GABATARWA
Bashakka al’amarin amfani da kaƴansa maye ya zama ruwan dare game duniya, domin babu wata ƙasa ko Jiha da ba a shaye – shaye, sai dai a sami bambance – bambance saboda yanayin wayewa ko tattalin arziki ko kuma ƙoƙarin shugabanni wajen daƙile harkar ta shaye – shaye.
A halin da muke a ciki mun samu kammu a cikin wani matsananciyar fitina ta shigar Mata da Ƙananan Yara da kuma Matasa a harkar shaye – shaye.
Babushakka wannan kan iya janyo fitintinu kamar haka:
Taɓarɓarewar tarbiyya da kulawar da iyaye mata suke bayarwa a matsayin gudummawa.
Samuwar rashe rashen lafiya da zai iya ɓullowa wanda bawanda ya san inda zai tsaya.
Taɓarɓarewar samun kwanciyar hankali da yawan fitintinu kamar su kisan kai, zinace – zinace, sace – sace, da dai sauran aikin alfasha da munkari (abunƙi). Allah Ya mana mafita Ya kuma taimake mu, Ya kuma yaye mana wannan fitinar data addabemu a wannan ƙasar da duniya baki ɗaya.