Page 1

AyAU ASABAR LEADERSHIP Don Allah Da Kishin Qasa

14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

JARIDAR HAUSA TA FARKO MAI FITOWA KULLUM A NIJERIYA

www.leadershipayau.com

Leadership A Yau

14.04.18

LeadershipAyau

No: 031

N150

Sojoji Za Su Ba Gwamnati Gudummawar Tabbatar Dimokuraxiyya —Buratai Daga Sabo Ahmad, Abuja

A ranar Alhamis ce, Kwamandan sojojin qasa, Laftana Janar Tukur Buratai, ya qara bai wa Shugaba qasa Muhammadu Buhari, tabbacin miqa wuya da biyayyar rundunar Soji a gare shi, da kuma tsayin dakan rundunar za ta ci gaba da yi wajen kare mulkin Dimokuraxiyya a qasar nan.

Buratai, ya qara bayar da tabbacin ne a qarshen taron Kwamandan Soji na qasa, na zangon farkon shekara ta 2018, da aka yi a Abuja. Buratai, wanda Manjo Janar Rasheed Yusuf, ya wakilce shi, ya kuma bayar da tabbacin rundunar Sojin za ta haxa kai da sauran sassan Jami’an tsaro domin ganin ci gaba da kuma bunqasan tattalin arzikin

qasar nan. Ya kuma alqawarta cewa, Sojoji za su ci gaba da kasancewa masu nu na qwarewa wajen gudanar da ayyukansu da tsarin mulki ya xora masu. Ya kuma bayar da tabbacin rundunar Sojin za ta yi duk mai yiwuwa wajen fuskantar qalubalen tsaron da ke fuskantar qasar nan. > Ci gaba a Shafi na 5

Kisa A Zamfara:

Masarautar Anka Ta Buqaci q Yin Azumin Kwana Uku 5

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kaduna Mista Austing Iwar; a tsakiya tare da wasu shugabannin al’ummar Ibo da ke Kaduna jim kaxan bayan kammala mitin tsakanin al’umma da jami’an tsaro a unguwa Narayi, Barnawa Kaduna jiya Juma’a. Photo: NAN

Xalibai 800 Da Gwamnatin Kano Ta Tallafa Aikin Hanya: Gwamnatin Tarayya Wa Sun Gama Karatunsu A Waje Shafi na 4 Za Ta Kashe Naira Biliyan 47Shafi na 7


2 RAHOTO

A Yau Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

Za A Fara Tura Masu Yi Wa Kasa Hidima Aikin Gona – Hukumar NYSC Daga Sabo Ahmad, Abuja

Baban Jamin Hukumar kula da masu yi wa qasa hidima NYSC, Bello Ballama ya bayyana cewa, Hukumar za ta xaukin ayyukkan noma su zama suna cikin aikace-aikacen da xalibai masu yi wa qasa hidima za su rika yi, lokacin da aka tura su domin yi wa qasa hidima Domin kuwa kamar yadda ya ce, yin haka zai taimaka wajen kawar da matsalar da ake samu na qin xaukar xalibai dea wasu ma’aikatu ke yi. Za a fara yin haka ne daga kan waxanda za su shiga sansanin horo na Hukumar wato Batch ‘A’ Stream I a ranar 19 ga watan Afrilu.” Daga bnan sai ya ci gaba da cewa, hukumar

PDM Na Nan Daram A Jihar Katsina

Daga Sabo Ahmad, Abuja

*Xalibai masu yi wa qasa hidima

ta keve filayen noma a duk faxin qasar nan domin xalibai masu yi wa qasa hidima. Daga karshe Ballama

Mama muna damuwa da rashin qoqarin yaronki a makaranta. Saboda ba mu san halin da zai shiga nan gaba a rayuwa ba.

yace hukumar na iya kokarin ta wajen kawar da duk matsalolin da masu yi wa kasa kan yi fama da su.

Wadannan matsaloli sun hada da samun wurin yi wa kasa hidima, rashin samun wurin zama da sauran su.

Ka da ka damu. Babu matsala zai shiga siyasa inda abokansa suke.

Shugaban jam’iyya PDM na jihar katsina Alhaji Qagimu Xanja ya bayyana cewa jam’iyyar PDM na nan daram tare da magoya bayanta a dukkan faxin jihar Katsina, Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da suke zan tawa da wakilinmu a gidansa da ke garin Xanja. Shugaban ya ce an daxe ana tayin kuruwar ibilis cewa, wai ‘yan jam’iyyar ta PDM za su narke su koma PDP, ya ce wannan labarin qanzon kurege ne. Ba bu qamshin gaskiya a cikinsa, saboda haka ya, abin da shugaban ya ce ya sani shi ne sauran jam’iyyu na ta kawo musu caffa amma dai su suna nan a kan bakansu na cewa ba za su sauya sheka zuwa wata jam’iyya ba.

Ofishin Hedimasta


A Yau Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

Leadership Hausa

ra’ayinmu

K

@leadershipHausa

3

Mu Hadu Mu Taimaka Wa Qasarmu Ta Ci Gaba

owannen mu na da irin gudummawar da zai bayar ta hanyar yin abin da ya dace tun daga shi kansa, sai kuma sauran mutanen da suke qarqashinsa, a ce ana yin haka wato duk hakkokin da ya kamata ya yi ya kasance yana yi, ai tuni da an yi nisa da kuma samun gaggarumin ci gaban da kowa zai yi sha’awa da kuma alfahari da shi. Wannan ma na magidanci xaya ne don haka idan abin ya kasance a na yin duk abubuwan da suka dace sai unguwa ta inganta, in ya kasance haka ashe ke nan da babu wasu matsalolin da ake fuskanta da suka yi kama da na yanzu. Kamar jinka idan ana buqatar a xora bisa tafarfara, ai mutane ke tashi su kama har a samu xora ita jinkar. Hakanan shi ma cigaba bai samuwa sai kowa ya bada haxin kai da kuma gudunmawa, ba wai ya tsaya daga wani wuri ba, ya riqa cewar masu qoqarin yin wani abin da zai kawo ci gaba ba su iya ba, shi kuma xin da yake ganin ya iya, bai da wata katavus. Maganar tafiyar da Nijeriya da kuma wasu abubuwan da zasu kawo ci gabanta hakkin kowa ne, ba wai sai wani ya tsaya yana hangen na wani ba, bayan shi kuma bai na shin ba, wanda abin da ya kamata ke nan. Kowa yana da abin da ya dace amma sai yaqi yana hangen na wani can , yana cewa ai bai dace ba, saboda dama ai laifi ance tudu ne taka naka ka hango na wani. Idan kowa yana yin abin da ya dace da shi tun daga ciki har waje ai da tuni zuwa yanzu halin da muke ciki ba wanda zai ji haushin wani dangane da wani abu can daban. Ita qasar Nijeriya duk ta qunshi dukkan abubuwan da mutum yake tsammani, a matsayinta na uwa da uba wadda ta haifi manyan ‘ya’ya har ma da jikoki, waxanda za a ce a shekarunta da suka kusa kai hamsin da takwas kamata ya yi, yanzu sai dai ta zauna, a riqa yi mata abubuwa. Maimakon haka sai aka samu rarrabuwar kai tsakanin ‘ya’yanta, aka koma ana yin zaman ‘yan marina wato kowa da inda yasa gabansa, duk wannan ma ba wani abu bane idan dai har daga qarshe za a tuna

cewar da akwai fa abubuwan da suka kamata ayi. Ba wani cigaban da za a samu musamman idan rarrabuwar kai ta yi qamari, ya zama ruwan dare gama duniya. Duk ba ayin hakan musamman ma idan aka yi la’akari da yadda ita Nijeriya ta kasance cikin nan

xumi can zafi, wani wurin kuma wuta c e ke ci bal- bal, wannan sai mutum ya tuna da yadda ake shekarun baya da suka wuce. Qara samun rarrabuwar kan da ake samu ku san wannan ana iya cewar duk rana ce, wanda hakan ya sa ba a faxawa wa juna

EDITA Sabo Ahmad Kafin-Maiyaki

MATAIMAKIN SHUGABA (NA MUSAMMAN) Christian Ochiama DARAKTAN SASHE Mubarak Umar

RUKUNIN KAMFANONIN LEADERSHIP SHUGABA Sam Nda-Isaiah

BABBAN MANAJAN DARAKTA Abdul Gombe BABBAN MANAJAN DARAKTAN KADARORI David Chinda MANYAN DARAKTOCIN KAMFANI Dele Fanimo Felicia Ogbonlaiye DARAKTAN KULA DA MA’AIKATA Solomon Nda-Isaiah DARAKTAN KULA DA KADARORIN KAMFANI Zipporah D. Tanko MANYAN MANAJOJI Ibrahim Halilu Femi Adekunle Ebriku John

manufarmu

LEADERSHIP A Yau jarida ce da ake bugawa a Abuja. Ta yi tsayuwar daka wajen tabbatar da shugabanci da wakilci nagari. Jaridar za ta ci gaba da kare muradun al’umma, ba kare ra’ayi da muradun mahukuntanta kaxai ba. Da waxannan qudirorin ne muke fatan jama’a za su xora mu kan Mizani. Haka kuma duk ra’ayoyin masu karatu da muke bugawa, ba manufar kamfanin LEADERSHIP ba ne, ra’ayin masu karatun ne. Sai dai, ba za mu tava mantawa da dalilin wanzuwarmu a doron qasa ba, wato: Don Allah Da Kishin Qasa!

gaskiya, bare ma har akai ga ma yin tunanin ya fa kamata a yi abubuwan da zasu kawo cigaba na ko ina ne ma ake tun daga unguwa har akai zuwa babban birnin tarayya. Ci gaba ai zai yi wuya da kuma nisa da al’umma muddin dai har ya zuwa wannan lokaci da ake ciki, akwai miji mai cutar matarsa, haka ita ma matar da akwai mai yiwa mijinta hakan. Xa yana zaluntar mahaifinsa, shi ma mahaifin sai ya kasance wani yana yin haka. Mahukunta su riqa cutar talakawa, suma idan sun samu damar ba bari zasu yi ba, shugaba ya riqa cutar na qasa da shi, hakanan suma idan sun samu damar sai sun yi sama da shi daganan su sako shi qasa su taka. ‘Yan kwangila wasu suna yin kashe mu raba da waxanda suka basu ita kwangilar, ana aikata ayyukan ashsha muraran a fili babu ko tsoron Allah, wani lokaci ma har wanda ya aikata abin zai fito yana bayyanawa mutane ai shi ne ya aikata abu kaza da kaza. Babu ko kunya babu tsoron Allah. Ta yaya za a cigaba bayan akwai wuraren da ake ba Fasiqai muhimmanci, mummunai su kasance ba a ganin mutuncinsu. Wasu ‘ya’ya yanzu su suke neman maye gurbin Iyaye, su Iyayen wasu kuma yanzu sune suka koma makwafin ‘ya’ya. Kamar yadda aka fara shimfixa tabarma da cewar shi cigaba kowa yana da gudunmawar da zai bada, wannan abu haka yake, sai kowa ya san matsayinsa da kuma duk wasu abubuwan da suka kamata ya yi. Amma ba yadda ake kara zube ba sai an canza alqibla, bayan nan a tuba kuma tubar ta kasance ba irin ta mazuru ba, ana iya yin sa’a ta hakan saboda ko da ace shi cigaba yana tafiya da kan shi domin zuwa wuraren da ya dace, to akwai fa wurare masu yawa da ba zai ko mafarkin zuwa ba. Gaskiyar al’amari an yi nisa da cigaba saboda kuwa duk ya gane ashe, bamu ma son junanmu, qwarai kuwa domin an yi nisa da gida qwarai da gaske. Bugu da qari kuma ga rarrabuwar kai wadda ke faruwa tsakanin ko wane jinsi, don an yi nisa da irin tafarkin so da qaunar juna wanda aka gina mu da shi.


4 LABARAI

A Yau

Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

Xalibai 800 Da Gwamnatin Kano Ta Tallafa Wa Sun Gama Karatunsu A Waje Daga Sabo Ahmad, Abuja

Gwamnatin jihar Kano qarqashin jagoranciin Dakta abdullahi Umar ganduje ta bayyana cewa, sama da xalibai 800 ne da ta xauki xawainiyarsu suka samu nasara gama karatunsu a fannin ilimi daban-daban suka samu nasarar kamala karatun nasu a makarantun da ke qasar waje daga watan Yuni na shekara ta 2015 zuwa wannan lokaci. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin sakatare mai kula da harkokin yaxa labaran gwamna jihar Malam Abba Anwar. Bayanin nya ci gaba da cewa, sakatariyar Hukumar bayar da tallafin qaro karatun ta jihar Farfesa Fatima Umar ita ta bayyana haka a wurin bikin miqa tallafin karatun

digiri na uku a jami’ar Near East University, wanda ya gudana a xakin taro na Africa House,da ke fadar gwamnatin jihar. Farfesa Fatima ta ce wasu xaliban da suka gama karatun nasu har sun samu. Haka kuma ta ci gaba da cewa, akwi yarjejeniyar da suka qulla da qasar Cyprus wadda tab a su damar tura xalibai domin yin karatu a can. Ta ce yanzu haka akwai xalibai guda goma sha tara wasu na karatun babban digiri wasu kuma na karatun digiri na farko. Ta ci gaba da cewa kwanan nan wasu xaliban xalibai guda goma da aka zava daga manyan makarantun qasar nan ciki har da jami’ar bayero za su tafi qasar ta Cyprus domin karo ilimi.

• Gwamna Ganduje

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Amince Da Biyan Masu Unguwanni Daga Idris Aliyu Daudawa

Gwamnatin jihar Kaduna ta amince da biyan albashi ga masu unguwanni 17,139, a cikin masarautu 34 da take da su na jihar, an yi hakan ne saboda su riqa ba da ta su gudummawar wajen allurar riga-kafi musamman wadda za ta taimaka wajen maganin kamuwa da munanan cututtuka. Kodayake ita jihar jihar Kaduna ba ta samu vullar wani al’amarin da ya shafi Polio tun shekarar 2012 lokacin da aka ba da sanarwa mai nuna cewar jihar ba tada wani al’amarin da ya shafi Polio ba. Da yake jawabi ga manema labarai kwamishinan qananan Hukumomi na jihar, Farfesa Kabir Mato, kwamishinan lafiya da jin daxin jama’a Dokta Paul Dogo, shugabar Hukumar lafiya matakin farko ta jihar Kaduna Dokta Hadiza Balarabe, sun yi bayani a kan irin gudummawar da masu unguwanni suke badawa, wajen allurer rigakafi wadda akan yi lokaci zuwa lokaci, wanda yin hakan ne ya sa aka bada sanarwa jihar ta yi bankwana da

cutar Polio. Mato ya bayyana cewar gwamnatin jihar za ta kasance Naira milyan 170 ko wane wata, saboda biyan ko wane mai unguwa albashin Naira dubu goma ko wane wata , a matsayin albashi. Matsayin wani taimako domino ana jin daxain gudummawar da suke badawa, musamman lokacin ake yin allurar Polio. Mato ya bayyana cewar lokacin mulkin gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El Rufa’i, ya daxe yana amfani da kuqin jihar, da kuma taimako daga abokan harkar jihar masu ta kasance da ci gaba saboda maganin mutuwar mata masu juna biyu lokacin haihwa, da kuma qananan yara. Da kuma taimakawa wajen bunqasa asibitoci wauraren da ake kula da lafiyar al’umma, tun shekarar 2015 an xauki matakai na xaukar muhimmanci alluran rigakafi bada wasa ba, wajen da an tabbatar da je ko wane saqo da kuma lungu na jihar, saboda aba yara abubuwan da suke so, domin kauce ma har sai an kai yin allurar rigakafi kamuwa da munanan cututtuka.

Kamar yadda kowa ya sani an sha yin su waxannan alluran rigakafin, ana kuma ci gaba da yin sa saboda a kare qananan yara daga kamuwa daga cututtuka, gwamnan jihar Kaduna ya nuna yadda ya kamata a riqa yi saboda ya kawo ‘ya’yan shi wajen allurar, wannan kuma ba domin komai ba sai saboda a jawo hankalin wasu iyaye suma , su yarda a yi ma ‘ya’yan nasu allurar riga-kafin. Bugu da qari ita gwamnatin da kuma masu taimaka mata, ta xauki matakan da duk suka kamata a xauka, na tabbatar da na ci gaba da yin alluran riga-kafin, wannan ya nuna ke nan dukkan kayayyakin da ake buqata dangane da allurar rigakafi, ana daxe da tanadarsu ko da kuwa shekara xaya zasu yi. Nasarorin da ka samu dangane da alluran rigakafin abin ya samo asali ne, a kan irin gudummawar da masu unguwanni suke badawa, saboda sune suka fi kowa sanin waxanda suke zaune dasu, da suka haxa da su yaran da kuma sauran waxanda ake buqata domin cim ma •Gwamna el-Rufai burin.


Babban Labari A Yau ASABAR 14.04.2018

5

Kisa A Zamfara:

Masarautar Anka Ta Buqaci Yin Azumin Kwana Uku Daga Sabo Ahmad, Abuja

Masarautar Anka da ke jihar Zamfara ta ayyana zaman makoki na kwana uku tare da yin azumi a cikin waxannan ranaku bisa neman sauqi kan bala’in kashe-kashen da ya zama ruwan-dare a jihar. Ranar Larabar da ta gabata ne dai gungun mahara suka kai farmaki qauyen KuruKuru da Jarkuka in da suka kashe mutun 26 suka kuma jiwa wasu da dama rauni. Wannan ya faru nne mako biyu ‘yan bindigar suka kashe mutum talatin a BawarDaji. Wazirin Anka, Alhaji Muhammad Inuwa, ne ya bayyana haka ga manema labarai a jiya juma’a, ya ce shawarar yin azumin ta biyo bayan tattaunawar da majalisar masarautar ta yi ne da wasu dattawa da ke marautar ta Ankan “Mun yi zaune-zaune da dukkahn ‘masu faxa a ji na masarautar Anka, dukkanmu muin

amince da cewa, mu yi zaman makoki na kwana uku. “Saboda haka muke rpqan daukkan al’ummar wannan masarauta da da mu yi azumi na kwana uku, da niyyar allah ya kawo mana gudummawar kawar mana da wannan bala’i da muka samu kanmu a ciki. “Wanann matsala na ci mana tuwo a qwarya, kuma mun lura cea akwai sakacin jami’an tsaro wajen faruwar wannan lamari”,in ji shi. Sannan ya ci gaba da cewa, ko da ma jami’an tsaron na son su yi aiki kamar yadda ya lkamata ba su da wadattatun kayan aikin da za su iya fuskantar waxannan ‘yan bindiga, saboda sun mallaki makamai na zamani “Kamar yadda kowa ya sani an kai hari ranar 26, Maris, 2018, qauyen Bawar-Daji inda aka kashe mutane 47, an kuma ji wa wasu da dama rauni. “Mako biyu bayan wanna hari, wato ranar 4, Afirilu, 2018,an sake kai irin wannan

harin a Kuru-Kuru inda nan ma aka kashe mutumr 26. “Saboda haka muke roqon

al’umma da su bayar da haxin kai wajen tabbatar da am samu tsaro a wannan jiha, baki xaya,

don haka da zarar sub ga wani abu dda ba su gane su gaggauta kai rahoto in da ya kamata.

•Ka’aba

Sojoji Za Su Ba Gwamnati Gudummawar Tabbatar Dimokuraxiyya —Buratai Ci gaba daga shafin farko “Ina kuma son na qara tabbatar maku cewa, rundunar Sojin Nijeriya za ta ci gaba da mutunta haqqin xan’adam, a lokacin da muke fafatawa da matsalolin tsaron da ke addaban qasar nan,” in ji shi. Ya ce, taron ya sake duba yadda ayyukan rudunonin tsaron nan na musamman, `Operation Lafiya Dole’ da `Ayem Akpatuma,’ ke gudana. “Mun gano dukkanin matsalolin mun kuma xauki darussan gudanar da ayyukan namu, da ma sauran wasu ayyukan duka. “A sa’ilin da muka tattauna kan wasu daga cikin waxannan matsalolin a wajen wannan taron, ina ba ku tabbacin duk matsalolin

da ke da buqatar mu samar masu da dabaru na musamman, za mu tabbata da mun yi hakanan xin. Ya yi nu ni da cewa, shiryeshirye ukun da ya qaddamar a wajen taron sun qunshi ainihin yadda za a bayar da horo ne, da kuma batun shugabanci a rundunar ta Soji da kuma kayan aikin ta. Xaya daga cikin shirye-shiryen ya qunshi tsari ne na yadda za a gudanar da shirye-shirye domin kyautata hanyoyin bin dokokin gida da na waje wajen gudanar da ayyukan namu. Sauran su ne; bayar da umurni a kan dokokin yaqi, da kuma dokokin da suka shafi yin amfani da qarfi da kuma tsarin yadda ake yin kamu, tsarewa da kuma bincike.

