakon laifinsa,” In ji Justice Emmanuel Ogola. Sai dai lauyan wanda ake zargin na da zarafin xaukaka qara idan bai gamsu da shari’ar ba.

• Barista Ibrahim Yakubu Umar


9

A Yau LAHADI 01.04.2018

Jiya Da Yau Adabi/Al’ada/Zamantakewa/Nishaxi

Nazari Kan Asalin Hausa Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN 08060869978 .......................................................................

Asalin Jinsin Hausawa Ta na iya yiwuwa, littattafan mu na addini sune suka fara kawo mana tarihin asalin jinsi da rarrabuwarsa. Saboda wannan wani tarihi ne daya faru wanda indai ba baiwa mutum iliminsa akayi ba, zaiyi wuya ya iya wassafa yadda tarihin ya faru. An ce Annabi Adamu da Matarsa Hauwa’u sune mutane na farko a duniya. Sune suka rinka haihuwar ‘ya’yaye biyu-biyu daki-daki, tare da haɗa aure tsakanin mace ɗaya da namiji ɗaya daga tagwaye mabanbanta, watakila wannan haihuwar tasu ita ce asalin qabilu, gamin gambizar kuwa shine asalin dangantakar jinsi da kuma rarrabuwarsa. Idan ma ba haka ba, ko labarin Annabi Nuhu A.S ya nuna cewar ya haifi ‘ya’yaye uku ne. Xakace Hamu shine ya haifi bakin mutum na farko a duniya, daga jikinsa kuma zuriyar Hindu ta fito. Samu shine na biyu wanda akace daga jikinsa turawa suka fito, sai kuma Yafisu wanda akace daga tsatson sa kabilun birnin Sin suka ɓulɓulo. Don haka, tanan kaɗai muna iya hasashen cewa cakuɗuwa ta silar auratayya da sauran kabilu ne silar haifar da wasu sabbin kabilun. Babban labarin dai shine, akwai ilimi na zamani dake bada damar fahimtar kwayoyin halitta tayadda har ake gane wane nada alaka ta jini da wane, da haka kuma muke son fahimtar hausawa da asalin waɗanda suke da alaka dasu, in yaso daga bisani sai mu kwatanta kokarin bin diddigin shekarun da rarrabuwa ta auku a tsakanin su. A bisa wancan ilimi na kwayoyin halittu (Genetic), dukkan wani ɗan adam dake doron kasa nada kwayoyin halitta waɗanda ana iya cewa kashi 99.5 na zubin kamanceceniyarsu ɗaya yake da juna. Wannan ke tabbatar mana da wancan ilimin da aka saukar mana cewa mutum ɗaya ne asalin ɗaukacin mutanen duniya, daga gareshi dukkansu suka fito. Abu na gaba shine, kusan muna iya cewa a yanzu babu wata kabila da zaka samu ‘yan cikinta da kwayoyin halitta zubi ɗaya tsura, sai dai zaka samu kaso sama da hamsin iri kaza ne, sannan da wasu kashe-kashen na sauran kabilu kaɗan-kaɗan aciki. Wani masani Ronald Fisher yayi bayani gwargwadon yadda zamu gane bisa tafarkin masanin ilimin kwayoyin halitta Gregor Mendel a littafinsa mai suna ‘The Genetical theory of Natural

Selection’ inda yake cewa dalilai biyu ne kesa wannan cuɗanyar tsakanin kwayoyin halittu. Dalili na farko shine, yanayin yadda ake gadon su kansu kwayoyin halitta na sanyawa na wancan yasha banban dana wannan koda kuwa uwa ɗaya uba ɗaya suke, domin ko a siffance, akan iya ganin uba da ‘yayansa uku, yaro na farko yayi kama da mahaifiyarsa, na biyu yayi kama da ubansa, yayinda na uku ya ɗauko kamannin kakansa. Dalili na biyu kuwa shine cuɗanyuwar kwayoyin haluttun ta hanyar auratayya. Watau, ɗan wannan kabila ya auri yar waccan kabila. Sai kaga kwayoyin halittar waccan kabila dana wancan sun haɗu a kabila xaya, amma sai akalli inda sukafi rinjaya ayi hukunci dashi. Asalin Jinsin Larabawa Da Yarabawa Ya na da kyau, kafin mu fahimci asalin jinsun mu mufara fahimtar ilimin dake cikin asalin kabilu makusantan mu. Su dai Larabawa wani bincike mai taken ‘National Geographic’s Genographic’ da aka gudanar a shekarar 2005 ya bayyana cewa akalla duk wata kabila balarabiya ta fito daga cikin yankuna huɗu ne. Yanki na farko shine Arabia Yanki na biyu shine Arewacin Afirka Yanki na uku shine gabashin Afirka Sai yanki na huɗu watau Asia. Sai wannan binciken ya ɗauki wasu kasashen larabawa tare da bayyana yadda asalinsu ya kasance. Misali, Daga ciki an ɗauki kasar Tunisia, wadda akace kaso 88 na kwayoyin halittar mazauna kasar ya nuna cewar suna da alaka ta jini da sauran larabawan Arewacin Afirka. Amma akwai sirki na larabawan Arabia da kaso 5, da sirki na turawa da kaso 4, da kuma sirkin bakaken fata mazauna afirka ta yamma da kaso 3. Wannan sirkin na nuna cewar an samu auratayya da gamin gambizar kwayoyin halittu shekaru da dama da suka wuce a tsakanin jinsosin da aka zayyana a sama. Labarin kusan haka yake ga Yarabawa domin kuwa wani bincike da wasu masana Adebuwale Adeyemo na jamiar Ibadan, da Chenchen Yianxiu na Cibiyar bincike ta ‘National Human Genome’ da kuma Charles Rotimi na jamiar Horward suka gudanar, sun samu cewar kwayoyin halittun Yarabawa, kusan ɗaya ne dana kabilun Igbo, Akan, da Gaa-Adangbe. Hakan na iya nufin cewar Asalin kabilun daga mutum ɗaya suke, watu daga ‘ya’yansa ko jikokinsa aka samu rarrabuwar waɗannan kabilu har ma

dana yare, tunda binciken yayi hasashen cewa duk yarukan kabilun suna da alaka da juna, asalinsu guda ne, daga bisani suka rarrabu, duk da dai binciken bai nuna sauran kabilun da suka shigar da kwayoyin halittun su cikin na waɗannan ɗinba.

na asali tare da fantsamuwa a sassan duniya musamman afirka ta yamma. Daga waɗannan zuriyar ne kuma akafi kyautata zaton bakaken fata Hausawa sun fito. To amma dai, munfi damuwa dabin diddigin salsalar da bata wuce shekaru dubu biyu zuwa biyar ba, domin ita muka fi gaskata kudantuwar ta garemu. Babu jimawa, farfesa Umar Elzakzaky Al-Bahaushe yayi hasashen cewa kwayoyin halittun hausawa dana tsoffin misirawa sunyi kamanceceniya, har ma yace yana kallon kamar firaunan dayayi zamani da Annabi Musa A.S bahaushe ne. Ina ga za mu qaru da ilimi idan mu ka kalli zancen nasa da kuma martanin hujjoji da masana su ka ba shi dangane da musanta wannan magana tashi.

Jinsin Hausawa Mu dawo kan asalin jinsin Bahaushe. Abinda wani bincike dangane da bakaken fata yayi hasahe shine shekaru masu yawa da suka gabata, mafi yawan bakaken fata suna wuri ɗaya ne a zaune, kuma tana iya gaskatuwa Cewa mutum ɗaya ne uba wanda daga jikinsa duk kabilun bakaken fata suka fito. Amma dai, anyi hasashen cewa tun shekaru dubu sittin zuwa dubu tamanin baya bakaken fata suka soma baro wancan mazaunin nasu

Arewa HipHop Manyan Arewa Ba Sa Ba Mu Qwarin Gwiwa –X_Dough Shafi na 22

K ANNY WOOD

Dutsen Dala Da Na Gwaron Dutse Ma Film Village Ne –Shehu Kano Shafi na 16

Kaucin Kaba

Sarqaqqiya Shafi na 20


A Yau LAHADI 01.04.2018

10

Wa’azin Kirista

Tare Da Fasto Yohanna Y.D. Buru 0806 871 8181 yyohanna@gmail.com

An Siffanta Mutum Cikin Zunubi

Wurin Aratu – Zabura 51:5 “Ga shi, cikin migunta aka sifanta ni, Cikun zunubi kuma uwata ta dauki cikinsa” (Zabura 51:1). “Babban Magana wai mahaukaci ya hau kura”. Na fara da wannan Karin maganan ne, domin in mun dauki lokaci muka dubi halin Dan adam, to za mu gane da dalilin da na fara da karin Maganan. Wani mawakin Hausa watau Alhaji Dan Maraya Jos, Yayi waka da cewa “Da Adam maiwuya gane Hali.” Ashe, wannan wakar na tafiya daidai da wannan ayar. Mai Zabura watau sarki Dauda ya dauki lokacinsa ya bayyana mana yadda shi kansa sarki Dauda da kuma kowane Bil Adama dukan an sifanta su a cikin mugunta. Sai da ya cigaba da bayyani da cewa “Cikin zunubi kuma uwata ta dauki cikinsa”. Anan muna tunani sarki Dauda mai zabura na nufi da cewa bayan da Adamu ya yi zunibi, to duk Bil Adama da aka haifesu bayan nan, dukansu sun gaji zunubi daga Annabi Adamu. Ashe zunubi gado ne daga Adamu zuwa ga dukan Bil Adama. Kuma a rayuwan kowane Bil Adama akwai cikakun shaidu ko hujjoji da suka gamsar damu cewa kowane mutum mai aikata zunubi ne ko mugunta. Manzo Bulus ya ruwaito wa mutanen Romawa da cewa: “Da shi ke dukan mutane sun yi zunubi sun kasa kuma ga darajar Allah” (Romawa3:23).

Amma menene dalilin da kowane Biil Adama ya yi zunubi ya kasa kuma ya darajar Allah? Mai karatu zai iya tambaya da cewa me yayi zafi haka? To gaskiyan maganan shine, masu iya magana sun ce, Tuna baya shine roko.” In mun tuna da baya, to zamu gane da cewa Romawa 3:23 na mayar da mu baya ne, da kuma tunatar da mu da tarihin zunubi. A cikin Littafin farawa sura 3, Allah Ubangiji ya bayana mana assalin zunubin Bil Adama. Daga littafin farawa sura 3 sai muka gan tabbacin wannan maganar a littafin farawa sura 8 wanda ke cewa: “. . . . . . Gama tunanin zuciyar mutum mugunta ne tun daga kuruciyassa. Ba kwa za ni sake bugun dukan mai – rai da dai, yadda na rigaya na yi” (Farawa 8:21b) Manzo Bulus ya tabbatar mana da gaskiyar wannan maganan da marubucin littafin Farawa sura 3 ya ruwaito. Manzo Bulus ya nuna mana da cewa, ai tawurin zunubi na farkon da iyayenmu na farko suka aikata shine ya shafi kowane Bil Adama. Manzo Bulus ya tabbatar mana da cewa, sanadin farkon zunubi da Adamu da Hauwa’u suka aikata shine ya kai dukan ‘Bil Adama ga faduwa daga darajar Allah (Roman 3:23).’ Shi kuma sarki Dauda mai zabura ya fabimci littafin Farawa 3 akan cewa, “Cikin mugunta aka sifanta shi, cikin zunubi kuma uwata ta dauki cikinsa.” Watau tun kafin shi

sarki Dauda ya shigo duniya, ya shiga duniya cike da zunubi da ya gada daga iyayen sa. Watau duk, kowane irin Bil Adama an sifanta shi a cikin mugunta ko zunubi ne, kuma an dauki cikinsa cikun zunubi ne. Domin da haka baa bin mamaki ba ne, in Bil Adama sun aikata zunubi. Ina an aikata zunubi, to alama ce kowane mutum ya gaji zunubi. Duk wanda ya aikata zunubi cikon nassi ne, sai dai kawai kowa ya tuba ga Allah domin samun gafaran zunubai. Dora da wannan, Farawa 8:21 na kara fahimtar da mu, akan gadon zunubi da ya kai dukan Bil Adama har ya baro! A littafin Farawa 8:21 an kara tabbatar mana da cewa; “tun daga kuruciyassa, tunanin zuciyar mutum mugunta ne” Abin tambaya anan shine, in mutum ko Bil Adama tunanin su tun daga kuruciyarsa mugunta ne, to wanene ya koya wa mutum ko karamin yaro yin mugunta ko zunubi?. In kwa babu wanda ya koya wa wani aikata mugunta ko zunubi tun a yarantaka, to ashe zunubi na na cikun kayan gado da ko wane Bil Adama ya gack tun daga farkonsa. Shi kuma Annabi Irimiya, ya kawo mana wata tabbaci akan matsayin zuciyar mutum ko Bil Adama kama yadda littafin Farawa 8:21 ya tabbatar mana game da yanayin zuciyar mutum ke tattare da rikici ko zunubi ko mugunta. Ga abinda littafin irimiya na

cewa: “Zuciyar tafi komai rikici, ciwuta gareta kwarai irin ta fidda zuciya: wa za ya san ta? Ni Ubangiji mai – bimbinin zuciya ne, ina gwada ciki, domin in saka ma kowane mutum bisa ga ayukansa, bisa ga yayan aikinsa” (Irimiya 17:9 – 10). In wannan shine matsayin zuciyar mutum ko Bil Adama, to ashe Allah ya tabbatar mana da matsayin mu akan maganan zububi. Allah ne da kansa ya kara tabbatar mana da cewa, “Zuciya ta fi komai rikici”. Domin da haka abin tambaya anan shine, Allah na karaya ko kuskure? Amsan shine Allah Ubangijinmu baya karya ko kuskure. Wannan matsayin da Allah ya nuna mana game da matsayin zuciyar mutum ya kamata ya zama mana cikakan darasi ne, domin kowa ya gyara halinsa. Wannan kiran domin gyara hali me. Wannan kira ga gyara hali shine tuban gaskiya. Kowane mutum ya yarda da matsayinsa Allah cewa mutum ne ya fada ga darajar Ubangiji Allah. Mutum ya juyo daga mugunta zuwa neman gafaran zunubai domin samun tsiran Allah daga hallaka, amma ba kame - kame ba. Tuba daga zunubi itace kadai mafitan Bill Adama. Ya Allah ka gafarta mana zunuban mu, ka kuma tabbatar mana da Aljanarmu, Amin Thumma Amin. Shalom ! Shalom!! Shalom!!!


A Yau

11

Lahadi 1 Ga Afrilu, 2018 (14 Ga Rajab, 1439)

KA SAN JIKINKA

Tsokar Jikin Mutum Kowanne gini yana buqatar tubali ko kuma bulo; amma kamar yadda kuka sani, bulo guda xaya yayi kaxan ya gina gida, saboda haka ana buqatar bulalluka. Duniyar jikin ka ginanniyar halitta ce wadda Sarki Gwani ya gina maka da tubali amma na tsoka. Tsokar nama na da matuqar muhimmancin da bazan iya faxar komai ba a rubutu xaya ba, duba da faaxin da take dashi, da kuma qaranci ilimi na. Amma hakan ba zai hana ni tavukawa ba wajen bayyana muku wannan tubali, wato tsokar jikin mutum. Jikin mu yana xauke da tsokar naaman da yawan su ya kai kimanin xari shida da hamsin (650). Wannan qiyasi ne kawai domin babu wani masani da zai bugi qirji ya faxa maka takamaimai adadin yawan tsokar jikin mutum. Kafin muyi nisa, ya kamata mu sani cewa, yadda muke da banbance-banbance a zahiri, kaama daga tsawo, faaxi, yanayin faata, girman jiki da sauran su, haka ma muke da banbanci daga ciki. Za’a iya samu wani yana da tsoka 650, wani 653, wata 649, wani 660, da sauran su. Tsokar jiki, ita ce ke bamu tallafi da taimako wajen motsin gudanar da abubuwan rayuwa take buqata masu yawa kamar waxanda muka saba dasu irin su tafiya, zama, kwanciya, tashi, gudu, tsalle, tsugunawa, daukar kaya, waiwaye, da sauran su. Tsokar nama kuma tana taimakawa wajen gudanar da abubuwan da ba kowa ne yasan tsoka tana taka muhimmiyar rawa a nan ba. Misali : gyatsine, murguxa baki, sigina, hamma, qifce, tauna, haxe gira, da makamantan su. Idan baku manta ba, na yi bayanin tsokokin fuska da suka rabu gida biyu: masu tauna da masu isar da saqon zuciya. Tsokar jiki ta rabu gida uku: 1. Wadda ta haxa qashi da qashi, ta kuma taimaka wajen jumullar motsin jiki (skelatal muscle). 2. Wadda ta ke a shimfixe a cikin gavvai masu hororon bututu kamar su tumbi, hanyoyin jini da sauran su. Ita kuma sunan ta (smooth muscle). Sai kuma ta 3. Itace tsokar da ba’a samun ta a ko ina sai

a zuciya, ana kiran wannan tsoka da (cardiac muscle). Sannu a hankali zamu ga sauran ajin na tsokar dake jikin, amma a yau, zan karkata akalar rubutun ga ajin tsokar da ake samu a sassan jiki da ake iya gani, wato (skeletal muscle). kamar yadda na faxa a baya, tsoka tana cikin qungiyar qwayoyin halittu da suke haxuwa guri guda domin su samar da gava. An raba tsokar jiki wadda take da zane-zane (striations) azuzuwa daban daban, duba da awon su, siffar su, aikin su, dabi’ar su, kamar su, mazaunin su, asalin su, da makomarsu. Zan bada misalan su a nan gaba kaxan. Ajin tsoka dangane da awon su akwai doguwa kamar wata tsoka da ake cewa “sartorius” da take a cinya, wadda ita ce tsoka mafi tsawo a jikin xan adam. Akwai gajeriyar tsoka da ake samun ta a cikin kunne, ana ce mata “stapedius”; Ita ma taafi kowacce tsoka gajarta a jiki. Tsoka mafi girma a jikin mutum ita ce wadda ake zama a kanta; ana Kiran ta da “gluteus maximus”. Ajin tsoka da aka kevance su saboda (kamar su) da wani abu akwai : mai kama da kama da mataji (pectineus) ana samun ta a ciya, mai kama da daalar gyaxa (pyramidalis) a bangon ciki, akwai mai kama da bandeji (splenius) a wuya take, tana taimakawa wajen miqar da kai, da kuma mai kama da mafici (pectoralis major), wadda a ke samu a qirji. Nonon namiji da mace na zaune ne akan wannan tsoka. Ajin tsoka dangane da aikin da suke gudanar wa: akwai masu tanqwasawa wato (flexors) da kuma masu miqarwa wato (extensors). Wannan aji na tsoka an fi samun. Su a damtse, da hannuwa, cinyoyi da kuma qafafuwa. Tun da suna da matuqar yawa, bari mu xauki misalin su guda 2 kawai. Akwai (flexor digitorum superficialis). Ma’ana : (tsoka mai tanqwasa yatsu ta waje-waje). Akwai kuma (extensor digitorum). Ma’ana: (tsoka mai miqar da yatsu). A wasu guraren a jiki, ana samu tsokar nama kaxan, a wasu guraren da yawa, a

Tare da Mustapha Ibrahim Abdullahi 08037183735 musteeibr10@yahoo.com

wasu guraren ma har ruvi 2, ko sama da haka ana samu. Kamar a tafin hannu, akwai tsoka ruvi 5 a wajen, tsoka guda 26 kamar yadda na faxa a baya. A taafin qafa kuwa, akwai tsoka ruvi 4 ne. Tun da Mun ga kaxan daga cikin ajin tsokokin dake duniyar jikin mu, ya kamata muga kaxan daga cikin ayyukan da tsoka keyi a jikin mutum. Na farko dai akwai TALLAFI. Tsoka tana tallafawa kusan duk wata gava ta jiki da ka sani domin wannan gavar ta gudanar da aikin ta yadda ya kamata. Na biyu kuwa shi ne MOTSI. Da taimakon tsoka ne muke iya cikakken motsi kala-kala. Xaukowa ajiyewa,

riqewa, jefarwa, damqewa. Bari ma in tuna muku; da taimakon tsokar dake hannun ku ne kake/kike riqe da jaridar da kake/kike karanta wannan rubutu a halin yanzu. Na uku, daga cikin ayyukan tsoka shi ne KARIYA. A gurare daban-daban a jiki, tsoka na bamu kariya sosai. Kayan cikin mu na rufe da bangon tsokoki da ake kira “anterior abdominal wall”, wanda Aikin sa ne yaba su kariya daga cutuwa. Qasusuwan haqarqari na samun kariya daga tsokar naman da ta rufe shi, kimanin ruvi uku. Mu haxu a wani satin domin ci gaba, da Yardar Mai duka.


12 TALLA 24TALLA

Lahadi 1 Ga Afrilu, Rajab,1439) 1439) Yau 28 Ga Maris, 20182018 (10(14 GaGa Rajab, A Yau ALaraba


A Yau

Lahadi 1 Ga Afrilu, 2018 (14 Ga Rajab, 1439)

TALLA

Gaba dai! Gaba dai “Super Eagles”

Bankin Zenith na taya ‘yan qwallon Nijeriya “Super Eagles”, murna sakamakon nasarar da suka samu ta kai wa gasar Cin Kofin Duniya wanda za a gudanar a qasar Rasha.

