Page 1

15.3.18

AyAU Alhamis

LEADERSHIP Don Allah Da Kishin Qasa

Jaridar hausa mai fitowa kullum ta farko a nijeriya

www.leadershipayau.com Leadership A Yau

15 Ga Maris, 2018 (26 Ga Jumadal Thani, 1439)

LeadershipAyau

No: 107

N150

Qungiyar Tsoffin Xaliban ABU Za Ta Karrama LEADERSHIP Daga Sulaiman Bala Idris, Abuja

Jaridar LEADERSHIP ta samu karramawa ta musamman na lambar yabo daga Qungiyar Tsaffin Xaliban ABU. Qungiyar ta Tsaffin Xaliban Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya za ta karrama LEADERSHIP ne a matsayin kamfanin da yayi zarra a shekarar 2018.

Qungiyar Tsaffin Xaliban ta ce ta yanke shawarar bayar da wannan lambar yabo ne ga LEADERSHIP saboda irin namijin qoqarin da kamfanin jaridar yake yi a rahotanninsa da wanzuwar Dimokraxiyya a Nijeriya. Yayin da yake bayani a wata ziyarar sada zumunci da ya kawo hedikwatar LEADERSHIP dake Abuja, Shugaban

Qungiyar Tsaffin Xaliban ABU na qasa, Farfesa Ahmed Tijjani moray a bayyana jaridar LEADERSHIP a matsayin wata samfuri kuma jagora ga hukumomi da sauran al’umma. Sannan kuma Farfesan ya yaba matuqa da namijin qoqarin da Kamfanin Rukunan LEADERSHIP ya yi wurin fara buga jaridar LEADERSHIP A Yau; a

matsayin jaridar Hausa ta farko a tarihin Nijeriya. Farfesan ya ce, wannan babban lamari ne da ya kamata a yaba, domin an kama hanyar raya al’ada da kuma qarfafa al’umma wurin yin karatu da harshensu na gida.

>Ci gaba a shafi na 2

Za Mu Hukunta Masu Hannu A Sace Matan Dapchi –Buhari 4

’Yan Sanda Za Su Yi Haxin Gwiwa Da Mafarauta Daga Bello Hamza

Rundunar ‘yansandan jihar kaduna ta shiga yarjejeniya da qungiyar mafarauta domin fustantar matsalar tsaro da ta addabi jihar. Kwamishinan ‘yansanda na jihar Mista Austin Iwar ya bayyana haka jiya Laraba bayan wani tattaunawar sirri da suka yi da qungiyoyin mafarautan, ya ce, zasu yi amfani da ximbin qwarewar mafarautan wajen fatattakan ‘yan ta’adda a jihar. Ya ce, waxanda za a yi aiki dasu a cikin mafarauta zasu samu horo na musamman kafin su fara aiki tare da jami’an tsaron jihar. Ya ce, wannan matakin ya zama dole domin a taqaita aiyukan mafarauta a jihar da buqatar da ake da shi na qarfafa waxanda suke xauke da makamai ba bisa qaida ba su miqa makaman su ga hukuma. • Shugaban Rukunan Kamfanin LEADERSHIP, Sam Nda-Isaiah tare da Farfesa Ahmed Tijjani Mora jiya a lokacin da yake amsar takardar shaidar karramarwar da Qungiyar Tsaffin Xaliban Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya za su ba LEADERSHIP a matsayin Kamfanin da ya yi zarra a shekarar 2018

>Ci gaba a shafi na 2

Hukumar NIS Ta Samar Da Naira Jigawa Za Ta Fara Safarar Biliyan 38 Ga Tattalin Arziqi Zovo Zuwa Qasar Mexico > Shafi na 5

> Shafi na 5


2 labarai

A Yau Alhamis 15 Ga Maris, 2018 (26 Ga Jumada Thani, 1439)

Waxanda Suka Yi Garkuwa Da Fasto A Akwa Ibom Sun Buqaci Fansar Miliyan 10 Daga Umar A Hunkuyi

Mutanan da suka sace Mista Akpan Udoneke, babban limamin Cocin Apostolic, na yankin Ikot-Akoa Idem, da ke Qaramar Hukumar Ukanafun, ta Jihar Akwa Ibom, sun bukaci da a biya su Naira milyan 10 a matsayin fansa kafin su sako shi. A ranar Talata ne aka ce masu garkuwa da mutanan sun yi magana da iyalan Limamin da kuma Cocin na shi ta waya. Qoqarin da wakilinmu ya yi na yin magana da jami’an Cocin ya ci tura, amma wata majiya daga iyalansa, wacce ba ta so a ambata sunanta ba, ta shaida mana cewa, masu garkuwa da Limamin sun kira iyalansa da kuma manyan Cocin a waya inda suka bayyana bukatar na su. An dai sace Mista Udoneke ne da misalin qarfe biyar na safiyar ranar Litinin, a daidai lokacin da yake jagorantar mata wasu addu’o’i a Cocin. Amma Kakakin rundunar ‘Yan Sandan Jihar, Mista Macdona Ogeche, ya ce, ‘Yan Sandan ba su da labarin wannan bukata ta masu garkuwa da mutanan. Sai dai kuma, Kwamishinan ‘Yan Sandan

Jihar, Mista Adeyemi Ogunjemilusi, ya yi hani ga dukkanin aikace-aikacen qungiyoyin asiri a Jihar. Da yake magana a wajen taron da ya yi da shugabannin al’ummun Jihar a ranar Talata, Ogunjemilusi, ya baiwa ‘yan ta’addan wa’adin kwanaki 21 da su miqa dukkanin makaman su, ko in sun qi su gamu da fushin hukuma. Da yake jimamin yadda ayyukan ‘yan qungiyoyin asirin ke qara tavarvara a Jihar, Kwamishina ya ce, ba zai yiwu gwamnati ta zura ido ba tana kallon ‘yan wasu qalilan suna yin barazana ga zaman lafiya da ‘yan’uwantakan mutanan Jihar. “Ba tare da zaman lafiya da tsaro ba, ba wata nasarar da za mu iya samu. Matuqar aka ce ana aikata laifi ko ana tsoron aikata laifin, ba wani abin kirkin da za a iya aikatawa, duk harkoki tilas ne su tsaya. Mutane kuma za su ji tsoron zuwa su zuba jarin su a Jihar ku. “Na fahimci cewa, yawanci Kiristoci ne a Jihar Akwa Ibom, aqalla kashi 90 na mutanan Jihar nan Kiristoci ne, sannan kuma duk mun san sama da kashi 60 ko ma 70, duk suna cikin qungiyoyin asiri ne.

An Bizne Marigayi Janar Shelpidi A Gombe Daga Umar A Hunkuyi

An bizne gawar marigayi Manjo Janar Timothy Mai Shelpidi, tsohon Kwamandan rundunar sa ido ta qasashen yammacin Afrika, (ECOMOG). Jiya ne da yamma aka bizne shi a qauyan su, Boh, da ke Qaramar Hukumar Shomgom, ta Jihar Gombe. Ya sami tsira a wani yunqurin kisa da wasu ‘yan bindiga suka kai ma shi a shekarar 2004, lokacin da suka iske shi a gidansa da ke Abuja, suka kuma yi ma shi harbi da dama. An haife shi ne a ranar 4 ga watan Satumba na shekarar 1948, Janar Shelpidi, ya mutu ne a ranar 2 ga watan Maris 2018, yana da shekaru 70 a duniya. Ya shiga rundunar Soji ta qasa a shekarar 1970. An naxa shi a matsayin Kwamandan rundunar

ta ECOMOG ne a watan Janairu na shekarar 1998. Ya yi ritaya daga aikin na Soja ne a matsayin Manjo Janar bayan ya shafe shekaru 29 yana yin aikin na Soja. Da yake jawabi a wajen jana’izar, Gwamna Ibrahim Hassan Xankwambo, ya ce, “Mun rasa wani babban Xa na mu, wanda ya taka mahimmiyar rawa wajen qirqiro Jihar Gombe a shekarar 1996.” Janar Shelpidi, ya shiga harkokin siyasa a shekarar 2003, inda ya yi takarar kujerar gwamna a zaven shekarar ta 2003. Ya kuma tava riqe muqamin Jakadan Nijeriya a qasar Rasha, inda aka haxa ma shi har da qasashen Belarus da kuma Georgia daga shekarar 2008 zuwa 2011. Ya mutu ya bar matar aure guda, mahaifiyarsa, da kuma ‘Ya’ya da Jikoki.

Tsaro: ’Yan Sanda Za Su Yi Haxin Gwiwa Da Mafarauta

Ci Gaba Daga Shafin Farko

“Suna xauke da makamai ba bisa qaida ba, muna son qarfafasu su mayar da makaman ga hukuma muna kuma son horar dasu yadda zasu fuskanci wannan sabo aiki da za a xora musu” inji Iwar “Ko wanne xan qasa na da haqqin bayar da gudummawa a harkar samar da tsaro shi yasa su da raxin kansu domin bayar da nasu gudommawarsu suka buqaci haxin kan mu, amma fa dole a koya musu yadda zasu gudanar da aiki, mu kuma sanya musu ido domin kada su wuce gonad a iri” A kan wa’adin mako biyu

da aka ba ‘yan sara suka su tuba ko a hukunta su, kwamishinan ya ce a halin yanzu a na nan ana ta kama su domin hukunta wa. “A halin yanzu rundunarmu ta kama da dama kuma za a gabatar dasu gaban kotu domin hukunta wa da zaran mun kammala bincikenmu” “Zamu ci gaba da aikin kama su muna kuma buqatar jama’a su bamu haxin kai domin samun nasarar wannan aikin” Kwamishinan ‘yansandan ya ziyarci unguwar Television da Sabon tasha inda ya tattauna da jama’a mahimmancin kula da tsaro a duk inda suke. Kwamishinan ya tabbatar

musu da qarin tsaurara matakan tsaro a tashar mota da kasuwannin jihar. “Duk inda ake da qarancin jami’an tsaro zamu qara jami’anmu duk in da ake da qarancin ofishoshinmu zamu buxe sabbi, muna matuqar buqatar goyon bayan ku domin samun nasarar wannan aikin” A jawabinsa, sakataren qungiyar masu manyan motoci na Talabishan garage Mista Sunday Kanu, ya yaba wa rundunar ‘yansanda a qaoqarin da suke yi na tsaftace jihar daga vata gari, ya nuna gamsuwarsa da fatan hakan zai dawo da zaman lafiya da tsaro a tashoshishin mota a faxin jihar.

Qungiyar Tsaffin Xaliban ABU Za Su Karrama LEADERSHIP Ci Gaba Daga Shafin Farko

Dangane da bayar da lambar yabo da qungiyar ta saba bayar wa, Farfesan ya ce a kowacce shekara suna zavo zaqaquran mutane da kamfanonin da suka yi zarra don a karrama su. A yayin ziyarar sada zumuntar, Farfesan ya samu tarba ta musamman ne daga Shugaban Rukunan Kamfanin LEADERSHIP, Sam NdaIsaiah. Farfesan ya sanar da Shugaban Rukunan Kamfanin na LEADERSHIP cewa; “A madadin majalisar zartaswar

TSoffin Xaliban Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, ina mai farin cikin sanar da kai cewa, qungiyar tamu ta cimma matsayar karrama kamfaninka da lambar yabo a jerin karramawar da za mu bayar na wannan shekarar ta 2018, wanda za a gabatar a ranar 14 ga watan Afrilu a Babban Birnin Tarayya Abuja. “Karramawar za ta qumshi jawabai wanda an saba gabatarwa duk shekara, sannan sai a bayar da lambar yabo. Muna zavo zaqaqurai ne da kamfanoni masu tasiri da amfani a cikin al’umma.” inji shi.

A taqaitaccen jawabinsa, shugaban Rukunan Kamfanin LEADERSHP, Sam NdaIsaiah ya bayyana godiyarsa ga wannan mutuntuwa da Qungiyar Tsoffin Xaliban ABU suka nunawa LEADERSHIP. ya kuma bayyana Farfesa Mora a matsayin babban wansa, wanda ke ba shi shawara a duk lokacin da buqatar hakan ta taso. Sam ya ce; “Mun gode qwarai da wannan karramawa taku. Zan so na bayyana farin cikina dangane da qaunar da kuka nuna mana, sannan kuma za mu ci gaba da baku goyon baya a dukkanin ayyukanku.”


3

A Yau Alhamis 15 Ga Maris, 2018 (26 Ga Jimadal Thani, 1439)

Ra’ayinmu

K

Mu Bayar Da Gudummawar Gina Qasarmu

owannen mu na da irin gudummawar da zai bayar ta hanyar yin abin da ya dace tun daga shi kansa, sai kuma sauran mutanen da suke qarqashinsa, a ce ana yin haka wato duk hakkokin da ya kamata ya yi ya kasance yana yi, ai tuni da an yi nisa da kuma samun gaggarumin ci gaban da kowa zai yi sha’awa da kuma alfahari da shi. Wannan ma na magidanci xaya ne don haka idan abin ya kasance a na yin duk abubuwan da suka dace sai unguwa ta inganta, in ya kasance haka ashe ke nan da babu wasu matsalolin da ake fuskanta da suka yi kama da na yanzu. Kamar jinka idan ana buqatar a xora bisa tafarfara, ai mutane ke tashi su kama har a samu xora ita jinkar. Hakanan shi ma cigaba bai samuwa sai kowa ya bada haxin kai da kuma gudunmawa, ba wai ya tsaya daga wani wuri ba, ya riqa cewar masu qoqarin yin wani abin da zai kawo ci gaba ba su iya ba, shi kuma xin da yake ganin ya iya, bai da wata katavus. Maganar tafiyar da Nijeriya da kuma wasu abubuwan da zasu kawo ci gabanta hakkin kowa ne, ba wai sai wani ya tsaya yana hangen na wani ba, bayan shi kuma bai na shin ba, wanda abin da ya kamata ke nan. Kowa yana da abin da ya dace amma sai yaqi yana hangen na wani can , yana cewa ai bai dace ba, saboda dama ai laifi ance tudu ne taka naka ka hango na wani. Idan kowa yana yin abin da ya dace da shi tun daga ciki har waje ai da tuni zuwa yanzu halin da muke ciki ba wanda zai ji haushin wani dangane da wani abu can daban. Ita qasar Nijeriya duk ta qunshi dukkan abubuwan da mutum yake tsammani, a matsayinta na uwa da uba wadda ta haifi manyan ‘ya’ya har ma da jikoki, waxanda za a ce a shekarunta da suka kusa kai hamsin da takwas kamata ya yi, yanzu sai dai ta zauna, a riqa yi mata abubuwa. Maimakon haka sai aka samu rarrabuwar kai tsakanin ‘ya’yanta, aka koma ana yin zaman ‘yan marina wato kowa da inda yasa gabansa, duk wannan ma ba wani abu bane idan dai har daga qarshe za a tuna

cewar da akwai fa abubuwan da suka kamata ayi. Ba wani cigaban da za a samu musamman idan rarrabuwar kai ta yi qamari, ya zama ruwan dare gama duniya. Duk ba ayin hakan musamman ma idan aka yi la’akari da yadda ita Nijeriya ta kasance cikin nan

xumi can zafi, wani wurin kuma wuta c e ke ci bal- bal, wannan sai mutum ya tuna da yadda ake shekarun baya da suka wuce. Qara samun rarrabuwar kan da ake samu ku san wannan ana iya cewar duk rana ce, wanda hakan ya sa ba a faxawa wa juna

EDITA Sulaiman Bala Idris

MATAIMAKIN SHUGABA (NA MUSAMMAN) Christian Ochiama

MATAIMAKIN EDITA Bello Hamza

DARAKTAN SASHE Mubarak Umar

RUKUNIN KAMFANONIN LEADERSHIP SHUGABA Sam Nda-Isaiah

BABBAN MANAJAN DARAKTA Abdul Gombe BABBAN MANAJAN DARAKTAN KADARORI David Chinda MANYAN DARAKTOCIN KAMFANI Dele Fanimo Felicia Ogbonlaiye DARAKTAN KULA DA MA’AIKATA Solomon Nda-Isaiah DARAKTAN KULA DA KADARORIN KAMFANI Zipporah D. Tanko MANYAN MANAJOJI Ibrahim Halilu Femi Adekunle Ebriku John

manufarmu

LEADERSHIP A Yau jarida ce da ake bugawa a Abuja. Ta yi tsayuwar daka wajen tabbatar da shugabanci da wakilci nagari. Jaridar za ta ci gaba da kare muradun al’umma, ba kare ra’ayi da muradun mahukuntanta kaxai ba. Da waxannan qudirorin ne muke fatan jama’a za su xora mu kan Mizani. Haka kuma duk ra’ayoyin masu karatu da muke bugawa, ba manufar kamfanin LEADERSHIP ba ne, ra’ayin masu karatun ne. Sai dai, ba za mu tava mantawa da dalilin wanzuwarmu a doron qasa ba, wato: Don Allah Da Kishin Qasa!

gaskiya, bare ma har akai ga ma yin tunanin ya fa kamata a yi abubuwan da zasu kawo cigaba na ko ina ne ma ake tun daga unguwa har akai zuwa babban birnin tarayya. Ci gaba ai zai yi wuya da kuma nisa da al’umma muddin dai har ya zuwa wannan lokaci da ake ciki, akwai miji mai cutar matarsa, haka ita ma matar da akwai mai yiwa mijinta hakan. Xa yana zaluntar mahaifinsa, shi ma mahaifin sai ya kasance wani yana yin haka. Mahukunta su riqa cutar talakawa, suma idan sun samu damar ba bari zasu yi ba, shugaba ya riqa cutar na qasa da shi, hakanan suma idan sun samu damar sai sun yi sama da shi daganan su sako shi qasa su taka. ‘Yan kwangila wasu suna yin kashe mu raba da waxanda suka basu ita kwangilar, ana aikata ayyukan ashsha muraran a fili babu ko tsoron Allah, wani lokaci ma har wanda ya aikata abin zai fito yana bayyanawa mutane ai shi ne ya aikata abu kaza da kaza. Babu ko kunya babu tsoron Allah. Ta yaya za a cigaba bayan akwai wuraren da ake ba Fasiqai muhimmanci, mummunai su kasance ba a ganin mutuncinsu. Wasu ‘ya’ya yanzu su suke neman maye gurbin Iyaye, su Iyayen wasu kuma yanzu sune suka koma makwafin ‘ya’ya. Kamar yadda aka fara shimfixa tabarma da cewar shi cigaba kowa yana da gudunmawar da zai bada, wannan abu haka yake, sai kowa ya san matsayinsa da kuma duk wasu abubuwan da suka kamata ya yi. Amma ba yadda ake kara zube ba sai an canza alqibla, bayan nan a tuba kuma tubar ta kasance ba irin ta mazuru ba, ana iya yin sa’a ta hakan saboda ko da ace shi cigaba yana tafiya da kan shi domin zuwa wuraren da ya dace, to akwai fa wurare masu yawa da ba zai ko mafarkin zuwa ba. Gaskiyar al’amari an yi nisa da cigaba saboda kuwa duk ya gane ashe, bamu ma son junanmu, qwarai kuwa domin an yi nisa da gida qwarai da gaske. Bugu da qari kuma ga rarrabuwar kai wadda ke faruwa tsakanin ko wane jinsi, don an yi nisa da irin tafarkin so da qaunar juna wanda aka gina mu da shi.