•Janar Buratai


6

RAHOTO

A Yau Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

Noman Abinci Ne Mafita A Nijeriya Daga Bala Kukuru

Alhaji Sunusi Tura sarkin noman qasar Galadiman Katsina hakimin Malumfashi ta jihar Katsina ya bayyana cewar yin cewa,noman abinci shi ne mafita a Nijeriya musamman idan aka yi la’akari da wasu qasashen duniya da ke fama da rashin abinci kuma qasarsu ba ta yin noman abinci za ka ga harkokin rayuwarsu na yau da kullum ba su ci gaba ba kamar yadda sauran qasashen da ke da abinci ke ci gaba Sarkin noma ya yi wannan kalami ne a lokacin da waxansu qananan manoma suka zomasa gaisuwar ban girma a gidansa da ke Tura ta qaramar hukumar Malumfashi da ke jihar Katsina. Sarkin ya bayaninsa na maraba game da wannan ziyara ta manoman ya yi kira ga manoman jihar Katsina da sauran jahohin Nijeriya wajen samar da yanayi mai kyau ta tsakanin manoma da Fulani makiyaya domin qarin samun zaman lafiya a tsakaninsu. Sannan ya nuna farin cikinsa ga xaya daga cikin iyayen qasar jihar Galadiman

Katsina hakimin Malumfashi da wannan jajircewar samar da kyakkyawan yanayi na zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya a duk faxin jihar Katsina Sannan kuma ya ci gaba

da bayanin kyakkyawan halin uban qasar Galadiman bisa kyakkyawan shugabanci da yake gudanarwa. Sarkin ya qara da cewa ana iya cewa shi kaxai ne dattijon da ya rage a Arewacin Nijeriya kuma ya

shiga wani yanayi na yawan shekaru amma har yanzu bai yi qasa a gwiwa ba wajen gudanar da shimfixa kyawawan ayyuka ga talakawan kasar nan, a cewarsa a kan haka ne yake godiya da fatan alheri

ga uban qasar. Sannan ya ci gaba da yi wa shugaban qasar Nijeriya Muhammadu Buhari da gwamnatocin qasar nan a qoqarinsu da quduri na samar da zaman lafiya da tsaro a duk faxin qasar nan.

Kwamishinan Raya Karkara Na Kano Ya Samu Yabo Daga Ibrahim Muhammad, Kano

An bayyana Kwamishinan ma’aikatar raya karkara na jhar Kano, Dokta Musa Iliyasu Kwankwaso da cewa mutum ne da ya riqe amanar da Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya xora masa wajen inganata ci gaban al’ummar jihar, musamman ta gudanar da ayyuka a dukkan sassa jihar. Wani xan siyasa a Kano, Alhaji Dini Falalu Fagge ne ya yi wannan yabon a wata zantawa da ya yi da wakilinmu. Inda ya bayyanace cewa zuwan Musa Iliyasu Kwankwaso a matsayin Kwamishinan raya karkara an kusa kammala dukkan ayyuka da ya zo ya samu ba a kai ga yin kashi 32 cikin 100 ba. Ya ce a yanzu an kai ga yin kashi 93 saura qarashe ya rage kawai. Ya qara da bayyana cewa irin ayyukan da ake yi a qarqashin ma’aikatar da suka haxa da na lunguna da Gwamnatin Ganduje ta bijiro da su, ana ta gyaran hanyoyi da sanya fitilu a lunguna, sannan akwai taransifomomi da aka samar da su a wurare da yawa. Dili Falalu ya ce yanzu haka akwai shirin da ake yi na samar da tiransifomomin

wutar lantarki guda 50 wanda tun a cikin shekarar 2016 aka yarje a saye su, amma sai zuwan Kwamishinan ya jajirce, yanzu an kusa saye a raba a birane da karkara dan inganta wutar lantarki. Dini ya yi nuni da cewa yanzu a Kano ba a maganar Kwankwasiyya sai dai

Gandujiyya, sakamakon irin ayyukanda ake gudanarwa da yake tava jama’a. Dan haka ya ce yanzu babu maganar tasirin Kwankwasiyya a Kano, mutane sun fahimta Ganduje da Buhari kawai ake. Daga nan sai ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar PDP a Kano

su yi maza su haxo kayansu su biyo tawagar Musa Iliyasu Kwankwaso zuwa APC. Ya qara dayin albishir ga al’ummar jihar Kano cewa nan gaba kaxan za su kwashi romon dimokaraxiyya ta tallafin da za a raba ga matasa maza da mata da magidanta domin su dogara da kai.

Sannan sai ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da qasa baki xaya kan su ci gaba da bai wa Gwamna Ganduje da Buhari goyon baya, su kuma sake zavarsu a shekara ta 2019 don ci gaba da kyautata tsaro da inganta ci gaban rayuwar al’umma jihar Kano da na qasa gaba xaya.

NDE Na Horor Da Marasa Sana’ao’i A Bauchi Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

A ranar Alhamis ne Hukumar samar da ayyukan yi ta qasa, wato (NDE) ta fara bayar da horo kan sana’o’in hanu wa mutane dubu xaya da basu da aikin yi a jihar Bauchi. Shirin dai gwamnatin tarayya ta kawo sa ne domin rage yawaitar jama’a marasa aiyukan yi a tsakanin jama’a domin samar musu da hanyoyin dogaro da kawukansu. Da yake jawabinsa a wajen buxe shirin bayar da horon a qaramar hukumar Darazo, babban jami’in hukumar ta NDE a jihar Bauchi, Mista Lawan Ali ya bayyana cewar horon haxin guiwa ne a tsakanin hukumarsu da babban mai tallafa wa shugaban qasa

Muhammadu Buhari kan aiyuka na musamman Alhaji Shehu Darazo. Ya bayyana cewar shirin an kawo sa ne domin a rage qarfin rashin aiyukan yi a tsakanin jama’an da suke rayuwa a jihar domin tallafa wa rayuwarsu, ya kuma qara da cewa gwamnatin tarayya ce ta umurci yin irin wannan shirin domin rage matasan da suke rayuwa ba tare da aiyukan yi a faxin qasar nan. Ya yi qarin haske kan waxanda za su ci gajiyar shirin da hukumarsu ta faro a Bauchi, “Waxanda masu cin gajiyar wannan shirin, daga cikinsu mata xari shida ne 600 ne, waxanda suke samu horon nan a kan fannoni irin su haxa man gashi, kayyakin shafe-shafe, man qamshin xaki, man shafawa, sabulai,

xinkin zamani na kayan mata da kuma haxa takalmai, da dai sauransu,” Ya qara da cewa, “Sannan kuma, maza xari huxu 400 ne suke cin gajiyar shirin, waxanda suke samun horo ta fannoni daban-daban da suke jivinci koyon sana’ar dogaru da kai,” In ji Ko’odinetan. Ya bayyana cewar wasu fannonin horon za su xauki tsawon makkonni biyu ana koyar musu, inda kuma wasu sana’o’in za su kai wata uku suna amsar horon dag wannan hukumar. Xaya daga cikin masu amsar horon, Shehu Musa ya nuna matuqar farin cikinsa da kuma godiyarsa a bisa samun kansa daga cikin masu cin gajiyar wannan tallafin, ya bayyana cewar

hakan zai taimaka musu gaya wajen inganta rayuwarsu. “Mu al’ummar qaramar hukumar Darazo muna matuqar godiya da yadda aka samu wannan shirin horon, hakan zai kawo ci gaba ta fuskacin rage rashin aiyukan yi sosai a faxin jihar nan ta Bauchi,” Kamar yadda Shehu ya bayyana. Ya bayyana goyon bayansu da kuma gamsuwarsu da yadda gwamnati mai ci ke qoqarin gudanar da kyawawan aiyukan a tsakanin jama’a. Wakilinmu ya labarto cewar hukumar NDE ta kuma yi irin wannan horon wa marasa aiyukan yi su dubu 2,000 a jihar, wanda suka yi a watan Junairu zuwa Maris na 2018 domin rage yawaitar marasa aiyukan yi.


A Yau

LABARAI 7

Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

Aikin Hanya: Gwamnatin Tarayya Za Ta Kashe Naira Biliyan 47

Daga Umar A Hunkuyi

Gwamnatin tarayya ta amince da kashe Naira biliyan 47 domin yin aikin wasu hanyoyi a qasar nan. Hanyoyin da za a yi da waxannan kuxaxe su ne, Hanyar Babban Lamba zuwa Sharam, a Jihar Filato, wacce za a yi ta kan Naira biliyan 19.2, sai ta Legas zuwa Otta zuwa Abeokuta, wadda ita kuma za yi ta a kan kuxi Naira bilyan 22, da kuma hanyar Enugu zuwa Fatakwal, ta sashen Aba, kan Naira biliyan 6.309. ministan Lantarki, Gidaje da Ayyuka, Babatunde Fashola ne ya bayyana hakan jim kaxan da fitowar su taron majalisar qasa, wanda Mataimakin Shugaban qasa, Yemi Osinbajo, ya jagoranta a Abuja. Ministan ya ce, hanyar Legas zuwa Otta zuwa Abeokuta, mai tsawon kilomita 81, an bayar da aikin ta a shekarar 2,000, amma sai aka yi watsi da aikin. Wannan gwamnatin tana son xan kwangilan ya koma bakin aikin sa ne, bayan an sabunta masa kuxin aikin. “Hanya ta uku kuwa, wadda ta tashi daga Enugu zuwa Fatakwal, wacce take matuqar bayar da matsala. A yanzun haka, xan kwangilar yana bakin aikin, amma sai mun canza fasalin aikin saboda ruwa da ya yawaita a kan hanyar, sai mun fitar da makwarara, a kan Naira bilyan 6.309.” Shi ma Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya sanar da cewa Majalisar ta amince da a kafa Jami’ar Sojoji a Biu, ta

Jihar Borno. Shi kuwa Ministan albarkatun ruwa, Suleiman Adamu, ya sanar da cewa, Ma’aikatar sa ta miqawa Majalisar wani tsari ne da ta shirya kan matsalar ruwa da kuma tsaftace muhalli, da yake addaban qasarnan, inda suka bukaci gwamnati da ta miqe tsaye domin ta yi wani abu kan hakan. A cewar sa, Ma’aikatar na shi ta nu na wa gwamnatin cewa, wadatuwan ruwa a birane da karkara yana qara ja baya ne, shi ma lamarin na tsafta yana ta ci baya ne, ta yadda in an ta fi a hakan, sashen ba zai iya cim ma burin nan na, ‘Millennium Development Goals,’ ba. Ministan harkokin cikin gida, Abdurrahman Dambazau, cewa ya yi, Majalisar ta amince da kammala aikin ginin tsangayoyi biyu, wajen hutawar xalibai da kuma xakin cin abincin xalibai a Kwalejin ‘Yan sanda ta Kano. Ya bayyana cewa, ayyukan suna daga cikin shingayen da aka gindaya wa cibiyar kafin ta sami amincewa a xaukaka ta. A watan Mayu ne na shekarar 2010, aka gabatar da buqatar xaukaka matsayin nata, a lokacin da aka xaukaki matsayin ta na wacce za ta iya bayar da shaidar karatun digiri. Jimillan kuxin aikin shi ne, Naira Milyan 234. Da zarar an kammala aikin, za mu gayyaci hukumar lura da Jami’o’i ta qasa, NUC, ta zo ta dubi wasu daga cikin darussan na ta da ba a rigaya an xaukaka matsayin na su ba, in ji shi.

•Fashola

Mai Talla Shi Ke Da Riba:

LEADERSHIP A YAU Ta Shirya Tsaf! Kamar yadda kowa ya sani ne, wannan jarida mai albarka, LEADERSHIP A YAU ta kafa tarihi wajen zama jaridar Hausa da ta fara fitowa a kullum. Wannan fara fitowa a kullum yana da alfanu masu yawan gaske, gare mu Kamfanin LEADERSHIP da ku masu karatu, musamman masu sana’o’i manya da qanana. Wannan ne ya sa muke farin cikin shaida wa masu karatunmu cewa mun shirya tsaf domin tallafa wa kasuwancinku, ta hanyar tallata maku shi zuwa inda ba ku zata ba. Domin a halin yanzu mu kanmu da muke buga wannan jarida ba za mu iya bayyana iya inda ta ke shiga ba. Muna da tsare-tasare da dama don talla ku da hajojinku, inda muka fitar da tsarin ‘IYA KUXINKA IYA SHAGALINKA.’ Wato akwai cikakken shafi, akwai rabi, akwai kwata, akwai kuma daidai iyaka abin da mutum ke so a sanya masa. Wanda a wannan shafin muna so masu sana’o’i, musamman manyan dillalai su tallata hajojinsu, su qananan ’yan kasuwa akwai

nasu tsarin. A wani tsarin ma da muke da shi, akwai yanayin da mutum zai tallata hajarsa, sannan ya tallata kansa, inda za a sanya hoton shagonsa, hotonsa da kuma taqaitaccen tarihinsa, kuma wannan duk a kuxi kaxan. Maza ku kasance cikin kashi na farko na masu cin moriyar wannan shiri. Ina ’yan Canji, dillalan yaduka, masu kayan masarufi, mayan da qananan ’yan tireda, dillalan magunguna, masu kamfoni da masana’antu, dillalan hatsi, dillalan mota, masu sayar finafinai da dai sauran masu sana’o’i, ga dama ta samu. A tuntuvemu a lambarmu ta 08148507210, 07036666850, 08039216372, 07037934034, 08032875238 da 08038011382: email leadershipayau@gmail.com. Ko kuma a tuntuvi wakilanmu na jihohi don qarin bayani.


8

NAZARI

A Yau Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

Qungiyar KADA Ta Yi Sabbin Shugabanni Daga Bashir Isah

A Lahadin da ta gabata ne aka rantsar da sabbin zavavvun shugabannin qungiyar Karofi Development Association da aka fi sani da KADA a taqaice da ke Unguwar Karofi Keffi, Jihar Nasarawa, domin ci gaba da jan ragamar harkokin qungiyar. Tun farko sa’ilin da yake jawabi a wajen taron, shugaban kwamitin zaven da aka gudanar Malam Adamu Salihu, ya bayyana cewa, kwamitin ya bi dukkan matakan da suka dace wajen gudanar da aikin da aka xora masa wanda a qarshe mutum goma sha takwas daga jerin ‘yan takaran da suka nemi muqamai daban-daban ne suka yi nasara. Da yake jawabin ban-kwana ga jama’a, shugaban qungiyar mai barin gado Malam Yahaya Labaran, ya shaida wa taron cewa an kafa qungiyar KADA ne sama da shekaru talatin da suka gabata da zummar haxin kai da cigaban yankin Karofi Keffi. Ya ci gaba da cewa, tun bayan kafuwar qungiyar zuwa yau sun samu nasarori da daman gaske waxanda jama’a suka amfana, ciki har da yin hanyar samun taransfoma na lantarki guda biyu don amfanin jam’ar Karofi da kewaye, samar da rumfar bugu ta zamani, gyara hanyoyi da samar da magudanan ruwa da dai sauransu masu yawan gaske. Alhaji Shamsuddin Abubakar (Fakacin Keff) ne ya

•Sababbain Shugabannin Qungiyar KADA

kasance babban baqo a wajen taron. Da yake tofa albarkacin bakinsa yayin taron, ya nuna cewa abin alfahari ne da Allah ya albarkaci qasar nan da ‘yan qasa masu kishi. Tare da cewa shugabanci abu ne mai muhimmancin gaske a tsakanin al’umma, don haka ya ce duk wanda Allah ya bai wa shugabanci sai ya riqe amana yadda ya kamata. Daga nan, Alhaji Shamauddin ya jaddada buqatar da ke akwai jama’a su kasance masu biyayya ga

shugabanni gami da dokokin qasa. Sannan ya qarasa da yi wa sabbin shugabannin KADA da aka rantsar fatan alheri, tare da yin kira ga sauran unguwannin garin Keffi da su yi koyi da KADA don cigaban al’umma. Da yake jawabi a madadin sabbin shugabannin KADA, sabon shugaban qungiyar Malam Nasara Abdullahi, ya nuna godiyarsu ga jama’ar Karofi da wannan dama da suka ba su na jagorancin al’amuransu. Tare da bayyana

tsarin aikinsa a matsayin shugaban qungiya mai ci da ya haxa yaqi da sha da saida miyagun qwayoyi a yankin Karofi. Kazalika, ya yi kira ga ‘yan unguwa da su ba su cikakken haxin kan da suke buqata domin ba su damar iya sauke nauyin da ya rataya a kansu. Kana ya yi fatan mahalarta taron Allah ya maida kowa gidansa lafiya. Tuni dai sabbin shugabannin suka sha rantsuwar sava layar kama aiki ta hannun Barista Hassan

Usman. Sabbin shugabannin qungiyar dai sun haxa da Nasara Abdullahi a matsayin shugaban qungiya, Yahaya Mika’ila a matsayin mataimakin shugaba na 1, sai Barista Nuhu Yusuf Yashi babban sakatare da Bala Muhammad Ango a matsayin ma’aji da dai sauransu. Taron dai ya samu halartar jama’a da dama daga sassan Keffi, ciki har da jiga-jigan ‘yan siyasa da dai sauransu. Yayin da taron ya watse lami lafiya.

Iska Mai Qarfi Ta Yi Ajalin Mutum Guda A Keffi Daga Bashir Isah

Biyo bayan iska mai qarfi sakamakon ruwan sama da aka samu a garin Keffi a Talatar makon jiya, hakan ya yi sanadiyyar rasuwar mutum guda tare da jikkata wasu bayan da iskar ta tumvuke wata qatuwar bishiyar xorawa har jijiya inda bishiyar ta faxi a kan wani masallaci da ke qarqashinta alhali da jama’a cikin masallacin suna fake ruwa. Wannan al’amari mai cike da tashin hankali ya faru ne a yammacin wannan rana da misalin magrib a mararrabar Unguwar Karai da ke Unguwar Lambu Keffi, Jihar Nasarawa, inda Rabo Alhaji Shuaibu da aka fi sani da suna Baba Rabo ya rasa ransa. Waxanda lamarin ya faru a kan idanunsu sun bada shaidar cewa, Baba Rabo tare da wasu mautane suna cikin

wannan masallaci ne suna fake ruwa, ruwan da ya zo xauke da iska mai qarfi. Ana haka ne sai aka ji faxiwar wannan bishiya ta xorawa a kan masallacin inda ta raba masallacin biyu tare da ragargaza shi. Bayanai sun tabbatar da cewa bayan aukuwar ibtila’in, nan da nan jama’a suka haxu domin ceto waxanda lamarin ya rutsa da su a cikin masallacin. Daga bisani an samu fitar da mutanen cikin masallacin inda aka taras da Baba Rabo rai ya yi halinsa, sauran mutanen kuwa sun samu raunuka daban-daban. Marigayi Baba Rabo mazaunin Unguwar Karai ne, magidanci ne har da ‘ya’ya, kuma ma’aikaci a jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi. Tuni dai aka yi jana’izarsa washegari Laraba kamar yadda addinin Islama ya tsara.

•Varnan da iska ta yi a Keffi


A Yau Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

Burinmu Shi Ne Mu Sauqaqa Muku

Ba a chaj in kuxin on ka cire d i j a h c a a B saqonnin watin waya kuxi daga ak na wasu banku

Da zaran an buxe asusu da mu, za a morewa rashin chaji idan mutum ya cire kuxi a akwatin wasu bankuna, haka kuma ba za a riqa cire kuxin saqonnin waya ba.

Domin cimma nasara a hada-hadar banki, ka yi mu’amala da bankin Sun Trust a Yau Ziyarci: www.suntrustng.com

TALLA 9


10

TALLA

A Yau Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

Gaba dai! Gaba dai “Super Eagles”

Bankin Zenith na taya ‘yan qwallon Nijeriya “Super Eagles”, murna sakamakon nasarar da suka samu ta kai wa gasar Cin Kofin Duniya wanda za a gudanar a qasar Rasha.