13


14

A Yau Lahadi 1 Ga Afrilu, 2018 (14 Ga Rajab, 1439)

Tare da Fadila H. Aliyu Kurfi fadilapeady@gmail.com tweeter @FadilaKurfi

RIGAR ’YANCI Talaka Ba Qashin Yarwa Ba Ne –Anty Kolo HAJIYA ZUWAIRA DAUDA KOLO ma’aikaciyar jinya ce, marubuciya kuma cikakkiyar ‘yar gwagwarmaya da qwato haqqin mata, sannan ta na cikin fitacciyar qungiyar nan ta mata marubuta wacce ake kira da Mace Mutum, kuma ita ce wakilar qungiyar a garin Jos babban birnin jihar Filato. Ga yadda tattaunawarta da wakiliyarmu, FADILA H. ALIYU KURFI, ta kasance: Ko za mu iya jin xan taqaitaccen tarihinki? Sunana Hajiya Zuwaira Dauda Kolo, akan ce Mini KOLO saboda Sunan yarene Yakolo, ni mutuniyar Borno ce gaba da baya, wato ta vangaren mahaifiya da mahaifina. An haifeni a garin Jos , na yi primary da secondary na duka a garin na Jos, daga nan na yi aure, ina aure na cigaba da karatuna har na samu takardar shaidar kammala N. C. E duk dai a garin Jos , bayannan ne na koma na yo health wanda yanzu haka ni ma’aikaciyar jinyace. Wane buri gare ki game da matasan qasar nan? Kishi na ga ci gaban matasa shine... A tallafama matasa ta hanyar basu ilimin Boko, kimiyya da fasaha, Sana,o’in hannu da kuma su ma a tafi dasu a siyasance. Idan aka tafi da su tahaka za a gane abubuwan da za su iya, wanda ake buqatar gyara a cikinsu sai a gyara masu, amma idan aka bar su haka sasakai duk lokacin da suka samu dama ba su iya tavuka komai tunda cen dama ba a koya ma su ba, a saka ma su kishi da kaunar qasarsu shine magana, a jawo su a jika ayi tafiyar nan da su. Wace shawara za ki ba shuwagabanninmu kan hakkonkin al’umma da ke kansu da nauyin qasa da ya hau kansu? Shawara ta ga shuwagabanni kuwa shine, su ji tsoron Allah, su zama ma su adalci da cika alqawurra su za mo masu tuna baya, kar bayan sun ci zave sumanta da talaka, ina so sudinga tunawa cewa talakan shi ya ba da gudummawa kashi 80 aka zave su , don haka bayan sun samu biyan buqata, kar talaka ya zama saniyar ware a tafi da wasu dabam maimakon shi talakan. Meye mahangarki kan makomar siyasar qasar nan? Mahangata kan makomar siyasar nan shiyasa na yi kira ga gwamnatin qasar nan ta buxe qofa ta baiwa talaka da matasa daman damawa a siyasa, kuma idan anyi haka to lallai za’a sami matasa a manya manyan muqamai na qasarnan, wata rana ma sai kaga matashi shine shugaban qasa. Tun da yanzu

matasa sun dage da neman ilimi savanin da, sun yi karatun ta natsu. Kasancewarki mace ‘yar gwaggwarmaya wane buri gare ki? Burina nan gaba shine in kafa wata qungiya ta mata wanda zan dinga koya mu su sana’o’in hannu in sun gama aba su xan qaramin jarin da za su dinga juyawa don su taimaki iyalansu. Yaushe kika fara rubucerubucenki ne kasancewarki marubuciyar litattafan Hausa? Na fara harkar rubutu 2006 abin da ya sa na fara rubutu babba ne domin kuwa duk abinda ya shafi aure da mata to ya tava al’umma ba ki xaya. Lokacin da nake ganin littafan Hausa na kan yi mamaki idan na ga mutane na vata lokaci wajen karantashi ... Sai daga baya dana gwada fara karantawa sai naga ashe sako babba marubuta ke son isarwa ga Al’umma, da ganan ne na fara sha’awar fara rubutu nima domin fara tura sako ga ‘yan uwana mata, misali za kaga mace takai mace tayi zurfin ilimi amma a gidan aurenta akwai matsalar data kasa warwareshi dole sai ta faxa ma qawaye ko iyaye, wanda waxansu qawayen qiris su ke jira su ba ka muguwar shawara. Amma ta rubutu idan kana daki azaune zaka karanta ka warware matsalolinka cikin ruwan sanyi ba tare da kowa ya ji sirrinka ba. Wannan dalilin shiyasa ja hankalina nafara rubutu. Zuwa yanzu littafi nawa ki ka rubuta? A yanzu haka na rubuta littattafai shida uku sun fito uku suna hanya, A cikin wadanda suka fito akwai Mardiyya, Zubar Hawayena, Bulalar Zuciya, sai ukun da suke kan hanya insha Allahu. Wacce shawara gare ki ga matasa ga ba xaya? Shawara ta ga matasa kan su jajirce kan siyasa ...Da farko dai su cire kwaxayi da son abin hannun ‘yan siyasa, su fito da qarfi su yi tsayuwar daka wajen ganin an dama da su kowane fage na siyasar, kuma su dena ma siyasa taka haye ita siyasa ba gadonta ake yi ba, sai an santa ake sanin yadda za a tafi da ita,

• Anty Kolo

karkace wane ya yi wancen ya yi nima kota halin qaqa zanyi maimakon haka su koma su jajirce wajen neman ilimin siyasar da yadda ake tafiyar da ita.

Al’umma za su Bata goyon baya, wata rana sai ka ji ana macece shugabar qasa kowa yasan mata da kula da tausayi. To, Hajiya Zuwaira Dauda mun gode qwarai da wannan shawarwari ga mata da kuma matasa. Ni ma na gode qwarai da wannan dama dana samu a wannan jarida mai albarka, wato LEADERSHIP A YAU LAHADI. Na gode.

Wannan shawara ta yi sosai wace zaburarwar zaki kuma yi ma mata? Zaburawar da zan wa mata ‘yan uwana kan lamarin rayuwa da siyasa shine; Da farko dai su san Allah S.W.T a komi nasu su ji tsoron shi azamantakewar rayuwarsu da kuma a siyasance. Mata dama akwaisu da gwagwarmaya saboda haka suyi tsayuwar daka wajen kare mutuncin kansu su nemi sana’ar dogaro da kai, su tallafama junansu kuma su dinga shiga fagen siyasa ana damawa dasu Shawara ta gaba da zan ba mata shine suma su zage, su fito ayida su karsu ce ni macece ba sai na yi siyasaba, siyasar qasarnan nan gaba zai zama kamar national I’d card ne, wato katin zama xan qasa, wanda in babu shi baka cika xan qasa ba. Uwa itace Al’umma da ita ake ko yi itace tarbiya, don haka in uwata fito ta yi dumu-dumu a siyasa • Anty Kolo


A Yau

15

Lahadi 1 Ga Afrilu, 2018 (14 Ga Rajab, 1439)

SHARHIN FINAFINAI

Tare Da: Saddiqa Habib Abba 09097438402 habibsaddiqa@gmail.com

Sharhin Fim Xin ‘Hangen Nesa’ Daga Saddiqa Habib Abba

Suna: Hangen nesa Tsara Labari: Yakubu M. Kumo Furodusa: Usman Mu’azu Bada umarni: Nazifi Asnanic Kamfani: MM Haruna English Academy Jarumai: Adam A Zango, Rahma Sadau, Hauwa Maina, Shehu Hassan Kano, Maryam CTV, Isa Bello Ja, Bashir Nayaya, Ibrahim Mandawari, Nuhu Abdullahi da Aina’u Ade. Sharhi: Saddiqa Habib Abba A farkon fim xin an nuna Zarah (Rahama Sadau suna soyyaya tare da Nazir(Adam A Zango) har ma an yi musu baiko tsakaninsu, a wani vangaren kuma an nuna Alhaji Habibu (Ibrahim Mandawari) tare da abokansa ‘yan siyasa suna taro wanda har a lokacin abokan aka yanke shawarar an tsaida shi takarar gwamna a jihar, bayan an kammala taro sun taho hanya shi da abokinsa Alhaji Umar (Shehu Hassan Kano) sai Alhaji Umar ya fuskanci cewar Alhaji Habibu yana cikin damuwa ya tambayesa dalilin damuwarsa sai ya faxamasa cewar shi babbar matsalarsa itace gashi an tsaida shi takara kuma amma matarsa bata jin turanci yaya zaiyi da ita a duk lokacinda aka yi baqin turawa wanda basa jin hausa ko kuma idan ana yin wani muhimmin taro wanda a gurin baza’a yi magana da hausa ba shi wannan shine babbar damuwarsa sai abokin ya bashi shawara akan ya saketa kawai ya kawo mai jin Turanci sai Alhaji Habibu yace shi bazai saketa ba domin Matarsa tayi masa halacci tun bashi da komai take tare da shi saboda har ma akwai lokacinda aka koreshi daga aiki itace wadda taringa ci da su ba tare da ta tava faxawa kowa ba saboda haka shi bazai iya sakinta ba sai Alhaji Umar yace masa to tunda haka ne to ya qaro mata kishiya wadda ta iya turanci idan yaso ita kishiyar sai a dinga damawa da ita a harkokin gwamnati ita kuma uwar gidan tunda bata jin turanci sai ta dinga kulawa da harkokin gida a take Alhaji Habibu ya karvi wannan shawarar bayan yadawo gida ya faxawa matarsa Amina (Hauwa Maina) cewar an tsaida shi takara amma sakamakon bata jin turanci zai qaro wata matar wadda take jin turanci ita kuma sai ta cigaba da kulawa da da harkokin gida Amina ta xaga hankalinta domin ta faxamasa ita tafiso ta cigaba da mallakar mijinta ita kaxai amma duk da haka bata ci mutuncin mijinta ba saboda an nuna ita macece mai hangen nesa da sanin yakamata acikin zamantakewar

rayuwar aure don wasu matan ma ‘yan uwanta wanda ma suka yi karatun bokon har zuwa suke yi gurinta neman shawarwari akan zamankewarsu ta aure saboda ita tanada wannan gogewar shiyasa ta cigaba da lallava mijinta akan kada ya yi auren amma fafur ya bijire mata akan shi lallai sai ya yi sai ta rabu da shi ya tafi ya cigaba da maganar neman aurensa har shi wannan Abokin nasa Alhaji Umar ya yi masa shawarar akan ya nemi auren ‘yar yayansa wato Zarah domin tana jin turanci don a qasar waje ma ta yi karatu Alhaji Habibu ya amince da hakan bada vacin lokaci ba har Alhaji Umar yaje gidansu Zarah ya sanar musu da halin da ake ciki Zarah da iyayenta suka yi murna sosai saboda suna ganin ‘yar su zata zama first lady Zarah ta kori Nazir ta faxamashi halin da ake ciki hankalin Nazir ya yi matuqar ta shi amma sai ya haqura ya rabu da ita, mutanan unguwar su Zarah ko ina ya xauka zata auri xan takarar gwamnan jihar har mata sun fara yi mata tururuwa tana yin taro da su domin tuntuni har an yi mata baiko da Alhaji Habibu, duk abinda yake faruwa a gari zan tukan suna komawa kunnen Amina har ta kai wataran ‘ya’yanta Rashida da Yassir(Nuhu Abdullahi) sun ji labari a gari sun zo sun sami mahaifinsu akan ya janye auren Zahra amma fafur ya qi janyewa. Wata rana ‘yan jam’iyyarsu Alhaji Habibu sun haxa wani gagarumin taro na duk ‘yan takarkaru kowanne da matarsa kuma matan ma zasu yi bayani amma da turanci hankalin Alhaji Habibu ya tashi a gurin taron domin yasan matarsa bata jin turanci ya tashi ya kirawota gefe yace ta ta zauna a waje kada ta shigo shi kuma zai san abinda zai je ya faxamusu Amina da taqi yarda amma daga qarshe sai ta yarda ta zauna amma yana shiga ciki kawai sai tabi bayansa ba tare da ya sani ba shi kuma adaidai lokacin ya karvi Mic yana yiwa mahalarta taron qaryar cewa bata da lafiya ita kuma a lokacin ta kawo kai ta karvi Mic hankalinsa ya yi matuqar tashi ganin cewar zata kunyata shi, ya koma ya zauna Amina ta fara bayani da turancin sahihi kuma bayanai masu ratsa jiki akan nawin shugabanci har ta kawo aya da hadisi tana ta zubda hawaye sannan a qarshe tayi wa maigidanta nasiha akan yaji tsoran Allah akan nawin da yake shirin hawa kansa a take jikin kowa a gurin ya mutu harda masu hawaye aciki harda maigidan nata aka tashi daga taro kowa ya watse, bayan sun dawo gida Alhaji Habibu ya jinjina mata akan abinda tayi ya nuna

farin cikinsa akai sosai sannan ya yi mata alqawarin cewar ya janye aurensa da Zahra tunda dama matsalar turanci ce kuma gashi ta iya kuma ya tambayeta a ina ta koyi turanci acikin qaramin lokaci? Amina ta yi farin ciki sosai sannan ta faxamishi cewar wata qawarta ce proffessor Ruqayya(Aina’u Ade) ta yi mata hanyar wata makaranta ta koyar turanci mai suna MM Haruna English academy to anan ta koya Alhaji Habib ya yabawa makarantar sosai. a vangaren gidansu Zarah kuwa Alhaji Umar yaje ya faxamusu an fasa aure hankalinsu ya yi matuqar tashi Zarah kamar zata haukace kuma rigima ta kacame musu da Alhaji Umar domin ya ranta musu kuxi an sayi kayan xaki da zummar idan aka yi aure abinda ta wawura a gwamnati za’a biya shi kuxinsa, daga bisani kuma Nazir ya kawo wa Zarah katin bikinsa tare da ‘yar gidan Alhaji Habib ya faxamata cewar ita bata zama first lady xin ba amma shi ga shi yanzu ya zama xan first lady don ‘yar gidan Alhaji Habib zai aura, Zarah tana jin haka ta sake gigicewa sosai. Abubuwan Birgewa: 1- Fim xin ya yi ma’ana sosai, sannan ya ilimantar ta kowanne fanni, addini da boko, kuma akwai darasi mai qarfi a ciki musamman a fannin zamatakewa irin ta auratayya. 2- Labarin ya sami cikakken tsari mai kyan gaske sannan ya tafi tiryan tiryan bai karye ba har ya dire. 3- An yi amfani da kayan aiki masu kyau da gurare wanda suka dace da labarin. 4-Jaruman sun matuqar qoqari gurin isar da saqon musamman Alhaji Habibu da Amina. Kurakurai: 1- Wasu daga cikin wuraren da akai magana da turanci kamar in da Yassir da Rashida suke magana

da babansu acikin harabar gidansu ba’a fassarawa mai kallo da hausa ba a rubuce ta yanda kowa zai fahimta saboda fim xin na hausa ne. 2-Akwai wasu wuraren an ji Yassir da Rashida suna yiwa Amina turanci tun kafin taje ta koya menene ma’anar yin hakan tunda sun san bata iya ba? ko dama suna faxa ne don ‘yan kallo suji ba don Amina ta fahimci me suke cemata ba? 3- Akwai lokacin da Alhaji Umar suke magana a office tare da Alhaji Habibu aka bugowa Alhaji Umar waya ya xaga akan screen xin wayarsa da aka hasko bai nuna cewa waya ake amsawa ba kawai kara ta ya yi. 4- Mahaifiyar Zarah ta sami tuntuven harshe a gurin da wani ya shigo gidansu ya sameta tare da Zarah ya faxawa Zaran cewa ta yi baqin mata a waje sai akaji mahaifiyarta tace a faxamusu su shiga xakin maigadi su jira ta shin mantawa ta yi ta faxi hakan a maimakon tace su jira kusa da xakin maigadi? domin yanda ta faxa xin sam bai kamata ba yaya za’ayi suna mata wata’il ma harda matar aure amma ace su shiga xakin maigadi su jira ‘yar gida. 5- Shin Alhaji Umar ba shida iyali ne? a matsayinsa na babban mutum yakamata ace ko sau xaya ne an nuno su ko kuma an faxesu a baki. 6- An faxa cewar Zarah tayi karatu a ingila amma sai gashi an ji iyayenta suna rigima da Alhaji Umar akan cewar ya ranta musu kuxi sun sayi kayan xaki, shin wanda yakai ‘yarsa karatu ingila shine har wani zai ranta masa kuxin kayan xaki? Qarqarewa: Fim xin ya yi matuqar kyau kuma ya yi ma’ana amma akwai abubuwan da ya kamata a kuma inganta su. Allahu a’alamu.


16

17

A Yau Lahadi 1 Ga Afrilu, 2018 (14 Ga Rajab, 1439)

KANNYWOOD

Dutsen Dala Da Na Gwaron Dutse Ma Film Village Ne –Shehu Kano SHEHU HASSAN KANO na xaya daga cikin fitattun jaruman Kannywood na farko-farko kuma jarumi ne wanda duniyar finafinan Hausa ta yarda da qwarewarsa tunda daga wancan lokaci har zuwa wannan zamani. Masu bibiyar tarihin masana’antar shirin finafinan Hausa sun ce, Shehu Kano ya fi kowane jarumi qarko a Kannywood, saboda shi kaxai ne a cikin mashahuran jaruman Hausa wanda bai tava shirya kansa fim ba, amma duk da haka ba a tava daina yi da shi ba, saboda tsabar qwarewarsa. To, amma duk da wannan nasara da ya samu, shi a wajensa ya na da sauran tafiya. To, da ma haka haziqan mutane su ke kasancewa; wato kullum a tsaye su ke cak! Wakiliyar LEADERSHIP A YAU LAHADI, BILKISU YUSUF ALI, ta samu zanta wa da wannan qwararren jarumi, inda ya tavo batutuwa da dama ciki har da batun badaqalar Alqaryar Finafinai da gwamnatin tarayya ta tava yunqurin yi a jihar Kano. Ga yadda hirar tasu ta kasance: Mene ne tarihin rayuwarka? An haife ni a 1967 a unguwar Fagge. Bayan karatu da na yi na makarantar allo an saka ni a makarantar Islamiyya Haido Islamiyya. Na yi makarantar Firamare ta Fagge daga nan na tafi makarantar sakandire ta Gwammaja 2 na kammala a shekarar 1986. Na yi koyarwar shekara xaya daga nan na tafi makarantar share fagen shiga jami’a CAS inda na yi remedial studies daga nan na kama aiki da kamfanin Dantata Organization daga nan na fara aiki da ministry of local government ( ma’aikatar qananan hukumomi) inda nake tare da su har yanzu. Na yi qungiyoyi da dama ciki akwai qungiyar sukawut inda na taka muqamai har na kai babban muqami a jaha a wancan lokacin. Ina da aure kuma da yara.

ilimin kallon fim xin. Don haka ana gane gudunmawar in har ka cire wani vangaranci ka kalla da zuciya xaya. Amma fim ya tava duk vangarorin rayuwa amma wasu daga talla suke farma ‘yan fim ba ma za su tsaya su kalli fim xin ba. Fim ya tavo rayuwa gaba xayanta addini kamar wani fim wani gari wanda jigonsa rabon gado a muslunci. Ana tavo al’ada da zamantakewa da tattalin arziki. Akwai fim xin Sandar Kiwo sai da wasu Turawa, ya da qanwa, suka musulunta, saboda an yi shi ne kan ’yancin mata a Musulunci. A fim xin sai suka lura hoton da aka ba su na yadda mata suke a baya a Musulunci da suka kalli fim xin sai suka lura farfaganda ce ashe. Ireiren wannan darasin ba su da adadi; ga su nan birjik kan darussan fina-finai.

Yaushe ka fara wasan kwaikwayo? Ni tun tasowata na ke wasan kwaikwayo tun Ina makarantar firamare har lokacin da na ke aiki da ma’aikatar qananan hukumomi Ina haxawa da wasannin kwaikwayo na dave tunda akwai qungiyoyi daban-daban waxanda mu ka yi tun kama daga matsayi na unguwa har aka zo ‘home’ bidiyo.

Ya a ka fara gwagwarmayar qungiya? A 1984 akwai qungiya da muka kafa a Fagge sunan qungiyar Fagge Dramatic Society har aka zo aka yi fagge so dangi dramatic society ko ma a lokacin da muke tamun akwai qungiyoyi da muke kallonsu iyayen tamu ce kamar anan Kano an yi qungiya kwaya xaya wadda ita ta haifi tumbin giwa ta haifar da qungiyar Dabo ta haifar da qungiyar tauraruwa ta haifar da jan zaki waxannan qungiyoyi an yi su ne qarqashin Kano State art council wannan su suka ja ragamar zuwa gidan talabijin na ctv inda aka din ga yin wata drama gani ga wane inda ake bin yan qungiyoyi suna taka rawa. Haka marigayi malam Abdullahi Sani Makarantar lungu yana gabatar da wani wasan kwaikwayo Duniyar nan tamu suma sun din ga xauko ‘yan qungiyoyin can ana yi da su wanda ni ma ina ciki. A lokacin kishi ne ya kai mu don kowa ki ka gani yana taka wata rawa a qungiya da aljihunsa yake yin ta.

