Page 1

14.2.18

AyAU Laraba

LEADERSHIP

www.leadershipayau.com Leadership A Yau

Don Allah Da Kishin Qasa

14 Ga Fabrairu, 2018 (27 Ga Jimadal Ula, 1439)

JARIDAR HAUSA MAI FITOWA KULLUM TA FARKO A NIJERIYA

LeadershipAyau

No: 090

N150

Shekau Ya Fara Sa Kayan Mata Don Vad Da Kama –Sojoji Daga Sulaiman Bala Idris

Rundunar Sojojin Nijeriya ta bayyana cewa an samu tabbacin cewa Shugaban Qungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya fara yin shiga irin ta mata domin ya vat da kamanninsa ta yadda zai samu damar arcewa. Kakakin rundunar sojojin

qasa, Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka ne ya tabbatar da hakan jiya, inda ya bayyana cewa Shekau ya sha wahala a hannun rundunar, don haka ne ma ya ke neman hanyar arcewa ya bar mabiyansa. “Neman hanyar da zai gudu ya tsira da ransa yake. Har shiga irin ta mata yake yi yanzu da

hijabi don dai ya samu ya gudu. “Bincike ya tabbatar mana da cewa Abubakar Shekau na canza kalan hijaban da yake sawa lokaci bayan lokaci. ya kan yi amfani da Baqi da ruwan bula. ganinsa na qarshe da aka yi, yana sanye ne da baqin hijabi. “Muna son sanar da dukkanin

sauran ‘yan Boko Haram xin da suka rage da su kwana da sanin cewa munafuki suke bi a matsayin jagora, wanda ke vad da kamanni a da shiga irin ta mata. “Sannan muna kira gare su da su miqa wuya cikin mutunci ta yadda za a sauqaqa musu hukunci.” inji Kukasheka

Mummunan Hatsarin Mota Ya Ci Xaliban Bauchi 25

• Birgediya Janar Kukasheka

4

•Daga hagu zuwa dama Shugaban Qasa Muhammadu Buhari; Bisi Akande; Bola Tinubu a yayin wata ganawa da shugaban ya yi da jagororin jam’iyyar jiya a fadarsa dake Abuja

Yadda Tambuwal Ya Inganta Patience Jonathan Ta Nemi Hukumar Kashe Gobara A Sakkwato Sulhu Da Hukumar EFCC > Shafi na 15

> Shafi na 2


2 LABARAI

A Yau

Laraba 14 Ga Fabrairu, 2018 (27 Ga Jimadal Ula, 1439)

Patience Jonathan Ta Nemi Sulhu Da Hukumar EFCC Daga Bello Hamza

Daga dukkan alamu Misis Patience Jpnathan matar tsohon Shugaban qasa Goodluck Jonathan ta gaji da shari’a dake tsakaninta da Hukuma EFCC a kotunan qasar nan saboda haka ta nemi sulhunta su a wajen kotu. Patience Jonathan ta rubuta wasiqa ne ta hannun lauyanta Cif Ifedayo Adedipe (SAN) in da ya bayyana shirin Patience Jonathan na shiga tattaunawar da zai kai ga sulhu a zarge-zargen da Hukumar EFCC ke yi mata. “A matsayi na na babban lauyan dake wakiltar Misis Dame Patience Jonathan da kanfanonin dake da alaqa da ita da ‘yanuwa da abokan arziqinta da kuma wasu qungiyoyi masu zaman kansu, mun tattauna mun kuma yi tunani a kan matalolin da ke tsakaninta da Hukumar EFCC domin

samar da hanyar maslaha na sulhu a kan dukkan qarar dake tsakaninmu da Hukumar” Ya qara da cewa, “Wannan zai taimaka wa dukkan vangarorin samun fahintar juna a yanayi na zaman lafiya, don haka muke ganin zamu yi murnar in har zaku samar mana da lokacin da zamu haxu domin tattauna abubuwan da suka shafe ta da ‘yanuwan na ta” “Muna da tabbacin cewa, sulhunta wannan lamari abu ne da zai taimaki hukumar da wadda muke wakilta” “Muna tabbatar muku da qudirimu na bayar da cikkken haxin kai a kan wannan lamarin don haka muke neman naku haxin kan domin samun nasarar wannan sulhun” Wannan wasiqar neman sulhu ya zo ne adaidai lokacin da Hukumar EFCC ta qara cin karo da wasu bayanai dake nuna yadda ta tara maqudan Daloli a bankin Skye da First

Bank da kuma yadda ta kashe wasu vangaren kuxaxen a tafiye tafiyen da ta yi qasashen duniya. Kuxaxen na daga cikin Dala $11,849,069.03, wanda Hukumar EFCC ta ce wasu mutane 31 da kanfanonin suka zuba a asusun bankin ta na Skye mai lamba 2110001712 da na First Bank mai lamba 2022648664 tsakanin shekara 2013 da 2017. Masu bincike na Hukumar sun gano $7,452,319.32 a asusun Skye Bank yayin da aka gano $4,036,750.00 a asusun First Bank. Bincike ya nuna cewa, matar tsohon shugaban qasar ta kashe kuxaxen ne a shagunan alfarma na TFS stores dana Selfridges da John Lewis da Kingsgate da Sainsbury da kuma kantin Harrods dana Marks da Spencer da kuma Dolce da Gabbana da na Gina. Ta kuma tafi qasashen Amurka da Birtaniya da Jamus da

na Hong Kong da Haxxaiyar Daular Larabawa da na Italiya da kuma qasar Sin. An kuma gano cewa, Misis Jonathan ta kashe kuxi mafi yawa ne a shagunan Goyard Beijing ta qasar Sin ranar 28 ga watan Janairu 2014 in da ta kashe Dala 28,388.72, a wannan ranar ce a Hulian Xinguang Beijing CN ta sake hallaka Dala $13, 069.68 a kan wasu kayayyakin alfarma. Bayanin dake fito wa daga Hukumar EFCC ta yabbatar da kavar wasiqar Msis Jonathan na neman sulhu, “Lallaimun samu wasiqa daga matar tsohon shugaban qasar muna kuma nazarin ko mu amince ko kuma mu bar doka ta yi aikin ta” Bayan maganar kuxaxe akwai wasu qaddarori guda 12 da wasu filaye da ake gini a kai,

Hukumar Gidan Yari Ta Qarawa Jami’anta 196 Girma A Kebbi Daga Umar Faruk, Birnin-Kebbi

•Patience Jonathan

’Yan Sanda Sun Ceto Makiyaya Da Shanu 200 A Jihar Borno Daga Muhammad Maitela, Maiduguri

Rundunar yan-sandan Nijeriya dake a jihar Borno ta bayyana cewa ta kuvutar da makiyaya tare da shanu sama da 200 daga hannun mayaqan qungiyar Boko Haram a yankin qaramar hukumar Nganzai dake jihar. Kwamishinan rundunar yan-sanda a jihar Borno, Mista Damian Chukwu, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Maiduguri, bayan tattàunawar qarshen wata da jami’an sa, a ranar litinin. Bugu da qari kuma,

Chukwu ya shaidar da cewa an ceto makiyayan ne ranar biyu ga wannan wata na Fabarairu, ta wani samamen haxin gwiwa a tsakanin yansandan da yan sa-kai na qatoda-gora (CJTF) a surquqin duhuwar Galte dake yankin qaramar hukumar. Haka kuma ya yi qarin haske da cewa sun aiwatar da samamen bin-saqun biyo bayan wani rahoton da suka samu bisa ga yadda mayaqan qungiyar sun yi garkuwa da wasu makiyayan tare da neman a basu kuxin fansa, kafin su sako su.

“wanda babban jami’in yansanda na yanki (DPO) dake yankin ya jagoranci samamen tare da samun nasara bayan bata-kashi da musayar wuta da ya wakana a tsakanin su da mayaqan qungiyar Boko Haram “. “yan-sandan sun ceto makiyayan tare da wannan adadi na dabbobin su, a lokacin da mayaqan qungiyar suka arce. Yayin da kuma yan-sandan sun sami bindiga mai sarrafa kan ta (GPMG) tare da albarusai waxanda mayaqan suka gudu suka bari”. Inji shi.

masu binciken sun bayar da shawarar cewa, hukumar ta yi amfani da sashe na 7 na dokar da ta kafa Hukumar EFCC da nufin mallake qaddarorin. Qaddarorin da aka alaqanta su da Misis Jonathan suna garin Fatakwal sun haxa da na “Former Customs Service officers mess” wasu gidajen alfarma a layin Bauchi da Filaye a layin Ambowei da kuma wasu gidaje na alfarma guda 3 a unguwan Ambowei da Otal xin Grand View dake kan hanyar filin jirgin sama a garin Yenagoa ta jihar Bayelsa, binciken ya kuma gano wasu qaddarorin Patience a GRA kan hanyar Isaac Boro da kuma wani katafaren gida a a kan hanyar Sani Abacha da rukunin shaguna na Akemfa Etie dake kusa da gidan man AP.

Hukumar Gidan Yari Ta qasa reshin jihar kebbi ta Karawa jami’anta 196 Girma a mataki daban daban. An gudunar da taron bukin Karin Girma ne a babban ofishin na hukumar da ke a GRA Birnin-Kebbi a jiya. Jami’an da aka Karama girma sun hada da DCP uku, ACP xaya, CSP xaya, DSP goma da kuma PIP ashirin da shida. Sauran mukaman sun hada da SIP arba’in da biyar, IP guda tara, CPA guda ashirin da takwas, SPA guda Talatin da bakwai, PA1 guda gona shabakwai da kuma PA2 . Kazalika jam’ai goma shatakwas an kara su mataki na gaba kan kammala karatu a jami’o’i da kuma kwaleje qasar nan. Da yake gabatar da jawabinsa bayan kammala bukin Karama jami’an na hukumar ta gidan Yari Ta qasa reshin jihar ta kebbi

•yayin qarin girmar

CP Sani Adamu Potiskum ya bayyana jin dadinsa da kuma yabawa shugaban hukumar na qasa CGPS Ahmad Jafaru Jega kan irin kokarinsa na ganin cewa an kyautatawa jami’an hukumar ta hanyar kara musu girma ga aiki da kuma biyan albashi kan ka’ida. Har ilayau Potiskum yayi kira ga jami’an na jihar kebbi da su zama jakadu kan aikin na gidan Yari a duk inda suka samu kansu. Daga qarshe ya godewa shugaban hukumar na qasa da kuma jami’ansa kan irin kyakyawar Kulawa da shugaban ke baiwa jami’an na hukumar. Mahalar ta taron bukin Karawa jami’an hukumar girma sun hada da kwamishinan ‘yan sanda na jihar kebbi, mataimakin daraktan jami’an tsaron farin Kaya na SSS, Kwamanda na NDLEA da kuma kwamanda na NSCDC. Sauran sun hada da kwamandan na FRSC, kwamandan bigilanti da kuma sauran su.


3

A Yau Laraba 14 Ga Fabrairu, 2018 (27 Ga Jimadal Ula, 1439)

Ra’ayinmu Kira Ga Hukumar Zave Mai Zaman Kanta ‘INEC’

B

ayan Njeriya ta yi sallama da mulkin soja a shekarar 1999, ‘yan qasar da dama sun riga sun amince da mulkin dimokuraxiyya a matsayin tsarin gwamnatin da ya fi karvuwa a gare su. Kamar yadda aka sani, idan aka ce dimokuraxiyya ana nufin tsarin shugabancin da zai baiwa jama’a dama su zavi shugabanninsu da kansu. Domin tabbatar da inganci da hanya mafi sauqi na zavin shugabannin; sai aka fito da tsarin yiwa waxanda za su riqa zave rajista tare da ba su katin shaida a matsayin katin da za su yi amfani da shi su jefa quri’a idan lokacin zaven shugabannin ya zo. Rajistar masu zaven tana da matuqar muhimmanci a sha’anin zave kasancewar ita ce take baiwa xaukacin waxanda suka cancanci kaxa quri’a damar zaven shugabannin siyasa. Hukumar Zave ta Qasa mai zaman kanta (INEC) ita ce aka damqa wa alhakin yin rajistar ga masu zave domin su yi amfani da ‘yancinsu na zave kamar yadda ya kamata. Hukumar takan gudanar da aikin rajistar a duk lokacin da buqatar hakan ta taso. Bisa hakan, waxanda ba su samu sun yi rajistar a wani lokaci ba za su iya yi a wani, sannan yaran da shekarunsu ba su cika na kaxa quri’a a yayin gudanar da aikin rajistar a baya ba, idan aka zo yin nagaba suna samun dama su yi. Wannan ya sa hukumar ta zave tun daga shekarar 2017 ta fara aikin rajistar zave ga waxanda ba su yi ba tare da gyara rajistar waxanda suka sauya wuraren da suke son kaxa quri’a a sakamakon sauya mazauninsu. A zaven qarshe da aka yi na qasa baki xaya, masu kaxa quri’a ba su fito qwansu da qwarqwata kamar yadda ya kamata ba. Domin daga cikin adadin ‘Yan Nijeriya milyan 120 da suka isa kaxa quri’a, milyan 70 ne kawai suka yi rajistar katin zavensu. Daga cikin milyan 70 xin kuma, milyan 30 kacal suka kaxa quri’a a zaven shugaban qasa kuma su ne kaxai suka yanke shawarar mutumin da ya cancanta ya shugabanci adadin ‘yan qasar mutum milyan 180. Ko ba a tambaya, tabbas wannan adadin ya yi kaxan, a ce mutum milyan 30 ne za su yanke hukunci kan wanda zai shugabanci mutum milyan 180. Wannan ba abu ne da za a yaba da shi a cikin duk qasar da ta rungumi dimokuraxiyya da hannu biyu-biyu ba. Bayanai sun nunar da cewa Hukumar INEC tana da rajistar masu kaxa kuri’a milyan 80 a cikin kundinta kuma tana da burin qara yawansu zuwa milyan 85 domin babban zaven 2019 nan da watan Disamba. Har ila yau, bayanai sun nunar da cewa akwai adadin katin jefa quri’a na dindindin kimanin milyan takwas da masu su ba su je sun karva ba. A baya, wataqila za a iya cewa yawo da hankulan masu kaxa quri’a, mugun

maguxin zave da aringizon quri’a na rashin imani sun hasala ‘Yan Nijeriya da dama har suka yanke shawarar ba za a sake ganin fuskarsu a rumfunan kaxa quri’a lokacin zave ba. Amma a halin yanzu abin ya sauya, qwarya-qwaryar gyarar fuskar da aka yi wa dokokin zave sun dawo da kima da martabar sha’anin zaven qasar zuwa wani mataki abin yabawa. Yadda sha’anin qasar ya fara daidaituwa a kan turba, an samu qarin ‘Yan Nijeriya masu yawa da suke da

muradin shiga a dama da su wajen zaven shugabannin qasar na gaba. Tuni har ma waxanda aka san su da rungume hannu a lokacin zavukan baya sun nuna alamar xokin zaven. Duk wannan saboda qwazon da gwamnati mai ci a yanzu take yi ne. Kamar yadda aka zata, an samu qaruwar wayar da kan jama’a daga sassa daban-daban na qasar a kan muhimmancin mallakar katin zave ga duk wanda ya kai munzalin kaxa quri’a. Ba a tava samun qaimi da kuzarin wayar

EDITA Sulaiman Bala Idris

MATAIMAKIN SHUGABA (NA MUSAMMAN) Christian Ochiama

MATAIMAKIN EDITA Bello Hamza

DARAKTAN SASHE Mubarak Umar

RUKUNIN KAMFANONIN LEADERSHIP SHUGABA Sam Nda-Isaiah

BABBAN MANAJAN DARAKTA Abdul Gombe BABBAN MANAJAN DARAKTAN KADARORI David Chinda MANYAN DARAKTOCIN KAMFANI Dele Fanimo Felicia Ogbonlaiye DARAKTAN KULA DA MA’AIKATA Solomon Nda-Isaiah DARAKTAN KULA DA KADARORIN KAMFANI Zipporah D. Tanko MANYAN MANAJOJI Ibrahim Halilu Femi Adekunle Ebriku John

manufarmu

LEADERSHIP A Yau jarida ce da ake bugawa a Abuja. Ta yi tsayuwar daka wajen tabbatar da shugabanci da wakilci nagari. Jaridar za ta ci gaba da kare muradun al’umma, ba kare ra’ayi da muradun mahukuntanta kaxai ba. Da waxannan qudirorin ne muke fatan jama’a za su xora mu kan Mizani. Haka kuma duk ra’ayoyin masu karatu da muke bugawa, ba manufar kamfanin LEADERSHIP ba ne, ra’ayin masu karatun ne. Sai dai, ba za mu tava mantawa da dalilin wanzuwarmu a doron qasa ba, wato: Don Allah Da Kishin Qasa!

da kan jama’a a kan muhimmancin katin zaven kamar yadda ake yi a yanzu ba, kasancewar abin ya cika gari lungulungu da saqo-saqo. A duk inda mutum ya juya zai ji ana batun katin zaven da muhimmancin yin sa. Hatta waxanda suka mayar da kafofin sadarwa na walwalar jama’a wurin tafka muhawara da cin diddigen juna ana wayar musu da kai cewa wannan ba za su fishe su ba, mafita gare su kawai su mallaki katin rajistar zave. Abin birgewa kan hakan shi ne yadda mutane suka amsa kira. Duk wanda bai yi ba yana qoqarin zuwa ya yi rajistar a cibiyoyin da aka tanada na musamman domin aikin. Sai dai wani abu da za a iya cewa ya zama ga-qoshi-ga-kwanan yunwa shi ne yadda mutane ke shan wuya kafin su samu a yi musu rajistar. Aikin yana tafiyar hawainiya kuma ga wahalar yi. Mutane da yawa sun ba da labarin yadda suka shafe sa’o’i da dama kafin a kammala yi musu rajistar. Wannan ma ga waxanda suka taki sa’a ke nan, amma wasu da abin ya yi musu tutsu da yawa sai sun shafe kwanaki suna zuwa wurin rajistar ba su samu yi ba. Masu neman a yi musu rajistar zaven galibi sukan bar gida tun kafin Karinkumallo kuma su shafe yini cur su dawo gida haka nan ba tare da an yi musu ba. Waxannan matsalolin ba su rasa nasaba da qarancin cibiyoyin rajistar, na’urorin aikin da kuma rashin isassun ma’aikata. A wasu wuraren kuma cibiyoyin da aka keve na aikin sun yi wa jama’a nisa. An ba da rahoton cewa an buxe cibiyoyin rajistar ne a shalkwatocin qananan hukumomi. A wasu qananan hukumomin kuma; babu ma cibiyar rajistar kwata-kwata, don haka sai mutane sun tafi qananan hukumomin da ke maqotaka da su kafin su yi rajistar. Hakan ta qara jidali ga masu neman a yi musu rajistar tare da kashe musu qwarin gwiwa. A sanadiyyar hakan, wasu sun haqura da lamarin, inda wannan zai sa su rasa damar amfani da ‘yancinsu na zaven shugabannin da suka kwanta musu a rai. Bayan duk wannan, wusa qananan hukumomin jami’ansu sukan hana a yi wa wasu rajistar saboda banbancin shiyyar da mutum ya fito saboda wai fargabar kar mutum ya zo ya zavi xantakarar da ba shi suke so ya ci zave a yankinsu ba. Tabbas, hakan ta sava wa qa’idar dimokuraxiyya. Saboda haka, Hukumar Zave ta Qasa (INEC) kina da jan-aiki a gabanki kuma duk da cewa mun lura ayyuka sun yi miki yawa, ya kamata ki miqe haiqan wurin ganin kin magance waxannan matsaloli da suke dabaibaye aikin rajistar masu kaxa quri’a. Ki duba yiwuwar qara yawan cibiyoyin aikin rajistar a manya da qananan garuruwa tare da na’urorin aiki da kuma isassun ma’aikata domin sauqaqa aikin kamar yadda ya kamata.


4 LABARAI

A Yau

Laraba 14 Ga Fabrairu, 2018 (27 Ga Jimadal Ula, 1439)

Mummunan Hatsarin Mota Ya Ci Xaliban Bauchi 25 Daga Muazu Hardawa, Bauchi

A jiya ne mutum 29 waxanda suka haxa da xalibai 25 da malaman su uku da direba sun rasa rayukan su a kan hanyar su ta zuwa nazarin ilimin tarihi a gidan xan Hausa da ke Kano. Xalibai da Malaman da suka rasu sun kasance a qarqashin qungiyar Hausa Fasaha dake makarantar Jeka ka dawo ta GDSS Misau da ke Jihar Bauchi. Hatsarin ya auku a kusa da garin Gaya dake Jihar Kano da misalin qarfe Goma na Safiyar jiya inda motar qirar ‘Toyota Hommer’ wacce aka cunkushe ta da xaliban ta yi taho mu gama da mota qirar tirela mai tayu goma sha biyu, wacce ke kan hanyar Kano zuwa Maiduguri, inda su kuma ke kan hanyar su daga Misau zuwa Azare zuwa Kano don gudanar da wannan nazarin tarihi. LEADERSHIP A Yau ta gano cewa xaliban sun kasance ‘yan ajin qaramar sakandare daga xaya zuwa uku waxanda suka qudiri yin wannan tafiya tare da malamansu sun gamu da hatsarin ne a dalilin aikin hanya da ake yi a wannan waje aka kuma haxe ana tafiya kan hannu guda. Lamarin dai ya yi muni sosai har sai da matafiya da mutanen yankin suka yi ta taimakawa kafin aka jawo gawarwakin xalibai 22 da malamai uku da direba yayin da kuma xalibai uku aka kai su asibiti kafin daga baya suma rai ya yi halin sa.

Ya zuwa wannan lokaci lamurra sun tsaya cik a fannin aikin gwamnati a Jihar ta Bauchi kamar yadda babban mai ba gwamnan Jihar Bauchi shawara kan harkar ilmi Kwamared Sabo Mohammed ya shaida wa wakilin mu. Inda ya miqa saqon gaisuwar ta’aziyya a madadin kwamishinan ilimi na Jihar Bauchi da xaukacin masu ruwa da tsaki kan ilmi da kuma gaisuwar ta’aziyya ta gwamna Mohammed Abdullahi Abubkar na Jihar Bauchi game da wannan rashi na xaliban inda ya bayyana cewa wannan babbar hasarace ga Jihar da ba za a tava mancewa da ita ba kan harkar da ta shafi ilmi. Sabo Mohammed ya qara miqa ta’aziyyar gwamnati da jama’ar Jihar Bauchi ga Mai martaba Sarkin Misau Alhaji Ahmed Sulaiman game da wannan babban rashi na yara masu kasancewa manyan gobe a Jihar Bauchi. Ya ce gwmnati ta kaxu sosai lokacin da ta samu wannan labari, kuma nan take jami’an ma’aikatar ilmi da sauran jami’an gwamnati suka xunguma zuwa garin na Misau domin yin jana’izar yaran wacce ta gudana a yammacin wannan talatar a garin na Misau. Malam Ya’u Mohammed da Malam Mohammed Kaka Misau Malamai ne a wannan makaranta, sun bayyanawa LEADERSHIP A Yau alhininsu kan wannan rashi da suka ce ya haifar da givi a fannin ilmi na makarantar ta jeka ka dawo da ke garin Misau, inda suka yi

•Motar da xaliban suka yi hatsari da ita

fatar Allah ya ba da haquri ga iyayen yaran da kuma abokan karatun su da malaman wannan makaranta da sauran ‘yan uwa da dukkan jama’ar wannan qasa, inda suka ce wannan babban rashi ne da ba za su iya mance wa da shi ba a tarihin karatun wannan makaranta. Jagoran ayyukan musamman na hukumar kiyaye haxurra ta qasa FRSC da ke Bauchi Kwamanda Paul E. Guar a lokacin da wakilin mu ya ziyarce shi a ofishinsa da ke Bauchi, ya tabbatar da aukuwar wannan hatsari, inda

ya ce xaliban sun tashi daga garin Misau zuwa Kano sun gamu da ajalin su a kusa da garin Gaya sakamakon taho mu gama da babbar mota, inda ya bayyana cewa yin sakaci da dokar tuqi ya temaka wajen haifar da hatsarin. Don haka ya roqi jama’a su kasance masu lura da rayukan jama’ar da suke xauka da kuma nasu shi ne zai taimaka a samu raguwar haxurra a qasar nan. Haka kuma Paul Guar ya bayyana takaici game da yadda aka cunkusa waxannan mutane har kusan 30 a motar da ke xaukar mutane

18, lamarin da ya bayyana a matsayin abu maras kyau da kuma sava dokar tuqi da lodi, saboda yin hakan na samar da qaruwar yawan mutanen da za su iya galabaita ko rasa rayukan su a duk lokacin da wani tsautsayi ya abko kan matafiya, musamman ganin cewa wannan hatsari ya auku ne a wurin da ake gyaran hanya. Daga qarshe ya ce ofishin hukumar da ke Jihohin Kano da Jigawa sune za su bayar da cikakken bayani game da yadda aikin su ya gudana a wajen wannan hatsari.

An Tsinci Gawar Wani Manomi A Xakinsa A Abuja Daga Abubakar Abba

A cikin satin da ya gabata ne, wani maqwabbacin ya shedawa wakilin mu cewar an ga gawar wani mai suna Ali dake qauyen Kubwa a cikin Birnin Tarayyar Abuja, a xakinsa wanda ya saba fita da duku-duku zuwa gona, bayan sun gaisa da safe da maqwabtansa, ba’a qara ganin

Ali ba a ranar, inda saida aka valla qofar ta manomin aka kuma same gawarsa a cikin xaki a cikin jin. Wakilin mu ya gano cewar, akwai wata hatsaniya data auku a tsakanin gungun wasu matasa dake yankin kwana xaya kafin aukuwar lanarin, inda hakan ya janyo aka lalata wasu wuraren da ake

gudanar da kasuwanci, har wasu mutane uku da ba’a san kosu wanene ba suka samu raunuka. Wani shugaban matasa dake yankin mai suna Daniel Christopher, wanda xan uwa ne ga marigayin, ya yi zargin cewar xan uwansa marigayin wataqilan hatsaniyar ce ta rutsa dashi. Wakilin mu ya ruwaito

cewar, an bizni marigayin a ranar Juma’ar data wuce. Duk iya qoqarin da wakililinmu ya yi don jin ta bakin DPO na gundumar ta Kubwa, (CSP) Ayobami Surajudeen, akan maganar hakan yaci tura domin ance ya yi tafiya a lokacin da wakilin mu yaje ofishin kuma an kira DPO a wayar tafi da gidan ka, amma layinsa baya tafiya.

Sai dai, wani babban jami’in ‘yan sanda a ofishin na ‘yan sanda, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace an kawo rahoton maganar a ofishin na gundumar ‘yan sanda, inda ‘yan sanda suka amince aka xauko gawar marigayin daga babban asibitin dake Kubwa bayan shugabannin dake yankin suka gabatar da buqatar a basu gawar.

EFCC Ta Fara Binciken Kuxaxen Da Maciji Ya Haxiye A JAMB Daga Umar A Hunkuyi

Hukumar hana cin hanci da rashawa EFCC, ta sha alwashin kamawa da kuma fexe narkeken Macijin nan da aka yi zargin wai shine ya haxiyi tulin takardun Naira har Milyan 36 a tashi guda, a Ofishin hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu JAMB, na Makurxi da ke Jihar Benuwe.