A Yau

RAHOTO 11

Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

Qwararru Na Qoqarin Samar Da Ingantaccen Irin Shuka A Qasar Nan —Dakta Maji Daga Sabo Ahmad, Abuja

A qoqarin da suke nyi na taimaka wa manufar wannan gwamnati na wadata qasa da abinci,tuni qwarru a fannin aikin gona suka duqufa wajen ganin an samu nasarar aiwatar da wannan kyakkyawar manufa ta gwamnati. Dakta Maji Alhassan Iswako qwararre a fannin irin shuka daga ma’aikatar Afirkan Rice, yana kuma cikin waxanda suka gabatarda lacca a wajen taron qarawa juna sani, wanda ake yi a Ciniyar binciken aikin gona da wayar da kan manoma da bayar da dabarun noma ta jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Taron wanda gwamnatin tarayya bisa haxin gwiwar African Development Bank suka xauki xawainiyar gudanar da shim asana sun baje ilim yadda za samar da hanyoyin da za dinda samun ingantaccen iri shuga domin amfani mai kyau • Dakta Maji Alhassan Iswako kuma mai yawa wanda zai sa ce an farfaxo da su, an inganta manomi ya ci ribar sana’ar ta sa iliminsu game da irin shinkafa shi ya sa muna qasa-qasa sosai. Mahalarta taron sun fito ne mutane daga wuraren nan. daga jihohi guda bakwai wato, Wannan shirin da muke yi jihar Imo da Anambura da yanzu mun gabatar da gayyatar Enugu da Kebbi da Sakkwato da mutane kamar hamsin daga Kano da Neja da kuma Jigawa, waxannan gurare, wasu sun zo wanda waxannan jihohin daga jami’o’i wasu sun zo daga ke kan gaba wajen samar da ADPs wasu sun zo daga National sarrafa iri, shi ya sa ma a ke Seed Concil wasu sun zo daga kiran waxannan jihohi da Crop Seed Companies don kawai mu haxa kai mu san yadda za mu Processing Zone. Baya ga maganar bunqasa inganta iri a qasar nan, shi . Kuma fatan wannan nya iri akwai kuma maganar samar zama kamar phase one ne, da kayan more rayuwa ga amma a phase two za a ce a bar al’ummar wannan qasa kamar, wannan states da muke yanzu gyara yanayin noma,ko hanyoyi ko ko a’a mu inganta abin da ko samar da ruwan shad a na muke yi a wannan states, a’a noman rani ko gina ko gyara wasu states ne? Yanzun ba za makarantun al’umma, kanmar mu iya fadi ba. Gasikiya abin da firamare ko a ginawa manoma zai faru. rumbunan da za dinda adana Dakta ya ce bisa hasashe amfanin gonarsu da kuma za mu iyawadata qasar nan taimakawa wajen harkar lafiya, da abinci, amma ba mu kai ta hanayar samar da qananan matsayin ba. Duk abubuwa da asibitoci da gyara su. gwamnati ke yi takan taimaka, Dakta Maji ya ci gaba da akwai taimako ana yin gaba, cewa, “a ma’aikatanmu ta amma kadan akwai wani African Rice, aikinmu shi ne na muhimmin abu da ba su yi ba shinkafa, wannan training da kuma sai sun inganta sun yi muke yi shi ne batun gyara irin wannan abun, duk wuraren shinkafa, saboda muna ganin cewa manomi ya shiga gona ba nan qasashen da ke kawo mana shinkafa a nan qasar ba iri ingantacce, to matsala ne, Sannan akwai abu muhimmi sa neman su dogara da ruwan da ke damun manomanmu na sama, sai da noman rani qasa, ba su da ingantaccen iri wannan gaskiya gwamnatin da za su shuka a gonakinsu, ya nan da na gaba da na baya ba za mu yi mu gyara yanayin daga su fahimci wannan ba, kuma ya wurare da yawa waxanda suke kamata su fahimta. Bari in gaya maka misali da fada a ji daga aikin noma? kamar Chana kamar Thailand Kamar su jami’o’i da cibiyoyin waxanda suke kawo mana binciken aikin noma kamar su shinkafa ba sa dogara da ruwan ADPsda makamantan su. sama, madatun ruwa suke Haka kuma ma’aikatar kula amfani da su. da iri ta qasa National Seed Haka Pakistan Indonesia Council dukkansu ya kamata a

• Jibrin Aliyu

wuraren nan ba wanda ke dogara ga noman shinkafa a dogara ga ruwan sama, kuma wuraren nan yanzu suna bada karfi ga rijiya, ruwan rijiya a gona, ruwan rijiya ai ba ruwa ba ne, kudi manoma suke kashewa kuma zai maida amfanin da tsada ka gane ko? Gwamnati ya kamata su tashi tsaye a ga cewa ko wane waje da a iya noma shinkafa a samar masu ruwa. Ai akwai hanyoyi da yawa, muna da irin rivers da yawa, wasu kanana wasu manya ko ba haka ba? Irin karamin dam za a iya yi, irin abin da ake kira head dikes za a iya yi, babban famfo wanda zai ba da ruwa arha ko ma manoman ne za su ba da kuxi a sai mai zai fi masu arha yana rike famfo nasu, ka gane ko? An gyara yanayin noman an yi masu channels a samu babban famfo wanda za a sa, su wannan Companies ai famfo suke amfani da shi kuma suna cin riba kuma famfo suke amfani da shi ko ba haka ba ne, a ce a samu wani famfo wanda zai iya tallafa manoma kamar dubu a wani lokaci ko ma dari biyar, source na ruwan su daga waje guda inji guda ne, ai wannan zai iya yi na taba ganin wannan a gurare da yawa in ka je Nijer, Chad suna da wanu river ana kiran shi River Tsari, kana tafe a bank na river din za ka ga pumps din nan sun yi targeting communities ana ba su ruwa, su manoman famfo ya zama nasu su za su kiyaye da shi, ba yan sun girba za a karba za a karbi amfanin gona daga kowa na kula da injin da mai, an yadda za a iya samun ruwa. A qarshe Dakta ya shawarci

• Muhammad Idi

da su mayar da hankali ga noman rani in suna so a samu shinkafa a qasar nan. Ga manoma kuwa, Ga manoma su koyi noman zamani, su maida noma ciniki. Jabiru Aliyu daga NAERLS na daga cikin waxanda suka halarci taron qarawa junanin wanda kuma ya nuna amfanuwar da ya yi wanda ya ce zai taimaka masa da sauran al’ummar havaka noman shinkafa. Haka kuma Muhammad Idi daga National Agricultural Seeds ya ce wannan taro kamar ma su aka shiryawa domin suke ada alhakin tabbatar da ingantaccen iri ya shiga hannun manoma.


Siy as a

A Yau Asabar 14.04.2018

Rigar 'Yanci

2019: Takarar Buhari Nasara Ce Ga ‘Yan Nijeriya – Sanata Ibrahim Ida Ci gaba daga jiya Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara a 2019, sai dai za mu iya kallon irin rikice-rikicen da suke faruwa a jam’iyyar APC, da kuma rikicerikice tsakanin gwamnoni da Sanatoci, ko gwamna da ‘yan majalisa, ba ka ganin hakan zai kawo wa jam’iyyar cikas? To ai mulki haka ya gada, kai sai a qarshen mulki a qyale k aka ci kai kaxai ba wata husuma? Duk inda ake mulkin duniya ko ina ne, wanda ke mulki da ke wajen mulki, wanda jam’iyyarsa da wand aba a ciki yake ba akwai wannan kiki-kaka xin, haka siyasa ta gada, kuma haka za a ci gaba, haka aka fara kuma haka za a ci gaba har gobe. Mu juyo kan maganar da kai, APC ta kafa gwamnati yau shekara uku ke nan da wani abu, in wannan wata na biyar ya zo shekara uku ke nan za a shiga ta huxu. Dole ne gwamnanoni ka gaya min shin ina ne ake da wannan rikicin? Akwai a Kaduna, akwai a Kano, akwai a Bauchi, ka san dalili? Duk masu kawo rigimar da jam’iyyar ba ta da tasiri, da ba zata iya cin zave ba, da za su damu da ita ba. Ai ganin qarfin jam’iyyar ne, waxanda ke kai sun tsaya sun jajirce suna yi wa jama’a aiki, akwai kura-kurai nan da can, amma ka gaya min, mu xauki jiha Kaduna me ake faxa? Ka ji an ce ya saci kuxin jama’a? babu, illa dai kawai ka ji an ce ya yi kaza, ya je ya kori jama’a, to gaya min in an ce ya kori ma’aikata 20,000 da wani abu, amma ya xauki 30,000 da wani abu su mayr gurbinsu, shin wai yau ka je ka gaya wa waxanda aka xauka su 30,000 xin nan cewa a a xaukar taku da aka yi aiki kuskure ne, sai su yarda? Kuma wanda ya sallami 20,000 ya xauki 35,000, ai shi mishi albarka za a yi, eh ya lura cewa akaw wasu abubuwa da ake na laifi ya tsaida su.

lokacin da el-Rufa’i ya zo Abuja gidaje ya riqa rushewa, ya hana bara, ya hana ‘yan babur, yau ka dub aka gani kowa xaga masa tuta yake. Waxannan masu kiki-kaka ba su suke zave ba, jama’ar gari su suke zave, yau idan ka je ka ajiye akwatin quri’a ina tabbatar maka cewa el-Rufa’i zai ci zave fiye da yadda ya ci a baya, ka ga shi ke nan, wannan rikicin cikin gida ne, kuma har yau duk maganar ake. Kwankwaso yana nan cikin jam’iyyar APC bai je ko ina ba, kuma har yau har gobe in ka dubi Ganduje har yau jar hula ya ke sawa, yadda aka taho a baya an samu savani kaxan, wannan ina tabbatar maka xinkewa za ayi. Zaven ya zo, Kwankwaso ya yi gwamna shekara takwas, ba zai koma gwamna ba, Sanata yake, wannan yana iya yi har illa masha Allahu har Allah ya xauki ransa. Gwamna ya yi shekara huxu ta farko zai koma, ba abin mamaki bne ka tarar gobe sun kama hannu ana sharholiya kamar yadda aka saba. Sai Sokoto tsakanin Wamako da shi gwamnan na yanzu ake ta iqirarin cewar akwai rashin jituwa, amma me yake faruwa? Kullum suna tare, shin wanda yake yayi hamayya da shi kan wannan abin har ya je kotu yana neman cewa Tambuwal ba shi ya kamata ba, me ya faru? Cikin satin nan tare suke ya ziyarce shi. Duk waxan nan abubuwa ka xauki Bauchi, eh akwai amma yanzu me? Duk qorafeqorafen da cikin jam’iyyar APC na waxannan jihohi, wallahi tallahi babu abinda ba zai iya gyaruwa cikin xan lokaci qanqani ba. Saboda haka ina so in tabbatar maka sanarwar da Shugaban qasa ya bayar ta cewa zai nemi ya sake tsayawa, yayi shi ne bayan masana da ‘yan siyasa da ke tare da shi da ‘yan uwa sun zauna sun dubi gaba sun ga cewa APC ba ta da matsalar cin zave a Nijeriya, sun ga cewa waxan nan jihohin da suke da qorafi da rikici, abu ne mai sauqi a gyara.

• Sanata Ibrahim Ida

Saboda haka babu wani abu da zai tayarwa da xan APC na gaskiya hankali, kuma dukkanamu yanzu qalubalenmu shi ne, mu tashi tsaye mu tabbatar cewa duk wasu qorafe-qorafe, duk wasu rashin jituwa tsakaninmu mun gyara. Mulki dai na Allah ne, wanda zai yi gwamna daga nan har duniya ta tashi Allah ya riga ya tsara abinsa. Amma ya ce mu nema, saboda haka su masu nema waxanda har neman yake kawo masu rashin jituwa da masu mulkin ba laifi sukai ba, illa iyaka kirana ga dukkan xan jam’iyya shi ne, eh ka nemi mulki halal ne, kuma ka yi hamayyar siyasa halal ne, abinda yake haram

shi ne, ka zo ka vata ruwan kai ka san ba sha za ka yi ba, amma ka zo ka gurvata shi, to shi ne ba shi da kyau. Saboda haka ina kira ga waxan nan don Allah don Annabi a zauna a yi maslaha, domin qalu-bale garemu wannan zaven da zai zo, ba don muna jin muma da rauni ba ko ba za mu iya cin zave ba a a, ko wane zave ka xauke shi kamar ba z aka iya cinsa ba, to sai kai aiki tuquru. Saboda haka waxan na qorafeqorafe ba za su yi wa APC illa ba domin za a gyara su. Yekuwar da Shugaban qasa ya yin a cewa zai tsaya, wallahi ta yi dai-dai, domin kamar yadda wasu suka ce in ma da bai tsaya ba da kotu

Ci gaba a shafi na 13


TATTAUNAWA 13

A Yau Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

‘Takarar Buhari Nasara Ce Ga ‘Yan Nijeriya’ Ci gaba daga shafi na 12

za su kai shi, to ina xaya daga cikin waxanda inda takarda ce zan sa hannu, domin na san mutum ne kamili, mutum ne mai aqida ta alheri ga wannan qasa To akwai wani tsagi na dattawan Arewa da suke ganin shekarun Shugaba Muhammadu Buhari sun ja, saboda haka kamata yayi ya b wa matasa masu jini a jika dama shi ya je gida ya huta, ya kake waxan nan dattawa da suke irin waxan nan kiraye-kiraye? To na farko dai akwai tsofaffi akwai dattawa, tsufa maganar shekaru ce, dattaku kuma maganar hankali da gabata. Saboda haka duk mai hankali ya san cewa girma na shekaru, in bai yi baka komai ba shi ne ya baka tunani, da hankali da za ka kalli gaba, kuma ya hana maka wasu abubuwa na guvata rayuwar xan-adam, in ka girma akwai wasu ababuwan da ba sa ma cikin zuciyarka, na xaya ke nan. Na biyu shi mulki da tsoho da yaro kowa yana da hurumin nema, illa iyaka mutanen da za su zo su jefa quri’a su ne za su yanke hukunci, kashi 60 bisa 100 na masu jefa quri’a matasa ne, shi wai me zai hana matasan nan su haxa kansu, jira suke sai an ba su? Babu wanda zai ba ka mulki ko waye kai, su zo su nema, su zo a yi gwagwarmaya da su, su tashi su kira ‘yan uwansu matasa su gaya masu cewa lokaci ya yi da za ku zavi ‘yan uwanku matasa. Wato matasanmu suna da wani abu, wai sai su ce a bar masu kamar wani na dole, a a ba haka bane, kamar ko wane xan Nijeriya. Ah to ina zuwa, xan shekara 70 ya ce zave a Amurka, xan shekara 40 ya ci zave a Faransa, Faransa tsofanta ya fi na Amurka, saboda haka magana ake ta shin zai iya aikin nan? Allah ya jarabce shi da rashin lafiya, kuma Allah ya sa ya warke, duk wanda ya ganshi a yanzu ya san ya wuce murmurewa ya ma warke. Saboda haka maganar wasu dattawan Arewa ni ban xauke su dattawan Arewa ba tsofaffi kawai, saboda sun ga lokacinsu ya wuce, ko sun nema ba su samu ba, ko suna nema ba za su samu ba, sai suka ga lokaci, don haka suke cewa duk wani wanda ke da shekaru irin nasu ya dawo. Nijeriya tana buqatar shugaba wanda ya san jiya ya san yau, zai iya hango gobe. Shugaba wanda ya kai lokacin da kuxi

• Sanata Ibrahim Ida

da kayan zamani ba su da wani tasiri a zuciyarsa, saboda haka duk wani wanda zai zo y ace lokaci ya yi zai bari, shi ne ya kamata ya bar maganar, kuma ba wani dattijo bane tsoho ne. Sannan kuma su matasa kada su zauna su haxa ahnnuwansu a girji su ce za a kawo masu mulki, babu wanda zai baka mulki sai ka nema, su tashi su nema, idan suka tashi Allah Ubangiji sai ya taimaka masu. Matasa su ke jefa quri’a, idan matasa suka jefa quri’a ga mai shekaru da yawa, ashe ke nan ba laifin mai shekarun bane laifin su matasan ne. Kuma kar su manta matasan yau su ne dattijan gobe fa, idan matashi yana tunanin shi matashi ne, sai ka ga kafin ya Ankara ya fara furfura, nan da nan sai ka ga lokacin ya wuce. Amma in ya zamana har yanzu ba su nema ba, sai ka ga xan shekara 80 ma ya zo ya karva daga hannun xan shekara 70. Kana cikin qungiyar Xattawa a wannan yanki na Arewa, wanda kuma a baya-bayan nan yankin yana fama da rikice-rikice na qabilanci da qabila kaza da qabila kaza, satar shanu ne da sace garkuwa da mutane, wanda har ta tsohon Ministan tsaro wato TY Xanjuma ya fito yana cewa sojojin Nijeriya ba za su iya kare jama’a ba don haka mutane su xauki makami su kare kansu. Ka san tsaro kamar yadda shi ma ya san tsaro, me kake jin wannan kalami ya za jawo? To Alhamdulillahi wannan

tambaya ce mai muhimmanci, kuma zan ba da amsar ta cikin sauqi. Kamar yadda ka faxa Janar xan Juma xan Arewa ne, Janar xan Juma xan Nijeriya ne, kuma gogaggen soja ne, idan zai fito yayi wannan furuci a halin yanzu, to menene dalili? Wannan dalili zan ba da shi cikin sauqi. Ina karanta ‘Whats’app’ sai na ga wani labari, ‘wai me ya kawo?’ Mutumin nan ya ce, a zamanin Abdullahi Bayero, sai aka kawo wasu ‘yan Nepu da laifin sun zagi Sarki an xaure su an kawo su gaban Sarki. Tunanin kowa a fada shi ne Sarki zai sa abuge su ko ya sa a xaure su, sarki ya gansu ya ce me ya faru, aka ce ai sun zagi Sarki ne, sarki ya ce a kwance su su tafi. kowa ya yi ta mamaki, abinda sarki ya ce, “Iyayen yaran nan da kakanninsu idan za mu wuce zuwa suna jinjina suke suna gaishe mu, suna Allah ya qara mana nasara, Allah ya kiyaye ka. So suke su gammu su ga iyayenmu su ga kakanninmu, ashe idan kuwa ‘ya’yansu suka zo suna zaginmu ai mu ya kamata mu zargi kammu.” To kada mu kalli Xan juma, mutum ne zai iya kuskure, amma mu kalli abinda y ace, ni na san sojan Nijeriya kashi 99 na sojan Nijeriya sahihai ne masu qaunar qasarsu, sun sadaukar da kansu don su kare Nijeriya, amma akwai bara gurbina xaya ke nan. Na biyu, yanzu zamani ya zo mutane satar kayan soja suke ko na jami’an tsaro su tare hanya, duk wanda ya gansu zai ce soja ne, ni xinnan an tava

tare ni akan hanya mutum ya sa kayan soja, amma da hango na san ba soja bane, saboda ni na yi mu’amala da soja. Ana sojan gona da soja ana yin abubwa, illa iyaka X juma ya kai matsayin da duk abinda zai wa Nijeriya ya yi, amma kuma duk abinda Nijeriya za ta yi masa ta yi masa, saboda haka ya sani cewa duk furucin da ya yi a yanzu duk abinda ya fax aba wai yana faxa ne a inda yake fax aba, yana mgana a Nijeirya gaba xaya da duk duniya, duk Kalmar da ya faxa za ta yi tasiri. Saboda haka don Allah don Annabi irinsu waxanda yau idan cewa yayi yana neman ya ga Shugaban qasa kafin magariban nan zai ganshi. Duk abinda aka yi ya vata masa rai ya lura da cewa babba fa shi juji ne, saboda haka ya sami hanyar da zai riqa yi wa masu mulki magana, ba sai ya fito ba yayi kalamai waxanda za su iya jawo wata husuma ba. Kuma gaskiya abinda y ace xin nan wallahi akwai mtsaloli a Arewar nan tsintsiya maxarinki xaya wadda Shugabbni su kai mulki ba tare da sun yi la’akari addininsu ko qabilancinsu ko jinsinsu ba. Saboda haka bai kamata irin waxan nan kalamai su riqa fita daga bakin irinsu ba. To amma mu kuma ‘yan Arewa abinda ya kamata mu yi gaskiya mu zauna mu yi tunani, idan muna son Arewa ta zama xaya, to mu zama xaya, ya zama farin cikin wancan shi ne na wannan, amma ba za mu zauna haka kawai kara zube ba.


14 NAZARI

A Yau Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

Da Sana’ar Rake Nake Ci Nake Sha Daga Bala Kukuru

Alqalin qungiyar masu sayar da rake Alhaji Lawal Xandume ya bayyana cewar sana’ar rake sana a ce ta rufin asiri domin kuwa da ita ce suke ci, suke sha, suke bikin dangi, suke biyan kuxin makarantar yaransu da sauran buqatu na rayuwar yau da kullum. Alhaji Lawal ya yi wannan bayani ne a kasuwar Sheme

ta qaramar hukumar Faskari da ke jihar Katsina yayin da qungiyar ke gudanar da taronta na mako domin tattaunawa a kan matsalolin da ke addabar qungiyar a ofishinta na garin Sheme. Alkalin ya ci gaba da cewa, game da sana’ar rake sai godiya domin kuwa a cewarsa sana’ar ta riqe su manyansu da yaransu, sun sai motocin hawa da na xaukar kaya, sun gina gidaje,

sun je Hajji, sun sauke farali da wannan sana’ar. Da ya juya kan garuruwan da ke zuwa wannan kasuwa su yi sayar da rake su koma gida cewa ya yi farko akwai Arewacin nijeriya wanda mutanenta na garin Illela da sauran waxansu garuruwan suna zuwa wannan kasuwa ta Sheme suyi kasuwancin rake sannan kuma ya ci gaba da ba da bayanin sauran wuraren da ake kawo wannan rake a

wannan kasuwa ta Sheme domin sayarwa. Garuruwan kuwa sun haxa da Makarfi da Hunkuyi da Giwa da sauran makamantansu sannan a xauke shi zuwa Arewacin NIjeriya irinsu Illela da Mafara da Gusau da Sakkwato da Kebbi da sauran garuruwa na sauran jahohin Arewacin Najeriya. Qarshe ya yi kira ga gwamnatin tarayya da

sauran gwamnatocin jihohi game da noman rake, a cewarsa kowane vangare na noma gwamnatin na ware wani kaso domin tallafawa amma ban da vangaren noman rake, a cewarsa a kan haka ne yake miqa kukansa ga gwamnatin tarayya da sauran gwamnatocin jihohi da su rinqa tallafawa vangaren noman rake domin manoman raken su ma su rinqa amfana.