4 labarai

A Yau Alhamis 15 Ga Maris, 2018 (26 Ga Jumada Thani, 1439)

Za Mu Hukunta Masu Hannu A Sace Matan Dapchi –Buhari Daga Muhammad Maitela, Damaturu

Shugaban qasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta sa qafar wando xaya, wajen hukunta duk wanda ta samu da sakaci ko hannu a sace xaliban makarantar Dapchi. Shugaban yayi wannan kashedin ne sa’ilin da yake ganawa da iyayen xaliban a a xakin taron gidan gwamnatin jihar Yobe na ‘Wawa Hall’ Damaturu. Ya ce, gwamnatin tarayya ta kafa kwamiti mai wakilai 12domin bin bahasin yadda aka sace yan mata a makarantar Dapchi. Tare da nanata cewa, wannan kwamitin ya qunshi vangarorin na jami’an tsaro haxi da wasu mazauna yankunan. Sannan ya ce” kuma mun qudurta aniyar duk wata hukuma ko mutum ko qungiya da muka samu da sakaci ko hannu a sace xaliban, to zai xanxana kuxar sa, daidai da yadda doka ta tanada”. “Bugu da qari kuma, gwamnatin tarayya tana ci gaba da haxa hannu qungiyoyin qasa da qasa tare da qasashen maqwabta domin ganin waxannanxaliban basu sangarta ba. Ko a cikin yan kwanakin nan na tattauna ingantattun hanyoyin da za a bi domin kuvutar da yan matan. Muna xaukar waxannan hanyoyin ne domin kauce wa jefa rayuwar waxannan yara namu faxawa haxari. “Yau gani a jihar Yobe domin mu nuna damuwa tare da yin jaje ga iyaye da iyalai da gwamnati haxi da baki xayan al’ummar wannan jiha ta Yobe, dangane da al’amarin sace yan mata ya shafa- waxanda wasu maqetata suka yi. “Wanda a ranar 19 ga Faburairun 2018, muka wayi gari da jin wannan mummunan labari mai sosa rai- na sace xalibai xari da

•Wasu daga cikin iyayen xalibai Matan Dapchi da aka sace jiya yayin da Shugaban Qasa Buhari ya ziyarci Makarantar

goma (110) a makarantar sakandire dake Dapchi. Tun daga ranar da wannan al’amari ya afku muke kai gwauro mari wajen lalabo hanyar da za ta kai mu ga yadda zamu ceto yan matan. Bisa ga hakan, na baiwa manyan hafsoshin soja da Safeto Janar na yan-sanda umurnin xaukar mataki tare da bani labarin abinda yake gudana kowacce safiya, a qoqarin da ake dashi wajen sake gano inda yaran suke. Yan matan basu cika kwanaki huxu sace wa ba, ministan yaxa labarai ya ziyarci Dapchi, wanda bayan kwana guda kuma, ministan kula da harkokin cikin gida- har wa yau, tare da ministan yaxa labarai sun sake kai ziyara a garin Dapchi domin bin bahasin lamarin. Shugaba Buhari ya nanata cewa, gwamnatin sa ba za ta numfasa ba muddin bata ga ta yanto baki xayan yan matan Chibok da Dapchi ba, daga hannun waxanda suka yi

garkuwa dasu ba. Waxannan yan matan, duk xaya suke da sauran yan mata, dole su ci gajiyar yanci tamkar sauran kuma su gudanar da rayuwar su da samun cikakkiyar kariya. “Xaliban mu na makarantar Dapchi haxi da na Chibok dukkan su yaran mu ne da yakamata ace sun rayu tare da cimma muradun da suke qunshe a zukatan su, na kasancewa manyan gobe waxanda zasu bayar da gudumawa gina wannana qasar su. Kuma haqqi ne a kan mu wajen kare rayuwar su. Muna aiki tuquru wajen ganin mun dawo da zaman lafiya a kowanne vangaren qasar nan.” “Muna sane dangane da kalaman da wasu vata-garin yan siyasa ke qoqarin amfani dasu domin cimma wasu muradun qashin kai. Kuma a kan wannan nake kiran yan qasa nagari kan suyi watsi da irin waxannan kalamai na rarraba kawunan qasa da xaukar doka a hannu”. Inji

Buhari. Buhari ya ce, mayaqan qungiyar Boko Haram sun tagayyara rayuwar al’ummar jihohin Yobe, Kano, Kaduna, Borno, Niger, wanda hatta babban birnin tarayya, Abuja bai tsira ba. Masallatan mu tare da coci-coci, basu kuvuta daga hare-haren qunar baqin wake ba. Inda jihohin Adamawa da Borno suka fi xanxana kuxar wannan mayaqan. “A yau ya qara bayyana haqiqanin alqiblar da muka dosa wajen yaqar qungiyoyin ta’adda waxanda suka zame wa duniya alaqaqai-al’amari ne wanda ya shafi duniya baki xaya. Kuma ba wai kawai mun rage qarfi da mallakar wani yanki da waxannan masu laifi ke yi ba, yayin da suma jami’an tsaron mu ke faxi tashin yi musu kwab xaya tare da ayyukan su”. Har wala yau kuma, shugaban qasa ya zarce zuwa garin Dapchi tare da ganawa da iyayen xaliban inda kuma

ya nuna matuqar damuwar sa dangane da lamarin. Shugaba Buhari wanda ya sauka a babban filin jirgin saman qasa da qasa a Maiduguri da kimanin qarfe 11:01 na safiyar yau. Wanda kuma daga bisani ya nausa Damaturun jihar Yobe, domin ganawa da iyaye da iyalan xaliban makarantar GGSTC Dapchi 110, waxanda aka sace ran 19 ga watan Faburairun 2018. Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima da hafsan a ma’aikatar tsaro ta qasa, Janar Obayomi Olonishakin, mai baiwa shugaban qasa shawara ta fuskar tsaro, (NSA) Manjojanar Babagana Monguno (mai ritaya), tare da sauran hafsoshin tsaro. Sauran sun haxa da ministan ilimi, Malam Adamu Adamu, da na matasa da wasanni, Solomon Dalong, sai ministan kula da lamurran cikin gida, Abdulrahman Dambazau haxi da ministan yaxa labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed.

Qungiyar BBOG Za Ta Maka Gwamnati A Kotu Kan Sace Matan Dapchi Daga Umar A Hunkuyi

Qungiyar nan mai fafutukar ganin an sako ‘Yan matan da qungiyar ‘yan ta’adda ta Boko Haram ta sace mai suna, “Bring Back Our Girls,” ta baiwa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 7, ko kuma ta xauki matakan shari’a kan tuhumar gwamnatin da yin sakacin da ya yi sanadiyyar sace ‘yan matan makarantan kwana ta Dapchi. Lauyan qungiyar, Femi Falana, ne ya bayyana hakan a wajen wani taron manema

labarai a ranar Talata, lokacin da qungiyar ta yi tattaki zuwa fadar gwamnati, inda take neman gwamnatin da ta ceto waxannan yara ‘yan mata kuma ‘yan qasa da ‘yan ta’addan suka sace. Falana ya ce, qungiyar za ta je Kotu ne ba wai kawai da bukatar a ceto yaran ba, har ma da neman a kama waxanda suke da alhakin sakacin sace yaran. “A bisa la’akari da abin da ke faruwa a wannan sashen na qasarnan, abin mamaki ne a ce an sake sace yara. Ko

so ake a shaida mana cewa, daman ba wani tsaron da aka baiwa yaran a makarantun su da ke yankin na Arewa maso gabashin qasarnan?” qungiyar ke tuhuman hakan. A can baya dai, qungiyar ta fitar da wata sanarwa wacce a cikin ta, ta yi wasu tambayoyi 14 da suka shafi sace ‘Yan matan, inda take neman gwamnatin tarayya da ta yi wani abu a cikin gaggawa. Qungiyar kuma tana zargin gwamnatin ta tarayya da yin sakaci kan sace yaran, inda take tuhumar dalilin da ya

sanya aka janye Sojoji daga garin na Dapchi, wa ya bayar da umurnin hakan, kuma da Sojojin za su bar garin wa suka bar wa tsaron garin? Qungiyar kuma ta yi mamakin yadda ‘yan ta’addan suka ci Karensu ba babbaka, a makarantar ta Dapchi na tsawon awowi ba tare da hukumomin tsaro na gwamnati sun taka masu burki ba, har ma qungiyar ke tambayar, ko dai akwai wani haxin baki ne a tsakanin Sojojin da kuma waxanda suka sace yaran. “Yanzun kuma ce mana ake

yi wai an kafa wani kwamiti, na dai su waxannan mutanan da ake zargi, kila dai so ake a rufe wani abu kawai. Don haka in dai ba wani abu, ya zuwa yanzun ya kamata ne a ce gwamnati ta kori duk mutanan da ake tuhuma, sannan kuma waxannan tambayoyi 14 duk na gaskiya ne. musamman, wane ne ya bayar da umurnin janye Sojojin? Wa kuma aka baiwa tsaron garin bayan janye Sojojin, in har ba amsar waxannan tambayoyin, to kamata ya yi a tuhumi mutanan.


labarai 5

A Yau Alhamis 15 Ga Maris, 2018 (26 Ga Jumada Thani, 1439)

Hukumar NIS Ta Samar Da Naira Biliyan 38 Ga Tattalin Arziqin Qasar Nan

An yi Watsi Da Katin Zave 62,066 A Ofishin INEC Ta Jihar Katsina

Daga Bello Hamza, Abuja

Daga Bello Hamza

Hukumar NIS ta bayar da gudummawar Naira Biliyan 38 ga asusun tattalin arziqin qasar nan daga watan Janairu zuwa Disamban shekarar 2017, shugaban Hukumar Alhaji Muhammad Babandede MFR ne ya bayyana haka a taron shekara-shekara na Hukumar daya gudana a babban ofishisu dake Abuja ranar Laraba 14 ga watan Maris 2018.Taron ya samu hakartar shugabanin Hukumar daga dukkan yankin qasar nan tare da wakilai daga ma’aikatan cikin gida ta tarayya. Shugaban hukumar ya ce, an tattaro Dala Miliyan 30 daga kuxaxen shiga na haraji daga qasashen waje a cikin shekarar 2017, ya ce, qididdiga ya nuna cewa, a cikin kuxaxen da aka samu a cikin gida an samu Naira 14,397,911,569.00 daga bayar da “Passport” ga ‘yanqasa da Naira 72,167,440,00 da ya shigo ta hanyar bayar da katin zirga-zirga na ECOWAS/AA da Naira 1,941,867,172.00 da aka samu ta tattance adireshin masu qarvar Paspo (Address Verification fees) an kuma samu Naira 186,069,700.00 a kuxaxen da aka qarva na tattance bayanan da mai neman paspo ya bayar abin da ake kira “Non Refundable Admin Feee” sai kuma Naira 20,316,989,000.00 daya fito daga harajin da hukumar ta karva na “CERPAC” da kuma Naira 1,617,146,137.96 da aka samu ta bayar da “e-PASS”. Shugaban hukumar NIS ya kuma ce, a cikin shekarar da ta gabata hukumar ta yi qoqarin gamsar da dukkan abokan hurxanta na cikin gida dana qasashen waje ta hanyar biyan su dukkanin haqoqinsu, waxanda kanfanoni sun haxa da kanfanin Iris Samart Technologies da Networks Solution Ltd da National

Fiye da katin zave 62,066 ne a ka tabbatar da ba a karva ba a ofishin hukumar zave ta jihar Katsina saboda rasuwa ko canjin wurin aiki daya faru da masu katin. Bayanin haka ya fito ne daga bakin shugaban hukumar zave na jihar Alhaji Jubril Ibrahim Zarewa, a lokacin da yake tattaunawa da ‘yan jarida jiya, ya ce, mutum 2,555 sun karvi katin su na dindindin a ragistan masu kaxa kuri’a da aka fara tun a watan Afrilu na shekarar da ta gabata. Ya ce, bincike ya nuna cewa, mafi yawan katin zaven da ba a karva ba na ‘yan makaranta ne da ke karatu a jihar Katsina kuma sun riga sun kammala karatunsu sun koma garuruwansu da kuma na wasu ma’aikata da aka yi musu canjin wurin aiki zuwa

•Wurin binciken baqi na Hukumar Kula Da Shige da Fice da aka inganta a babban filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas

e-Goevernment da kuma Greater Washinhton da Contec (CERPAV/ePASS) da IPTELCOM sai kanfanin NSPMC waxanda sune ke sarrafa wa Hukumar takardu da paspos da ake ba ‘yan qasa. Alhaji Muhammad Babande ya hori jami’an hukumar dasu qara qaimi wajen gudanar da aiyukansu musamman ta la’akari da tsarin da Shugaba Muhammadu Buhari ya qirqiro na ma’aikatu su fito da hanyoyin sauwaqa wa ‘yan Nijeriya masu hurxa dasu sauqi a yayin da suke buqatar wani abu a ma’aikatunsu, tsarin da ake kira “Ease of Doing Business Reforms in Nigeria”, ya kuma nuna farin cikinsa ga qoqarin jami’an rundunar inda suka yi zarra a tsakanin hukumomin gwamnati wajen bin wannna tsarin sau da qafa, abin da ya kai su ga lashe kofin da ofishin shugaban qasa ya a tsakanin ma’aikatun gwamnati. Ya

kuma hori manya da qananan jami’an rundunar dasu guje cin hanci da rasha wa a yayin gudanar da aiyukansu su kuma kasance a cikin cikakken “uniform” a ko da yaushe (Service Dress Code). Daga nan shugaban Hukumar NIS xin ya ce, zasu ba hukumar zave ta qasa INEC cikakken haxin kai da goyon baya a shirye-shiryen da ta ke yi na zaven shekarar 2019 “Zamu tura jami’an mu aikin tabbatar da shirye shiryen da ake yi na zave, yana tafiya yadda aka tsara da kuma tattabar da baqi ‘yan qasashen waje basu shigo qasar nan domin gudanar da zave ba” inji shi. Daga qarshe ya yaba wa shugabanin hukumar na shiyyar Kadana da Binuwai da kuma Adamawa saboda qwazon su wajen gudanar da aiki, ya kuma buqaci sauran shuwagabannin rundunar na jihohi su yi koyi dasu.

Jigawa Za Ta Fara Safarar Zovo Zuwa Qasar Mexico Daga Munkaila Abdullah, Dutse

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce, ta shirye tsaf domin fara safarar zovon da al’ummar jihar suke nomawa zuwa qasar Mexico. Gwamnan jihar ta Jigawa wadda ya sami wakilcin mataimakinsa Barista Ibrahim Hassan Hadeja ne ya bayyana haka a lokacin da ganawa da manema labarai jiya a ofishinsa. Ya ce wannan yunquri ya biyo bayan amincewar da wasu masana suka yi kan

cewa Zovon da manoman Jigawa ke nomawa na sahun gaba cikin kyawawan kuma ingantaccen zovon da ake buqata. ‎Mataimakin gwamnan ya qara da cewa, tuni dai wasu qasashe ciki harda qasar Mexico suka nuna sha’awarsu na siyan wannan zovo yadda suka amince da tallafawa manoman da ingantaccen iri da taki domin bunqasa noman na Zovo a faxin jihar. Haka kuma ya yi kira da manoman jihar dasu garzaya domin yin rijista tareda

gujewa yin algus domin cin moriyarsu da bunqasa tattalin arziqin jihar baki xaya. Shi ma da yake nasa jawabin a wurin, mataimakin daraktan hukumar tantance ingancin amfanin gona ta ma’aikatar gona na qasa yace zasu buxe rumbuna na musamman a yankunan Dutse,Taura da Maigatari. Ya ce, hukumar tasu zasu sayi zovon daga hannun manoma kuxi hannu tareda ingantashi domin fitar da duk wani qwaro kafin fitar da shi zuwa qasashen waje.

wasu jihohi da waxanda suka canza wurin zama tun bayan ragistan zaven da aka yi a shekarar 2011. “Koda mutum xaya ne bai karvi katin zavensa sa abin zai dame mu, domin ba zai samu daman sauke haqqinsa na xan qasa ba, ba ma son kowa ya kasa sauke nauyin da ke kansa na jefa kuri’a” in ji Zarewa. Zarewa ya kuma qara da cewa, ya zuwa yanzu an yi wa mutum 167,112 tun da aka fara aikin ragistan masu kuri’a a watan Afrilu na shekarar 2017, “Rabin waxann mutane sun yi ragistan ne a cikin mako 6 da aka fara aikin ragistan masu kaxa kuri’a a jihar. Ya ce , wannan nasarar ta samu ne sakamakon jajircewar jami’an hukumar da kuma shiga lungu-lungu da suke yi domin zaqulo waxanda suka cancanci a yi musu ragista.

Kotu Ta Umurci Majalisar Wakilai Ta Dakatar Da Bincike Game Da Taqaddamar Hijabin Amasa Firdausi Daga Bello Hamza

Shugaban kwamitin majalisar wakilai a kan harkokin shari’a Hon. Abdulrazak Atunwa ya ce, kwamitin haxin gwiwa da ke binciken taqaddamar da ta taso a kan rashin amincewa da kamala karatun Malama Amasa Firdausi daga makaranra qwarewa a kan Shari’a saboda zargin da hukumar makarantar tayi mata na karya dokan makaratar wajen hijabin da ta sanya ranar bikin kammala karatunsu zai dakata daga ci gaba da binciken daya ke yi saboda umurnin kotu da suka samu na su dakata daga ci gaba da binciken. Atunwa ya ce, an xage zaman binciken ne har karo biyu saboda buqatar haka da qungiyar lauyoyi ta yi amma a wannan karon kotun tarayya ce ta Abuja ta bayar da umurnin a dakatar da binciken. Ya kuma ba masu ruwa da tsaki hakuri na rashin ci gaba da sauraron ba a sin daga jama’ar da suka yi cincurondo domin sauraron yadda za a ci gaba da zaman kwamitin. Atunwa ya kuma gabatar da kwafin odar da ta fito daga Maisharia A I Chikere, na babban kotun tarayya ta yankin Abuja wanda ragistan kotun Ben Mulokwu ya sanya wa hannu, qarar mai lamba FHC/ABJ/CS/110/2018 da

Adeniyi Ojo Esq da wasu mutane 7 suka shigar. Wasu ganayyar qungiyoyin da suka halarci zaman kwamitin sun nuna rashin jin daxinsu na rashin ci gaba da zaman binciken da aka yi. Shugaban qungiyar “Muslim Rights Concern MURIC” Farfesa Ishak Akintola ne ya tattauna da ‘yanjarida in daya nuna xacin ransa a yadda ake ta xage zaman binciken, y a ce, waxanda suka garzaye kotu domin samun umurmin kotu na tsayar da zaman bincike na tsoron sakamakon gaskiyar da zai fito ne daga binciken da za a gudanar. Ya ce, “Dole a qaddamar Amasa Firduasi a matsayin cikakkiyar lauyar Nijeriya kamar yadda aka yi wa sauran takwarorinta na wannan shekarar, Amasa jaruma ce muna kuma bata goyon baya xari bisa xari duk da matsalolin da zaman kwamitin binciken ke fuskanta” Sun kuma buqaci kwamitin ta yi watsi da batun sauraron ba’asin a bainar jama’a, su ci gaba da aiki a kan takardun qorafi 87 da aka turo musu wajen rubuta rahoton su. Gamayyar qungiyoyin sun haxa da “Muslim Rights Concern (MURIC)” da “Association of Muslims Legal Practitioners (AMLP)” da kuma “Coalition of Muslim Students Society of Nigeria (MSSN)”.