Hukumar ta sha alwashin, wannan Maciji,imma mutum ne ko aljan, qaryarsa ta qare, domin kuwa ko sama ko qasa ya yi da milyoyin kuxin tabbas sai ya dawo da su. Wata dai ma’aikaciyar hukumar ta JAMB ce, Philomina Chieshe, a sa’ilin da take amsa tuhuma kan inda ta kai kuxaxen har Naira milyan 36, ta yi zargin wai wani Qaton

maciji mai siddabaru ya shigo ofishin na ta ya lanqwame milyoyin kuxin a kan idonta. Hukumar ta EFCC, ta sha wannan alwashin ne a shafin ta na Tiwita ranar Litinin xin nan, inda ta tabbatar da wannan yunqurin na ta. Da misalin qarfe 6:30 na safiyar litinin xin sama da mutane 5,349. ne suka mayar wa da hukumar martani a kan

wannan maganan, mutane 5,286 kuma suka yaba wa hukumar a kan wannan yunqurin da ta xauri aniyar yi, an kuma samu sama da mutane 1000 da suka yi sharhi a kan zancen. Wasu dai da suka yi sharhin, roqon EFCC, xin suke da ka da ta sanya siyasa a cikin binciken da za ta yi, wasu kuma yaba mata suke yi, inda suka nu na

cewar sun zura ido domin su ga yadda za a fafata a tsakanin Mikiya da Maciji, suna masu roqon hukumar da ka da ta bari Maciji ya baiwa Mikiya kunya. A wata sabuwan kuma, ,hukumar ta JAMB, ta bayar da sanarwar dakatar da ma’aikaciyar nata, Chieshe, daga aiki, a kan wannan lamarin.


LABARAI 5

A Yau Laraba 14 Ga Fabrairu, 2018 (27 Ga Jumada Ula, 1439)

Fayose Ya Rubutawa Buhari Wasiqa Kan Canza Sunan Jami’ar Oye-Ekiti Daga Umar A Hunkuyi

Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya rubuta takardar tuni ga Shugaba Muhammadu Buhari, a kan canza sunan Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Oye, Ekiti (FUOYE) zuwa, Jami’ar Adeyinka Adebayo, watau tsohon gwamnan mulkin Soja na tsohuwar shiyyar shiyyar yamma, marigayi Janar Robert Adeyinka Adebayo. A ranar 20 ga watanMayun shekarar 2017, ne dai Adebayo, ya rasu a qauyensu na Iyin-Ekiti. Mataimakin Shugaban qasa, Farfesa Yemi Osinbajo, a lokacin da yake muqaddashin Shugaban Qasa ne wajen jana’izan Adebayon,ya bayyana wannan shawarar

da gwamnatin ta tarayya ta yanke, na canzawa Jami’ar suna zuwa Jami’ar gwamnatin Tarayya ta Adeyinka Adebayo, domin jinjinawa ga gudummawar da tsohon gwamnan yankin ya bayar. Yanzun kimanin watanni tara kenan da bayar da waccan sanarwar, amma har yanzun ba a fara aiki da ita ba. Jami’in hulxa da manema labaran gwamna Fayose, Idowu Adelusi, ne ya bayyana hakan a cikin wata takarda mai kwanan watan 29 ga watan Janairu 2018, mai lamba, EK/GOV/28/93, inda aka nemi Shugaban qasan da ya tabbatar da alqawarin canjin sunan da ya yi. “Kamar yadda mai girma Shugaban Qasa ya sani, Marigayi Adebayo ya rasu ne a

shekarar da ta gabata. “Mataimakin Shugaban Qasa ne ya wakilce ka a wajen jana’izan wacce aka yi a ranar 20 ga watan Mayu na shekarar ta 2017. “A wajen ne Muqaddashin Shugaban Qasan ya bayyana wannan shawara ta gwamnatin Tarayya na canza sunan Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Oye-Ekiti, zuwa Jami’ar Adeyinka Adebayo, domin yabawa da shugabancin da marigayin ya baiwa wannan yankin namu. “Sai dai kuma, yau sama da watanni bakwai kenan bayan waccan sanarwar, ba wani abin da ya wakana. “Ya Mai Girma, wannan takardar, ta tuni ce, a kan wancan muhimmiyar shawara da gwamnatinka ta zartar.”

Gwamnatin Kaduna Ta Xauki Nauyin Xalibai 6 Su Karanto Ilimin Lafiya A Cuba Daga Umar A Hunkuyi

Babban Sakataren ma’aikatar ilimi ta Jihar Kaduna, Adamu Mansur, ya ce, gwamnatin Jihar Kaduna ta tura xalibai shida qasar Cuba,domin su karanto ilimin kiwon lafiya a qarqashin shirin nan nata na tura xalibai qaro karatu a qasashen waje. Mansur, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai a ranar Talata cewa, xaliban da aka tura sun qumshi biyar mata ne da kuma namiji guda. Kamfanin dillancin labaran, ya hakaito cewa, a watan Yuni ne na shekarar 2017, gwamnatin Jihar ta

Kaduna, ta shelanta keve gurabe 30 ga xaliban da suka ci nasara domin zuwa qaro ilimi a qasar ta Cuba a fannonin na kiwon lafiya, domin cike guraban da ake da su a wannan sashen. Mansur ya ce, xalibai 970 ne suka xauki jarabawar cancantan, inda 124 suka sami matsakaicin maki, aka sake gwada su, aka fitar da 24 daga cikinsu. Sakataren ya ce, domin tabbatar da sakamako nagari, sai aka sake tsananta gwaji a kan 24 xin, inda a qarshe aka fitar da zarata 6, waxanda sune masu tafiyan a halin yanzun. A cewarsa, su ma 24 xin, za a zave su a wani shirin ne

a nan gaba. “Mun zavi Cuba ne saboda zarran da ta yi a wannan fannin na kiwon lafiya, a yanzun haka kuma muna da sama da xalibai 100 waxanda gwamnatin Jiha ta tura su qaro ilimi a waje. “Wasu sun ta fi karanto digiri ne wasu kuwa sun je karanto digirin-digirgir ne, a kan fannin na lafiya da wasu fannonin a qasashen Malesiya, Uganda, Turkiya, Afrika ta kudu da kuma qasar Cyprus. Mansur, ya qarqare da cewa, dukkanin xaliban namu suna yin abu mai kyau, muna samun sakamakon jarin da muka zuba.

•Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose.

An Tsinci Gawar Wani Xan Sanda A Nasarawa Daga Bello Hamza

An tsinci gawar wani jam’in ‘yansanda a unguwar Adudu dake qaramar hukumar Obi ta jihar Nasarawa ranar Talata. Xansandan da ba a san sunansa ba har zuwa yanzu, a na zargin wasu ‘yan ta’adda ne suka kashe shi. Jami’in watsa labaran rundunar ‘yansanda na jihar Nasarawa, Idrissu Kennedy ya tabbatar da wannan labarin

’Yan Nijeriya 136 Da Aka Kuvutar Daga Libya Sun Iso Fatakwal Daga Umar A Hunkuyi Kaso na biyar na ‘yan Nijeriyan da suka sagale a qasar Libya sun iso Fatakwal da jijjifin ranar Talata, Mista Martins Ejike, shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta shiyyar Kudu maso kudu ne ya bayar da sanarwar hakan. Ejike, wanda shugaban sashen ma’aikatan hukumar, Mista Ebhodaghe Eric, ya wakilta wajen karvan mutanan da aka dawo da su xin a cikin Jirgin saman Med-View mai lamba,5N-MAB da misalin qarfe 1:10 na safiya. “Duk sun iso lafiya, face mace guda kaxai da muka kai ta asibiti domin a duba lafiyarta,” in ji shi. Ejike, ya ce, har yanzun akwai

ragowar wasu da aka dawo da su a kashi na huxu, waxanda sun fito ne daga Jihohin Osun da Ekiti. A nan ne ya yi kira ga gwamnatocin Jihohin su da su gaggauta zuwa su kwashe su. Joy Job, xaya daga cikin mutanan da aka dawo da su xin, ta yi godiya ne ga gwamnatin Tarayya a kan cika alqawarin da ta yi na dawo wa da su. Inda kuma ta kwatanta zaman na su a qasar Libya a matsayin, abin tsoro, firgici da kuma tashin hankalin da ba zai yiwu a manta da shi ba. Joy Job, ta ce, ba tare da sanin ta ba, xan Nijeriyan da ya xauke ta a bisa alqawarin sama mata aiki a Kano, ashe wai har ya sayar da ita

ne domin yin aikin bauta ga wani xan Nijeriyan da yake zaune a qasar ta Libya. “’Yan Nijeriya ne suke sayar da ‘yan’uwansu ‘yan Nijeriya domin su yi aikin bauta a can qasar ta Libya, yau a sayar da mu ga wannan, shi ma in ya gama biyan bukatarsa da mu sai kuma ya sayar da mu ga wani, a kullum a hakanan ake. Su mutanan Libya, a hannun ‘yan Nijeriya ne suke sayan mu, sai su yi duk abin da suka ga dama da mu, komai suke so shi suke sanya mu komai xaci komai wahala, ba ka da ta cewa face biyayya kaxai. “A lokacin ni ban san inda nake kan iyaka ne ba a Kano xin, tsakanin Nijeriya da wata qasar ta

daban, ganin kaina kaxai na yi an kewaye ni da bindigogi. “Waxanda suka kama ni xin ne suka gaya mani cewa, matsawar na nemi tayar da qayar baya a wajen za su harbe ni ne, a matsayin sun kashe banza su yi gaba. Hakan ya sanya ba ni da zavi face na bi su. Daga nan, sai Joy Job, ta shawarci ‘yan Nijeriya masu mafarkin zuwa wajen qasarnan da su canza shawara, tana mai cewa, ba abin da ya fi rayuwa a qasarka daxi. A qarshe ta yi kira ga gwamnatin Tarayya da ta ci gaba da kwaso sauran ‘yan Nijeriyan da suke can qasar ta Libya, tsare a gidajen yari daban-daban.

a tattaunawarsa da gidan talabijin xin Channels. Ta ce, xansandan na aiki ne cikin rundunar dake aikin samar da zaman lafiya a kudancin jihar, mutane wasu qauyuka na guje ma gidajensu saboda harin ta’addanci da ake kyautata zaton Fulani Makiyaya ne suka kai. Kennedy ya qara bayyana cewa, an kashe xansandan ne a yayin da shi da abokan aikinsa ke qoqarin kora harin da ‘yanta’addan suka kawo in da suka qona gidajen da mutane suka riga suka fita a qauyukan. Ya ce, hukumarsu na nan tana qoqarin ganin ta kama tare da hukunta waxanda suka aikata wannan munmunan aikin. Matsalolin tsaron da ake fama da shi a faxin qasar nan bai bar fararen hula ba ballatana jami’an tsaro, an ga gawar xaya daga cikin ‘yansanda guda 2 da aka bayyana vacewarsu a jihar Binuwai ranar Litinin 12 ga watan Fabrairu. Haka kuma an kashe jami’ai 2 daga hukumar NSCDC a wani qauye a jihar Binuwai kwanakin baya, ana zargin Fulani Makiyaya ne suka kashe su a qauyen Awange dake mazavar Kasseyo a qaramar hukumar Guma ta jihar.


6 LABARAI

A Yau

Bani Da Alaqa Da Kungiyar Masari Zalla, Inji Gwamna Masari

Laraba 14 Ga Fabrairu, 2018 (27 Ga Jimadal Ula, 1439)

ZIK Leadership Za Su Karrama Gwamna Masari Da Mutane Takwas A Legas Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina na xaya daga cikin manyan mutane tara da aka zava domin karramawa da lambar girma ta ZIK Leadership 2017 a jihar Legas. Sauran manyan Mutanen sun haxa da gwamnan jihar Ribas, Barrister Nyson Wike wanda shima za a karrama da lambar girma ta qyaqyawan shugabanci tare da wani kamfani mallakar tsohon shugaban qasar Afrika ta kudu, Nelson Mandela da tsohon shugaban qasa Ghana Jerry Rawling. Wannan dai yana xauke ne a cikin wata takardar manema labarai da mai taimakawa gwamna na musamman akan harkokin yaxa labarai, Abdu Labaran Malunfashi ya sanyawa hannu kuma ya rabawa manema labarai a Katsina. Kazalika sanarwar ta ce

shugaban kwamitin bada kyaututuka na ZIK, Ferfesa Pat Utomi ya ce an zave waxanda za a karrama ta hanyar lura da irin gudunmawar da suka bayar a sha’anin shugabanci. Ya kuma qara da cewa wannan karramawa ta ZIK ta zama wata babbar lambar yabo tun daga lokacin da aka kirkita shekaru 24 da suka gabata, saboda haka zavan mutane irin su gwamna Aminu Bello Masari a matsayin wanda za a karrama na nuni da yadda wannan lambar yabo take da qima da kuma mahimmanci Shugaban kwamitin shiya wannan gaggarumar karramawa ta ZIK Ferfesa Pat Otomi ya ce za a sanar da ranar da za a yi wannan babban biki na bada kyaututuka ga waxanda aka zava saboda irin gudunmawar da suka bada wajen sha’anin shugabanci a matakin jaha da kuma qasa baki xaya.

bayyana kansa domin cimma nasara akan gwamnatinsa ta kuma qasa baki xaya. Saboda haka sai gwamna Aminu Bello Masari ya ce

duk wanda ya yi wata hulxa da wannan kungiya mai suna ‘Masari Zalla’ ya yi ta akan qashin kanshi ba da yawon gwamna masari akan yi ba.

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

•Gwamnan Masari

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Gwamnan jihar Katsin, Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana cewa baya da wata alaqa ta nesa ko ta kusa da wata kungiya mai suna Masari Zalla saboda haka jama’a su zama shaida akan haka. Wannan yana kunshe ne

acikin wata takardar manema labarai da mai taimakawa gwamna masari akan hulxa da ‘yan jarida, Alhaji Abdu Labaran ya sanyawa hannu kuma akan rabawa manema labaraina Katsina ciki harda Leadership Ayau. ‘’Ina son jama’a su zama shaida bani da masaniya

game da ayyukan wannan kungiya da take ikirarin tana goyan bayana, saboda haka na nisanta kaina da ita baki xaya’’ in ji sanarwar Gwamna Masari ya bada tabbacin cewa yana tare da duk wata kungiya ko wani mutun da ya nuna goyan baya ga gwamnatinsa matuqar ya

Mai Talla Shi Ke Da Riba:

LEADERSHIP A YAU Ta Shirya Tsaf! Kamar yadda kowa ya sani ne, wannan jarida mai albarka, LEADERSHIP A YAU ta kafa tarihi wajen zama jaridar Hausa da ta fara fitowa a kullum. Wannan fara fitowa a kullum yana da alfanu masu yawan gaske, gare mu Kamfanin LEADERSHIP da ku masu karatu, musamman masu sana’o’i manya da qanana. Wannan ne ya sa muke farin cikin shaida wa masu karatunmu cewa mun shirya tsaf domin tallafa wa kasuwancinku, ta hanyar tallata maku shi zuwa inda ba ku zata ba. Domin a halin yanzu mu kanmu da muke buga wannan jarida ba za mu iya bayyana iya inda ta ke shiga ba. Muna da tsare-tasare da dama don talla ku da hajojinku, inda muka fitar da tsarin ‘IYA KUXINKA IYA SHAGALINKA.’ Wato akwai cikakken shafi, akwai rabi, akwai kwata, akwai kuma daidai iyaka abin da mutum ke so a sanya masa. Wanda a wannan shafin muna so masu sana’o’i, musamman manyan dillalai su tallata hajojinsu, su qananan ’yan kasuwa akwai

nasu tsarin. A wani tsarin ma da muke da shi, akwai yanayin da mutum zai tallata hajarsa, sannan ya tallata kansa, inda za a sanya hoton shagonsa, hotonsa da kuma taqaitaccen tarihinsa, kuma wannan duk a kuxi kaxan. Maza ku kasance cikin kashi na farko na masu cin moriyar wannan shiri. Ina ’yan Canji, dillalan yaduka, masu kayan masarufi, mayan da qananan ’yan tireda, dillalan magunguna, masu kamfoni da masana’antu, dillalan hatsi, dillalan mota, masu sayar finafinai da dai sauran masu sana’o’i, ga dama ta samu. A tuntuvemu a lambarmu ta 08148507210, 07036666850, 08039216372, 07037934034, 08032875238 da 08038011382: email leadershipayau@gmail.com. Ko kuma a tuntuvi wakilanmu na jihohi don qarin bayani.


A Yau Laraba 14 Ga Fabrairu, 2018 (27 Ga Jimadal Ula, 1439)

Burinmu Shi Ne Mu Sauqaqa Muku

Ba a chaj in kuxin on ka cire d i j a h c a a B saqonnin watin waya kuxi daga ak na wasu banku

Da zaran an buxe asusu da mu, za a morewa rashin chaji idan mutum ya cire kuxi a akwatin wasu bankuna, haka kuma ba za a riqa cire kuxin saqonnin waya ba.

Domin cimma nasara a hada-hadar banki, ka yi mu’amala da bankin Sun Trust a Yau Ziyarci: www.suntrustng.com

TALLA 7


8 TALLA

A Yau Laraba 14 Ga Fabrairu, 2018 (27 Ga Jimadal Ula, 1439)


A Yau Laraba 14 Ga Fabrairu, 2018 (27 Ga Jimadal Ula, 1439)

TALLA 9

Gaba dai! Gaba dai “Super Eagles”

Bankin Zenith na taya ‘yan qwallon Nijeriya “Super Eagles”, murna sakamakon nasarar da suka samu ta kai wa gasar Cin Kofin Duniya wanda za a gudanar a qasar Rasha.


10 LABARAI

A Yau

Laraba 14 Ga Fabrairu, 2018 (27 Ga Jumada Ula, 1439)

• Shugaban Jam’iyyar NRM, Sanata Saidu Dansadau (na biyu a hagu) a ranar bukin qaddamar da jam’iyyar wanda aka gabatar ranar 3 ga watan Fabrairun 2018 a Babban Birnin Tarayya Abuja.

Dole Mu Kauda Qabilanci Idan Ana Son Xorewar Qasar Nan –Dokta Imam Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

An bayyana rashin kishi da mayar da tsarin qasar nan baya a matsayin jigon abinda ya janyo mana halin da muke ciki yanzu, ya zama dole duk wani kishi da son ci gaban qasar ya lalubo hanyar da za a samu haxin kai da zaman tare ba tare da nuna bambamci ba muddin ana son ci gaban tattalin arzikin qasar nan. Dokta Muhammad Ibn Imam na kwalejin horar da Malamai ta qasa da ke Kontagora ya bayyana hakan a wani lakcar da ya gabatar a babban taron Muryar Talaka ta qasa karo na bakwai da ya gudana a Kontagora. Dokta Muhammad Ibn Imam, wanda ya wakilci Farfaesa Ibrahim A. Gambari, tsohon wakilin Nejariya a majalisar xinkin duniya, ya bayyana qalubalen da ke fuskantar qasar nan, bai rasa nasaba da mayar da tarihin qasar a lokacin mulkin mallaka baya, da tavarvarewar tattalin arzikin qasa da rashin daidaito, sai shi kan shi kundin tsarin mulkin qasar na buqatar gyaran fuska da kuma rashin ingancin hukumomi da shi kan shi tsarin

dimukuraxiyyar qasar, wanda ya samar da rashin nagartar shugabanni. Daktan bai tsaya nan ba, ya ci gaba da cewa duba da irin yadda cin hanci da rashawa, da boko haram wanda rashin aikin yi ga matasa ya haddasa wanda ya taimaka wajen gurgunta karatun jami’o’in a yau, yace abin bai tsaya nan ba, har yanzu qasar na fuskantar matsalar muhalli da rashin samun kayan more rayuwa kamar yadda ‘yan siyasa ke alqawartawa a lokuttan yaqin neman zave ya taimaka wajen qaruwar haxurra a qasar saboda rashin ingantattun hanyoyi. Taron na qungiyar Murtar Talaka na qasa karo na bakwai qarqashin shugabanta na qasa, Malam Zaidu Bala Qofar Sabuwa, Birnin Kebbi. An dai gudanar da taron ne ranar Juma’a 9 zuwa 10 ga watan biyun nan da muke ciki kuma taronta na biyu tun bayan kafa qungiyar a shekarar 2003. Dokta Aliyu Muhammad Muri na xaya daga cikin masu gabatar da qasidu, ya mai da hankali akan qalubalen Arewacin Nijeriya kan matsalar Ilimi da Arewacin Nijeriya ke fuskanta, ya bada

shawarwari yadda za a rage cunkuso a makarantu, da yadda za a rage ma gwamnati nauyin da ke kanta da ya shafi ilimi, da inganta rayuwar malamai. Dakta Mori ya jawo hankalin Iyaye da shugabannin makarantu ta yadda za a sanya Ido da lalubo hanyoyin da ya kamata a mai da hankali dan qarfafawa malamai. Taron ya mayar da hankali kan yadda za a farfaxo da tattalin arzikin Nijeriya da yadda za a inganta tsarin ilimin zamani da na addini a Arewacin qasar. Hakan taron ya samu wakilcin ministan matasa da wasanni, kuma uban qungiyar na qasa Solomon Dalung, wanda Malam Maiwada Xanmalam ya wakilta. Shugabannin qungiyoyi da dama daga sassan jahohin qasar nan sun samu halartar taron. Fittaccen marubucin nan, wanda ya taba lashe kyautar YALI ta Mandela Washington Fellowship wato Ibrahim Aboki daga jihar Bauchi ya bayyana cewar ya zama wajibi shugabanni su san tasirin talaka a qasar nan, su kuma sani irin tafiyar da ake yi yau talaka na yin na shi bisa amana, ya ko zama wajibi a bi duk hanyar da ta da ce wajen ‘yan siyasa

da shugabannin masu mulki sun tsare tare da kare rayukan talakawan qasar nan bisa amana. Yau talaka bai da burin da ya wuce a kyautata mashi rayuwarsa, a samar masa da yanayin zai samu natsuwa, ya iya samun kulawa a fannin ilimi, kiwon lafiya, inganta harkar noma, ingantaccen tsaro ta yadda zai iya samun walwala da cin moriyar arzikin qasar. Da yake bayani ga mahalarta taron, shugaban qungiyar na qasa, Malam Zaidu Bala Qofar Sabuwa, yace ya yabawa mambobin qungiyar bisa nagarta da juriyar da suke nunawa na ganin xorewar wannan tafiya. Yace Muryar Talaka, qungiya ce da ta himmantu akan gwagwarmayar ganin an samar da shugabanci na adalci tare da bayyana ra’ayin talakawa akan quduri ko muradun gwamnati ta yadda zai inganta haxin kai, samar da ingantaccen zaman lafiya a qasa. Dan haka muna yabawa al’ummar qasar nan da juriyar da suke nunawa da haxin kan da suke da shi na haxuwa waje xaya dan ci gaban qasar mu Nijeriya. Shugaban ya tabbatarwa duniya cewar kan mambobin qungiyar haxe yake, dan haka ya jin-jinawa al’ummar

Nijeriya musamman talaka da ya haxiye kwaxayinsa ya jure wajen yin gwagwarmayar ganin qasar nan ta zama dunqulalliya, ina tabbatarwa duniya cewar Nijeriya ita ce kan gaba wajen bunqasar tattalin arzikin qasa bisa jajircewa da qoqarin shugabanninta. Taron ya samu halartar manyan ‘yan siyasa, ma’aikatan gwamnati daga sassan qasar nan, haka an karrama wani jajirtaccen attajiri kuma xan kasuwa, Alhaji AbdulRahman MK da xan majalisar dokokin jiha, Hon. Nura Garba GT bisa qwazo da gudunmawar da suke baiwa al’umma. A qarshe shugaban qungiyar ta jihar Neja, Alhaji Murtala Maigyaxa, ya yabawa qungiyar bisa amincewa da baiwa jihar Neja daman xaukar nauyin wannan muhimmin taro da qasar nan ke buqatar haxa kan ‘yan qasa dan qasar ta zama dunqulalliya. Murtala ya ci gaba da cewar lallai wannan tafiyar zai ci gaba da mai da hankali wajen gwagwarmaya da baiwa shugabanni da gwamnati shawarwari a inda ake buqatar hakan, wannan inuwa ce ta talaka kuma ta himmantu dan kare buqatun talakawa ne.


LABARAI 11

A Yau Laraba 14 Ga Fabrairu, 2018 (27 Ga Jumada Ula, 1439)

Ma’aikatan NHIS Sun Jaddada Goyon Baya Ga Sakataren Hukumar Daga Khalid Idris Doya, Abuja

Wasu daga cikin ma’aikatan hukumar da ke bayar da Inshuran lafiya ta Nijeriya (NHIS), a shekarani jiya ne suka jaddada aniyarsu na ci gaba da mara goyon baya wa babban Sakataren hukumar Inshuran Lafiya Farfesa Usman Yusuf wadda aka dawo da shi muqaminsa na sakataren hukumar biyo bayan zarginsa sama da faxi da dukiyar hukumar. Da suke jawabi wa manema labaru qarin bayani kan dalilainsu na mara masa baya, a shalkwatan NHIS da ke Abuja, Uchenna Ewelike, da kuma Mohammad Shehu Gajo, waxanda suke qarqashin sashin kula da ma’aikatan NHIS, sun nuna qarin guiwarsu ga Usman Yusuf haxe da bayyana sa a matsayin wadda zai cire kitse a wuta. Sun buqaci dukkanin

ma’aikatan hukumar bayar da Inshuran Lafiya da su ci gaba tafiyar da harqoqin aikinsu kamar yadda suka saba ba tare da qoqarin kawo ruxani ko hargitsi gami da zargin juna ba, haxe kuma da qaurace wa biye wa dukkanin masu qoqarin haifar da rikici. Har-ila-yau, sun kuma buqaci vangarorin jami’an tsaro da su tashi tsaye wajen yin aikinsu da bin dokokin da aikinsu da ya shimfixa musu don hukunta dukkanin wani ko gungun jama’an da suke qoqarin kawo ruxani gami da neman haddasa tashintashi a tsakanin ma’aikatan hukumar a yayin da suke kan aiyukansu. Suka ce, “a matsayinmu na ma’aikatan gwamnati, muna da qa’idojin da kuma sharuxan da aikinmu da ya gindaya mana, don haka ba za mu amince da qoqarin wasu na kawo ruxani waxanda manufarsu baiwa

cin hanci da rashwa gindin zama ne, za mu tava basu qofa ba, don haka za mu ci gaba da yin aikinmu yadda ya dace”. Sannan kuma, sun yi qira ga vangaren qungiyar ma’aikatan lafiya, MHWN da ASCSN da su yi qoqarin xinke barakar da ke akwai a tsakanin vangarorin d suke qarqashin hukumar NHIS haxe da samar da ci gaba mai ma’ana domin tafiyar da aiki yadda ya dace, kana sun kuma shawacesu daure su ci gaba da bayar da gudunmawarsu domin taimaka wa jama’an qasa. Uchenna Ewelike ya gode wa shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a bisa wanke babban sakataren hukumar Inshuran lafiya ta Nijeriya Farfesa Yusuf bisa zargin cin hanci da rashawa haxe da wawuson dukiyar hukumar da aka yi zarginsa da yi.