An Fara Garkuwa Da Qananan Yara A Giwa Daga Idris Umar, Zariya

A ranar juma’ar da ta gabata ne wasu mutane waxanda ba a San ko su waye ba suka sungumi wani yaro mai suna Aminu Yakubu xan shekara 7 a wata unguwa Madara a cikin garin Giwa ta jihar Kaduna. Alhaji Yakubu shi ne uban yaron wanda ya ce, “ Wallahi ba zan iya cewa komai ba sai dai addu’ar Allah ya bayyana min wannan yaron” amma wani bawan Allah abokin uban yaron da aka sace, wanda ya ce a sakaya sunansa amma shi ma cewa ya yi “Tabbas a ranar Juma’a ne da misalin qarfe 4 zuwa 5ny, Aminu ya fito yana wasa a qofar gidansu da ke unguwar ta Madara. Kafin magariba sai iyayen Aminu suka lura bai shigo gida ba, sai aka fara nemansa tare da sanarwa ga duk inda ake sa ran ganinsa, amma babu labarinsa har zuwa wannan lokaci da muke wannan magana babu wani labari amma yanzu babu abin da muke yi illa roqon Allah ya bayyana mana wannan yaron”. Ya zuwa yanzu bincike ya muna cewa, masu garkuwa ne suka shigo garin na Giwa inda suka sami sa’ar yin garkuwa

da shi Aminu da wani yaro amma wancen yaron da suka tambaye shi cewa ina babanka? Sai ya ce musu “ Ai babana ya rasu” sai suka ce to mamanka fa? Sai ya ce “Ita ma ta mutu “ hakan ya sa suka sake shi amma sukaqi Aminu. Majiyarmu ta shaida mana cewa, masu garkuwar har sun kira wayar yayan Aminu tare da shaida masa cewa, sun yi garkuwa ne da Aminu har sai an ba su wasu miliyoyin kuxi za su sako shi. Wakilinmu tuntuvi jami’an ‘yan sanda na garin Giwan don jin ko wane mataki suka xauka a kan lamarin. DPO mai kula da wannan qaramar hukumar bai samu damar cewa komai ba saboda alokacin suna tattaunawa kan maganar tsaro qaramar hukumar. Su ma qungiyar tsaro na Civil Defence sun qi yarda su ce uffan, saboda al’amarin na gaban magabatansu. Dakta Yahaya Ibrahim shi ne kantomar qaramar hukumar ta Giwa wanda ya bayyana cewa, “A gaskiya ban ji daxin faruwar wannan lamari ba amma tuni na rubuta rahoto a kan lamarin na tura ga amma ina kira ga jama’ar qaramar

•Dakta Yahaya Ibrahim hukumata da su tashi tsaye wajan addu’a a kan wannan bala’i da ya shigo cikin qasa

baki xaya kuma za mu xauki duk matakan da suka dace wanda ba sai mun yaxa ba.

Saboda haka ina kira ga jama’a da su kula da yara tare da lura da duk wani baqon ido

Mulkin Buhari Alheri Ne Ga Nijeriya Daga Bala Kukuru

Wani matashin xan siysa, Musa rayuwa Kankiya wanda ake yi wa laqabi da Buhari, da ke qaramar hukumar kankiya ta jihar katsina, ya ce mulkin Muhammadu Buhari alheri ne ga ‘yan Nijeriya a halin yanzu idan aka yi la’akari da abubuwan da mulkin ya kawo na ci gaban qasar nan a halin yanzu. Rayuwa ya ci gaba da faxin cewa, jama’ar Nijeriya kada su manta da irin matsalolin

da aka baro a baya kafin zuwan wannan gwamnati. Amma a halin yanzu ana ta samun ci gaba ta fanni daban-daban. Idan aka dubi sha’anin tattalin arzikin qasar nan, an samu ci gaba na ban mamaki. Ballantana kuma sha’anin rayuwar jama’a kamar kiwon lafiya da ilimin zamani da na addini, sanin Allah da sauran makamantansu duka waxannan abubuwan gwamnati ta samu nasarar samunsu.

Idan kuma aka dubi sha’anin noma uwa uba ke nan tun da wannan gwamnati na iyakar qoqarinta wajen kare martabar noma. Sannan ya ce ko a yanzu ma gwamnatin tana ta bayar da tallafi game da noman rani da na damina. Rayuwa ya qara da cewar ko a haka gwamnatin ta tsaya ta riqe wuta a kan waxan nan tsare-tsare babu shakka ‘yan Nijeriya sun samu abubuwan jin daxi da more rayuwa.

Musa rayuwa ya ci gaba da magana akan yan siyasar najeriya musamman masu amfani da wasu kafofin yada labarai na kudi suna batama wannan gwamnati suna to su sani fa shi sharri kukuyo ne mai yinsa yake bi, abaya ya kara da cewar yan najeriya su ci gaba da yima wannan gwamnatin addu’a domin ta kara samun nasarorin gudanar da ayyukan alheri domin al’ummar najeriya su amfana da shuganci shugabanni

wajen abubuwan da suka shimfidawa na alheri. Dan siyasar ya ci gaba da nuna farin cikin sa game da kokarin gwamnatin janaral Muhammadu Buhari na karbo yammatan makarantar sakandire na Dapci a hannun yan boko haram da sauran ayyuka makamantan wadannan, da fatan Allah ya ci gaba da yi masa jagora dashi da sauran masu madafun iko. Da fatan Karin samun zaman lafiya a kasar najeriya Amin.


Wasanni A Yau

Asabar 14.4.2018

Na Yanke Hukuncin Da Ya Dace – Machael Oliver

> Shafi na 17

Tafiyar Neymar Alheri Ne A Wajena.

> Shafi na 18

An Haxa Arsenal Da Atletico Madrid A Gasar Europa

> Shafi na 18

> Shafi na 17

Kovac Ya Zama Sabon Mai Koyar Da Bayern Munchen Nijeriya Ta Zama Ta Shida A Afirka Kuma Ta 47 A Duniya In Ji FIFA

> Shafi na 17


16 WASANNI

A Yau

Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

Zan Yi Ritayar Dole Sakamakon Abin Da Oliver Yayi Mana – Buffon

Kyaftin xin qungiyar qwallon qafa ta Juventus, Gianluigi Buffon, ya ce alqalin wasa ya zalunce su a wasan da Real Madrid ta fitar da su daga gasar cin kofin zakarun Turai a ranar Larabar data gabata. Alqalin wasan xan qasar Ingila, Mark Oliver ya baiwa Real Madrid bugun fanareti a mintin qarshe bayan da Mehdi Benatia ya ture Lucas

Vazquez, sannan kuma ya bai wa Buffon jan kati. Buffon yace a zahiri take cewa fanaretin bogi ne kamar yadda Buffon ya shaida wa kafar yada labaran qasar Italiya. Buffon ya qara da cewa kamata ya yi Oliver ya zauna a cikin ‘yan kallo ya ci dankali saboda yadda ya lalata musu burinsu.

Real ta samu nasara da ci 3-0 a wasan farko amma sai Juventus suka rama a wasa na biyu, inda Mario Mandzukic ya ci qwallaye biyu sannan Blaise Matuidi ya ci ta uku. Sai dai a lokacin da ake shirin tafiya qarin lokaci, sai Oliver ya bai wa Madrid fanareti kuma Cristiano Ronaldo ya narka qwallon a cikin raga a minti na 97.

Buffon ya zaqe wurin nuna vacin ransa abin da ya sa aka ba shi jan katinsa na farko a gasar zakarun Turai a wasansa na 650 a Juventus. Kyaftin xin na Juventus ya ce babu yadda za a ce wannan fanaretin gaske ne kuma bazai tava mantawa da Oliver ba a rayuwarsa saboda haka zaiyi ritayar dole daga qwallo.

A Karon Farko A Tarihi An Fara Wasan Tseren Keke Na Mata A Qasar Saudiya A Karon farko qasar Saudi Arabia ta gudanar da gasar tseren keke na mata, a qarqasin sauye sauyen da Yariman qasar, Muhammad ibn Salman ke aiwatar wa. Rahotanni sun ce an gudanar da tseren kekunan ne a birnin Jeddah da ke qasar ta Saudi Arabia, inda mata 47 suka shiga gasar ta kilomita 10. Wadda ta shirya gasar Nadima Abu al-Enein ta ce ta yi mamakin ganin yawan

A Yau

EDITA Mubarak Umar

Wasanni

EDITA Abba Ibrahim Wada TSARA SHAFUKA Sulaiman Idris group

Shugaba Sam Nda-Isaiah BABBAN DARAKTAN GUDANARWA Abdul Gombe

matan da suka shiga gasar, wanda a shekarun baya abu ne mai wuya a faxin qasar. Nadima ta ce da an shirya mata 30 za su shiga gasar, amma kuma ganin yawan matan da suka fito ya sa suka qara zuwa 47. Qasar Saudi Arabia na ci gaba da ganin sauye sauye tun bayan kama mulkin Sarki Salman bin Abdulaziz, wanda ya naxa xan sa Muhammad a matsayin Yarima mai jiran gado.


A Yau

Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

Nijeriya Ta Zama Ta Shida A Afirka Kuma Ta 47 A Duniya In Ji FIFA NIjeriya ta xaga sama da aqalla mataki biyar a jadawalin da FIFA ke fitarwa kowanne wata kan qasashen da suka fi iya qwallo a Duniya.Yanzu haka dai NIjeriyar ita ce ta 47 a duniya kuma ta Shidda a Afrika da aqalla maki 635. A jadawalin da ya gabata kafin na yau Najeriyar ita ke a matsayin ta 52 a jerin

qasashen da suka fi iya qwallo da maki 609. A nahiyar Afrika Tunisia ce a qololuwa kuma ta 14 a duniya sai kuma qasashen Senegal da Jamhuriyar Dimocradiyyar Congo da ke mara mata baya a matsayin na 28 da 38 a duniya. A duniya baki daya kuma qasar Jamus ce ke ci gaba da riqe kambunta a matsayin ta

xaya sai kuma Brazil ta biyu yayinda Belgium wadda a baya ke matsayin ta 5 yanzu ta dawo ta 3. A ranar 17 ga watan Mayu mai zuwa ne Fifar zata qara fitar da wani jadawalin wanda hukumar take la’akari da yadda qasashe suke buga gasa da kuma yadda suke samun nasarori a wasan qwallon qafa.

Real Madrid Da Bayern Munchen Da Kuma Liverpool Da Roma A Gasar Zakrun Turai Qungiyar qwallon qafa ta Real Madrid za ta kara da qungiyar Bayern Munich a gasar cin kofin zakarun Turai yayin da Liverpool za ta kara da Roma wadda tayi waje da Barcelona a gasar. A jiya ne hukumar kula da qwallon qafar nahiyar turai ta raba qungiyoyin huxu da suka rage a gasar bayan qungiyoyin sun samu nasara a wasannin da suka buga na kusa dana kusa dana qarshe. Za a yi wasannin a ranakun 24/25 na watan nan na Afrilu, sai zagaye na biyu a ranakun 1/2 ga watan Mayu mai zuwa kuma a watanne za’a buga wasan qarshe. Za a buga wasan qarshe na gasar zakarun Turai a birnin Kiev, na Ukraine, ranar 26 ga

watan Mayu. Real Madrid ta fitar da Juventus a wasan dab da na kusa da na qarshe, yayin da Roma ta fitar da Barcelona. Ita kuwa Liverpool ta doke Manchester City, sai Bayern da ta yi waje da Sevilla ta qasar sipaniya a wasanni biyun da suka fafata A bara ma Real Madrid, wacce ke riqe da kanbun, ta fitar da Bayern a kan hanyarta ta lashe gasar sai dai Bayern Munchen na qoqarin lashe gasar a karon farko tun shekara ta 2013. Bayern ce za ta fara karvar baquncin wasan farko, yayin da Roma za ta ziyarci Liverpool a wasan farko.

WASANNI 17

Na Yanke Hukuncin Da Ya Dace – Machael Oliver

Alqalin wasan daya busa wasan qungiyar qwallon qafa ta Real Madrid da Juventus, Macahel Oliver, ya bayyana cewa ya yanke hukuncin daya kamata a wasan da yabawa Real Madrid bugun fanareti a ranar Larabar data gabata. Sai dai wannan fanaritin ya haifar da cece-kuce, inda wasu musammam magoya bayan Juventus ke caccakar alqalin wasan da ya bada damar bugun na daga kai sai mai tsaren gida. Alqalin wasan daga Ingila, Michael Oliver ya bada fanaritin bayan Mehdi Benatia na Juventus ya hana Lucas Vazquez na Madrid zura qwallo bayan ya kawo ma sa hari ta baya a dab da gida. Alqalin wasan ya kuma bai wa mai tsaren ragar Juventus, Gianluigi Buffon jan kati bayan ya yi jayayya da shi kan hukuncin da ya xauka, kuma ana ganin wasansa na qarshe kenan a gasar cin kofin zakarun Turai. Buffon da ake saran ritayarsa na ba da jimawa ba, ya buga gasar zakarun Turai har sau 125 amma bai tava lashe kofin gasar ko sau xaya ba. A martanin da ya mayar, Ronaldo ya ce, bai ga dalilin da ya sa ‘yan wasan Juventus ke bore ba saboda wannan bugun fanaritin da aka ba shi. Yanzu haka dai Real Madrid mai rike da kambi ta shiga matakin gaba a gasar, in da za ta haxu da Bayern Munich yayinda kuma Roma zata kece raini da Liverpool A karon farko kenan cikin wasanni 22 da ta yi a gidanta a gasar zakarun Turai da Bayern Munich ta gaza zura kwallo.


18 WASANNI

A Yau

Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

An Haxa Arsenal Da Kovac Ya Zama Sabon Mai Koyar Da Bayern Atletico Madrid A Munchen Gasar Europa A gasar Europa qungiyar qwallon qafa ta Arsenal za ta kara da Atletico Madrid ta qasar sipaniya a wasan kusa da na qarshe a gasar Europa, yayin da RB Salzburg ta qasar Jamus za ta haxu da Marseille ta Faransa. Arsenal za ta fara wasan farko ne a gida a ranar Alhamis 26 ga watan Afrilu, sai kuma ta je gidan Atletico a ranar 3 ga watan Mayu mai kamawa Za a yi wasan qarshe na gasar ne a ranar 16 ga watan Mayu a birnin Lyon na qasar Faransa, inda duk qungiyar da ta lashe kofin za ta samu

gurbin zuwa Gasar Zakarun Turai na baxi kamar yadda dokar take Arsenal ta samu nasarar kai wa ga matakin wasan kusa da na qarshe ne bayan ta doke CSKA Moscow da jumullar kwallo 6-3 yayinda Atletico Madrid tayi waje da Sporting Lisbon ta Portugal kafin takawo wannan matakin. Ita kuwa Marseille ta doke RB Leipzig ne ta qasar Jamus a wasansu na baya yayinda Salzburg tayi waje da Lazio ta qasar Italiya a fafatawarsu ta kusa dana kusa dana qarshe.

Qungiyar qwallon qafa ta Bayern Munchen ta tabbatar da cewa tsohon xan wasan qungiyar, Nico Kovac shine zai zama sabon mai koyar da qungiyar a kakar wasa mai zuwa bayan vangarorin biyu sun amince da juna. Kovac, xan qasar Crotia wanda tsohon xan wasan qungiyar ne daga shekara ta 2001 zuwa ta 2003 yanzu shine yake koyar da qungiyar Eintrancht Franfurt ta qasar Jamus wadda kawo yanzu take mataki na biyar akan teburin gasar kuma zata buga wasan kusa dana qarshe a sati mai zuwa a gasar cin kofin qalubale na qasar. Daraktan wasanni da qungiyar ta Bayern Munchen, Hassan Salihamidic ya bayyana sabon mai koyarwar a matsayin wanda yasan tarihin qungiyar ta Bayern Munchen sannan kuma yasan yadda qungiyar take

tafiyar da harkokinta na wasanni. Daraktan yaci gaba da cewa zasuyi aiki tare da sabon kociyan qungiyar domin ciyar da qungiyar gaba inda kuma yace tuni qungiyar ta shirya bashi duk irin goyon bayan dayake buqata a matsayinsa na mai koyarwa. Tuni dai Kovac ya amince zai saka yarjejeniyar shekara uku a qungiyar idan kakar wasa ta qare inda zai karvi aiki a hannun Jupp Heynckes, wanda ya karvi qungiyar tana cikin wani hali a hannun tsohon mai koyarwa Carlos Ancelotti bayan da qungiyar ta koreshi sakamakon rashin qoqari a farkon kakar wannan shekarar. Bayern Munchen dai tuni ta lashe gasar Bundes liga ta wannan shekarar kuma yanzu haka zata haxu da Real Madrid a gasar cin kofin zakarun turai a wasan kusa dana qarshe a qarshen wannan watan.


A Yau Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

TALLA 19


20

A Yau Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

Soyayya Da Shaquwa Tare da Muhievert Abdullahi

08083104306 (Tex kawai)

Assalama alaiki yake annurin zuciyata ki nutsu ki saurari Zuciya ki ji abin da za ta faxa a kanki yake hubbina. Wasalam Ina sauraranta yayin kuma da hankalina da zuciyata suka tahallaqa a kan ka ya kai sanyin idaniyata. A duk lokacin da taurari suka haska sararin samaniya ni kuma a wannan lokacin hasken kyakkyawar fuskarki ke haskaka idanuwana yake annashuwar zuciyata, yake burin zuciyata raina fansa ne a kanki yake hasken ruhina abar sona abar begeta a kodayaushe. Na yi farin ciki yayin dana san Kai ne zavin zuciyata kuma me sanyaya mata ako wane lokaci. Ke ce masoyiyata ke ce nake ji a zuciyata ke ce duniyata saboda ke ce rayuwata masoyiyata ki matso kusa da ni a kowane lokaci nakan yi kewarki ako wane dare nakan tava tunaninki. Zan so mu rayu kuma mu mutu tare a cikin taska wadda ta kasance daga masoya kuma haxaxxu Yake masoyiyata hasken ruhina akwai suddabaru a tattare da ke akwai qamshin farin ciki aziqinki wanda ni kaxai nakan ji hakan da bugun zuciyata my love. Kar ka yi tunani ko tantama a kan soyayyata ya kai masoyina ka kalli hannuna na dama yayin kuma da nake so ka rufe idanunka kyauta ce zan ba ka daga cikin zuciyata, Na kira ka my lollipop na kira ka my sweet angel mataye da dama na hange daga nesa amma na san ba za su hango abin da idaniyata suka gani ba. Allah na gode ma da ka ba ni aminiyar zuciyata wacce a kodayaushe zuciyata take bugawa a kanta masoyiya soyayyarki ta riga da tamun xibankaran-mahaukaciya. Nakan yi tinani a cikin qayataccen lambun soyayya wanda ya cika da kayan marmari zoka riqe hannuna masoyi rabuwa da kai kamar qarewar kayan marmari ne a cikin qayataccen lambu. Na taho na miqo hannuna zuwa gare ki ya ke gaddaran zuciyata a shirye nake da in amsa babbar kyauta daga zuciyar da tafi kowace zuciya kyawu wacce kyawun ta ta fi ta zinari kyau da qyalqyali. Na gode da nuna soyayya tabbas ka cancanta ka karvi babban kambu wanda ya gagari maza da dama ya kai abin alfaharina kuma mafarkina. Abar sona na taho na miqo hannuna gareki ki miqo mun hannunki mai laushi tamkar tumfafiya in kai ki lambun masoya ki buxe kyakkyawan bakinki mai cike da hasken annashuwa in tsinki tuffa in ciyar da mallakar zuciyata in shayar da ke giyar soyayya ta ki bugu a cikin soyayya ta yake a bar qaunata. Godiya nake ya kai gwarzona kuma jarumi abin alfahari nakan ji haske da nushaxi idan Ina tare da kai yaka taho masoyi mu zauna na yi ma hirar masoya kwalelen maqiya. Wow you are my love i feel you in my heart because you my heart and U my soul ever day i miss you baby

Samfuran Kalaman Soyayya

ever night i miss you touch ke ce al jannat dausayina ke ce soyayyata ke ce mallakata burina ke ce annashuwar zuciyata na ba ki kaina da kaina yake my heart I don’t know what is life without you. I am mighty glad that God gave you to me, and my dream comes true don’t leave me my lollipop Matsayika ya tabbata acikin fadar zuciyata me tartare da shunfid’u na alfarma me xauke da jajayan furanni Wanda suka haskaka doman soyayyar ka my only Na ji kira na amsa yake hasken ruhina makiya sun buga sun kasa na riga da namasu fintinkau a kan soyayyarki tuni na daxe da mallaka maki fadar zuciyata ke kaxai ce kike mulkin mallaka a cikin ilahirin birnin zuciyata. Tabbas na durqusa na karvi wannan kyauta daga kyakykywan masoyi me kyawun Aniya manifata in a ce na mallaka ma komai idan ban mallakeka ba to tabbas zuciyata tana cikin sarqa a xaure yayin da ruhi ke kasance ba a gangar jiki ba. Haqiqa na zama sarkin zuciyarki kin zama sarauniyar zuciyata my heartbeat na shigo zuciyarki mai cike da tsananin kyawu wanda babu irinsa a duniya wanda a cikinta na samu annashuwar tawa zuciyar. Wayyo masoyiyata de na wannan maganr a kodayaushe ke ce burin zuciyata ki sani ni wata ke ce zarata a kowane lokaci ba ma rabuwa da juma hanta kin zamo jinin hantar wanda a kodayaushe xaya ba zai iya rabuwa da xaya ba zan so ki zama nono in zama fura muhaxu a kwaryan soyayya Kar ka yi tinanin zan dena sonka amma kayin tinanin yadda zamanmu ze kasance cikin yadda da amana my lv. A kodayaushe tunanina da naki xaya ne wanda ni na fassara na ki ke ma kika fassara tawa fassarar kuma kala xaya ce shi ne ni da ke mutu ka raba takalmin kaza haqiqa ni da ke za mu yi zama na amana har se mun bar tarihin soyayyar da babu wasu masoya da suka bar kalansa yake bugun zuciyata, Abar qaunata shirunki na minti xaya a gare ni ba qaramin asara ba ce a zuciyata maganarki kaxai yakan annashuwar zuciyatane. Ina tare da kai ya kai madarar idaniya me sa zuciya farin ciki ka kasance mutum me farin jini cikin qoqon raina bazan iya tina sau nawa nake mararunkaba ka kula dani zan baka soyayya zan ba ka madara wadda tafi Zuma masoyina Ku gafara ku ba ni wuri in yabi my queen heart xina kyuki tum hiho ab tum hiho zindagi ab tum hiho only for you in my heart,Haqiqa nasan cewa zara bata iya nisa da wata haqiqa nayi dace da samun sarauniyar kyawawan matan duniya kuma farin cikin zuciyata burin ruhina. Na fika son nai ta yabeka my sweet lov domin ina so duniya ta shaida ba nida wani Wanda ya fika kuma zuciyata kai take marari cikin dare ko rana

safiya ko yamma zaune ko a qwance nakan yi murmushi idan na tuna cewa tomorrow will belongs tome my beautiful handsome my oga,Idan nayi duba izuwa masoya nakan ga kamar nasu wasane Amma nakan yi alfahari da soyayyarmu Kai ne kasa na zamo ta daban a rayuwata godiya da haxaxxe kuma haxaxxe a cikin masoya.