Me ya ja ra’ayinka har ka fara yin wasan kwaikwayo? Wannan yana da nasaba da kallo, domin lokacin da mu ke firamare akwai wani shiri da ake yi a gidan talabijin na qasa NTA akwai kakanni kamar yadda ni nake kallonsu a wannan harkar misali a Kaduna akwai su Alhaji Qasimu Yaro anan Kano akwai irin su Xanhaki a Sokoto irin su Baba Soja Bauchi irin su Gauxe da dai sauransu.ire-iren wasanninsu yana ba ni sha’awa sai nake da burin da na girma ni ma wasan kwaikwayon zan yi.Wannan sai ya sa daga firamare in aka kai mu filin maraba da yara na NTA ni ba wani abin da na fi so irin sashen da za a ce mu yi wasan kwaikwayo daga haka aka fara har zuwa inda ake a yau. Ya ka ji a ranka lokacin da ka fara wasan kwaikwayo? Har yanzu Ina jin ban kai gaci ba, saboda har yanzu Ina da buri, amma dai Ina jin mafarkina ya na ta tabbata, don a farkon lokacin da mu ka fara ba a xaukar wasan kwaikwayo, sai ranar Asabar da Lahadi, saboda ma’aikata kuma kyauta mu ke yi mu. Mu ke ma biya, amma yanzu alhamdilillah a cikin irin cikar burin abin ya zama sana’a ingantacciya. Ya ka ke haxa ayyuka guda biyu; aikin fim da aikinka na gwamnati? To, ba yadda za a yi sai na je ayyukan guda biyu. Don haka sai muke yin tsari tunda su masu shirya fim xin su na la’akari da irina; sai su raba abin kashi uku; mu mu na yin namu daga rana zuwa dare; in kuma za a bar gari ne mu na neman izini wajen aikinmu in an yarda mu je. Wacce irin gudunmawa masana’antar ke bayarwa? Gudunmawar ai ba za ta musaltu ba. Amma ana samun wannan gudmmawar in har mai kallon fim xin yana da

Wanne tasiri qungiya ta yi ma ka? Tasirin qungiya da ta yi min shi ne wanda ake kallo a shekarar 1999 aka kafa qungiyar Kanywood lokacin ba Kanywood ake kiranta ba, an ace mata Kano State Producers Association waxannan daraktocin su suka haxu suka ce za su fara yin fim a kaset, don suna ganin tasirin abin da suka koya a qungiyoyi zai fito a ciki mutane za su amfana. A lokacin samari da dama sun •Hasan Kano sami aiki da a dave kawai ake yi amma yanzu dole a nemi mutum zai yi fim mai inganci ya shiga kasuwa sai a mai xaukar hoto dole a sami mai kwalliya ana buqatar qyale a qi saye, amma idan fim xin da aka kwafi Indiya wanda zai kawo kayan saw a da direba mai dafa abinci ya shiga kasuwa sai a yi rububinsa ya za a yi wanda ya da sauransu. Wannan ta sa sai aka ga waxannan mutane yi marar ingancin zai fahimci abu ya yi marar kyau? da ke cikin waxannan qungiyoyi wa zai xauki wannan Amma a ‘yan shekarun nan an sami ci gaba inda ake ta layi da wancan sai aka karkasa. Abin sai ya tasirantu ya karatu ake ta tarurrukan sanin makamar aiki a yanzu su koma sana’a.A qungiyoyin nan mun sami ilimi hatta a da kansu masu irin wannan halin da suke wankar fim labarai a cikinmu akwai malaman islamiyya da za su sai suka fahimci ashe ka xau fim ka wanka matsala ne zo su kawo wata kissa ko tarihi a zauna a yi bitarsa a ba ma ya birgewa. mayar wasan kwaikwayo don jama’a su amfana a lokacin wannan qungiyoyi makaranta ce babba nan z aka goge Batun Film Village da aka yi caaa! Sai aka ga kamar tun kana yi da sigar koyo. Su kuma na yanzu da suka gwiwarku ta yi sanyi a harkar bakixaya. shigo bas u sami wannan horon ba sai abin ya zama da Ai mu Fim Village bai sa mun yi sanyi ba; ba dai mun naqasu saboda ba gogewa. Shi ya kai ga har a xauki fina- qara bi ta kanta ba ne. Ai idan ma ban da Nura Husaini finan indiya a wanka. da wasu xaixaikun mutane ba, waxanda ya ma tsaya ya yi wani jawabi kai. Saboda ai ma mutane ba su fahimci Ana kuka da finafinai marasa inganci a yau. Ina matsalar mene ne fim village xin ba, mu kuma abin da muke gani ta ke? kasuwar Jakara ma Fim Village ce, Qofar Nasarawa da su Ai laifin masu kallo ne ya haifar da waxannan. A yau Dutsen Dala da Goron Dutse duka shi ne tunda gurare

haxa kaya kawai. Fim xin qara’i fim ne da ya zo da savanin yadda ka saba fitowa ya ka ji da ka ji ka ga script xin? Lokacin da aka kawo min script xin qara’i aka faxa min ga abin da za a yi a jikiin shirin sai nake jin ina ma a yanzu da aka kawo min a yanzu za fara xaukar shirin har shi furodusan mamaki ya kama shi ya ce chairman ya daga kawo w aka ce ko yanzu a fara sai y ace me ne dalilinka? Sai na ce a qasar Hausa akwai mutanen da kulva na varna amma ana cewa java ce akwai mutanen da ga shekaru sun cimma su kuma sun sami kuxi amma bas a tunanin taimakon ‘ya’yansu da al’umma ko dai su ba da tallafin ilimi ko sana’a ko wani muhimmin vangare illa su burinsu su sheqe aya tunda sun ga wasu na yi kuma a tunaninsu suna jin daxi za su sa qananan kaya su yi bariki. Ya zama da iyali yake da sana’ar Fim b aka samun matsala da uwar gida? Gaskiya ina cikin waxanda suka yi sa’a tsakaninmu da iyalanmu matata mun fahimci juna sannan ita ma ‘yar wasan kwaikwayo ce lokacin tana sakandire ta Kabo ta yi Hausa cultural group ta karanta wani abu kaxan game da wasan kwaikwayo don haka da Allah ya haxamu da ita sai ya zama wani lokaci mukan jarraba yi acting ni da ita a cikin gida in zan tafi wani shiri musamman kamar shirin da nake gani zai wahalar da ni misali a ce na zo a kwarto y azan yin a shiga falon gidan kuma in na zo wacce irin Magana zan yi wa matar in na zauna wanne irin sakin jiki zan yi wani lokcin nakan jarraba irin wannan da me xakina daga nan sai na sami kwaringwiwar fita.

ne da gwamnati ta sahale mana mu je mu yi fim xinmu; ba mu matsawa kowa ba, hankali kwance. Wancan babba da aka hana mun yi la’akari da ma mutane ba su ma fahimta ba sai an wayar musu da kai a hankali, don sun xauka manyan gidaje za a buxe a ba mu mu shiga. Don mutumin da yake yin yawo ya je qasashe irin su Egypt su Marocco ya san me ye fim village don in ya je aka ce ma ya koma ba zai koma ba, don daga inda ya sauka zuwa inda fim village xin yake kuxin da zai kasha ba kaxan ba ne, sannan kuma in ya isa wajen fili zai gani fetal don dajin Allah aka yanka aka yi kuma kome na wajen daga katako sai roba in an kammla amfani da shi naxewa ake a ajiye sai kuma wani amfanin ya taso.Fim village wajen adana tarihi ne. Ai da ma an yi fim village ci gaban ya kai iyaka watakil ma mu sai dai mu zama ‘yan kallo swatakilma muna zaune daga saudiyya ko ingila za a zo a yi tarihin Kano ko wata al’ada saboda kuxi za a kasha masu yawa kuma kuxi za a nema daga haya zuwa masu yin sai ka ji ana batun miliyan xari a

Ka na fatan magaji a cikin iyalinka? Ai ‘ya’yana sun fara fim ni na xan dakataar da su saboda ina son su yi karatu saboda sana’ar fim sana’a ce da idan ba ka da ilimi ko na arabiyya ko na boko idan b aka da ilimi z aka zama xan kallo ne waxanda ke shura a sana’ar duk ‘yayan makaranta ne. Babban xana Abdallah ni na xauke shi aka yi wani fim da shi Uwar gida. Baba Hassan mai bin sa shi ma ya yi wani fim ga qoshi ga kwanan yunwa. Akwa wani qalubale ku da kuke masana’antar ba kwa auren abokanan sana’arku me ya sa? Ey to haka dai mutane ke faxa amma ba haka ba ne misali bari na xauko miki daga can nesa akwai wani tsohon jarumi Ibrahim Buba matarsa da ya aura Rabi Musa acting ne ya haxa sun a fim akwai Sani Mu’azu daga Jos matarsa da ya aura acting ne ga Sani musa ya aur Faty Muhammad mansura sun yi aure da Sani Danja da Muhibbat da mijinta Gigs ga Abida Muhammad da Xanzaki mutuwa ta raba su To, akwai kuma batun in matan sun yi auren ba sa zama. Laifin daga gun mazan da suke aurensu ne . dalili yarinya ce aka yi mata kwalliya ta shiga gida me tsada aka ba ta mota mai tsada daga ganin haka tsaf da ita sai y ace sai

ya aureta zai kasha kuxi har ta zo gida to kuma bayan ta zo sai zama ya garara saboda aure ne na son zuciya ba don Allah ba. Sannan akwai qaddara mutuwar aure a yau ta zama gidan kowa akwai amma gas u nan dayan gaske suna zamansu. Ina su Zahara’u Shata da Maijidda Abdulqadir da Aishan ki yarda da ni su Hindatu Bashir duk suna gidajensu da yaransu lafiya. Ai ma waxanda ke gidajensu sun fi waxannda suka fito yawa. Ya ka ke ji in an s aka a sarki ko wani mai mulki musamman in an xaura ma kamara? (Dariya) Na tava ji sau xaya da daxewa a wani shiri a Kaduna na fito a shugaban qasa ga masu tsaro ga motoci na alfarma amma ni a lokacin motata bitil ce aka yi komai aka yi kaxe-kaxe aka ba ni filawar nan da aka tare ni na biyo red carfet ga jiniya ina ta xaga hannu. Lokacin da aka gama shiri sai nag a mutane na darewa n ace yay a haka? Suka cee y to y aba za a yi haka ba. Nan dai aka bar ni ‘yar bitil xin tawa ma aka ce ba me shiga sai ni kaxai.Sai da na ji abin a raina anan na qara gano ashe masu mulki in aka ce su sauka bas a jin daxi. Yadda aka bar addini da al’adunmu a fina-finai a yau ci gaba ne ko ci baya? Gaskiya ci baya ne don duk a sha’anin fim kowane yanki ko qasa ko nahiya qoqari suke su tallata hajarsu wato zamantakewarsu da addininsu da al’adunsu Bayan kasancewarka xan wasa kai ma ka rikixe ka zama mai shirya fim ko bayar da umarni? Tun da nake ban tava rubuta fim ba ko shiryawa ko bayar da umarni ni jarumi ne kawai sai dai a xauko ni na taka rawa. Saboda ni shin a zava. Ni na yarda da ka xauki vangare guda ka ginu a wajen saboda in k ace z aka raba qafa to a qarshe z aka yi biyu babu tsalle-tsallen bay a kawo ci gaba. Wanne Kira Gare ka Ga ‘Yan Fim Musamman Masu Tasowa? Kirana kullum gare su shi ne su nemi ilimi. Ilimin nan shi ne qashin bayan kome a yau. Wanda ke sha’awar shiga harkar aqalla ko diploma ce ya kawo sannan ya daure ya zamana yana da ido a addini. Saboda harkar Fim hark ace ta ilimi. Wanne Qalubale ne ke Ci Ma Tuwo a Kwarya a Harkar Fim? Gaskiya qalubalen da nake samu shi ne irin mutanen da wani zai tare ni saboda na taka wata rawa a fim ba zai bari na yi masa bayani ba ko ya bari ya fahimci me yasa na taka rawar kawai sai yah au ni da faxa da hayaniya wani har da zage-zage wannan abu na ci min tuwo na tava cin karo da irin wannan ma lokacin da na taka rawa a wani fim Adon gari. Labarin na kalla don na zo a matsayin xan daudu har masoyana suka ga wannan rawar bai dace ba duk da a qarshe na zama malami na shiryu. Amma fa na sha qalubale. Malam Shehu Hasan Kano, mun gode qwarai. Ni ma na gode.


18

A Yau Lahadi 1 Ga Afrilu, 2018 (14 Ga Rajab, 1439)

HAYAQI...

Tare da Mu’azu Harxawa 08062333065 hardawamuazu@mail.com

Yaushe Buharin Nijeriya Zai Qarasa Buharin Daji? Tun daga lokacin da Nijeriya ta faxa cikin rigingimu kala kala waxanda suka shafi yin mu’amala da makamai da satar dabbobi da mutane, domin neman kuxin fansa da sauran rigingimu da suka shafi makiyaya da manoma da hayaniya irin ta qungiyar boko haram masu gwagwarmaya da makami kan siyasa da rigimar mutanen kudancin Nijeriya wacce ta shafi man fetir da neman a ware da makamantan su. Babu wata fitina mai xaure kai a yanzu da ta wuce irin ta Jihar Zamfara inda masu makamai ke yin dirar mikiya a cikin gari su yi ta kashe mutane ba kama hannun yaro kuma su tafi shiru sun sha, al’amarin da har zuwa wannan lokaci ba wanda zai ce ga dalilin da ya sa waxannan mutanen ke wannan aiki da ke shafar maza da mata da qananan yara. Bayan haka kuma ga ta’addanci na kwashe shanu da qona gidaje da gonaki da dukiyoyin bayin Allah lamarin da a kullum sai sake sabon salo wannan fitina ke yi kamar babu gwamnati a wannan jiha ko jami’an tsaro. Wani abin takaici da ke ba mutane mamaki shine yadda a kullum ake jita-jitar cewa akwai hannun wasu masu ruwa da tsaki a cikin gwamnati ko jami’an tsaro, saboda tsammani ko ganin yadda masu cin moriyar wannan fitina ke bayar da cin hancin dabbobi da kuxi wa jami’an gwamnati da na tsaro don a jima ana cin zarafin mazauna wannan yanki. Wannan batu ne da ya kamata gwamnati ta tsawaita bincike don tabbatar da gaskiyar wannan zargi ta hanyar janye dukkan jami’an tsaron da ke aiki a wannan jiha a musanya su da wasu, musamman daga kan sajen xan sanda ko soja ko civil depence zuwa sama, hakan zai taimaka a san inda aka nufa kan wannan fitina da ta qi ci ta qi cinyewa tun zamanin mulkin Goodluck Jonathan har zuwa wannan gwamnatin. Matuqar da gaske ake yi ya zamo wajibi gwamnatin tarayya a qarqashin jagorancin Muhammadu Buhari ta tashi tsaye domin magance wannan matsala ta kashe kashe wanda bayan farar hula har ya kai ga a cikin makon jiya an kashe

sojoji 11. Yayin da kuma a halin da ake ciki wasu garuruwan mutane sun watse an bar jama’a cikin tashin hankali duk da kasancewar dama yankin Sokoto da Zamfara da Birnin Kebbi na cikin yankunan da suka fi talauci a wannan qasa mai tarin arziqin da mutum xaya ke da kuxin da ya fi na Jihar sa kuma yana zaune a Jihar ba tare da taimakon kowa ba. Bayan haka akwai buqatar idan abu ya qi ci ya qi cinyewa shugaba Buharin Nigeriya ya kamata ya nemi masana harqar tsaro na farin kaya da masu kayan sarki da malaman jami’a da tsoffin jami’an tsaro a nemi shawarar su ta musamman game da yadda za a shawo kan wannan matsala. Musamman ganin yadda shi Buharin daji wanda ya zama wani Abubakar Shekau a yankin zamfara, amma shi an ga iyakarsa don an kashe shi, amma ya zamo tamkar mushen gizaka ko ka mutu kana ba yaro tsoro. Bayan haka kuma lamari ya zamo an kashe maciji amma har yau ba a sare kai ba. Don haka dole Buharin Nijeriya ya tashi tsaye wajen kafa doka game da irin kisan da jami’an tsaro suke yi wa masu laifi a lokacin da aka bukaci ganin bayan muggan ayyukan da suke aikatawa, saboda yadda ake kashe su ba tare da samun bayanan da za su taimaka wajen tsaron qasa da hana ci gaban wannan laifi. Misali shi ne tun daga kan Mohammed Yusuf shugaban Boko Haram a Maiduguri, kisan da aka masa ya zamo wata babbar fitina wacce ayyukan magoya bayansa ya ci gaba da wanzuwa kusan shekara goma kenan Allah kaxai ya san rayuwakan da suka salwanta da dukiyar da aka rasa, bayan haka kuma ga zubar mutuncin mutane a cikin qasa da duniya baki xaya. Amma idan da lokacin da aka ci galba kan mohammed Yusuf an bar shi a raye an bincike shi an tattauna an gano wasu abubuwa da ke birne game da shi kan rigimar boko haram da bata kawo wannan lokaci ana kai ruwa rana ana ta’adi ba. Ganin irin jawaban da

•Shugaban Qasa Muhammadu Buhari

Buharin daji ya yi tun yana raye inda ya ke hasashen ko an kashe shi za a ci gaba da fitina da magoya bayansa har tsawon wata goma, biri ya yi kama da mutum musamman ganin yadda ana murnar kashe Buharin daji sai magoya bayansa suka yi dirar mikiya a wasu qauyuka suka kashe kusan mutane 40 bayan kusan mutane xari da suka kashe kwanakin baya. Duk haka bai ishe su ba sun sake dawowa sun kai wa kusan mutane xari da suka je makabarta domin jana’izar waxanda aka kashe, nan aka sake bin su aka kashe da dama daga cikin su lallai rashin tausayi da imani ya kai maqura. Masalar ta bayyana qarara akwai lauje a cikin naxi kuma biri ya yi kama da mutum game da hasashen da shi Buharin daji ya yi tun yana raye na cewa mutanensa za su ci gaba da assasa gwagwarmayar da ya xora

su a kai don cimma burin su na rikita zaman lafiyar Jihar Zamfara da kewaye. Don haka akwai buqatar Buharin Nijeriya wanda Allah ya zuba amanar mutane a qarqashin sa ya tashi tsaye wajen gano bakin zaren wannan rigima. Kuma shugabanni da jami’an tsaro su gane cewa kashe mai laifi baya haifar da alheri matuqar ba an samu cikakken bincike game da yadda za a magance matsalar da ta haifar da aikata laifin ba don mutane su samu natsuwa. Saboda idan muka xauki misali da rigimar Boko Haram tun farkonta a lokacin shugabancin Umar Musa Allah ya masa rahama ya bayar da umarnin a je a gama da su, yayin da a wancan lokacin masana kan harqar tsaro da tsohon shugaban qasa Obasanjo sun yi ta bayar da shawarar duk faxan da ya wuce kwana huxu da soja har ya kai wata guda to a dakata a

Ci gaba daga shafi na

19


19

A Yau Lahadi 1 Ga Afrilu, 2018 (14 Ga Rajab, 1439)

Yaushe Buharin Nijeriya Zai Qarasa Buharin Daji? Ci gaba daga shafi na

18

gudanar da bincike mai tsawo kan waxanda aka kama idan ya zamo wajibi a yi sulhu da su to yin hakan zai taimaka a magance matsalar. Amma ganin irin qarfin sojan da gwamnati ke da shi da kayan aiki a lokacin aka nuna a shafe boko haram a bayan qasa shi ne maganin lamarin. Haka aka ci gaba da yaqi har aka shigo cikin gwamnatin Goodluck Jonathan ya gama turmin farko ya koma karo na biyu duk ana cikin yaqi kullum lamarin sai qara muni ya ke yi har aka ga qarshen gwamnatinsa aka shigo ta Buhari. Cikin gwamnatin Buhari an samu lafawar lamurra amma duk da irin kuxi da rayukan jami’an tsaro da ake kashewa da kayan aiki har yanzu an gagara shawo kan wannan lamarin da sauran aiki a gaba. Don haka wuta bata kashe wuta sai ko ruwan sanyi da sulhuntawa idan ta faskara. Ganin yadda jami’an tsaro a kullum ke aniyar ganin bayan wannan fitina ta Boko Haram amma lamarin ya faskara, akwai abin dubawa sosai musamman ganin yadda ita gwamnati a kullum ta kasa gano sahihiyar hanyar magance lamarin a ruwan sanyi kullum rayuka sai salwanta suke yi. Daga waccan rigimar wutar boko haram da ta kama a gabas yanzu kuma rigimar wutar Buharin daji da muqarrabansa ta kama a yamma, yayin da kuma rufe kan iyakar Nijeriya ya sa mutane da dama suka rasa ayyukan yi musamman a arewa inda a halin yanzu wasu matasa suka abka cikin aikata laifuka domin neman abin da za su ci ko da tsiya ko da arziki. Haka yankin Kaduna da Benuwai da sauran tsakiyarqasa rigimar varayin shanu da manoma da makiyaya da masu garkuwa da mutane don neman kuxin fansa ke barazana wa zaman lafiyar mutane. Don haka akwai buqatar gwamnati ta natsu wajen yin nazarin irin halin da ake ciki a qasar nan ta hanyar fito da sabbin dabarun samar da zaman lafiya musamman game da abin da ya shafi samar da ayyukan yi ta tilasta gwamnoni su cike guraban ayyuka da ake da su a qananan hukumomi da ma’aikatun gwamnatin jiha don matasa su rage zaman kashe wando, a kuma farfaxo da ayyukan gwamnati da aka rufe saboda rashin ma’aikata.