Sakataren Hukumar Ciyar Da Xaliban Zamfara Ya Fara Rangadi Daga Hussaini Baba Gusau

Sakataren Hukumar ciyar da xalibai na Jihar Zamfara, Malam Atiku Sani Maradun, Sa’in Zamfara, ya fara rangadi a makarantun kwana da na jeka ka dawo dake faxin jihar ta Zamfara. Wannan rangadi an fara shi ne domin ganin yadda ake ciyar da xalibai a cikin makarantu. Tawagar Sakkataren ta dira a Makarantar Sakandiren jeka ka dawo da ke ‘Yandoton daji da ta Shemori. Malam Atiku Maradun ya bayyana wa shugaban Makarantar Yandoton daji cewa, tawagar Hukumar na ziyarar ba-zata ne don gane wa idanunsu yadda ake dafa wa xalibai abinci da kuma abubuwan da muke bayar wa yana isa, kuma babu wata matsala ga ‘yan kwangilar masu kawo abincin, idan kuma akwai matsala muna son a bayyana mana su don magance su. Shugaban Makarantar Sakandiren ‘Yandoton Malam Shuaibu Aliyu Ibrahim ya bayyana jin daxinsa ga tawagar Sakataren Hukumar, inda ya bayyana masa cewa, babbar matsalarsu ita ce wajen dahuwar abincin ciki kenan yana da matsala don ba shi da wadata, wasu tukwanan a waje ake ajiye su don yin dahuwar abincin. “Dan haka muna roqon da a qara faxaxa mana shi. Sai kuma muna buqatar qarin Biredi da qwai don wannan zangon karatun xalibai na qaruwa.” in ji shi Shugaban ya yaba wa Sakataren da yake rangadi makarantun dan

warware matsalar ciyarwar xalibai. Shima Shugaban Makarantar Sakandiren Shemori, Malam Garba Umar ya bayyana cewa, wannan tawagar, tawaga ce ta tabbatar da ganin amanar da aka bamu mun riqeta tsakanin da Allah, lallai wannan Hukumar na iyaka qoqarinta na jin daxin xalibai Kuma sanadiya Wannan ciyarwa ya sa xalibai na zuwa Makarantar da wuri, dan sun san akwai abincin tara nan najiran su.muna godiya akan haka.sai kuma ya bayyana matsalolin sa Kamar yadda takearansa na ‘Yandoton ya bayyana. Ansa jawabin Sakataren Hukumar Malam Atiku ya bayyana cewa’’ Gwamnatin Gwamna Abdua’ziz Abubakar Yari na iyaka qoqarinta na ganin ta ciyarwa da xaliban makarantun Kwana da na jeka kadawo dan ganin an samu ingantacen Ilimi a faxin jihar. dan haha duk lolaci bayan lokaci tawagar mu nazagauawa danganin yadda ake ciyar da xaliban. Kuma Sakataren ya Umarci shugabanin Makarantun da su riqa duba hatsin tunkafin adafa shi kuma su Tabbatar sune suka fara xanxanawa kafin arabawa xalibai dan idan akwai matsala nan take Sai axau mataki.kuma duk abincin da basu gamsu da ingancin sa ba karda su bari adafa shi a sanar da mu dan daukar mataki.kuma aduk qarshe watau idan an samu qarin xalibai a gaggauta samar da mu.kuma naji xaxin yadda ake dahuwar abincin da Kuma yadda ake rabawa xalibai abincin. Haka kazalika ma Tawagar

•sakataren NHIS, Farfesa Yusuf.

A makon jiya ne dai wasu ‘ya’yan qungiyar da wasu manyan ma’aikatan lafiya suka gudanar da wani zangazangar lumana kan qin amincewa dawo da Farfesa

Gwaman Bauchi Ya Rushe Dukkanin Shuwagabanin Gudanarwa Na Kwalejin Aikin Gona Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

•Sakataren Zartarwa na hukumar ciyar da xalibai na jihar Zamfara.

Sakkataren Hukumar ta ziyarci fadar unaban Qasar ‘yandoton Alhaji Aliyu Garba Marafa, Sakataren ya bayyana ma Uban Qasar cewa, hukumar ta fito ne dan gane ma idanun ta yadda ake dafawa xalibai abinci da rabashi da Kuma ingancin sa.kuma muna godiya da gudunmuwar da iyayn qasa ke badawa wajan cigaban wannan Hukumar. Uban Qasar ‘yandoton, Alhaji Aliyu Garba ya bayyana cewa’ mu babu abunda zamu cema wannan gwamnati sai Allah sanbar ka, ita Kuma wannan Hukumar Allah ya qara maku ikon ciyarwa da wannan Hukumar gaba Kuma wannan amar da kuke bibiya dan ganin ku tababtar da gaskiya yadda ake ciyar da xalibai akan haka kun cancanci yabo a wajena.

Yusuf kujerarsa ta sakataren hukumar Inshuran lafiya biyo bayan zargin da hukumar EFCC ta yi masa na sama da faxi da dukiyar hukumar.

Gwamnan Bauchi Muhammad Abdullah Abubakar ya sanar da rushe dukkanin shuwagabanin gudanarwa na kwalejin ilimin nazarin albarkatun qasa ‘gona’ ta jihar Bauchi ba tare da vata wani lokaci ba. Bayanin hakan na qunshe ne a cikin wata sanarwa daga fadar gwamnatin Bauchi xauke da sanya hanun Sakataren gwamnatin Bauchi, Alhaji Muhammad Nadada Umaru wadda wakilinmu ta yi tozali da kwafin takardar a Litinin xin nan. Gwamnan ta cikin sanarwarsu ya bayyana cewar wannan dakatarwar nan take zai fara aiki ba tare da jiran-jira ba, haka kuma gwamnan jihar ya amince da naxin kwamitin riqo na kwalejin aikin gona domin ci gaba da tafiyar da harqoqin kwalejin yadda ya dace. Kwamitin da gwamna ya naxa a matsayin na riqo su ne Farfesa Muhammad D. Abubakar a matsayin shugaban kwalejin na riqo, Abubakar Gabi kuma ya kasance shugaba mai kula

da sha’anin kuxi, Dakta Ali Hussaini kuma ya kasance a matsayin magatakarda kwalejin na wucin gadi. Sanarwar gidan gwamnatin ta bayyana cewar wannan rushewa da kuma kafa hukumar gudanarwa na qikon nan take zai fara aiki ba tare da vata wani lokaci ba. Idan dai baku mance ba; wannan jaridan mun sha kawo muku rahotonni kan hatsaniyar da ke cikin wannan kwalejin, inda qungiyar ASUP na kwalejin suka yi ta shelanta matsaloli da suke zargin shuwagabanin gudanarwa da aikatawa ciki kuwa har da batun bayar da takardar kammala kwalejin ta barauniyar hanya, wadda hakan ya yi nuni da cewar kwalejin na fuskantar matsalar shugabanci, haka kuma sun yi zarge-zarge da dama. Daga bisani dai ASUP ta rubuta takardar kokenta ga gwamnatin jahar, wannan dalilin ne wasu ke ganin gwamnatin ta bincika gami da yanke wannan hukuncin na rushe dukkanin shuwagabanin gudanarwa na kwalejin nan take.


12 LABARAI

A Yau

Laraba 14 Ga Fabrairu, 2018 (27 Ga Jumada Ula, 1439)

Qabilar Fulani Suna Cikin Qunci Fiye Da Sauran Qabilu A Nijeriya, In ji Maigamo Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

An bayyana halin da al’umman Fulani suke ciki a faxin Nijeriya da cewar wani hali ne na qunci wadda sauran qabilu suka fi su cin ribar romon demokraxiyya wadda kuma hakan bai kamata ake samun irin wannan banbancin a tsakanin qabilu ba. Babban Akauta Janar na Jihar Bauchi, Alhaji Abdullahi Maigamo shi ne ya bayyana hakan a lokacin da ke jawabi a wajen wani taron da ya shirya wa ‘yan uwansu Fulani domin tattaunawa kan muhimman matsalolin da suke ci wa Fulani tuwo a qarya da nufin shawo kansu don daidaita adalci a tsakani haxe kuma da zaburar da shuwagabani kan hoqqoqin Fulani a kawukansu wadda ya guda a Asabar xin nan a IBB Square da ke Bauchi. Maigamo ya yi amanar cewar al’umman Fulani suna da muhimmanci wajen ci gaban al’umma ta fuskoki da daman gaske, yana mai bayanin cewar samar musu da ababen more rayuwa ka iya taimaka musu wajen ci gaba da wanzuwar tattalin arziki. A bisa haka ne ma ya yi qira da babban murya ga gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar domin ya tashi tsaye don yi wa al’umman Fulani aiki daidai da kowace qabila don wanzuwar adalci. Ya ce, maqasudin shirya

taron domin su haxu su koka wa gwamnan jihar ta Bauchi dangane da buqatun da Fulani suke da shi domin su ma su samu cin moriyar romon demokraxiyya “dalilin shirya wannan taron domin mu taru mu koka wa mai girma gwamna Bauchi Barista M.A Abubakar saboda buqatun da Fulani suke da shi a qasar nan. A dukkanin qabilun da suke cikin Nijeriya babu qabilar da take cikin qunshi kamar qabilar Fulani. Don haka muka taru muka kuma kawo wa gwamnan jiharmu kukanmu domin ya yi mana aiyuka kamar yadda ake yi wa sauran mutane,” A cewarsa Ya ce, “daga cikin buqatun da Fulani ke da su a halin

yanzu sun haxa da shanunmu, su samu ruwan da za su sha, shanunmu su samu abincin da za su ci. sannan kuma mai girma gwamna ya tsaya ya taimaki Fulani ta fuskoki da dama. Allurar da ake yi na su rigakafi a da cancan muna qira a sake dawo da shirin domin Fulani su amfana”. Kamar yadda ya shaida. Maigamo, wadda kuma har-ila-yau shi ne Dattowa Mangan Wunty ya yi bayanin cewar sun so su yi ido huxu da gwamnan Bauchi a wannan taron, amma sakamakon ta’aziyyar da ya je yi wa shugaban qasa bai samu halartar wannan taron ba, sai ya buqaci Fulani da cewar za su kuma sake shirya wani

babban taro wadda gwamnan zai samu zuwa a ranar lahadi mai zuwa, don haka ne ya buqaci Fulani a duk inda suke a faxin jihar Bauchi da su fito su halarci wannan taron domin tattauna muhimman matsalolin da suka addabi al’umman Fulani a jihar Bauchi da ma qasa baki xaya. Da yake jawabi a madadin gwamnan jihar Bauchi, sabon Kwamishinan ma’aikatar kuxi na jihar Bauchi, Garba Muhammed Sarki Akuyam ya jinjina wa dukkanin Fulani makiyaya da suke jihar Bauchi a bisa haxin kai da suka baiwa gwamnatin jihar ta fuskacin tabbatar da zaman lafiya a faxin jihar, sai ya gode musu da hakan da buqatar su

qara ninka azamarsu domin wanzar da wannan zaman lafiyar da ta ke kawo ci gaba ta fuskacin komai. Ta bakinsa “Dukkanin duniyar nan babu mai zuri’a kamar ta Fulani, saboda haka babu wani mutum ko kansa da qahune da zai zo ya ce wai wani bafulatani ba zai keta wani jeji ko ba zai keta wani qasa ba; babu wannan mutumin a duk duniya”. A cewar gwamnan. Saboda haka gwamnan ya ce dukkanin wasu dokokin da suke qoqarin kawo ruxani da kuma haifar da rikici a tsakanin manoma da makiyaya ya ce tuni gwamnati ta fitar da tsarin da yanzu haka ake kan aiki a kai domin wanzar da zaman lafiya a tsaqani, sai ya shaida wa fulanin cewar nan gaba kaxan za su yi walwalasu yadda suke so a faxin jiharsa ta Bauchi ba tare da wani tsangwama ba, ya horesu da su kasance masu ci gaba da mara wa shiryeshirye da kuma tsare-tsaren gwamnati baya domin a samu kaiwa ga gaci. Ababen da suka faru a wajen taron tattauna matsalolin da suka jivinci fulanin wadda ya guda a Bauchi, an karrama babban Akwauta Janar na jihar Bauchi da lambar yabo mutum mai gwazo wajen ci gaban jama’arsa, lambar yabon wadda wani shugaban wata jarida ya ba shi.

Rayuwar Sarkin Zazzau Alheri Ne Ga ’Yan Nijeriya -Alhaji Ali Ba-Kware Daga Balarabe Abdullahi, Zariya

An bayyana rayuwar mai martaba Sarkin Zazzzau Alhaji Shehu Idris a matsayin Sarkin Zazzau shekara 43 da suka gabata da cewar, alheri ne ga duk wani xan Nijeriya, musamman in an dubi yadda yak e bayar da gudunmuwarsa na tabbatar zaman lafiya a shekarun day a yi a karagar Zazzau. Wannan bayani ya fito ne daga bakin tsohon shugaban ‘yan kasuwar takin zamani da ke P/Z a zariya, a lokacin day a zanta da wakilinmu kan cikar sarkin Zazzau shekara 43 da naxa shi Sarkin Zazzau a shekara ta 1975. Alhaji Ali Ba-Kware ya ci gaba cewar, babu ko shakka duk wanda ya ke saurarorn jawaban mai martaba sarkin Zazzau, zai yadda cewar, babu abin da ya sa a gabansa kamar batun zaman lafiya, da in

ya samu, daga nan ne za a sami duk wani ci gaban da ake buqata. Wannan batu na zaman lafiya da Mai martaba sarkin Zazzau ya sa a gabansa shekara 43 da suka gabata, al’ummomin wasu jihohi ma sun amfana, musamman in an tuna, a cewar Alhaji Ali Bakware, a lokacin mulkin tsohon shugaban qasa Cif Olusegun Obasanjo, mai martaba sarkin Zazzau ya jagoranci kwamitin tabbatar da zaman lafiya a Yelwan Shandam, wanda wannan kwamiti, shugaban qasa Obasanjo ya kafa. Kuma tun kammala aikin da aka xora wa wannan kwamiti, batun duk wata tashin-tashina ta zama tarihi a xaukacin yankin Yelwan Shandam, da sauran garuruwa da suke kusa da wannan gari da aka daxe ana yin faxace-faxacen qabilanci, matsalolin suka

zama tarihi har zuwa yau. a cikin xan qanqanin lokaci. Alhaji Ba-Kware ya yi A qarshen ganawar alhaji amfani da wannan daman a Ali Ba-Kware da wakilinmu, zantawa da wakilinmu, inda ya yi kira da sauran ya yi kira ga gwamnatin sarakuna da suke arewacin tarayyar Nijeriya, da Nijeriya das u riqa koyi da qarshen wannan shekara ta 2018, ta sa sunan mai martaba Sarkin Zazzau a cikin jerin sunayen waxanda za a bas u lambar girmama ta qasa, a ba shi lamban yabo, kan gudunmuwar day a ke bayarwa, domin ci gaban ‘yan Nijeriya da kuma Nijeriya kan ta. Da kuma Alhaji Ali Bakware ya juya ga batun matsalolin tashin-tashinar da ke faruwa a tsakanin wasu qabilu da makiya kuma, sai ya yi kira ga gwanatin tarayya da ta kafa kwamiti mai qarfi a qarqashin mai martaba Sarkin Zazzau, wanda ya na da tabbacin in har aka sa mai martaba Sarkin Zazzau a gaba, ire-iren waxannan matsaloli za su zama tarihi • Sarkin Zazzau

mai martaba Sarkin Zazzau na tabbatar da zaman lafiya a masarautunsu, kamar yadda sarkin Zazzau ya saw a gaba shekara 43 da suka gabata.


LABARAI 13

A Yau Laraba 14 Ga Fabrairu, 2018 (27 Ga Jumada Ula, 1439)

Hana Xaliba Zama Lauya: FOMWAN Ta Buqaci Gwamnatin Tarayya Ta Shiga Lamarin Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Qungiyar Mata Musulmai wato FOMWAN ta yi qira da babbar murya ga gwamnatin tarayya da ta shiga cikin rikicin Xalibar da aka hanata samun zarafin kasancewa LAUYA bisa sanya hijabi da kuma qin amincewa da kauce wa dokar hijabi da xalibar ta yi. Shugaban qungiyar mata musulmai ta qasa FOMWAN reshen jihar Bauchi, Hajiya Yagana Muhammad Gidado ita ce ta yi wannan qiran a wajen taron bikin ranar Hijabi ta duniya wadda ya gudana a birnin Bauchi, taron wadda aka yi a xakin taro na babban masallacin Bauchi a ranar Lahadi. Yagana ta bayyana cewar da buqatar gwamnatin tarayya ta shigo cikin lamarin wannan baiwar Allah da aka hanata zama lauya a sakamakon sanya hijabi, tana mai bayanin cewar hijabi umurnin ne na Allah maxaukaki ga dukkanin wata baliga don haka bai dace a ce a qasa irin ta Nijeriya a samu aukuwar irin wannan matsalar ta qin amincewa da mace a sakamakon hijabinta ba. Ta bayyana cewar hijibi suturace wacce ta zamana wajiba ga kowace baliga don haka ba za su zura ido ake keta haddin hijabi haka

siddan a qasar nan ba. Wakilinmu ya shaida mana cewar an gabatar da jawabi da kuma muhimman lakcoci kan muhimmancin sanya hijabi da kuma dokar Allah a kan ‘ya mace kan sanya hijabi, an qarfafi taron ne dai da bayyana cewar ita hijabi wajibi ce ga kowace baliga wanda Allah maxaukaki ya sanya mata domin kare mata mutuncinta da kuma kiyayewa, kana taron ya

maida hankali kan masu amfani da hijabi wajen vata haqiqanin hijabi ta fusakcin yin aiyukan ta’addanci ko na savon Allah. Da take jawabi a wajen taron, matar Gwamnan Bauchi, Hajiya Hadiza Muhammad Abubuakar ta bayyana cewar shi wannan hijabin da mata ke sanyawa umurni ne na Allah Ta’ala ne, kuma dokarsa ce domin kare mutuncinsu mata, ta

•Firdausi da aka hana zama Lauya kwanakin baya saboda Hijabi.

bayyana cewar duk matar da take yin wasa da wannan dokar Allah zai hukuntata. Ta qara da cewa, a gefe guda bayan bayyana muhimmanci hijabi da suke yi, suna kuma faxakarwa kan abubuwan da suka kamata wanda a bisa hakan zai taimaka ta fuskacin fahimtar da kowa muhimmancin hijabi “har waxanda suke qyamar hijabin ma su dawo suna son sanya shi. Faxakarwar nan kuma ta fuskokin da suka dace kamar a nuna masu cewar hijabin nan ba rigar ta’addanci bace, ba kuma tauye haqqin mata bane, ba quntata wa mata bane. Hijabi rigace ta musulunci ta kare haqqin mata da kuma mutunuta su kana hijabi na qara wa mata kima”. In ji ta Daga bisani ta shawarci ‘yan uwa mata da su daure suke qoqarin bin wannan umurnin na Allah na sanya hijabi, ta bayyana cewar wannan ranar na hijabi ta duniya ranace da ke da muhimmanci a wajen mata “Yanzu ka ga har kiristoci kan taya mu yin wannan ranar, inda suke sanya hijabi a wannan ranar domin nuna mana goyon baya kan sanya hijabin”. Da take yi wa LEADERSHIP qarin bayani kan wannan taron, shugaban qungiyar mata musulmai reshen jihar Bauchi, Yagana Muh’d

Gidado ta bayyana cewar abun takaici ne a samu wasu mata na sanya hijabi suna aikata munanan halaye ta bayyana cewar tun da fari ma ya kamata ne mata suke sanin cewar hijabin an sanya musu shi ne domin kare musu mutuncinsu. Ta kuma bayyana cewar bai kamata mata suke sanya hijabin da nufin aikata muggan xabi’u ba. Ta nuna cewar yana da muhimmancin gaske kowace mace ta sani wajibi ne a kanta sanya hijabi, ba wai ana sanyawa ne domin ra’ayi ba. Wakilinmu ya shaida mana cewar an raba hijabai da daman gaske wa mahalartar, hijabin wanda ya wadatu da kuma hava kamar yanda ya dace ba irin hijibin zamanin nan ba. Har ila yau an raba kyaututuka ga wasu qugiyoyin mata da suke halarci tarun. Wasu da muka zanta da su sun sha alwashin sauya xabi’unsu na yin sakaci da kula da martabar hijiabi da kuma bin dokokin da ke tattare da hijabi domin kaucewa fushin Allah a garesu. Sun yi kuma bayanin cewar wannan taron da jawaban da suka ji ya qara musu azama da kuma qumajin ci gaba da kiyaye dokokin hijabi a garesu. Mahalartan dai sun sanya manyan hijabai da kuma nuna alaminsa ga mahalarta.

Jami’ar Filato Ta Kammala Shirin Xaukaka Darajar Kwasa-Kwasai 15, Inji Dohnan Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Shugaban jami’ar Jihar Filato (PLASU) Farfesa Dohnan Sheni a Litinin xin nan ya bayyana cewar jami’ar ta kammala dukkanin shiryeshiryen xaukaka darajar kwasa-kwasai xai-xai har guda goma sha biyar 15 biyo bayan samun amincewa da kuma cike sharuxan hakan daga hukumar da ke kula da jami’o’i ta Nijeriya (NUC). Shugaban jami’ar wadda ya bayyana hakan a lokacin da suke ganawa da manema labaru a ofishin majalisar zastarwa na jami’ar da ke kuma cikin jami’ar. Ya ce, “Dukkanin abubuwan da suka dace tuni aka samar da su domin xaukaka darajar kwasa-kwasai guda goma sha biyar 15 wadda muka samu izinin hakan daga hukumar NUC, za kuma a yi qarin xaukaka daraja wa kwasakwasan ne zuwa watan Mayun wannan shekarar”.

“Kwasa-kwasai guda 17 ne aka yi mana qarin girmar xaukakansu a shekaru biyu da suka gabata, yanzu kuma muna kan shirye-shiryen samu qarin guda 15 daga hukumar NUC”. Sheni, ya shaida cewar wa’adin aikinsa zai kai ga qarewa ne zuwa watan Fabrairu, yana mai nuna matuqar godiyarsa ga Allah a bisa dumbin nasarorin da ya kai ga cimmawa a wa’adomsa karo na biyu da ya shafe yana shugabantar jami’ar, wadda ya ce ya samar wa jami’ar ciki gaba sosai a yayin da ke bakin aikinsa. Ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da ya cimma, daga ciki ya bayyana cewar akwai qarin xaukaka darajar kwasakwasai 17 tun lokacin da aka qirqiri jami’ar a shekaru 12 da suka shuxe, haka kuma ya bayyana cewar an shirya babban taron jami’ar a shekarar da ta gabata. Ya qara da cewa bayyana wasu daga cikin nasarorinsa

a matsayin shugaba da cewa “mun iya samar da kammalalle kuma ginannen xakin bincike da nazarin ilimi ‘Library’, mun kuma samar da hanyoyin sadarwa, gyaran wurare, samar da filin wasanni, mun kuma samar da xakunan gwajegwajen ilimi daban-daban da suka haxa da na harshen nasara Ingilishi, sashin yanar gizo-gizo, hasken wuta daga NESCO haxe kuma da gina xakunan kwanan xalibai masu dumbin yawa”. “Iyaye da daman gaske suna haba-haba ‘ya’yansu su samu izinin karatu a wannan jami’ar domin yadda aka inganta PLASU a wannan lokacin ma mun baiwa xalibai 1,500 izinin karatu a wannan jami’ar.” Da ya juya kan dumbin matsalolin da suke jibge suka maqale a cikin wannan jami’ar ta jihar Filato, shugaban jami’ar ya bayyana cewar matsalolo da qalibalen sun haxa da qarancin rowan amfanin yau da gobe, xakunan kwanan ma’aikata,

wutar layin kan hanya, qaracin ma’aikata da kuma qarancin kuxi day a dabaibaye jami’ar. Shugaban dai ya yi amanan cewar kwasa-kwasan da suka ta faxi tashin ganin sun samu

• Farfesa Dohnan Sheni

qarin xaukaka hakan zai kai ga inganta jami’ar da kuma xaukaka darajar koyo da koyarwa a faxin jami’ar wadda ya shaida hakan a matsayin ci gaba kuma gagaruma.


14

A Yau

Laraba 14 Ga Fabrairu, 2018 (27 Ga Jumada Ula, 1439)

Daga Na Gaba...