Saqonnin Masu Karatu Makon Da Ya Gabata Na Yi Tambaya Ne A Kan “Tsakanin yarinyar da ba ta tava soyayya ba da wadda ta tava soyayya wacce za ka iya aura? Kawo dalilai a kan hkan. Ke ma da namijin da be tava soyayya ba da wanda ya tava wanne za ki aura? Kawo naki dalilan a kan hakan” Na kuma samu saqonni kamar haka: Al’amin Hamisu Japanis: Hmm Ni Wadda Ba ta Tava Soyayya Ba. Dalilina shi ne ni ne mutum na farko da zan xorata akan tsarin soyayyar da nake da buqata ta gaskiya kuma zan koya mata yadda nake son zamammu ya kasance sannan hakan zai sa dukan abin da na koya mata zai zama na farko a gunta na soyayya kuma zamu fi shaquwa savanin wanda tasan samfur kala kala na qaryar soyayya da yaudara tana sona ba ta sona ba zan gane ba sannan duk wasu abubuwa baki zan riga gani wanda ni basu yimin ba vangaren zamantakewa ta soyayya. Aminu Hamisu Japanes Kano State 07032206226 Abbah Obi: Ni dai a nawa tunanin gwara yarinya wadda ba ta tavayin soyayya ba,sakamakon in harta horo da soyayya to gaskiya soyayyar zai zamo abu mai wuya murabu,soyayyar farko itace soyayya bata tava rabuwa koda an rabu

to gaskiya akwai shauqin qauna acikin zukata, sannan zakafi samun kulawa da yarda da aminta agareta. Abba obi karaye 08107379600 Njib Farhn: E! to gaskiya nafisan na auri mace wacce bata tava Soyayya ba, hikimata a nan shi ne, zan gina ta a kan soyayyar gaskiya wacce babu Qarya ko alguss acikin ta, sannan tasan dukkan tsarukana, da duk wata kafa wacce za ta guji faxawa da maqaryatan ‘yan soyayya. Najeeb Farhan Kawo Lambu 07069113538 Nana Hawwer: Hmmm ni dai wanda bai tava soyayya ba, Dalili na anan shine wanda ya tava soyayya baya tava mancewa da wacca ya so xin ko shekara nawa za a yi musamman in ita ce first love xinsa yana da wuyar futa daga zuciya kona aureshi zai dinga tunanin wadda suka rabu da ita xin, Amma wanda bai tava soyayya ba a kaina ya fara zan san yadda zai sa ya so ni sannan kuma in tsara masa yadda soyayyarmu za ta kasance cikin kwanciyar hankali Nana Hawwa Fagge Shukurat Kano State 09059343485 Ummzee: Ni Wanda Bai Tava Soyayya Ba, Dalilai na shi ne idan wanda ya tava soyayya ne kuma ya shaqu da ita sosai kuma tazo ta yaudare shi to da wuya ya kumayin soyayya kuma ya shaqu da wata cikin sauqi kamar yanda ya shaqu da ta da kuma kullum cikin tunanin ko wata za ta yaudare shi ne kamar yanda waccan ta yi masa a da.Wannan shi ne dalilai na. Ummzee Lagos state. 09067978040


21

A Yau Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

Noma Tushen Arziki Dabarun Noman Albasa

Tare da Yahaya Usman Alfadarai 07084634387 09096984945 NAERLS/ABU ZARIA Samaru Zariya

Gabatarwa Albasa na xaya daga cikin muhimman abinci na yau da kullum a kasashen Afrika wajen gyara miya, sannan kuma ga saurin kawo naira. A Nijeriya an fi nomata a jihohin Arewa, kuma a kan nomata rani da damina. Zaven Wuri Zabi wuri mai ni’ima mai isasshen taki wanda baya cin ruwa, kuma marar duwatsu ko marmara. • A lokacin rani sai a zabi bakin fadama ko kusa da rafi ko kogi ko madatsun ruwa don samun ruwa. Zaven Iri Akwai “Wuyan Bijimi”, da “Jar Albasa”, zabi nagartaccen irin da ya dace da karkarar ku. Tuntubi baturen gona ko Director AERLS/ ABU Zaria don shawara. Gyaran Wurin yafi Iri •Zavi wurin da ya dace. Yi kaftu da bubbuge bangarorin kasar ka gyara ya yi lebur. •Shirya bedi mai matsakaicin fadi (mita 1 - 1 1/2) mai isasshen tsawo ( ya yi tudu da damina, amma ya yi kwari da rani). Yafin irin albasa •Ja layuka inda za ka yafa irin. Kada zurfinsa ya wuce centimita 1.3 kuma tsakanin layi da layi kada ya wuce centimita 10 zuwa 15. •Samo yashi ka cude irin sannan ka yi yafin ko kuma kana iya yin yafin sannan ka barbada yashin, bisanshi. •Lullube kan yafin da ciyawa sannan ka yi ban ruwa •Idan sabon tsiron ya fito sai a cire ciyawar •Idan ka ga sabon tsiro ba ya girma kamar yadda a ke so to sai ka kara masa taki kamar haka: Auna takin CAN cikin fankon ashana 11 ka zuba cikin ruwa gallon daya ka dama, har ya narke. Daga nan sai ka malala ruwan a fili mai murabba’in fadin mita biyu. •Sabon tsiro zai is a dashe bayan sati 6 zuwa 8 da yin yafi, ko idan ya kai tsawon centimita 15 zuwa 23. Gyaran Wurin Dashen Albasa Yi kaftu ka zuba isasshen takin dabbobi (FYM) ko buhu 2 1/2 na supa ga kowace hekta. •Idan da rani ne sai ka shirya kunyoyi masu dan bisa wadanda za a rinka yin ban ruwa ta kwarinsu, ko kuma a shirya fangaloli masu zurfi wadanda za su iya ajiye ruwa, kuma a yi ban ruwa ta cikinsu. •Da damina kuma sai a yi fangaloli masu tudu (dan bisa) •Akan noma Albasa har sau uku a shekara a jihohin Arewa wato farko da karshen damina da kuma lokacin rani. Ga karin bayani: Fasalin Shuka 1. Albasa ta farko, lokacin yafin irinta karshen watan Afrilu, lokacin yin dashe tsakiyan watan Yuni, lokaci diba cikin Agusta ko satunba. 2. Albasa ta biyu, lokacin yafin iri cikin watan june, lokacin yin dashe July zuwa August, lokacin diba November ko

December 3. Albasa ta uku lokacin yin yafi September zuwa December, lokacin yin dashe November zuwa December, lokacin diba March zuwa April. Yin Dashe A Gona •Tugo yabanyar da lura ka dasa daidai zurfin yanda ka cirota. Kana iya rage tsawon ganyayen zuwa centimita 10 idan har sunyi tsayi. •Yi dashen kan layuka masu nisan tsakanin centimita 15, nisan tushe da tushe centimita 15. Karin Taki Bayan takin da aka sa lokacin gyaran fili, akan so kuma a yi karin takin CAN buhu 5 ga kowacce hekta. Ga yadda za ka yi: Yi ga naka da buhu 2 1/2 bayan mako 2 ko 3 da yin dashe, sai kuma ka kara wadansu buhu 2 1/2 bayan sati 4 da sawan farko. Ga Shawara •Ka yawaita yin noma, amma ka yi da yar karamar fartanya. •Kada karufe duk kwayar albasar da ka gani a waje da kasa. Yin hakan zai sa Albasar ta rube. •A lokacin rani sai a yawaita ban ruwa. Yi sau biyu ko uku ya wadatar bisa ga yanayin kasa. •Amma a yi hattara. Yawan ruwa ga albasa ya kan sa ta rube. Kulawa Da Lafiyar Albasa Qwari da Tsutsotsi Da CuceCuce 1. Kwari da Tsutsotsi (a) Tsanya (Gyare) yakan yi barna ga Albasa tun a bedi da bayan an yi dashe. Ga magani. Cuda 1/2 kilo, na maganin Agrocide, da kilo 45 1/2 na dusa ka zuba a kan bedin ko a gonar don gyaran ya ci. (b) Kwarin Albasa (Onion thrips) Wadannan kwari ne masu zama kan ganyen Albasa suna tsotse ruwan jikinsa har ya yankwane, ya lalace. Maganinsu (I) Idan an gansu (sati 4 zuwa 8 da yin dashe) sai a yi feshi sau uku da maganin cymbushi U.L.V. lita 2 1/2 ga kowace hekta a kowane sati har sai sun mutu. (ii) Ko kuma a yi amfani da kilo 1.32 na Vetox 85 cikin ruwa lita 110 ga kowace hekta. 2. Cuce-Cuce (a) Ciwon ganye (Purple blotch) Wannan ciwon wadansu kananan kwayoyin cutuka na ‘fungus’ ne ke kawo shi. Kuma ciwo ne na rani da damina ya kan sa ganyen Albasa ya yi fari-fari, sannan sai ya canza kasa-kasa nan da nan da zaran yanayin dumi ya samu. Idan abin ya yi tsanani, sai launin ya zama garura - garura. Daga nan sai ganyen ya lakube, ya zama rawaya ya mutu. Yadda Za A yi Maganinsa A lura da canjin wurin shuka A yi amfani da maganin Dithane M45 kuma a rinka yin dashe da wuri (b) Rubewar Albasa Ciwone wanda wasu kananan

kwayoyin cutuka na hunhuna ke kawo shi. Yakan kama Albasa tun a gona har ya zuwa sito wurin ajiya. Alamomin kamuwa sune ‘kambori’ a saman ganyayen Albasa da rubewar saiwoyi. A kasan kwayar Albasan kuma za a ga farin hunhuna a sashen da ya rube. Maganinsa A yawaita canjin wurin shuka. A tuge duk tushen da ya harbu a binne. A rinka yin dashe a wurin da ruwa baya kwantawa. Kada a yi amfani da takin da bai rube ba. Kada a zuba ruwa ya wuce misali in an zo yin ban ruwa. (c) Murdewar Ganye Alamun wannan ciwo shine murdewar ganyen Albasa. Idan ya tsananta kwayar Albasa takan kankance ko ta ksance babu sai dogon tsiro. Wannan cuta ta fi yawa ga Albasar damina. Maganinta Dama 1/2 kilo na Benlate da ruwa lita 500 ka fesa ga kowacce hecta. Ko kuma ka dama 1/2 kilo na Benlate da 1/4 - 3/4 na Antracol da ruwa lita 500 ka fesa ga kowacce hekta. A fara yin feshin kafin cutar ta tsananta, kuma a yi ta yi bayan kowanne mako. Cirar Albasa Albasa ta kan isa cira idan mafi yawan ganyayenta sun bushe ko sun zama rawaya. Cire ta da hannu sannan ka kwantar da Albasar ta gefe har misalin kwanaki biyu domin ta tsane ta bushe. Daga nan sai ka kwaso ta ka tara ta a cikin inuwa har na kwana 7 - 14. Sannan sai a yanke ganyen a bar dan guntu kamar dan yatsa (3 - 5 cm) daga nan sai a zabi kwayoyi masu kyau daga kanana da rubabbu. Ajiyar Albasa Kwayoyin Albasa masu matsakaicin girma da fadi kawai ya kamata a ajiye. Kada ka ajiye

wadanda suka fara yin fure da wadanda basu kosa ba, da kuma manya ainun. Kada ka ajiye kwayar Albasar a kasa. Ajiyeta kan wani abu domin iska ta samu damar ratsawa. * Ka rinka bi kana tsince duka Albasar da ta rube ko wanda ta fara tsira bayan kowane sati biyu. * kana iya yin amfani da maganin maleic hydrazide don hana tsirar Albasa a sito. Tanadin Irin Albasa Ka da ka yi iri daga Albasar da ta yi fure a shukar farko. Irin da aka samu daga wannan Albasar ba ya jure ajiya kuma yana da saurin ruba. Ya fi kyau a yi shukar iri dabam a lokacin rani. Ga yadda za ka yi. * Zavi qwayar Albasa matsakaiciya mai kyau wanda bata taba yin hure ba, kuma wanda ta yi misalin wata 5 - 7 a ajiye. * sai ka yanke ta a kwance gida biyu ka shuka bangaren kasan (wato gindin) a kan bedi mai isasshen takin gargajiya. * Ci gaba da yin ban ruwa misalin sati uku har ya tsiro. * Bayan mako 5 - 6, sabon tsiran tsawonsa zai kai misalin sentimita 15 - 20. Daga nan sai ka rarraba su ka dasa cikin bedi kan layuka masu nisa sentimita 20 nisan tushe sentimita goma goma. * Yawan tsiron da akan samu daga kwayan Albasa ya danganta ga girmansa ko fadinsa. Amma akan sami 7 ga kanana, 10 ga matsakaita, 20 ga manyan kwaya. A maimakon wannan hanyar da muka ambata a sama ta samun iri, kana kuma iya shuka kwayan gudan Albasar cikin bedi kan layuka masu nisan tsakanin sentimita 25, nisan rami da rami sentimita 25.


22

A Yau Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

ADABIN HAUSA

Tare da Sabo Ahmad 08065533969 saboahamad@gmail.com

Mahammadu Gambo Mai Waqar Varayi: Tsakanin Tuba Da Adabi (3) Daga Ibrahim A.M. Malumfashi

Tsakanin ra’i da ra’ayi Dalilin da ya sa ake nuna wa wannan fage irin na adabin Gambo wariya bai wuce madafar nazari ba. Yawancin nazarin adabi bai wuce jigo da warwara ba, in an motsa a qara salo da zubi da tsari. Sai dai mun manta ko mun qi mu amince tuni an wuce wannan ra’i, Wanda muka yi wa shimfixa, ya kuma zaune yawamcin nazarcenazarcenmu. Shi kuma ra’in lalatattun lamurra (Queer Theory) da suka haxa da sata da luwaxi da karuwanci da maxigo da batsa da bore da makamantan su, da qila zai iya yi mana jagora bai da mazauni a yawancin adabin Afirka, (dubi Olaniyan & Quason;2007). Kamar yadda masu nazari sukan yi bayani, maxigo da luwaxi da karuwanci da sata, baqin al’amurra ne a nahiyar Afirka. Idan ana maganar su a cikin aikin adabi ana kallon su ne ta yadda suka shiga cikin rayuwar mutanen Afirka, ba irin yadda suka wakana a rayuwar ba, ma’ana waxannan abubuwa al’ada ce irin ta Turawa da Hausawa suka gamu da ita a wani zamani. Shi ya sa ko a ra’in lalatattun lamurra aka rasa yadda za a vullo musu, sai dai a fito da bayanin yadda Adabawan suka shirya shi. Wannan shi (Dunton(1989) da Desai da Munro(2007) suka yi a nazarce-nazarcensu. Luwaxi a tsakanin sojoji da waxanda ke yin maxigo a makarantun kwana na ‘yan mata waxanda zuwan boko ne ya ta’azzara su, hakan ne ko ba haka ba ne ya danganta ga irin ra’in da mai nazari ya yi amfani da shi. Da kila waxannan masana sun ci karo da waqoqin Gambo da kila sun yi wa nazarinsu bita, domin a nan ne aka fito da abin da ra’in ke buqata sosai. Domin abin da Gambo ke cewa ke nan tun asali, shi ba waqa yake yi ba, nazarin

• Gambo Mai waqar Varayi al’umma yake yi, ya buga ganga ne domin ya shaida wa al’ umma abin da yake yi, mai kyau ko maras kyau, ko ka yarda ko kada ka yarda. Ke nan da sata gaskiya ce, faxarta a waqa ma gaskiya ce, nazarnta ma gaskiya ne! An ya kuwa ana tuba da faxar gaskiya? Ashe ramin gaskiya qurarre ne? Ana kuma tuba daga aikin adabi? Eeeeh aaaa’a. Kila dai mu ce ana yin ritaya ko murabus ko ajiyewa domin magada su ci gaba daga inda aka tsaya ko kuma dai aikin adabi ya qi aikatuwa, ma’ana waqar ta qare, ko alqalamin ya bushe, ko hikimar ta buwaya, dole ta sa a bar fagen, ba don ana so ba. To amma Gambo ya ce ya tuba, kila ma nan gaba a yi bikin qona ganguna da sauran kayan kixa, ban sani ba. Shin me ya sa Gambo zai tuba, in tubar ya yi? Shin a tunaninsa waqar varayi laifi ce? shi ya sa ya tuba daga yin ta? Shin nazarin al’ummar da ya yi a baya ashe laifi ne ya daxe yana yi wa Hausawa? Shin satar jiya ko ta gargajiya da ya faxa a waqoqinsa da

kuma satar zamani da ya kitsa daga baya sun ware ne tsakanin Hausawa? Wa ya qaru daga tubar Gambo? Ni dai ba zan iya sani ba, domin na xauka ba tuba ya yi ba, ga a in da yake faxa: Dud da ana yanke ni gobe, Dud da ana halbe ni gobe, Ba ni barin mugun kixan ga, Don ba tuba nikai ba, Sai in mutuwa tax xauki raina, Ko in kuma Allah ya hukunta. Jawabin kammalawa Da alama Allah ne ya hukunta, Tun kafin Gambo ya mutu, ya bar waqa bayan ya cika shekara 60 a doron qasa. Da yake kuma ba magaji ya bari da zai ci gaba daga inda ya tsaya ba, bari na qare wannan sharhi da irin tambayoyin da Gambo ya yi wa Nazaqi da ya ce ya tuba da yin sata, kila mu gane inda gaskiya lamarin yake. Kodayake ban da murya irin ta Gambo, amma duk da haka, kai, kai, a jinjina ganga! Wai Gambo na son tambayarka,

In ka tuba da waqar sata duniyag ga, Don ka tsira kiyama ka tuba Gambo, Ko Don ka kama ibada kab barin ta? Na ce in don ka tsira qiyama ka tuba Gambo, To, gobe qiyama Indi za ka, Ba wani sauqi za ka ji ba, Ka cika littafinka dauri, Had bisa bainai an rubuta. Shin Gambo ka tuba da waqa ne Don gudun gaba, To ka tuba yanzu ‘ya’yanka, Ubansu mawaqin nan na qwari, Shi ne sunan babansu bar abada. Gambo in ka zama babban malami, mai karatu, Tun da ba ka zama sarkin Musulmi, Gambo mai waqar nan ta qwari za a ce ma, Ba walwale suna za ka yi ba. Shin Gambo, ko ka tuba da waqa ne Don yau ba sata har varayi? Ka sani kai fa Gambo, ka tuba, ka tube har Mahadi Satar nan ba a barin ta To ina amfanin tubar? Wannan shi ne qarshen wannan maqala.