6 labarai

A Yau Alhamis 15 Ga Maris, 2018 (26 Ga Jumada Thani, 1439)

Majalisa Za Ta Binciki Biliyan 10 Da Aka Fitar Daga NHIS Ba Bisa Qa’ida Ba

Daga Umar A Hunkuyi

Majalisar Wakilai a ranar Alhamis ta bayyana shawarar da ta yanke na bincikar kuxin da ake zargin an fitar da su waxanda yawan su ya kai jimlar bilyan 10 daga kuxaxen hukumar Inshoran lafiya ta qasa, (NHIS), kuxaxen an ce an ajiye su ne a cikin asusun bai-xaya na gwamnatin tarayya a babban Bankin qasa. A lokacin da Majalisar ke amsar bukatan hakan wanda Shugaban kwamitin Majalisar kan harkokin da suka shafi lafiya, Mista Chike Okafor, ya bayar a wajen zaman Majalisar wanda Shugaban Majalisar Yakubu Dogara, ya jagoranta, Majalisar ta bukaci samun bayanai kan kuxaxen daga, Ministan Kuxi, Kemi Adeosun, Gwamnan babban Bankin na qasa, Mista Godwin Emefiele, da kuma babban Akanta Janar na qasarnan, Ahmed Idris. Majalisar ta sanya kwamitin ta a kan kiwon lafiya da kuma almundahana da ya binciki maganan, ya kuma kawo mata sakamakon abin da ya gano a cikin sati huxu. Da yake jagorantar tattaunawa a kan maganan, Okafor, ya yi zargin cewa, a lokacin da kwamitin na

•Babban Sakataren NHIS, Usman Yusuf

shi ya ziyarci ofishin hukumar ta NHIS, kwanan nan, ya gano wasu kuxaxe masu alamar tuhuma, bilyan biyarbiyar sau biyu, waxanda aka cirata daga asusun hukumar da ke babban Bankin qasa a ranar 28 ga watan Disamba na shekarar 2016, da kuma ranar 11 ga watan Janairu na wannan shekarar ta 2018. A daidai lokacin da aka dakatar da Shugaban Hukumar ta NHIS, Farfesa Usman Yusuf, daga Shugabancin hukumar. Okafor, ya yi zargin an ciri kuxaxen ne ba tare da yarjewar

Yusuf, ko wani jami’in hukumar ba, inda ya yi zargin, Ministar kuxin, Adeosun, ce da kanta ta bayar da umurnin ciran kuxaxen, ta hanyar da ta savawa doka. Inda ya ce, matuqar ba a takawa irin wannan lamarin burki ba, to a ma daina maganan wani abu wai shi yaqi da cin hanci da rashawa, wanda wannan gwamnatin ke tutiyan yi. Maganan dai ta janyo hankulan ‘yan majalisan sosai, inda nan take, Edward Pwajok, (PDP Flatau) ya bukaci da majalisar ta kira Adeosun, da

ta zo ta yi bayanin dalilin da ya sanya ta bayar da umurnin ciratar kuxin. Shi ma, Oghene Egoh, (PDP Legas) cewa ya yi, ya zama tilas ga Majalisar da ta kare muradun ‘yan Nijeriya, ya qara da cewa, tilas ne a miqawa hukumar EFCC, wannan maganan domin ta hukunta masu laifi da gaggawa. Mohammed Sani Abdu, (APC Bauci), ya nu na kaxuwarsa ne da kuma mamakin sa kan hanyar da aka bi wajen fitar da irin waxannan maqudan kuxaxe,

inda ya ce, wannan ya nu na akwai bukatar da a binciki shi kan shi asusun na baixaya. Sai dai, Abdurazak Namdas (APC Adamawa) da Daniel Ofongo (PDP Bayelsa), sun qarfafa bukatar da a ji ta bakin Minista Adeosun ne tukunna, kan dalilinta na zare kuxaxen da aka keve su da nufin samarwa da ‘yan Nijeriya ingantattan lafiya. Hakanan kuma dai a jiyan, Majalisar ta Wakilai, ta sake dawo da Abdulmumini Jibrin, wanda ta dakatar saboda zargin da ya yi mata na yin cuwa-cuwa a kasafin kuxin shekarar 2016. Shugaban Majalisar, ya karanta takardan ban haqurin da Abdulmumini Jibrin, xin ya aiko mata, inda kuma ya bayyana cewa, Xan Majalisar ya cika dukkanin sharuxxan da Majalisar ta gindaya masa, kafin ta amince da dawowa da shi cikinta. Daganan ne sai Shugaban Majalisar ya bayyana cewa, Abdulmumini xin zai iya ci gaba da wakilcin sa a cikin Majalisar bayan ya cika sauran sharuxxan. Shugaban masu ladabtarwa na Majalisar, Ado Doguwa, ya yaba da wannan shawarar da Majalisar ta zartar na maido da Abdulmumini Jibrin xin.

Mai Talla Shi Ke Da Riba:

LEADERSHIP A YAU Ta Shirya Tsaf! Kamar yadda kowa ya sani ne, wannan jarida mai albarka, LEADERSHIP A YAU ta kafa tarihi wajen zama jaridar Hausa da ta fara fitowa a kullum. Wannan fara fitowa a kullum yana da alfanu masu yawan gaske, gare mu Kamfanin LEADERSHIP da ku masu karatu, musamman masu sana’o’i manya da qanana. Wannan ne ya sa muke farin cikin shaida wa masu karatunmu cewa mun shirya tsaf domin tallafa wa kasuwancinku, ta hanyar tallata maku shi zuwa inda ba ku zata ba. Domin a halin yanzu mu kanmu da muke buga wannan jarida ba za mu iya bayyana iya inda ta ke shiga ba. Muna da tsare-tasare da dama don talla ku da hajojinku, inda muka fitar da tsarin ‘IYA KUXINKA IYA SHAGALINKA.’ Wato akwai cikakken shafi, akwai rabi, akwai kwata, akwai kuma daidai iyaka abin da mutum ke so a sanya masa. Wanda a wannan shafin muna so masu sana’o’i, musamman manyan dillalai su tallata hajojinsu, su qananan ’yan kasuwa akwai

nasu tsarin. A wani tsarin ma da muke da shi, akwai yanayin da mutum zai tallata hajarsa, sannan ya tallata kansa, inda za a sanya hoton shagonsa, hotonsa da kuma taqaitaccen tarihinsa, kuma wannan duk a kuxi kaxan. Maza ku kasance cikin kashi na farko na masu cin moriyar wannan shiri. Ina ’yan Canji, dillalan yaduka, masu kayan masarufi, mayan da qananan ’yan tireda, dillalan magunguna, masu kamfoni da masana’antu, dillalan hatsi, dillalan mota, masu sayar finafinai da dai sauran masu sana’o’i, ga dama ta samu. A tuntuvemu a lambarmu ta 08148507210, 07036666850, 08039216372, 07037934034, 08032875238 da 08038011382: email leadershipayau@gmail.com. Ko kuma a tuntuvi wakilanmu na jihohi don qarin bayani.


A Yau Alhamis 15 Ga Maris, 2018 (26 Ga Jumadal Thani, 1439)

Burinmu Shi Ne Mu Sauqaqa Muku

Ba a chaj in kuxin on ka cire d i j a h c a a B saqonnin watin waya kuxi daga ak na wasu banku

Da zaran an buxe asusu da mu, za a morewa rashin chaji idan mutum ya cire kuxi a akwatin wasu bankuna, haka kuma ba za a riqa cire kuxin saqonnin waya ba.

Domin cimma nasara a hada-hadar banki, ka yi mu’amala da bankin Sun Trust a Yau Ziyarci: www.suntrustng.com

talla 7


8 talla

A Yau Alhamis 15 Ga Maris, 2018 (26 Ga Jumadal Thani, 1439)


A Yau Alhamis 15 Ga Maris, 2018 (26 Ga Jumadal Thani, 1439)

talla 9

Gaba dai! Gaba dai “Super Eagles”

Bankin Zenith na taya ‘yan qwallon Nijeriya “Super Eagles”, murna sakamakon nasarar da suka samu ta kai wa gasar Cin Kofin Duniya wanda za a gudanar a qasar Rasha.


10 labarai

A Yau

Alhamis 15 Ga Maris, 2018 (26 Ga Jumada Thani, 1439)

•Mataimakin Shugaban Qasa, Farfesa Yemi Osinbajo tare da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha jiya yayin da Mataimakin Shugaban Qasar ya jagorancin zaman majalisar zartaswa a fadar shugaban qasa

Qungiyar Wayar Da Kan Al’umma Ta Fara Zagayen Qananan Hukumomi 23 Dake Kaduna Daga Ibrahim Ibrahim, kaduna

Qungiyar faxakar da Al’umma akan ayyukan ci gaban Gwamnatin Jihar kaduna, wanda a turance ake kira da kaduna state Awareness Network, ta fara wani rangadin zagayen Qananan Hukumomi 23 dake faxin Jihar kaduna, domin faxakar da Al’umma irin ximbin ayyukan ci gaba da Gwamnatin Jihar kaduna, qarqashin jagorancin Malam Nasiru Ahmed El-rufai, ta samarwa Al’ummar Jihar kaduna. A yayin jawabinsa wajen tarbar ‘ya’yan qungiyar da suka kai masa ziyar ban girma a ofishinsa, Shugaban Qaramar hukumar kudan, Honarabul Shehu Muhammad, ya bayyana farin cikinsa da wannan ziyarar gani da ido, da wannan qungiya ta kawo Qaramar hukumar kudan. Honarabul Shehu Muhammad, ya kuma qara da bayyana cewa, kafa wannan qungiya yazo a dai dai lokacin da Al’ummar Jihar kaduna ke ci gaba da kurvar irin romon ci gaban ayyukan alheri da Gwamnan El-Rufai ya kawo ma Al’ummar Qaramar hukumar kudan, da jama’ar Jihar kaduna baki xaya. Shima a nasa jawabin a yayin da yake tarvar ya’yan qungiyar a Qaramar hukumar Maqarfi, Shugaban Qaramar hukumar Maqarfi, Honarabul Garba Sani Aliyu, ya jinjina

ma ya’yan wannan qungiya, sannan ya umurce su da cewa, ka da su gajiya wajen shiga lunguna da saquna, domin faxakar da Al’umma akan irin ximbin ayyukan ci gaba da Gwamnatin Jihar kaduna qarqashin jagorancin Malam Nasiru Ahmed Elrufai, ke aiwatarwa a cikin birane da qauyuka. A yayin da yake bayyana maqasudin qirqiro da wannan qungiya, Shugaban qungiyar na Jihar kaduna, Alhaji Rabiu Baddiko, ya bayyana cewa,

sun yanke qirqiro da wannan qungiya ne domin shiga lungu da saqo domin zaqulo irin ximbin ayyukan ci gaba da gwamnatin El-rufai ta samar, sannan su fito domin su bayyana ma Al’umma. Alhaji Rabiu Baddiko ya qara da bayyana cewa, akwai ximbin ayyukan ci gaba da wannan gwamnati ta samar, amma abin mamaki da takaici shi ne, har yanzu wasu na nan a gefe, babu abin da suka sanya a gaba sai sukar wannan gwamnati ta

hanyar yin qarya da vatanci, amma dai dai da rana xaya basu tava fitowa fili sun nuna jin daxi da godiyarsu a bisa irin ayyukan da ake yi masu ba. Daga nan sai Shugaban qungiyar na kaduna state awareness network, ya roqi Al’ummar Jihar kaduna, da su ci gaba da baiwa wannan gwamnati goyon baya, domin ganin ta sami nasarar qasara ayyukan ci gaba da ta xauko wajen yi ma Al’ummar Jihar kaduna.

A yayin ziyarar da qungiyar ta kai Qaramar hukumar kudan da Maqarfi, qungiyar ta duba wasu muhimman ayyukan da Gwamnatin Jihar kaduna ta gudanar, wanda suka haxa da, ginawa da gyara makarantu firamari da na sakandire, da kuma duba wasu daga cikin asibitoci da aka xaga darajarsu zuwa manyan asibitoci domin sawwaqe ma Al’umma, ba sai sun shigo birni wajen ganin qwararren likitoci ba.

Badaqalar Kasafin Kuxi: Majalisar Wakilai Ta Xage Dakatarwar Da Ta Yi Wa Jibril Daga Aabdullahi Usman, Abuja

Majalisar wakilai ta tarayya ta xaje dakatarwar da ta yi wa tsohon shugaban kwamitin kasafin kuxo na majalisar wakilai, Xan majalisa Abdulmumin Jibril. Jibril wanda aka dakatar har na tsawon kwanakin aiki na majalisar 180, a watan Satumbar 2016, Jibril, Jibril dai ya kwashe sama da shekara xaya da wata huxu ba tare da ya shiga majalisar wakilai xin ba, saboda wannan dakatarwa da aka yi masa, sai a ranar talata bayan an xage wannan dakatarwa. Xan majalisar dai, wanda ya fito daga jihar Kano ya

nemi gafarar takwarorinsa na majalisar kan zargin da ya yi a wancan lokaci na sama na naira biliyan40 da ya ce an saqasu a kasafin kuxi. Wanda hakan ya jawo majalisar ta dakatar da shi. Shugaban majalisar, Mista Yakubu Dogara ne ya xaga wata wasika a zaman majalisar, da ya bayyana da cewa Abdulmumin Jibril ne ya aiko da saqon baiwa majalisar haquri kan abin da ya yi. Dogara dai ya bayyana cewa ba da haqurin da Jibril ya yi na daga cikin abin da majalisar ta nema kafin dawowa da shi cikin majalisar. “Wannan takarda ta ba da haquri da Jibril ya yi, ya nuna cewa ya cika

qa’idojin da aka shimfixa masa. Saboda haka zai iya dawowa zaman majalisar, face kuma ya sake aikata wani abin na daban. A shekarar 2016 ne Dogara ya kori Jirbil daga shugabancin kwamitin majalisar wakilai na kasafin kuxi, wanda ake jin ba zai rasa nasaba da badaqalar kasafin kuxi ba. Wasu daga cikin waxanda Jibril ya zarga da wannan aiki sun haxa da Mataimakin shugaban majalisar, Yusuf Lasun, mai tsawatarwa, Alhasana Ado Duguwa da kuma shugaban marasa rinjaye Mista Leo Ogar. Jibril kuma ya yi zargin cewa wasu ‘yan gata a

majalisar an sanya masu kuxaxe a cikin kasafin kuxin. Sannan ya yi kira ga shugabannin majalisar da su sauka daga muqamansu, sannan EFCC ta hukunta su kan almundahana xin da suka aikata. Daga baya majalisar ta bincike Abdulmumin Jibril, sannan ta fitar da cewa ya kunyata majalisar kan wannan almundahanar da ya yi zargi. Daga baya kuma majalisar gaba xaya ta amince da dakatar da shi na tsawon kwanaki 180 na zaman majalisar. Ofishin xan majlisar dai ya bayyan cewa xan majalisar zai dawo aiki jiya laraba.


labarai 11

A Yau Alhamis 15 Ga Maris, 2018 (26 Ga Jumada Thani, 1439)

Qungiyar NATA Ta Yi Kira Ga Ganduje Ya Cika Musu Alqawarin Samar Da Sansanin Gyara Na Zamani Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Quniyar makanikan motoci na qasa. “Nigerian Automobile Technician Association”Reshen jihar Kano ta yi tuni ga Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje kan alqawarinda yayi musu na sama musu cibiyoyin sansanin gyaran motoci a jihar. Shugaban qungiyar na”NATA”Reshen Jihar Kano. Injiniya Kwamared Idris Muhammad Kanwa ya bayyana hakan. Ya ce matsallin quniyar bai wuce daga Gwamnati ba, amma sun godewa Gwamna Ganduje wanda ya nuna kishin sana’arsu domin ya xauki yara 72 a kano an horar dasu a Kaduna sannan kuma a xauki 150 waxanda suka qunshi mata 50 da za a yaye nan gaba ana koya musu gyaran motoci. Injiniya Kwamared Idris Muhammad Kanwa ya ce babban abin da suke nema a Kano a basu cibiyoyi na sansanin gyaran motoci na zamani, akwai alqawari da Gwamna a gidansa na Miyangu ya ce zai samar musu sansanin gyara na zamani kamar a qasar Dubai, zai kuma ba su muqamin mai bada shawara, yanzu ya basu mai bada shawara ga Gwamna akan makanikai a wannan jiha suna alfahari da hakan. Ya qara da cewa illa suna buqatar tallafin kuxi dan gudanarda ayyuka. Sannan kuma akwai wani abu da jahohi

ke samu na aikace-aikacen gyaran motocin Gwamnati, amma anan kano sai dai akai wani waje ba’a basu a matsayin qungiya duk kuwa da cewa a jiha suke aiki da biyan haraji a Gwamnati amma ayyuka basa zuwa kai tsaye ga qungiya wannan yana rage musu karsashi. Injiniya Kwamared Idris Kanwa ya ce ga kuma irin gudummuwa da Gwamnati take baiwa qungiyoyi dasu basa gani. Ya kaa misali da jihar Imo inda Gwamnatin jiha ta baiwa makanikai sansani ta kuma haxa musu da N100, 000, 000. Dan yin gyare-gyare ya haxa musu da motocin Bas guda Huxu qirar homa, duk sanda taro ya kama na qasa kona shiyyarsu sai su xauko xaya su tafi a ciki, amma su a jihar Kano sun gode Allah an basu motar a kori kura”Hilux”ita suketa lallavawa. Shugaban na “NATA”Reshen Kano ya ce su anan jihar basu da wata ma’aikata da suke iya zuwa kai tsaye da buqatunsu na qungiyar Makanikai dan haka suna neman gudummuwa ta haxin kai tsaninsu da Gwamnatin Kano aikaceaikace su riqa shigowa ta wajen quniyar kai tsaye. Daya juya kan nasarar da reshen qungiyar na jihar Kano na samar da zavavven shugabancin qungiyar na qasa. Injiniya Idris Kanwa ya nuna godiyarsa ga Allah kan wannan nasara wanda hakan

•Injiniya Kwamared Idris Muhammad Kanwa.

ya samune sakamokon gaskiya da riqon amanar shugaban qungiyar na qasa Injiniya Magaji wanda a baya shine shugaban”NATA”Na Kano ya kuma zama Mataimakin shugabanta na shiyyar arewa maso yamma kafin su zaveshi ya zama shugaban qungiyar na

qasa da yake yanzu. Ya ce suna fata ya cigaba da gaskiya da riqon amana kamar yanda suka sanshi akai dan cigaba da bunqasa qungiyar. Injiniya kwamared Idris Muhammad Kanwa ya ce qungiyar tanada reshe a

dukkan qananan hukumomi 44 na Kano da kuma cibiyoyi 156 sunada makanikai samada 32, 500 suna samarda aiki a birni da karkara wanda a kowane shekara suna samarwa da ma’aikata samada 1000 a qarqashin vangarori daban-daban na sana’ar makanikanci da ya haxa da gyaran mota, gyaran wayoyin lantarkinta, penti, tada komaxa, masu gyaran taya da faci”vulcaniser”masu yin rigar kujerar mota , gyaran burki da masu gyaran sitiyari. irin waxannan sune suke koyawa matasa da suke tasowa da sana’a ta dogaro dakai kuma suke kuma cigaba da karatu. Injiniya kwamared Idris Muhammad Kanwa yayi kira ga ‘ya’yan qungiyar su cigaba da bada haxin kai wanda idan babu shi ba’a samun nasara kuma su riqa halartar taron qungiyar duk lokacinda buqatar hakan ta taso. Ya koka da cewa wani lokacin idan aka kira taro sai kaga waxanda zasuzo daga qananan hukumomi basu wuce 40 huxu basu zoba sai anyi wani abu mai muhimmanci su riqa cewa basu da suce basu sani ba, saboda haka zuwa taro da baiwa shugabancin qungiya a kowane mataki yana da muhimmanci dan a raqa fitowa da shawarwari da za a kaiga nasarar cigaban harkar Makanikanci a jihar Kano dan tafiya daidai da zamani.