•Shugaban Qasa Muhammadu Buhari

Bayan haka kuma a tabbatar duk kamfanin da ya rufe daga kan gidan bulo ko gidan biredi ko gidan ruwa da sauran manyan kamfanoni a tallafa musu ko da rancen kuxi don su farfaxo, bayan haka gwamnati ta rage buri kan haraji da yawan tatsar kuxi a jikin ‘yan qasa da irin waxannan kamfanoni da ‘yan kasuwa lamarin da ya sa a kullum ‘yan kasuwa ke karyewa kamfanoni ke rufewa ma’aikata ke barin aiki ba tare da an basu hakkokin su ba. Hakan ya haifar da kullum mutane ba sa addu’ar alheri ga gwamnati sai la’ana da tsinuwa saboda ‘yan Nijeriya sakalu ne basu da buqatar irin wannan manufa ta gwamnati wacce ta haifar da taluci da matsaloli da a halin yanzu suka sa komai ke neman jagwalgwalewa a cikin qasa a lokacin da gwamnati ke buqatar mutanen da za su zave ta. Halin da ake ciki na nuna akwai yiwuwar rashin samun nasara ga wannan gwamnati matuqar ba ta sake yanayin tafiyar ta ba, saboda hatta waxanda aka vatawa rai da ‘yan adawa murna suke yi, batun yi wa qasa addu’a na neman zama tarihi sai ko

addu’ar Allah ya kawo karshen matsalar talauci da yunwa da aka shiga, kuma gwamnati ke gaba wajen amsa tambayoyin da suka jawo talauci da yunwa. Hakan ya sa an daina yi wa qasar addu’ah sai ko addu’ar neman sauqi kurum ake yi, musamman ganin yadda gwamnatin bata damu da taimakon masu qaramin qarfi ba. Musamman malamai da fastoci da almajirai da suka jajirce da addu’ah da kuma matasa da suka bayar da rayuwar su wajen yunqurin kawo wannan gwamnati ta canji yanzu sun duqufa wajen yunqurin ganin bayanta da addu’ar Allah ya fitar da su cikin halin da suka shiga na matsaloli saboda waxanda ke cikin gwamnatin basu cika taimako ba don suma da yawansu basu qoshi ba, don haka duk abin da ya shiga hannun su sai ko su tanada wa kan su. Bayan hakan kuma kafin zuwan gwamnatin an san a bi mutane ana neman addu’ar su har ana taimaka musu, amma yanzu yawancin masu riqe da muqamai a wannan gwamnati basu da kyauta ga talakawa kamar yadda aka saba gwamnatin baya ke yi. Hakan

kuma ya taimaka wajen tsanar jami’ar gwamnati inda ko ba a zage su a fili ba ake hararar su, da nufin za a ga yadda za su tunkari mutane wajen neman guri’a ko addu’ar su ko neman goge katin da ake saya domin turawa Buhari gudummowar kamfen, saboda wancan da suka yi ba wata godiyar kirki da aka musu sai ko sakamako da talauci da fatara da tashin hankali da sauran wahalhalun rayuwa da rufe kan iyakar ‘yan arewa da suka kawo gwamnatin. Duk da irin abubuwan da na zayyano ya zamo wajibi mutane su yi haquri a taimaki Buharin Nijeriya da addu’ah game da yadda zai shawo kan matsalar yaran Buharin daji da kuma manyan yayun su ‘yan boko haram waxanda suka zama gangaran a fagen yaqi ta ta’addanci kala kala a Nijeriya har da qasashen maqobta. Haka suma mutanen da suke cikin gwamnati ya kamata su fahimci idan an tafi a haka ba za su samu yadda suke so ba. Kuma duk abin da suka tara ba zai biya musu buqatar rayuwa ba qarshen su ba zai yi kyau ba za su tsiyace ne ko su faxa cikin takaici ko jinya ko bincike kamar yadda suka yi wa gwamnatin da suka gada. Don haka ya kamata wannan gwamnati ta ci gaba da ganin kimar ‘yan qasa don a samu ci gaban qasa da mutanen ta, kuma ya kamata gwamnati ta yi wa wasu manufofinta garambawul ta hanyar nesanta kanta da neman dukiya ta ko halin qaqa a hannun ‘yan qasa don yi wa mutanen qasa aiki, hakan ba abin da zai haifar ace an gina qasa mutane suna wulakance cikin talauci da rashin abin yi da fatara da yunwa, sai a fiskanci lalacewa da shiga fitintinu kala kala waxanda ba za a san ranar fita daga cikin su ba sai lokacin da Allah ya kawo shugabannin da za su sunkuyar da kan su a fiskanci gaskiya don samu zaman lafiya. A sani duk wata ribar siyasa a duniya mutane ke neman ta ba wanda zai yi siyasa da nufin ya mutum da talauci ko yunwa ya je lahira don tsammanin wa rabbukan neman shiga aljanna daga santsin siyasa, alhali aikin qwarai ke bayar da aljanna, a yanzu kuma mutane talauci ya sa da dama sun qauracewa aikin qwarai wasu kuma suna son yi amma basu da lafiya ko halin yi, da fatar Allah ya haxamu da waxanda suke qaunar mu na alheri ba waxanda muke qauna suke da nufin tozartawa ko wahalar da mu ba.


20

A Yau

Kaucin Kaba Sha Nema Sarqaqqiya A kowace shekara miliyoyin mutane ne suke kamuwa da son juna. A kowace shekara kuma miliyoyin aure ake xaurawa. Amma abin takaici kuma a kowace shekarar dai miliyoyin auren ne suke watsewa! Saboda wancan son da suke yi wa juna a baya, yanzu ya gushe! Daga cikin waxanda suka tsaya suka ci gaba da zaman auren kuma,wani kaso mai tsoka suna yin zaman a xosane ne. wato dai irin zaman nan da fargabar halin da za a shiga bayan rabuwa ne kawai ya sa ake ci gaba da tattalinsa. Wani kaso kuma wanda wataqila shi ne mafi qaranci, shi ne na mutanen da suke zaune cikin wancan yanayi na tsohuwar soyayyarsu tun irin ta farko, ko kuma ma wadda ta fi ta farkon. Wannan kuma yana faruwa ne yayin da mata da mijin suka fahimci bambamcebambamcen da ke tsakaninsu, kuma suke yin la’akari da su a zamantakewarsu da juna. Ina Gizon Ya Ke Saqa? Abu mafi rikitarwa a cikin zamantakewarmu, shi ne yadda xabi’u da yanayin kallon da muke yi wa lammura su ka sha bamban. Ka nufi abokin zamanka da kyakkywar niyayar taimako, ya yi mata kallon akasin hakan. Wannan kuma yana faruwa ne sakamakon xabi’u da aka gina mu a kan su. Wadda wataqila babbar hikimar hakan kuma ba zai wuce don Allah Ya jarrabe mu Ya ga waxanda za su jure su kyautata wannan zama mai cike da sarqaqqiya. Yi nazarin qorafe-qorafen da mu ka fi yi a cikin zamantakeawarmu. Mata Babban qorafin da mata suka fi yi game da maza shi ne, maza ba sa saurarensu. Wato ba sa ba su isasshen lokaci yadda suke so yayin da suka tashi bayyana abin da yake damun su. Wai da zarar sun fara magana sai mazan su katse su. Abin da kuwa yake faruwa shi ne, yayin da mace ta fara magana game da wata matsalarta, sai mijin ya yi sauri kafin ta kai inda take son tsayawa ya katse ta ta hanyar ba ta shawarar da yake tsammanin za ta zama warakar matsalar. Yakan cika da mamaki shi ma kuma yadda matar take nuna rashin

gamsuwa da yadda ya tunkari maganar tata. Amma abin da shi bai sani ba shi ne, ita fa ba wai shawara ko mafita take buqata a wannan lokacin ba. Abin da kawai ta fi buqata shi ne a tattauna game da matsalar. Wanda ita a wurinta hakan wata babbar hanya ce ta magance raxaxin abin da ya dame tan. Saboda haka, babban abin da take nema a wurinsa a wannan lokacin bai wuce ya tsaya kawai ya saurare ta ba. Idan abin na damuwa ne, ya nuna ya fahimce ta. Ya kuma tabbatar mata da cewa lallai abin ya kai a damu a kansa. Abin da mata bas u sani bas hi ne, shi namiji yana jin kansa ne a matsayin Chief Security a gidansa, wanda duk lokacin da wata ‘yar matsala ta dami wani, shi ne zai kawo mafita cikin gaggawa. Shi ya sa daga kin far Magana zai fara tunanin kawo miki mafitar damuwarki. Misali Watarana Zainab ta dawo daga aiki a gajiye tiqis. Ta ce wa Bashir: “Kai ni fa ayyukan nan sun yi min yawa, sam ma ba ni da wani lokaci na kaina!” Bashir wanda a tunaninsa taimakon ta zai yi, kai tsaye ya ce: “Kawai ki dena wannan aikin, kina takura wa kanki sosai. In ya so ko wata ‘yar sana’ar ki riqa yi daga gida.” Ta ce: “Ni ina son aikina. Kawai dai suna takura min ne, wai sai a tara wa mutum aiki, a ce sai ya yi a rana guda, kamar wani inji.” Ya ce: “ Manta da su, kawai ki yi iya abin da za ki iya yi.” Ta qara cewa: “Kai! Ka ga na manta ma ban kira Inna ba sam!” Bashir ya ce: “ Kar ki damu, ai ta san yanayin ayyukanki. Za ta yi miki uzuri ita ma.” Ta ce: “ Za ta damu fa. Ka san fa tana so na sosai.” Ya qara cewa: “ Kin cika takura wa kanki, shi ya sa kullum kike cikin damuwa.” Zainab cikin xaure fuska ta ce: “ Ni ba kullum nake a cikin damuwa ba. Kai ba ka sauraren mutum in yana magana, kawai sai dai ka fassara shi da abin da ka ga dama.” Ya ce, cikin fushi: “ To,ina sauraren ki.” Sai hirar tasu ta qare cikin wani yanayi mai xaci

ga kowannensu. Zainab tana jin haushi cewa, matsaloli iri-iri sun gallabe ta, ta dawo gida don ta sami wanda za ta tattauna da shi ta sami sauqi. Amma an qi sauraron ta. A xaya vangaren kuma, Bashir ya fusata yana ganin ya taimaka mata ta hanyar ba ta shawarar da yake tsammanin za ta magance mata matsalarta, amma ita kuma ta nuna shawarwarin nasa ba su da wani amfani. Amma bayan wani lokaci, Bashir ya sami uzurin karanta bambance-bambancen dake tsakanin maza da mata a waxannan fannoni. Don haka daga nan sai ya fahimci yadda ya fi kamata ya fuskanci matarsa. Ya kuma fihimci irin amsoshin da idan aka bat a za ta fi fahimta. Domin tana maganganu game da matsalarta ne kawai don ta sami kulawa, a taya ta nuna damuwa a kuma qarfafa mata gwiwa ta hanyar barin ta ta yi maganarta son sai, a saurare ta. Sannan daga bisani a yabi qoqarin da take yi. Bawai tana magana ne don a ba ta shawara ba. Don haka daga wannan lokaci sai hirarsu ta sauya. Yanzu idan Zainab ta dawo gida a gajiye, ta ce da Bashir: “Kai, ayyukan nan sun yi min yawa, sam ba ni da wani lokaci na kaina ma!” Sai Bashir ya xan yi shiru na xan lokaci, sannan ya ja dogon numfashi, ya ce: “Ai gaskiya kina qoqari ma

Lahadi 1 Ga Afrilu, 2018 (14 Ga Rajab, 1439)

Tare Da Hamza Dawaki 08034753238, hamzadawaki@gmail.com

sosai, da ganin ki ma an san kin gaji matuqa!” Ta ce: “To ayyuka ne sai a tila ma su, a ce kuma wai duk so ake ka yi su a lokaci guda. Ni na rasa yadda zan yi da mutanen nan!” Ya xan yi shiru, sannan ya xan nisa, ya ce “Uhmmm!” Ta ce: “Ka ga sam na manta ma ban kira Aunty ba!” Ya kalle ta cikin alamun mamaki, tare da cewa: “Ah, haba?” Ta ce: “Wallahi, abin ne da yawa. Shi ya sa ma duk na qara damuwa, Aunty tana so na sosai.” Bashir ya dube ta, ya yi murmushi, yayin da yake ce mata: “Ni na san da wannan. Ai ke dole ne kowa ma ya so ki, saboda kin haxa dukkan xabi’un da suka cancanci a so mutum don su. Na san za ki gaji, domin na tabbata aikin babba ne. Ba kuma kowace mace ce za ta iya shi ba. Sai gwaraza irin ki.” Yayin da ya ga ta fara sakin ranta kuma sai ya qara cewa: “Matso kusa ma ki huta a jikina!” Cikin farin ciki ta matso jikinsa. A lokacin da ta xora kanta a tsakanin kafaxa da qirjinsa ta xan huta na wani gajeren lokaci, sai ta ji nan take dukkan damuwarta ta gushe. Cikin sanyin murya ta ce da shi: “Ina jin daxin magana da kai. Kana matuqar faranta min rai! Na goge da sauraren kokena da kake yi!”


21

A Yau Lahadi 1 Ga Afrilu, 2018 (14 Ga Rajab, 1439) Tare Da Bilkisu Yusif Ali – 08054137080– bilkisuyusuf64@gmail.com

Daga Na Gaba...

SP Magaji Musa Majia: Gwarzonmu Na Mako Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja A makon jiya ne, wato daidai da ranar 14 ga Maris, 2018, rundunar ’yan sanda ta jihar Kano a qarqashin jagorancin Mai girma Kwamishinan ’yan sanda na jihar, Alhaji Rabiu Yusuf, ta sanya sunan SP Magaji Musa Majiya daga cikin waxanda ta yiwa qarin girma daga muqamin Muqaddashin Sufurtandan Xan Sanda (DSP) zuwa muqamin cikakken Sufurtanda, wato SP. Idan za a iya tunawa, SP Majiya, wanda shi ne jami’in hulxa da jama’a na rundunar ’yan sanda jihar Kano, a shekara ta 2015 ma ya na cikin jajirtattun ’yan sandan da su ka yi abin a zo a gani a ka yi mu su qarin girma, inda ya sami kai wa ga muqamin da ya wuce a yanzu na Muqaddashin Sufurtandan ’yan sanda, wato DSP. Hakan ya na gwada irin qwazon SP Majiya ya ke nuna wa a kan aikinsa na wayar da kan jama’a da samar da kyakkyawar alaqa tsakanin rundunar da jama’ar jihar ta Kano. Waye SP Magaji Majia? An hafi SP Magaji Musa Majia a ranar 15 ga Satumba, 1978 a yankin qaramar hukumar Kumbotso ta jihar Kano. Mahaifinsa shi ne Alhaji Musa Magaji Majia. SP Majia ya na da shaidar babbar difloma (HND) a vangaren daqile aikata miyagun laifuka (National Diploma in Crime Management, Prevention and Control) kuma yanzu haka ya na karatun digiri na malumta a fannin Turanci da Hausa da ke Jami’ar Bayero ta Kano. SP Magaji ya na da aure da kuma ’ya’ya. Abinda ya fi sha’awa a raywarsa shi ne warware rikici da wasan kati. Wane Ne Shi A Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya? SP Majia ya shiga aikin xan sanda ne a matsayin Sufeton Kadet (Cadet Inspector) a ranar 15 ga Agusta, 2002. Ya yi aiki da rundunar ’yan sandan a yankunan Nijeriya daban-daban, kamar jihohin Lagos, Nasarawa, Zamfara da kuma Kano da ya ke aiki a halin yanzu a matsayin jami’in hulxa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar. Majia ya samu xare wa muqamin Mataimakin Sufurtanda (ASP) ne tun a ranar 1 ga Janairu, 2009. Ya zama jami’in hulxa da jama’a na rundunar ’yan sanda ta jihar Kano ne a ranar 13 ga Yuni, 2010. Wato bayan shekara xaya da watannin sa samun wancan muqami na ASP. Amma gabanin naxa shi wannan muqami, shi ne mai riqe da muqami na biyu (Second in Command) na sashen kula sha’anin laifukan ababen hawa na rundunar jihar, Motor Traffic Division (MTD). Tun a ranar 16 ga Disamba na 2015 ne Malam SP Magaji ya samu cigaban muqami, inda ya zama Muqaddashin Sufurtanda (wato DSP). SP Majia ya ya samu damar halartar kwasa-kwasai da dama, waxanda su ka taimaka ma sa wajen gogewa da naqaltar aikinsa na xan sanda, wanda hakan ke sake tabbatar da irin nasarar da ya ke samu a bakin aikinsa ba a banza ta samu ba.

Ya halarci irin waxannan kwasakwasai kamar haka; Citizenship and Leadership Training a Shere Hills da ke Jos, Combat Training Course a garin Gwoza da kuma First Aid Training da a ke yi a makarantar National Institute of Public Relations Practitioners (NIPR) Course a birnin Ikko. Ya kuma halarci wani kwas na qwararru mai suna Capacity Building Workshop da a ke shirya wa jami’an hulxa da jama’a wanda a ka gudanar a jihar Kaduna. Sai kuma Capacity Building Workshop a jihar Akwa Ibom da samina kan Responsibility to Report a Babban Birnin Tarayyar Nijeriya Abuja. Bugu da qari, sabon SP, Malam Magaji Majiya, ya samu karrama wa daban-daban, waxanda su ka haxa da ta jami’in hulxa da jama’a mafi qwazo a 2014, “Most Outstanding Police Public Relations Officer in Nigeria 2014”, wanda Security Watch Africa ta ba shi. Ya samu kambun yabo na Kwamishinan ’Yan Sanda Kan Aiki Don Allah Da Jin Qai, wato Commissioner of Police Commendation Award for Service to Allah and Humanity, wanda qungiyar masu ruwa da tsaki ta Kano State Stakeholders and Police Partnership ta ba damqa ma sa. Ita ma qungiyarmu ta ’yan jarida reshen jihar Kano, NUJ Kano, ta karrama SP Majia xin da lambar yabo ta Chapter Award for Good Public Relations. Haka nan SP Malam Magaji ya zama Jakadan Zaman Lafiya jaridar Translator News, Ambassador for Peace Award by Translator News da kuma kyautar girmamawa ta Excellence Award, wacce qungiyar xalibai ’yan asalin jihar Kano reshen jami’ar Bayero su ka ba shi, wato National Association of Kano State Students (NAKSS) BUK Chapter. Majia bai tsaya a nan ba, sai da ya lashe kyautar Mafificin Jami’in Hulxa da Jama’a a yankin Arewa maso Yamma, wato Best Police Public Relations Officer in North West Zone Award daga Nollywood Motivational Leadership Award Series 2014. SP Majia ya kuma samu lambar yabo daga qungiyar ma’aikatan rediyo da talabiji ta Nijeriya, RATTAWU, kan bai wa manema labarai haxin kai da ya saba yi, wato Positive Response Given to the Press. Haka nan qungiyar Abokai ta gidan rediyon Freedom, Friends of Freedom Radio Association (FOFA) Kano Nigeria, a shekara ta 2016 ita ma ta ba shi karrama wa ta Efficiency for Dedication to work in Kano State. Sannan ya samu satifiket xin yabo daga Kano State Peace and Conflict Resolution Association and Inuwar Marayu Trust, baya ga wata takardar yabon kan dangantaka tsakanin ’yan sanda da jama’a a Kano da Nijeriya, Police Public Relations in Kano and Nigeria, wacce gidajen rediyon Cool da Wazobia su ka ba shi mai taken Cool/ Wazobia FM COWA AWARDS a 2016. SP Magaji ya kuma samu kyakkyawan yabo daga kwamandan rundunar sojin Nijeriya Bataliya ta uku, Birgediya Janar Abbah bisa hazaqarsa wajen xaukar matakin gaggawa a kwamitin haxaka musamman kan Boko Haram a jihar ta Kano.