08036954354

Tare da Abdurrahman Aliyu

Su Wa Ke Yi Wa Talakawan Nijeriya Tunani? Irin halin da wannan qasar ta shiga tun daga shekaru huxu da suka wuce, ya zuwa yanzu ya kamata ace talakan wannan qasa ya shiga taitayinsa, musamman ta fuskar zave da tura wakilai a inda suka dace. Amma wani abin mamaki kullum wuri guda ake ba wani cigaba ko wata sabuwar hanya wadda zata nuna cewa lallai talakawan wannan qasar sun ji a jikinsu. Duk qoqarin kiran sauyin da suke a baki ne kawai, amma a zahiri ba haka abun ya ke ba, domin a zukatansu da aikace babu sauyin , asali ma ba su san me ake kira da wannam sunana sauyi ba ko kuma canji. Abin da na lura talakawan wannan qasa ke nufi da canji shi ne a fitar da wani wanda ke bisa mulki a kawo wani ko da kuwa wanda za a kawo xin bai kai nagartar wancen ba in dai an fitar da shito su a wajensu buqata ta biya. Shi ma wannnan xin da aka kawo kuma ba sai ya xauki lokaci ba wasu daga cikin talakawan za su fito su fara ikirarin sai sun sauya shi, wannan xabi’a kusan tana cikin abin da ya ke ciwa wannan qasa tamu tuwo a qwarya. A yau wanan fili zai yi duba ne kan wasu abubuwa da kullum suke kawo wa wannam qasar tarnaqi da koma baya, musamman ta la’akari da ,aven qananan hukumomi da aka gudanar a Kano ranar asabar xin da ta wuce 10/2/2018. Wannan zave da aka gudanar akwai abubuwan dubawa da yawa a cikinsa, da farko dai zave ne wanda Jihar Kano ta shirya a qarqashin hukumar zaven jihar, shi wanda ke shugabanci hukumar gwamnatin ce ta naxa shi bisa wannan muqami, kuma tun da aka naxa shi ake ta tayashi murnar ya samu babbar kujera, sannan wani abun mamaki shi wanda aka naxa wannan hukuma wai Farfesa ne, wanda ana ganin cewa ko ba kome ya na da wani tunani dabam da na sauran mutane, musamman a vangaren ilimin boko, shi ya sa ake ganin zai iya jagorantar duk wani abu da aka bashi wanda za a iya yi wa al’umma adalci kuma a qwato masu haqinsu, sannan a matsayinsa na Farfesa kuma mai ilimi ana tunanin zai yi koyi da sauran Farfesa ya yi abin da zai bar wa kansa da iyalansa tarihi mai kyau ta yadda na xalibansa za su iya yin alfahari da shi kuma su yi koyi da shi a matsayin wanda ya yi wani abu mai kyau. Tun tashin farko yadda aka sayar da takardar shedar yin

takarar da kuxi tsagaga alamu suka nuna cewa ba za a yi adalci ba ga zaven wanda hakan ne ya sa wasu jam’iyyun adawa suka kasashiga, zaven saboda a matsauinsu na waxanda basu da gwamnati a hannu kuxaxen da aka sanya ya yi masu yawa, amma hakan bai sa aka rage waxannan kuxaxe ba. To duk ba ma wannan ne qbun qorafi ba ko tayar da hankali,sai yanayin yadda aka gudanar da zaven, na farko dai an samu mutuqar jinkiri na rashin kawo kayan aiki a rumfunan zave da wuri, inda wasu rumfunan sai qarfe biyu na rana aka kawo kahan aiki, sannan aka fara zaven duk da cewa ba a samu mutane sun fito da yawa ba wajen kaxa quri’a. Babban abin da ya fi kome takaici shi ne yadda aka riqa nuna hotuna da bidiyon yadda ake gudanar da zaven, in da a rumfuna da yawa aka samu qananan yara sun bi layi zasu kaxa kuri’a kuma an basu sun dangwala sun jefa. Sai kuma bidiyon da aka samu wanda ya nuna yadda ake ta dangwale quri’un ana jefawa, wasu ma ba a runfunan zaven ba ne a gidaje ne ake dangwalewar. Kusan dukan kagafen yaxa labarai na qasar nan sun haqalto wannan kwamacala wadda ake ce wai zave ne. In da tashin hankalin yake ta yadda shi shugaban hukumar zaven ya fito ya ayyana cewa jam’iyyar APC mai mulkiita ta cinye wannan zave baki xaya, kuma an yi zaven cikin lumana da kwanciyar hankali ba tare da samin qorafin maguxi ko wani abu da ya savawa doka ba. Yanzu ace mutumin da ya kai girman Farfesa ya shirya irin wanan abun kuma bai ji kome ba a rayuwarsa, gani yake ya yi daidai? Shin yaushe ne to qasar nan zata gyaru in har mai ilimin kamar farfesa zai ba da goyan baya a aikata rashin daidai a qasar nan kuma ya nuna daidai ne, wannan ya nuna ko a cikin aji ba bu abin da ya ke koyawa xalibansa sai abin da yake ba daidai ba, wanda ya haxa da rashin gaskiya da kuma hanyoyin vatar da al’umma. Babban qarin tashin hankalin shi ne yadda shi Maigirma gwamana ya shirya bikin rantsar da waxannan mutane da aka ce zavarsu aka yi ba tare da yaji kome ba a rayuwarsa, wannan wace irin qasa ce wadda za a ce mutum mai shekaru kamar na Maigirma gwamanan Kano, kuma sannan mai riqe da muqamin gwamna zai goyi bayan qarya qiri-qiri domin

kawai ya na son cimma wata manufa ta shi wadda iyakar ta nan duniya, shin mai girma gwamna bai tunanin cewa akwai mutuwa? Kuma za a tambayeshi kan abin da ya shuka, me yasa mai girma gwamna ba tuna cewa waxannan mutane da ya rantsar a bisa muqaman da ya naxa su, ba zasu iya tsinana mashi kome ba a lahira, iyakar shi da su nan duniya. Ya na da kyau ko ba kome idan shekaru suka taru ga mutum to ya riqa tunanin lahira kawai ba wai abin da zai zama a duniya ba. Su kuma waxanda suka shirya wannan kwamacala su tuna cewa da yawa sun yi makamancin irin abin da suka yi a baya, amma yamzu suna ina? Idan muka koma ta vangaren talakawa kuwa zamu ga cewa lallai lamarin talakan Nijeriya akwai sake cikinsa, na farko ya kasa gane cewa an hana shi ilimi, sannan ya kasa gane cewa shi bawa ne na wasu ya tashi ya nemi ‘yanci tun wuri bai qure masa ba. Domin duk mutanen da suka yi wannan aikin zaven talakawa ne, ya kamata su gane cewa waxannnan mutane da suka sanya su yin wannan aiki tsallakewa kawai za su yi su barsu domin ba zasu amfane su da kome ba, amma saboda tsabar Jahilci da rashin sanin ciwon kai, sai ga su a hoton bidiyo, wani sokon ma a cikin gidansa suna dangwale quri’un mutane kan kuxi qalilan, waxanda tabbas na san yazuwa wannan rubutun kuxin sun qare.

Ya na da kyau tallakan Nijeriya ya sani cewa, damar kawo gyara ko sauyi a hannunsa ta ke, in ya gyaru to kome zai gyaru, in kuwa tallakawa za su vigaba da yin irin wannan hali da sukayi a Kano to lallai babu ranar da wannan qasa zata samu canji, za ai ta tafiya ne wuri buda ba gaba ba baya. Don haka, yana da kyau talakawa su shiga taitayinsu, su sani cewa wannan hali da suka sa kansu ciki to fa ba zai ville ba, kuma ba nufo hanyar gyara ba, talaka a bangar siyasa ai banza a banza ne kawai. Babban qalubale kuma ga jam’iyyar APC ya ke, in dai da haske jam’iyyar APC su ke na ganin sun kawo sauyi mai amfani to ya zama wajibi su faxi matsayarsu kan wannan zave na Kano, su takawa wannan zave burki kuma su fito su barranta da shi, domin in har za su riqa cewa, jam’iyyar PDP ta lallata qasar nan, sannan sun kawo maguxin zave da sauran abubuwa na cin hanci da rashawa, amma kuma su shirya zave irin na qananan hukumomin Kano to lallai ba a xauko hanyar gyara ba kuma ba da gaske suke, sannan su vannar su ma ta fi ta bayan, domin su an zave su ne saboda ana kyautata masu zaton zasu kawo gyara, amma kuma abun ya gagara. Don hakaqalubale ne garesu su tashi tsaye su magance wannan matsala, kuma a hukunta duk mai hannu a cikinta, domin masu iya magana dai sun ce, “ Juma’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake gane ta”


A Yau Laraba 14 Ga Fabrairu, 2018 (27 Ga Jumada Ula, 1439)

RAHOTO 15

Yadda Tambuwal Ya Inganta Ayyukan Hukumar Kashe Gobara A Sakkwato Daga Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto

Duk da muhimmanci da tasirin da ke ga Hukumar Kashe Gobara a rayuwar al’umma amma Jihohi 15 ne kacal suke ta Tashoshin Kashe Gobara a qasar nan wanda hakan yake matsayin babban qalubale da haxari ga al’umma da dukiyoyinsu. A watannin da suka gabata kafafen yaxa labarai sun ruwaito Kunturola - Janar na Hukumar Kashe Gobara ta Qasa , Joseph Anebi yana bayyana cewar sun damu qwarai da rashin ingantattun tashoshin kashe wuta a wasu jihohin domin a cewarsa Jihohi da dama ba su da Hukumar Kashe Gobara wadda ke aiki yadda ya kamata. Shugaban Hukumar ta Qasa ya bayyana hakan ne a yayin da manbobin Kwamitin Ayyukan Cikin Gida na Majalisar Wakilai suka ziyarci Hedikwatar Hukumar a Abuja tare da kira ga Majalisa da ta hanzarta wajen gyaran fuska ga Kundin Dokar Kashe Wuta ta 1963 domin qarfafa kafa Cibiyoyin Kashe Wuta a faxin qasa bakixaya. Shakka babu ruwa da wuta a cikin tsarin rayuwar al’umma suna matsayin sinadarin maslaha ko akasinta. Hasalima yawaitar ko rashin xaya daga cikinsu a kan iya canza matsuguni, masalaha a kai, annobar varnar ruwa a qarshe ta kan iya zama gyara, savanin annobar bala’in gobara wadda jaje, neman taimako, da addu’o’i kan biyo baya. A bisa ga gani ko jin tarihin yadda bala’in annobar wuta ke salwantar da rayuka da dukiyoyin al’umma, shigarsa ofis zuwa yau, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yi hovvasar qwazon inganta Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Sakkwato. A bayyane yake cewar a Jihar Sakkwato wadda Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ke shugabanta a qasa da shekaru uku ba wai kawai akwai ingantacciyar Hukumar Kashe Gobara kawai ba a’a , akwai kuma wadatattun kayan aiki da qwararrun ma’aikata waxanda ke zaune a shirin ko-ta-kwana domin kai xaukin gaggawa idan buqatar hakan ta kama. A yau Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Sakkwato ta samu nasarori da ci-gaba daban-daban waxanda al’ummar jihar ke yabawa kan muhimmancin da Gwamnatin Jiha ta baiwa fannin wanda a wasu jihohin aka samu akasin hakan . A qoqarin ganin ayyukan Hukumar sun riqa tafiya yadda ya kamata Gwamnatin Tambuwal ta siyo sababbin motocin kashe gobara na zamani guda 10 tare da gyara tsofaffinmotoci n da Hukumar ta ke da su wanda hakan ya kawo adadin motoci 18

da Hukumar bakixaya take da su . Ba sai an faxa ba samar da wadattaun ruwa abu ne mai matuqar mihimmanci ga ayyukan Hukumar Kashe Gobara a ko’ina a duniya domin idan har babu wadatattun ruwa to a kan samu tangarxa sosai, domin kamar yadda aka sani baya ga motocin aiki ruwa su ne qashin bayan tafiyar da ayyukan Hukumar. A kan wannan Gwamnatin Jiha ta yi hovvasar qwazon gina rijiyoyin bohol guda biyu wato xaya a Hedikwatar Hukumar a Arkilla da kuma xaya a ofishin Hukumar da ke a kan titin Sarkin Musulmi Abubakar tare kuma da samar da manyan motoci biyu masu xaukar litar ruwa dubu 30, 000 waxanda ke biye da motocin kashe wuta a cikin shirin ko-ta-kwana. A bisa ga faxaxar Birnin Sakkwato da qaruwar yawan al’umma a yanzu haka Gwamnatin Jiha ta sha alwashin gina sababin tashoshin kashe wuta guda takwas waxanda za a samar a Tsohuwar Kasuwa da Sabuwar Kasuwa domin kare afkuwar gobara a kasuwannin waxanda a lokutan baya ‘yan kasuwar suka tafka asarar ximbin dukiya. Sauran sababbin tashoshin za a yi su ne a unguwannin Bado, Kalambaina, More, Mana, Mabera da titin Sama duka a cikin qwaryar Birnin Sakkwato. Haka ma a qoqarinta na ganin ta qara bunqasa ayyukan Hukumar Kashe Gobara tare da baiwa xaukacin al’ummar Jihar Sakkwato kariyar da ta kamata, a yanzu haka Gwamnatin Tambuwal ta bayar da himma wajen samar da Tashoshin Kashe Goabara a Yankunan Majalisar Dattawa uku a Yammaci, Kudanci da Arewacin Sakkwato wato a Qananan Hukumomin Wurno, Gwadabawa, Tambuwal da Tangaza domin bayar da agajin gagawa idan buqatar hakan ta kama a waxannan yankunan. Baya ga wannan Hukumar ta kan wayar da kan al’umma kan haxari da illar gobara tare da bayyana matakan da za a iya xauka domin kaucewa faxawa cikin mummunan haxarin gobara. Ire-iren waxannan faxakarwar Hukumar kan yi su ne a kafafen yaxa labarai na Radiyo da Talbijin duka dai domin ganin sun sauke hakkin da ya rataya a wuyansu na ilmantar da jama’a haxarin gobara da muhimmancin xaukar matakin gaggawa domin kaucewa faruwar hakan a yau da gobe. Shin ko Hukumar Kashe Goabara a Sakkwato ta na xaukar matakin gaggawa a yayin da gobara ta tashi a gidajen al’umma? Ita ce tambayar da wakilin mu yayi wa Shugaban Hukumar Kashe Goabara ta

Jihar Sakkwato, Alhaji Murtala Mohammed wanda ya amsa da cewar “Muna kai xaukin gaggawa a duk lokacin da muka samu rahoton tashin wuta ba tare da vata lokaci ba domin ma’aikatan mu suna zaune a cikin shirin kota-kwana. Baya ga motocin kashe wuta, muna kuma tafiya tare da manyan motoci (tirela) da ke xauke da ruwa domin ganin dai an samu shawo kan wuta cikin hanzari.” Shugaban Hukumar ya kuma bayyana cewar a can inda aka fito su kan yi jinkirin zuwa wuraren da aka samu matsalar gobara, hasalima jama’a kan xauki lokaci suna jiran jami’ansu lamarin da ya bayyana a yanzu ya sha bamban domin sun magance wannan matsalar suna gudanar da aiki cikin hanzari yadda ya kamata ba tare da vata lokaci ba. A qoqarin ganin an fito da sababbin hanyoyi da dabarun bunqasa ayyukan Hukumar tare da tafiya da zamani kwatankwacin yadda Hukumomin Kashe Gobara a qasasehn duniya ke yi; Hukumar a Sakkwato ta bayyana cewar nan gaba kaxan za ta fito da tsarin tafiya wuraren kashe gobara da motocin asibiti na tafi da gidanka domin bayar da agajin gaggawa ga waxanda suka samu raunuka a yayin ibtila’in gobara tare da kai su asibiti cikin hanzari kamar yadda Shugaban Hukumar ya bayyana tare da cewar abubuwan da ke haddasa gobara sune ganganci da rashin kiyayewa don haka yake kira ga al’umma da su riqa lura. Bugu da qari domin ganin ma’aikatan Hukumar sun samu horo domin gudanar da aiki a matakin qololuwa na qwararru, a lokaci zuwa lokaci Hukumar kan tura ma’aikatan ta a kwasa-kwasan dabaru da sanin makamar aiki a Kwalejin Kashe Gobara a Kano da Abuja a inda suke samun ingantaccen horo da sake samun horo kan yadda za a riqa gudanar da aikin da suka fi iyawa, wayo da laqanta a cikin nasara. A kan wannan Shugaban Hukumar Murtala Mohammed ya bayyana cewar suna da burin samar da Kwalejin Horas da Ma’aikatan Kashe Gobara a Cibiyar ta Daular Usmaniyya ta yadda idan haqa ta cimma ruwa maimakon zuwa karvar horo a wajen jiha, ma’aikatan su za su riqa samun horo a cikin gida kamar kuma yadda sauran jami’ai daga wajen jiha za su riqa zuwa Sakkwato domin karvar horo. A bisa ga ximbin asarar da ‘yan kasuwar Jihar Sakkwato suka yi a dalilin mummunar gobarar da ta afku a Tsohuwar Kasuwa da

•Darakta Janar Na Hukumar Kashe Gobara Reshen Jihar Sakkwato, Murtala Mohammed

buqatar da ke akwai ta tallafawa waxanda lamarin ya shafa domin sauqaqa masu asarar da suka yi; Gwamnatin Jiha ta ware milyoyin kuxaxe waxanda ta rarrabawa ‘yan kasuwar a wani xan qwarya-qwaryan taro a shekarar da ta gabata, tallafin da ba wai kawai yayi tasiri ga waxanda a ka baiwa ba, ya kuma qara bayyanar da Gwamnatin Tambuwal a matsayin mai jinqai da taimakon al’ummarta tare da share masu hawaye a lokaci mafi dacewa. A kan kayan aiki da sinadaran kashe wuta kuwa, Shugaban ya bayyana cewar “Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya samar mana da dukkanin kayan aiki domin ganin aikin mu yana tafiya cikin tsanaki ba tare da wata matsala ba. Muna kuma da ma’aikata da ke qoqari sosai amma duk da hakan muna buqatar qarin ma’aikatan da za su taimaka ga gudanar da aikin kariya da xaukin gaggawa ga al’umma. Ya ce a shekarar da ta gabata a Jihar Sakkwato, sun shaidi gobara 553 wadda ta zama silar asarar qadarori da dukiya na bilyan 3.1 a faxin jihar amma kuma sun yi nasarar kiyaye asarar qadarori na naira bilyan 4.1 a tsayin lokacin. LEADERSHIP A Yau ta labarto cewar a watan Nuwamban shekarar da ta gabata a bisa ga muhimman nasarorin da Gwamnatin Tambuwal ta samu a sha’anin kashe gobara tare da tallafawa waxanda annobar gobara ta shafa a Jihar Sakkwato, haxakar Kwamitin Al’amurran Cikin Gida na Majalisar Dattawa da na Majalisar Wakilai tare da haxin guiwar Qungiyar Kiyaye Afkuwar Haxarin Gobara ta Qasa (FDPSAAN) sun karrama Gwamna Tambuwal da lambar girma ta 2017 domin yabawa qwazonsa na inganta Ayyukan Hukumar Kashe Gobara a Sakkwato.


16

Siyasa A Yau A Yau

Laraba 14.2.2018

Haxa Aikin Jarida Da Siyasa Na Buqatar Goge Wa (II) –Habila

Ci gaba daga Jiya Kasantuwarka dattijo a wannan aikin, akwai matsalar rashin daxa da ta haiwaita a wannan aikin jarida ko kana da abun cewa don ganin abun ya ragu? Ka san shekara da shekaru an sha yin wannan maganar, amma ba a xauki matakin da za a ce a kawo daxa xin ba. abun da qungiyoyin aikin nan na jarida suke yi shi ne a zo kawai a nemi muqamai a yi zave a samu kujerar mulki. Amma basu tava cewa wannan aikin bari a tsaftace shi ba. ya kamata ce a ce a yi kamar yanda lauyoyi suke yi, a samar da hanyoyin girmamawa, wanda ya shiga da farko a martabashi a ba shi kimarsa. Amma irin wannan matsalar ba zai qarasa nasaba da yanayin aikin ba, sabili da yanayin aikin, aiki ne na kwakwalwa zaka ga wani ya tashi yau ya fi wanda ya yi shekara ashirin yana aikin kwarewa, amma a aikin jarida babu wani tsarin da za a ce Khalid ya fara aiki da jimawa ya riga Iliya fara aiki sabili da haka rinqa martabashi a bisa jima’arsa kan aiki, amma ina, da zarar wani ya shigo aikin ya ga na tashe sai ya xauka shi ne kaxai ya fi kowa iyawa, amma ya mance tun yana xan makaranta waxannan suke aiki. Kamar su lauyoyi idan ka gansu ko a kotu ne, wanda yake gabanka a aiki zaka ga akwai wani girmamawa a tsakininsu koda kuwa shari’a ta haxasu. Mu a aikin jarida muna buqatar a samar da hanyoyin da zasu kau da raini da irin waxannan halayen rashin girmama na gaban shi ne zai kawo xa’a a aikin jarida sosai. Ko Habila Iliya ya samu wani alfanu a wannan sana’ar tasa kuwa? Alfanu da nasara a aikin jarida suna da yawa, da farko kamar yanda na faxa maka lokacin da na shiga jami’a ina karatun share fage, zuciya ta na raya min abubuwa biyu, ko na je na karanci aikin jarida ko na karanci lauya. Amma cikin taimakon Allah sai na zavi aikin jarida, tun da na zavi wanna aikin na yi ta samu alfanu da nasara. Domin a cikin aikin nan ne kawai zaka zo ka ci abinci da sarakuna, ka ci abinci da shuwagabanni. A akin jarida ne duk girmanka, ko duk kuxinka zaka yi hira da

ILIYA HABILA•

talaka, shugaba, mai kudi, ka dawo kasa ka durkusa wa kansila ka yi hira da shi, ka samu irin wannan damar ma nasarace. Kamar ni yawancin abun da na yi a shekaru 20 a aikin jarida babu inda zan shiga na gagara sanin wani wanda na sani a vangaren arewa. Ta fuskacin arziki kuma kamar yanda na shaida maka babu yabo babu fallasa a aikin jarida haka nima Alhamdulla. A cikin aikin na na jarida yau ina da mutanen da ko a ina na ke zaka ga wani mutum da na tava zama da shi ko na tava aikin da shi. Amma babbar nasarar da zaka samu a aikin jaridar nan shi ne ka ga aikin da ka ke yi k ayi kokarin kyautata wa mutanen da kake musu hidima, ka kyautata rayuwarsu wannan zai sanya ka samu nasara kuma kuma ji daxi. ina da yakinin akwai lada sosai a aikin jarida”. Ko ka tava ketare hazo a wannan aikin? A aikin kungiya mun yi tafiyetafiye da yawa, na je qasashe da yawa. A cikin Nijeriya kuma ba’a magana. Ta fuskacin tafiye-tafiye a kan aikin nemo labarai kuwa, na je Ethopia. Aikin jaridar nan na je hajji a qasar Isra’ila har sau biyu, na je Rom Batikan na je inda Fadar Fafaroma yake domin na je aikin hajji na addinina har sau biyu, kuma a aikin jarida na samu wannan damar. Mun dosa lokutan zave, ko kana da wasu shawarori ga abokan aikinka wajen ganin sun saita labaransu musamman wajen yin adalci ga kowani janibi?

Shi xan jarida kullum yana tattare da hatsari, tun ba lokacin siyasa ba. amma kamar yanda na faxi maka idan ka tashi yin abu ba wai kawai zaka yi da son zuciyarka ko don ka yin aiki ma wani ba. kai kana aiki ne wa jama’a. ka duba duk wani wanda yake aiki ma wani ne ko ma wata qungiya ne sai ka ga ne hakan a wajen da xan jarida yake bada labari. Abun da ya dace ‘yan jarida su yi a irin wannan lokacin ba a ce kowa dole kowani xan jarida kada ya shiga siyasa ba; shi ma xan jarida yana iya yin siyasa, amma kada ya nuna a cikin aikinsa na jarida, wajen siyasa ka yi siyasarka, wajen da kake yi wa jama’a aiki kuma ka yi musu aikinsu. Kowani xan adam xan siyasa ne, daga gidanka kai xan siyasa ne. amma fa idan ka zo tuburinka na aikin jarida dole ne ka baiwa kowani sashi zarafi da kuma ikonsu da damarsu da aikin jarida ya basu na su faxi haqqinsu da ke bakinsu. Dole ne kuma ka yi wa kowani xan siyasa ne, qungiya ne, jama’a ne walau kana cikinsu ko baka cikinsu dole ne kai xan jarida ka yi musu adalci. Shi aikin jarida aikinka aka xauke ba, na siyasar da ka shiga ba, idan ka kula sosai da wannan za ka iya siyasarka, ka kuma gama da kowa lafiya a aikinka na jarida, za ku ka ji daxin aikinka. Ganin cewar kai aikin jarida ka qware, yanzu kuma ga ka a fagen siyasa, yaya abun suka haxu maka biyu, Siyasa da aikin jarida? Eh to gaskiya aikin da na ke yi

yanzu baida wani babbanci sosai da aikin da na ke yi da, domin ina nan a fagena na aikin jarida ne. sai dai yanzu kai tsaye na maida hankali ne kan yanda za a taimaka wa shi Spekar Yakubu Dogara kan harkokin yaxa labarai. Don haka lallai qwarewata a aikin nan na jarida ya taimakeni sosai, sanin yanda zan tafiyar da komai. Ka ga qwarewata ita take taimakona domin na tafiyar da aikin bisa nasara. Da ka sani bana cikin siyasa sosai-sosai, amma yanzu ka ga wannan aikin dole Kaman da zan maka yanzu da aiyukan da zan yi dole ka ga kamar nima na zama xan siyasa. Amma haka abun ya gada. Don haka aikin jarida na yana taimaka min wajen hulxa da jama’a. Kamar yanda ka ce, kuma dai ka qware a aikin jarida yanzu kana siyasa baka ganin wasu za su iya ganin ka koma aiki ga wani baki xaya a maimakon jama’a? Eh to aikin kare wani ne amma a aikin da ya shafi sana’ar da na qware, yanzu ka ga yawancin aikina rubuta labarai ne da sauransu. Ba canza sheka na yi ba; qarin samun ilimi a aikin jarida ne, domin idan baka sani wannan sashin ba yanzu ga shi ka shige sa sai ka nemi iliminsa. Babu wani banbanci a aikin da na ke yi da, da kuma yanzu da na ke tallafa wa Dogara. A matsayinka na wanda ya san aikin jarida sosai, ita siyasa ta gaji gaba da nuna isa. Ta yaya kake yi wajen maida martani? Ka san aikin jarida idan ka xauki ainuhin siyasa ka sanya a ciki to ba zaka ci nasara ba; amma aiki mu muke yi, ba mune masu ainuhin siyasar ba; mai gidanmu ne muke son mu yayata aiyukan da yake yi. Muna qoqarin rage shiga cikin harqoqin siyasa, sai abun da shi mai gidan ka ya baka ko kuma na dubi ina ya hanga kai ma sai ka sa gaba. To ka ga ba kai ne a gaba ba. don haka dole ne ka yi taka-tsantsan sosai a wannan kujerar da na ke. Idan ka zo yin magana dole ne ka yi maganar da shi mai gidanka yake so, don haka kana tsoron ka yi kuskure, domin akan iya kuskure a komai a gyara cikin sauqi amma banda irin aikinmu dole ne muke sanya taka-tsantsan sosai, a irin wannan lokacin. Aikin jarida da tallafa ma xan siyasa da buqatar sanya qwarewa sosai.


SIYASA 17

A Yau Laraba 14 Ga Fabrairu, 2018 (27 Ga Jumada Ula, 1439)

Ni Ba Xan Amshin Shatan Majalisa Bane –Shehu Sani Daga Ibrahim Ibrahim, Kaduna

Sanata mai wakiltar mazavar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa Sanata Shehu Sani, ya bayyana cewar shi baije Majalisa domin zama xan amshin Shata ga kowa ba, shi zavavven ne wanda jama’a suka zava ba naxaxxe ba, saboda haka aikin shi a majalisa shi ne kare muradun jama’ar da suka zave shi, da kin amincewa da dukkanin wani abu xaya wanda yaci karo da ci gaban qasa. Sanata Shehu Sani ya bayyana hakan ne, lokacin da yake mayar da martani dangane da kiran da wasu qungiya mai suna Kaduna Concern Farum, suka yi, qarqashin shugaban qungiyar mai suna Aliyu Sa’idu Rigachikun, inda suka bayyana aniyar yi wa Sanatan kiranye, bisa ga zargin kasa aikin da aka tura shi yi a Majalisa, maimakon haka sai ya dawo yana adawa da sukan Gwamnatin Buhari da na El-rufa’i, a yayin wani taron manema labarai da ya kira a cibiyar ‘yan jaridu ta

qasa reshen Jihar Kaduna. Sanata Shehu Sani wanda ya bayyana hakan ta bakin Mai taimaka masa na musamman akan harkokin hulxa da jama’a, Malam Sulaiman Muhammad, ya zargi Gwamnatin El- rufa’i, da xaukar nauyin waxannan mutane masu iqirarin yi mishi kiranye, inda yace ba sabon abu bane ga Jama’ar Jihar Kaduna dama Nijeriya baki xaya. A cewarsa, Elfufa’i, yasha xauko hayar mutane daga wasu wurare su tara ‘Yan jaridu suna surutu a kanshi, anyi haka yafi so shurin masaqi, kuma aniyar El-rufa’i, da muqarraban shi ita ce vatanci a gareshi, amma su jama’ar da ya ke •Sanata Shehu Saniun wakilta a mazavar Kaduna aci musu albasa, a tsawon ta tsakiya mai Qananan zaman da nayi a Majalisar Hukumomi 7, sune Alqalai kimanin shekaru biyu da a tsakanin shi da El-rufa’i, rabi, ‘Yan Kaduna ta tsakiya kuma sune suke da haqqii na sun san ayyukan da nayi cewar za suyi kiranye amma musu, kuma tabbas ina tare ba a xauko wasu mutane da jama’a ta, saboda haka a daga waje ba. daina yiwa ‘Yan Kaduna ta Sanata Shehu Sani, tsakiya katsalandan a barsu yace, “ jama’ar Kaduna ta suyi hukunci akan ci gaban tsakiya mutane ne wayayyu su, ba’a xauko hayar wasu waxanda suka san abin da daga waje suyi magana da suke yi, ba mutane bane yawun su ba.” waxanda za’a ari bakin su

Za Mu Ci Gaba Da Bunqasa Havvakar Bunkure -Rabiu Bala Daga Ibrahim Muhammad Kano

An yi kira ga al’ummar Qaramar hukumar Bunkure akan su ci gaba da bada goyon baya ga Gwamnatin jahar Kano qarqashin jagorancin Dokta Abdullahi Umar Ganduje domin ci gaba da bunkasar yankin. Zavavven shugaban Qaramar hukumar Bunkure Alhaji Rabiu Bala Bunkure ya bayyana hakan bayan miqa masa takarda shedar nasarar zavenda akayi masa a matsayin shugaban Qaramar hukumar Bunkure da Hukumar zave mai zaman kanta tayi a harabar hedikwatarta na Kano. Alhaji Rabiu Bala wanda shima ya sami nasarar zama shugaban qaramar hukumar a zango na Biyu ya ce baiwa Gwamnati haxin shi zai

bada dama ta samun ci gaba ta fannoni da dama, musamman idan aka yi la’akari da irin ayyukanda Gwamnatin Kano take duk kuwa da qarancin kuxi da matsalar koma bayan tattalin arziqi daya shafi qasarnan amma hakan bai hana Ganduje ririta xan abinda ake samu ba, wajen gudanarda muhimman ayyuka. Zavavven shugaban na qaramar Hukumar Bunkure ya qara da cewa a matsayinsu na zavavavvu zasu baiwa manufofin ci gaba da Gwamnatin APC da Gwamna Ganduje yasa a gaba don gina ci gaban al’umma. Alhaji Rabiu Bala Bunkure ya gode wa al’ummar Bunkure a bisa goyon baya da haxin kai da suke ba shi, wannan nema tasa suka sake zavensa sakamakon

gamsuwa da irin ayyikanda ya aiwatar a baya, wanda kuma yake fata ya sake xorawa akai domin samun ci gaba mai nagarta a yankin. Ya ce daga cikin burinsa shine bunqasa harkar noma wanda shine qashin bayan aikin al’ummar yankin rani da damina da kuma bunqasa ilimi da gima matasa domin su zama bayan sunyi ilimi su riqa dogaro da kansu. Alhaji Rabiu Bala Bunkure ya ce zai ci gaba da barin qofarsa a buxe dan karxar shawarwari dazai kai ga kawo ci gaban al’ummar yankin ba tareda la’akari da banbancin siyasa ba.Anyi zave an gama abinda ya rage da wanda suka yi nasara da waxanda suka sami akasin haka azo a haxa kai gaba xaya dan kai yankin ga ci gaba.