Yarjejeniyar AfCFTA: Gwamnatin Tarayya Ta Yi Taka Tsantsan –AON Daga Abubakar Abba

Ranar Talatar data gabata ce qungiyar masu jiragen sama na qasa (AON) suka shawarci gwamnatin tarayya da ta yi dubi akan matakin da ta xauka akan yunqurin rattaba hannu akan yarjejeniyar (AfCFTA) ta gudanar da kasuwanci a nahiyar Afrika kyauta. Shugaban qungiyar Kaftin Nogie Meggison ne ya yi kiran a sanarwar da fitar a jihar Legas. An ruwaito cewar yarjejeniyar ta (AfCFTA) an tsara shugabannin qasashen nahiyar Afrika zasu rattabawa yarjejeniyar hannu a taron su da zasu aka tsara zai gudana a Kigali a cikin qasar Rwanda daga ranar 21 zuwa ranar 22 na watan Maris na shekarar 2018. Aikin yana xaya daga ajanda qungiyar nahiyar

qasashen Afrika na 2063 kuma manufar aikin shine don qirqiro da kasuwa xaya tilo ta sayar da kaya da gudanar da ayyuka ta shigar kaya da alumma don gudanar da hada-hadar kasuwanci kyauta. Meggison yace, qungiyar su ta soki yunqurin akan sanya hannu na barin yin zirga-zirgar jirgi zirgi zuwa kasuwar da shugabannin na nahiyar Afrika a garin Addis Ababa cikin qasar Ethiopia a ranar 28 ga watan Janairu. Shugaban yaci gaba da cewa, sanya hannun na (SAATM) anyi shi a cikin gaggawa idan akayi dubi akan matsaloli da dama da har yanzu ba a shawo kansu ba waxanda kuma suka qara zama turniqi akan tattalin arzikin qasar nan. Acewar sa,in ba’a yi hankali ba gwamnatin tarayya zata qara mai-maita kuskuren da ta tabka a baya wajen sanya

hannu yarjejeniyar (AfCFTA) a baya, inda hakan zai iya zomowa Nijeriya koma baya wajen samun shiga cikin kasuwar. Ya yi nuni da cewa, “hakan zai iya janyowa qoqarin gwamnatin tarayya naqasu akan shirye-shiryen ta da ta shinfixa don farfaxo da tattalin arzikin qasa da kuma qoqarin ta wajen tsamo da qasar daga cikin matsain tattalin arzikin qasa.” Meggison ya qara da cewa, dole ne gwamnati tabi a sannu wajen qaddamar da shirin (SAATM) ta kuma dakatar da sanya hannu akan yarjejeniyar ta(AfCFTA) har sai an shawo kan matsalar da take a kwance don ta amfani Nijeriya da kuma ‘yan qasar nan. Acewar sa, maganganun sun haxada, rashin shawo kan qalubale da suka shafi samar da Biza kyauta ga ‘yan kasuwa ‘yan Nijeriya da

yawan haraji da aka karva barkatai da aka xorawa ‘yan Nijeriya masu hada-hadar jiragen sama da kuma nuna rashin adalci wajen gudanar da kasuwanci a tsakanin Nijeriya da sauran qasashen dake cikin nahiyar Afrika. Meggison ya bayyana cewar, “qasashe 23 ne kacal daga cikin qasashe 54 a nahiyar Afrika, waxanda suke qasa da kashi hamsin bisa xari da suka sanya kansu a cikin shirin na (SAATM). Ya bayyana cewar, “waxancan qasashen, har yanzu basu rattaba hannu akan yarjejeniyar ba, inda ya yi nuni da cewar, ba makawa qasashen suna so ne su kare martabar kasuwannin su, inda har sai sunga cewar an samar da kasuwa wadda za’a iya dinga yin gogayya. Meggison yace, “abin tambaya shine, me ya sanya Nijeriya take ta azamar ta rattaba hannu akan

yarjejeniyar ta (AfCFTA) alhali har yanzu bamu xora masana’antun mu ba akan turba mai xorewa ba, musamman don qarawa hada-hadar kasuwancin mu ta cikin gida qarfi yadda zasu gudanar da hada-hadar kasuwancin kafaxa-dakafaxa da takwarorin su na nahiyar Afrika ba? Yace, amsar a taqaice itace, “Nijeriya bata shirya ba wajen ganin an ci gaba da nuna rashin aldalci don gudanar da gasa musamman idan ta qaddamar da shirin ta na(SAATM) ko kuma ta rattaba hannu akan yarjejeniyar ta (AfCFTA). Shugaba Meggison ya yi nuni da cewa, wannan kamar wani koma baya ne domin qaddamar a cikin wannan yanayin da Nijeriya take ciki, zai janyo rasa ayyukan yi musamman ga matasan mu da kuma sayar da alqiblar ‘yayan mu.”


12 labarai

A Yau

Alhamis 15 Ga Maris, 2018 (26 Ga Jumada Thani, 1439)

Gwamnatin Bauchi Za Ta Yi Aiki Da ECOWAS Kan Shirin Inganta Zaman Lafiya Daga Muazu Hardawa, Bauchi

Gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar ya bayyana aniyar gwamnatin jiha don haxa kai tare da yin aiki don magance matsalar rashin zaman lafiya da ake fiskanta a wasu sassa na afirka. Inda ya yaba game da shirin na ECOWAS game da inganta zaman lafiya da magance tsaurin raayi da ake samu tsakanin matasa inda suke jefa wannan nahiya cikin yanayin tashin hankali da yaqe yaqe, don haka yace gwamnati a shirye take wajen kawo qarshen matsalar ta hanyar temaka wa qungiyar Kamar yadda Jihar ta Bauchi ta himmatu wajen kawo qarshen fitinar matasa da aka yi fama da ita a baya. gwamnan ya bayyana hakane a yayin buxe taron tattauna wa da bita kan muhimmancin zaman lafiya da magance matsalar tsaurin raayi da qungiyar ECOWAS ta shirya na kwana biyu aka buxe a chart well hotel Bauchi a jiya laraba. Dokta Isaac Armstrong jamiin tsara taron magance rigingimu a qasashen Afirka ta yamma shine ya jagoranci tawagar ECOWAS a taron Wanda ya samu halartar gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abdullahi

Abubakar, cikin jawabinsa a gaban maharta taron a yayin buxe taron ya bayyana cewa qungiyar ta ECOWAS ta shirya wannan taron a Bauchi don wayar da kan jamaa kan muhimmancin zaman lafiya da yadda za a magance matsalar tsaurin raayi na addini ko qabilanci Wanda ya jefa qasashen afirka da dama cikin matsalar rashin zaman lafiya. Shima kwamishina matasa da wasanni na Jihar Bauchi Alhaji Ibrahim Madaki Sale cikin jawabinsa ya bayyana irin nasarorin da gwamnatin jiha ta samu wajen Samar da zaman lafiya da daidaita xabiu matasa game da rungumar zaman lafiya. Shima sarkin Bauchi dokta Rilwanu Sulaiman Adamu Wanda galadiman Bauchi Alhaji saidu Ibrahim Jahun ya wakilta ya bayyana jin daxi game da kawo wannan taron bita jihar ta Bauchi inda ya yi fatar taron zai taimaka wajen inganta zaman lafiya na wannan nahiyar da kuma yankin afirka ta yamma. Don haka ya ja hankalin mutanen wannan shiyya ta arewa maso gabas su kasance masu qaunar zaman lafiya. Inda ya bayyana cewa sarakuna sun himmatu wajen ganin an kawo qarshen matsalar rashin zaman lafiya da ake fiskanta a wasu sassa

•Farfesa Bilbis na miqawa Gwamna Yari rahotan Gina jami’a jihar Zamfara.

na qasar nan. Shima gwamnan Jihar Bauchi Batista Mohammed Abdullahi Abubakar cikin jawabinsa a yayin buxe taron ya bayyana takaici game da matsalar rashin zaman lafiya na boko haram Wanda ya raba mutane da muhallansu a shiyyar Arewa maso gabas. Ya bayyana cewa hakkin kowane ya taimaka wajen bayyana illar tashin hankali da xaukan matakin magance wannan matsala a qasashen

afirka ta yamma don ganin ba a sake fiskantar matsalar da aka shiga a Sierra Leone da Liberia da wasu qasashen afirka ta yamma ba. Gwamnan Jihar ta Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar ya ja hankalin mahalarta taron da su kasance sun yi aiki da abin da suka koya don ilmantar da jamaa game da tasirin zaman lafiya a rayuwa. Don haka yace dole a tashi tsaye don ganin an kare wannan yanki na

afirka ta yamma daga faxawa mawuyacin halin yaqi irin Wanda qasashen Afghanistan da Somalia suka shiga. Don haka gwamnan ya ce zaman lafiya shine gaba da komai saboda haka ya yaba wa mahalarta taron da qungiyar ta ECOWAS kan wannan maudui kuma ya kamata kowa ya Isar da saqon da ya samu zuwa gaba don ganin an samu ci gaba ta fiskar zaman lafiyar jamaar wannan yanki na afirka ta yamma.

An Yi Taron Qungiyar Hausa A Kwalejin Arabiyya Ta Karau-Karau Daga Balarabe Abdullahi, Zariya

Haxaxxiyar Qungiyar Havaka Harshen Hausa ta makarantar Sakandare tunawa da Shekh Ibrahim Arab ta musamman wadda ke Karau-Karau, amma wani yanki na ta ke Zariya, a jihar Kaduna, ta gudanar taron shekara-shekara tare da karrama wasu fitattun mutane da suke bayar da gudunmuwarsu wajen ciyar da Harshen Hausa gaba. A jawabinsa wajen wannan gagarumin taro, babban malami a kwalejin ilimi ta gwamnatin tarayya da ke Zariya [F. C. E. ZARIA] Malam Habibu wanda aka fi sani da xan qasa, ya nuna matuqar jin daxinsa na yadda malaman da suke koyar da Harshen Hausa a wannan makaranta suka suka sa xalibansu a gaba, ha aka kafa wannan qungiya

da nufin ciyar da Harshen Hausa gaba. Malam Habibu Xan Qasa ya ci gaba da cewar, wannan taro da aka yi, taro ne da ya ce na cikin sahun hanyoyin da suke ciyar da Harshen Hausa gaba, ba a nan Nijeriya ba, a cewarsa a qasa baki xaya. Kan haka, masanin Harshen Hausan ya nunar da cewar, wajibi ne xaliban wannan makaranta ta Karau-Karau su qara tashi tsaye, na ganin sun nazarci Harshen Hausa, domin su ma su sami dammar da za su bayar da gudunmuwarsu, na ganin Harshen Hausa ya ci gaba da samun xaukaka a duniya, fiye da yadda yak e samun xaukaka a halin yanzu. A qarshen jawabinsa, Malam Habibu Xan Qasa ya lashi takobin yin duk abin da ya kamata, na ganin

wannan qungiya ta sami ci gaban da ta ke buqata a ciki da kuma wajen wannan makaranta. A na ta jawabin jagorar wannan qungiya Malama Hudal Islam, ta fara da nuna matuqar gamsuwarta da goyon baya da kuma shawarwarin da Malam Xan Qasa ke bat a a matsayinta na xalibar Hausa da kuma yadda ya ba su shawarwarin da suka zama silar nasarorin da suka samu a wannan qungiya ta Havaka Harshen Hausa a kwalejin tunawa da Shekh Ibrahim Arab da ke Karau-karau. Ta yi kira kuma ga xaukacin xaliban da suke wannan makaranta da su tashi tsaye na ganin an haxa hannu da su na ganin an ciyar da wanna qungiya gaba. A saqonsa wajen taron

shugaban makarantar Malam Maiwada ya yaba wa malaman Hausa da suke wannan makaranta, na yadda suka kafa wannan qungiya da ta sa gaba na ganin ta ciyar da Harshen Hausa da kuma kyawawan al’adun Hausa gaba, ya ce, babu ko shakka zai ci gaba da ba wannan qungiya duk taimako da kuma shawarwarin da suke buqata. Shugaban makarantar wanda Na’ibinsa Malam Isa Babajo ya wakilce shi, ya yi amfani da wannan taro, inda ya yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna da ta duba matsalolin qamfar azuzuwa da makarantar ke fuskanta, wanda a dalilin haka ne yasa mahukumtan makarantar suka raba xaliban makarantar biyu, da ma su zuwa da safe da kuma ma su zuwa da rana.

Sauran waxanda suka yi jawabi a wajen taron sun haxa da wasu ‘yan jarida da suka fito daga kafar watsa labarai ta ALHERI RADIO da ke zariya da suka haxa da Yahay Rayyan Jingle da Umar Mahmud Tangas da Halima Aliyu Balarabe Kauru da kuma Maryam Sa’id Jibril, waxanda dukkansu suka nishaxar da waxanda suka halarci wajen wannan taro da ya gudana a harabar wannan makaranta. A qarshen taron jagoran taron Malam Yusuf Nadabo, ya jagoranci miqa kyautttuka ga wasu da suke bayar da gudunmuwarsu na ganin an ciyar da Harshen Hausa gaba, cikinsu a kwai Malam Habibu Xan Qasa da xaukacin ma’aikata Alheri Rediyo da ke Zariya da aka bayyana sunayensu a baya.


labarai 13

A Yau Alhamis 15 Ga Maris, 2018 (26 Ga Jumada Thani, 1439)

WAEC Ta Riqe Sakamakon Jarabawar Mutum 1,021 Daga Umar A Hunkuyi

Hukumar shirya jarabawar kammala manyan makarantun Sakandare ta Yammacin Afrika, (WAEC) ta bayar da sanarwar sakamakon jarabawar da ta shirya a tsakanin watannin Janairu da na Fabrairu 2018, a ranar Talata. Shugaban hukumar a wannan qasar, Olu Adenipekun, shi ne ya bayyana sakamakon a Legas, inda ya ce, hukumar ta riqe sakamakon jarabawar na mutane 1,021. An dai amince da shirya qarin yin jarabawar ce ga xaliban na bayan fage a wannan qasa tamu da ma sauran qasashe biyar da ke yankin, a taro na 65 da hukumar ta yi a watan Maris na shekarar 2017, wanda hakan ya mayar da jarabawar da hukumar ke shirya wa suka zama uku a duk shekara. A cewar Olu Adenipekun, hukumar ta riqe sakamakon jarabawar mutanan ne sabili da sun aikata laifukan maguxi daban-daban a lokacin jarabawar. Ya ce, ana bincikar laifukan na su, da an gama binkcika kuma za a hannata matsalolin na su ga kwamiti na

•Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu

musamman domin ya duba ya yi hukunci. Bayan nan ne za a sanar da mutanan da abin ya shafa hukuncin da kwamitin ya yi a kansu. A cewar sa, mutane 11,721, ne suka yi rajistan xaukar jarabawar, amma mutane 11,307, ne suka zauna xaukan jarabawar. Da yake bayyana sakamakon jarabawar dalla-

dalla, Shugaban ya ce, mutane 8,113 ne suka sami cinye jarabawar da makin Kiredit zuwa sama a darussa biyu. Sannan ya ce, mutane 6,375 sun ci jarabawar da makin Kiredit zuwa sama a darussa uku, sa’ilin da mutane 4,762 suka sami cin jarabawar da makin Kiredit zuwa sama a darussa huxu. Olu Adenipekun, ya

ce, mutane 3,263 sun ci jarabawar da makin Kiredit zuwa sama a darussa biyar, inda kuma mutane 2,010 suka ci jarabawar da makin Kiredit zuwa sama a darussa shida. “Jimillan mutane 1,937, kimanin kashi 17.13, sun sami cin jarabawar da miqidarin Kiredit a darussa biyar zuwa sama, da suka haxa da darussan Turanci da

Gwamnatin Tarayya Ta Agazawa Manoman Shinkafa 330,000 Da Naira Biliyan 43.92 Daga Umar A Hunkuyi