RAHOTO 23

A Yau Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

Yadda Vata-Gari Ke Cin Karensu Ba Babbaka A Kasuwanin Yobe Daga Muhad Maitela, Damaturu

Masu cin kasuwanin makomako a jihar Yobe, suna fuskantar barazana daga wasu vata-gari, ta yadda suka qirqiro sabbin hanyoyin yi wa jama’a damfara tare da amshe abin hannunsu. Mazambatan kan yi amfani da salo kala-kala wajen ha’intar mutumin da tsautsayi ya faxa kansa. Yayin da wani lokacin, sukan xana tarkon damfarar jama’a ta hanyar fake wa da qaramar sana’a ko qirqirar sana’ar cajin wayar tafi-da-gidanka, inda ta hakan sai su tara kayan jama’a ko su sayi kayanka, da sunan je ka dawo, daga bisani sai ka neme su qasa ko sama. A lokaci guda kuma, vata-garin kan yi amfani da qananan yara -ka za ta tare suke, su sayi kayanka sai su bar maka yaron, shi ke nan zancen ya sauya. Inda a wani jiqon su fake da wasa da maciji- bayan sun haxa baki, sai su ba mutum tsoro, wanda da zarar ya firgita sai su tsame shi. Wani binciken musamman da wakilinmu a jihar Yobe ya gudanar a kasuwanin mako da ke Babban-Gida, ta qaramar hukumar Tarmowa, da GarinAlkali a Bursari da Jajimaji a Karasuwa, sai kuma Gaidam, da takwarorinsu. Inda ya lura da yadda masu cin kasuwanin ke ci gaba da qorafin yadda waxannan vata-gari ke cin karensu babu babbaka. LEADERSHIP A YAU ASABAR ta zanta da xaya daga cikin masu cin waxannan kasuwanni, a kowanne mako- Sama’ila Alhaji Sa’idu Gashuwa, ya shaidar da cewa, “ A gaskiya, halin da ake ciki yanzu wasu mazambata sun addabi kasuwaninmu na mako-mako a nan jihar Yobe, saboda kuma yadda suka vullo da sabbin hanyoyi kalakala waxanda suke amfani da su wajen damfarar jama’a, su qwace musu dukiya.” “Wani sa’in sai ka ga mutum sanye da babbar rigar alfarma, kai ka ce wani hamshaqin mai kuxi ne ko wani babban ma’aikacin gwamnati ne, ashe xan damfara ne; qiri-damuzu ya zare maka idanu ya qwace maka kuxi. Irin hakan ya sha faruwa ga abokanmu masu sana’ar dabbobi a nan kasuwar Babban-Gida, da takwarorinta. Sannan kowanne lokaci canja salo tare da bin hanyoyi kala-kala suke yi wajen qwace wa jama’a kuxi. Saboda haka muke kira

•Wata kasuwa a Jihar Yobe

ga jama’a su rinqa yin kaffakaffa da mazambata”. “Ko a makon da ya wuce, akwai wani abokin sana’armuxan Shuwa, daga jihar Borno, wanda kowanne mako yake zuwa sayen dabbobi a wannan Kasuwar, ya zo da kuxi kusan Naira miliyan xaya (1,000,000), kawai sai wani mutum ya ja shi gefe, inda ya zare masa ido tare da nuna masa cewa, jami’in tsaro ne, yayin da ya ce ya kawo kuxin da suke a hannunsa. Bai yi gardama ba ya miqa masa kuxin kuma a haka ya tafi abin sa. Kuma irin hakan na faruwa bila adadin, a Kasuwar”. In ji xan Kasuwar. Bugu da qari kuma, wakilinmu ya gano yadda wani xan damfara yake amfani da kasa dankali wajen ha’intar jama’a a kasuwar Jajimaji a jihar Yobe. A irin wannan nau’in zamba, inda vatagarin ke sayo buhun dankali tare da karkasa shi a bakin rumfa wanda hakan zai jawo hankalin ‘yan’uwansa ‘yan kasuwa wajen amincewa da shi. A cikin wannan halin ya karvi kayan jama’a da dama, ciki har da turamen atamfa, kayan koli da makamantan su, da nufin idan yamma ta yi su dawo su karvi kuxaxensu. Yamma tana yi, masu bashi suka yi cincirindo a bakin rumfar mai dankali, shiru ba batu ba labarinsa. A haka mai buhun danklin ya tattara abin da ya rage, sauran kuma suka xauki na damo.

Har wa yau dai, a kasuwar dai, shi ma wani taqadari mazambaci ya tattara wayoyin tafi-da-gidan ka- waxanda jama’a suka ba shi caji, kan ka ce ‘biyar’ ya yi gaba da su, wata qila sai gobe qiyama. Yadda ya tsara al’amarin, shi ne ya nemo wani kwarakwaran injin bayar da hasken wutar lantarki, ya samu mahaxar jama’a a kasuwar, ya kafe janaratan tare da kayan cajin waya; ya sa kixa. Kan ka ce me, jama’a sai kawo wayoyin su suke- manya da qanana. Can, bayan da ya ga babu ido mai yawa a kansa, a haka ya cusa wayoyin jama’a a buhu ya kauce. A haka injin janarato ya yi ta bada wuta da hayaqi, xaya bayan xaya jama’a suka yi ta taruwa, ana jiran mai cajin, har kusan magariba babu amo ba labari. A lokacin da na leqa kasuwar Gaidam, can kuma wata irin sata ce ake yi wa jama’a ta qiri-da-muzu tare da haxi da renin wayau. Inda gungun ‘yan sane suka vullo da sabuwar hanyar qwace kuxin jama’a, a cikin baki alaikum. Yadda suke yi a kasuwar Gaidam, da zarar ‘yan shaukun sun kula akwai kuxi a jikinka, to sai abin da Allah ya yi, za su datse ka a wata kwana, su yi maka sane (tsame kuxin aljihunka) ta hanyar ba ka tsoro da macijin da suke wasa da shi, a lokacin da ka firgita, kafin ka dawo

hayyacinka sun gama maka aiki. Kuma ka neme su sama ko qasa- har da mai wasa da macijin, ka rasa. Wakilinmu ya zanta da jama’a da daman gaske a kasuwar ta Gaidam, sun bayyana cewa, baya ga sane damfara tare da wala-wala, wani sa’in kuma har da damfara ta hanyar sojangona; idan mazambatan suka ga kuxi a gunka, kuma da zarar sun ganka ‘haka-haka’ sai su ce maka su jami’an tsaro ne, su tuhume ka da kasancewa xan Boko Haram, nan take jikin mutum ya xauki tsima. A haka za su amshe ‘yan kuxin da ke jikinka. Bisa ga wannan ne ‘yan kasuwar haxi da sauran jama’a suka yi kira na bai-xaya ga gwamnatin jihar Yobe tare da jami’an da nauyin kare jama’a da dukiyoyin su ya hau kan su da cewa su kawo xauki domin shawo kan wannan matsala, wadda idan aka bar abin ya ci gaba zai ta qaruwa ne. Saboda haka ya zama wajibi ga dukkan jami’an da ke da alhakin daqile wannan babbar annoba da su tashi tsaye wajen ganin sun kawo qarshenta. Ga su kuma al’umma ya kamata su kiyaye, sannan duka wani wanda suka gab a su amince masa ba kar su yarda su qulla wata hulxa da shi, sannan da zarar wani ya fara yi maka barazana maza ka tona asirinsa. Kada a bari a dinga yin fargar jaji.


24

A Yau Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

Tare da

Umar Saleh Anka MNES,MEM

MUHALLI

usanka01@gmail.com

08036005151

Taqaitaccen Tarihi Game Da Shirin Yarjejeniya Ta Duniya (EarthCharter) (3) Tsarin Gudanarwa Game Da Faxaxa Aikin Yarjejeniyar Duniya, Wurin Hana Cinkoso

Gabatarwa: Yarjejeniya Ta Duniya tsakanin qasa da qasa(ECI) tana qarfafa kowa, ya taimaka wajen cim ma manufar shirinta. Ana bukatar cikakken goyon bayan da hadin kan ka. A wannan fanin, ECI tana kokarin daukak shirin a duniya baki daya, wajen karfafa ayukan da za su hana cinkoso wuri guda, a kuma bai wa mutane, da al’umomi, da qungiyoyi ikon tafiyar da ayyuka. Yayin da ECI ke villo da sabon tsari, ta za kuma cigaba da daukaka Yarjejeniya Ta Duniya, ta muhimman hanyoyi daban-daban,tsakanin qasa da qasa. Tana kuma iya shirya ta kuma tafiyar da dan vangare kawai, a yawan ayyuka da ake buqata domin aiwatar da burin Yarjejeniya Ta Duniya. Manufar wannan tsarin gudanarwan shi ne domin tabbacin gudanar da ci gaba kan hana cinkoson ayyukan a madadin Yarjejeniya Ta Dunimaya. Ka yi tunani kan tsarin gudanarwa a matsayin na’urorin haxa kan ayyuka na shirin Yarjejeniya Ta Duniya, yayin da take shirin fadadawa ta hanyar rage cinkoso, wanda ya qunshi aikin miliyoyin mutane a fadin duniya. Cikkaken aiwatar da mafi yawan manufofin Yarjejeniya Ta Duniya,za ta buqaci qoqarin gwamnatoci, hukumomi da sauran kungiyoyi. To amma batun bada kai wajen samar da shugabanci da kuma canji a duniya, da goyon bayan da ake bida zai samu ne kawai gun mutane su kansu. Tsarin gudanarwan, bai kasance kammalalle ba. Majalisar Yarjejeniya Ta Duniya tsakanin kasa da kasa za ta rika sa ido da yin ‘yan gyare-gyare lokaci-lokaci, bisa irin darussa da ake koyarwa game da kokarin aiwatar da Yarjejeniyar a wurare dabamdabam. Majalisar kuwa tana na’am da duk wani bayyani ko goyon baya da ka ke da shi game da su. Tsarin Gudanarwa 1. A fara da Yarjejeniya Ta Duniya:- ka bar Yarjejeniya Ta Duniyar ta kasance muhimmin tsarin da kake

da shi wajen tafiyar da shirye-shiryen ka, da ayyuka da kake gudarwa domin cim ma tabbacin aiki. 2. Kasance abin koyi:- ka yi kokarin zama abin koyi wajen cusa dabi’un Yarjejeniyar cikin aikin ka na yau da kullum, a gida, wurin aiki da kuma cikin al’umma. 3. Qarfafa kanka:- yi aiki gaba gadi, ka kuma kau da shakkan za ka yi nasara a matsayinka na mutum guda, da kuma cewa ayukan ka za su ingiza na mutane da dama. 4. Hada ka:- ka hada kai ka kasance da ikon iya canje-canje,wajen gina dangantaka da hadin kai da sauran mutane, ka kuma bidi yin nasara, da samar da hanyoyin yin nasara. 5. Karfafa wasu:- rarraba aiki, don baiwa kowa daman iya magance matsaloli, daukan shawarwari, da jagoranci, da gudanar da ayukan taimakon al’umma. 6. Inganta halin daraja juna da ganewa:- a tabbatar da gina dangantaka, da daraja juna, daga kungiyoyi ko al’umomi da al’adu dabam-dabam. A kuma iya sasanta rigingimu ta hanyar tattaunawa, don kawo cigaba. 7. Ka duqufa wajen shiryeshiryenka:- ka dukufa wajen bayyana shirin ka karkashin Yarjejeniya Ta Duniya, ba tare da ka jagorance su ba. Domin su cimma burin kaiwa ga kungiyoyin al’umma, har ga cimma nasara. 8. Ba da karfi kan ababan da suka haddasa:- ka bada karfi da tunani kan

manyan dalilan da suke janyo matsaloli da kalubalai da ke fuskantar biladam, kada kuma ka bar ayuka da ke janyo rashin cigaba, ya dauke hankalin ka daga aikin. 9. Ka bada kai, ka kuma saki jiki:- kada ka gaza kan batun mika kai,game da manyan manufofi, ka kuma tabbata cewa matakai da za ka dauka suna dai-dai da manufar Yarjejeniya Ta Duniyaa, amma ka saki jiki,inda akwaihanyoyin cimma nasara hakan na dabam. 10. Ka kasance da basira wajen samar da hanyan aiki:kada ka kyale hakalinka da aikinka ya kasance kan neman kudi ba, ka yi amfani da tunaninka domin ka kasance da basira wajen samar da hanyar aiwatar da aik. 11. Yi amfani da kimiya ciki azanci:- ka fahimci cewa mafi yawan mutane ba su da damar kaiwa ga samun kayayyakin kimiya da suka cigaba. Yayin da kuma za ka yi amfani da kimiya wajen magance matsaloli,ka tabbatar ya kasance dai-dai. 12. Ka kare darajar Yarjejeniya:yayin gabatarwa, ko samun bayyane daga ciki,ko fasarar yarjejeniya Ta Duniyar, ka tabbatar da aminci wajen amfani da kalmomin da ke cikin rubutu na ainihi, ka kuma gama Yarjejeniyar da kungiyoyi kawai,ayuka da ke tafiya dai-dai da dabi’u da manufa. Amincewa Da Yarjejeniya Ta Duniya: Amincewa da mutane da

kungiyoyi suka yi wa yarjejeniya Ta Duniyar, ya nuna ke nan akwai niyyar aiwatar da shirin Yarjejeniyar bisa hanyoyin da suka dace. Amincewan yana nufi har ila yau, bada kai ne ga aiwatar da manufofin yarjejeniyar, da kuma niyyar hada kai da sauran mutane. Akwai wasu hanyoyi da dama, da wadanda suka amince da Yarjejeniyar za su taimaka wajen daukaka manufar shirin Yarjejeniya Ta Duniya. Misali, wata kungiya zata iya amfani da Yarjejeniyar wajen tsarafa ayukan ta, domin su cimma burin nan na Yarjejeniya Ta Duniya, za su iya amfani da ita a fagen ilimi. Rattaba hannu ko amincewa da Yarjejeniya ta Duniya abu ne wanda kowace kungiya zata iya yi. Yarjejeniya Ta Duniya ysakanin kasa da kasa na kokarin tabbatar da kungiyoyin da suka amince da Yarjejeniyar,ECI tana kuma tabbatar da cewa yin hakan ya kunshi yarda cewa za a bayyana mai amincewa a fili a matsayin mai amincewa ko rattaba hannu kan Yarjejeniyar. Bayanai Kan Amincewar: Za ka iya amincewa da yarjejeniya Ta Duniya ta yanar gizo ko kuma ka aika mana da bayannan ma na amincewa. Za ka iya amfani da wannan samfurin. “Mu da muka rattaba hannu,mun amince da Yarjejeniya Ta Duniya. Mun rungumi manufofin wannan rabutacen Yarjejeniyar. Muna alkawarin hada kai ne da sauran kungiyoyi na duniya domin samun amintacciya da jurariyar kasa cike da zaman lumana, mu kuma yi aiki don cimma burori da manufofin Yarjejeniya Ta Duniya. Bugu da kari, ana sa ran mai amincewan zai: 1. Daukaka Yarjejeniya Ta Duniya ba ji ba gani, ya kuma bi tsarin gudanarwa da aka bayyana a sashe na vi. 2. Ka bada naka gudumawa kan aikin Yarjejeniya Ta Duniya, da kuma wasu ayuka karkashin shirin Yarjejeinyar a hanyar da ta fi dacewa. 3. Ka aiwatar da Yarjejeniya Ta Duniya a wurin aikin ka/ki da kuma cikin rayuwarka.

earthcharter. org/invent/ images/uploads/ EarthCharter_ Hausa.pdf


25

A Yau Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

Ko Kun San?

Amfanin Tsamiya A Jikin Xan’adam Daga Yusuf Shuaibu, Abuja

Kamar yadda ya kasan ce sanannen abu ne gurin mu Musulmi, ba wani icen da Allah (SWT) ya halitta face da irin ta sa fa’idar, sai dai ya kasan ce an gano wannan fa’idar ko kuma ba’a gano ta ba. Duk da tsamiya aba ce me tsami amma tana da abubuwa da yawa na qarin lafiya , sannan tana kunshe da sinadaran qara lafiya da kuzari da sauransu. A cikin dukkan kayan marmari tsamiya tana da ingantattun sinadaran iron, magnesium, niacin, phosphrous, protein, da potassium amma me ciwon siga zai yi qoqarin kada ya sha saboda tana qunshe da sikari. Har ila yau tsamiya tana da mahimmanci game da al’ada saboda ingancin abubuwan gina jiki da ta quntsa. Ciwon Mara lokacin Al’ada; Ana haxa tsamiya da man zaitun dan a sha domi maganin ciwon mara na lokacin al’ada dama wanda bana al’ada ba. Ana shan tsamiya saboda kumburin ciki ko rashin bayan gida, ciwon hanta da mafitsara da kuma ciwon ciki. Ana maganin sanyi da zazzavi, akan baiwa yara saboda tsutsar ciki. Akan sarrafa yayan tsamiya don maganin karaya. Ruwan yayan tsamiya na maganin bushewar ido akan disa shi a ido. Wasu daga cikin amfanin tsamiya dai sun qunshi: - Yaqi don hana kamuwa da cutar ‘cancer’. - Kariya daga qarancin sinadarin ‘vitamin c. - Sauqaqa ciwon zazzavi. - Kariya daga kamuwa da mura. - Taimakon jiki wajen narkar da abinci. - Saukaka cushewar ciki. - Ragewa jiki yawan kitsen ‘cholesterol’. - Taimako wajen inganta lafiyar zuciya. - Kurkura ruwanta na saukaka kaikayin makogwaro na mura. - Dafaffen ganyenta na maganin ciwon ‘ulcer’ da taimakawa wajen kashe tsutsar ciki ga yara. - Tana maganin basir. - Taimako wajen tace jini. Kazalika ana iya amfani da ita don magance cututtuka da dama, kaxan daga ciki su ne: •Maruru.

• Tsamiya

•Gudawa. •Amai. •Cututtukan hanta. •Kuturta. •Cututtukan fata. •Ciwon ido. •Guba. Da dai sauran cututtuka. •Amfanin Namijin Goro Namijin goro dai wani nau’i ne na goro wanda akasari ake amfani da shi a kasashen Afrika. Turawa na kiransa da suna “bitter kola” Masana a fannin kiwon lafiya sun bayyana namijin goro da antibiotics mai matuqar amfani ga rayuwar bil’adama. A nazari da aka gudanar dabandaban a sassan Afrika da ma na Turai, an tabbatar da cewa namijin goro na da amfani kamar haka:-

• Namijin Goro

1. Kamar yadda kwararriya a fanin nazarce-nazarce a sashin kiwon lafiya na Nijeriya Natural Medicine Development Agency (NNMDA), Mrs. Chinyere Nwokeke ta tabbatar da cewa, namijin goro yana taimakawa masu dauke da cutar HIV ko kanjamau ta hanyar rage radadi da gubar da cutar ta HIV take dauke da shi saboda sinadarin “antibacterial” da kuma chemical na “Saponin” da yake cikin ta. 2. A wani nazari da masana suka gudanar a sashin horar da likitoci na jami’ar tarayya dake Lagos, masanan sun bayyana kamar yadda aka wallafa a mujallar “Middle East African Journal of Opthamology” cewa, namijin goro na kashe cutar Glaucoma wacce take lalata idanun bil’adama. 3. Har ila yau, masana a fannin kiwon lafiya sun tabbatar da

cewa, namijin goro na maganin cutar cizon sauro wace ake kira da “malaria” saboda sinadarin “kolaviron” da ke cikin ta. 4. Qwararru a fannin nazarce-nazarce a sashin kiwon lafiya na jami’ar Obafemi Awolowo dake Ile’ifi, sun tabbatar da cewa, namijin goro na magance amosanin gabbai (arthritis). Har ila yau, a nashi jawabi Dr. Olayinka O. Adegbehingbe ya jaddada hakan a wani nazari da ya gabatar kuma aka wallafa a mujallar, issue of the Journal of Orthopaedic Surgery and Research, a watan Juli na shekarar 2008. Kwararren ya tabbatar da cewa namijin goro na matukar magance cutar gabobin jikin. 5. Har ila yau, an tabbatar da cewa namijin goro na qarawa maza kuzari.