Dangane da zargin cewa Sanatan na sukar Gwamnatin Buhari, sakamakon kalaman da ya yi na cewar Buhari ya huta a 2019 ya xora wani, Xan Majalisar Dattawan yace ko kaxan ba sukan Gwamnatin Buhari yake yi ba, sai dai ya yi la’akari da halin da qasa take ciki ne, biyo bayan tsadar rayuwa da jama’a suke ciki, da yawaitar kashe

- kashe tsakanin Manoma da Makiyaya, da yin garkuwa da Mutane da fashi da Makami, wannan shi ne dalilinsa, domin Buhari na qoqari amma wasu muqarrabansa na cin dunduniyarsa, shi ya sanya ya bayyana ra’ayin shi da kiran Buhari ya huta ya xora wani Amintaccensa domin ci gaban Nijeriya da Jama’arta baki xaya. A cewar Sanata Shehu Sani.

Tsoron Shan Kaye Ne Ya Sa Jam’iyyar APC Ta Xage Zaven Qananan Hukumomi A Filato -Jam’iyyar PDP Daga Lawal Umar Tilde Jos

Jam’iyyar PDP reshen jihar Filato ta bayyana xage zaven kana nan hukumomi da Jam’iyyar APC, mai mulki a jihar tayi akan dalilan tsaro bakomai bane ill kawai ta ga zata sha kaye ne a zaven da hukumar zave mai zaman kanta a jihar ta shirya yi ran 17 ga wannan wata. Shugaban Jam’iyyar PDP, na jihar Cif Damishi T. Sango, ne ya bayyana haka a taron da yayi da Yan- Jarida a Jos jimkadan da samun labarin gwamnatin jihar ta dage zaven zuwa waxansu lokuta da bata bayyanaba. Cif Sango, yayi misali da zabubbukan da gwamnatin da ta gabata ta gudanar na kan nan hukumomi da na kasa da akayi a Alib 2015, duk alokutan ya ce akwai barazanar reshin tsaro irin wannan amma bai hanata gudanar da zavenba kuma ya ce hatta ma jihar Borno inda ake fama da rikicin Boko-Haram amma bai hana

gwamnatin jihar gudanarda zaveba ya ce hatta ma wadanda suke sansanin yan gudun hijira ankai masu akwatunan zave suka jefa kiri’unsu , ya ce jam’iyyar a jihar bata amince ba da irin hajjojin da jam’iyyar APC din ta bayar kuma tayi kira ga al’ummar jihar dasuki amincewa da dage zaven. Indan ana’iya tunawa a ran Litinin din nan da ta babata hukumar zave mai zaman kanta a jihar a taron gaggawa da shugabanta Mista Fabian Ntung, yayi da yan- Jarida a Jos ya sanar cewa hukumar ta dage zaven da ta shirya gudanarwa ran 17, ga wannan wata bisa sakon data samu daga hukumar tsaro na jihar, cewa akwai barazanar rashin tsaro tattare da zaven da zata gudanar din . Mr. Ntun ya ce kafin wammam samarwar hukumar tarigaya ta kammala dukkan shirye shiryen da yakamata ta yi don gudanarda zaven cikin nasara.


18 TATTAUNAWA

A Yau

Laraba 14 Ga Fabrairu, 2018 (27 Ga Jumada Ula, 1439)

Ba Za Mu Zuba Ido Ana Raina Harshen Hausa Da Al’adun Bahaushe Ba -Jibrin Sidi Adamu MALAM JIBRIN SIDI ADAMU shi ne shugaban qungiyar kare harshen hausa da al’adun bahaushe (KUCHIKA) matashi xan gwagwarmaya, mai kishin harshen Hausa da al’adun bahaushe, a tattaunawarsa da wakilin mu a Kano Abdullahi Muhammad Sheka ya bayyana ta’annacin da ake yiwa harshen hausa da kuma kyawawan al’adun Bahaushe. Haka kuma ya yiwa masu yiwa harshen na hausa kallon raini da cewa ahir xinsu, ya bayyana cewar zasu qafar wando xaya kuma tsala da masu gurvata harshen hausa da al’adun bahaushe, sannan kuma ya tava yadda ko a wayoyin hannu saboda raina hausa ake sa waxanda basu san darajar harshen ba an amfani da gwarancinsu wajen aika saqonni. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance:

Za mu so ka gabatarwa da mai karatu kanka. Alhamdulillahi ni sunana Jibrin Sidi Adamu an haifeni a unguwar Darma dake cikin birnin Kano, daga nan na aka koma da ni Azare inda nayi karatun firemare da Sakandire, Haka kuma na koma cikin Garin Bauchi inda na halari Sashin Jamai’ar Maiduguri dake Bauchi inda na karanta Turanci dadangoginsa,Yanzu haka ina aikin da Jami’ar Bayero dake Kano, kuma ni ne shugaban wannan qungiya ta kare harshen hausa da a’adun bahaushe, Mene dalilin kafa irin wannan qungiya a wannan lokaci? Alhamdulillahi dalilin kafa wannan qungiya bai wuce yadda ake yiwa harshen hausa hawan qawara ba, da kuma yadda akayi shakulatin vangaro da kyawawan al’adun bahaushe, sai kuma yadda ake neman mayar da cimakarmu koma baya, wannan tasa muka yi wannan tunani domin nemawa harshen hausa da al’adun bahaushe makoma da kuma sama masa gata. Mun fahimci mun zauna an cimma na musamman ta yadda zaka ga kowa na yin yadda ya ga dama da harshen hausa walau ta hanyar Magana ko gurvata mana kyawawan al’adun da muka gada iyaye da kakanni. Waxannan dalilai suka sa muka zauna tare da gudanar dogon bincike kan abubuwan da ake yiwa wannan harshe mai daxaxxen tarihi, harshen hausa ya wuce hashen da za’a yiwa xibar karan mahaukaciya, kuma ko rantsuwa kayi da wuya kayi kaffara idan za’a lissafta manyan harsunan Duniya da wuya ka wuce na uku ba harshen hausa a ciki. Balle kuma al’adunsa wanda ba wani harshe da ya kai harshen hausa kyawawan al’adui, amma abin takaici yanzu al’amari nema yake zama lahaula wala quwwata. Jama’a zasu yi mamakin yadda wannan al’amari ya kasance, kila akwai buqatar ka xan tava alli a wannan qadamin? Da farko duk mai hankali kuma bahaushe na haqiqa mai kishin ci gaban wannan harshe da al’adunmu kyaywawa, kullum yana kwana cikin baqinci idan kaji yadda ake yin walagigi da wasu abubuwan da bahaushe ya gada iyaye da kakanni, da yawa yanzu yaranmu sun zama marasa takamaiman alqibla ta fuskar harshe da kuma al’adu, suna neman zama basu a tsuntsu basu a tarko. Dubi yadda aka mayar da mu wasu shawaraki yanzu kawai sai wani ya maqale murya yana

ta soki burutsun sa da sunan bahaushe. Wannan tasa yanzu haka muke shirin baje komai a faranti domin yi masu duban tsanaki mu ware tsaba daban sannan kuma tsakuwa ma daban. Amma baka ganin har sashi guda hausa ke dashi a jami’o’in mu? Mene amfanin baxi ba rai duk da wancan sashi ba kaji irin kasassavar da aka yiwa harshen ba, Hausa bata cikin darasin da yake da wata qima a idon mahukunta, da zarar an fara maganar xaukar xalibai sai kaji ana cewa sai wanda yake da turanci da lissafi. Kaje qasar Indiya ko Jamus da China duk da yarensu ake koyar da kowane fanni, bilhasalima sai ka kwashe shekara guda kana koyon yaren qasarsu kafin ma ka shiga cikin harkokin karatu a makarantunsu. Amma mu anan sai Inyamuri ko bayarabe ya buxe makaranta a tsakiyar birnin Kano amma sai ga an rubuta NO Vanacular, wannan takaici da me ya yi kama, ka isa kaje kudu ka buxe makaranta ka ce No Ibo ko No Yoruba? Wannan ai rainin hankali ne da cin zarafin harshen hausa. Yi wa mai karatu dalla dalla me wannan qungiya zata fi mayar da hankali akansa cikin waxannan tulin qalubale? Alhamdulillahi da farko muna son fara cusawa yaranmu kishin harshen Hausa da al’adunmu kyawawa, sannan kuma mun tsara shiga lungu da saqo domin tattaunawa da shehunnan malaman Jami’a musamman waxanda suka goge a wannan fanni na harshen hausa da al’adunmu domin yi mana fashin baqin inda aka yi mana qulunboton da ake neman watsar mana da harshen hausa. Wannan ya haxa da gabatar da qudurce qudurce kama daga majalisun mu na Jihohi har zuwa na tarayya, sannan kuma zamu zauna da kamfanonin sadarwa masu tura saqonnin karta kwana ta wayoyinmu na hannu inda ake yin amfani da wata gurvatacciyar hausa kuma ana aikawa hausawa dasu. Haka zalika zamu tabbatar da ganin an yiwa dokoki garanbawul ta yadda za’a ci gaba da koyar da fannonin kiwon lafiya abinda wanda ya haxa da aikin llkita, injiniya da sauran abubuwa masu muhimmanci, kasancewar ba mu muka fara ba qasashe irin Indiya China da Jamus duk da yarensu ake koyarwa a makarantunsu, wannan tasa suke da kwarewa matuqa aduk fannonin al’amuran yau da kullum. Saboda haka muke ci gaba da gudanar

•Jibrin Sidi Adamu.

da tuntuba domin samar da kwararrun masana harshen hausa waxanda zasu taimakawa wannan qugiya domin ganin anci nasarar abinda aka sa gaba. Yanzu haka daga cikin ‘ya’yan wannan qungiyar akwai wanda ya samar da littafin koyon ilimin harkokin na’ura mai kwakwalwa (Computer) da hausa littafin na nan a kasuwa ana sayar dashi. Amma baka ganin akwai wasu vangarorin al’umma da tuni suke rajin kula da harkokin al’adun bahaushe, musamman masu sana’ar shirya finafinan hausa? Ka ji wata babbar matsalar cikinsu mutun nawa ne hausawan na haqiqa? Ai waxannan sune waxanda suka gurvata al’adar bahaushe, kuma muna nan zamu tsara yadda za’a samu fahimtar juna musamman da masu kishin harshen na hausa ba ‘yan yaki halak yaki haram ba. Wannan tasa kullum muke kallon nasara ya yi nasara akanmu domin ya cusa mana qaunar nasa harshen sannan ya cusa mana tsanar namu yaren, domin yanzu har xokin kai yara makarantar da aka rubuta No Vanacular ake, ko wasu da suke cewa idan kayi hausa tara za’a cika. Wannan ai cin fuska ne wane qabila a Najeriya zaka shiga cikin jama’arsa kuma ka nuna kyamar harshensa ya saurare ka idan ba bahaushe ba. Kayi magana bayan al’adu har ma da batun cimakar bahaushe, shin a wannan vangaren kuma me kuka kalla har kuka sako shi cikin abubuwan da kuke fatan kawo gyara acikinsu? Haka ne kamar yadda aka sani duk al’umma suna da tsarin cimakarsu ta al’ada wadda alokuta da dama wasu nau’in abincin mu na gargajiya duk magani yake, dubi batun zogale da dangoginsa, ko ka dubi gwaxoso da sauransu, yanzu yaranmu idan ka tambayesu mene gwaxoso basu sani ba, sannan kuma cimakar bahaushe tana da sauqi kwarai da gaske, amma sai muka watsar muka xau na aro wanda yake cike da matsaloli iri daban daban, saboda haka mun shirya koyar da yaranmu cimakar bahaushe ta gargajiya har ma da sana’unmu. Su ma sana’un akwai na garagajiya? Kwarai da gaske su muka watsar yaranmu suka fantsama birane neman

kuxi saboda lalaci, kamar yadda tarihi ya nuna kowane gida ko unguwa ada zaka tarar suna da irin tasu sana’ar ta iyaye da kakanni misali rini, saqa, dukanci, fawa, wazanci da sauransu. Amma saboda xokin sai anyi kuxi duk mun watsar mun xunguma cikin birane da suna neman kuxi, kenan ka baro wurin da ake da cikakkiyar hausa ka faxa ingausa, ka baro sana’ar ka ta gargajiya ka afkawa wadda baka san sirrinta ba a qarshe idan ba’ayi sa’a ba ka qare a shaye shaye ko maula da tumasanci. Babban abinda ya zaunar da iyayen mu lafiya kenan rashin kwaxayi da kuma batun dole sai mutun sya yi kuxi ta kowacce hanya. Yanzu tunda kun xauko wannan babban aiki, shin ta’ina kuke fatan zaku fara? Alhamdulillahi gashi ma mun fara domin haxa qarfi da ‘yan Jaridu shi ne zai bamu damar isar da saqonnin mu zuwa ko ina, sannan kuma mun fara kaiwa shehunnan malaman Jami’a ziyara da yawa sunji daxin wannan tunani namu, wasunsu ma godiya suka yiwa Allah cewar ashe za’a samu matasa da wannan matsala ke ciwa tuwo kwarya? saboda haka suka bamu tabbacin goyon bayansu tare da xora mu akan tafarki mai xorewa. Sai kuma yadda shiri ya yi nisa na tattaunawa da masana harkokin sana’un gargajiyar bahaushe wanda zamu haxa hannu dasu wajen koyar da qananan sana’un dogaro da kai wanda zai kawar da kwaxayi da tumasanci. Mene fatanka ko kiranka na qarshe? Alhamdulillahi babban kiran da muke shi ne matasa su tuna cewar kowa ya bar gida gida ya barshi, kuma su sani zanen aro baya rufe katara sannan kuma guntun gatarinka ya fi sari ka bani, dole matasa mu haxa qarfi wuri guda domin kare qimar harshen hausa da al’adunmu, sannan mu amince da fifita cimakarmu sama da wadda ta shigo mana daga inda bamu da cikakken ilimin tasu al’adar domin bahaushe na cewa abincin wani gubar wani. Muna qara miqa godiya ga iyayenmu musamman shehunnan malaman Jami’a wanda basa qosawa da zirga zirgar da muke zuwa ofisoshin su don neman qarin bayani. Haka kuma akwai manyan mutane da suka yi mana alqawarin dafawa wannan tafiya muna godiya kwarai da gaske.


TATTAUNAWA 19

A Yau Laraba 14 Ga Fabrairu, 2018 (27 Ga Jumada Ula, 1439)

Sai Iyaye Sun Canza Ne Za A Iya Kawo Qarshen Fyaxe –Barista Aisha Za a iya cewar matsalar fyaxe ga qananan yara matsalar tan a gab da zama gagara-badau ga al’umma da kuma mahukumta, domin a duk rana sai ka ji matsalar sai qaruwa ta ke yi tamkar wutar daji, wannan ne ke sa zargi ya yi yawa ga ma su riqe da madafun iko cewar su ke da alhakin kawo qarshen matsalar fyaxe, amma sai aka sami akasin haka. BARISTA AISHA AHMAD, lauya ce mai zaman kanta a Zariya, ita ta ce, duk matakan da gwamnati za ta xauka sai iyayen yara da kuma al’umma sun canza, san nan matsalar fyaxe za ta zama tarihi. Bayanin da ta bayyana wa wakilinmu BALARABE ABDULLAHI ke nan, a zantawar da suka a ofishinta da ke Zariya. Ga yadda tattaunawar ta kasance. Ya ki ka dubi yadda matsalar fyaxe ke yawaita, tamkar wutardaji a yau? Duk bayanan da zan yi ma ka, ina fatan ba za ka ce a matsayi na mace, na so kai na ba, ni a nawa tunanin duk mai aikata fyaxe ga qananan yara, ya na yi ne domin son ransa, saboda haka son ran da na faxi, shi ne kan gaba ga dalilan da vata-gari ke furtawa bayan sun aikata fyaxen, kuma zalunci ne yi wa qananan yara fyaxe, ba zan gushe da faxin haka ba a tsawon rayuwa ta. Kuma, in ba zalunci ba, tun da akwai mata waxanda ba sa kishin rayuwarsu, su jiran maza su ke yi a ko wane lokaci, me zai sa mai son yin fyaxen ba zai je ga waxancan matan ba? A gaskiya, duk wani na-miji da ya ke aikata fyaxe, ba shi da dalilin da zai faxi da mutane nagari za su yadda da shi. Wannan matsala ta fyaxe, babban laifi ne, ko kuma qaramin laifi? Ai in har ka furta fyaxe, a shari’ance ya kasu kasha biyu, wato akwai fyaxe da ake yin a qananan yara sai fyaxe da ake yi wa balagaggun mata. Kuma duk fyaxe biyun nan da na faxa ma ka dukkaninsu manyan laifi ne, wannan laifi, dai-dai ya ke da kisan kai da fashi da makamai. Wani abu da na ke son ka fahimta shi ne duk wanda aka yi wa ‘yarsa fyaxe, babu yadda za a yi ya ce ya yafe, kuma duk waxannan tanade-tanade, suna cikin addinin musulunci da kuma tsarin mulkin Nijeriya. Ka ga in mace bat a kai shekara goma sha shida ba, in har aka yi amfani da qarfi ko kuma da yaddarta, na miji ya sadu da ita ya aikata laifi, kuma babban laifi, kamar yadda na bayyana ma ka a baya. Amma a mace babba, akwai wasu abubuwa da ake dubawa,

sai an tabbatar da furucinta, sai an duba, wato a wani yanayi aka yi ma ta fyaxen? Inda aka yi ma ta fyaxen akwai mutane? Shin za ta iya ihu a lokacin da za a yi ma ta fyaxen ko bayan an yi ma ta fyaxen? Shin ta yi dambe da wanda ya yi ma ta fyaxen? Ta kare kanta? Kuma dai sai na miji ya sanya zakarinsa a farjinta, daga nan ne laifi zai iya tabbata, in an ce an yi wa babbar mace fyaxe. Kuma tabbatar da waxannan abubuwa, musamman na qarshe, likita ne zai tabbatar, ta binciken da zai gudanar, sai an sami wannan sakamakon bincike daga likta, daga nan za a tabbatar da laifi ga wanda ya aikata fyaxen. Amma in babbar mace ta ce an yi ma ta fyaxe, sai an tabbatar da abubuwan da aka bayyana. Kaza-lika, likita ne zai je kotu, ya bayyana yadda ya gano abubuwan day a bayyana wa kotu. To, wasu abubuwa ake dubawa a tabbatar da fyaxe ga qananan yara? To, yarinya qarama dab a ta kai shekara goma sha shida ba, ba a duba abubuwan da ake tabbatar da fyaxe day a shafi qananan yara, kotu za ta yi ‘yan tambayoyi ga qaramar yarinyar da aka yi ma ta fyaxe, kamar a ce ma ta, menene hukumcin wanda ya yi qarya, sai ka ji yarinyar ta ce za a sa shi a wuta, da dai sauran tambayoyi da kotu za ta fahimci yarinyar da aka yi wa fyaxe tan a da hankali ko a’a?Da zarar an yi wa yarinya fyaxe, a gaggauta kai ta asibiti, rahoton likita, shi ne hujja mai qarfi, da kotu za ta dogara da shi. ta yanke hukumci ga wanda ake zargin ya aikata laifi. Idan laifi ya tabbata, ya batun da hukumci? Ai hukumcin a bayyane yak e a tsarin mulkin Nijeriya, wato akwai xaurin rai-da-rai da za a yi wa wanda ya aikata laifin, kuma in a musulunci ne

• Barista Aisha Ahmad.

akwai tanadin dokar da babu sassauci. A na zarginku lauyoyi da Alqalai da sakin waxanda aka samu da aikata fyaxe, kin yadda da zargin da ake yi ma ku? In ka tuna a baya, na bayyana ma ka buqatun vangaren da kotu za ta yarda su ta yanke hukumci, in kuma ba a tabbatar da laifin da ake zargi ba, dole a duba abin da dokar qasa ta tanada a kansa na zargin da ake yi ma san a aikata laifin fyaxe. Kuma ko da an sami mutum turmi-da-tavarya ya na aikata laifin, sai kuma an duba abin da hukumci ya tanada, ka ga in an saki wanda ake zargi dai-dai ne, domin ba a same shi da aikta zargin da ake yi ma sa ban a aikata fyaxe. Ya ki ka dubi iyayen yara a batun fyaxe a yau? Ai a nan matsalolin suke, domin za ka an sami wanda ya lalata yarinya ta yi ma ta fyaxe, an fara nisa a cikin bincike, ana kuma ganin alamun nasara, sai a wayi gari iyayen yara su ce sun janye qarar da suka yi, ko kuma a fara halartar kotu, sai ka ga iyayen yaran da aka yi ma su fyaxen sun dai na zuwa kotu, to sai Alqali ya duba mai shari’a ta tanada ga wanda ake zargi, sai ta yanke hukumci. Sai ma su ce in an ce za a ci gaba da yin shari’ar, sai ka ji iyaye na cewar, su sun janye, wai ka da a vata sunan ‘yarsu a nan gaba. Dagan an sai wanda ke tsare ya nemi lauya, domin ya karve shi, ko kuma ya fitar da shi daga gidan yari da aka garqame shi, sai lauya ya je kotu ya kare shi, a qarshe, sai ka ga an saki wanda ake zargi.

A gaskiya, in har ana son kawo qarshen fyaxe, to sai fa iyaye sun canza halin da na bayyana ma ka suna yi, na juya bayansu da taimaka wa kotu da lauyoyi, na ganin an hukumta wanda aka kama da zargin yin fyaxe. Ina tabbatar ma ka da cewar, babu Alqali ko kuma`lauya nagari da zai amince a bar mai yin fyaxe ya tafi sasa-kai ba. To rashin hukumci ne ko kuma ko in kula daga iyaye ke sanya taki ga matsalar fyaxe a yau? Duk biyun suna da muhimmanci, sai fa iyaye sun da goyon baya ga vangarorin jami’an tsaro da vangaren shari’a za su sami dammar yin hukumci ga wanda ake zargi da aikata fyaxen. Kuma da iyaye na bayar da dammar binciken wanda ake zargi, aka tura wanda aka samu da aikata laifin fyaxe, zuwa gidan yari da zai shafe sauran shekarunsa, to ba za a sami ma su aikata fyaxe ba a nan gaba. Yau an wayi gari, ana aikata laifin ba a yin hukumci, kuma mafi yawan laifin na iyaye ne kamar yadda na faxi a baya, ba za iya kawo qarshen wannan matsala ba, domin sai iyaye da jami’an tsaro da kuma Alqalai sun sami goyon bayan yin aiki daga iyaye, za a sami mafitar wannan matsala ta fyaxe. qarshe, Barista Aisha Ahmad, wani saqo kike da shi ga iyaye? Ai saqon xaya ne, kamar yadda na bayyana a bayabayan nan, dole iyaye su canza halin da ke da shi, na su suke kai qara, amma daga baya sai su janye jikinsu, in sun canza, kamar yadda n ace, matsalar fyaxe za ta kau baki xaya a cikin al’umma.


A Yau Laraba 14.2.2018

20

CINIKI

Kasuwanci MASANA’ANTU

INSHORA

HANNUN JARI

Editan Kasuwanci Mohammed Shaba Usman

KASUWAR SHINKU

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Ware Naira Biliyan 9.7 Don Faxaxa Fitar Da Kaya Zuwa Wasu Qasashe Daga Idris Aliyu Daudawa

Ministan ciniki sana’oi da kuma sa jari Dokta Okechukwu Enelamah ranar litinin ce ya bada bayanin, za a farfaxo da maganar taimakawa ta vangaren kayayyakin da ake kaiwa qasashen waje, wato wani tsarin da ma’aikatar key i wanda kuma zai laqume kuxaxen da suka kai fiye da Naira bilyan 9 .75, a cikin kasafin kuxi na shekarar 2018. Ministan ya bayyana ma’aikatar ta samu kuxaxen shiga da suka kai Naira milyan 730 a shekarar data wuce ta 2017, koda yake dai an yi qiyasin za a samu Naiara milyan 812 ne. Ya ce, kuxaxen da aka samu ntuni aka tura su asusun bai xaya na gwamnatin tarayya. Ministan ya yi wannan bayanin ne lokacin da yake gabatar da bayanin yadda ma’aikatar ta kashe kuxaxen da aka bata a kasafin kuxi na 2017, da kuma yadda ta shirya, kashe kuxaxen kasafin kuxi na 2018.