Gwamnatin tarayya ta saki tallafin kuxi kimanin Naira bilyan 43.92 domin rabawa manoma shinkafa 330,000, a qoqarin da gwamnatin ke yi na qara yawan shinkafar da ake nomawa a qasarnan da miqidarin Tan milyan biyu a shekarar 2018. Ministan harkokin mata, Hajiya Aisha Alhassan, ce ta bayyana hakan a birnin New York, wajen wani taro na 62 a kan inganta matsayin Mata a duniya. Taken taron na bana shi ne, “Cimma manufa kan bunqasa tattalin arziki: Ta fuskacin samarwa mata zaman lafiya da tsaro, a matsayin tubalin ci gaban ‘yancin matan karkara a Nijeriya.” Ministan ta ce, “Wannan tsarin na havaka aikin noma, an shirya shi ne domin qara xaukaka matsayin noman, wajen magance matsalar yunwa a qasa, samar da isasshen abinci da kula da lafiyar abincin, da kuma samar da ayyukan yi, da yalwatan arziki ga milyoyin manoman. “Tsarin nan da gwamnatin tarayya ta fito da shi wanda

kuma ake aiki da shi yanzun wanda a turance ake kira da, “Anchor Borrowers Programme,” a yanzun haka ya saki kuxi kimanin dala milyan 122 ga qungiyoyin manoman 13. “An kuma yi hakan ne domin manoman shinkafar 330.000, su samar da qarin Tan milyan biyu na shinkafar da za a noma a wannan shekarar ta 2018, waxanda mafiya yawan su matan karkara ne.” Ta kuma ce, gwamnatin Shugaba Buhari, da gaske take yi a qoqarinta na cimma manufar yakice talauci da kuma qarfafa matan karkara wajen cimma wannan manufa na ta ya zuwa shekarar 2030. A cewar ta, gwamnatin ta Nijeriya, ta xauki manyan matakan qarfafa waxannan manufofi na ta, da kuma shirya matakan daidaitawa a tsakanin jinsin maza da na mata, ta hanyar qarfafa wa matan. Ta ce, wasu tsare-tsaren da yawa an yi su ne ta yanda za su fitar da qimar matan da yawan su ya kai milyan 83.3 na yawan al’ummar wannan qasa ta mu. A kan ilimin yara matan

kuwa, cewa ta yi, gwamnati ta na yin hovvasa wajen ganin ta baiwa tsarin ilimin bai-xaya na, “universal basic education programme,” mahimmanci, wanda an shirya shi ne musamman domin havaka ilimin yara mata musamman mazauna karkara. Ta kuma ce, qaddamar da shirin nan na samawa matasa aiki mai suna, “N-Power job Creation and Youth Employment Programme,” wanda aka shirya shi musamman ga matasan maza da mata, ya yi nasarar samarwa da matasan da suka kammala karatun su dubu, 500,000, da kuma ma waxanda ba su kammala karatun na su ba dubu, 100,000, ayyukan yi. “Kan hakan, wannan shiri na N-Power, ya yi nasarar tura matasan da suka kammala karatun su dubu 200,000 yankunan karkara na qasarnan domin su bayar da ta su gudummawar, tare da qarin wasu da aka keve su dubu 300,000,” in ji ta. Uwargida Alhassan, ta ce, an kuma samar da qarin wasu dubu 10,000, ma su sana’ar hannu, waxanda aka horar da su kan ayyukan gine-gine da

gyaran mota, ta hanyar haxin gwiwa da qungiyar masu gine-gine ta qasa, da kuma Hukumar masu haxa motoci. Ta kuma ce, gwamnati tana tafiyar da shirin bayar da agaji na Naira 5000 ga matalauta a duk wata, in da ta ce, ya zuwa watan Disamba na shekarar 2017, sama da matalauta dubu, 622,649, ne suka ci gajiyar shirin, gami da wasu 439,859, da su ma aka sanya su a cikin kundin waxanda za su ci gajiyar shirin, waxanda sun fito ne daga Qananan Hukumomi 233 na Jihohi 23 na qasar nan. “Shirin ciyar da abinci kuma ga yaran makarantu, shi ma yana daga cikin abin da aka tsara na ganin yaranmu sun sami ingantaccen abinci mai gina jiki, inda a kullum ake ciyar da yaran makarantun Firamare milyan 5.5, da suka haxa da mata ‘yan aji xaya zuwa aji uku. “Ya zuwa watan Disamba na shekarar 2017, sama da yara milyan shida ne ake ciyarwa a kullum a duk faxin qasarnan. Wannan shirin ya qara qarfafawa manoman karkara da mata masu dafa abinci,” in ji Ministan.

Lissafi. Kwatankwacin su da suka sami wannan matsayin a jarabawar ta shekarar 2017, shi ne kashi 26.01. “Daga abin da muka bayyana na wannan sakamakon, za mu iya cewa, an faxi a jarabawar, in an kwatanta da abin da aka samu a shekarar 2016 da ta 2017. “Don haka muna kira ga xalibai da su xauki wannan jarabawar da mahimmanci,” in ji shi. Shugaban ya nu na jin daxinsa da yadda ‘yan Nijeriya suka rungumi wannan qarin shirya jarabawar da aka yi. Olu Adenipekun, ya ce, vullo da qarin shirya wannan jarabawar zai magance, matsalar cuwa-cuwar jarabawar da wasu mutane sukan so yi. Ya kuma ce, Hukumar shirya jarabawar ta yammacin Afrika, ta vullo da wannan qarin ne domin ta tallafawa qoqarin gwamnatoci a dukkanin matakai na faxaxa sha’anin ilimin su a nahiyar ta Yammacin Afrika. Olu Adenipekun, ya bukaci dukkanin mutanan da suka san sun zana jarabawar da su binciki sakamakon jarabawar na su a shafin hukumar na yanar gizo.

Rikicin Siyasa Ya Jawo Jikkatan Mutane Da Dama A Bayelsa Daga A. A. Masagala, Benin

Aqalla mutum uku ne suka jikkata da munanan raunuka daban-daban a wani artabu da ya afku tsakanin magoya bayan jam’iyyar mai mulkin qasa A.P.C. da kuma jam’iyyar adawa ta PDP mai mulki a jihar. Kamar yadda rahoto daga jihar ya bayyanar ce wa wannan artabun ya faru ne a qaramar hukumar Brass a cikin jihar a yayin da magoya bayan xan majalisar jihar na jam’iyyar A..P.C. mista Isreal Sunny da kuma magoya bayan shugaban riqon qwariyar kwamitin qaramar hukumar mista victor Isaiah. Kuma an ce faxan ya yi muni sosai yayin da dukkan vangarorin biyu suka fitar da munanan makamai bindigogi da sauransu suka fara farwa juna acikin makaman akwai bindigogi na gargajiya da wasu kayan aiki na gona.


14 labarai

A Yau

Alhamis 15 Ga Maris, 2018 (26 Ga Jumada Thani, 1439)

Nijeriya Za Ta Zama A Sahun Gaba Wurin Fitar Da Tataccen Man Fetur –Kachikwu Daga Idris Aliyu Daudawa

Qaramin Ministan albarkatun man fetur Dokta Ibe Kachikwu ya ce, Nijeriya zata fara fitar da man fetur wanda aka tace da kuma sauran kayayyakin albarkatun man fetur, daga shekaru huxu masu zuwa, idan tsarin da aka yin a gyara matatun man fetur ya tafi kamar yadda aka shirya. Ministan ya bayyana hakan ne a Abuja lokacin da yake yi ma ‘yan jarida kan tsarin da yake na vangaren manfetur. Ya ce, idan aka samu cin nasarar wani sabon tsari da aka yin a yadda sababbin matatun man da aka shirya ginawa za, ayi amfani da jarin a zuba, matatun da ake dasu a Kaduna, Warri, da kuma Fatakwal, abin an samu nasara. Sai kuma sabuwar matatar man ta Xangote, ita ma na gaba zata kasance. Najeriya zata samar da man fetur daya buqatarta. Ya qara jaddada cewar zai xauki a qalla shekaru uku kafin a samu cimma al’amuran ci gaba na vangaren man fetur, saboda su sababbin matatun waxanda zasu fara aiki, daga shekarar 2019 da kuma 2020. ‘’Kamar yadda ya bayyana ‘’Ana buqatar lokaci na daga watannin goma sha biyu zuwa goma sha takwas, a fita maganar sawo man fetur daga qasashen waje’’. ‘’Abin bai yi ma qasa qyau,

bai kuma yi daidai da qimarta ba, idan bata samar da ayyukan yi, bayan nan kuma na rasa haraji, idan abin ya kai zuwa ga gwamnati, ga kuma maganar mutane suna bin dogayen layi na sayen man fetur. Ya yi arin bayani mai cewar Nijeriya wadda take sawo yawancin albarkatun manfetur xinta, amma sai ga shi tana yin iyakar qoqarinta, na neman mutane waxandazasu zo su kafa sababbin matatun man fetur. ‘’Mun buga tallar akan bada daxewa ba maganar sababbin matatun man fetur, muna buqatar mutane su zo su kafa sababbin matatun manfetur cikin matatunmu, ta haka sai muyi amfani da bututun mai da kuma tankoki, muna kuma aiki yadda ya kamata muga , cewar mun kammala duk wani gyaran da ya dace , nan da watanni goma sha biyui zuwa goma sha takwas. Sai kuma maganar sababbin matatun man, a ga cewar an kammalasu nan da shekaru biyu zuwa uku. Ya kuma yi bayani mai nuna cewar ‘’Idan ba a cimma wannan manufa ba kammal sababbin matatun man fetur xin, duk da haka zamu kasance muna da isasshen man fetur, bayan kuma ga maganar Xangote, shi ma da akwai maganar sabuwar matatar man, wadda ita ma ana sa ran zata fara aiki tsakanin shekarar 2019 da kuma 2020.

• Kachikwu

‘’Saboda haka ya kamata mu fara tunanin fitar da albarkatun manmu zuwa qasashen waje, abin da kuma ya kamata mu fara tunani ke nan, idan muka duba yadda yanayin farashin mai ya kan kasance a wannan lokaci da muke ciki’’. Ministan ya qra magana akan qara taimakawa masu zaman kansu, su shigo su taimaka, domin a bunqasa harkar iskar gas a Nijeriya da kuma yadda za a rarraba shi. Hakanan na maganar ayyuka dangane da iskar gas, tuni an fara harkokin a ma’aikatar ya ce, za a tattauna wannan nan gaba , da manyan kamfanonin mai domin a samu tasu gudunmawa.

‘’Ya dace a kammala maganar nmatakan da aka xauka dangane da iskar gas, akwai tawaga a ma’aikatar wadda ta fara aiki sosa da soasai, zata fito da matakan da aka xauka da su manyan masu kamfanonin mai, idan an cimma matsaya masu sa hannun jari zasu amince, idan kuma babu wani wasi wasi, shike nan sai a fara tafiyar da abubuwa’’. Ya qara jadda cewar ’’ Da zarar ana dawasu hanyoyi da kuxin shiga zasu riqa shigowa, bugu da qari kuma ga maganar Petrochemicals , dogaro akan xanyen mai zata wuce,don haka maganar iskar gas nada muhimmanci’ba wai kawai ga maganar kuxaxn da suke

shigo mana ba, akawai ma mganar wutar lantarki, saboda harkar wutar lantarki a Nijeriya ba qaramin abu bane.’’ ‘’Ina iya tunawa cewar ma’aikatar samar dawutar lantarki, ta sa ran samu megawat,7000 a shekarar 2016, da kuma wani a shekara ta 2017. ‘’Akwi abubuwan da muke buqatar domin mu samu iskar gas ta hanyar NPDC ko kuma mai sa jari na uku, wannan zai sa mu samu isasshen iskar gas, domin a ba turbine sinadari qarfi na wutar lantarki, don haka muna aiki saboda a samu cimma shi mizanin, ina ganin shekara xaya ko biyu muna iya kai wa zuwa can.

An Buqaci ’Yan Kasuwan Nijeriya Su Zuba Jari A Jihar Kano Daga Hussain Suleiman

Matuqar manya da qananan ‘yankasuwar qasar nan tare da masu zuba jari daga qasashen duniya suka zo jihar Kano domin gudanar da harkokin kasuwanci tare da kafa kamfanoni idan Allah Ya so ba za su ji kunya ba. Wannan bayani ya fito ne daga bakin mataimakin shugaban cibiyar ciniki da masana’antu da ma’adanai da aikin gona ta jihar Kano KASSIMA Jakadan zaman lafiya Usman Hassan Darma, a lokacin da yake zanta wa da manema labarai jin kaxan da dawowarsu daga qasar Ingila domin nemo

masu zuba jari da kafa kamfanoni a jihar Kano da qasa baki xaya. Jakadan zaman lafiyan wanda har ila yau shi ne shugaban kamfanin shirya tafiye tafiye na Darma Invesment dake Kano, ya qara da cewa, jihar Kano Allah ya albarkace ta da yawan jama’a da kuma iya gudanar da harkokin kasuwanci tsakanin qasashen Afrika, wannan dalili ne ya sa wannan cibiya ta shirya tafiya qasar Ingila tare da wasu ba’adin yankasuwar jihar da kuma manoma inda aka haxasu da takwarorin su na wannan qasa sun kuma tattauna yadda za su shigo Kano domin aiwatar da shirin gudanar

da harkokin kasuwanci da kafa kanfanoni nan ba da jimawa ba. Mataimakin shugaban ya qara shaida wa manema labaran cewa, nan gaba kaxan za a gudanar da wani taro na masu zuba jari na kusan Fam Miliyan 20 kuxin qasar ta Ingila a ciki akwai waxanda za su zuba a kan farfaxo da masana’antun da suka durqushe a faxin qasar nan musamman na jihar Kano. Mataimakin shugaban na KASSIMA ya ce, masana’antun da suka durqushe a jihar Kano cibiyarsu za ta haxa hannu da gwamnatin jihar Kano domin farfado da su, wannan zai sa mutane su samu aikin yi domin

• Ambasada Usman Hassan Darma.

idan ka samar da aikin yi harkokin tsaro za su inganta sosai. Daga nan sai ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da su qara taimaka musu da addu’a da kuma goyon baya domin kai wa

ga samun nasaran da ake buqata. Sannan duk wani mutum ko qungiyoyi ko wanda zai ba da shawara matuqar zai kawo ci gaba cibiyar za ta yi amfani da shi tare kuma haxa kai.


15 labarai

A Yau Alhamis 15 Ga Maris, 2018 (26 Ga Jumada Thani, 1439)

Gidauniyar Na’iro Za Ta Bai Wa Ilimin Mata Muhimmanci Daga Hussain Suleiman

Gidauniyar Ibrahim Na’iro dake unguwar Dakata a qaramar hukumar Nassarawa dake jihar Kano, har yanzu na bai wa ilimin mata da koya masu sana’oi daban-daban muhimmanci Wannan bayani ya fito ne daga shugabar gidauniyar Malama A’isha Ibrahim Abdullahi, a lokacin da take zanta wa da manema labarai kwanakin baya a harabar ofishin gidauniyar ciki har da. Malama A’isha Ibrahim Abdullahi, ta qara da cewa bayan harkokin kula da kuma faxakar da manya da qananan matan da suka haxa da

‘yanmata zawarawa da matan aure takan kuma koya musu sana’oin da za su dogara da kan su ba sai sun jira mazajen su sun ba su ba matan da suke da marayu kuma sun samu hanyoyin ciyar da marayun nasu. Makarantun da suka samar domin matan zalla suna koya musu yadda mace za ta fahimci addinin musulunci da kuma ilimin zamani. Bayan haka gidauniyar na xaukar nauyin biya wa mata kuxin jarabawar JAMB da NECO da WAEC inda suke kuxaxe ne masu yawan gaske, ya zuwa yanzu inji ta sun xauki nauyin wasu mata zuwa jami’ar BUK karatu

A cikin masu tafiyar da jagorancin gidauniyar a kwai waxanda aka ware domin kula da harkokin kula da lafiyar mata da qananan yara musamman idan aka kawo musu shaida daga likita. Ta fannin koya wa mata sana’oi kuwa ta ce, sun qware sosai wajen koya wa mata yadda ake saqar kayayyakin jirajirai da kuma yadda ake haxa lemun sha iri daban-daban da kuma koya musu keken xinki da sauran sana’oi masu tarin yawa. Wani abu da gidauniyar da qware a kai shi ne yadda take hana yara talla inda take koya musu sana’oi idan kuma sun qware gidauniyar take saya .

Al’umma Sun Nemi Talban Katagum Da Ya Yi Takara

•Talban Katagum, Babayo Daga Abubakar Abba

Dakta Musa Babayo Phd, Talban Katagum ba voyayye bane a qasar nan har a wasu qasashen duniya, musamman idan aka yi la’akari da ci gaban da ya samar a fannin ilimin zamani wajen inganta jami’oi da kwalejin ilimi da makarantun kimiyya da fasaha dake xaukacin faxin qasar nan a lokacin da ya shugabanci Kwamitin amintattu na gidauniyar (TETFUND) da a baya ake kira(ETF). Talba wanda al’ummar jihar sa ta Bauchi musaman talakawa suke yi masa laqabi da baya goya marayu, an haife shi ne a garin Azare dake qaramar hukumar Katagum a cikin jihar Bauchi. Qwararre akan fannin ilimin kasuwanci da mulki

da kuma fannin Banki, Talba ya shugabanci hukumar TETFUND a shekarar 2009, inda ya yi amfani da ilimin sa da qwarewar sa, musamman ba tare da nuna wani bambanci ko qabilanci ba wajen samar ximbin nasarori akan inganta makarantun qasar nan da har a yanzu, qwararru da masu ruwa da tsaki akan harkar ilimin zamani suke ganin ba’a samu irin takarawar da ya yi ba a gidauniyar. Alal misali, wasu kaxan daga cikin nasarorin da basaraken kuma xan siyasar Dakta Talba ya samar a lokacin daya shugabanci gidauniyar sun haxa da; qara samar da haxin gwiwa tsakanin gidauniyar da hukumar tattara haraji ta Gwamnatin Tarayya (FIRS), ya kuma qirqiro da horar da ma’aikatan gidauniyar kuma

sama da ‘yan Nijeriya 7,000 suka je qaro karatu na babban digiri da har ila yau wasu kuma sun qaro karatu na digiri a fannoni da-ban-da- ban a gida Nijeriya da kuma qasar waje. Bugu da qari,an aiwatar da ayyuka da dama na farfaxo da kayan aiki na jami’oin da kwalejin ilimi da dama da kuma basu xauki don gudanar da ayyuka a makarantun waxanda har ayau ana amfana a faxin qasar nan. Har kwanan gobe almummar jihar Bauchi suna taqama da yadda Dakta Talba a lokacin yana shugabantar gidauniyar ya inganta Kwalejin dake Azare), inda mafi yawancin al’ummar suka yi ittifaqin cewar, ko a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar Tatari Ali, ba a inganta ilimin boko kamar yadda Dakta Talba ya

Hajiya Aisha ta ce, mafi yawan lalacewar mata da ake samu musamman daga arewacin qasar nan daga talla ake samu, a kan haka ta ce, akwai wata makaranta a unguwar Dakata da suka xauki nauyin gudanar da aiki kyauta domin dai a qara bunqasa harkokin ilimi a jihar Kano da qasa baki xaya Ta yi amfani da wannan dama dan kira ga duk mai son tallafa wa gidauniyar, ya taimaka musu da kayayyakin ilimi ko na koyar da sana’oi tare da ba su kwangila domin samar da kayayyakin da suke saqawa ko sarafawa a gidauniyar. Sai ta ce, yana da kyau mutane su riqa

sanya idanu domin kula da halin da unguwarsu ke ciki domin akwai mata da yara da suke buqatar tallafi sosai musamman waxanda aka mutu aka bar su da yara qanana . Malama A’isha ta ce, sun gaji wannan gidauniyar ne daga mahaifinsu marigayi Ibrahim Na’iro, ta kuma ce, da yardar Allah za su ci gaba da tafiyar da jagorancin gidauniyar tsakanin iyalan da ya bari . Daga qarshe ta ce, tana matuqar jin da xin da ake zuwa har gidauniyar domin yi musu godiya a kan aikaceaikace da suke gudanarwa musamman samar da ilimi da koyar da sana’oi.