• SP Majia

Wacce Rawa SP Majia Ya Taka? Haqiqa SP Majia ya amsa taken nan na ‘Xan Sanda Abokin Kowa’, musamman idan a ka yi la’akari da yadda ya ke tafiyar da aikinsa a yayin alaqa da jama’ar gari da kuma abokan aiki, wato ’yan jarida. Ya na gabatar da shirye-shirye na wayar da kai a kafafen yaxa labarai daban-daban a jihar, domin tunatar da al’ummar jihar matsayin doka da kuma xora su a bisa turba ba tare da sun taka ta ba, ballantana a kai ga matsala, wanda hakan ya taimaka gaya wajen rage aikata laifuka a faxin jihar. A irin waxannan shirye-shirye da ya ke gabatarwa a kafafen yaxa labarai na kai-tsaye ya na amsar koke-koken jama’a, domin xaukar matakan da su ka dace, sannan kuma ya na yarda da suka na gaskiya da a ka yiwa rundunar ko ma’aikatanta, domin gyarawa ba tare da vatanci ba. Ya yi qoqari wajen ganin an samu dangantaka mai kyau tsakanin jagororin addinai, qabilu da na gargajiya a jihar, domin dama wa da kowane vangare. Shi ne wanda ya qirqiro dabarar nan ta amfani da raba takardu ga jama’a, domin qalubalantar yaxa jita-jitar da wasu masu alaqa da Boko Haram su ke yi a yankuna irin na unguwannin Hotoro, Tishama, Haye, Kawo, Wuro Bagga a yankin qaramar hukumar Nassarawa da kuma ungwannin Bubbugaji, Farawa da saransu a yankin qaramar hukumar Kumbotso na jihar ta Kano a zamanin tsohon kwamishina a jihar kuma a yanzu mataimakin babban sufeton ’yan sanda na qasa, IGP Ibrahim K. Idris. Kyakkyawar alaqar da SP Magaji ya ke da ita ce ta sa shi kaxai ya kashe wutar rikicin da ta kunno kai a jihar Kano lokacin da a a zargi wani mutum da cin zarafin Manzon Allah (SAW), inda wasu daga cikin al’ummar garin, musamman matasa, su ka banka wa kotun Shari’ar Musulunci, wacce a ka gurfanar da mutumin, wuta a unguwar Rijiyar Lemo a zamanin IGP Ibrahim Idris (NPM, mni). Isowar SP Majia wajen ke da wuya sai matasan su ka risina ma sa bayan da ya yi mu su kalaman kwantar da

hankali, inda ya roqe su da su mayar da wuqar, ya na mai tabbatar mu su da cewa, qone kayan gwamnati ba shi ne mafita ba, illa dai a saurara a ga hukuncin da zai biyo baya. Wannan qwarewa ta kashe wutar rikici da harshe ba da takobi ba da SP Majia ke da ita na nuni da yadda ya sauya salon irin kallon da a ke yi xan sanda yanzu a jihar ta Kano. Bugu da qari, a wata rana Majia ya sake nuna irin hazaqarsa da qwarewarsa ta aiki a yayin da wata wutar rikici ta tashi a kan Titin Haxeja lokacin da a fara tayar da qayar baya sakamakon hatsari da wasu jami’an ’yan sanda su ka haifar a hanyar ranar wata Asabar da a ke gudanar da tsaftar muhalli a 2015. Duk da cewa, shugabannin gargajiya da na addini sun yi iyaka qoqarins wajen roqar matasan da su ka datse hanyar fiye da kimanin awannin uku, amma ba su bari ba, zuwan Majia wajen ne ya kashe wutar rikicin bakixayanta nan take. Gabanin zaven 2015 qabilun da ba ’yan asalin jihar Kano ba ne sun yi ta faman ficewa daga garin, saboda fargabar abinda ka-je-ya-komo, wanda hakan ba qaramin vatanci ba ne ga Kanawa da a ka san su da karvar baqi. Nan da nan SP Majia ya yi ta-maza ya shirya ganawa ta musamman da shugabannin waxannan qabilu ya na mai tabbatar mu su da kula da rayukansu da dukiyoyinsu. Maganar Majia ta kuwa tabbata, domin an gudanar da babban zaven 2015 a jihar Kano ba tare da an kashe ko xan tsako ba a zamanin tsohon kwamishina Ibrahim Idris. Shi ma kwamishinan ’yan sandan jihar Kano na yanzu, CP Rabiu Yusuf, ya nuna wa duniya yadda ya gamsu da qwarewar SP Majia, ganin yadda ya naxa shi kula da wani tsari na amsar qorafi daga jama’a, Public Complaint Forum, inda waxanda ke da qorafi kan jami’an tsaro da su zuwa gidajen rediyo su kai kukansu, sai a riqa gabatar wa ga Forum xin, don warware matsalar cikin sauqi. Haqiqa shi ma wannan mataki ya dawo da martabar rundunar ’yan sanda ta jihar a idanun al’umma qarqashin SP Majia.


22

A Yau

LAHADI 1.4.2018

Arewa HipHop

Tare da UMAR MUHSIN CIROMA ‘Smartkid993@gmail.com Instagram: Smartkid.skd_official 08104314052

Manyan Arewa Ba Sa Ba Mu Qwarin Gwiwa –X_Dough Xaya daga cikin sanannun mawaqan Hausa na Hiphop, AHMAD IBRAHIM BABAJO, wanda aka fi sa ni da ABOKINA X_DOUGH, ya yi maganganu masu mahimmanci ya kuma bayyana cewa manyan Arewa ba sa ba su qarfin gwiwa. Ya bayyana hakan ne a wannan muhimmiyar tattaunawar da su ka yi da wakilin LEADERSHIP A YAU LAHADI, UMAR MUHSIN CIROMA. Ga yadda hirar ta kasance:

To, da farko dai masu karatun mu za su so mu san cikakken sunanka da kaxan daga cikin tarihinka. To, ni sunana Ahmed Ibrahim Babajo. Kuma haifaffen garin Kaduna cikin birnin zazzau, a Kaduna na girma, mu a gidan mu mu biyar ne mata huxu ni kadai ne na miji. Ko za mu san abun da ya ja hankalinka ka fara waqa? To, ni gaskiya tin ina yaro mutun ne mai sha’awan jin waqe-waqe da qoqarin rera wa, baran manta ba na fara yin waqa a studio tin ina dan Jss 1, gaskiya waqan lokacin ta karvu sosai a makarantan mu lokacin. Ko zaka iya gaya mana sunan waqar? Sunan waqan TIRED OF RUNNING. A wani shekara ka fara waqa? Na fara waqa ne a shekaran 2009.

Za mu so mu ji kaxan daga cikin tarihin karatunka? Ni nayi firamari xina a Capital School dake kaduna, daga nan kuma na koma karshi dake Abuja nayi sakandiri, sannan na sake dawo wa Kaduna nayi Imperial College, nayi karatun a Ghana telecom university, anan nayi jami’a. Ya ka ke gurin qoqarin haxa waqa da karatu. Abu ne mai wahala gaskiya, amma haka nake qoqartawa.

Amma wani qoqari ka ke na ganin kun samu haxin kai gaba daya? Idan mun haxu ina cire girman kai inje mu gaisa kuma in qarfafa masu, Amma ina nunan musu da ina yin haka ne saboda dikan mu ‘yan Arewa ne. ni kwata kwata ban gasa da kowa ko in haxa kaina da wani dika ni banyin haka. Za ka iya gaya mana wasu daga cikin lambar yabo daka samu daga lokacin daka fara waqa kawo yanzu? Eh, Har nagama Secondary School ni nake cinye best artist a wancan lokacin, kuma na samu Kaduna best rap actist 2016, da dai sauransu. Wane irin qalubale ka fuskanta daga lokacin da ka fara waqa? Na samu matsaloli da dama a gun dangi na, Saboda na fito daga babban gida a Zariya, Kuma bamu gaji sana’ar waka ba. Dan haka ban samu goyon baya ba daga yan uwana a harkan waqa, Duk waqoqi na ni ke rubutawa kuma nike xaukan nauyin kuxin buga abuna. Ya ka fuskanci Duniya lokacin da aka fara gayyatar ka wasanni? Gaskiya na samu qwarin gwiwa da aka fara gayyata na wasanni a biya ni Kuma a karramani yanda ya kamata.

Ko za ka iya lissafa mana sunanyen wasu daga cikin waqoqinka? Darasi, Illuminati, Tuwon Zafi ft NT4 Ghana, My life , Yallabai ft Classiq, Love Me Later. Kwanan nan na saki sabon Mixtape Album Mai suna AOTM. akwai waqoqi 16 da ya fita ya na kasuwa da kuma intanet.

Wani irin qoqari kake don ganin ka faranta ma masoyan ka musamman ta hanyar sada zumunta? Ina qoqarin sada zumunci ga masoyana a kafofin sada zumunta, Ina qoqarin amsa wasikun masoya kuma na mai da musu martini dik wanda zan iya saboda saqonni ke shigowa iri iri da yawa sosai daga Nijeriya har sauran qasashen African.

Waqar Darasi na xaya daga cikin waqoqinka da suka karvu matuqa a ko’ina, musamman nan Arewa. Ko za ka iya gaya mana darussan da su ke qunshe a cikinta? Darasi waqa ce dana yi da Freestyle inda a cikin nake gabatar da kai na ga al’umma baki xaya.

Baya ga waqan da ka ke yi ka na da wani sana’a ne? Ina sana’ar kai kawo da ababen hawa kamar mota da keke napep Wanda ake mun aiki dasu, Kuma a harkan wakan aka sa mu dukiyar da ake sana’ar dasu.

Me kalmar AOTM ta ke nufi? Ma’anar AOTM shi ne, Aboki On The Mic.

Wani irin qalubale ka ke fuskanta a matsayinka na mawaqin Arewa? Gaskiya mawaqan Arewa gaba xaya bamu da haxin kai, kuma bama samun qarfin gwiwa daga manyan mutanen Arewan. Ko za ka iya gaya mana dalilin da ya sa ka ce mawaqan Arewa ba su da haxin kai? Eh, ni ma bansan dalilin da ya sa Babu hadin kai a tsakanin mu ba.

Ko za mu iya sanin sunan wasu muhimman garuruwan da ka je wasanni? Kano, Kaduna, Sokoto, Kebbi, Abuja, Nasarawa, Jos, Zamfara, Minna, Katsina, Lagos. Daga yanzu zuwa nan da shekara 5 wani kalan hidima kake shirin ma Arewa Hiphop? Nan da shekara 5 insha Allah zamu sa duniya hankalinta ya karkata akan Hausa hip hop. Ka na da qungiya ne ko kana zaman kanka? Ba ni da qungiya; ni kaxai na ke abuna, amma Ina da kyakkyawan mu’amala da Arewa Mafia,

mun fahimci juna da su. A matsayinka na shahararren mawaqin Hiphop kuma abin koyi ga wasu al’ummar, wacce irin shawara zaka ba ma matasa masu tasowa waxanda su ke da ra’ayin waqa? Shawara na shi ne matasa suyi qoqari su bada himma wajan makaranta da kuma su daina kwaikwayon mawakan qasashan waje. Ko za mu ji dalilin da ya sa ka ce matasa su dai kwaikwayon mawaqan waje? Saboda da yawan matasan mu suna karya harshe kuma suna son shiga irin nasu, Saka xan kunne, Ass down da sauran su, Wanda ba al adan malam Bahausha ba ne. To, bari mu dan tava nishaxi kaxan akan abun da ya shafe ka. Wacce kalar mota ka fi so? Wane irin abinci ka fi so? Wacce qasa ka fi sha’awar ka je? Ina sha’awar Black Car. Abinci kuma Ina son tuwo da miya. Ina sha awar zuwa Amerika, don qaro ilimin harkar waqa. Daga qarshe kuma me za ka ce wa masoyanka? Ina ma kowa fatan alkhairi kuma a ci gaba da bamu goyan baya, shi zai qara min qarfin sa ka Hausa a cikin Map xin Duniyar mawaqa, Kuma su bini a Social Media na domin samun sababbin waqoqi na. Instagram @xdough_abokina, Twitter da Facebook ma haka. Na gode.


23

A Yau Lahadi 1 Ga Afrilu, 2018 (14 Ga Rajab, 1439)

Gwamnatin Bauchi Na Kawo Cikas Kan Ayyukan Da Ahmed Yarima Ya Kawo –Usman Misau Ofishin mazavar xan majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar Misau da Dambam a Jihar Bauchi MALAM AHMED YARIMA Sarkin Malaman Misau ya jima yana qorafi game da cikas da ake kawo musu a yayin gudanar da ayyukan da aka nemo daga gwamnatin tarayya don gudanar da su a mazavar. Amma suna qorafin samun matsala game karan tsaye da gwamnatin Jihar Bauchi ke kawowa na gayyatar jami’an tsaro don hana gudanar da ayyukan da wakilai ke samowa daga gwamnatin tarayya a yankunan, inda muqarraban gwamnan a duk lokacin da za a gudanar da irin waxannan ayyuka ke sanar da gwamnati don a kawo cikas da nufin ba a son wani aiki sai na gwamna. Amma yankin Misau sun fi samun wannan matsala yadda a kullum ake kai ruwa rana kan hana irin waxannan ayyukan. Don haka wakilin mu a Bauchi MUAZU HARDAWA ya gana da ALHAJI USMAN BELLO MISAU Kodinetan Ahmed Yarima a yankin Misau da Dambam, don jin ta bakinsa ga yadda tattaunawar su ta kasance: Me za ka ce game da matsalolin da ku ke fiskanta tsakanin ku da gwamnati kan wannan lamarin? Sunana Usman Bello Misau Kodinetan Ahmed Yarima xan majalisar wakilai mai wakiltar Misau da Dambam a Jihar Bauchi, haqiqa game da yadda muke gudanar da ayyukan da xan majalisa ya samo daga gwamnatin tarayya mun fiskanci matsaloli da dama na kawo cikas kan gudanar da ayyukan da xan majalisar tarayya mai wakiltar Misau da Dambam Hon. Ahmed Yarima Sarkin Malaman Misau ya ke nemowa daga gwamnatin tarayya a matsayin sa na wakili. Irin waxannan ayyuka da muka nemo suna da yawa amma waxanda muka fiskanci matsala kafin suka gudana sun kai guda shida amma mun gudanar da su cikin wahala da adawa mai tsanani, yadda an kai wani yanayi da sai mutanen gari sun tashi tsaye suna gadin ayyukan da aka fara dare da rana kafin a samu damar kammala irin waxannan ayyuka. Kamar waxanne ayyuka kuka nemi gudanarwa amma aka hana ku aiwatarwa? Ayyukan suna da yawa amma mun yi qoqari kuma mutane tunda suka fahimci ba ci gaban su gwamnatin ke so ba ta fi mayar da hankali wajen gaba da adawa don haka suke tashi su tsaya har sai sun ga komai ya kammal kafin su bar kwana a wurin. Game da irin ayyukan da muke yi, musamman akwai gina tankunan ruwa da rijiyoyin burtsatse da xan majalisa Ahmed ya kawo a yankinsa daga gwamnatin tarayya gwamnati ta yi tsaiwar mashi qarqashin kantoman Misau na lokacin wajen ganin ya daqile gudanar da su har sai da mutanen garuruwan suka tashi a tsaye kafin aka kammala. Gwamnatin Bauchi sun kai yanayin da suke gayyato jami’an tsaro don cirewa ko hana gudanar da ayyukan a Sarma yadda aka buqaci yin tankin ruwa da rijiyoyin burtsatse sai da suka tsaya da nufin ba za su bari a yi ba amma mutanen gari suka bijire musu suna kwana suna tashi a wurin kafin aikin ya kammala. A garin Akuyam mun gina

azuzuwan makaranta guda shida da bayan gida huxu lokacin aikin gwamnati ta ce ba za a yi ba sai da aka tsaya sosai kafin ya kammala bayan gwamnati ta hana gudanar da aikin mutane sun tsaya ba dare ba rana kafin aka yi aikin. Akwai magudanar ruwa a garin Gwaram da aka buqaci yi sai da aka kai ruwa rana kafin mutanen gari suka tsaya suka nunawa kantoman Misau na lokacin wato Mohammed Lele suna buqatar wannan aiki kafin aka bari aikin ya gudana. A Dallari da Tofu akwai tankin ruwa da aka yi sai da aka tsaya aka jajirce kafin suka bari aikin ya kammala. Haka a garin Jarmari akwai ayyuka da su ma sai da aka tsaya kafin aikin ya kammala. A Hardawa an kai transformer da suka jima suna nema gwamnatin Bauchi ta samar musu amma sama da shekara babu, sai suka koka wa xan majalisa Ahmed Yarima ya sayo ya kawo aka sanya wuta ta dawo musu amma sai kwamishinan kuxi Alhaji Garba Sarki Akuyam ya zo da jami’an tsaro da nufin sai an cire gwamnati za ta kawa, amma mutanen gari suka tashi tsaye hard a qone qone aka jibge jami’an tsaron soja da ‘yan sanda har Allah ya taimaka da kyar mutanen suka tsaya kafin ya zamanto ba a cire ba bayan sun yi watanni sha huxu sun gagara kawowa kafin xan majalisa ya kawo. Don haka jami’an tsaro sun yi aikin hankali sun nemi kwamishinan ya tafi ba za a cire ba don haka aka bar wannan transformer kafin idan gwamnati ta ga dama sai ta kawo nata a sa a duk inda ake so. Yaya kuke nazartar wannan rigima da ke faruwa tsakanin gefen gwamnati da ‘yan majalisu? Gwamnatin Mohammed Abdullahi Abubakar a Jihar Bauchi tana kawo cikas ga wakilan da suke son yin aiki domin mutanen su, duk da cewa ta gaza kawo ayyuka da za su inganta rayuwar mutane kamar yadda gwamnatocin baya suka aiwatar. Don haka yawancin ayyukan da wannan gwamnati ta sa gaba don aiwatar da su basa gudana yadda aka tsara saboda za ka taras da aikin da aka bayyana cewa za a kammala cikin shekara

guda amma har yau shekara uku ba a kammala aikin ba sai jan qafa. Amma idan wakilai da ke tarayya sun tashi tsaye sun nemo ayyukan sai a fara rigimar cewa ba za su yi aikin ba da nufin cewa ba a buqata sai ko a jira aikin gwamna alhali cikin jiha ba aikin yadda ake zato ballantana aje zuwa wajen jihar Bauchi, kuma duk ‘yan jami’iyya gudane APC amma son zuciya ya sa ana kawo cikas wajen samar da ayyukan ciyar da qasa gaba. Ahmed Yarima ya yi qoqari wajen samar da ayyuka don ya nunawa mutane ya damu da damuwar su amma gwamnatin jihar Bauchi tana kawo cikas wajen hana gudanar da yyukan ciyar da qasa gaba, basa tunanin idan sun kawo aiki wani ya kawo sai a taru a gina qasa. Amma abin da suke yi wajen nuna tsantsar adawa da ayyukan da wasu ‘yan siyasar tarayya ke nemowa wannan ba alheri cikin lamarin sai ko kawo cikas da hana ruwa gudu wanda ke haifar da naqasu wa al’umma da ci gabanta. Kowane wakili a tarayya ya kan anemo ayyukan da za su taimaki mutane don ciyar da su gaba amma musamman wannan gwamnati basa qaunar ayyukan da mutane za su amfana idan ba wanda suke son gudanarwa wannan kuma ba ci gaba cikin lamarin. Mutane na qorafi wakilai irin su Ahmed Yarima sun tare a Abuja ba sa zuwa yankun su me za ka ce? Ai dama an zave su ne don su tafi yin wakilci ne kuma su nemo ayyukan ci gaba daga kasafin kuxin qasa tare da tattauna matsaloli da magance su ta hanyar bayar da qudiri da za su taimaki mutane tare kuma da tabbatar da cewa an yi amfani da wannan qudiri yadda ya kamata. Kuma Ahmed Yarima yana zuwa mazavarsa gwargwadon hali yana ganawa da mutane a duk lokacin da ya shigo, don haka idan an ce baya zuwama mazavarsa ta Misau da Dambam don jin ra’ayoyin mutane da damuwar su wannan magana ce ta adawa, kuma ana ganinsa a talabijin game da irin qoqarin da ya ke yi wajen kare qasa da mutane tare da neman talaka ya amfana daga ayyukan da ya ke buqata da kuma bayar da wakilci mai kyau don amfanin mutanen qasa da yadda za a musu ayyukan

•Usman Bello

da za su amfana.

Mutane na qorafin ana kiransa shi Ahmed Yarima ba a samun sa ko ba xaga waya? Wannan aiki ne na masu gulma da mita da adawa wanda a kullum ya na samun xaruruwan saqonni da kira kuma ba wanada ya san a irin yanayin da aka qira ta yiwu yana hidimar aiki ko ta iyalansa ko hidimar qashin kansa amma idan mutum ya ji bai xaga ba sai ya yi ta qorafi, alhali ko waye ke samun yawan kiran da ake musu shima ba zai xaga wani kiran ba sai ya gaji. Kuma idan an qira bai xaga ba yana bitar qiran yana kiran su xaya bayan xaya amma waxanda suke kiran sun mance kowa buqatarsa ke bayyanawa ba ta jama’arsa ba, iya alaqar da zai yi da mutane yana yi a matsayin sa na xan adam ba zai iyarma kowa ba, don za ka taras kira xari ko fiye ya shiga cikin wayar sa a awa guda to yaya mutum zai yi ko shi ake qira a irin wannan yanayi. Don haka irin wannan magana ce ta neman a vata mutum a idon duniya don haka mutune ya kamata su fahimci yanayin rayuwar mai hulxa da mutane kamar xan majalisa akwai bambanci da ta sauran jama’a wajen samun lokacin xaga waya a kowane lokaci aka qira shi.