Wannan bayanin ya yi shi ne a gaban kwamitin sana’oi na majalisar tarayya, a qarqashin shugabancin Honorabul Hussein Moriki. Ministan ya qara da cewar gwamnati ta yanke shawarar faffaxo da tsarin ne, wanda gwamnatocin da suka gabata, suka bar aiwatar da shi, dawo da shi wannan tsari yana da qyau ne domin yana taimakawa vangaren kasuwanci wanda aka yi tsakanin qasa da qasa saboda ai kayayyakin da ake fitarwa zuwa qasashen waje. Ya jaddada cewar yawancin kuxaxen za ayi amfani da sune ta vangaren, fitowa da sababbin dabaru akan fitar da kayyayyaki zuwa qasashen waje domin sayarwa, bugu da qari kuma akwai wasu shirye-shirye da aka yi niyyar aiwatar dasu, saboda da a samu damar ci gaba, da abubuwan da aka fara, amma kuma gwamnatocin da suka gabata suka dakatar. Ministan ya bada sanarwar kasafin kuxin ma’aikatar na shekarar 2018 wanda ya kai

Naira bilyan26, daga ciki kuxaxen da za ayi aiki sune fiye da Naira bilyan 23.3, sai kuma kuxaxen ayyukan yau da kullun, milyan 722.8. da kuma Naira bilyan 2.1 waxanda na albashin ma’aikata ne. Ya qara jaddda cewar ‘’tunda yake harkar masana’antu ta na vangaren tattalin arziki, al’amarin da gwamnatin tarayya, ta ba shi muhimmanci.Abin kuma yana daga cikin abubuwa uku waxanda suka kasance na sake farfaxo da qasa, wato yqai da karvar rashawa da cin hanci, tattalin arziki, da kuma tsaro. Abin yana buqatar gudunmawa da kuma haxin kan majalisun qasa domin ya kasancea samu cimma buri’’. Shugaban kwamitin Honorabul moriki ya ba ma’aikatar shawara cewar ya kamata ta miqe tsaye akwai abubuwan da za a qaru, musamman ma vangaren ci •Ministan Kasuwanci Okechukwu Enelamah gaban masana’antu waxanda sune ginshiqin tattalin arziki ita ma’aikatar da ta shirya su mayar dasu doka, domin wasu manufofi, waxanda kada a gaba a samu wata na ko wace qasa. Ya kuma bada shawarar da zata tura wa majalisun qasa, matsala danganda manufofi.

Gwamnatin Tarayya Ta Dasa Qarin Tiransifroma A Apo Da Katampe Daga Idris Aliyu Daudawa

Gwamnatin tarayya ta ce, tana qara qarfafa vangaren samar da wutar lantarki ne, domin a samar wa wasu wurare 15 na babban birnin tarayya, ta hanyar sa tiranfoma biyu, mai 200MVA a Katampe da kuma Apo cikin Abuja. Qaramin Minista na 2 na

ma’aikatar wutar lantarki, ayyuka , da kuma gidaje Mr Hassan Sulaiman Zarma wanda ya qaddamar da tiransfoma wadda kuxinta ya kai dalar Amurka $2.3 million, wanda ya kai Naira milyan (59.7) a Katampe, ya ce, abin an yi shi ne saboda ana buqatar a qara qarfin wutar lantarki ne da megawatt 7,000. Mai wakiltar minista

Babatunde Fashola a lokacin da ake qaddamar da tashar wutar lantarki ta 24, a taron wanda tashar samar da wutar lantarki, ta jagoranta, a Katampe, ya qara jaddada qudurin ita ma’aikatar na taro qungiyra masu masana’antu na Nijeriya, na yadda za a yi amfani da megawatt 2,000 a qarqashin wani tsarai na yadda mai amfani

da ita wutar lantarkin, a qarqashin dokar Hukumar kula da yadda ake samar dawutar lantarki. Manajan aikin na MBH Power Ltd wanda shi xan kwangila ne na Katampe Mr Rakesh Manapatra, suna kuma yin aiki awa 24 domin su cimma yadda aka yi yarjejeniya akan ita kwngilar, da kamafanin ya bada, domin shi kamfanin

ya ce, idan har ba a kammala shi aikin ba, kamar yadda aka xaura shi al’amarin, ya nuna ke nan kamar an maidawa shi kamfanin TCN aikin. Sabon shugaban na kanfanin samar da wutar lantarki (TCN) Mr Usman Gur Mohammed , a lokacin da ake qaddamar da tasher wutar lantarki ta Katampe ya bayyana cewar, an qarawa MVA 100 ne wanda ake da shi na da mai 120MVA, bayan nan kuma an sa wani a, Apo wanda yake da 190MVA domin ya taimaka wajen samar da wutar lantarki ga garuruwa 15 da suka haxa da Gwarinpa, Maitama, da kuma filin sauka da tashin jiragen sama. Ya ce, ‘’Da wannan abin ya nuna ke nan an qara qarfin wutar vlantarki zuwa 22OMVA, bayan haka kuma shi kuma 132/33KV yanzu an qara mashi qarfi daga 190 zuwa 290 MVA.


A Yau

21

Laraba 14 Ga Fabrairu, 2018 (27 Ga Jumada Ula, 1439)

Waxanda Kamfanin Dangote Ya Horas Sun Sha Alwashin Kawo Qarshen Wahalar Man Fetur Daga Idris Aliyu Daudawa

Sababbin ma’aikatan matatar manfetur ta Xangote injiniyoyi waxanda suka samu horarwa dangane da aikinsu, sun sha alwashin kawo qarshen matsalolin mai da ake fuskanta, a Nijeriya idan ita matatar ta fara aiki. Injiniyoyin sun dawo ne daga wata horarwar da aka yi masu a Bharat Petroleun corporation Ltd a qasar Indiya, kamar yadda kamfanin ya bada sanarwa. Injiniyoyin sun yi alqawarin su yi amfani da ilmin da suka sama da qaruwa da shi, lokacin da suka samu horarwa, domin tabbatar da cewar sun fidda qasar Nijeriya daga kunya ta maganar qarancin mai, idan matatar ta fara aiki. Injiniyoyin sun ce qaruwar da suka samu dangane da horo akan sanin makamar aiki ce ba tada ta biyu a Nijeriya, idan dai ana maganar manfetur ce da kuma iskar gas. Sun kuma ce abin ba zai sake faruwa ba, ace wai an samu matsalar mai a Naijeriya. Saboda sun ce ita matatar za a yi amfani da ita ne kamar yadda ya ce. Kamar yadda bayanin ya kasance matatar man ta Xangote qoqarin da take na fara aiki, ta na aikawa da ma’aikata, a hankali –a hankali, take tura injiniyoyinta zuwa matatar mai ta Bharat Indiya, ku san ita ce matatar mai babba a duniya, wajen horar da ma’aikata akan harkan tatar man fetur. Matatar man fetur ta Xangote ita ce babba a Afirka, wadda tana dama ta samar da gangunan mai

650,000, ana dais a ran nan bada daxewa bane zata fara aiki. Injiniyoyin Nijeriya sun bada labarin qaruwar da suka samu, ta vangaren aikin na tatar man fetur, su dai shugabannin matatar man fetur, wurin da matatar ta ke a Lekki. Sun ce sun qaru ta vangaren yadda ake yin aiki a rubuce da kuma bayyane yadda ake yin abin ba wata qunbiya qunbiya. Injiniyoyin sun ce a wurinsu wata dama ce yadda zasu ga a fili, yadda za a fara gina ita matatar man fetur xin, tun daga farko. Opeyemi Oyedepo wanda shi Injiniya ne na yadda ake yin abubuwa wato hanyoyin da ake bi , da kuma Igwe John shi kuma Injiniya ne na vangaren fetur da kuma iskar gas, sun shaidawa su shugabannin nasu yadda, suka sha wahala wajen

horar dasu da aka yi, sun kuma ce hakan, ya sa sun qaru da yadda zasu suka ma fuskantar aikin gaba xaya. Su injiniyoyin sun bayyana cewar sun qaru wajen horon da suka samu wanda suka haxa da yadda ya kamata, da kuma samar da ingantaccen aiki. Mai ba kamfanin shawara ta vangaren fasaha Mr Babajide Soyede ya nuna jin daxinsa cewar daga cikin injiniyoyi masu qwazo, na matatar man fetur ta Xangote suna daga cikin waxanda aka yi alfahari da yadda qwazon su yake. Ya ce, su shugabannin suna alfahari da su injiniyoyin saboda sun nuna lalle ba was suka koyo daga qasar Indiya ba. Soyode ya qara jaddada cewar matatar man ta Xangote ta zavi Bharat ne a

matsayin inda za a yi masu horo, saboda ita ce babbar matatar manfetur a duniya, a kuma shirye take wajen horar da matasan injiniyoyi, ba kamar yadda al’amarin yake ba, a qasashen Turai da kuma sauran wurare na yammacin duniya. Darektan kamfanin na sashen da ya qunshi ma’aikata da kuma yadda za ayi shi aikin, Mohan Kumar lokacin da yake bayanin dawowar su injiniyoyi daga wurin , da suka samu horo, ya ce , shi kamfanin yay i babbar dabara, yadda zai yi amfani da su injiniyoyi wajen fara gina ita matatar manfetur xin. Ya qara bayanin su matsan injiniyoyin an horar dasu yadda zasu iya aikin tatar man fetur yadda ya dace a yi ta, bugu da qari ma sun samu isasshen horon da ya kamata na yadda ilmin

aikin matatar man fetur. An kuma xauki su injiniyoyin aikin ne da kuma horar dasu saboda su fara ganin yadda za a gina ita matatar a gaban idonsu tun daga farkon fara abin. Injiniyoyin sun yi watanni biyar ne a Indiya, biyu a cikin aji, ukun kuma a wajen yadda ake yin shi aikin. Waxanda kuma suka horar dasu qwararru ne waxanda suke da shekaru fiye da 45 akan aikin matatar man fetur da kuma yadda ake tafiyar da ita. Kuma shi al’amarin horar da su ya zama dole ne, saboda shi Xangote yana matuqara son bada ta shi gudunmawar ne ta hanyar kamfani na xan qasa, suma injiniyoyin ana fatan yadda aka koya masu da horarwa, suma su yi hakan , idan matatar ta fara yin aiki nan gaba kaxan.

Badaqalar Naira Miliyan 124: EFCC Ta Gurfanar Da Tsohon Ma’aikacin Banki bisa tuhuma guda sha biyu akan zargin satar A ranar Litinin data kimanin naira miliyan wuce ne, Hukumar 124 da yin bugi da kuma Yaqi da cin hanci da canza alqalumman wni rashawa da yi wa tattalin kundaye. arzikin qasa zagon qasa Wanda ake tuhumar, (EFCC) dake shiyyar ya gurfana ne a gaban Ibadan ta gurfanar da Alqali mai shari’a A.A wani tsohon ma’aikacin Akinyemi,inda wanda Banki Adejare Sonde ake tuhumar, ya amsa a gaban Babbar Koto laifinsa akan zargin da dake garin Abeokuta a ake yi masa. cikin ta jihar Ogun a

Daga Abubakar Abba

Lauyan na EFCC Cosmos Ugwu ya roqi kotun data sanya ranar da za a ci gaba da shari’ar ya kuma roqi Kotun data sa ajiye wanda ake zargin a gidan Yari. Sai dai, shi kuwa lauya mai kare wanda ake tuhumar, E. E. Jacob ya sanar da Kotun cewar, tuni an gabatarwa da Kotun takardar bayar da

belin wanda ake tuhuma. Jacob ya kuma roqi Kotun data bari wanda ake tuhumar yaci gabada zama a ma’ajiyar hukumar ta EFCC, har zuwa lokacin da za a saurari takardar ta bayar da belin wanda ake tuhumar. Alqalin Kotun Mista Akinyemi ya amince da roqon lauyan da yake

kare wanda ake tuhuma, na cewar a ajiye shi a ma’ajiyar ta EFCC, har sai an saurari takardar bayar da belin. An kuma xaga sauraron qarar zuwa ranar Juma’a 16 ga watan Fabarairun shekarar 2018 don ci gaba da sauraron qarar da kuma sauraron takardar ta bayar da belin wanda ake tuhuma.


22

Kiwon Lafiya

A Yau

Laraba 14.2.2018 Tare da Aminu Shehu Ilu Dambazau (ASID)

Dogara Ya Xaukin Nauyin Jinyan Mutane Dubu 15,000 Kyauta A Bauchi Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Sama da mutane dubu goma sha biyar 15,000 ne ake sa ran yi musu aiki jinya kyauta wadda Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya, Yakubu Dogara ya xauki nauyin. Inda za su samu kulawar jinyar daga wajen kwararrun likitoci a Jihar Bauchi kan cututtuka daban-daban har sa ma da goma da suka jivinci bin adama. A wajen kaddamar da aikin jiyyar a jiya Litinin wadda yake guda a babban asibitin koyarwa na jami’ar ATBUTH Bauchi, Kakakin Majalisar Wakilai ta Nijeriya Honorabul Yakubu Dogara ya yi bayanin cewar wannan tallafin jinyar yana daga cikin shirinsa na taimaka wa gajiyayyu da kuma marasa qarfi da suke ciki al’umma, yana mai bayanin cewar xaukan nauyin jinyar wani shiri ne domin taimaka wa jama’an jihar ta Bauchi, ‘yan Arewa Maso Gabas da ma jama’an Nijeriya baki xaya. Kakakin majalisar qasa wadda ya samu wakilcin xan majalisa dokokin jihar Bauchi Aminu Tukur ya qara da bayanin cewar aikin nasu zai kwashe mako guda ana gudanar da shi a cikin garin Bauchi daga bisani ya yi bayanin cewar tuni aka samar da dukkanin magunguna da kuma kwararrun likitocin da za su yi wannan aikin bayar da jinya kyauta ga jama’an da za su amfana da tallafin. Yakubu Dogara sai ya yi fatan Allah ya baiwa jama’an da basu da lafiya, lafiya ya kuma qara wa masu lafiya qoshin lafiya da kuma amfani da ita. Daga nan kuma sai Dogaran ya kaddamar da shirin tallafin jinya kyautan, wadda duban jama’a za su mora. Da yake jawabi a wajen buxe aikin jinyar, shugaban sashin jinya na asibitin koyarwa ta ATBUTH, Dakta Muhammad Alkali wadda ya samu wakilcin muqaddashin Daraktan sashin (M.A.C) Rabi’u Gwadabe ya bayyana cewar tuni aka tanadar da dukkanin kayyakin aiki da kuma kwararrun likitoci da ma’aikatan jinya da za su jagoranci wannan aikin cikin kwarewa da bin dokokin aiki, sai ya buqaci masu cin gajiya tallafin da su kasance masu

bin dokoki da qa’idojin da aka shimfixa domin samun nasarar aikin yadda ya dace. Da yake qarin haske wa manema labaru kan wannan aikin jiya kyautar, Dakta Joseph Haruna Kigbu ya bayyana cewar a shekarar da ta gabata Yakubu Dogara ya yi aikin jinya kyauta wa mutane sama da dubu ashirin 20,000 a faxin jihar Bauchi da sauran jahohin da suka ci moriyar shirn, inda kuma a wannan shekarar 2018 ake sa ran mutane dubu sha biyar za su amfani da shirin, ya bayyana cewar sun ware wuraren duba cututtuka xai-xai har goma waxanda za su yi aikin duba jinya kyauta “kowace rana za mu ke duba marasa lafiya dubu 1,500 zuwa 1,800 inda kuma a sashin kula da lafiya kuma kowace rana za mu ke duba mutane xari biyar kowace rana, wadda za mu shafe tsawon mako guda muna yi”. A cewar shi Joseph xin. Dakta Joseph ya ci gaba da bayanin cewa “za mu daba lafiyar jama’a kuma za mu bayar da magunguna kyauta, daga cikin jinyar da za mu yi har da fixa (tiyata), baya ga tiyata kyauta, za mu mu duba sauran vangarori da suka haxa da ciwon suga, hawan jini, da jama’an da suke fama da cutar nan ta yanan ido dukkaninsu za a yi musu aiki, haka waxanda basu iya

karanta Qur’ani ko Baibul a sakamakon ciwon da idonsu ke yi dukka za a duba su kuma za a basu magungu kyauta, masu buqatar tabarau duk za a basu kuma kyauta”. Dakta Kigbu ya xaura da cewa “za mu yi gwaje-gwaje kala-kala, kuma za mu yi aikin xaukan hoto (scanning) kyauta wa dukkanin waxanda suke da buqata, masu buqatar gwaji na cutar nan mai karya garkuwar jiki HIV duk za mu yi musu aikin”. Ya ce, dukkanin wadda suka samu yana da cutar da aka yi masa gwaji za su bashi magani kyauta da ya jivci cutar da ke damunsa, domin tallafa wa jama’an da basu da qarfi. Ya xaura da cewa wata guda ne za su a dukkanin wannan aikin jinyar a faxin jihar Bauchi “za mu shafe mako guda muna duba lafiyar jama’a a wannan asibitin na ATBUTH, idan muka kammala mako na gaba za mu je babban asibitin garin Azare inda za mu yi aikin makamancin wannan, daga bisani a mako na uku kuma za mu je qaramar hukumar Dass, sai a qarshe mu je Tafawa Balewa-Bogoro domin yin wannan aikin kyauta don jama’an da basu da qarfin tattalin arziki na yin jinya su mori tallafin daga Kakakin Majalisa”. A cewar kwararren likitan. Da yake qarin bayani kan wannan tallafin, babban mai

tallafa wa Kakakin majalisar Dokokin Nijeriya kan hulxa da ‘yan jarida, Iliya Habila ya bayyana cewar dukkanin jama’an da suke Arewa Maso Gabashin Nijeriya suna da ikon cin gajiyar shirin, inda kuma ya xaura da cewa ba ma su kaxai ba har da wasu jahohi mutum ka iya zuwa a cikin waxannan makoninin domin samun tallafin ta bakin Kakakin Dogata, “shi Kakakin majalisa, tun ma kafin ya zama kakakin majalisa yake irin wannan tallafin a vangaren jinya. Bayan da ya zama kakakin majalisa sai ya ce bar ya faxaxa irin wannan tallafin nasa”. Habila ya xaura da cewa “a halin da ake ciki, dukkanin qananan hukumomi 20 na jihar nan za su zo cikin garin nan domin cin moriyar wannan tallafin, haka jama’an da suke Arewa Maso Gabashin Nijeriya, kai har jahohin Filato, Kano da irin su Jigawa da wasu jahohin ketare sukan zo domin cin gajiyar wannan tallafin, wadda muka yin a shekarar da ta gabata sun zo, wannan ma za su zo, kuma gasu nan ma kamar yadda kuke gani”. Habila ya ce jama’a na cikin wani yanayi na buqatar irin wannan tallafin sosai “Wani a nan bai da kuxin jinya ko ma na sayen katin duba likita, akwai jama’a da dama da suke cikin wani yanayi na

Ci gaba a shafi na

23


A Yau

23

Laraba 14 Ga Fabrairu, 2018 (27 Ga Jumada Ula, 1439)

Dogara Ya Xaukin Nauyin Jinyan Mutane Dubu 15,000 Kyauta A Bauchi Ci gaba a shafi na

22

rashin lafiya amma basu da qarfin da za su iya kula da lafiyarsu wannan dalilin ne ya sa Speaker ya ce bar ya kawo xauki wa jama’a a nan domin ya taimakesu”. A cewarsa. Xaya daga cikin iyayen da suka ci gajiyar wannan tallafin, wadda Allah ya basu haihuwa wata biyu da mako guda da suka shuxe, inda suka haifi wasu jarirai biyu a manne da juna, xaya da rai xayan kuma ba ta da rai, inda suka kawo kansu asibitin domin neman lafiyar ‘yarsu amma rashin kuxi bai iya kaiwa an yi musu tiyata domin raba jarirai da ke da rai da macacciyar ba, inda shi kuma Kakakin Majalisar ya xauki nauyin aikin tiyatar wadda kuxin tiyatar ya kai sama da miliyan xaya da kuma rabi. Shu’aibu Dan Galadima shi ne mahaifin jariran ya bayyana godiyarsa da cewa abun da aka yi musu basu

da kalmomin godewa sai dai Allah ya biya “ni mazaunin qauyen Maina Maji ne da ke qaramar hukumar Alkaleri, Allah ya ba mu haihuwa amma jariran xaya da rai xaya kuma babu rai, don haka muka tsinci kanmu cikin wani tashin hankali sakamakon matsanancin rashin babu da ke addabarmu, ni hatta kuxin zuwa asibitin nan ma gagarata yake yi, domin tun da muka haihuwa sama da wata biyu muke jigilar zuwa wannan asibitin. Don haka muna godiya sosai wa wanda ya xauki nauyin yi mana wannan tiyatar, inda fatan yadda kuka zo kuka samu an fara aikin ina fatan Allah ya sa a gama lafiya”. In Ji Mahaifin jariran da aka haifa a manne. Ita kuma matar jariran, Ikilima Sarkin Baka ta bayyana cewar ta haifi jariran ne xaya da rai da dukkanin hallitan xan adam xaya macen

kuma sam babu kai “ni ban ji canjin yanayi da ‘ya’yan na baya a lokacin da nake xauke da cikin waxannan jariran ba, dukkanin wani lokaci muna zuwa awu amma ba a shaida min ‘yan biyu na ke xauke da su ba. sai bayan da na haihu kuma sai xaya daga cikin jajiran ta fito babu kai, wannan dalilin ya sa muka zo neman jinya bamu da kuxi sai aka zo aka ce mana Dogara ya xauki nauyi. Yanzu haka ana kan tiyatar nan mun gode masa sosai”. A cewarta. Wasu ma dai da muka zanta da su a cikin masu amsar maganin a ranar ta farko sun nuna matuqar godiyarsu a bisa gudunmawar da Kakakin Majalisar ya kawo musu domin samar musu da lafiya kyauta. LEADERSHIP A Yau ta habarto cewar masu fama da jinya daban-daban ne za su samu wannan tallafin aikin

ce kawai. Wannan quduri ya kamata aamince da shi domin ya zama doka.’’ Shugaban qungiyar likitoci ta qasa ya nuna qin amincewarshi cewar duk wani abin da ake sa ranan asibitin zazzavin lasa ne,akai asibitin Irrua Specialist Hospital, a cikin motar marasa lafiya wadda ba ta qunshi abubuwan da suka kamata ba ta qunsa.Ya yi kira da gwamnatin tarayya da cewar lokaci ya yi da ita gwamnati zata xauki matak na tabbatar da cewar su yiwani abu akan cibiyoyin da aka daxe ana jira, da kuma abin da zai riqa taimaka masu, a qaddamar da shi abin sassan qasa shidabva

tare da vata lokac ba. Akwai wani tsari da aka yin a buxe a qalla xaya wato cibiya ta virology centre, a ko wanne sashe cikin sassa shida na qasa, amma yanzu biyu kaxaiake dasu, don haka muna cewar ya dace gwamnati ta aiwatar dsa qudurinta. Nijeriya ta yi ma cibiyoyi biyu girma. Ya ce, Qungiyar likitoci ta qasa NMA ta na mai matuqar murna ta ji cewar duk idana ka xauki matrakai na yin dukkan abubuwan da suka dace, z.q a daxe ana cin moriyar shi al’amarin Yanzu dai yaxuwar zazzavin Lasa ya shafi jihohi goma sha biyar, an kuma samu gwajinnda aka yi har

kyauta, haka zalika, dukkanin wannan aka duba lafiyarsa kowace irin cuta aka samu dukkanin tsadar kuxin jinya Dogaran ya xauki nauyi a cikin wannan adadin kamar yadda suka shaida domin taimakon jama’a. Kamar yadda suka bayyana sama da mutane dubu 15,000 ne za su samu tallafin jinyar a cikin Bauchi, inda kuma a sauran qananan hukumomi uku da za a je suma za a samu adadi masu tsoka wadda za a basu tallafin kyauta. Kawo yanzu dai jama’a na ta tururuwan zuwa asibitin ATBUTH da ke Bauchi domin samun shiga cikin masu cin gajiyar wannan tallafin jinya kuma kyautan. Yanzu haka dai tuni aka fara dabu lafiya da kuma bayar da magani ga waxanda aka tabbatar da cutar da suke xauki da shi, inda kuma aka fara da yin tiyata da sauransu.

Cutar Lassa: Cibiyar NMA Ta Buqaci Majalisa Ta Zartas Da Dokar NCDC

Daga Idris Aliyu Daudawa

Qungiyar Likitoci ta qasa ta yi kira da majalisun qqsa da su amince da dokar da zata bada danar kafa Hukuma mai hana yaxuwar cututtuka da kuma maganinsu. ‘’Qirqiro wannan Hukuma zai taimaka wajen yaqi da yaxuwar cuta a cukin qasa, bama kamar zazzavin Lassa, a cewar shugaban qungiyar na qasa, Mike Ogirima ya shaidawa jaridar Premiym Times ranar Alhamis.. Qarshen watan Nuwamba na shekarar data gabata Shugaban kwamitin kafiya ,matakin farko da kuam cututtukan da ke saurin yaxuwa, na majalisar dattawa ta qasa, Mao Ohuabunwa,ya ce, qudurin da zai samar da dokar kafa Hukumar yaqi cututtuka da kuma hana yaxuwarsu, za ayi qoqarin zartar da dokar kafin qarshen shekarar 2017. Shi dai wannan quduri an yimai karatu na xaya dana biyu a majalisar wakilai, bugu da qari kuma ya samu cikakken goyon baya, na masana harkar lafiya, amma har yanzu ba a zartar da shi ba, ya zama doka. ‘’Wannan wani bin ba, asi ne sabida asan irin halin da ake ciki, wato bayan an gabatar dashi amajalisar qasa, aka yi sauraren ra’ayin jama’a, ba zamu vata wani lokaci ba, muna qara maimata manufarmu

105 da cewar wannan lallai an kamuda ita cutar, akwai kuma mutuwa 31. Kamar yadda Ministan lafiya ya ce, a wannan shekara ta 2018 Nijeriya ta samu matsalolin 77 waxanda suka shafi zazzavin Lasa. Su waxannan an same su ne a jihohin Bauchi, Plateau,Taraba, Nasarawa, Binuwai, Kogi, Ebonyi, Rivers, Imo, Anambra, Edo, Dekta, Ondo, Osun,da kuma jihar Lagos. Ma’aikatan lafiya masu taimakawa su abin ya shafi wasu mutum goma daga cikinsu, a jihohi huxu, bakwai a Ebonyi,xaya a Nasarawa, xaya a Kogi, sai kuma sauran xayan a Binuwai.