An Bizne Marigayi Janar Shelpidi A Gombe Daga Umar A Hunkuyi

An bizne gawar marigayi Manjo Janar Timothy Mai Shelpidi, tsohon Kwamandan rundunar sa ido ta qasashen yammacin Afrika, (ECOMOG). Jiya ne da yamma aka bizne shi a qauyan su, Boh, da ke Qaramar Hukumar Shomgom, ta Jihar Gombe. Ya sami tsira a wani yunqurin kisa da wasu ‘yan bindiga suka kai ma shi a shekarar 2004, lokacin da suka iske shi a gidansa da ke Abuja, suka kuma yi ma shi harbi da dama. An haife shi ne a ranar 4 ga watan Satumba na shekarar 1948, Janar Shelpidi, ya mutu ne a ranar 2 ga watan Maris 2018, yana da shekaru 70 a duniya. Ya shiga rundunar Soji ta qasa a shekarar 1970. An naxa shi a matsayin Kwamandan rundunar

ta ECOMOG ne a watan Janairu na shekarar 1998. Ya yi ritaya daga aikin na Soja ne a matsayin Manjo Janar bayan ya shafe shekaru 29 yana yin aikin na Soja. Da yake jawabi a wajen jana’izar, Gwamna Ibrahim Hassan Xankwambo, ya ce, “Mun rasa wani babban Xa na mu, wanda ya taka mahimmiyar rawa wajen qirqiro Jihar Gombe a shekarar 1996.” Janar Shelpidi, ya shiga harkokin siyasa a shekarar 2003, inda ya yi takarar kujerar gwamna a zaven shekarar ta 2003. Ya kuma tava riqe muqamin Jakadan Nijeriya a qasar Rasha, inda aka haxa ma shi har da qasashen Belarus da kuma Georgia daga shekarar 2008 zuwa 2011. Ya mutu ya bar matar aure guda, mahaifiyarsa, da kuma ‘Ya’ya da Jikoki.

yi ba. Gwagwarmayar Talba ba a kan intanta ilimin zamani kawai ta tsaya ba domin mutum ne mai tausayin talakawa a kullum ba wai kawai talakawan Jihar Bauchi ba harda wasu sauran talakawan qasar nan suma sun amfana da tagomashin Dakta Talba kuma ba tare da nuna wariyar jinsi kota addini ba qabilanci ba. Misali, shearu uku baya da iftila’in annobar zazzabi da amai da gudawa suka varke a wasu sassa da qauyukan jihar, Talba ya xauki nauyin duba lafiyar waxanda suka kamu kyauta a garin Azare da qananan hukumomin Zaki da Itas/Gadau da Jama’are da Shira/Yana da sauran su. Ya rabar da barguna

da suttura da takalma ga makarantun Allo dake qananan hukumomi da mazavu. Dakta Talba har ila yau, ya tallafawa ‘yan gudun hijira da nakasassu da wadanda basu iya biyan kuxin Asibiti ya gina masallatai da makarantun Islamiyya. Ganin irin wannan gwagwarmayar da har yau Dakta Talba yake kan yi, mafi yawancin al’ummar Katagum suke ganin lokaci ya yi da musamman jigogi ‘yan siyasa dake yankin Katagum za su ajiye maganar siyasa da ko shiyya a gefe guda don a marawa Dakta Talba baya ya fito takarar Sanata a zaven 2019 a qarqashin jam’iyyar sa ta APC.


16

Siyasa A Yau A Yau

Alhamis 15.3.2018

Qin Sanyawa Dokar Zave Hannu: Matakin Da Za Mu Xauka Kan Buhari -Majalisar Dattawa Daga Abdullahi Usman, Abuja

Majalisar Dattawa har yanzu ba ta tattauna ba kan wasiqar da shugaban qasa ya aike mata na qin sanyawa gyaran da suka yi wa dokokin zave, mai magana da yawun majalisar Dattawa Sanata Aliyu Abdullahi ne ya bayyana haka. A cikin takardar da aka karanta a majaalisun Dattawa da na Wakilai ranar talata, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana dalilan da suka hana shi sanya hannu a wannan doka. In da ya ce hakan ya tauyewa hukumar zave haqqinta na mai zaman kanta. Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai bayan kammala zaman da majalisar ta yi, Sanata Abullahi Sahabi Aliyu ya bayyana cewa takardar kamar kowace takarda ce ta sanarwa tsakanin shugaban qasa da majalisar. “Ina magana a madadin majalisar dattawa, saboda

haka majalisar dattawa ba ta tattauna kan wannan takarda ba. Wannan ita ce maganr gaskiya a halin yanzu.” In ji Sanata Aliyu Sahabi. Ya ci gaba da cewa “Eh, an karanta takardar yau a majalisa kuma ba wannan bane karo na farko da shugaba Buhari ya aiko wa da majalisa kuma ba ita bace ta farako da aka karanta a mjalisar. Kamar kowace takarda ce da shugaban ke aikewa majalisar. Mun ga takardar kuma an karanta ta majalisa, abin da ya rage yanzu shine majalisa ta tattauna kan takardar.” “Haka takardar qin sanya hannu kan ‘yan Peace Corps, ta zo mana. Dukkan waxannan wasiqu sun xauki hankulan jama’a da kuma Sanatoci da kuma ‘yan majalisar wakilai. Saboda haka na tabbata majalisun za su zauna su duba wannan takarda da shugaba Buhari ya aiko. AMma ya kamata a sani cewa idan doka ta tsallake

karatu na uku kuma majalisar wakilai na irin wannan amma ba su cimma matsaya ba ba abin da za mu iya yi. Abin da muke da shi yanzu shine a bayyane takarda ce aka aiko mana kuma an karanta ta a. Saboda haka gobe za a zartar da abin da za a yi a kanta. Idan kuma akwai wani abu da ya kamata a yi za mu sanar da ku cikin lokaci.

Ita dai wannan doka da sahugaban ya qi sanya wa hannu ta canza yadda za a gudanar da zavuvvukan shekara ta 2019 ne. ‘Yan majalisar na son a fara gudanar da zavensu ne farako, daga nan sai na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi, in da za a gudanar da zaven shugaban qasa a qarshe. Wasu da suka soke wannan

canji ciki har da wasu ‘yan majalisar sun yi zargin cewa wannan canji da aka samu an yi shi ne don a karya shugaba Buhari. Yanzu dai abin da zai biyo baya ko dai ‘yan majalisar su haqura a ci gaba da tsarin da hukumar zave ta qasa ta tsara ko kuma zartar da dokar da kansu kamar yadda tsarin mulki ya basu.

tanadi na musamman don bai wa koya dama kamar kowa a jam’iyyarmu. Dukkan zavukanmu na fid da gwani za su gudana ne cikin gaskiya da adalci kuma a bayyana za mu

yi kowa na gani. Tun daga na jihohi har na tarayya.” “Saboda ha mun tabbata da goyon bayan ‘yan Nijeriya, duk wanda ya sami nasarar samun tikitin takarar shugaban qasa

a jam’iyyarmu, zai iya kada shugaba Buhari cikin sauqi. Sannan zai gajoranci Nijeriya don dawo da ita kan hanyar da jam’iyyar APC da Buhari suka fitar da ita.” In ji sanarwar.

PDP Ta Zargi Shugaban Qasa Kan Qin Amincewa Da Dokar Zave

Daga Abdullahi Usman, Abuja

Jam’iyyar adawa ta PDP ta yi Allah wadai da matakin da shugaban qasa ya xauka na qin amincewa da sabbin dokokin zaven da majalisun tarayya suka aike masa don ganin an canza yadda jaddawalin zaven kamar yadda aka saba yi. Shugaban ya aikewa da majalisun biyu takarda ranar talatar da ta gabata in da ya bayyana cewa ba zai sanya wa wannan doka hannu ba, saboda ta yi wa hukumar zave karan tsaye a matsayinta na mai zaman kanta. An kuma karanta wannan takardar ne a zaman da aka yi ranar talata a majalisar. A cikin takardar da sakataren watsa labaran jam’iyyar, Kola Ologbandiyan ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa ba su mamakin qin sanya wa wannan

takarda hannu ba da shugaba Buhari ya yi, domin a cewarsa har yanzu yana nuni da cewa ba sanin siyasa ya yi ba. “Jam’iyyar PDP ta yi imanin cewa dimokraxiyya ta tanadi abubuwa da dama, daga cikinsu har da daraja vangaren dokoki kan ikon da tsarin mulki ya ba shi na gudanar da dokoki da kuma gyara dokokin idan buqatar hakan ta taso.” “Saboda haka yanzu jam’iyyar PDP da ‘yan Nijeriya sun sanya ido ga majalisun dokoki don ganin matakin da za su xauka kan wannan doka. A matsayin mu na jam’iyyar siyasa ba ma tsoron zaven shekarar 2019, sabosda mun san cewa ‘yan Nijeriya tuni suka yi watsi da shugaba Buhari da jam’iyyarsa ta APC.” jami’an ya ci gab da cewa “A jam’iyyarmu ta PDP mun yi


A Yau Alhamis 15 Ga Maris, 2018 (26 Ga Jumada Thani, 1439)

Xan Majalisar Wakilai Ya Samu Goyon Bayan Al’ummarsa Daga Muhammad Maitela, Damaturu Al’ummar mazavar xan majalisa mai wakiltar qananan hukumomin Damaturu, Tarmowa, Gujba, da Gulani dake jihar Yobe a zauren majalisar wakilai ta qasa, Hononrabul Abdullahi Usman Kukuwa, sun bayyana ci gaba da cikakken goyon su ga xan majalisar dangane da kyakkyawan wakilci da halin dattakun da yake nuna musu, tun bayan zavar sa a majalisar. Jama’ar mazavar xan majalisar sun bayyana hakan a cikin wata tattaunawar jin ra’ayi da wakilin mu a jihar Yobe ya gudanar daga bakunan jama’a dabandaban a mazavar. Sun bayyana Hon Abdullahi Usman Kukuwa matsayin haziqin xan siyasa wanda ko yaushe qofar sa a buxe take wajen sauraron ra’ayoyin waxanda yake wakilta. “Ya kawo gagarumin sauyi a mazavar sa, ta fuskacin bunqasa matasa dangane da basu jarin yin qananan sana’o’in dogaro da kai, tallafin karatu, xaukar nauyin matasa zuwa cibiyoyin koyon sana’o’in hannu dake Kano da basu alawus-alawus a lokacin da suke karvar horon samun qwarewar tare da basu kayan sana’ar da suka koya. Uwa uba kuma, kowanne lokaci a shirye yake da xaukar xawainiyar wani mutum daga wannan mazava tashi- kuma ba tare da gajiyawa ba”. Alhaji Saleh Bakoro Sabon FegiDamaturu, kuma babban qusa a qungiyar ‘Muryar Talaka’ ta qasa, ya bayyana xan majalisar wakilan da cewa” matsayin mu na matasa masu magana da yawun talaka a qasar nan, bisa ga haqiqanin gaskiya mun yaba matuqa dangane da halin dattakon Hon Abdullahi Usman Kukuwa. Sannan mun yi hakan ne ba don komai ba sai ta dalilin qoqarin da yake, a zahiri wajen bunqasa rayuwar al’ummar sa, kuma da yadda muke jin kalaman yabo da Allah-san-barka daga bakin waxanda yake wakilta”. “Sannan xaya daga cikin wasu alamu da zaka yi amfani dasu wajen baiwa kowanne shugaba wanda yake wakiltar al’umma shi ne ta hanyar gudanar da ayyukan ci gaba masu ma’ana. A wannan yanki namu- da ma kowanne vangaren qasar nan, al’amari ne mai muhimmanci a baiwa matasa kulawa ta daban, saboda yadda sune shugabani na gobe kuma ta hanyar su ake gane makomar kowacce al’umma. Ta wannan fannin, Hon Kukuwa ya zarta sauran, ya baiwa matasa sama da 100 tallafin karatu, waxanda ke karatu a jami’o’i da kwalejojin ilimi da na kimiyya”. Inji shi’ Saleh Bakoro ya qara da cewa, baya ga wanda ake dasu a qasa, yanzu haka ya tsara tura xaruruwan matasa cibiyar koyon sana’o’i’n hannu ta Kano- domin su koyi sana’o’in hannu dabandaban, wanda kuma za a rinka basu alawus-alawus tare da basu tallafin kayan sana’ar da suka samu horo a kai. Ya ce, wannan shi ne

abinda ya kamata ace wakilai suna yi domin rage zaman kashe wando a tsakanin matasa. “Jama’ar wannan jiha tamu ta Yobe sun shaida yadda Hon Abdullahi Usman Kukuwa ya raba wa al’ummar qananan hukumomin mazavar sa kayan abinci domin rage musu raxaxin matsalar tsaron da ta shafi yankin sa. Waxanda suka haxa da shinkafa buhu 2500 da masara muhu 2800, taliya katon 3000 da magi katon 1000 haxi da mai- galan 2500. Al’ummar wannan yanki basu tava samun irin wannan tallafi ba, sai a wannan karon. Duk da waxanda suka gabace shi suma sun yi iya nasu qoqari”. Inji Saleh. Bugu da qari kuma, ya ce xan majalisar bai tsaya nan ba inda ya kada baki tare da bayyana cewa” ta fannin samar da ruwan sha kuma, ya tono manyan rijiyoyin burtsatse uku a Gulani kuma yanzu haka jama’a na amfana dasu. Ya tona qarin wasu a unguwar Maisandari da Nasarawo da makamantan su a cikin Damaturu. Inda yanzu haka ana shirin tona wasu guda uku a Tarmowa. A taqaice, babu lungun da zaka shiga a wannan mazavar face ka tarar da ayyuka masu ma’ana waxanda Hon Kukuwa ya aiwatar ga jama’a.” “Har wa yau, Hon Abdullahi Usman Kukuwa ba ya daga cikin yan majalisa masu xumama kujeru a zauren majalisar wakilan tarayyar Nijeriya. Ya gabatar da qudurori masu ma’ana da shiga kwamitoci da dama dangane da ci gaban jihar sa dama yankin arewa maso-gabas baki xaya. Musamman kan halin matsalar tsaro da yadda ya kamata gwamnatin tarayya tayi domin sake farfaxo da yankin. Sannan kuma kowanne lokaci yana zuwa mazavar sa domin jin ra’ayoyin jama’ar da yake wakilta- shi ba irin yan siyasar nan bane waxanda tsakanin ku dasu sai ranar zave”. Ya nanata. Shi kuma Abdullahi Dauda Damaturu, shugaban matasa ya bayyana xan majalisa Kukuwa da cewa” gaskiya mu matasa muna nan tare da Hon Abdullahi Usman Kukuwa- xan majalisa mai wakiltar mu a majalisar wakilai, saboda yadda ya nuna muna halacci a cikin dukkan buqatun mu waxanda muke bijiro masa. Kuma wannan shi ne matsayin duk wani matashi da yake a nan Damaturu. Kuma mu bamu san kowa ba sai shi- bamu da wani wanda muke da fata a kan sa da ya kai shi.” “Tun a lokacin yana xan majalisar dokokin jihar Yobe, jigo ne gare mu kuma mai share muna kukan mu, bayan da ya koma majalisar wakilai, nan ma bai manta da mu ba. Wanda zancen da nake yi da kai ya samarwa da matasa sama da 100 ayyukan yi, baya ga tallafi na musamman da yake yiwa jama’ar wannan yankin, ga sauraron koke-koken waxanda yake wakilta. Saboda qoqarin da yake yi a kwanan baya saida Gwamna Alhaji Ibrahim Gaidam ya fito qarara ya yaba masa tare da

Siyasa 17

• Hon Kukuwa. kira ga takwarorin sa kan su yi koyi dashi”. Inji shi. “Bisa ga wannan muke qara shelanta wa duniya kan cewa mun gamsu da wakilcin Hon Abdullahi Usman Kukuwa, kuma bamu san kowa ba sai shi kaxai. Sannan da ana gadar da wannan kujera ta majalisar wakilai to da mu matasan wannan yankin mu sallama mashi ita. Bugu da qari, zamu ci gaba da bashi goyon baya wajen cimma muradun da yasa a gaba”. Ta bakin shi. Usman Yusuf daga qaramar hukumar Tarmowa ya bayyana cewa” gaskiya mun yaba matuqa da wakilcin Hon Abdullahi Usman Kukuwa a zauren majalisar wakilai, ba domin komai ba sai saboda yadda yake kula da buqatun waxanda muka zave shi a matsayin wakilin mu. Kuma baya ga yadda yake xaukar mu da muhimmancita hanyar sauraren kuken mu kuma ba tare da alamar gajiya wa ba, ya kula da rayuwar mu matasa ta vangaren tallafin karatu da bamu jarin qananan sana’o’i”. “ yanzu haka na san xalibai sama da 30 waxanda suka ci gajiyar tallafin karatu, waxanda suke karatu a jami’ar jihar Yobe da a jami’ar gwamnatin tarayya dake Gashuwa. Sauran sun haxa da masu karatu a kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya (Federal Polytechnic, Damaturu) da kwalejin Ilimin jihar Yobe dake Gashuwa. Akwai matasa da dama waxanda ya tallafa wa da jari domin yin sana’a- wasu naira dubu 50,000 wasu 40,000 wasu kuma fiye da haka. Sannan ya saya wa wasu ‘Keke Napep’ ciki harda wani abokina, domin su samu sana’ar dogaro da kai”. Inji matashin. Alhaji Muhammed Kukuwa dake qaramar hukumar Gulani, wanda kuma jigo ne a siyasar mazavar Hon Abdullahi Usman Kukuwa, ya bayyana cewa, duk yadda xan majalisar bai daxe a zauren majalisar ba, ya taka muhimmiyar

rawa wajen kawo ci gaban al’ummar qananan hukumomin da yake wakilta. Kuma yayi qarin haske da cewar, mutum ne mai jin shawara da koken jama’ar da suka zave shi, kuma kowanne lokaci qofar sa buxe take ga jama’ar sa. “Tun kafin wannan lokacin, ya riqe xan majalisar dokokin jihar Yobe kuma kowa ya san shi da haba-haba da mutane, kuma kowanne lokaci yana tare da jama’ar sa a cikin farin ciki ko damuwa. Duk tsawon wannan lokaci na matsalar tsaro da aka shiga a Yobe, bai tava fashin zuwa cikin al’ummar sa ba, kuma ba ya qosawa da mutane a nan Yobe ko Abuja. Saboda haka tsakanin mu da shi sai fatan alheri, yayi muna halasci matuqan gaske”. “Bugu da qari kuma, ya kula da matasa da dattijai- maza da mata, baya wasa da buqatocin jama’ar sa, ballantana kuma mu yan siyasa; duk wata matsala wadda muka kawo masa nan take zai bincika tare da xaukar qwaqqwaran matakin agance ta. Har wala yau, yana shawartar mu tare da sauraron koke-koken da muka tunkare shi dasu dangane da al’amurran jama’a. Tattare da hakan ne muke sake jaddada goyon bayan mu tare da sauran waxanda duk suke tare damu ga Hon Abdullahi Usman Kukuwa da nuna gamsuwar mu bisa yadda yake wakiltar mu a zauren majalisar wakilai ta tarayyar Nijeriya”. Ta bakin sa. An zavi Hon Abdullahi Usman Kukuwa a gurbin yar majalisar wakilai, Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim, bayan naxa ta muqamin qaramar ministar kula da harkokin qasashen waje da gwamnatin Muhammadu Buhari. Wanda a zaven cike-gurbin da hukumar zave ta INEC ta gudanar a watan Afirilun shekarar 2016, yanayin da ya bashi nasara a kan abokin hamayyar sa na jam’iyyar PDP, Nasiru Hassan Yusuf.


