Leadership A Yau 11 Ga Afrilu 2018

Page 1

11.4.18

AyAU Laraba

LEADERSHIP Don Allah Da Kishin Qasa

JARIDAR HAUSA MAI FITOWA KULLUM TA FARKO A NIJERIYA

www.leadershipayau.com Leadership A Yau

11 Ga Afrilu, 2018 (24 Ga Rajab, 1439)

LeadershipAyau

No: 122

N150

Karatun Jabu: An Fara Tantance Digiri 40,000 Na Qasashen Waje Daga Bello Hamza

Gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin mutum 16 ta hannun ma’aikatan ilimi domin tantance takardar shaidan karatu na matakin digiri guda 40,000 da ‘yan Nijeriya da suka yi karatu a qasashen waje suka karvo. Ministan ilimi Adamu Adamu ya ce, tantance digirin ya na da

matuqar mahimmanci saboda a gano takardun digiri na bogi da aka shigo da su daga bara gurbin jami’oi marasa inganci a wasu qasashen Afirika da sauran qasashen duniya. Adamu ya yi wannna sanarwar ce a taro na musamman na “National Standard Committee on Evaluation and Accreditation of Foreign Qualifications” inda ya qara da cewa, binciken farko ya nuna akwai

takardar shaidan kamamla karatun jami’a fiye da 40,000 dake a hannun ‘yan Nijeriya dake aiki wasu manyan makarantun qasar nan ko kuma suna aiki a wasu ma’aikatun gwamnati. Ya ce, ma’aikatar ilimi ta gano cewa, yawancin waxannan digirin bogin sun fito ne daga qasashe irin su jumhoriyar Benin da togo da Cameroon. “A kwai matuqar buqatar tantance takardun shaidan karatun

da suka fito daga qasashen waje domin tabbatar da sahihancinsu da matsayin da za a xora su a cikin gida” “Shawarwarin da wannna kwamitin zai bayar yana da matuqar mahimmanci domin shi ne zai tattabar da ingancin takardun shaida karatun da aka karvo daga makaratun qasashen waje”

Dubu 960,000 Ministocin Nijeriya Ke Amsa Duk Wata

>Ci gaba a shafi na 2

4

—Amaechi Yadda Na Samu Miliyan 100 A Mutum 50 Da Na Sace -Muritala Daga Bello Hamza

Daga hagu zuwa dama: Sakataren din-din-din na Babban Birnin Tarayya, Chinyeaka Ohaa; Ministan Yaxa Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed; Ministan Babban Birnin Tarayya, Mallam Mohammed Musa Bello tare da Ministar din-din-din ta Ma’aikatar Yaxa Labarai da Al’adu, Grace Isu-Gekpe jiya yayin wata ziyarar sada zumunci da Ministan Yaxa Labarai ya kai ofishin Ministan Babban birnin Tarayyar

Rundunar ‘yan Sandan Nijeriya Reshen Jihar Edo ta gabatar da wani qasurgumin mai garkuwa da jama’a, Muritala Umaru, wanda a baya ya sha zuwa kurkuku saboda wannan muguwar sana’a. Wanda ake zargi xin ya bayyana cewa tawagarsa ta samu adadin kuxi har naira miliyan 100 a sakamakon wannan xanyen aiki na garkuwa da mutane. Bayan an damqe shi, an same shi da bindigar AK47 wacce ke xauke da lambar rajista da kuma harsaisai. Ya bayyana cewa, ya fara garkuwa da mutane ne tun bayan shekaru huxu da suka gabata a garin Okenne dake Jihar Kogi.

>Ci gaba a shafi na 2

An Daqile Yunqurin Fasa MTN Ya Biya Rabin Naira Bilyan 330 Da Aka Ci Tarar Sa Cibiyar Mai A Delta > Shafi na 2

> Shafi na 4


Turn static files into dynamic content formats.

Create a flipbook
Issuu converts static files into: digital portfolios, online yearbooks, online catalogs, digital photo albums and more. Sign up and create your flipbook.