24 TALLA

A Yau

Laraba 14 Ga Fabrairu, 2018 (27 Ga Jimadal Ula, 1439)


A Yau Laraba 14 Ga Fabrairu, 2018 (27 Ga Jumada Ula, 1439)

RAHOTON MUSAMMAN 25

Abubuwa 13 Da Ba A Sani Ba Dangane Murtala Muhammad Daga ISB Daurawa

Murtala Muhammad ya na xaya daga cikin shugabannin Nijeriya da ba zai yiwu a manta da su ba. Matashin shugaba xan shekaru 37, an yi mishi kisan gilla a ranar 13 ga watan Fabrairu, shekaru 43 kenan cur da su ka gabata; a wani shirin juyin mulkin da ba a yi nasara ba, qarqashin shirin Laftanar Kanar Buka Suka Dimka. Duk da an xauki shekaru da yin wannan xanyen aiki na kashe Murtala, amma jimamin rashinshi bai gushe ba a tsakanin sojoji da farar hula. An haifi janar Murtala Ramat Muhammed ranar 8 ga watan Nuwambar shekarar 1938 a garin Kano, ya yi karatu a kwalejin Barewa da ke Zaria. A shekarar 1959 ya shiga aikin soji, inda ya yi karatu a makarantar sojoji ta Royal Military Academy ta Sandhurst da ke Burtaniya. Janar Mutala ya samu mukamin Laftanal a shekarar 1961. Gabanin komawarsa Nijeriya a shekarar 1962, ya je rangadin aiki a qasar Kongo a matsayin wani wakilin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar xinkin duniya. A shekarar 1964 ne a ka ba shi muqamin Manjo na wucin gadi, bayan da a ka ba shi ragamar kula da sashin sadarwa a hedikwatar rundunar soji ta Kaduna. Janar Murtala ya koma Lagos inda ya zauna tare da kawunsa Alhaji Inuwa Wada a lokacin da ya zama ministan tsaro, kuma ya kasance a can har lokacin da a ka yi juyin mulki na farko a shekarar 1966. Shugaban qasa manjo janar Aguiyi-Ironsi ya qara masa girma zuwa Laftanal Kanal duk da kuwa shi ma wannan qarin girma na wucin gadi ne, a watan Afrilun shekarar 1966. Bayan juyin mulki na farko, sau uku janar Murtala ya na neman haxa kan sojojin arewa da ke Legas domin a yi juyin mulki na biyu, sai dai wannan yunquri bai yi nasara ba sakamakon harbe wasu sojoji da a ka yi a Abeokuta. Janar Murtala Ramat Muhammed ya taka rawar gani a yaqin basasar da a ka yi a shekarar 1967 lokacin

da Laftanal Kanal Ojukwu ke neman valle yankin Biyafara daga cikin tarayyar Nijeriya. A wancan lokacin janar Murtala ne ya jagoranci rundunar sojin da su ka murqushe sojojin Biyafara tare da kawo qarshen yaqin basasar kamar yadda ya bada sanarwa a ranar 21 ga watan Satumbar shekarar 1967. Ya na matsayin Birgediya ne sojojin da su ka yi juyin mulki na uku a Nijeriya su ka naxa shi a matsayin shugaban qasa , inda a watan Janairun shekarar 1976 a ka qara masa girma zuwa janar mai anini huxu, wato qololuwa kenan. Har wa yau a wannan lokaci ne janar Murtala ya qirqiro da sabbin jihohi 7 waxanda su ne Neja, Bauchi, Gongola, Benuwai, Ogun, Imo da Bendel. Sannan kuma ya bayyana buqatar mayar da babban birnin Nijeriya zuwa Abuja da kuma alqawarin miqa mulki ga farar hula a shekarar 1979. Kisan Janar Murtala Muhammad al’amari ne wanda ya girgiza Nijeriya, domin kuwa al’umma sun tsinci kawunansu a karo na farko an halaka shugaban qasa me mulki. Janar Murtala Muhammad ya na xan shekaru 38 a duniya a lokacin da a ka aikata mishi wannan xanyen aiki. Da yawan ‘yan Nijeriya ba su san wanene Murtala Muhammad ba, kawai dai an san shi ne a jikin kuxi Naira 20, sai kuma abubuwan da magabata su ka faxi wa ‘ya ‘ya da jikoki dangane da wanene shi. Saboda wannan dalilin ne LEADERSHIP A Yau ta tattaro muhimman abubuwa guda 13 waxanda ya kamata a sani dangane da Murtala. Su ne kamar haka: 1. An haifi Murtala Muhammad a ranar talata, 8 ga watan Nuwamban 1938, a jerin gidajen Kurawa da ke cikin birnin Kanon Dabo. Sunan Mahaifinshi Risqua Muhammad, mahaifiyarsa kuma sunanta Uwani Ramatu. Su takwas ne a gidansu, mace guda da maza 7. Kuma Murtala Muhammad ne na biyu. 2. A ranar 26 ga watan Janairun 1952, a ka xauki Murtala a matsayin xalibi na 941 a kwaleji, Kwalejin da a ka assasa ta a shekarar

1909. Ya na xaya daga cikin xalibai 10 da su ka je makarantar daga Kano. Xaya daga cikin abokan karatunsa shi ne marigayi Muhammad Shuwa, wanda ‘yan bindiga daxi su ka harbe shi har lahira a gidansa da ke garin Maiduguri a watan Nuwamban 2012. 3. Murtala ya halarci wata makarantar horas da soji a qasar Ghana wacce a lokacin a ke kiranta da ‘Regular Officers Special Training School, ROSTS’, wacce a yanzu a ka sauyawa suna zuwa ‘Ghana Military Academy. A can ne Murtala ya fito a matsayin mataimakin Laftanar. Obasanjo da Gowon duk sun yi wannan makarantar. 4. Murtala soja ne kaifi xaya, amma fa a wurin iyalinshi mutum mai sauqin kai. A shekarar 2006 matarshi Hafsat Ajoke Muhammad, wacce •Janar Murtala Muhammad bayarabiya ce, ta bayyana da kasantuwarta matar cewa; “A gida da wurin aiki, shugaban qasa a wancan mijina ba shi da bambanci. lokacin, ba ta yi xagawa da Kamar yadda bay a baki wuce gona da iri ba. Allah biyu a wurin aiki, haka ya albarkaci aurenta da ma a gida. Mutum ne Murtala da ‘ya ‘ya shida, su mai dattako da sanin ya ne; Aishat, Fatimah, Zakari, kamata.” Risqua Abba, Zalihatu, da 5. Ko kun san, Kawun kuma Jummai. Gabaxayansu Murtala ne ya yi sanadiyyan sun yi aure. haxuwarshi da matarsa 9. Ko kun san a qarshen Hafsah? Bayan da kawun 1964 ne Murtala ya kai na shi ya haxa su, su ka fara matsayin Manjo (amma na soyayya, haxuwarsu ta farko wucin gadi) ‘T/Major’. a jihar Kaduna ne, a can ne 10. Yaqin basasan da a ka kuma Murtala ya sanar da yi a Nijeriya wanda ya xauki ita burin zuciyanshi har ta watanni 30 a na gwabzawa kai ga an xaura musu aure (1967 zuwa 1970), Murtala a shekarar 1963 bayan ta na daga cikin waxanda su ka kammala karatunta, kuma fuskanci wannan gumurzu a wannan shekarar ne dai daga farko har zuwa ya kai muqamin Kaftin a qarshenshi. gidan soja. A shekarar 1965 11. Da yammacin ranar Allah ya albarkace su da xiya 30 ga watan Yulin 1975, mace, wacce daga bisani ta yi Murtala Muhammad ya karatu a kwalejin sarauniya gabatar da jawabi ga ‘yan ‘Queens college’ da ke Yaba a qasa a matsayinsa na sabon jihar Legas. shugaban qasa, kuma babban 6. A lokacin da a ka yiwa kwamandan askarawa. Murtala kisan gilla, xiyarsa 12. Murtala Muhammad Zalihatu ta na ‘yar shekara ne ya samar da wani kwamiti biyu da haihuwa, ita kuma wanda mai shari’ah Ayo xiyarsa Jummai ta na ‘yar Irikefe domin samar da jinjira. qarin jihohin Neja, Bauchi, 7. Bayan an kashe Gongola, Benuwai, Ogun, Murtala, yayin da labarin Imo, da Bendel a watan ya iso ga matarsa Hafsah, a Disambar 1975. Kwamitin take ta yanke jiki ta zube a kuma ya zo da rahoton da qasa cikin kuka da jimami, a ka yi amfani da shi wurin wanda hatta waxanda su ka samar da sabbin jihohi a kawo labarin sai da su ka shekarar 1976. firgita bisa tsoron halin da 13. Murtala namijin gaske za ta iya faxawa. ne, dakakke kuma marar 8. Ya zuwa yanzu dai tsoro. Sojoji ‘yan uwansa sun matar Murtala, wato Hafsah shaide shi da cewa bai san Ajoke tsufa ya kamata, a wargi ba, kuma ba ya amsan na matuqar ganin qimarta wargi balle ya yi wasa da a qasar nan, saboda duk mai kawo wargi.


RA’AYI 26

A Yau Laraba 14 Ga Fabrairu, 2018 (27 Ga Jumada Ula, 1439)

Gwamna Dankwambo: Alheri Ga Gombawa? Daga El-Mansur Abubakar, Gombe

Gwamnan jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo Alheri ga jama’ar jihar Gombe jihar da take da mutane sama da miliyan uku. Dankwambo gwamna ne mai kishin al’umma da kuma jiharsa wanda a lokacin sa ne aka samu matasa sama da dubu uku suka ajiye makamai daga harkar ta’addancin siyasa da ake kira Kalare suka zama masu amfani a tsakanin al’umma domin sun zama matasan gwamnan da ake kira Marshal suke kuma karvar albashi duk qarshen wata. Waxannan matasa suna taimakawa Dogarawan kan hanya wato (Traffic) wajen bada hannu akan titunan jihar wajen ganin an rage yawan aukuwar haxura, sannan sukan taimaka a bakin Makarantu wajen tsallakar da •Gwamnan Jihar Gombe, Dankwambo. yara zuwa makaranta haka Makaranta idan ba Malamai ya zama aikin banza. idan aka tashi. Baya ga firamaren Hassan Gwamna Dankwambo, ya Central anyi wasu ma ciri tuta wajen yiwa jiharsa domin kowanne mazabar ayyukan madalla na raya, dan majalisar tarayya ma’a qasa domin daga hawansa kowanne senatorial district karagar mulki a shekarar 2011 zuwa yanzu ya samar da an zabo makaranta daya ta hanyoyi ba adadi a dukkanin firamare an mayar da ita bene faxin jihar wasu unguwannin dan inganta karantun Yaran ma ko ta ina ya haxe su da Talakawa wanda zai yi dai dai tituna sannan ya mayar da da na ‘ya’yan attajirai da suke jihar tamkar Abuja, domin zuwa wasu kasashen duniya. A bangaren Makarantun duk wata mahaxa a jihar Sakandare kuwa kusan an sanya mata wutar hanya duk makarantun dake jihar mai bada hannu saboda rage Gombe dai dai ne wanda aukuwar haxura domin yana gwamnan talakawa Talban kishin talakawansa. Cikin gwamnoni 36 dake Gombe bai gyara ba saboda faxin Nijeriya, Alhaji Ibrahim yace shi abun alfaharin sa Hassan Dankwambo ne dama ilimi dan yana son gwamna xaya tilo da ya yi ‘ya’yan Talaka su shaida ribar ayyukan da kowa ke sa masa mulkin siyasa domin babu albarka har ake ganin ma a gadon da za’a bai wa Yaro da shekarar 2019 shi zai gaji ya wuce Ilimi dan idan kai shugaban qasa Muhammadu Uba baka bai wa Yaro ilimi Buhari wajen a matsayin ba ka tara masa dukiya ne ba lailai arzikin ya dore ba. zaxaxxen shugaban Nijeriya. Baya ga ilimin Firamare Daga shekara ta 2011 da da na Sakandare da ya ya xare bisa karagar mulkin inganta, ya samar da qarin jihar Gombe, ya shaidawa manyan Makarantun gaba duniya cewa abun alfaharinsa da sakandare a jihar don cike na xaya da na biyu da na gurbin yaran da ba sa samun uku shi ne Ilimi, don haka shiga jami’oi saboda yawan ne ma ya cannja tsarin wasu da ake da shi hakan ya sa makarantu a faxin jihar Talban Gombe ya samar da musammam Makarantun Kwalejin koyon aikin Shari’a Firamare waxanda idan aka gansu za a xauka cewa jami’oi ta Legal a garin Nafada, sannan ga Kwalejin Kimiyya ne. Misali a cikin garin Gombe da Fasaha ta jiha wato (State Firamaren Hassan Central Polytechnic) a garin Bajoga tana cikin mummunan ga kuma Kwalejin ilimi ta jiha yanayi, amma yanzu ya mayar COE a garin Billiiri wanda tuni da wannan makaranta ta sun fara aiki don samarwa da zama ta zamani kuma bene yaran Gombe gurbin karatu. Gwamna Dankwambo bai gidan sama, sannan aka tsaya anan ba ya kuma yi rage cunkoson xalibai daga kokari wajen sake samar da dari zuwa arba’in da biyar Jami’ar Kimiyya mallakar a kowanne aji ga Malamai jihar a garin Kumo Gombe nagartattu masu hazaka State University of Science waxanda aka dauka aikin and Technology wacce ita ma koyarwa domin dan an gyara

yanzu ake shirin fara karatu a cikin ta wanda hakan zai tabbatarwa da duniya cewa Dankwambo gwamnan ilimi ne gwamna mai kaunar talakawa da al’ummar sa. A bangaren aikace aikace na raya kasa har yanzu haka gwamna Dankwambo ya ginawa al’ummar jihar wani babban asibiti na Mata da kananan Yara mai gadajen kwana dari biyu wanda duk yankin arewa maso gabas babu irin sa shi ma an kammala saura kawai a bude shi ya fara aiki. A hanyar samarwa da jiha kuxaxen shiga ya gina wani katafaren dakin taro na kasa da kasa wato International Conference center akan hanyar Gombe zuwa Bauchi wanda zai dinga samarwa da jihar kuxin shiga. Don ganin ya rage cunkoso kuma ya magance matsalar tsaro Dankwambo, ya gina wata babbar tashar Mota da za ta haxe duk wata tashar mota a jihar wanda a cikin ta akwai caji ofis na ‘yan sanda akwai ofishin ‘yan kwanakwana masu kashe gobara, sannan akwai asibiti da wajen kwanan baqi idan suka zo wanda ita ma wannar tashar za ta qara samarwa da jihar kuxin shiga, sannan akwai gareji wajen gyara da koda direba ya zo motar sa ta lalace akwai inda za’a gyara masa a cikin tashar ba sai ya fita wani waje ba. Kasancewar gwamna Dankwambo masanin harkokin ci gaba yanzu a cikin fadar jihar Gombe idan karfe bakwai na dare ta yi akan kunna fitulun kan hanya wanda suke haska gari anyi hakan ne ma saboda kara kyawun gari idan dare ya yi

sannan kuma munafuki ba zai samu wajen fakewa ya cutar da mutane ba saboda ko ta ina akwai haske shi kuma munafuki bai son haske. Irin waxannan ayyukan da mai girma Gwamnan Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo yake yi ne yasa jama’ar Nijeriya suke rokon al’ummar Gombe da su yarda su basu Ibrahim Hassan Dankwambo dan ya amince ya amsa kiran su ya tsaya takarar shugabancin Nijeriya a zaven dake tafe na shekarar 2019 domin zai iya kuma zai yi abunda wasu basu yi ba. Masana suna cewa dalilin da yasa ake neman sa da ya amsa kiran yan Nijeriya shi ne ai ya yi aiki da shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo da kuma Marigayi Yar’aduwa da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonatan a matsayin babban akanta na kasa kuma ya taka rawar gani wanda duk shugabanin nan sun jinjina masa na irin fice da ya yi wajen rike kuxin Nijeriya ba’a sameshi da wata badakala ba. Yanzu dai a’lummar Nijeriya ta kowanne vangare kira suke da cewa Mai girma gwamna Dankwambo ya amsa kiran su ya yarda ya fito takara dan shi ne ake ganin zai iya cirewa Nijeriya kitse a wuta kuma zai iya xinke duk wata varaka da qasar take fama da shi na tsakanin Manoma da makiyaya da na qabilanci har ma da na ‘yan ta’adda. Kasancewar Dankwambo xan jam’iyyar PDP ne jam’iyyar da ta daxe tana mulkin Nijeriya kafin ta kuvuce mata tunda yake siyasa bai tava canja sheqa, ya bar ta ya koma wata jam’iyya ba; shi ya sa ma ake masa ganin shi xan jam’iyya ne mai aqida wanda bai da rawar qafa. Kuma saboda jajircewarsa da gaskiyarsa ne ya sa duk yadda aka fafata a zaven shekarar 2015 guguwar canji ta APC ta kada ta bar shi wanda shi ne gwamnan da guguwa ta kasa kai shi qasa a jam’iyyar sa ta PDP. Ganin hakan yasa gwamnonin qasar nan na jam’iyyar PDP na kudu da na Arewa da ma yankin yarbawa kai har da uwar jam’iyrar su ta PDP da wasu Sanatocin su suke goya masa baya na cewa shi ne dan takarar da suke ganin idan suka marawa baya zai iya kai su ga nasarar lashe zaven 2019 a matsayin sabon Angon Nijeriya idan Allah ya kai mu. Yanzu dai abun jira a gani shi ne yadda za ta kaya ko shi Dankwambo zai iya amincewa ya amsa kiran al’ummar Nijeriya ko ba zai amsa ba shi ne abun jira a gani.


27

A Yau Laraba 14 Ga Fabrairu, 2018 (27 Ga Jimadal Ula, 1439)

Tare da

Hangen Nesa

Kwamared Sunusi Mailafiya 0803 606 4695

NIJERIYA: Qasar Da Masu Kuxi Da Mulki Ke Sheqe Ayarsu

Abin yana bani mamaki idan natuna cewa muna zaune a qasar da ake ikirarin DIMOKRADIYYA ne, wato dai qasar dake da tsarin Shugabanci wanda Shuwagabanni suke da alhakin aikatawa talakawa ayyukan raya kasa, kyautata harkokin lafiya, ilimi, tituna da sauran jin daxin yau da kullum. Abu mafi mahimmanci shi ne kyautata harkokin kasuwancin kasa, wanda talakawa za su dinga samu amatsayin wata hanya ta samun kwandalolin da za su riqe kawunan su, tare da biyawa kan su buqatun da ya rataya a wuyansu. To, amma abin bakinciki, tashin hankali har ma da rainin hankali ga Shugabannin qasar nan, shi ne yadda suka bar talakawan qasar na shiga cikin taskun rayuwa, qasqanci har ma da talauci, ayayin da su kuma masu mulkin kullum suke kara samun na gwamna masu gidan rana, haka sauran masu kuxi ke kara kuxince wa duk da cewar dubunnan talakawan da ke qarqashin su, amma ba sa tausayin su ballantana har suma watarana su zama iyayen gidan kansu. Maganar gaskiya a Nijeriya ne kaxai talakawa kullum suke kuka da Shugabannin su, da kuma yanda masu hannu da shuni basa basu taimakon daya kamata, a qasar mune kawai

talaka ba shi da ‘yancin kansa, ba shi da mai taimakon sa, ba shi da wanda zai share kukan sa, gwamnati na zalintar sa, yayin da masu kuxi suke nuna musu rashin so qiriqiri, a qasar mune kaxai talaka ke mutuwa saboda YUNWA, dubunnan talakawa sun mutu saboda takaicin talauci, dubunnan mutane sun yanke jiki sun fadi saboda damuwar rashin halin xaukar nauyin iyalan su, dubunnan talakawa na guduwa subar iyalan su saboda rashin kuxin tattalin su, dubunnan al’umma da suke qarqashin ‘yan kasuwa sun hakura sun gudu, saboda cin mutuncin iyayen gidan su, wai laifin su kawai saboda su TALAKAWA ne. Idan har qasar nan za taci gaba da tafiya cikin irin wannan nuna tsagwaron banbanci tsakanin masu hannu da shuni, masu mulki, da talakawa, to tabbas mutane irin mu ba zamu zuba idanu ana cin mutuncin talakawa ‘yan uwan mu, dole ne mu fito mu yaqi masu xaukaka darajar kuxi, fiye da darajar dan’adam, wannan shi ne babban kuskure da zai janyo boren da bazai qare ba, idan har gwamnati takasa nuna wani tausayin ta da jin qanta ga talakawan qasar ta. Adalci na gwamnati ne daya kamata ta tarairayi ‘yayanta a mataki iri daya, ikon gwamnati ne data kula

da haqqoqin talakawa wanda yahau kanta, bawai a roqeta ta duba halin talakawa ba, abune daya zame mata dole data daidaita rayuwar ‘yayan ta, batare da nuna banbance tsakanin su ba, aikine akan gwamnati ta san cewa Adalci shi ne mataki na farko da za ta nunawa talakawan ta wanda zai nuna kokarin ta wajen gina dawwamammiyar kasa. Ban yadda da cewar gwamnati za ta kasa daidaita rayuwar talakawan ta ba, kasashen duniya da dama da suke mutunta haqqoqin mutanen qasar su, sun kokarta wajen daidaita rayuwar masu kuxi da talakawa, masu mulki da sarauta dukkanin su na tafiya a ma’auni iri daya, suna cuxanya a makarantu iri daya, suna rayuwa a gidajen da bai fi karfin kowa ba, suna hawa ababen hawa da duk kankantar albashin ka, zaka iya siya matsayin ka na talakan kasa, babu wariyar launin fata wajen xaukan aiki, makarantu, kotuna da sauran mu’amulayyar juna, a gwamnatan ce talakawa na da ‘yancin su, a siyasance talakawa na da ra’ayoyin su, duk hakan yasamu kawai saboda mutunta al’ummar su, talakawan qasar su kuma waxanda suke mulka. Cikin shekaru goma sha takwas da suka wuce babu wani abin kirki da talakawan qasar nan za su bugi kirji suce

gwamnati ta nuna damuwar ta a kansu, ita bata basu ilimi kyauta ba, bata basu magani kyauta ba, tsaro ya gagari gwamnati, yayin da ta vangaren kasuwancin ma wasu mutane ne kullum ke kara kuxanceea, hanyoyi babu kyau, ruwa da wuta sun gagari talakawan qasar su samu yadda ya kamata, ayayin da kowane laifi aka aikatawa talakawa, karshe shi ne yake juyewa ya koma mai laifi, wannan wane irin rashin adalci ne da imani? Ina kira ga Gwamnatin tarayya, gwamnatocin jihohi, majalisosin tarayya, da sauran masu hannu da shuni dasu kalli rayuwar talakawan qasar nan, su tuna cewar talakawa su ne kashin bayan kowace al’umma, talakawa ne ke kafa gwamnati, talakawa ke aiki a qarqashin masu hannu da shuni, don haka suna buqatar kulawa, suna buqatar akula da rayuwar su, suna buqatar a tabbatar da DIMOKRADIYYA a kansu, suna buqatar kyakykyawar rayuwa wacce suke gani a sauran kasashen duniya, suna buqatar adalci a zamantakewar su, suna gudun nuna banbanci da wariyar launin fata, suna buqatar a daidaita rayuwar su da sauran tsirarun al’umma da ake fifitawa fiye dasu idan har ana son kwanciyar hankali a qasar nan. Allah ya taimaki qasar mu Nijeriya Amin.


28

Tauraruwa Mai Wutsiya

A Yau

Laraba 14.2.2018 08174743902 wutsiya2019@gmail.com

Mai Zamba Da Sunan Aljani Ya Sami Matsuguni A Gidan Yari Daga Balarabe Abdullahi, Zariya

Yanzu haka rundunar ‘yan sanda ke Birnin Zariya a jihar Kaduna, ta sami nasarar yin kamun kazar kuku ga wani mutum mai suna Suleman Abdulrahman day a qware wajen yin muryar Aljannu, ya na zambatar mutane a sassa daban-daban a jihar Kaduna. Jami’in da ke gabatar da waxanda ake zargi da aikata laifi a kotun majastare da ke Birnin Zariya, ya bayyana haka ga Alqalin kotun Barista Umar Bature, a lokacin day a gabatar da wanda ake zargi a gaban Alqalin. Xan sandan ya ci gaba da cewar, wani mutum mai suna Malam Suleman Mohammed da ke gida mai lamba 34 a Unguwar Liman a Birnin Zariya ya kai qarar wanda ake Zargi a wannan ofishi cewar wanda aka damqe ya umurci wanda ya kai qarar day a sayar da motarsa, ya kawo ma sa kuxin zai yi masa addu’ar da zai sami kuxi fiye da yadda ya ba shi kuxin. A cewar xan sanda mai gabatar da ma su laifi a wannan kotu, Malam Suleman Mohammed ya ba wanda ake zargi Naira dubu sittin da biyar da farko, amma day a ga bai sami biyan buqata ba, shi ne ya shaida wa ‘yan sanda, bayan ya ce ma say a qara ba shi naira dubu arba’in da biyar. Wanda ake zargi ya ce wa mai qarar da ya kai ma

sa dubu arba’in da biyar, shi ne ya shaida wa ‘yan sanda wannan batu, a nan ‘yan sanda suka yi shigar manoma suka je inda wanda ake zargi ya ce a kai ma sa kuxin, suka yi kamar suna yin noma a gonarsu, sai wanda ake zargi ya tsaya nesa da inda ya ce a kai ma sa kuxin, suna ta waya da wanda ya kai kuxin cewar ya na ganinsa, ya ce wanda ya kai kuxin ba zai gan shi ba, domin shi Aljani ne. Bayan Malam Suleman Mohammed ya aje kuxin inda wanda ake zargi ya ce ya a je kuxin, sai wanda ake zargi ya je zai xauka, a nan fa ‘yan sanda suka yi ma sa qofar-rago, suka daqe shi a nan take. Bayan ‘yan sanda sun kawo Suleman Abdulrahman da

ke zaune a Layin DattawaRigasa ofishinsu, suka yi ma sa wasu ‘yan tambayoyi, a cewar xan sanda mai gabatar da waxanda ake zargi a kotun, sai suka gabatar da shi a gaban wannan kotu, domin yanke ma sa hukumci. Xan sanda mai gabatar da waxanda ake zargi a kotun ya ce, in zargin da ake yi ma sa, za a hukumta shi a qarqashin dokoki ma su lamba 377 da kuma 307. Bayan mai gabatar da waxanda ake zargi ya kammala bayani a gaban Alqalin kotun Barista Umar Bature, sai Alqali ya tambayi wanda ake zargi, cewar ya ji zargin da ake yi ma sa? Sai ya ce lallai ya ji, kuma ya aikata laifin da ake zarginsa das hi, amma sai ya ce, ya

na roqon Alqali ya yi ma sa sassauci wajen yanke ma sa hukumcin laifin da ya aikata. Alqalin kotun ya ce, tun da wanda ake zargi ya qi amincewa da cewar bai tsoratar da wanda ya kai qara ba, sai Alqalin ya ce za a ci gaba da binciken wannan zargi, amma tun day a amsa zargin ya zambaci Suleman Mohammed, a nan ta ke sai ya yanke masa hukumcin xaurin shekara goma a gidan yari, ko kuma ya biya tarar Naira dubu xari biyu. A qarshe, Alqalin kutun Barista Umar Bature, ya umurci rundunar ‘yan sanda su ci gaba da binciken wanda aka yanke masa hukumci na batun tsoratar da Suleman Abdulrahman da ya ce bai yi ba.

An Samu Nasarar Kashe Wani Qasurgumin Xan Fashi A Taraba Daga Idris Aliyu Daudawa

wamni tsarin bincike mai suna. Operation stop adnda Kwamishinan ‘yansanda search a faxin duk jihar. na jihar Taraba, Mr Dave Kamar yadda ya ce, shi Akinyemi ranar Asabar wanda ake tuhuma da ya bada sanarwar data aikata laifiun, ya shiga nuna rundunar ‘yansandar motar haya ne daga Jalingo jihar ta kashe xanfashi zuwa Takum, ya yi qoqqarin da makami, a Qaramar tserewa, lokacin da jami’in Hukumar Bali ta jihar, rubndunar suka tsayar da lokacin da ake ci gaba da motar da yake ciki, suka

duba suka kuma kama shi. Akinyemi ya qara jaddada cewar ‘An tsayar da motar domin a dubata, sais hi wanda ake tuhumar yay i tsalle ya fita daga motar ya aje jakar shi. Sai su jami’an suka yi tsammin da akwai wani abu, sai suka harbe shi a qafa, lokacin da yake gudu,

yana son voyewa a daji. ‘’Lokacin da aka duba jakar sai l guda ukuaka samu bindiga qirar Pistol, da kuma albarusai, da kuma wani magani duk a cikin jakar. Kwamishinan ‘yansandan ya ce wanda ake tuhuma da aikata laifin ya mutu ana kan hanyar kai shi asibiti.