18 TATTAUNAWA

A Yau Alhamis 15 Ga Maris, 2018 (26 Ga Jumada Thani, 1439)

Idan Aka Ba Al’umma Ilimi An Samar Masu Sana’a -Dakta Muhammad DAKTA MUHAMMAD BADAMASI BABANGIDA shi ne babban darakta mai kula da makarantar Al-Amin International School da ke minna kuma shi ne shugaban gidauniyar Al-Amin Foundition. A tattaunawarsa da wakilin mu MUHAMMAD AWWAL UMAR ya tavo batutuwa da dama musamman sakacin Arewa akan ilimin zamani, ya bayyana muradinsa na tallafawa marasa qarfi. Ga hirar kamar haka: Daga Muhammad Awwal Umar, Minna Da farko mai karatu zai so sanin ko waye muke tare da shi. Suna na Muhammad Badamasi Babangida, an haife ni a Kaduna, ina da shekaru 46 da haihuwa. Na yi karatu ina da masters digiri guda biyu ina kan neman darajar dakta na ilimi da shugabanci. Ranka ya daxe me ye dalilin samar da wannan gidauniya ganin kana xaya daga cikin matasan da Allah Ya tarfawa garin su Nono kana da abin hannun ka. Da farko kamar yadda ka faxi na yi tunanin samar da wani muhimmin abu da zan yi da zai taimakawa ‘yan uwana matasa masu tasowa musamman waxanda ba sa sha’awar karatu akan dalilin rashin hali ko wani abu daban, la’alla hakan zai sa su iya anfanar da kansu ta fuskar ilimi dan ya zama masu alheri. Shin ita wannan gidauniyar daga ina ta ke samun kuxaxen shigarta? Tana samun kuxaxen shigarta a waje na ne, sai kuma ‘yan uwa da qannai na masu sha’awar taimakawa kowa na bada na shi gudunmawa, ta haka ne muke tafiyar da ita.. Akwai aikace-aikace da ku ka fara da xan dama, shin kai tsaye me ku ka fi mayar da hankali a kai? Mun fi mayar da hankali akan inganta ilimi a rayuwar matasa tun daga faramare har zuwa jami’a. Bayan sun kammala karatun kuma mu san yadda zamu taimaka masu su samu aikin yi, babban burin mu shi ne idan mun taimaka an samu ilimi kuma sun samu aiki ya zama na suma zasu iya taimakawa na bayansu. Bisa al’ada a qasar nan musamman a Arewacin qasar nan za ka ga gwamnati na magana akan ilimi amma idan ka shiga sosai sai ka tarar ba wani tsarin kirki da aka yiwa ilimi. Ita wannan gidauniyar me ta ke yi wajen faxakar da Iyaye da shugabanni wajen inganta ilimi a tsarin rayuwarsu. Abu biyu mu ke yi na farko mu kan shiga anguwanni

•Dakta Muhammad Babangida.

mu ga waxanda ke da rauni akan kula da yara wajen bada ilimi, mu kan xauki nauyin ire-iren waxanna yaran ta yadda zamu xauki nauyin kafa harsashe mai muhimmanci da zai inganta rayuwarsu ta vangaren ilimi. Na biyu kuma idan mun samu damar haxuwa da ‘yan jarida mu kan bayyana manufarmu ta hanyar jawo hankalin gwamnati da Iyaye ta yadda zamu haxa hannu wajen bada gudunmawar da zai taimakawa yara masu tasowa. Mu kan jawo hankalin Iyayen mu su gane muhimmancin karatu ga matasan Arewa, mu lurar da su nisan da aka yiwa yankin mu da kuma bada shawarwarin hanyoyin da ya kamata a bi wajen ganin mun lalubo bakin zaren. Yanzu ka ga muna ‘yan tafiye-tafiyen mu haka kuma anai mana gori ana ce mana mu ‘yan Arewa ba abinda muka sani sai bara, wanda idan ka duba baran al’ada ce ba addini ba, sai kuma kula da shanu mu kuma abin na yi mana ciwo. Idan muna son Arewa tai gaba ya zama wajibi mu lalubo hanyar da zamu ceto rayuwar matasa mu daga yawon barace-barace da

rayuwar rashin aiki da muka xora kan mu akai, in ba haka Arewa kullun a baya ta ke. Ganin kai matashi ne, kuma kana daga cikin ‘yan gaba-gaba na ganin rayuwar matasa ta inganta. Kuma bara na da tasiri, shin me ka ke ganin ya janyo hakan? Ka ga Iyayen mu ba a baya ba sa tunanin makomar rayuwarmu a gaba suna ganin ai Allah na nan, ba su damu da yadda zasu xora rayuwar yara ba suna ganin kawai za su bar su kara zube sai abinda Allah yayi, don haka ba sa tunanin xora wrayuwar yara akan tsarin ilimi, in ma yaro zai iya fita ya bi titi yana roqo ya samo naira xari ya kawo gida, ka ga in su goma ne an samu naira dubu xaya ke nan, ba damuwarsu abinda gobe zai shaifar ba ka ga wannan matsala ne babba. Amma a gaskiya za ka tarar da mutumin kudu koda a shekarun baya ne kuwa, in ma yara uku zuwa huxu yake da su zai himmantu wajen neman hanyar taimakonsu, taimakon nan kuwa shi xora su akan turbar ilimi ta yadda in sun kammala zasu iya fantsama neman mafita a rayuwa,

amma mu a nan Arewa abin ba haka yake ba, dole mu canja tunanin mu, in har ba mu iya canja tunaninmu ba. haka abin zai xore, duk irin tsarin da gwamnati za ta kawo ba zai yi tasiri ba. Yawan yaran da muke samu abin daga Allah ne, amma ya zama wajibi koda yara goma ka haifa ka san suna da haqqi akan ka a matsayin ka na uba, don haka ba yawan haihuwar ba kula da haqqi shi ne abu mai muhimmanci, ka bai wa yaran ka ilimi, idan sun samu ilimi sun gama samun komai na rayuwa. Ya kamata shugabanni da gwamnatocin Arewacin qasar nan su vullo da hanya mai xorewa da zai taimakawa matasa masu tasowa hanyar da za su iya samun damar riqe kawunansu, ya zama harkar bangar siyasa da barace-barace ya kawo qarshe, domin rashin hakan ba zai haifar mana xa mai ido ba, amma baqin ciki ne yadda muke tafiya yanzu idan an cigaba a haka domin ba zamu iya qyanqyashe nagartattun mutane ba. Duk tsarin da gwamnati za ta vullo da shi a harkar ilimi mu Arewa ba zai anfane mu ba dan ba mu da irin wannan tarbiyar.

Ci gaba a shafi na

26


19

A Yau Alhamis 15 Ga Maris, 2018 (26 Ga Jumada Thani, 1439)

Adabi

Tare da Dakta Aliyu Ibrahim Qanqara 07030797630 imel: ibrahim@fudutsima.edu.ng

Zuwan Malam Bahaushe A Qasar Hausa (7) Savanin yanda mu ka furta a baya qyas, a wata ruwayar an nuna cewa Mallam Bahaushe a Qasar Hausa ya soma ne daga wani yanki ko wasu yankuna na Qasar Tahoua ta Qasar Nijar da ake kira Illela (ko Lalle da Boso) An ce daga nan Hausawa su ka fallatsa zuwa sauran sassan Arewaci da kudancin Afirka. Farfesa Ado Muhamman, shugaban Jami’ar Tahoua, a wata zantawa da mu ka yi da shi ya nuna cewa tun usulan akwai Hausawa na gidi (na asali) da su ke zaune a nan yankunan qasar Tahoua da a da ba su tava zuwa ko’ina ba sai daga baya su ka fantsama cikin Duniya su ka yi sansani. Irin Hausar su ma ta zo daidai da irin Hausar Qasar Sakkwato da Qwanni. Watau tatattar Hausa ce ba ta da gami ko surki. Daga cikin su akwai ma masu tsaga irin ta Bahaushe na asali. Bugu da qari har yanzu ba su daina yin irin waccan al’ada ta Malam Bahaushe na farko ba, duk da yak e addinin Islama ya zo ya kawo sauye-sauye da gyare-gyare ga al’adojin da ya tarar. Nan da nan fa gadangadan sai Malam Bahaushe ya himmatu wajen aiwatar da sana’o’i. Wannan hanyoyi ne na inganta tattalin arzikinsa da na iyalinsa. Daga cikin su akwai waxanda ya gada tun daga kan kakanninsa. Kamar su noma da kiwo da kuma uwa uba fatauci. Sun taimaka ma Hausawa wajen kawo zaman lafiya da zumunci ma a tsakanin su. Domin a wancan lokacin, kowanne mutum bahaushe ya xauki irin sana’ar da ya gada a gidan su da matuqar muhimmanci. Ina? Ba ka is aka tsallake gidan ku ka tafi wani gida ka yi ko ka koyi irin sana’ar sub a, kai ga na ka? To ita sana’ar gidan ku w aka bar ma wa ya yi? Ka ga ba ta yiwuwa. A wancan waqati kuma bahaushe bai isa ya tsallake maganar iyayen sa ko magabatan sa ba. Wurin Malam Bahaushe aka ga wannan halayyar. Maqasudin kowa ya riqe sana’ar gidan su shi ne don kada gidan yam utu, sannan kuma kowa ya dogara da kan sa don a lokacin ba a san maula ko zuwa wurin wani don nuna halin qasqanci ba. Wannan

shi ya qara xaga martabar Mallam Bahaushe ya nuna shi a idon Duniya a matsayin wani muhimmin mutum, karimi. Kuma sannan da yaro ya fara girma sai a nuna masa sana’a irin ta gidan su. Misali, noma shi ne sana’ar Malam Bahaushe na farko. Noma shi ne ma qashin bayan tattalin arzikin qasa. Noma sana’a ce ta kowa da kowa, kama daga mai arziki zuwa talakka, ko mace ko namiji, ko babba ko yaro. Lokacin da wani Bature jar fata Ba’ingile da ake kira Dokta Henrich Bath xan yawon Duniya ya zo Katsina cikin shekarar 1850 daidai ya hudo ma garin ta arewa, watau daga qasar Tasawa. Ya bayyana cewa da ya ratso ya ga babu saura ko fili wanda ba komi a cikin sa. Ko’ina gonaki ne na jama’a. Ya kuma ga jama’a sun noma dawa da gero da taba da auduga da dankali da makani da sauran su. Wannan ya samu nasara ne domin Qasar Hausa kaf xin ta ta na da fadamu na noma da jigawa masu albarka gami da yawan ruwan sama matsakaici. Hausawa sun fara yin tunanin zama wuri guda don su riqa yin ayyuka tare, su taimaki kawunan su su kuma yi aikin gayya tare. Babban misalin da za mu buga a nan shi ne kewayen Birnin Katsina tun gabanin zamanin mulkin Sarki Muhammadu Korau (13881448) A cikin littafin sa, R. Soper ya tabbatas cewa kushewoyin da aka samu a

wuraren da ke kusa da birnin Katsina ya nuna cewa akwai jama’a a wuraren tun shekaru aru aru da su ka gabata Waxannan Adawa su na da girma sosai kuma ba su da wata sana’ar da ta wuce qereqere na kayan halbi, su kan shiga jeji su kashe manyan namun jeji. A cikin qarni na 15 kewayen birnin Katsina ya cika da jama’a da fatake masu tasowa daga kudu su nufi arewacin Katsinar. Dalilin bunqasar Katsina kenan, waxanda su ka fara kafata su ka shiga kafa kan maqeru a inda su ka sami matsugunni suna yin qira. Wannan wata dabara ce da su ka vullo da ita ta maishe da qarfe abin amfani ga xan Adam. Sannan a hankali mutanen su ka fara qera makaman yaqi da na noma, kamar; bindiga, fartanya, gatari, dagi ko diga, sarqa (ta doki), wuqa, adda da dai sauran su, su na fansar wa fatake ma su zuwa su yada zango su wuce qasashen Nijar kamar Maraxi, Damagaran, ko Yamai, da sauran ayarin manoma. Mutum guda, a bisa kan maqerar sa sai ya yi hauya sama da xari ukku (300) Wannan shi ya sanya suma mahalba da manoma su ka qulla qawance da maqera, har su ma su ka zo su ka kafa sansanin su. Har ya zuwa wannan waqati na qarni na 15 babu wuri ko kuxi na ciniki a wannan zamani sai dai abin da su ka kira ‘bani-in-baka’, wanda Turawa ke ce ma trading by bata. Ma’anar haka shi ne su manoman sai

su ba maqeran gero da dawa ko masara, da sauransu. Su kuma maqeran sai su mayar masu da abubuwan da su ka qera. Mahalba kuma sai su ba maqeran xan naman dabbobin da su ka halbo ko wasu abubuwan daban, su kuma su basu kayan halbin da su ka qera. Ko wannensu a cikin ukkun ya dogara akan kowanne kan zaman sana’ar sa. A daidai lokacin kuma wannan wuri ya qara bunqasa, domin ana ma tunanin unguwar Ambuttai aka fara kafawa a cikin birnin Katsina, to daga nan sai qananan sansani na kewaye da ita su ka tsira. Mahalba na sare itacen su na mayar da su itacen bindigogi. Maqera kuma, waxanda a sa’annan a ka fi kira da ‘yan tama su na saro itace su na qonawa, su na kuma amfani da garwashin wajen gasa qarafa. Cinikin tama fa ya gawurta. Wannan bauta a na yin ta a ko’ina a cikin Arewacin qasar nan. Kamar dai yanda mafi yawancin jama’a ke yi, na zamani na baya, mutanen Katsina sun samu matsalar fahimtar wanene Ubangiji. Kuma su ka rasa gane shin minene bambanci a tsakanin Ubangiji da rana da wata da taurari da ma sararin samaniya da haske ko walqiya ta lokacin ruwan sama da kuma tsawa. Kowanne sun xauka shi ne Allah. Saboda jahilcin ma hatta duwatsu an sha bauta masu, ana cewa daga sama su ka faxo, wai daga duniyar Marik. Mu kwana nan.


A Yau Alhamis 15.3.2018

20

Ciniki

Kasuwanci Masana’antu

inshora

hannun jari

Editan Kasuwanci Mohammed Shaba Usman

kasuwar shinku

Na Fara Sana’ar Qota Tun Ina Karami -Silas Wannan wata tattaunawa ce wacce EDITAN KASUWANCINMU yayi da SILAS JOSEPH, wanda ya bayyana cewa ya fara sana’ar yin qota tun yana xan qaramin yaro. Silas ya bayyana yadda ya sauya sana’a daga yin Qota zuwa Sana’ar yin turmin daka. ga yadda hirar ta kasance: Masu karatu za su sanin sunan wanda muke tare da shi Suna na Silas Joseph. Ni xan asalin Jihar Kaduna ne a wani qauyen da ake kira Gwaba. Qauyen na qarqashin qaramar hukumar Kagarko ne. An can aka haife ni, kuma a nan nake zaune da iyalai na; mata biyu da yara bakwai. Shin wanne Aikin hannu ka fara yi a rayuwarka? Gaskiya ba wannan ba ne aikin hannu na farko da na fara, da can ina yin Qota ne kafin na zo na fara koyan wannan sana’ar ai shi wannan ban dade da fara shi ba, aikin kota ne na dade ina yi saboda tun ina dan saurayi na nake yin Qota ma manuma kuma nima ina yin numan karan kan sa ko wani lokaci. Mene ne ya sa ka bar yin Qota ka koma wannan sana’ar yin turmi? Toh akwai wani mutumi da yazo nan garin yana yin turmi da injin daga nan abun sai yabani sha’awa kawai yanda haka yi na fara sha’awar aikin kenan a gaskiya ko kai ne sai abun yabaka sha’awa kuma yafi mun sauki akan yin Qota. A ina ka koyi yin shi wannan turmi? Na koyi yin turmi ne a wajan wani mutum da muke kira masta Tony, masta Tony de dan labilan Idoma ne ye zo nan Gwaba yana yin wannan aikin tun ina zuwa ina kallo har abun ya fara shigan mun rai sai na same shi cewa ina son na koyi wannan sana’ar sai yace mun to naje na kira Baba na su yi magana abun nufi suyi yarjejeniya sai na samu Baba na nagaya ma shi sai suka zauna kawai na zo na fara koyan aiki da masta

Tony da na yiya bayan kwana biyu sai masta Tony ya bar garin mu sanadiyan na fara yin aikin ni kadai kenan a wurin nan, na je na sayi injin kera turmi da kuma wadan su karafa na yin zane a jikin turmin. Shekaru nawa ka xauka kana koyan wannan aikin? Ban kai shekara ba ma na de yi kamar wata shida zuwa bakwai, saboda aiki ne mai sauki idan mutum ya sa ido, kasan komi saida niya na sa son shi a zuciya na shi ya sa na yiya shi nan da nan kasan idan kana son abu kafi sa ido fiye da abun da aka saka dole cewa kayi, kaga wannan abun yana cutar da yara da kuma matasa, misali kana da yaro da kake son ya koyi sana’ar hannu na farko ka fara tanbayan yaron wani aikin hannu yake son yanda koya, sannan ka dauke shi ka kai shi wurin da kan ka idan kayi wa yaro haka yafi sa ido a wannan aikin fiye da wanda haka sa dole. Kaga ba wai an tilasa mashi bane. Ka lura da yaran da suke koyan aiki kwanan nan saikaga yaro guduwa daga wurin aiki wani ma har ya zagi mai gidan shi saboda an tilesa ma shi ne ba wai yana son aikin ba. Saboda haka dan Allah iyaye mu dinga lura da abun danka ko yarka take so kafin ka yanka hukunci. Yanzu ina da yara biyu da suke koyan aiki a wuri na duk kuma daga sona zuwa kallo yanda nake yin aikin har suma abun ya shiga rahayin su. Waxanne abubuwa ake kawo wa idan za a koyi wannan aikin? Toh duk wanda yake son ya koya wannan aikin a wuri na, na farko de shine zai zo da Baban shi ko kawun shi ko kuma maman shi, cikin

•Silas a bakin aiki.

mutane ukun nan de ba za a rasa mutum daya ba, dalili shine zamuyi yarjejeniya da duk wanda ya kawo a kan tsarin koyan aikin da kuma kudin da zai biya a lokacin da zai biya su. Kudin da wani lokaci ne mutum zai biya su? Za a kawo abun sha a lokacin da muka zauna baban shi kamar miniras ko pami a sanda yaron zai fara koyan aiki kuma a wata shida zan ba shi yaron inshaa Allahu a cikin wata shida nan zai yiya aikin sannan za a biya ni kudin sai na yi ma sallama (freedom). Turmi kawai kake yi ko da wani abun kuma da wannan injin din yake yi? Gaskiya akwai abubuwa da yawa da wannan injin din yake yi, kamar abun zuba abinci, cokula da kuma faranti daura abun zuba abincin sai kuma kofin shan ruwa da sauran su. Wannan itacen da na gani da su kake haxa turmi? A da su nake duk abun da nake so nayi da turmi, takparya da kuma sauran su. Akwai itacen sa ne da kuma

a ina kake sayan shi itacen? Sayo su nake yi kuma akwai itacen su ne daban ba wai ko wani itace bane suke yin turmi ba wani lokacin ma ina yin hasara idan itacen bai yi yanda ya kamata ba, sai de na yi hasara kawai. Wani kalubale kake fiskanta a nan wurin? Toh kaga na farko nan kauye ne ba abu bane wanda za a ce kullun a na saya na, I babban Matsalar MA shine rashin ciniki anan kauyan sai kuma mai da nake a injin na yi aikin da shi shima ya kara kudi su kuma masu sayan ba su son suji cewa ka kara kudi a kan abun da suke saya da kuma ya zama dole ne na kara tunda komai ina saya ne kuma dan riba nake aikin. Wani shawara zakaba matasa da kuma gwamnati Nijeriya? Toh ni de ban da wani magana da yawa da zan fadan ma matasa illa su tsaya su koyi sana’ar hannu shine kawai. Gwamnati kuma dan Allah su tallafa mana mu da bamuda karfi wajan sandy mu don Allah su sauqaqa mana.