24

ADABI A YAU

A Yau LAHADI 01.04.2018 Tare da Adamu Yusif Indabo 07038339244 ay1indabo@gmail.com

Marubuci Da Jigo Daga Daga Lawan Muhammad

Prp 08166473270 Email address: muhdlawanprp@gmail.com

A ranar Lahadin qarshen makon da ya gabata ne 25/03/2018, qungiyar marubutan Hausa zalla ta HAUSA AUTHORS FORUM ta gabatar da taronta na al’ada da ta saba a ranar Lahadin qarshen watan mai jan kunne, a KURNA SPECIAL PRIMARY dake kan titin Katsina, Kano. Taron dai ya tara manyan marubuta da suke ‘ya’yan qungiyar, da shugabanni na da da kuma na yanzu. Maqasudin yin taron dai shi ne, don tattauna lamuran da suka shafi qungiyar, tsefe littattafan ‘ya’yan qungiyar da kuma qarawa juna sani. To a wannan watan Malam Lawan Muhammad Prp, marubucin littafin GIDAN HAYA, KWANAN GIDA, BAQIN DARE da dai sauransu, shi ne ya gabatar da maqala mai taken MARUBUCI •Wasu daga cikin marubutan qungiyar HAF DA JIGO maqalar da ta sha yabo saboda tarin ma’anoninta da yadda rubutu a kansu, ko kuma yin tattalin arziki, jarumtaka, fashi, aka fayyace komai daki-daki, kuma duba da sashen wasu mutane zamba cikin aminci, soyayya, ta sha ragargaza ta wani vangaren. a rayuwarmu ta zahiri wanki kiyayya, zaman banza, da Ga dai maqalar tsaraba ga rayuwarsu a mayar da ita labari sauransu. mabiya wannan shafi da wakilin cikin sauki. Irin wannan labarin Jigo yakan kunshi abu mai ADABI A YAU ya zo mana da ita. A shi ake cewa ‘true life story’ (wato kyau da mummuna. Misali, a sha karatu lafiya. labarin da ya faru a gaske) duk labarin da ya kunshi karuwanci da masana sun tabbatar babu ko sata ko fashi da makami ko Kafin mu yi magana akan jigo ta yadda za a yi ka dauki labarin zamba cikin aminci. Marubucin yana da kyau mu fara sanin wane gaskiya ba tare da ka cudanya zai nuna hanyoyin da masu ne Marubuci. shi da tunaninka (na kirkira) wadannan harkoki ke rayuwarsu Marubuci shi ne mutumin ba. Irin wannan karin gishiri shi kafin a karshe ya nuna yadda dake zama ya kirkiri labari ya ke kara armasa labari, ta yadda suka kare ba da kyau ba, wato rubuta da nufin fadakarwa, za a samu rike mai karatu ta dai Marubuci zai nuna illar nishadantarwa, gami da hanyar kyautata rukunan gina wadannan abubuwa a karshen ilmantarwa akan abin da ya shafi labari, wato Jigo, Salo da Sarrafa labarinsa. rayuwar yau da kullum. Haka harshe, Zubi da tsari. Misali, littafin ‘’Yar tsana’ kuma ana kallon marubutan Wadannan rukunan suna da na Malam Ibrahim Sheme ya al’amuran yau da kullum a jarida matukar muhimmanci wajen nuna illar karuwanci ne, yayin ko mujalla a matsayin Marubuta. samar da labari, ta yadda idan da littafin ‘Karshen alewa kasa’ Rabe-raben Marubuta babu daya a cikinsu ko kuma ba a yake nuna illar daukar fansa ta - Marubutan litattafan addini yi shi yadda ya kamata ba labarin mummunar hanya. (na shari’a) zai zama lami (miyar da ba - Marubutan Alkur’ani gishiri ko shayin da ba sukari). Ire-Iren Jigo - Marubutan Kimiyya Akwai muhimman abubuwa Jigo ya rabu iri biyu kuma - Marubutan kirkira da suke jinginuwa da wadannan ana samun su a kusan kowanne Da duk wani marubucin wani rukunan, amma dai za mu fara labari. abu da ya shafi rayuwamu ta daukar wadannan rukunan daya Su ne, karamin jigo da babban zahiri. Duka wadannan ana yi bayan daya domin saukakawa ga jigo. musu kallon Marubuta. masu bibiyar filin. Babban jigo shi ne abin da aka A takaice dai duk wani mutum gina labarin a kansa, wanda kai da zai yi rubutu ya yada a cikin Jigo tsaye ya shafi babban tauraron al’umma don amfanin al’ummar Jigo shi ne gundarin abin da labarin, misali, Zainab (Asabe) sunansa Marubuci. labari ya kunsa, kuma shi ne a littafin ‘’ Yar tsana’ da kuma Wannan shi ne ma’anar tushen gina kowanne labari. Duk Mailoma a littafin ‘Karshen Marubuci a takaice. labarin da ba shi da jigo aka ce za Alewa Kasa’ Amma za mu tattauna ne akan a samar da shi, to kamar a yi gini Karamin jigo kuwa yana shafar rubutun kirkira, sauran nau’ikan ne babu tushe (foundation). kananan taurarin labarin walau rubuce-rubucen kuwa bincike da Dole ne kowanne labari ya kai tsaye ko kuma a hikimance. ilmi ne ke samar da su. Duk da samu jigo kafin rubuta shi. cewa shi ma rubutun kirkirar na Jigo Tahaqiqi Da Jigo Jimla bukatar bincike. Misalan Jigo: Dukkanin wadannan jigogi Jigo yana da yawa, kuma ya guda biyu suna jinginuwa i zuwa Yaya Ake Samar Da kirkirarren danganta da yadda Marubucin sunan labari. Ma’ana daga sunan Labari? ya shirya rubuta labarin ko aka labarin za a fahimci jigo tah’ki’ki Ana samar da labari ne ta sa shi ya rubuta. ne ko jigo jimla. hanyar tunani akan rayuwar Misali, akwai jigon sata, Shi jigo tah’ki’ki shi ne sunan wasu mutane da ake son yin daukar fansa, karuwanci, talauci, labarin da ba za a taba gane me

labarin ya kunsa ba (kai tsaye) daga jin sunansa, har sai mai karatu ya karanta labarin gaba daya. Misalin irin wannan labari shi ne, Zuciya Da Kwanji na Maimuna Idris Sani Beli. Mafi yawan sunan labari mai kunshe da jigo tah’ki’ki kalmominsa ba su da tsawo kamar na jigo jimla, wato wata ‘yar kalma ce ko guntayen kalmomi da aka kirkiri jigon labarin da ita. Jigo Jimla kuma shi ne sunan labarin da daga jin sa mai karatu zai gane ina ya dosa. Misali, littafin Tsallake Rijiya Da Baya na Jamilu Haruna Jibeka. Mafi yawan jigo jimla an fi amfani da karin magana ko kirari ko suna wajen gina shi. Misalin masu kirari ko suna: Sihirtacce - Bala Anas Babinlata Kulu - Bala Anas Babinlata Rayya - Kabiru Yusuf Fagge In Da So Da Kauna - Ado Ahmad Gidan Dabino Tarzoma - Aminu Ladan Abubakar (Ala) Da sauransu. Misalin masu karin magana: - Sara Da Sassaka... - Bala Anas Babinlata - Idan Bera Da Sata... - Dan azumi Baba Cediyar ‘Yan Gurasa - Dan Kuka... - Rabi’at Adamu Shitu - Karshen Alewa Kasa - Bature Gagare Da sauransu. An karanta wannan takarda a taron Marubuta na kungiyar marubuta litattafan Hausa ta Hausa Authors Forum (HAF) ranar Lahadi 25 ga watan Maris, 2018.


RAHOTO

A Yau Lahadi 1 Ga Afrilu, 2018 (14 Ga Rajab, 1439)

25

Umar Buba: Jihar Kogi Ta Yi Rashin Nagartaccen Shugaba, In ji Gwamna Bello Daga Khalid Idris Doya, Abuja

A shekaran jiya Juma’a ne Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya nuna matuqar ximautarsa bisa rasuwar xaya daga cikin shahararrun ‘yan siyasa a jihar Honorabul Umar Buba Jibril. Marigayin wanda shi ne ke wakiltar mazavar Lokoja/Kogi a majalisar wakilai ta qasa, ya rasu ne a Juma’a nan da ta gabata a birnin tarayya, sakamakon wata

gajeruwar rashin lafiya. A cikin sanarwar da ya fitar xauke da sanya hanun Darakta Janaral kan harqoqain watsa labarai na gwamnan, Kingsley Fanwo, ya misalta marigayin a matsayin wani mutumin da ya rayu da son zaman lafiya da wanzuwarta a kowani bigire, ya bayyana cewar jam’iyyar da ke mulki a jihar ta yi rashin wani givi mai wuyar cikewa. Marigayi Umar Buba Jibril wanda mamba ne da ke wakiltar

mazavar Lokoja/Kogi a majalisar dokoki ta qasa, kuma tsohon Kakakin majalisar dokokin jihar Kogi, har-ila-yau kuma gwamnan ya misaltasa a matsayin mutum mai son jama’a da qaunar juna. Gwamna Yahaya Bello ya ce, “Marigayi Jibril an shaideshi da kyautata wa jama’an mazavarsa ya kuma zauna da su lafiya. Ya samu nasara gaya a hidimar siyasarsa domin ya koyar da darasussa masu tarin yawa, mutum ne wanda a kowani

lokaci ya kasance kusa da kusa da jama’ansa da kuma talakawansa,” Ya qara da cewa, “Za mu ci gaba da tunawa da irin salon shugabancinsa da ya yi a lokacin da ke raye da kuma lokacin da ke aikin hidima wa jama’a a matsayin ma’aikaci,” Gwamna Bello ya kuma ce, “tabbas mun xauki darussan sosai daga rayuwarsa a lokacin da ke raye.” Gwamnan ya bayyana shi a

matsayin wani gwarzo, haziqi kuma nagartacce, daga bisani kuma ya yi addu’ar Allah gafarta masa ya kuma jiqansa. Umar Buba Jibril, ya rasu yana da shekaru 58 a duniya, gabanin ya rasun shi ne mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta Nijeriya, haka kuma ya kasance mamba a majalisar wakilai ta qasa ne da ke wakiltar Lokoja/Kogi a qarqashin lemar APC, ya rasu ne a Abuja Jiya Juma’a.

Sojoji Sun Kame ’Yan Boko Haram Uku A Borno Daga Khalid Idris Doya, Abuja

Rundunar sojojin Nijeriya ta 23-Brigade, a qarqashin sashin musamman na ‘Operation Lafiya Dole’ sun samu nasarar kame mambobin qungiyar nan na ta’addanci wanda aka fi saninsu da sunan ‘yan Boko Haram su uku, kamen na mambobin boko haram su ukun wanda sojojin suka samu nasarar yi a qaramar hukumar Bama da ke cikin jihar Borno. Kakakin Rundunar sojojin Nijeriya, Birgediya Janaral Texas Chukwu shi ne ya shaida hakan a cikin wata kwafin sanarwa da ya raba wa manema labaru a garin Maiduguri a shekaran jiya, yana mai cewa sun kama waxanda suke zargi da Boko Haram xin ne a cikin qauyen Ngurore. Ta bakinsa, “waxanda muke zargi da kasancewa mambobin Boko Haram xin

da muka kama su ne masu suna kamar haka: Adam Yagga, Musa Kamsulum da kuma Abba Djidoum dukkaninsu sun fito ne daga Darajimal da ke qaramar hukumar Bama na jihar Borno,” In ji Texas. Chukwu ya qara da cewa, “Xaya daga cikin waxanda muke zargin mai suna Abba Djidoum, wanda ya gamu da munanan raunuka na harbin bindiga a ciniyar, ya bayyana da bakinsa kan cewar ya kasance daga cikin mayaqan Boko Haram masu aikin ta’addanci da suka addabi jama’an yankunan Izza, Wudula and Blakule dukka a Bama” kamar yadda ya shaida. Daga bisani ne kuma ya jinjina wa ‘yan qato da gora masu dafa wa sojojin wajen yaqar ‘yan ta’adda wato (Civilian JTF), sai ya buqacesu da su ci gaba da taimaka wa sojoji wajen kawo qarshen • A yayin rantsar da kwamitin musamman na majalisar wakilai kan National Assembly Legislative miyagu. Aide Forum (NASSLAF) wanda shugaban kwamitin, Kwamred Sam Melaye, ya gudanar.

Atiku Ne Ya Fi Cancanta Ya Zama Angon Nijeriya A 2019 Daga Munzir Yusuf Ali Allah kada ya kawo ranar yabo; haka Bahaushe ya ce. Haqiqa mu ’yan Nigeria yau ido buxe mu ke nema da rokon Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar da ya amsa kira ya tsaya takarar shugabancin kasar Nan a Shekara ta 2019 a karkashin Jamiyyar PDP bisa tabbacin da mu ke da shi shine kawai mafita a Nigeria Muna ta Kira da babbar murya da ka fito ka amsa kiranmu ka zama Dan takarar shugaban kasarmu saboda kyawawan halayensa da iya mu’amala da taimako da kishin kasa. Kowa ya na da shaidar da ya ke bayarwa ta Alhaji Atiku Abubakar mutum ne Mai hakuri, hadari ne in har yasa gabansa gabas na Alkhairi baya juyawa. Wasu sukace kishinsa da addinin Musulunci da San zama lafiya da kishin arewa shine jigonmu na rokonsa da ya fito. kasancewar shi haifaffen Kano ne, ya taso da tarbiyya da Jin Kai,Kuma da tausayi da rikon Amana irin na kanawa da dogaro da kansa,a kananan shekarunsa

saida ya mallakawa kakarsa gida sukutum da Jin kai da zafin Nema. Mutum ne da take Jin korafin jama’a a duk inda suka tareshi ba hantara baya guduwa ya bar kasarsa Sabanin manyanmu saidai suyi masanaantarsu akasashen ketare kada Yan asalin kasarsu su amfana . Duba da Alhaji Atiku Abubakar Wanda duk wata harkarsa ta kasuwanci a kasarsa Yake Dan Yan kasarsa su amfana ,Kuma ya rage Zaman banza. A kaf fadin Nigeria Bayan Alhaji Aliko Dangote babu Wanda Yake Samar da aikin yi sama da wazirin Adamawa. Kadan daga cikin abinda Yan Nigeria suke amfana da shi na masana’antar ruwa da ya bude wato faro. wato a kalla wadanda suke cin abinci masana’antar ba zasu lissafu fa ,ga Kuma property development company,Intels, ga Kuma noma Wanda Yake sawa ake masa kuma ya bawa mabukata abinda Yake nomawa Yafi hekta 2500. Wannan duk Muna Jin labari Kuma Muna gani bamu Kara tabbatar da Haka ba da gamsuwa saida mace Mai kamar maza Mai son talakawa

wacce kwamishiniya tayi na Dan wani lokaci ta kawo cigaban da ba a taba kawowa ba a jihar Kano wajen tallafin noma,samarwa da Matasa aikin yi, taimakon gina makarantu na islamiyya, samarwa da Mata Abinyi, har ake Mata kirari da garkuwar matan Nigeria da wayarwa da Matasa Kai a wajen Neman na Kai wato Sanata Dr baraka Umar( senator baraka) tsohuwar kwamishiniya ta noma. mun santa,mun San halinta da kishinta a Kan kasarmu mun san tana son ta ga Nigeria ta fi Haka, da muka ganta a tafiyar mun San kyakkyawan zaton da mukewa wazirin Adamawa ya wuce haka Tunda muka ga itama tana cikin tafiyar sosai. Sannan Kuma kawo maganar Karatu Wanda har makarantu yake da su Dan ilimantar da Yan Nigeria a Basu ilimi ingantacce shiyasa a jami’ar Nigeria babu kamar ta sa Wanda duk malamai Yan Nigeria suke koyarwa Kuma Yana bada gurbin Karatu kyauta ga maraya, ga Wanda bai da Hali ko Kuma Wanda ya Zama haziki . Nigeria Muna cikin wani yanayi marar misaltuwa inda muke kuka

wiwi har wani baya iya rarrashin wani saboda halin da muka tsinci kanmu Wanda bangarori mafi tsada a gun kowanne Dan Adam Mika rasasu. muhimman bangaren da ayau muke Dora hannu a ka ,shine ilimi duk Wanda ya Kwana ya tashi a Nigeria yasan ilimin Yan kasar Yana Kara tabarbarewa ga harkar lafiya,tsaro, duk wani Jin dadi da ya kamata Dan Nigeria ya huta an gaza Samar Masa da Haka shine muke rokon Dr sanata baraka Umar da ta ja jama’ arta na fadin Nigeria zuwa ga wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar da Ya amsa kiranmu, ya fito takarar shugaban kasa ,ko ma Zama yantattu mu fita daga halin bauta da fargaba da yunwar da muke ciki mu Yan Nigeria dan min gwada da yawa amma da sun hau kujerar Sai su manta da mu ,mun gaji da tura mota tana bade mu da hayaki . Shiyasa muka hada Kai muke da tabbacin Alhaji Atiku Abubakar shine amsar Nigeria. Munzir, shugaban qungiyar Nigeria Ina Mafita, ya rubuto ne daga Kano


TATTAUNAWA 26

A Yau Lahadi 1 Ga Afrilu, 2018 (14 Ga Rajab, 1439)

Qur’ani Da Hadisi Ne Dogarona – Sheikh Abduljabbar (5) A makon jiya SHEIKH ABDULJABBAR NASIRU KABARA ya tsaya ne kan dangantakarsa da gwamnati. Ga yadda tattaunawar ta cigaba tsakaninsa da wakilin LEADERSHIP A YAU LAHADI, RABIU ALI INDABAWA: Dafawa irinmu gina al’umma ne, yanzu masallatan nan da nake haxa sadaqa ni ne kaxai ba alfahari ba, Malamin da ba xan kasuwa ba, ba ma Malamin da ba Malami almajiri, amma duk Masallataina ba wanda na yi lancin haka makarantuna, idan mun tashi da ni xaliban nan muke haxa kwabo da xari, in ka ga wani daga waje shigowa ya yi. Ka duba katafaren ayyukan da muka yi, don haka ake ganin wata duniya ce a qarqashina take dafa min, yanzu dubi iya Liburaren nan, ko gwamnati ce za ta samar da littattafan nan sai an yi cikecike an kai an komo. Littattafan nan yanzu miliyan 50 ba za ta haxa su ba, amma da kwabo da xari ba sisin kwabo na gwamnati a ciki, kuma a qarshe dai me ake? Jiha ake wa aiki da su, ba jiha ba qasar gaba xaya, ba qasar ba wallahi Nahiyar Afirka gaba xaya. Littattafan nawa sun fara shiga wurare a sassan duniya suna fito da Nijeriya ana mamaki a Nijeriya akwai irin waxannan, wannan ba zai xaga Nijeriya ba? Kamar da Inyamuri ko wani mara kirki ya je ya yi damfara ko ya yi fashi qasa ta ce sunanta yake vaci, a hana biza in kun je wajen shiga ‘Airport’ a ware ku saboda wani xan qasar ya zo ya yi ba dai-dai ba? Haka sadda idan aka samu xan qasa ya yi irin wannan xaga qasar ya yi, akwai wanda ya gaya min ya ga irin littafina, ya ga Muqaddima a Tunis Foto kwafi a gidan wani babban Malami Foto kwafi. Yanzu duk gwamnati ba za ta kalli irin waxannan abubuwa ba, to ba ta dafa ba an ji kar ta dafa akwai Allah, amma sai a qyale mutum kuma ya je ya ji da kansa. Ba su dafan ba amma kullum a cikin ka wo min hari suke. To wannan shi ne babbar matsalarmu, wasu abokan rigimar mu da suka ga maganar zagin Sahabbai ta qi tasiri acikin jama’a, sun yi qoqari sun juya tunanin gwamnati sun shigo da ita cikin faxa da ni, da cutata da zalunta ta. To wannan ita ce gaskiyar magana game da zagin Sahabbai, duk wand aka ji ya faxa qarya yake, littattafai kuma Alhamdulillah gas u nan an buga, wasu kuma ma suna tafe.