29

A Yau Laraba 14 Ga Fabrairu, 2018 (27 Ga Jumada Ula, 1439)

Qasashen Waje Shugaba Biya Na Qasar Kamaru Ya Yi Bikin Haihuwarsa Cikin Barazana

A ranar Talata shugaba Paul Biya na Kamaru daya kwashe shekaru 35 kan karagar mulki ke bikin cika shekaru 85 da haihuwa, a dai dai lokacin da qasarsa ke fuskantar barazanar ‘yan aware. A irin wannan lokaci da Biya ke biki, kaso mafi yawa na matasan qasar da ke da

shekaru qasa da 30 sun buxi ido ne da ganin wannan shugaba kan karagar mulkin da xare tun 1982. A saqonsa ga matasan qasar, Biya ya buqace su da su fito don kaxa kuri’a a zaben qasar da za a yi qarshen wannan shekara, zaven da har yanzu shugaban bai bayyana

sha’awarsa ta neman wa’adi na bakwai ba. Tuni dai ‘yan takara da dama suka bayyana buqatarsu, in da a vangaren kujerar shugaban qasa kuma mutane ke taka tsan-tsan saboda abin da ka iya biyo baya. A ‘yan kwanakin nan dai shugaban na yawan balaguro zuwa qasashen waje musamman qasar Switzland, abin da yasa ake da shakku game da ingancin lafiyarsa, in da masu adawa da gwamnatin ke diga ayar tambaya kan lafiyar wannan shugaba da galibin al’ummar qasar ke rayuwa kasa da Euro 2 a kowacce rana. Bikin na yau na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da fama da tashe-tashen hankula a yankin Ambazonia da ke amfani da turancin Ingilishi, in da al’ummar yankin suka buqaci vallewa don cin gashin kai.

Tare da Rabiu Ali Indabawa 08069824895

Shugaban Qasar Jamus Ta Cimma Matsaya Kan Haxakar Jam’iyyun Manyan jamiyyun siyasar Jamus sun cimma yarjejeniyar haxin-gwiwa don kawo qarshen tankiyar da ake samu a tsawon watanni 6 tsakanin jamiyyar shugabar gwamnatin qasar, Angela Merkel da jamiyyar Social Democrat. Jamiyyun sun fitar da matsayarsu ta qarshe da suka bayyana da turbar tsira game da sabaninsu da kuma qasar ta Jamus da ke kan gaba a qarfin tattalin arzikin Turai, wadda kuma a fayyace za ta bada damar tazarce ga shugaba Merkel a karo na 4 a cewar ministan kuxin qasar Peter Altemier. Shugaba Merkel da ake ganin kwarewarta wajen jagoranci a Turai lura da rawar da ta ke takawa a nahiyar, an lura cewa kuzarinta ya ragu saboda yadda rikicin siyasar qasar da kuma sha’anin batun haxakar ya yi ki ci ya ki cinyewa. To sai dai ga dukkanin alamu, haxakar ka iya fuskantar cikas lura

da matakin shugaban jam’iyyar SPD, Martin Schulz na watsi da tsarin, abin da ya harzuka sauran jamiyyun gabanin zaman qarshen da za su yi wanda ake tsammanin anan ne zai bayyana matsayarsa ta buqatar wasu manyan kujeru da suka hada da na qasashen waje da na kuxi. Merkel wadda ta kwashe fiye da shekaru 12 kan mulki na fuskantar matsin lamba ne kan wasu manufofinta da suka haxa da na shigar baki qasar da kuma batun vallewar Birtaniya daga Turai. Cikin zazzafar mahawarar da suka tafka game da manufar shigar baqi ‘yan gudun hijira, manyan jamiyyun sun ce, za su rage adadadin zuwa dubu 180 daga dubu 220 da aka saba gani a duk shekara. Kuri’ar baya-bayan nan dai ta nuna farin jinin dukkanin jamiyyun na CDU da CSU ya ragu matuka daga kashi 33 zuwa30.

Jamiyyar ANC Ta Bai Wa Zuma Wa’adin Kammala Mulkinsa Rouhani Ya Fara Ziyarar Aiki A Qasar India

Jam’iyyar ANC mai mulki a Afirka ta Kudu ta bai wa shugaba Jacob Zuma wa’adin sa’oi 48 da ya sauka daga kujerarsa bayan kwashe dogon lokaci ta na gudanar da taro a asirce. Wannan shi ne mataki na qarshe da Jam’iyyar da shugabannin gudanarwarta 107 suka xauka na kawar da shugaban daga karagar mulki. Kafofin yaxa labaran qasar sun ce, shugabannin gudanarwar jam’iyyar ANC

sun cimma matsayar cire shugaban daga jagorancin qasar kuma nan take suka aike ma sa da matsayarsu ta cire shi daga mukamin shugaban qasa. Wata majiya ta shaida wa jaridun kasar guda uku cewar, jam’iyyar za ta rubuta wa shugaba Zuma wasiqa a yau Talata domin ba shi shawarar qarshe ta sauka daga muqaminsa bayan qin amincewa da buqatarsa ta yi ma sa jinkirin ‘yan watanni

qadan. Ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance da jam’iyyar ta bayar bayan taron, amma dokar qasa ta bai wa jam’iyyar damar janye shugaban qasa domin maye gurbinsa da wani, sai dai ba dole bane ya amince da buqatar haka. Idan dai shugaban ya qi amincewa da matsayin jam’iyyar, to ta na iya amfani da ‘yan majalisunta wajen tsige shi da kuma maye gurbinsa.

Shugaban Iran Hassan Rohani ya fara ziyarar aiki ta tsawon kwanaki uku a India domin havaka kasuwanci da kuma musayar fasaha a vangaren makamashi tsakanin qasashen biyu. Ziyarar shugaban ta farko zuwa India tun bayan hawansa mulki za ta xauke shi tsawon kwanaki 3 ta yadda za su tattauna muhimman batutuwa da suka shafi hulxar kasuwancin da ke tsakaninsu kafin komawarsa gida a ranar Alhamis din makon nan. Akwai dai kyakkyawar alaqa a tsakanin qasashen biyu, tun

daga lokacin da Firaministan India Nerendra Modi ya ziyarci Iran a shekara ta 2016, inda shugabannin biyu suka qaddamar da gina wata tashar jiragen ruwa a Chabahar kudu maso gabashin Iran. Haka kuma India na daga cikin jerin manyan qasashe uku da ke ci gaba da sayen man fetur xin Iran ko a lokacin da takunkuman Amurka ke tsaka da aiki a kan Iran. A lokuta da dama dai qasashen biyu kawayen juna kan tsoma baki kan al’amuran cikin gidan junansu kamar yadda ya faru a bara Inda jagoran addinin Iran


Wasanni 30

A Yau Laraba 14.2.2018

Tare da Abba Ibrahim Wada Leadership Ayau@yahoo.com

Hukumar Qwallon Qafa Ta Qasa Ta Naxa Sababbin Masu Horaswa

’Yan Wasan Najeriya Mata Sun Sauka A Qasar Ivory Coast Domin Fara Gasar WAFU

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Tawagar yan wasan qwallon qafar Nigeria ta mata wadda ake kira Super Falcons ta sauka a birnin Abidjan na qasar Ivory Coast, domin fafatawa a gasar WAFU CUP da za a fara a yau Laraba. Sabon mai koyar da yan wasan wanda da ya ja ragamar ‘yan wasan shi ne Thomas Dennerby wanda Wemimo Mathew da kuma Maureen Madu za su taimaka masa

wajen gudanar da aikin. Super Falcons mai tarihin lashe kofin nahiyar Afirka karo takwas za ta fara wasa da qasar Benin a ranar Alhamis, sannan ta kece-raini da Senegal ranar 17 ga watan Fabrairu da kuma Togo a ranar 19 ga watan nan da muke ciki. Mai koyar da yan wasan qungiyar yace sunyi shiri sosai domin bawa marada kunya a gasar domin basa zuwa kowacce irin gasa batare da burin lashe gasar ba inda yace buqatarsu kawai a gara gasar. Ya qara da cewa gwamnatin Najeriya tabasu kowacce irin gudunmawa domin tunkarar gasar tun daga lokacin da suka fara shiga sansani har kawo yanzu da ake shirin fara gasar wadda suke ganin zasu iya lashewa. A qarshe yace yana roqon yan Najeriya dasu cigaba da basu gudunmawa domin ganin sun lashe gasar sannan kuma suma zasuyi qoqarin ganin sun bawa marada kunya da zarar anfara buga gasar.

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Hukumar dake kula da qwallon qafar Nigeria ta nada masu horarwar da za su ja ragamar tawagogin qwallon qafar qasar, domin fuskanatar qalubalen da ke gabanta. Sai dai kuma nadin bai shafi mai horar da Super Eagles da mai jan ragamar matan Nigeria ‘yan shekara 20 da wanda ke horar da Flamingos waxanda suke da yarjejeniya da hukumar ba. Shugaban kwamitin tsare-tsare na hukumar, Alhaji Yusuf Ahmed Fresh ya ce an bi duk hanyar da ta dace wajen nada masu horarwar kuma sun fara aiki nan take. Ga jerin sunayen masu koyarwar da hukumar NFF ta nada don jan ragamar tawagoginta dake wakiltar qasar nan. Super Eagles ta ‘yan wasan gida da masu buga Olympic Koci: Salisu Yusuf Masu taimaka masa: Imama Amapakabo da Kennedy Boboye da Fidelis Ilechukwu da kuma Alloy Agu mai horar da masu tsaron raga. ‘Yan shekara 20 maza Flying Eagles: Koci: Paul Aigbogun

Masu taimaka masa: Abdullahi Maikaba da Abubakar Bala da Hassan Abdallah mai nemo ‘yan wasa da kuma Suleiman Shuaibu mai horar da masu tsaron raga. ‘Yan shekara 17 Maza Golden Eaglets Koci: Manu Garba Masu taimaka masa: Nduka Ugbade da Jolomi Atune Ali da Bunmi Haruna mai nemo ‘yan wasa da kuma Abideen Baruwa Olatunji (mai horar da masu tsaron raga. ‘Yan shekara 15 Future Eagles Koci: Alala Xanladi Nasidi Masu taimaka masa: Haruna Usman ‘Ilerika da Ahmed Lawal Xankoli da Patrick Bassey mai nemo ‘yan wasa da kuma Ernest Salolome mai horar da masu tsaron raga. U13 BOYS TEAM: Jolomi Atune Ali (Head Coach); Jude Agada; Abdullahi Umar Tyabo; Adewale Laloko (Scouting); Adeoye Onigbinde (Goalkeepers’ Trainer) A qarshe Fresh yaja hankalinsu dasu dage domin bada gudunmawa sosai don qasar ta cigaba da taka manyan matakai a harkar qwallon qafa ciki da wajen qasar nan.


WASANNI 31

A Yau Laraba 14 Ga Fabrairu, 2018 (27 Ga Jumada Ula, 1439)

PSG Ba Ta Gama Girma Ba Tukunna, In Ji Cavani

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Xan wasan qungiyar qwallon qafa ta Paris Saint German, Edison Cavani ya ce har yanzu Paris St Germain tana tasowa a fagen tamaula, bai kamata a saka buri a kanta a Gasar cin Kofin Zakaraun Turai ba. PSG, wadda ke mataki na daya a kan teburin gasar Faransa, za ta ziyarci Real Madrid a wasan farko na zagaye na biyua na Gasar Cin Kofin Zakarun Turai a ranar Laraba. Cavani ya shaida wa Manema labarai cewa bai zama dole sai sun lashe kofin na Zakarun Turai nan kusa ba saboda sun sayi sababbin ‘yan wasa kuma fitattu saboda haka suna gina qungiyar ne tukunna. Xan wasan ya ce karawar da za su yi a Bernabeu da Real madrid wani tsani ne da zai qara musu qwarin gwiwar da zai kai qungiyar mataki na gaba a wasanninta sannu a hankali. A bara a irin wannan matakin PSG ta doke Barcelona 4-0 a wasan farko, amma Barca ta yi nasara a karawa ta biyu da ci 6-1 jimilla wanda hakan yasa PSG din tafita daga gasar. A qarshe yace yana fatan yan wasan qungiyar zasu dage sosai domin ganin sun doke Real Madrid duk da cewa Madrid din c eke kare kambu a gasar bayan ta doke qungiyar Juventus a wasan qarshe na kakar da suka fafata a shekarar data gabata.

Ina Shan Wahala Idan Na Ce A Siyo Min Sabon Xan Wasa A Chelsea -CONTE Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Mai koyar da yan wasan qungiyar qwallon qafa ta Chelsea, Antonio Conte, ya ce yana shiga tsaka mai wuya wajen shawo kan mahukuntan qungiyar su sayo sababbin ‘yan wasa. Chelsea, mai riqe da kofin gasar firimiya ta kasa sayo fitattun ‘yan qwallo a lokacin da kasuwar musayar ‘yan wasa ta Turai ta ci a watan Janairu shekarar data gabata. Conte ya ce wani lokaci yana

Magoya Bayan Chelsea Sun Burge Ni Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Mai koyar da yan wasan qungiyar Chelsea, Antonio Conte ya jinjina wa magoya bayan kungiyar kan yadda suka mara ma sa baya bayan nasarar da ya samu ta doke qungiyar West Brom da ci 3-0 a filin wasa na Stamford Bridge a gasar firimiya ta Ingila. Magoya bayan na Chelsea sun yi ta rere waqa da sunan Conte, abin da ke nuna cewa, suna tare da shi duk da cewa qungiyar bata qoqari kamar irin na shekarar data gabata a qarqashin mai koyarwar. Wannan nasarar ta rage matsin lambar da Conte ke fuskanta, in da har aka fara nazari game da makomarsa a qungiyar bayan ya gaza samun nasara a akan qungiyoyin Bournmouth da Watford. Yanzu haka Chelsea mai riqe da kambi ta koma mataki na hudu a teburin gasar firimiyar, yayin da Conte ya ce, ya zama dole ya miqa godiyarsa ga magoya bayan Chelsea. Ya qara da cewa suma yan wasan qungiyar sun nuna halin girma da jajircewa da kuma sadaukarwa a wasan da suka buga saboda kowa yasan halin matsin lambar da suka tsinci a kansu a kwanakin baya. A qarshe yayi kira ga magoya bayan qungiyar dasu cigaba da dagewa domin cigaba da samun nasarori a qungiyar inda yace nan gaba kaxan komai zai wuce kuma abubuwa zasu koma daidai.

tattaunawa da wasu masu horar da qwallon qafa waxanda suka qware wajen shawo kan qungiyoyinsu kan fitar da maqudan kudin sayo ‘yan wasa. Conte ya kuma ce yana zaune lafiya tare da Roman Abramovich, sannan ya qara da cewa ba gaskiya ba ne cewa dangantakarsu ta yi tsami sakamakon rikici akan sababbin yan wasan da qungiyar ta siyo Chelsea ta sha kashi da ci 4-1 a hannun Watford a gasar firimiyar

data gabata sai dai a ranar Litinin ta lallasa qungiyar West Brom daci 3-0 a wasan mako na 27 na gasar. Chelsea zata kara da qungiyar qwallon qafa ta Barcelona a gasar zakarun turai sannan kuma har yanzu ba’ayi waje da itaba a gasar cin kofin qalubale na FA na qasar ta ingila. Ana tunanin dai Chelsea zata rabu da Conte a kakar wasa mai zuwa inda ake rade-radin zata dauki tsohon mai koyar da yan wasan Barcelona, Luis Enrique

Ko Ka San Qungiyoyin Da Messi Ya Fi Zura Wa Qwallo A Raga A Filin Wasa Na Nou Camp? Xan wasan qungiyar qwallon qafa ta Barcelona, Lionel Messi ya buga wasan da qungiyar ta buga canjaras da qungiyar qwallon qafa ta Getafe wanda kuma shine wasa na 300 a manyan wasanni bugawa qungiyar a filin wasa na Nou Camp Cikin wasa 300 da ya yi a filin wasan ya ci qwallo 212 a wasanni 201 a gasar La Liga, ya kuma buga wasa 56 a gasar cin kofin Zakarun Turai nan kuma ya ci qwallaye 55. Xan wasan na tawagar kwallon kafa ta Argentina ya yi wasa 34 ya ci qwallaye 31 a gasar Copa del Rey, sannan cikon tara ya buga Super Cup ya ci kwallo 11 a dai filin na Camp Nou. qungiyar da Messi yafi zurawa qwallo a filin Camp Nou ita ce Sevilla wadda ya zura wa qwallo 19, sai Espanyol 19, sannan Valencia da Osasuna da Athletic waxanda ya ci kwallo 16 kowacce. Xan wasan ya nuna farin cikinsa ga wannan nasara daya samu inda yace abin alfahari ne ace yana kafa irin waxannan tarihi a qungiyar sai dai yace zai cigaba da dagewa domin cigaba da samun nasarori musamman a gaban magoya bayan qungiyar A ranar Lahadi Barcelona ta buga canjaras tsakaninta da Getafe a gasar cin kofin La Liga a wasan mako na 23.


AyAU

LEADERSHIP 14.2.18

Laraba

Don Allah Da Kishin Qasa

JARIDAR HAUSA MAI FITOWA KULLUM TA FARKO A NIJERIYA

www.leadershipayau.com Leadership A Yau

LeadershipAyau

No: 090

N150

WASANNI

Jamiyyar ANC Ta Bai Wa Zuma Wa’adin Kammala Mulkinsa > shafi na 30

Muqalar Maciji Da Vera Sun Zama Laraba Manya A Gwamnatin Buhari El-Zaharadeen Umar, Katsina

08062212010

D

uniya rawar ‘yan mata, na gaba ya koma baya inji masu iya magana, wannan karin magana ya yi dai dai da irin abubuwan da suke faruwa a wannan qasa da ake kira Nijeriya wajen canza abu daga yadda yake zuwa wani abu da ban musamman idan abun ya shafa al’umma kai tsaye. Muna iya cewa Nijeriya ce qasa qwara xaya da take da wayayyo kuma goggagun mutane da suka san yadda za su tafiyar da ‘yan qasa yadda suke so ba tare da sanin cewa kan mage ya waye ba, kuma Makaho bai san ana kallonsa ba sai ya ga bai da sanda. Shi yasa yanzu idan wasu qasashen suka kalli Nijeriya ko ‘yan Nijeriya suka ce baku waye ba, baku da Ilimi, tsiya ta yi maku kanta, ba ku san abinda kuke ba, ba ku da shuwagabanni, har yanzu baku san inda ke yi maku ciwo ba, dabbobi sun fi ku kima da jamurta a qasarku, bana tunanin wani zai xaga yatsa ya ce an yi ba dai dai ba. Domin kuwa a yanzu hakan bayanan da suke yawo a kafafen sadarwa musamman na sociyal midiya a yanzu su ne, yadda aka samu wani gawurtaccen maciji ya yi wa naira miliyan 36 haxiyar kafino a ofishin hukumar jarabawar shiga jami’a (JAMB) wanda hakan irin sa ne na farko a tarihin wannan hukuma da kuma qasa baki xaya. Abin lura anan shi ne, matar dai ta yi wannan bayani ne, a matsayin iyakar gaskiyar ta a wajan ‘yan Nijeriya sai dai ana iya samun wasu bayanai kila idan za a zurfafa bincike domin qara jin wasu batutuwa masu xauka hanali da haushi da kuma ban dariya. Haqqiqa duk wanda ya ji batun da farko dariya ya yi, amma daga baya saboda sanin hali, wai kare ya ci alli, sai kawai a basar saboda a Nijeriya ne abubuwan da ake da tabbacin ba za su faru ba sai su faru, waxanda ake da tabbacin za su faru sai kuma a ga aqasin haka, domin haka Nijeriyar ta koma. Abinda yasa na yi wa wannan rubutu na yau taken Maciji Vera sun zama manya a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, shi ne ko ba komi, ba a da da xai daga fita daga badaqalar yadda vera ya hana shugaban qasa zuwa ofishinsa a cikin faxar gwamnatin tarayya ba nkwatsam sai ga wannna sabuwar al’amarar ta Maciji ya cinye naira miliyan 36. Bayanan da za su biyo baya sune za su tabbatar da kasancewar waxannan dabbobi sun zama manya a cikin wannan gwamnati domin a tunani irin na xan adam ko mutun ne ya yi abinda waxannan dabbobin suka yi sai ya fuskancin fushin ‘yan Nijeriya balantana dabbobin da ba sa zaune a cikin mutane. Lokacin da wannan lamari ya faru kowane xan Nijeriya ya yi fatan cewa ina ma za a ba su dama su yi fito-na-fito da waxannan veraye domin dai ko ba komi za su cutar da ‘yan qasa saboda hana shugaban qasa aiwatar da aikinsa yadda ya

kamata. To, amma wani batu da yake xaure kan ‘yan Nijeriya shi ne, sun kasa gane wanda ya yi dogon bincike ya gano cewa duk abinda aka faxawa ‘yan Nijeriya za su amince su kuma yadda da shi ya zama daiadai ba tare da neman qarain bayani ba saboda yadda ake kallonsu cikin bakin jahilci. Kodayake wasu da dama sun nemi a yi masu bayani dalla-dalla (Interpretetion) akan sabbin qyanqyasan verayen da suka gawurta sannan suka samu wurin zama a cikin faxar shugaban qasa, bayan haka kuma har sun sami damar hanashi shiga ofis domin gudanar da aikinsa a matsayinsa na shugaba mai cikakken iko. Alal haqiqa ire-iren waxannan kalamai ko batutuwa sun taimaka wajen qara zubar da kimar Nijeriya da ake ganin ta rage a idon ‘yan qasa da kuma sauran qasashe musamman waxanda suke tsararrakinta ne, sannan ga su kuma ‘yan qasa ya zama abin kunya irinsa na farko a tarihin qasarsu. Babu shakka akwai abubuwan da suke faruwa a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari sun yi kama da yadda dabbobi ke rayuwa a cikin dokar da ji, inda ya zamana babu mai iko sai wanda ya fi karfi, babu mai shanawa sai masu mulki, babu mai cewa a’a sai wanda ya murje idonsa. Idan ba haka ba, me yasa Malam Garba Shehu ya qware wajen tozarta Nijeriya da maganganu marasa amfana da kima a idon duniya? Me yasa duk wata wauta a wajansa ake jiran a ji fitowarta? me yasa yake ajiye abinda ake kira doka ya yi abinda ake kira san rai? Me yasa kullun yake mantawa da haxuwa da ubangijinshi? Me yasa ya fifita duniyarsa akan lahirarsa? Rashin kula da abubuwan da na zayyana wanda Garba Shehu ya xauka amatsayin aikin da ke gabansa wanda kuma yake a shirye wajen yin su kodayaushe ba zai tava bari ba, ‘yan Nijeriya su gane cewa Vera ba qaramin abu bane a wannan gwamnatin da ake kallo kamar ta sahabai.

Bari mu dawo akan maganar macijin da ya yi wa naira na gogar naira har naira miliyan 35 haxiyar kafino kila ko ruwa bai haxa da su ba, kai kasan wannan maciji ya cuci ‘yan Nijeriya da dama kuma bayanan da muke samu shi ne ba a nasarar damke macijin ba sai dai mai wannan maciji yana fuskantar bincike a halin da ake yanzu. Wannan batu kamar yadda na faxa tun da farko ya zo ma da wasu da mamaki wasu kuma tuni sun sa za ayi haka, tunda Nijeriya ce komi na iya faruwa amma dai wasu sun ce wannan lamari akwai rainin wayau sanfarin farko a cikinsa. Ga dai wasu ra’ayoyin ‘yan Nijeriya dangane da wannan wulakanta kai, inda wasu ke cewa kun tava ganin maciji ya hadiye naira miliyan 36? Rahotanni sun ce an tara kuxin ne daga sayar da katin da ake duba sakamakon jarrabawa. Haka kuma masu amfani da shafukan zumunta a Nijeriya sun yi ta arashi da suka kan yadda wata ma’aikaciyar hukumar tsara jarrabawar shiga jami’a JAMB, ta ce maciji ya haxiye naira miliyan 36 na hukumar, reshen jihar Benue. Ita dai Philomina Chieshe ta yi ikirarin cewa wani “hatsabibin maciji” ya shiga ofishin hukumar inda ya je wurin da ake ajiye kuxi ya haxiye naira miliyan 36. Haka rahotanni sun ce an tara kuxin ne daga sayar da katin da ake duba sakamakon jarrabawar ta JAMB. Ya zuwa yanzu bayanan da ke fitowa sun tabbatar da cewa an dakatar da matar, sannan an kaddamar da bincike kan yadda “maciji ya haxiye kuxin.” Hukumar EFCC, wadda ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati, ta aike da sakon Twitter inda take cewa ba za ta yi rahama ga macijin da ke haxiye kudi ba.” A Nijeriya dai an sha samun yanayi daban-daban da kuxin gwamnati ke yin batan dabo, amma a iya cewa wannan ne karo na farko da aka tava zargin wata dabba da dauke kuxi sai dai an tava zargin vera da hana shugaban qasa shiga ofis nya gudanar da aikinsa.

Idan muka yi karatun ta nutsu akan waxannan abubuwan da suka faru akwai darussa da daman gaske da yakamata kowane xan Nijeriya ya xauka ta yadda nan gaba komi zai faru za a san ta inda za a vullowa abin, amma idan aka riqe hannu aka zuba ido to akwai abubuwan da za su faru masu yawan gaske. Daga cikin abubuwan rainin wayau da wasa da hankali da za su biyo bayan waxanda suka gabata suna da yawa kuma za su fi so sa zuciyar ‘yan Nijeriya, kila nan gaba ace wani shaho ya xauki akwatin zave mai xauke da kuri’a miliyan xaya kuma maganar ta tafi a haka. Kila nan gaba a ce motar shugaban qasa ta sha man fetur na miliyan 100 a ranar xaya da dai sauran maganganu marar sa tsari. Kazalika wasu sun yi tunanin cewa hatta waxanda suka gama mulki a shekarun baya da wahala su yi abinda waxannan mutanen suke yi. Gaskiyar maganar shi ne, dole hukumomin tsaro da kungiyoyi masu fafutukar yakin da cin hanci da rashawa su nuna jan ido akan irin wannan badaqala irinta ta farko a tarihin duniya domin hana wasu damar nan gaba qara yin wata kashashava. Kuma idan har hukumomi da masu mulki za su riqa amfani da karfin mulkinsu wajen raina hankalin ‘yan Nijeriya ta hanyar yin maganganun ‘yan matan amarya abubuwan da za su biyo baya nan gaba, ba masu kyau ba ne, kuma nan gaba sai an rasa wanda za a kalla a yi masa kwatankwacin irin waxannan maganganu. A qarshe muna jiran Garba Shehu da martani daga fadar shugaban qasa domin jin wani sabon al’amarin mai ban mamaki tunda anan vangaran ya fi qwarewa, tunda yanzu ayar tambaya tana nuna shi, in dai ka ji ya yi magana to xayan biyu sannan a jira, za a ji maganar ba xadi ba hikima cikinta balanta tausayawa.

Babba Da Jaka Maciji ya haxiye miliyan 35 a ofishin JAMB –Labarai

Ha ha ha! Kat kenan..

Ana shiryawa da buga LEADERSHIP A Yau a kamfanin LEADERSHIP GROUP LIMITED, lamba 27, kan Titin Ibrahim Tahir, a Gundumar Utako, Abuja. Tarho: 09-2345055; Fax: 09-2345360. P. O. Box 9514, Garki II, Abuja. Ofishin mu a Legas: 34/36 Titin Adegbola, Anifowose, daidai Oba Akran, Ikeja. Tarho: 01-8963459. E-mel: leadershipayau@yahoo.com

A Yau February 14, 2018  

A Yau February 14, 2018

A Yau February 14, 2018  

A Yau February 14, 2018

Advertisement