26

Tare da Rabiu Ali Indabawa 08069824895

A Yau

Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

Daga littattafan Hausa (3) Na’ara ashussa’a daaniyyah wata baiwar Allah ce mai haquri, kuma tanaqaya daga cikin xawayen Zeenatuzzaman a vangaren Bin Adama, mata ce ga wani mutum manomi, ita ce ta karvi Hamdiyatul’aini don shayarwa, har ta kai matsayin ‘ya mace. Ganin haka ya sa ta riqa biyan lada ana koya mata harkokin yaqi da sauran abubuwa na bajinta, domin ta san daga Nahiyar da aka xauko ta, amma a voye ake koya mata ba tare da sanin Zeenatuzzaman ba, saboda a duk sa’ilin da Zeenatu za ta zo sai ta zo mata a suffar mutane, sannan ba ta ta va yarda an bayyana mata daga inda aka xauko ta ba. Wani masani akan qabi’un xan Adam da qwarewa wajen bayar da horon yaqi, wanda kuma ya halarci yaqe-yaqe da dama, wanda ke da riqe da makullan Hadeeqatur rauhaniyyah tsohuwar fadar babban dogarin Sarki Sulvaanil’usfuur, ana kiransa Nuurul’ainaini, shi ne yake ba ta horo, shi kuma an haqiqance cewa in dai ya baka horon yaqi, to sai an sanka a wasu sassa na duniya. Bayan an gamsu da horon da ta samu, sai aka mayar da hankali wajen janye hankalinta ga barin bibiyar qawaye na nesa da na kusa don gudun kada wancananka sirri ya bayyana, ta gane su ne iyayen ta ba, saboda waxanda suke riqe da ita ba su tava nuna mata ba sune iyayenta ba. A l ’ a m a r i n Zeenatuzzaman kenan a gonakin Shahyaalu. Sarki Nuurussabri Al’akabar mahaifin Asadulmuluuk, ne sadauki, yana da tarin dukiya da dakaru majiya qarfi da jarumtaka, kai al’amarin ya wuce kwatance, kai dai ka iya kalonsa daga nesa a marmarce, amma idan ya fito fili, to aikin fa sai jurarre. Adali ne cikin lamarin mulkin da ya ke gudanarwa, ba ka iya jin da qai wani talaka a qasarsa yana kukan yinwa ko abin da ya yi kama da haka. Sa’ilin da Asadulmuluuk ya cika

• Shatan Zazzau Da Makaxansa shekaru ishirin da biyar, kamannin mahaifinsa suka fara bayyana a jikinsa, ga kyau kai ka ce shi ya zava, ga qira irin ta ‘yan mazan jiya ga qarfi kamar zaki a jeji, farin jini kuwa kamar an rubuce masa Suratu Yusufa, iya magana ko Huquba cikin fasihancin kalami wane Imru’ulqaisi, haddar Qur’ani kuwa wane. Hudah-hudah, haquri kuwa kai ka ce damo wurinsa ya gada. Haka ya taso kowa yana haba-haba da shi. sai ya zama a wannan shekara babansa ya yi quduri niyyar wata tafiya zuwa qasar da abokinsa ya ke mulki, wato Sarki Ainunnasruddeen Al’askandari, wanda ya ke sarauta a qasar Masar don yin ziyara. Ya aika masa cewa ga shi nan tafe, zai zo ya yi wata guda. ya faxawa ‘yan aiken idan sun je su zauna, domin tafiyar kwanaki tara ce daga Lardin Tanzeemussalaam zuwa can. Bisa al’adarsa idan zai yi irin wannan tafiya mai nisa ya kan bar babban xansa Abdulwahhab wanda ake masa laqabi da Sulqaan, da kuma wazirinsa su riqe qasar. To da ya ke Asadulmuluuk shi ma ya fara girma sai Sarki ya yanke shawara kan ya yi wannan tafiya da shi, lokacin ya zo dai-dai lokacin da

Sarakuna manya da qanana ke zuwa don kallon kayan tarihi. A ranar xaya ga watan Almuharram tawagar Sarki ta kama hanya, tawaga ce mai kama da ayarin fatake daga nesa saboda mutum xari da hamsin kacal suke cikin tafiyar, wadda idan yaqi za su yi sai su iya gamawa da runduna guda, saboda ko wanne daga cikinsu sadauki ne, kuma dukkaninsu sun halarci yave-yave ba xaya ba, ba biyu ba. Ranar tara ga Muharram suka doshi ga qasar Bahrun Nil, misalin lokacin sallar azzuhur, suka samu jama’ar Sarkin sun zo dan tarbar su, bayan sun yi salla suka xora dawakan su cikin kwalekwale aka qetare da su kogin. Sun samu garin a cike da Sarakuna waxanda suka zo daga qasashe dabandaban, aka ba su masaukai na alfarma kowa ya je ya ajiye kayansa ya xan huta kafin lokacin sallar la’asar. Sun isa ranar Alhamis baban Asadulmuluuk ya ce; “Idan Allah ya kaimu ranar asabar za su je kallon kayan tarihi, sannan ya umarci Asadulmuluuk lallai a cikin wannan dare ya je ya gaida iyayensa wato yana nufin matan Sarki. Da dare ya yi aka haxa shi da wani bawa

ya yi masa rakiya, suna cikin tafiya suna hira sai aka zo wata farfajiya wani wuri mai fili da wasu fitilu masu haske, sai bawa nan ya ce; “Ranka ya daxe wannan hanyar ita za ka yi ta bi za ta sada ka da wata doguwar rumfa, to wannan rumfar ita ce za ta kai ka har wurin da matan Sarki suke hutawa.” Asadulmuluuk ya dube shi ya ce; “Bawan Allah kana sane da kalaman su ke fita daga bakin ka kuwa?” “Ina sane da abinda na ke faxa mana, ai yana yin gidan ne haka, idan ka yi gaba ba zaka rasa wadda za ta jagorance ka zuwa ciki ba.” Ya sake kallonsa ya ce; “Ba ka tunanin ni baqo ne? ni ma fa xan Sarki ne, kuma na san yadda irin gidajenmu suke da sarqaqiya, ba ka tsoron kada in bi wata hanya da zan ga wani abu da bai halatta ba, gidan iyaye na fa zan shiga?” Bawa ya ce; “Ranka ya daxe ai irinmu ba ma wuce nan, duk namijin da ka gani a ciki, to tuni an daxe da fiqiye shi.” Asadulmuluuk ya yi firgigit ya ce; “Fiqiya kuma ajikin xan Adam?” bawa ya amsa “qwarai kuwa fiqiya, babu a masarautar ku ne?” Asadulmuluuk ya yi shiru zuwa wani lokaci sannan ya ce; “Ka jira ni a masauki na idan fito zan nemeka.”


A Yau

Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

nazari

27

Xanbilki: Jagoran Da Ya Tsaya Kan Kariya Ga Manufofin Shugaba Buhari Daga Ibrahim Muhammad

Idan ka xauke harkar Kasuwanci, jihar Kano wata babbar cibiya ce ta siyasar qasar nan, musamman idan aka yi la’akari da irin zaqaquran ‘yan siyasa da take da su tun dauri, irin su Marigayi Malam Aminu Kano, Abubakar Rimi, Sabo Bakin zuwo, Lili Gabari da dai sauransu. Ammani Inuwa da saura da dama da wasunsu suka rigamu gidan gaskiya, amma har yanzu ana cin gajiyar darasin siyasarsu, sai dai mu ce ana kuma ci gaba da sambarka da irin rawar da suka taka. Akwai kuma waxanda suke a raye ake damawa da su, da kuma masu tasowa da har yanzu dake kwaikwayon ayyukansu na alkhairi . Wannan ta sa duk jam’iyyar siyasa da xan takararta ya sami karvuwa ga al’ummar Kano, to ya sami nasarar sa ran samun kaiwa ga nasarar muradinsa, musamman ma takarar da ya tsaya a matakin da yake nema. Babbar manufa ta siyasa ga masu son ci gaba ita ce riqe aqida da tsayuwa qyam a inda kake, duk wuya duk daxi. Saboda manufa da sanin inda aka sa a gaba za ka taras xan siyasa mai aqida bai fiye rawa ba. Abin da nake nufi shi ne, ba zai yarda da mutum a matsayin wanda yake bi a siyasa ba, sannan kuma ya juya masa baya idan ba a kai ga nasara ba. Ba ma a siyasar baya ba ma da tarihi ba zai tava mantawa da wasu zaqauran Mutane a zamanin NEPU da PRP da su ne jam’iyyun da suka yi fafutuka akan talaka ya sami sa’ida a zamantakewarsa ta yau da kullum a lokacinsu. A wannan loton ma, akwai xaixaikun mutane da suka biyo sawu da tsayuwa kyam akan aqida. A wannan lokaci, da ake ganin jama’a da dama sun kauce wa siyasar tsayawa akan aqida akwai xaixaiku da koyaushe suke qyam akan manufa ta son ci gaban talaka. Ga wanda yake biye da yadda siyasar take a jihar Kano, tun daga soma shiga harkokin siyasar Shugaban qasa Muhammadu Buhari, ba zai rasa jin sunan Abdulmajid Xan Bilki ba, Wanda ake wa laqabi da Kwamanda. Ba don komai ba saboda yadda ya tsaya ba dare ba rana wajen nuna qauna da biyayya ga manufofi da aqidu irin na Buhari. Tun soma fitowar takarar Buhari Kwamanda yake faxi-

tashin ganin ya kai ga gaci a wannan muradi nasa na sanya qasar nan a turba ta mulkin da zai amfani ci gaban al’ummar qasar nan. Da ma ita siyasar kuxi ko mulki ba ta sa ya sauya daga ra’ayin da Xan Bilki yake da ita ta yarda da Muhammadu Buhari ba, ya tsaya qyam bai tava yin rawa ba, tun tasowarsa a tafiyar siyasar Muhammadu Buhari, duk inda ya sa qafa anan Xan Bilki yake ya sauke tasa. Wannan ya nuna irin yarda da riqo da ya yi da irin manufofi na Buhari da ya yi a lokacin da Buhari ya zo Kano yana jam’iyyar ANPP da babu ita yanzu, ya zame wa jam’iyyar ANPP nasarar kafa Gwamnati a jihar albarkacin irin qauna da al’ummar Kano suke yi wa Buhari, duk da qarfin mulki da aka sami rashin fahimta da Buhari da Gwamnatin wancan lokacin, duk da qarfin iko da dama ta mulki, da zai iya anfanar Gwamnati, amma Alhaji Abdulmajid Xan Bilki Kwamanda bai bi Gwamnatin ba, bai damu da zaqin Gwamnati ba, ya kauda kansa ya tsaya akan aqidar siyasar Muhammad Buhari ya jure duk tsangwama da hamayya da aka yi masa a kowane mataki. Tun farkon fara siyasar da Muhammadu Buhari ya yi ta shiga cikin tsohuwar Jam’iyyar da ya soma yin takarar neman shugabancin qasar nan a qarqashin inuwarta, wato ANPP Abdulmajid Xan Bilki Kwamanda yake tare da shi ko bayan an yi zave, bai tava barin mara wa Muhammadu Buhari baya ba. Kullum maganarsa ta goyon baya ne ga Buhari da kyakkyawar niyya, da sa ran kaiwa ga nasara domin tabbacin da yake da ita na sanin dukkan nasara daga Allah take. Akwai mutane da dama da aka taho ana wannan tafiya da su da suka rasa irin wannan yaqinin, sai ma suka qaqu suka riqa ja da baya, wasu suka bar ma tafiyar, ta yiwu dama sun zo ne da niyyar su fake da Buhari in an sami kafa Gwamnati su sami cimma wani buri nasu, amma sai suka nuna kansu tun kafin akai ga gacin da ba su yi zato za a kai gare shi ba. In banda irinsu Abdulmajid Xan Bilki, wanda dama burinsu na kawo sauyi ne na samar da ci gaba ga al’umma, musamman ma talakawa, don haka bai ma tava tunanin zai bar tafiyar Muhammad Buhari ba. Kusan kowa, ba a jihar Kano kaxai ba, a duk faxin Arewacin qasar nan in aka ambaci sunan

•Alhaji Abdumajid Kwamanda Abdulmajid Xan Bilki Kwamanda abin da zai soma tunani shi ne Buhari, saboda saninsa da tsayuwa, qyam akan mara wa tafiyar Buhari baya. Domin yardarsa da siyasa ta manufa da aqida dan tallafa wa ci gaban talaka ba tare da son rai ba. Abdulmajid Xan Billing Kwamanda, a lokacin da shugaban qasar yanzu Muhammadu Buhari suka kafa jam’iyyar CPC Xan Bilki na daga cikin sahun farko da suka shiga suka riqa tallata manufofinsa, duk kuwa da ba a kai ga nasara ba, amma wannan sam, bai sagewa kwamanda qafa ba. Shi ya sa duk wanda ya san Xan Bilki ya san shi ne a masoyi na amana ga Buhari. Ko lokacin da aka samar da jam’iyyar APC dama yana tare da Buhari. A lokacin da wasu suka gaza saboda sun fidda tsammani daga ikon Allah, amma Xan Bilki yana daga sahun farko da bai tava jin gazawa ko qosawa akan marawa Buhari baya ba. A haka ya ci gaba da yaxa manufofin Buhari da har ta kai ga cikar Burin da suka sa a gaba na cimma nasarar da aka samu na lashe zaven shugabancin qasarnan a zaven 2015 da Buhari ya yi. A wannan fage na riqe aqida da manufa da jajircewa ta tsayawa qyam akan goyon baya ga Muhammad Buhari, za a sa shi a sahun gaba-gaba cikin sahun farko wanda sai dai a biyo bayansa, domin ya sadaukar da lafiyarsa dukiyarsa da lokacinsa har sai da haqarsu ta cimma

ruwa, kuma har zuwa yau xin nan yana kan wannan manufa ta a ga an tallafa. Duk wannan gwagwarmayar siyasa da Abdulmajid Xan Bilki Kwamanda ke yi, hakan kuma ba ta hana shi tausaya wa da taimakawa wajen gina al’umma da abin da Allah ya huwaye masa ba. Domin taimakon mutane a dunqule ko xaixaikunsu yana daga cikin abin da ya sa a gaba, sannan a wani vangaren yana ta qoqari wajen sama wa matasa ayyukan yi a ma’aikatu da hukumomi daban-daban tare da taimaka wa al’umma. Shi ya sa ma wasu suke jin haushin irin rawar da yake takawa wajen tsage gaskiya kuma suke ganin zai hanasu rawar gaban hantsi. Don haka suke binsa da kalaman vata suna, suke son ganin bayansa, kamar yadda wani cikin makusantansa ya shaida min. Sannan kuma shi jagora Abdul’majid Xan Bilki Kwamanda ba wanda za a yi wa barazana ba ne da vata suna da qazafi, shitsayayye ne da ya dogara da Allah, duk da xauri da aka yi masa a baya da abin da ake masa a yanzu ba zai sa ya ja da baya wajen kare manufofin Gwamnatin Shugaba Buhari ba wacce suka kafata saboda a samu cigaba. Kullun Xan Bilki yana tabbatar wa da ‘yan qasa irin qoqarin Gwamnatin Buhari wajen inganta tsaro, yaqi da masu wawashe dukiyar al’ummar qasa da kuma inganta harkar noma da ake ci gaba da samun nasara akai.


28 NAZARI

A Yau Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

Alamomin Gane Masoyiya Ta Gaskiya

A lokacin da kake qoqarin gano matsayin ka a zuciyar budurwarka shin tana son ka ko akasin haka da akwai buqatar ka nazarci wasu abubuwa waxanda wasu sun kasance waiwaye ne wasu kuma suna kan faruwa. Farkon haxuwar ku. A yayin gabatar da soyayyarka gare ta ka yi amfani da salo ne mai qarsashi wato sai da ka gama jan hankalinta da ra’ayinta a kan ka sannan ka bayyana a gare ta da lamari na soyayya? Furta kalaman amince wa na soyayya ga wanda suke so abu ne da mata suke jin qunyar furta wa a karon farko ga samarin na su, sai dai duk da haka zata nuna maka alamun tana son ka kuma zata nuna maka wasu alamomi da suke nuni da so. Salon da kake bi wajen gudanar da soyayyar ta ku shi ne sikelin auna ci gaba ko ci bayan soyayyar ta ku, misali a lokacin da kuke tsaka da soyayya sai ta samu wani da ya fika iya kalaman soyayya da barkwanci da rashin yawan mita da dai duk wani salo mai burge wa to babu shakka zai iya xauke hankalinta da ga kan ka, sai dai ta tsaya da kai dan kuxinka. A saboda haka akwai buqatar ka kasance mai sabunta salonka na soyayya tun daga kan kalamai da yanayin yadda kake bata kulawa da sauran su lokaci bayan lokaci. A dukkan lokacin da ka buqaci mace ta baka amsar amince wa tana son ka sai ka ga ta yi murmushi ko ta kasa furta hakan a karo na farko to hakan yana daga cikin alamu na so domin kuwa wanda ake so ake jin kunya. Karda ka damu da sai ta furta maka kalmar tana son ka kai dai lura da waxannan abubuwa kamar haka: Sau nawa kake kira kafin ta amsa? Idan har da so zata amsa

a kira na farko idan kuma bata amsa ba zata amsa a kira na biyu har ta baka uzurin da zaka gamsu na dalilin rashin amsa kiran, idan har bata amsa a kira na biyu ba sai ka bar kiranta haka idan har da so zata kira ka da zarar ta ga kiranka da ta rasa har ta baka uzurin kare kai. Matuqar tana son ka za ta kasance mai karvar shawarar da duk ka bata kuma za ta kasance mai son abun da kake so. A duk lokacin da ka je wajen ta zance za ta fito cikin farin ciki kuma ba zata nuna qosawa da jin firarka ba matukar ka iya zance har zuwa lokacin da za ku yi sallama. Idan har ka saba kiran ta a waya matuqar ta damu da kai, idan ka kwana biyu baka kira ta ba to za ta kira ka ta ji ko lafiya, idan ma bata kira ba saboda wani dalili bayan ka kira za ta yi kalamai na nuna ta yi kewar ka. Idan har tana son ka a kullum za ta ke qoqarin yin abun da zai faranta ranka, za ta qoqarin guje wa abun da zai sa ka yi fushi. A lokacin da soyayyarku ta yi nisa zata iya bayyana maka wasu sirrikanta da suka shafe ta. A lokacin da ka nuna vacin ranka a kan wani abu da ta aikata da ba dai-dai ba, a yayin baka haquri da shawo kan ka za ta iya zubar da hawaye. Zata qoqarin bayyana ka ga qawaye da kuma ‘yan gidansu. Zata ke qoqarin turo maka da kalamai na soyayya. Zata kasance mai tambaya a dangane da ‘yan’uwa da kuma abokanka da ma dai duk wani da ta san kuna a tare. Za ta ke damuwa da damuwarka. Irin waxannan abubuwa da sauran ire-iren su duk zai kasance ta na nuna maka su.

Yanayinta Da Kuma Halayyarta Akwai buqatar ka fahimci yaya yanayinta da kuma halayyarta suke, shin tana da jan aji ne da yawa? wanda hakan ka iya sawa ko tana son ka ba zata amince da kai a karon farko ba har ma za ta iya yin wasu abubuwa da zaka iya tinanin wulaqanci ta yi maka, amma da sannu matuqar ka iya allonka za ka wanke. Tana da kunya ne? ta yadda ba za ta iya sakin jiki da kai ba a karon farko kuma bayan tana son ka, idan ka yi haquri da sannu soyayyarka za ta cire mata wannan kunyar da take ji a kan ka domin kuwa idan aka juri zuwa rafi da sannu tulu yake fashe wa. Koda a ce bata da son kuxi farkon soyayyarku sai ya kasance ka fara yi mata kyaututtuka to da sannu idan ka matsa da yi mata kyauta son abun hannunka zai rinjayi son da take yi maka na gaskiya, an dai kuma ce kyauta tana qara soyayya, amma kuma komai ya yi yawa to zai kawo matsala. Shawara Ga Samari ‘Yan Soyayya 1. Yi ammafani da kalaman soyayya masu daxi da inganci a lokacin da kake gwagwarmayar samun amincewar zuciyar dukkan wata yarinya da ka gani kana son mallakarta. 2. Kasance mai lissafawa tare da tauna dukkan wata magana kafin ka furta ta ga masoyiyarka bayan ta nuna maka amincewarta a soyayyarka. 3. Karda ka kasance mai takura wa tare da matsantawa a kan dole sai ta yi wani abu da ta nuna maka bata son yi a zahiri ko ta nuna maka alamun hakan, domin kuwa hakan zai sanya ta fara gajiya tare da kosawa da

kai. 4. A dukkan lokacin da kake son ta yi maka wani abu to ka gabatar mata da bukatar ka cikin siyasa da zolaya amma idan ka nuna mata dole to kuwa ba zaka samu yadda kake so ba idan ka samu an yi ma kenan. 5. Kasance mai yin dukkan wani abu da ka san zai faranta mata ka kuma guji yin dukkan wani abu da ka san zai kuntata mata. Yi mata kyauta a lokacin da bata zaton samun hakan daga wajen ka, yin hakan zai sanya ka burgeta zai kuma qara sanya soyayyar ka a cikin zuciyar ta. 6. Karda ka cika yi mata kyautar kuxi ko bata wasu abubuwa barkatai domin kuwa yawan yin hakan zai sanya ka kasa banbance cewa soyayyar gaskiya take yi maka ko kuma kuxin ka take so. 7. Mace ba ta son takura, ba ta son kafiya, da maimaita mata abu xaya, kuma ta son ka cika kushe wani ko wata a gabanta. Haka zalika ba ta son a duk lokacin da kuke tare ka riqa nuna kulawa ko fifiko ko nuna wata ta fita kyau ko wani abu makamancin haka. Mata suna son ka riqa yabon kyawunsu. 8. Sannan ka kasance mai bayyana mata cewa ita kyakkyawa ce a duk lokacin da kuka yi waya ko kuma kuke tare, ka riqa bayyana mata cewa muryarta na da daxi sosai, kana samun nutsuwa a duk lokacin da ka ji sautin muryarta, ka nuna mata cewa ta iya kwalliya kuma tana da tsafta. 10. A duk lokacin da kuka haxu a hira a waya ko a zahiri ko saqo ka tura mata to lallai ka bayyana mata kana sonta kafin ku rabu.