Baya ga gwagwarmayarka da Qadiriyya waccan da Izala da kuma Tijjaniyya Faira, a wani lokacin kuma sai a ji ka dira kan ’yan Shi’ar da wasu ke ganin ka karkata gare su. To, yaya lamarin ya ke? Kun ji dai abinda ya ke; akwai ’yan Shi’ar da su ke maganganu kaina marasa daxi, amma me ya jawo? Ka ga wannan shi ke tabbata ma ashe waccan tuhumar ba gaskiya ba ce. Idan nix an Shi’a ne ya za mu saxa da su a wasu wuraren? Mun sava da su a wurare muhimmai, wanda ina tare da Mazhabar da aka sanni da ita, SUNNAH, wanda Shi’a ba su yarda da wannan aqidar ba ni kuma akai nake, ka ga wannan ma wata amsa ce muhimmiya da za ta za alqali da zama tsakanina da masu jifana da Shi’a, na ‘am kawai mun dace da Shi’a ne a kowane wurin da zama suna da gaskiya, ba don wannan abu Shi’an ci bane, in da wannan abu zai zama a Izala yake zan kare shi, ni tsarina ne haka. Ai mu kan haxu da Izala a wasu mas’alolin, yanzu kamar wannan zikiran na Manzon Allah, ai ‘yan Izalar ne suke ta maganarsa cewa ba a zikiran Annabi, “ ‘Yan Xariqa ba sa zikiran Annabi, ‘yan Xariqa sun gabatar da zikiran Shehunai,” amma yanzu lallai ni na xauko su na ce lallai Izala suna da gaskiya a wannan maganar da suka yin a kula nag a bamu fiya yin su ba, na kula na ga a rubuce-rubucen da na yi ma babu su gaba xaya, sai ka ga mutum ya yi maganar Xariqa ma ba zikiran Annabi jiki, in ka gansu waxannan zikiran sai tsofaffin littattafai. Yanzu littafi ya na nan da na rubuta kwanannan ‘Alkunnaasul mutawassil’ za ka gani a Muqaddinmarsa kawai shafi 100 na yi, ga ‘Waqafatun ma’assalafiyya’ akwai Malamin Izala da ya ce akwai littafin Shehu Abdulqadir RTA, mai suna Algunya “Duk wanda ya sa shi zan buga littafin Trailer guda in raba” in ji shi. Saboda suna cewa littafin yana yaqarmu mu ‘yan Qadiriyya, to da aka kwan biyu ya ji ba a sa ba, sai ya ce; “Kai in fa ‘yan Qadiriyyah suka sa littafin nan, zan biya a rediyo zan sa jama’ata mu yi kuxi-kuxi a sa a gidan rediyo Kaduna a dinga sawa.” Sai na ce to shike nan,

•Sheikh Abduljabbar

ina jin haka sai na xakko littafi na sa. To ana kwana ana tashi, da yake ba littafin ne ya dame shi ba, wani babi ne ya dame shi mai suna ‘Babu ma’arifatu sami’u azza wajalla’. Su ke ta wannan karaxin, to da aka zo wannan babin sai na zauna na yi masa rubutu na ciro shi daga littafin, shi ya sa suka daina maganar littafin, gaba xaya ba sa son sunan littafin yanzu. Saboda na warware masu zare da Abawa duk suke ganin matsala ce na nuna masu ga yadda abin yake, kuma sun ga haka ne, irin waxannan littattafan sun fi 20 bugaggu fa. Ga wannan kuma kwanannan na yi shi ‘Riyadhul Jannah min ad’iyati wa’azkaaril kitabi wassunnah’ me na tara a ciki? Ko daga sunan dai ka ji me na ce, Zikiran Alqur’ani da Sunna ne, to su ne nan. Amma za ka taho tun daga shafi na xaya sai ka zo shafi na 100, ina bayanin kuskuren

da mu kayi na barin zikiran Annabi a baya, shafi xarin nan faxa nake da ‘yan Xariqu, ina faxa masu littattafansu da shafikan, da maganganun Shehunan akan cewa zikiran Annabi nasu ne, me ya sa yau bakwa yi? Ga suna iri-iri, na kira babin Ryadhuttasbihi, in ka gama ka ko Riyadhul Jalal, sannan Hailala, sannan Riyadhul istigfari, ga sunan dai, na yi ta kawo riwayoyin. Na yarda da cewa duk abinda ba Allah ya tsaro shi a sauke ba, a iya kuskure, wannan bai tava girman Shehi na ba, bai tava muqaminsa ba, sai dai kuma ba dai-dai bane in kai shi inda Allah bai kai shi ba, cewa ma’asumi ne ba zai kuskure ba, in ya yi kuskure nema masa gafara kai yi dai-dai, ka tsare girmansa ba tare da raini ba, in dai ta tabbata kuskuren ne, kuma mun tarar ma ba su suka yi kuskuren ba daga baya mabiyansu suka yi.

Ci gaba daga shafi na

27


27 TATTAUNAWA

A Yau Lahadi 1 Ga Afrilu, 2018 (14 Ga Rajab, 1439)

“Qur’ani Da Hadisi Ne Dogarona” Ci gaba daga shafi na

26

Ba’a zikirin nan su sun rubuta na naxi wuraren, kuma da babu da yanzu an yi raddin littafin sun tsani wannan littafin, ka ga dai zikiran Annabi ne, akwai wanda ya ce gwamma Baibul, ‘Bible’ duk da dai Baibul xin ban san wanda yake nufi ba, in na asalin ne haka ne gwamma shi da wannan. Amma in yana nufin wannan da aka sauya, to ka ga yana nufin gwamma tasuniyoyin kirista waxannan zikiran na Manzon Allah, ko da yake a gaskiyar magana ma ko Baibul na asalin ma bai kai wannan ba, domin ayoyin Qur’ani ne masu tsarki, gaba kuma suke da na Annabi Isa (AS), ko dai ya zama gaba da sunan littafin ko ya zama gaba da abinda yake ciki. To ala ayyi halin dai, su ‘yan Shi’a in ka ji sun soke ni, wasunsu wasu suna da adalci, suna cewa wannan bawan Allah mu gode wa Allah da ya zamana mai son gaskiya, ya yi mana yaqi a abubuwa da yawa har ana zaginsa ana ce masa mu muka sa shi ko a cinmu yake. To bai kamata kuma don ya sava da mu a wani wuri kuma mu ce bai isa ya faxi ra’ayinsa ba. Ma su adalcin cikinsu suna faxar haka, cewa “Lallai yana gaskiya, wannan yake nuna mana ba munafunci yake ba, in da munafunci yake yi ai da ko ina sai ya yi ta yabonmu, abinda ya ga bai gamsu ba ya fito ya faxa mana, sai mu duba ra’ayinsa mu gani. In gaskiya ya faxa mu koma kan ra’ayinsa, in ya yi kuskure mu gyara masa”. Akwai masu hankalin cikinsu suna faxar haka, to ka ji yadda abin yake. Akramakallahu a qarshe wane jan hankali za a yiwa ’yan uwa malamai masu wa’azi dangane da aqida? To, Malam Rabiu, Allah Subhanahu wata’alah yana faxa “Inda za ka bi waxanda suka vata da dukkan hujja ba za su bi ka ba.” Wannan maganar sai dai in yi ta kawai don waxanda zuciyarsu take buxe, ba tare da tsatsar hassada a ciki ba. Irin waxanda suke da tsatsar hassada daga Malamai ba a yi masu nasiha, shi ne za ka ga duk Malamin da yake zaune da Allah lafiya, ku kula da abu biyu. Duk abinda zai xora mutane a kai ya tabbata ba son rai bane, saboda addinin nan fa ban aka bane ba kai ke wa ba, in ka ga kana faxa mutane na aikatawa kar kai zaton wani lasisi ne da kai na son rai, akwai ran da za a titsiye ka a tambaye ka hujjoji, ka tuna wannan, ka auna irin abunda duk da za ka iyar wa da jama’a ya zamana tsakaninka da Allah ka yi shi.

•Sheikh Abduljabbar

Yadda Allah ya nuna ko da ya zama kuskure ne, amma ya zama ba gangan kai ba, ka yi iya yinka iya fahimtarka haka ya zama amma ka gazaka yi kuskure. Wannan abu na xaya muhimmi da nake kiran Malamai su dubi Allah su kula da shi, duk abinda za su yi su fifita gaskiya akan son rai. Da yawa Malami zai buxe littafin abokin savani, kafin ya duba da ya xauka zai fara jin ai xauki littafin mutumin banza xan iska, xan wuta vatacce. Don haka ba zai tava yarda ada abinda yake cikin littafin ba. Zai ga gaskiya qiri-qiri an qure shi an fi shi hujja, amma tunda bai yarda gaskiyar ba ce, ya qi karva ya fita waje ya ci gaba da kira kan vatansa. Me ya jawo masa? Ya fifita gaskiya kan son rai. Tun kan ya duba littafin zai xauka ai wannan littafin na maqiyi na ne vatacce, amma fa ba dole gun Allah ya zama haka ba. Amma in ya shiga littafin da kyakkyawar niyya ya tsaya ya nutsu ya duba ta, in ya nutsu ya duba tan nan ya yi wa kansa nasiha ba wai wannan mutumin ya bi ba, gaskiyar ya bi, kuma ba sai ka fito ka nuna wa jama’a ba in kana so ka gyara, amma abinda ya fi kyau ma qarara ka fito ka faxa, kai jarumta ka fito ka faxa, “Abinda na gaya maku jiya ko shekaran jiya ko shekara 20, jama’a dai-dai ilmi

na ne a lokacin, a mam yanzu Alhamdulillah an samu ci gaba, ga irin yadda Allah ya fahimtar da ni gaskiyar magana. Da can ga dalilina, amma yanzu na fahimci wannan dalili ba gaskiya bane, don haka ni kam wannan fahimta da nake da ita a baya na tuba daga ita, kuma ina baku shawara da ku dawo kanta, shi ke nan an wuce, wanda ya dawo ka kuvuta, wanda ya qi dawowa ma ka kuvuta. Ka ga wannan abu na xaya da yake wa Malamai wuya, amma sai ya ce, “An sanni a kai don haka sai dai a mutu a kai.” Sannan Malamai su ji tsoron Allah, su yi duk abinda za su yi don Allah, rashin yi don Allah xin nan Mushkilarsa ba kaxan bace, sai a kawo kafafe iri-iri, son rai ya shiga, shexai ya shiga har sai mutum ya kai kansa wuta, kuma su Malamai sun sani ba wanda ya fi saurin shiga wuta irin Malami in zai bar Allah, domin yanzu zuciya za ta kwashe shi ya zama bawan son rai, yanzu ya zama xan wuta. Saboda haka wannan kiran guda biyu nake yi. Me yake kawowa wannan ya ce ni xai Izala ne, wannan ya ce xai Xariqa ne, nix an Shi’a ne a yi ta gaba? Wallahi mafi yawa iy don kai, son kai, amma yanzu za ka ga cewa abin nan da nake kai iya fahimtata ke nan, ta yiwu dai-dai ne ta yiwu kuskure ne, wancan bawan Alla da yake kan savani nawa ta yiwu ya fini

gaskiya. To in da wanna a rank aba z aka ji kana gaba da shi ba, amma daga inda ka sa a ranka ni ni ne mai gaskiya duk wanda bai bini ba shi ne vatacce, shi ne yake kawo wannan bala’in da ake yi. Imamu Maliku, Imamu Abu Hanifa, sun sava, amma da zamana kowa savani ne yake don Allah in sun haxu girmama juna suke, don haka almajiransu suke girmama su, don haka ba’a ji kansu ba. Imamusshafi’i zamaninsu xaya da Ahamdu bn Hambali, kuma almajirinsa ne, suka sava a mas’aloli da yawa, amma savani ne aka yi don Allah ba don son rai ba, don haka ba su yi fitina ba, wallahi wannan fitinar ma babu abinda yake kawota illa son rai, da Malamai za su daina son rai su koma son gaskiya, da Malamai zasu sa tsoron Allah a ransu su dinga yin abu don shi, to da al’umma kansu ya haxu an daina savani, wannan it ace nasihata ga kaina amatakin farko, sannan a mataki na biyu ga sauran Malamai da dukkanin al’umma, Alhamdulillahi rabbil’aalamin. To Shehi mun gode, Allah ya saka da alkhairi. Ni ma na gode, Allah ya xaukaka ku ya qara maku qwarin qwiwa. Wannan ne qarshen tattaunawar tamu.


28

Sharhin Wasanni A Yau

Lahadi 1 Ga Afrilu, 2018 (14 Ga Rajab, 1439)

Tare da Abba Gwale

Wacce Qasa Ce Za Ta Iya Lashe Gasar Cin Kofin Duniya A Rasha? Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Gasar cin kofin duniya dai tana cigaba da qaratowa bayan da a satin daya gabata qasashe suka buga wasannin sada zumunta duk dai a shirye shiryen da qasashen sukeyi na buga gasar ta cin kofin duniya wanda qasar Rasha zata karvi baqunci. A wasannin sada zumuntar da aka fafata dai manyan qasashe da dama sun gwabza a tsakaninsu misali qasar Jamus ta kece raini da qasar Brazil da sipaniya a wasanni biyun data buga sai itama sipaniya ta fafata da qasar Argentina yayinda Portugal ta buga da qasar Holland. Ingila ma ta fafata wasanni biyu da qasashen Holland da Italiya sai Faransa itama ta fafata da mai masaukin baqi qasar Rasha yayinda anan gida Super Eagles ta Najeriya ta fafata wasa da qasashen Poland da Serbia wasannin da aka fafata duk a qasar ingila. Shirye-shirye suna qara nisa na tunkarar gasar bayan da a jiya hukumar qwallon qafar ta duniya ta fitar da jadawalin sunayen alqalan wasan da zasuyi alqalanci a gasar. Amma waxanne qasashe ne ake tunanin zasu iya lashe gasar ta cin kofin duniya?

zasuja ragamar qasar zuwa Rasha sai kuma yan wasa irinsu Philliph Coutinho da Willian na Chelsea da Gabriel Jesus na Manchester City sai kuma xan wasan tsakiya Casemiro da kuma Marcello xan wasan baya. Duba da tarihi da kuma yadda qasar take buga wasa a a yanzu tabbas qasar Brazil tanada qarfin yin awon gaba da gasar ta cin kofin duniya.

BRAZIL A qwallon qafa idan akace qasar Brazil ansan ana Magana ne akan qasar da ta iya buga qwallo kuma take da shahararrun yan wasa a baya da kuma yanzu waxanda suka iya taka leda yadda yakamata kuma qasar Brazil itace wadda tafi kowacce qasa adadin gasar cin kofin duniya. Brazil ta lashe gasar cin kofin duniya a shekarun 1958 da 1962 da 1970 da 1994 da kuma 2002 jumulla guda biyar kenan a tarihi kuma kowacce shekara idan za’a fara gasar ana sakata acikin qasashen da ake saran zasu iya lashe gasar. A wannan shekarar ma qasar ta shirya tsaf domin lashe gasar bayan data tanadi shahararru kuma qwararrun yan wasan da zasu wakilceta a gasar kuma tuni aka fara bayyana cewa babu qasar da zata iya taka mata burki. Shahararren xan wasan qasar, Neymar, wanda a yanzu haka yake jinya sakamakon rauni dayaji kuma aka yimasa tiyata yana xaya daga cikin yan wasan da ake tunanin

SIPANIYA A shekara ta 2010 ne qasar sipaniya ta lashe gasar cin kofin duniya wanda aka fafata a qasar Africa ta kudu bayan data doke qasar Holland daci 1-0 ta hannun xan wasa Iniesta sai dai kafin wannan nasarar sipaniya bata tava zuwa wasan qarshe ba a gasar. Qasar ta sipaniya tanada manyan yan wasa kuma qwararru manya da yara waxanda zasu taimaka mata wajen lashe gasar cin kofin duniya a Rasha idan akayi la’akari da yadda qasar ta doke qasar Argentina daci 6-1 a wani wasan sada zumunta da qasashen biyu suka fafata a ranar Talatar data gabata. Amma za’a iya cewa qasar ta sipaniya bata da irin yan wasan data lashe gasar cin kofin duniya dasu a baya irinsu Xavi da David Villa da Fernando Torres da Xavi Alonso da kuma Iker Casillas da Carles Puyol da sauransu. Sai dai kawo yanzu ma akwai manyan yan wasa irinsu Pique da Sergio Ramos waxanda duk sun buga

a wancan lokaci da Sergio Basquet da Andries Iniesta, wanda shine ya jefa qwallo xaya tilo a ragar Holland kuma tabasu nasarar lashe gasar. A wannan shekarar ma qasar sipaniya zata shiga sahun manyan qasshen da zasu iya lashe gasar idan akayi la’akari da yawan yan wasan qasar da kuma yadda qungiyoyin qasar, Real Madrid da Barcelona suka mamaye qwallon qafa. JAMUS Jamus ce mai riqe da kambun gasar bayan data doke qasar Argentina a wasan qarshe da suka fafata a qasar Brazil a shekara ta 2014 bayan qwallon da suka jefa guda xaya tilo ta hannun matashin xan wasa Mario Gotze. Tabbas za’a iya cewa har yanzu qasar Jamus tanada qarfin da zata iya komawa da gasar idan akayi la’akari da yan wasan da qasar take dasu yanzu qwararru kuma masu bugawa a manyan qungiyoyin qwallon qafa na duniya. Banda shekarar 2014, Jamus ta lashe gasar a shekarun 1954 da 1974 da kuma 1990 wanda hakan yakenufin tanada gasar sau huxu kenan. Toni Kroos da Mesut Ozil da Muller da da matt Hummels da ilkay Gundogan da Emre Can kusan sune qwararrun yan wasan da suke wakiltar qasar sai dai kuma qasar Jamus tanada abin mamakin fitowa da matasan yan qwallo kuma suzo su

bawa duniya mamaki. A wasan da suka buga da qasar Brazil a kwanannan Jamus tasha kashi daci 1-0 sannan kuma sun buga canjaras da qasar sipaniya kafin wasan wato 1-1 wanda hakan yake nufin qasar Jansu dole sai ta tashi tsaye ta tantance yan wasan da zata xiba ta tafi dasu Rasha. FARANSA Idan akace Faransa a gasar cin kofin duniya kawai ana tuna shekarar 1998 ne shekarar data doke qasar Brazil daci 3-0 a qasar ta Faransa wanda wannan wasa yabawa duniya mamaki idan aka duba yanayin yadda qasar Brazil ta fara gasar tana lashe wasanni. Bayan shekarar 1998, Faransa taje wasan qarshe a shekara ta 2006 inda tai rashin nasara a hannun qasar Italiya a bugun fanareti a wani na ban ammaki kuma wasa na qarshe da babban xan wasan qasar Zidane yayai ritaya kuma aka bashi jan kati a wasan. A daidai wannan lokacin dai kusan za’a iya cewa babu wata qasa a duniya da takai qasar Faransa matasan yan wasan da zasu bawa duniya mamaki idan har qwallon ta karvi yan wasan kuma mai koyar da yan wasan qasar ya xabi yan wasan da suka dace. Paul Pogba da Griezman da Mbappe da Dembele na Barcelona da Antony Martial da Lacazatte da Kante da Varane da Umtiti da Thomas Lemar na Monaco da sauran


29

A Yau Lahadi 1 Ga Afrilu, 2018 (14 Ga Rajab, 1439)

Wacce Qasa Ce Za Ta Iya Lashe Gasar Cin Kofin Duniya A Rasha? matasa kuma mashahuran yan wasa qasar Faransa take dasu. Kuma tabbas idan har qasar zatayi amfani da damarta na tafiya da yan wasan da suka dace zata bawa duniya mamaki kuma dole a saka qasar ta Faransa acikin jerin qasashen da zasu iya lashe gasar a Rasha. Har ila yau qasar Faransa tana iya doke wasu qasashe irinsu Brazil da Jamus da Ingila cikin sauqi wanda hakan yake nufin idan har zasuyi da gaske to babu mai iya taka musu burki a Rasha. ARGENTINA Rashin nasarar da sukayi a hannun qasar sipaniya daci 6-1 a wannan satin shine yaqara nunawa duniya cewa har yanzu akwai sauran aiki a gaban Messi idan har yanason lashe gasar cin kofin duniya domin cike tarihinsa a duniya. Duk da cewa bai samu damar buga wasan ba saboda ciwo da yake dashi amma hakan yana nufin koda ace yaje gasar kuma yaji ciwo ana tsaka da buga gasar qasar bazata iya buga komai ba idan baya cikin fili domin wasan qasar Sipaniya ya nuna haka. Qasar Portugal ta lashe gasar cin kofin nahiyar turai batare da

Cristiano Ronaldo ba bayan dayaji rauni ana cikin wasan kuma hakan bai karya musu gwuiwa ba na ganin tunda babu babban xan wasansu bazasu iya komai ba. Manyan qasashe suna buga wasa babu manyan yan wasansu misali wasannin da Brazil ta buga a kwanannan babu Neymar kuma duk suka samu nasara akan qasar Rasha da kuma Jamus. Tabbas akwai yan wasa irinsu Angel Di Maria da Huguin na Juventus da Dybala shima na Juventus xin da kuma wasu manyan yan wasan qasar irinsu Sergio Aguiro da Marcos Rojo amma tabbas akwai sauran gyara a qasar idan har bazasu iya lashe wasa ba babu Messi, wannan babban qalubale ne ga mai koyar da yan wasan qasar qwallon qafar qasar. Argentina ta lashe gasar cin kofin duniya sau biyu a jere a shekarun 1978 da kuma 1986 wanda xan wasa Diego Maradona yaja ragamar qasar zuwa ga nasara. Sai dai wannan shekarar baza’a iya cewa bazasu iya lashe gasar ba amma tabbas akwai manyan a gabansu kuma basu shirya ba kamar yadda ragowar manyan qasashe suka shirya.

