10.4.18
AyAU Talata
LEADERSHIP Don Allah Da Kishin Qasa
JARIDAR HAUSA MAI FITOWA KULLUM TA FARKO A NIJERIYA
www.leadershipayau.com Leadership A Yau
10 Ga Afrilu, 2018 (23 Ga Rajab, 1439)
No: 121
LeadershipAyau
N150
Rikicin Makiya Da Manoma: Ministocin ECOWAS Za Su Yi Taro A Abuja Daga Abdulrazaq Yahuza Jere, Abuja
Ministan Kula da Harkokin Cikin, Laftanar Janar Abdulrahman Bello Dambazau mai ritaya, ya sanar da cewa ministocin kula da harkokin cikin gida na qasashen Qungiyar Bunqasa Tattalin Arziqin Qasashen
Yammacin Afirka (ECOWAS) za su yi taro a Abuja domin lalubo bakin zaren warware rikicin makiyaya da manoma. Ministan ya bayyana haka ne a zantawarsa da LEADERSHIP A Yau, jim kaxan bayan ya qaddamar da wasu ayyuka a shalkwatar Hukumar Kula da Shige da Fice ta Qasa da ke hanyar filin
Babbar Magana...
jirgin saman Nnamdi Azikwe a Abuja. Abdulrahman Dambazau ya ce ana sa ran taron ya fara gudana nan da makwanni biyu masu zuwa. “A halin yanzu da muke magana mun riga mun shirya da ECOWAS Comission (Sakatariyar Qungiyar Bunqasa Tattalin Arziqin Qasashen
Yammacin Afirka) da ke nan Abuja, qarshen watan nan za a yi babban taro na ministocin harkokin cikin gida da kuma ministocin aikin noma. Duk ministocin qasashen ECOWAS za su hallara a Abuja nan da sati biyu domin fara taron.
>Ci gaba a shafi na 2
Zan Yi Takara A 2019 –Buhari 4
Wannan Damuwar APC Ce –PDP Bai Kamata A Sake Zavensa Ba –Farfesa Moghalu
Shugaban Qasa Muhammadu Buhari a jiya yayin da zai bar Babban Birnin Tarayya Abuja don tafiya qasar Ingila inda zai tattaunawa da Firayiminista Theresa May tare da halartar taron CHOGM
An Kashe Mutum 8 A Za Mu Sake Fitar Da Sunayen Gidan Giya A Filato Varayin Gwamnati –Minista > Shafi na 2
> Shafi na 2