A Yau

RAHOTO 29

Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

Gwamnatin Buhari Ta Gyara Qasar Nan –Zainawa Daga Ibrahim Muhammad, Kano

An bayyana amsa kiran al’umar qasar nan da Shugaban qasa Muhammadu Buhari ya yi na amincewa ya sake neman takarar shugabancin qasa a 2019 amsa addu’a ce da Allah ya yi ga mutanen qasar nan. Wani jigo a Jam’iyyar APC a jihar Kano, Alhaji Murtala Alasan Zainawa ya bayyana haka a wata zantawa da ya yi da wakilinmu a wannan makon a Kano. Ya ce, wannan amsawa wata addu’a ce da mutane masu yi wa Nijeriya fatan alheri suka yi. Kamar yadda Shugaban qasar a baya ya yi rashin lafiya aka fito a wajen ibadoji na Musulmi da Kirista suka yi addu’o’i, kuma Allah ya ba shi lafiya har yake ayyuka na farfaxo da qasar nan daga durqushewa. Alhaji Murtala Alasan Zainawa Ya kuma yi nuni da cewa kafin zaven Buhari a 2015 qasar nan ba ta san inda ta dosa ba, musamman kan matsala harkar tsaro,ilimi, tattalin arziqi da zamantakwarta, amma da zuwan Buhari ya dawo da qasar kan tsari. Ya ci gaba da ce wa abubuwan da ke faruwa na waxanda suka yi ganima da dukiyoyin qasa

da yadda ake kamasu dukiyar take fitowa, saboda an yi wasoso an maida arziqin qasa kamar kayan gado a baya. Ya ce idan da wani ne yake mulki ba Buhari ba, da wannan badaqala ba za a ji ta ba, da ‘yan Nijeriya ba su san abin da yake faruwa na sace dukiya da ake a qasar nan ba. Zainawa ya ce irin biliyoyin kuxaxe na qasar nan da aka xiba duk mai tausayi in ya ji sai ya yi Allah-wadai ,amma da yake Allah yana son qasar nan da rahama ya kawo Buhari ya zama shugaban qasa, wannan na daga dalilai da ya tona asirin masu kwashe dukiyar qasa. Ya ce ‘yan Nijeriya ba za su gane tasirin mulkin Buhari ba sai nan gaba. Dan haka ya zama wajibi a gode wa Allah kan zaman lafiya da aka samu a halin yanzu, Wanda a baya idan mutum zai je kasuwa ko wajen ibada ko makaranta abubuwa sun kusa gagara, abokai da yan’uwa kowa a tsorace yake. Sai Allah ya dubi zuciyar al’umma ya kawo zaman lafiya sanadin zuwan Buhari. Alhaji Murtala Alasan Zainawa ya ci gaba da bayyana ce wa masu cewa Buhari ya gaza, to sun jahilci ikon Allah, don Buhari ya tsaya zave sau

• Shugaban Buhari

uku sai a na huxu ya ci, wanda suke ganin ba zai sake cin zave ba a halin yanzu daqiqai ne, da ba su san ikon Allah ba. Alhaji Murtala ya ce quncin rayuwa da ake aka a kai akwai qasashe irinsu Nijar, Libiya, da Siriya da suke cikin quncin rayuwa da ya fi wannan, duk sai a ce wani ne ya kawo? “Daxi da wahala duk Allah ne ke kawowa, yayin da ka ce wani ya sakaka a daxi ko wahala, to akwai rashin yarda da cewa

Allah ne ke bada komai”, in ji shi. Alhaji Murtala Alasan Zainawa ya kuma ce lokacin da Buhari ya karvi qasar nan, da Gwamnatin Jonathan ce ta wuce, da ba a san makomarta ba a yanzu. Ya ce yanzu Buhari ya zo yana aikin gyaran qasa ne, zafin da ake ji na gyaran varna ce da Gwamnatocin baya suka yi. Alhaji Murtala Alasan

Zainawa ya ce idan har ‘yan Kudanci da Yammacin qasar nan za su yaba wa qoqarin Buhari, bai kamata a ce ‘yan Arewa Hausa/fulani su faxi laifin Buhari ba. Ya warfare da cewa waxanda suke faxan maganganu kan Buhari, to ba sa kallon abin da yake yi na daidai sai a karkace. Don haka su sani, shi mulki na Allah ne kuma shi ya baiwa Buhari kuma zai sake tabbatar masa a karo na Biyu.

Jihar Kano Ta Yi Bankwana Da Cutar Polio – Dakta Muhammad Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

Jihar Kano na bikin murnar cika watanni 45 ba tare samun rahoton vullar cutar polio ba a qananan Hukumomin Jihar 44, Babban Sakatare a Hukumar kula da lafiya a matakin farko na Jihar Kano Dakta Muhammad Nasir Muhammad ne ya bayyana haka a lokacin Qaddamar da shirin allurar rigakafin cutar ta Polio na watan Aprilun shekarar 2018 a qaramar Hukumar Wudil dake Jihar Kano. Dakta Muhammad Nasir Muhammad yace wannan nasara ta samu ne bisa jajircewar masu ruwa da tsaki a cikin harkokin yaqi da wannan mummunar cuta mai kassara qananan yara, saboda haka sai bayyana gamsuwarsa bisa aikin haxin guiwar da ake gudanarwa, musamman Gwamnmatin Jihar Kano, qungiyar ci gaba a duniya da

kuma Masarautar Kano bisa samun wannan gagarumar Nasara wadda ya yi fatan xorewar ta. Dakata Nasir Muhammad ya buqaci mata masu rainon ciki da su tabbatar da ziyartar cibiyoyin lafiya domin karvar alluran rigakafi tare da adana katunan alluran nasu. Hakazalika Dakta Muhammad ya hori al’umma dasu yi qoqarin kiwon lafiyarsu ga cutuka masu yaxuwa ta hanyar tabbatar tsaftar muhalli da abinci tare da kwanciya a wuraren da ke da wadatacciyar iska domin kaucewa kamuwa da cutar Sanqarau. Yace haka zai tabbata ne idan aka tabbatar da tsafta yara tare buxe tagogi domin watayawar iska. Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II na bayar da kyakkyawar kulawa wajen yaqi da cutar ta Polio, inda sarkin ya bayar da umarnin ga dukkan Hakimai, Dagatai da masu unguwanni

domin tabbatar da cewa ana kai yara wajen allurar rigakafin cutar Polio a kowane lokaci. Domin tabbatar da samun nasarar yaqi da cutar

ta Polio Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi II ya bayar da umarnin gabatar da rahoto daga dukkan hakiman Kano kan nasarar allurar polio da

kuma qididdgar yaran da aka Haifa da waxanda akayi vrinsu domin samun tabbacin yadda za’a ci gaba tunkarar abubuwa.


30 TALLA

A Yau Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)


31

A Yau Asabar 14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

Qasashen Waje

Tare da Rabiu Ali Indabawa 08069824895

Mugabe Yaqi Fice Wa Daga Gidan Gwamnatin Qasar Tsohon shugaban qasar Zimbabwe Robert Mugabe yaqi fice wa daga fadar shugaban qasa watanni biyar bayan kauda shi daga karagar mulkin qasar. Mai magana da yawun fadar shugaban qasa, George

Charamba ya ce har yanzu tsohon shugaban yaqi kwashe kayan sa daga fadar shugaban qasa. Charamba ya ce ba wai suna buqatar korar tsohon shugaban ba ne, amma dai bisa qa’ida ya dace a ce ya bar

gidan tunda an samu sabon shugaban qasa. Mugabe ya kwashe shekaru 37 yana jagorancin Zimbabwe har zuwa lokacin da ya’an jam’iyyar sa ta ZANU PF suka yi bore, suka kuma kauda shi daga mulki.

Jam’iyyar MPN Ta Fice Daga Qawancen James Comey Ya Caccaki Jam’iyyun Da Ke Mulkin Qasar Nijar Shuga Trump A Littafinsa Shugaban jam’iyyar MPN Kishin Kasa Ibrahim Yacuba kuma tsohon ministan harkokin qasashen waje na Nijar har ya zuwa jiya da ya bar aiki ya yi wa Manema labarai qarin bayani kan ficewarsu daga qawancen jam’iyyun da ke mulkin qasar. A cewarsa duk lokacin da aka yi zave sulhu a ke yi da mutane amma kundin tsarin zave da gwamnatin qasar ta nace a kai, wai bashi da niyyar yin sulhu. Baicin haka kundin ya qunshi wasu matakai da za su kawowa qasar matsala nan gaba. cewar Malam Yacuba kwanciyar hankali a kowace qasa ya ta’allaka ne kan yaddar da jama’ar qasar ke da shi a zaven sugabanninsu. Sun kira a yi sulhu, a samar da kundin zaven da kowa ya yadda da shi domin bunqasa Dimokraxiya. Jam’iyyar ta ce daga rana

ta jiya da ministocinta suka ajiye mukamansu, ta fita daga gwamnati kuma bata marawa gwamnatin qasar baya. Ficewar jam’iyyar ba wargi ba ne ba kuma da gangan suka yi ba saboda jagoranci babban nauyi ne da al’umma ke bayarwa Allah kuma zai

tambayesu abun da suka yi da amanar da aka basu, inji Yacuba. Sai dai wani jigo a jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulki Alhaji Asumanu Muhammadu ya qi ya yi magana amma ya bada shawarar a jira nan gaba a ji bahasin koli na jam’iyyarsu.

Magoya bayan shugaba Donald Trump, suna shirin maida martani ta yanar gizo kan littafin tarihin rayuwar James Comey, da tsohon darektan hukumar ta FBI ya rubuta. Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar Republican, jiya Alhamis, ya kaddamar da wani shafi a internet da suka lakabawa suna LyinComey. com, wadda a ciki suka wallafa kalaman fitattun ‘yan jam’iyyar Democrat suna sukar tsohon darektar na FBI a lokutan baya. Jam’iyyar ta Republican tana da niyyar bibiyar sahihancin littafin, kuma ta yi amfani da shafin wajen nuna kare-rayi da

sabani da ke cikin littafin, kamar yadda tashar talabijin ta Fox ta bada labari. Littafin na Comey mai suna “A Higher Loyalty: Truth, Lies and Leadership, da turanci, ranar Talata mai zuwa ake sa ran fara sayar dashi ga al’umma. Kamfanin dillancin Labarai na Associated Press ya ce, Comey ya caccaki Trump, a zaman mutumin da bashi da da’a, wanda ba ruwansa da fadin gaskiya. Ya kwatanta shugabancin Trump,mai dogaro ko gudana kan tinkaho da jiji-da-kai da kuma biyayya sau da kafa kan gaskiya da kariya.

Mahukumtan Iran Sun Kame Wasu ‘Yan Canjin Qasar Su 12 Mahukuntan Iran sun kame a kalla mutane 12 da ke harkan hada-hadar kasuwancin kuxaxen qetare a qasar. Ana zargin waxannan mutanen ne dai da kasuwancin da kuxin qasar ta hanyar data sabawa doka. An yi wannan kamen ne domin xaukar matakin ganin darajar kuxin qasar bai zuve ba idan aka kwatanta martaban sa da dalar Amurka.

A cikin wani rahoton da kanfanin dillacin labarai na qasar, ISNA, ya wallafa a jiya Laraba, ya ambato babban sufetan ‘yan sandan birnin Tehran, Hosseini Rahimias, na cewa an tsare waxannan ‘yan kasuwan su 12 ne a babban birnin qasar domin samunsu da kokarin yiwa kasuwancin kudin qasar zagon qasa. Rahimi ya ce an kwace wasu adadin kuxin da bai bayyana

ko nawa ne ba daga hannu su kuma aka kulle shagunan su na hada-hadan kuxaxen qasashen waje har 16, duka a matsayin matakin da hukuma ke xauka akan su. Darajar kuxin Rial na qasar Iran dai, a cikin satin da ya gabata ya faxi qasa inda dalar Amurka daya aka sayar da it rial dubu 60 a kasuwar bayan fage, kamar yadda kanfanin dillacin labarai na Reuters ruwaito.

Qasar Dimokraxiyar Kwango Ba Za Ta Halarci Taron Neman Mata Tallafi Ba Yayinda masu bada tallafi ko gudumawa na qasa da qasa suke shirin zasu hallara yau jumma’a a birnin Geneva, domin yin wani babban taron neman gudumawa da Majalisar Xinkin Duniya, MDD, ta shirya domin agazawa qasar Jamhuriyar Demokuraxiyyar Kwango, gwamnatin wannan qasa da ke yankin Afirka ta tsakiya, wacce Allah Ya yi wa albarkatun ma’adinai tana kan bakarta cewa ba zata halarci taron ko ta bada haxin kai kan taron ba. Wakiliyar Muryar Amurka Anita Powell, ce ta aiko mana da wannan rahoto daga Johannesburg.

MDD ta ce fiye da yara miliyan biyu suke fuskantar barazanar mutuwa saboda matsanancin rashin kayayyakin abincin gina jiki. Wani mai baiwa shugaban qasar shawara Patrick Nkanga, ya gayawa MA cewa, gwamnati bata amince da yadda aka shirya taron neman gudumawar ba, kuma tilas ne a mutunta diyaucin qasar. Ya qara da cewa dagan-gan wadanda suka shirya taron suka gabatar da yanayin da kasar take ciki da nufin zubda mutuncin qasar. Ya ci gaba da cewa an gaza cika

sharuddan da gwamnatin kasar ta gindaya domin taron. Mr. Nkanga ya ce baki daya makasudin taron kamar yadda wadanda suka shirya taron suka gabatar bai yi dai dai da har gwamnatin qasar za ta bada hadin kanta ba. Sai dai majami’ar Catholika a qasar bata goyi bayan gwamnatin kan kin halartar taron ba. Har aka ji wani babba a darikar a birnin Kinshasa yana gayawa mabiya cocin a ranar Lahadi cewa, “Ba zamu ki agaji ba yayinda muke zaune hannu banza bamu da komai.”


14.04.18

AyAASABAR U LEADERSHIP Don Allah Da Kishin Qasa

www.leadershipayau.com

14 Ga Afrilu, 2018 (27 Ga Rajab, 1439)

QASASHEN WAJE

Mugabe Yaqi Fice Wa Daga Gidan Gwamnatin Qasar

JARIDAR HAUSA TA FARKO MAI FITOWA KULLUM A NIJERIYA

Leadership A Yau

LeadershipAyau

No: 031

N150

> Shafi na 31

Muhimmancin Haquri A Rayuwa Idris Aliyu Daudawa

H

aquri wani abu ne wanda ake buqatar mutum ya sa tawali’u, dauriya juriya, da rashin damuwa a ransa, musamman ma idan yana buqatar mallakar wani abu a rayuwarsa, ya jira sai yadda hali ya yi, wato shi duk yadda Allah ya yi, babu wata damuwa. Ba wai sai ya ce shi dole sai ya samu wani abin da ya sa a gabansa ba, wanda shi kuma a wannan lokacin yake son sai ya kai ga mallakar, ko kuma ta halin qaqa duk ya tashi ya damu kansa har ma ya damu na wasu. Bayan kuma Allah maxaukakin sarki ya yi mana horon da mu riqa yin haquri a kan al’amuran rayuwa, saboda duk yadda ake cikin tsanani , sauqi fan a nan zuwa, saboda sai an yi haquri kafin a samu cim ma buri, ai an haxa da haquri kafin a samu nasara a dukkanin abubuwan da aka sa gaba, gaggawa dai kowa ya san aikin Shaixan ce, saboda duk wani abin da aka yi shi cikin gaggawa, ba kasafai ake cim ma wani buri mai amfani da gamsarwa ba, daga qarshe kuma ana yin da-na-sani ne wadda qeya ce kowa ya sani, a kuma baya take. Ba kowa ba ne yake iya zama shugaba, duk yadda aka yi sai wani ya sa haquri tukunna, idan kuma haka mutum ya xaukar ma ransa, zai daxe yana shan wahalar rayuwa ta duniya, domin bai san yadda Allah ya tsara ma shi a rayuwa ba. Haquri baya vaci kamar yadda marigayi Alhaji Adamu Xanmaraya Jos ya bayyana cikin wata waqarsa, wadda yake cewa ‘’Haquri ba ya vaci haquri abin Manzon Allah, in mutum ya cuce ka, in mutum ya zage ka, sai ka bar shi da ya Allah, tun da Allah shi yay yi shi, kuma Allah shi yay yi ka, sai ka bar shi da ya Allah, sakayya na gun Allah. Sau da yawa a rayuwa abubuwa da dama suna faruwa, idan ma mutum ya dubi yadda Allah ya halicci ‘yan yatsun hannun shi,

idrisdaudawaaliyu@gmail.com ai wannan ma ya isa ya kasance wani babban misali, kuma wani wa’azi ne wanda mutane ya dace ace, tuni sun fahimci hakan, to amma ina ai ba duka ne suke tunanin hakan ba. Idan yana son ya mayar da duk yatsun hannun su kasance dogaye, ko kuma gajajjera ai da yayi hakan ba tare da yin shawara da wani ba. Ya kuma fi mu sanin halin kowa, shi yasa yake ba kowa duk abin da ya ga ya fi dacewa da shi. Duk abin da mutum ya ga Allah subhanahu wata’ala ya ba shi, shi ya ga ya fi dacewa da shi, duk wata maganar ma da zai yi , ta ko abin bai burge shi ba, wannan kuma ba za ta yi ma sa wani amfani ba. Ai dama shi tagumin mutum dama baya wuce havar shi. Halin da ake ciki yanzu rashin haquri shi ne ya mamaya yawancin wasu al’amura na rayuwar wasu, saboda su ba su san a ba su haquri ba, ko kuma su ga lalle ya kamata su yi haqurin, idan muka dubi misali idan jarabawa ce aka yi a makaranta, kowa akwai abin da Allah yake ba shi, ba kuma dole ba ne, ya yi dai dai da na wani ba. Koda kuwa ita amsar jarabawar ce aka rubuta akan Allo, wani ba zai iya juya ba, koda kuwa an ma ace ma shi ya juya xin, a ce ma amsar ce aka rubuta. Wani zai samu digiri mai daraja ta xaya, wani ta biyu wadda take sama, sai kuma wadda take qasa-qasa, akwai digiri mai daraja ta uku, sai kuma na qarshe ana kiran shi (Pass) amma abin ba wani yabo bare fallasa dangane da shi sakamakon, haka ne da dace da shi, sai kuma na qarshen shi gaba xayan ma bai tare da wata nasara, sai dai rashinta. To haka abin yake a rayuwa bama sai kawai a makaranta ba, rayuwa ta yau da kullun tana buqatar yin haquri, tsakanin mata da miji akwai buqatar a riqa yin haquri, idan aka ce babu shi, to za a daxe ana kasancewa

cikin matsala har akai ga yin zaman manja da doya, idan ma ba sa’a aka yi ba to shi auren ba zai yi wani nisa ba, sai an samu rabuwa. Idan muka kalli shi al’amarin shugabanci muka kuma kale shi ta ko waxanne vangarori na rayuwa , za mu iya gane cewa matsaloli na tasowa, a duk lokacin da wata maganar da ta shafi zave ta taso, ba fa kowa ba ne yake kasancewa shugaba ba, watakila ma shi mutum bai da masaniyar, sai yayi shugabancin ba, koda kuwa na shugaban masu share kasuwa ne, idan dai ba a son shi fa, to bafa a son nasa ke nan , duk yadda, zai yi sai dai yasa haquri, idan kuma yaqi to sai ya haxu da ikon Allah, wanda sai ya girgiza shi watarana , duk kuwa yadda yake ganin shi al’amarin. Amma ka wai hakanan, sai kaga wasu suna ta kai gwauro su kai mari muddin dai, wata maganar shugabanci ta taso, wani shi yana iya yin har ma abin da bai dace ba, yana iya yi, saboda dai kawai a riqa kiran shi da sunan shugaba, koda kuwa na masu sharar

Baqon Baqon Marubuci Marubuci

08065683849

kasuwa ne, abin Allah ya daxe da tarfa wa garin shugabanci ruwa. Sai kaga ana ta tada qura, wasu ma har su kai ga kauce hanya suke yi, basu ko tunawa da shi wannan bawan Allah wato haquri, idan ka ga ma wanda ke yin shi sai a riqa ce mai, idan bai yi sa’a ba, har ma sai duniyar ta kai ga kware mai bai san halin da ake ciki ba, ko kuma ya kasance kamar ya rako wasu duniyar ne, su suna tatsar nono, shi kuma ya riqe masu qahon. Haquri shi ne wanda idan aka yi juriyar yin shi watarana sai dai kawai mutane su riqa maganar Allah sarki dubi wane don Allah sai kace ba shi bane wane xan gidan wane, da shekarun baya ba, ya shiga cikin kwata ko kuma ya faxa manja ya kuma vare ma shi, amma kuma da ya yi haquri, yau ga shi, ya zama wanda kowa yake son yin hulxa da shi. Amma shi kuwa xan’uwan xayan wanda ya biye ta wasu, yana ganin shi bai sanwata maganar haquri ba, shi ma xin bai wuce watarana a wuce da shi yayi wani abin faxin saboda, ya sa rashin haquri a zuciyar

shi, sai yayi yadda wane da wancan suka yi, yaya za ayi ace kamar shi har su wane ake maganarsu, amma shi ba ma wanda ke maganar shi, da haka ne wasu suna iya ganin abin kamar da wasa yake yi wato ita maganar daya furta, to ashe shi bada wasan yake yi ba, sai ya kai ga aikata abin da, ko abubuwan da ba shi kaxai zai shafa ba wato shi kanshi sai kashin kajin, ya kai ga shafin shi ,sai mutane da yawa, ba don komai ba, sai saboda yayi watsi da haquri ne, ya rungumi shi rashin haqurin. Duk idan rashin haquri ya haxu da qarya saboda ai dama gidansu xaya ne, suna kuma haxuwa sosai, saboda kamar nau’in turaruka ne, akwan waxanda za a haxa, qamshin abin ba a cewa komai, akwai kuma waxanda za a haxa sai kawai aga mutane suna ta toshe hancinsu saboda wari. Akwai kuma wadda take taka masu baya wato son zuciya, wadda ita ta kasance ne tamkar daddawa, gishiri , maggi kai har ma da Onga wajen tallavo hankalin wanda dama shi ‘’Mai neman kuka ne, sai kuma ga shi har an kai ga jifar shi da kashin Awaki’’. Idan har aka samu shi irin wannan haxin to shikenan sai kowa ya samu wuri ya zauna, domin sanin lalle bada daxewa ba ne, sai an samu labarai da xumixuminsu.

Babba Da Jaka

Za Mu Maka Shugaba Muhammadu Buhari Kotu In.... —Gwamna Ganduje

To fa!

Ana shiryawa da buga LEADERSHIP A Yau a kamfanin LEADERSHIP GROUP LIMITED, lamba 27, kan Titin Ibrahim Tahir, a Gundumar Utako, Abuja. Tarho: 09-2345055; Fax: 09-2345360. P. O. Box 9514, Garki II, Abuja. Ofishin mu a Legas: 34/36 Titin Adegbola, Anifowose, daidai Oba Akran, Ikeja. Tarho: 01-8963459. E-mel: leadershipayauasabar@gmail.com

Leadership A Yau Asabar 14 Ga Afrilu 2018  

Leadership a yau 14 ga afrilu 2018

Leadership A Yau Asabar 14 Ga Afrilu 2018  

Leadership a yau 14 ga afrilu 2018

Advertisement