INGILA Idan za a je gasar cin kofin duniya qasar ingila tana xaya daga cikin qasashen da suke fin kowacce qasa shiryawa sai dai haka suke zuwa su dawo babu wani abin arziqi sai dai kawai zasu tafi da yan qwallo da kuma magoya bayan da sukafi na kowacce qasa yawa. Sai dai a wannan karon magoya bayan qasar bazasu je Rasha da yawa ba sakamakon taqaddamar diplomasiyya dake tsakanin qasashen biyu wanda yakawo shakku a yanayin dangantakar manyan qasashen biyu. A shekarar 1966 ne qasar ingila ta lashe gasar cin kofin duniya wanda kuma shine xaya tilo da qasar ta lshe tun fara gasar a shekarar 1930 wanda hakan yake nufin akwai buqatar qasar ta dage domin ganin ta samu nasara a karo na biyu a gasar. Sai dai idan akayi maganar shahararru kuma qwararrun yan wasa bazaka saka qasar ingila ba sai dai akwai matasan yan wasa amma kuma idan anje gasa basa iya buga komai domin ko a gasar cin kofin nahiyar turai da Portugal ta lashe qasar Iceland ce tayi waje da ingila. ’Yan wasa irinsu Harry Kane da Delle Alli da Rashford da Lingard da

Verdy da kuma Jack Wilshere sune ake tunanin zasu wakilci qasar a gasar ta kofin duniya. Sai dai kowacce shekara dai a haka ake qarewa da qorafe qorafe a gasar kuma tuni aka fara saka alamar tambayar akan yan wasan qasar da za’a gayyata domin tafiya a Rasha. PORTUGAL Cristiano Ronaldo kaxai ya isa yasa qasar Portugal ta shiga cikin qasar da zasu iya lashe gasar ta cin kofin duniya duba da yanayin yadda xan wasan yake dagewa da kuma zuciyar xan wasan da kuma yadda yake qarawa yan wasan qasar qwarin gwuiwa. A wasannin da qasar ta buga na sada zumunta a wannan satin portygal tasamu nasara akan qasar Masar daci biyu da xaya ta hannun xan wasa Cristiano Ronaldo sannan kuma tayi rashin nasara daci 3-0 a qasar Holland. Sai dai qasar ta Portugal batada wasu manyan wasan da za’a iya cewa sun shahara a duniya sai dai akwai tsofaffin yan wasa waxanda zasu taimakawa qasar da suka haxa da Nani da Pepe da Quarizma da Jao Mario na Inter Millan da sauran tsofaffin yan wasan qasar.


Wasanni 30

Rossi Ya Shawarci Buffon Da Ya Cigaba Da Buga Wasa Har Sai Qarfinsa Ya Qare

Shahararren xan tseren gudun babur Valentino Rossi xan Italia mai shekaru 39, ya yi alla wadai da masu sukarsa, da kuma mai tsaron gida na tawagar kwallon kafar Italiya Gianluigi Buffon, saboda qin ritaya daga wasanni da suka yi duk da yawan shekarunsu. Rossi wanda ya tava lashe kofin gasar Tseren babur ta duniya, ya mayarwa da masu sukarsu raddi ne bayan da ya rattaba hannu akan sabuwar yarjejeniya ta shekaru 2 da kamfanin Yamaha, da yake wakilta a gasar tseren Babur, wanda zata qare a tsakiyar shekarar 2020. Rossi ya shawarci Buffon wanda a yanzu yake da shekaru 40 ya kwaikwaye shi wajen ci gaba da fafatawa a fagen wasanni har sai inda qarfinsu ya qare. Tun a shekarar 1996 Rossi ya fara tseren babur, kuma a cewarsa har yanzu jin sa yake garau sumul da karsashi tamkar yanzu ya fara. Ya qara da cewa xan wasa yana haqura da wasa ne idan yaji alamu a jikinsa cewa qarfinsa yafara raguwa amma nasa dana Buffon kamar yanzu suke qara samun kuzari.

A Yau

Lahadi 1 Ga Afrilu, 2018 (14 Ga Rajab, 1439)

Tare da Abba Ibrahim Wada Leadership Ayau@yahoo.com

Ko Kun Sa Dalilin Da Ya Sa Babu Xan Birtaniya A Alqalan Gasar Cin Kofin Duniya Na Rasha?

A karon farko cikin shekaru 80, wato tun daga 1938, babu wani alqalin wasa daga Birtaniya da zai halarci busa wasannin gasar cin kofin duniya da za a yi a qasar Rasha a wannan shekarar ta 2018. Wannan tarihi mai xaukar hankali a duniyar wasanni ya tabbata ne bayan da FIFA ta wallafa sunayen alqalan wasa 36 da mataimakansu 63 da ta zava, domin busa a wasannin da za a yi, ba tare da bayyanar sunan ko da alqalin wasa xaya ba daga Ingila, Scotland, Wales da kuma Northern Ireland.

Haka zalika babu xan Birtaniya a cikin mataimakan alqalan wasa 63 da za su yi aiki yayin wasannin na gasar cin kofin duniya, wanda wannan ba qaramin abin dubawa ba ne. A shekarar 2016 dai, Mark Clattenburg shi ne alqalin wasa xaya tilo daga qasar Birtaniya da sunansa ke cikin jerin wanda hukumar FIFA ta tattara, kafin daga bisani ya janye. A halin yanzu dai alqalan wasa da kuma mataimakansu da FIFA ta zavo daga nahiyar Turai sun fito ne daga qasashen

Jamus, Faransa, Rasha, Holland, Poland, Spain, da Italiya, sai kuma Turkiya, Slovenia, da kuma Serbia. Wannan na zuwa yayin da dangantaka ta yi tsami tsakanin Rasha da Birtaniya wadda qawayenta suka mara mata baya, wajen korar jami’an dilflomasiyar Rasha aqalla 150 daga qasashensu, saboda zargin Rasha na da hannu wajen sanyawa tsohon jami’in leqen asirin Birtaniya Sergai Skrippal da ‘yarsa Yulia Guba gidansa da ke Salisbury a Ingila.

Xan Wasan Manchester United Ya Na Son Bugawa Najeriya Wasa Xan wasan qaramar qungiyar Manchester United Tosin Kehinde ya ce a shirye yake ya taka wa tawagar Najeriya wasa idan har qasar zata bashi dama. Kehinde mai shekara 19, wanda yake wasa a qaramar qungiyar Manchester United ‘yan qasa da shekara 23 yana da damar buga wa Najeriya, ko kuma qasar Ingila wasa, amma ya ce shi ya fi son Najeriya. Matashin xan wasan yace a kodayaushe yana tare da Najeriya. An haife shi a can. Duka ‘yan gidansu ‘yan Najeriya. ya fito daga gidan da suke da iko sosai akansa saboda haka idan akace yakoma gida ya buga wasa zai koma. A ranar Lahadin da ta gabata ne xan wasan ya gana da shugabannin

hukumar qwallon qafa ta Najeriya (NFF) don fara bin matakan da za su ba shi damar yi wa Super Eagles xin wasa.

Xan qwallon ya gana ne da jami’an tare da rakiyar iyayensa a birnin Landan bayan da Najeriya ta buga wasannin sada zumunta da qasashen Poland da Serbia. Kehinde ya ce yana so ne ya zama kamar xan wasan Arsenal Alex Iwobi wanda shi ma, a shekarar 2015, ya zavi yi wa Najeriya wasa a maimakon qasar Ingila. An haifi xan wasan ne a birnin Legas amma ya tashi ne a Birtaniya kuma yafara makaranta daga baya kuma yashiga makarantar qwallon qafa ta Manchester United. Ya kuma koma qaramar qungiyar Manchester United ne lokacin da yake da shekara 13, kodayake ya ce a yanzu yana da burin yi wa babbar kungiyar United xin wasa anan gaba.

Van Gaal Maqaryaci Ne Kan Zamansa A United –Paul Scholes Tsohon xan wasan Manchester United Paul Scholes ya bayyana cewa Van Gaal qarya ya ke yi bai so Manchester United ta buga wasa ba kamar yadda Guardiola ya ke bugawa saboda ya siyar da manyan ’yan wasan qungiyar. A ranar Juma’a ne dai Tsohon Kocin Manchester United Louis van Gaal ya ce ya so qungiyar ta yi irin salon wasan da Manchester City ta ke yi yanzu karkashin jagorancin Pep Guardiola. Xan asalin qasar Netherlands xin ya sha suka lokacin da yake jan ragamar United daga waje, saboda salon da ya ke amfani da shi, musamman lokacin da qungiyar ta samu nasara a wasanni huxu kacal cikin 16 da ta buga. Sai dai an sallame shi ne a shekarar 2016, inda Jose Mourinho ya maye

gurbinsa bayan ya jagoranci qungiyar ta lashe kofin qalubale na FA. Ya ce ‘yan wasan Guardiola suna buqatar su samu nasara ne a wasanni biyu kawai gabanin su lashe gasar Firimiyar bana, saboda sun haxa jumullar maki 81 yanzu daga wasanni 30 da suka buga. Van Gaal yace Pep Guardiola mutumin sa ne, don a halin yanzu shi ne kocin da ya fi kowa a gasar Firimiya. Guardiola ya mayar da Manchester City kamar wani inji, Ya qara da cewa Yana irin salon wasan daya so yi a lokacin da yake United. Amma shi ya yi sa’ar samun qwararrun ‘yan wasa. Amma da shine da abin ya xauki dogon lokaci. Kodayake bai samu lokacin ba, Sai dai ya musanta zargin cewa ba sa

jituwa da mutumin da ya maye gurbinsa a United wato Jose Mourinho inda yace Mourinho mutumin sane kuma sun tava aiki tare dashi a Barcelona.

Amma ya soki xaya daga cikin manyan shugabannin kungiyar Ed Woodward wanda ya ce ya saxa alqawarin da ya xaukar masa bayan lashe kofin FA.


WASANNI 31

A Yau Lahadi 1 Ga Afrilu, 2018 (14 Ga Rajab, 1439)

Ina Son Cigaba Da Zama A Real Madrid –Zidane Mai koyar da ’yan wasan qungiyar qwallon qafa ta Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana cewa, ya

na son cigaba da koyar da qungiyar har zuwa kakar wasa ta gaba domin cigaba da samun nasarori.

Qungiyar qwallon qafa ta Real Madrid dai ta na matsayi na uku akan teburin laliga maki 15 tsakaninta da Barcelona wadda take mataki na xaya akan teburin yayinda Atletico Madrid take mataki na biyu akan teburin. A yanzu dai gasar zakarun turai kawai ya ragewa qungiyar ta Real Madrid ta laashe idan kuma bata iya lashe gasar ba to zata kammala kakar bana batare da kofi ko xaya ba bayan da Barcelona tayi mata nisa sannan kuma akayi waje da ita a gasar cin kofin Copa Del Rey. Real Madrid dai zata kai ziyara birnin Turin domin fafata wasan kusa dana kusa dana qarshe da qungiyar qwallon qafa ta Juventus a gasar zakarun turai sai dai zidane yace nasara a gasar zakarun turai ce kawai zata iya sawa yacigaba da aiki a qungiyar. Ya cigaba da cewa tabbas yanason yacigaba da zama a qungiyar, kuma daman tun farko ya bayyana haka kuma bai canja ra’ayinsa ba amma dole sai yacika sharuxan qungiyar wato cin kofin. A qarshe yace shekararsa 18 a qungiyar saboda haka qungiyar ta bashi dama yayi duk abinda yakeso kuma yanayi saboda haka idan aka tambayeshi cewa yanason cigaba da zama a qungiyar zaice Eh, saboda daman shine burinsa.

Ronaldo Mutum Ne Mai Wayo, In Ji Buffon

Mai tsaron ragar qungiyar qwallon qafa ta Juventus, Gianlugi Buffon xan qasar Italiya ya bayyana cewa xan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo xan wasa ne mai wayo kuma ya iya kula da lafiyarsa yadda yakamata duk da girma yafara zuwa. Buffon da Ronaldo dai zasu sake kece raini a ranar Talata a wasan gasar zakarun turai da zasu fafata a wasan kusa dana kusa dana qarshe

a filin wasa na Turin dake qasar ta Italiya. Ronaldo dai bai fara kakar wannan shekarar da kyauba sai daga baya cikin wannan shekarar yafara qoqari inda ya zura qwallaye 37 cikin wasanni 35 daya buga kuma har yanzu kakar wasan bata qareba. Buffon ya ce, Ronaldo ya na da wayo sosai, domin ya na tafiyar da lafiyar jikinsa da wayo da dabara sosai kuma yasan girma yafara

kamashi saboda haka baya gujeguje kamar shekarun baya kuma hakan ba qaramar dabara bace. Ya cigaba da cewa duk da cewa baya gudu kamar da amma kuma cin qwallayensa bai raguba hakan yana nufin ba qaramin wayo gareshi ba kuma yanada tunani mai zurfi sosai. A gasar zakarun turai Ronaldo ya zura qwallaye 12 cikin wasanni 8 daya buga a wannan kakar.

Lashe Kofi A Ingila Abu Ne Mai Matuqar Wahala –Conte

Mai koyar da yan wasan qungiyar qwallon qafa ta Chelsea, Antonio Conte ya bayyana cewa lashe kowacce irin gasa a qasar ingila abune mai matuqar wahalar gaske domin dole sai yan wasa da mai koyarwa da masu qungiya sunyi da gaske. Conte ya bayyana hakane a wata hira da yayi da manema labarai inda yace idan har mai koyarwa yanason ya dinga lashe kofi a duniya to kada yazo ingila domin abune mai wahalar gaske. Mai koyarwar dai ya lashe gasar siriya A da qungiyar Juventus guda uku a jere sannan kuma a shekararsa ta farko a Chelsea ya lashe kofin firimiya sai dai wannan kakar qungiyar tasa bata tunanin lashe kofin na firimiya. Ya cigaba da cewa a qasar ingila kowanne wasa kamar wasan qarshe haka ake bugawa babu qaramin wasa babu babba kuma kowacce qungiya zata iya doke babbar qungiyar saboda haka babu gwani a gasar. Sai dai ya ce, kowacce qungiya da mai koyarwar qungiyar da yan wasa suna iya qoqarinsu don ganin sun lashe kowacce irin gas ace saboda haka kawai sai abinda qungiya tagani idan kakar wasa ta qare. Chelsea dai anyi waje da ita a gasar zakarun turai sannan kuma tana mataki na 5 da maki 56 amma kuma takai wasan kusa dana qarshe na gasar cin kofin qalubale na FA inda zata kece raini da qungiyar Southampton a qarshen wannan watan.


01.04.18

AyAU LAHADI LEADERSHIP Don Allah Da Kishin Qasa

www.leadershipayau.com Leadership A Yau

01 Ga Maris, 2018 (14 Ga Rajab, 1439)

WASANNI

Wacce Qasa Ce Za Ta Iya Lashe Gasar Cin Kofin Duniya A Rasha? > Shafi na 28

JARIDAR HAUSA MAI FITOWA KULLUM TA FARKO A NIJERIYA

LeadershipAyau

No: 029

N150

Mahanga tare da

Barace-baracen Qananan Yara A Titinan Qasar Nan: Ina Mafita?

Musa Muhammad 08148507210 mahawayi2013@gmail.com Akwai abubuwa da dama, waxanda idan mutum ya yi dubi zuwa garesu za su dagula masa rayuwa ya ma rasa abin da ke masa daxi, musamman idan aka yi dubi da yadda wasu abubuwan ke jawo wa ga rayuwar al’ummar da abin ya shafa. Wasu daga cikin waxannan abubuwa, waxanda kuma zan iya cewa babu wani mai farin ciki da shi, shi ne yadda ake samun qananan yara masu qananan shekaru suna bara a kan tituna, musamman a wasu manyan garuruwan qasar nan. Irin waxanan yara, wasu lokuta ma za ka tarar da cewa qanana ne matuqa, ta yadda in da suna gidan iyayensu ne, hatta wanki ko wanka mai sai an yi masu, wasu ma ba su wuce kwana da iyayensu mata a gado xaya ba. To amma sai ya zama an raba su da iyayen nasu an jefa su bariki, wa zai yi masu wanka, wa zai yi masu wanki da sauran hidindimu? A irin wannan ne wata rana yi kicivis da wasu yara maqale da xan kwanonsu wai suna bara. Waxannan yara, yara ne qanana, waxanda idan da kai ne mahaifinsu, ko ke ce mahaifiyarsu, ba za ku iya sa su kowane irin aiki ba. Kuma kamata ya yi a ce suna zaune tare da iyayeynsu suna zuwa makarantar Islamiyya da ta boko. Idan aka rinqa kwasar irin waxannan yara ana turasu wasu garuruwa da sunan wai karatun allo, to wane irin karatu ne waxannan yara za su yi, waxanda hatta abincin kirki ba ishesu ba? Ya ake son su yi rayuwarsu, ya ake ganin tasowarsu za ta kasance? Idan duk aka je aka dawo za a taras da cewa waxannan matsaloli ne da suka dabaibaye qasar Hausa, abin takaici! Kuma yawanci ana fakewa ne da addini, sai a ce wai yaro zai tafi neman ilimin addini, alhali ga yara nan suna haddace Alqur’ani mai girma a gaban iyayensu, suna zuwa makaranta su dawo gidajensu ana lura da lafiya da tarbiyyarsu. Shi kuwa wancan an tura shi wani gari an haxa shi da wasu, ba uwa ba uba, Malaminsu, wanda shi kuma yaran sun yi masa yawa, wasu lokuta ma yaran kan faxa cikin wani mawiyacin hali, ko ya kwashi wasu miyagun halaye, shi Malamin bai ma sani ba. A matsayina na xan jrida na sha haxuwa da irin waxannan matsaloli

da dama, na sha samun labarai masu baqanta rai game da irin halayen da waxannan yara kan shiga, wanda wasu labaran ma ba a iya yaxasu saboda takaicin da ke ciki. Domin akwai wani lokaci da ake samun yanayin da ake kama irin waxannan yara da aikata luwaxi. Saboda haka ne nake ganin wannan aiki ne da ya rataya a wiyan kowa, musamman iyaye, gwamnati da shugabannin al’umma. Domin ita tarbiyya ta kowa da kowa ce, idan ta gyaru, to al’umma ce za ta ji daxi, idan kuma ta lalace, to al’umma ce za ta kwashi kashinta a hannu. Ina so a yi mani kyakkyawar fahimta a nan, ba wai ina so ne in hana masu ra’ayin tattara yara don koya masu karatun allo ba, abin da nake nufi a nan shi ne, a samu yaran da suka san inda ke masu ciwo mana, waxanda za su iya yi wa kansu hidindimu, waxanda za su iya

bambance damansu da hagunsu. A kwanakin baya na xan rubuta irin wannan abu na liqa a shafina na facebook, domin abin ya dameni. To irin yadda na ga jama’a na mayar da martani, sai na gane ashe dai abin yana damun kowa. Ga abin da na rubuta da kuma wasu daga tsokacin da aka yi: Abin da na rubuta Lallai akwai hisabi! Dubi waxannan yaran, waxanda ba su wuce kwana da iyayensu mata a gado xaya ba, amma an tura su wani gari na nesa, su ke fita su nema wa kansu abinci. Anya babu matsala a nan Duniya da gobe qiyama, musamman ga iyayensu? Wasu daga cikin martanin da aka yi. HASAN GARKO Mutane suna Xaukar wa kansu nauyi, kuma sai su kasa saukewa. Iin ka bincika uban su ba matarsa

xaya ba. MUHAMMAD IBRAHIM Malam, yau xin nan waxannan yaran sun shigo NUJ suna ’yan tsince-tsince har suka zo shan ruwa a masallaci, ina kallansu. Akwai dai matsala a Arewa. Allah ya ganar da mu. HAJIYA RABI SALISU Allah ya kyauta. Ina da guda biyar a cibiyata ta kula da marayu ‘orphanage’ yanzu haka. Imanin Malam Bahaushe na da buqatar gyara don ya yi daidai da addinin musulunci da hankali !!! ABDULRAZAQ YAHUZA Gaskiya kam, Malam... Abin sai dai addu’a kawai!!! Amma akwai rashin imani a ciki. AWWAL BAUCHI Tabbas akwai matsala. ALHAJI UMARU DIKKO Jahilce ne ke kawo shi. NASIRU YAKUBU Matsala fa ai sai dai Allah ya yauta RABI’U INDABAWA Allahu Akbar, Allah ya kyauta JIBRIL SHUAIBU Haqqun SANI HASAN Bahaushe mai ban-haushi. Zan rufe wannan rubutu nawa na wannan makon da yin kira ga Hukumomin da abin ya shafa su dubi wannan lamari, don a san gyaran da za a yi don gyaran al’umma. Su kuma iyaye su sani ’ya’yan da Allah ya ba su, ya ba su ne amana, don haka zai tambayesu amanar da ya ba su.

Babba Da Jaka ’ Yan Boko Haram Ba Su Zalunce Mu Ba

-’Yan Matan Dapchi

Ina Leah Sharibu?

Ana shiryawa da buga LEADERSHIP A Yau a kamfanin LEADERSHIP GROUP LIMITED, lamba 27, kan Titin Ibrahim Tahir, a Gundumar Utako, Abuja. Tarho: 09-2345055; Fax: 09-2345360. P. O. Box 9514, Garki II, Abuja. Ofishin mu a Legas: 34/36 Titin Adegbola, Anifowose, daidai Oba Akran, Ikeja. Tarho: 01-8963459. Shafinmu: leadershipayau.ng, E-mel: leadershipayaulahadi@yahoo.com ko Edita: +2348032875238


Turn static files into dynamic content formats.

Create a flipbook
Issuu converts static files into: digital portfolios, online yearbooks, online catalogs, digital photo albums and more. Sign up and create your flipbook.