A Yau Alhamis 15 Ga Maris, 2018 (26 Ga Jumada Thani, 1439)

KASUWANCI

21

Badaqalar Ma’aikatan Banki Na Qara Hauhawa —NDIC

Daga Abubakar Abba

Hukumar sanya ido akan Kuxin inshora ta qasa (NDIC) ta danganta mafi yawancin alumundahar da ma’aikatan Bankuna suke tabkawa ta qaru daga yawan 231 a shekarar 2016 zuwa 320 a cikin watan Yuki na shekarar 2017. Shugaban sashen adana bayanai da huxxa da jama’a na NDIC Mohammed Ibrahim ne ya sanar da jakan a cikin sanarwar da ya fitar a ranar lahadin data wuce, inda ya ce, wannan adadin yana cikin rahoton hukunar data fitar a kwanan bayan data sanya ido akan kuxaxen da ake ajiyewa a bankuna. Rahoton ya dogara ne akan jimlar martani guda 286 da aka samu daga bankuna 26 a cikin lokacin kuma wattani 22 da ba a samu martani daga bankuna ba har zuwa qarshen ranar 31 ga watan Disambar shekarar 2017 ba. Mayar da martani guda 286 da aka samu daga bankuna a shekarar

2017, ya nuna yawan badaqala guda 26,182 da kuma yin bogi wanda ya kai kasha 56.30 bisa xari idan aka kwatanta da badaqala guda 16,751 da aka bayar da rahoto a kai a shekarar 2016. Har ila yau, yawan aikata badaqalar ta qaru zuwa naira biliyan 3.33 daga cikin naira biliyan 8.68 da aka bayar da rahoto a kai a shekarar 2016 zuwa naira biliyan 12.01 a shekarar 2017 koda kashi 38 bisa xari. Bugu da qari, asar da ake sa ran zata auku ta ragu kaxan akan naira miliyan 24.42 ko kashi 1.03 bisa xari daga cikin naira biliyan 2.39 a shekarar 2016 zuwa naira biliyan 2.37 a shekarar 2017.” Ibrahim ya sanar da cewa, hada-hadar banki ta kafar Internet da kuma yin amfani da katin ATM da ya shafi irin wannan badaqalar da aka kawo rahoto akai, ya kai yawan kashi 24,266 ko 92.68 bisa xari na dukkan rahotannin da aka kawo, inda ya kai yawan naira biliyan 1.51 ko kuma kashi 63.66 bisa xari na

asarar da aka tabka a shekarar 2017. Ya ci gaba da cewa, rahoton ya kuma qunshe da sauran bayanai na aikata wasu laifuffuka kamar na tabka badaqala wajen tura kuxi da fitar da kuxi da danne kuxaxe da bayar da basussukan da a hukumaci bankunan basu bayar da izini ga ma’aitan su yi ba da kuma canja chakin na kuxi. Sauran karkatar da kuxin masu ajiya a bankuna da karkatar da cajin da bankuna keyi da kuma gabatar da chek na sata da na bogi. Ibrahim ya qara da cewa, bankuna 22 na hada-hadar kasuwanci da aka basu lasisi da kuma bankunan Merchant guda huxu, sun mayar da kuxin shiga har guda 286 bayan sun kori ma’aikatan su a bisa zargin aikata badaqala da yin bogi a cikin wannan shekarar. Ya ce, daga cikin badaqala guda 26,182 da bankunan 26 da aka bai wa lasisi suka kawo rahoto akai, badaqala guda 320 an danganta su ne ta hanyar haxin

baki da wasu ma’aikatan bankin. “Jimlar ma’aikatan banki guda 320 kodai an kore su daga aiki ko kuma an dakatar dasu a a shekarar 2017, savanin jimlar ma’aikatan banki guda 231 da aka sallama daga aiki a shekarar 2016. “Wannan yana nuna qarin adadin da ya kai kashi 38.53 bisa xari na jimlar yawan rahoton badaqalar da aka tabka a shekarar 2017.” Har ila yau dai, asarar da aka tabka a bisa rahoton da aka kawao ta ragu daga naira miliyan N760 a shekarar 2016 zuwa naira miliyan 682 a shekarar 2017. A cewar Ibrahim,” hukumar NDIC ta danganta nasarar magance hakan akan matakan cikin gida da bankunan suka xauka wajen tabbatar ana bin qa’idojin da suka gindaya da shugabanci a bankunan. Ya bayyana cewa, NDIC zata binciki wasu bankuna akan sakacin su na barin aikata badaqala da yin bogi da ake zargin

wasu ma’aikatan su da hannu dumu-dumu a ciki waxanda kuma aka kora saboda aikata almundaha. Ibrahim ya ce, NDIC ta yanke wannan shawarar ce a bisa qarin samun rahoton aikata badaqalar. Ya bayyana cewa, a sashi na 35 dana 36 na dokar hukumar NDIC mai lamba 16 na shekarar 2006 da aka yi wa kwaskwarima ya buqaci bankuna dasu dinga gabatar da bayanai a duk wata akan abin da suka samu na aikata badaqala ko yin bogi ga hukumar. Ya yi nuni da cewa, duk da cewar akai matakan da bankunan suka xauka na inshorar bankunan su, don daqile ma’aikatan su daga aikata badaqala, har yanzu dai akwai buqatar bankunan su qara qarfafa sanya ido da xaukar matakai na cikin gida. Ibrahim ya bayyana cewa, wannan saboda daqile aikata alumundaha da yin bogi ta hanyar kafar internet wadda har yanzu take qara zamowa barazana ga bankuna.


22

Kiwon Lafiya

A Yau Alhamis 15.3.2018

Nijeriya Na Buqatar Sa Jarin Dala Biliyan Takwas Don Samar Da Ingantaccen Ruwa –UNICEF Daga Idris Aliyu Daudawa

Zaid Jurgi ya bayyana cewa Nijeriya na buqatar aqalla Dala Biliyan Takwas domin samar da ingantaccen ruwa. Zaid Jurgi wanda shi ne shugaban Sashen WASH dake Hukumar UNICEF, a yayin da yake gabatar da qasidarsa a wurin taron tattaunawa dangane da samar da ingantaccen ruwa, wanda ya gudana a garin Jos na Jihar Filato. Ana buqatar kamar dalar Amurka bilyan 8 ko wacce shekara saboda a samar da tsaftataccen ruwan sha a Nijeriya, idan har ana son ta cimma muradan cigaba na shida daga ciki, nan da shekara ta 2030. Shi dai wannan muradin ci gaban na shida shi ne yadda za a samar da tsafatatacce kuma isasshen ruwan shag a dukkan al’umma, wani jami’i na majalisar xinkin duniya na sashen asusun gaggawa na kulawa da yara majalisar xinkin duniya, Zaid Jurgi shi ya ya bayyana haka ranar Talata a Jos, a wani taro na aka yi domin tattauna matsalar samar da ruwan sha da kulwa da tsaftace shi a Nijeriya. Taron dai Hukumar kula da asusun yara na taimakon gaggawa na majalisar xinkin duniya, tare da haxin

cibiyar akan hakkin yara, ta ma’aikatar watsa labarai da al’adu. Mr Jurgi ya ce su kuxaxen gwamnatocin tarayya, jihohi da kuma Qananan Hukumomi zasu samar dasu, tare da haxin kan Hukumar kula da asusun yara na taimakon gaggawa na majalisar xinkin duniya, da kuma sauran wasu masu taimakawa, ta hakan ne Nijeiya zata samu taimako wajen samar da tsaftatacen ruwan shag a al’umma. Mr. Jurgi, shi babban jami’i ne vanagren tsafatace ruwan sha (WASH)a Hukumar kula da asusun yara na taimakon gaggawa na majalisar xinkin duniya, ya qara jaddada cewar Nijeriya mai yawan jama’a fiy da milyan 60, har yanzu ba tada isasshen tsatataccen ruwan sha, don haka akwi buqata ta aqara sa kuxi domin a tabbatar da an samu isasshen ruwan. Idan kuma Nijeriya ta ci gaba a yadda take na maganar ci gaban samar da ruwa, wannan ya nuna ke nan zata ci gaba da tafiya hka, haka kashi 72 ne, zai samu tsatataccen ruwa nan da shekara ta 2030. Hanyar smun tsatataccen ruwa zai kare yara waxanda basu kai shekaru biyar ba, waxanda ke mutuwa duk shekara, a cututtukan da za aiya maganinsu, saboda yawancin cututtukan adaliliin

rashin tsaftataccen ruwa ne. Mr Jurgi ya qara bayyana cewar kamar kashi 88 na cututtukan da suka shafi amai da gudawa a Nijeriya, suna fitowa daga jihohin da basu cika haruxxan samar da isasshe kuma tsaftataccen ruwan sha. Kashi 25 na al’ummar Nijeriya suna yi kashi ne a waje ba tare da ruwa mai qyau ba, y ace wannan kashin ya fi yawan jama’ar qasar Canada. Amma kuma a nata qoqarin

wajen samar da yanayin da za a daina yin kashi a waje, Mr Jurgi ya ce Hukumar kula da susun kula da yara na taimakon gaggawa, da haxin guiwa na ma’aikatar samar da ruwa, zasu fara rangadin wayar da kan jama’a akan akan muhimmancin samar da tsatataccen ruwan sha. Rabin mutane milyan xari da saba’in basu da wata dama da zasu samu tsaftataccen ruwan sha, yawanci kuma suke samarwa kansu ruwan

sha , ta hanyar gigina rijiyoyin burtsatse, ko kuma su xebo daga fadamu da kuma qoramu. Tun farko a taron Bankin duniya yayi kira kira da gwamnatin Nijeriya data a qalla zuba kashi 1.7 na kuxaxen da ake samu kafin a cire masu haraji, zuwa vangaren samar da tsaftataccen ruwan shan. Sabboda kuxaxen da take sawa yanzu abin bai kai ko kashi xaya ma bisa xari ba.

Rashin Yin Karin Kumallo Na Sabbaba Babbar Illa Ga Hanyoyin Jinin Bil’adama Daga Abubakar Abba

Binciken masana fannin lafiya ya fayyace cewa, Mutanen da suke qin yin karin kumallo, ko kuma suke sakaci wurin yin sa yadda yakamata, kama daga yin karin kumallon da abinda yakamata, ko kuma lokacin yin, sun fi daman kamuwa da cutar daskarewar manyan hanyoyin Jini da suke dakon Jini daga Zuciyar Mutum, zuwa sauran sassan jikinsa, wanda hakan kuma kai tsaye yana haifar da babbar illa da kuma sabbaba ciwon Zuciya. Binciken da Jaridar kiwon lafiya vangaren matsalolin da suka shafi Zuciya da ke Qasar Amurka su ka yi, sun gano cewa, sai manyan Jijiyoyin dakon Jinin Bil’adama sun gama daskarewa da lalacewa

da daxewa, sannan alamomin ciwon Zuciya ke bayyana. Masu binciken sun bayyana cewa, abubuwan da suka gano yayin binciken zai taimaka matuqa wajen yaqi da ake yi da cututtukan da suka danganci Zuciya, wanda ya fi kowane irin cuta laqume rayukan Bil’adama, wanda yayi sanadin mutuwar aqalla Mutane miliyan 17.7 a shekara ta 2015. Mutanen da suke qin yin karin kumallo, sun fi waxanda a kullum suke yin karin kumallon samun matsalolin rashin lafiya, kamar yadda marubuci, kuma mai yin bincike a fannin matsalolin Zuciya Mr. Valentin Fusta ya wallafa. Wannan bincike, yana qunshe da shaidun da suke tabbatar da cewa, mummunar al’adar nan da wasu Mutane

suke yi, na qin yin karin kumallo, idan har suka canza daga hakan, to za su iya kaucewa ximbin matsalolin cututtukan da ka iya kama da kuma sabbaba musu ciwon Zuciya. Binciken, an gudanar da shi ne a kan Mutane 4000, masu matsakaicin shekaru, kuma dukkanin su ma’aikata a Qasar Spaniya. Binciken, ya bibiye su har na tsawon shekaru 6, inda kowanne 1 cikin Mutum 4 suna cin Abinci mai sanya qarfi ne yayin karin kumallo, wanda yake qunshe da kaso 20% ko fiye, na abububwan da ke sanya qarfi ga jikin Bil’adama a gaba daya yini. Mafi yawancin Mutanen da aka gudanar da binciken a

kan su, kimanin kaso 70 cikin 100 suna cin abubuwan da suke xauke da abubuwa masu rangwamen saka qarfi ga jikin Bil’adama da bai haura kaso 5% ba. Kaso 3 kuma cikin su sun ce, ba sa yin karin kumallo, ko kuma su na yi kaxan kaxan, wannan kaso binciken ya gano sun fi ragowar fama da matsalolin rashin lafiya, da kuma kamuwa da nau’ukan ciwuwwukan da suke da alaqa da Jijiyoyin Jini da na Zuciya. Waxanda ba sa yin karin kumallo kwata-kwata an gano suna fama da matsalolin da suka shafi yanayin girma, da kuma qirar Qugunsu, yanayin nauyi da qiban su, da hauhawan jini, da kuma abubuwan da suke sabbaba ciwon Sukari. Akwai bincike masu yawa

da aka gabatar a baya da suka nuna cewa, yin ingantaccen karin kumallo yana da alaqa kai tsaye da ingancin qoshin lafiya, kamar yadda wasu binciken suka nuna cewa, rashin yin karin kumallon suna sabbaba manyan matsaloli da cututtukan hanyoyin jinin bil’adama. Farfesa a fannin kimiyyar magunguna na Jami’ar Kalifoniya da ke Qasar Amurka, Mr. Prakash Deedwania, ya tabbatar da cewa, duk da cewa mutanen da ba sa yin karin kumallo ba su fiye fama da matsalar cutar qiba ba, amma dai rashin yin karin kumallon yana da matuqar illa ga kiwon lafiyar bil’adama. “Karin kumallo, shi ne Abinci mafi muhimmanci da Dan’Adam ke ci a tsawon rana”.


A Yau Alhamis 15 Ga Maris, 2018 (26 Ga Jumada Thani,

kiwon lafiya 23

Majalisa Ta Buqaci Gwamnati Ta Zartas Da Dokar Ta Vaci A Vangaren Lafiya Daga Idris Aliyu Daudawa

Majalisar dattawa ta yi kira majalisar zartarwa da cewar data aiwatar da dokar ta vaci akan al’amarin da ya shafi harkar lafiya, saboda abin ya vaci ta wancan vangaren. Wannan qoqarin yin hakan ya biyo bayan da aka amince da shawarar Sanata Sulaiman Hunkuyi, wanda ya gabatar da qudurin mai taken ‘’Yadda al’marun da suka shafi harkar lafiya ke neman agaji’’ ranar Talata. Sanata Hunkuyi ya jaddada cewar hakan tana faruwa ne saboda saboda lalacewar abubuwan more raruwa a asibitocin gwamnati, kamar rashin isassar wutar lantarki, rashin isasshen ruwa, abin da ke sa a samu shiga wani yanayi na rashin tsafta, wannan kuma shi ne zai sa a samu hanyar da wasu cututtuka za su yaxu a asibiti. Ya ce bugu da qaru majalisar ta lura cewar, akwai wasu kayayyakida ake amfani dasu a asibiti kamar MRI, CT, Scan Ultrasound, da dai sauransu. Waxanda ake amfani dasu, sun kasance ko dai basu amfani, ko kuma basu da yawa.

‘’Shi yasa majalisar ta damu saboda yadda al’amuran suka lalace, abin ba zai iya jan hankalin wasu qwararru ta harkar lafiya da sauran wasu , suke barin Nijeriya suna zuwa asibitoci masu zaman kansu, ko kuma su je qasashen waje. Majalisar ta qara nuna damuwarta akan irinhalin sukurkurcewar dada asibitocin gwamnati suka yi, dalilin da kuma ya sa

wasu marasa lafiya, ke zuwa qasashen waje, kamar yawon buxe idanu, da kuma wani na yadda ake fitar da kuxaxe milyoyi da yawa, saboda neman lafiya duk shekara. Ko dai aje Yurof, Amurka, Asiya, kai har ma wasu qasashen yammacin Afirka, bayan mu kuma nan muna da asibitoci. ‘’Majalisar ta ce, saboda yaddav asibitocinmu suke wato halin shi yasa suka kasance basu da wani

amfani, wannan kuma ba qaramin ci baya baye ga al’ummar qasa.’’ Wannan dalilin shi yasa wani qiyasin qididdiga da ya fito daga ma Hukumar kula da asusun gaggawa na yara na majalisar xinkin duniya’, wanda ya nuna cewar qasar Nijriya ita ce ta biyu a duniya, da take rasa kusan yara 2300 waxanda basu kai shekara biyar ba, da kuma mata 145 waxanda suna iya

haihuwa, suke mutuwa kullum. Da suke nuna amincewarsu dangane da ita shawarar majalisar ta yi kira da shugaban qasa Muhammadu Buhari, da ya zartar da dokar ta vaci a vangaren lafiya. Majalisar har ila yau ta yi kira da majalisar zartarwa data aqalla gyara asibitin gwamnati daga cikin sassa shida na qasa, a kasafin kuxin wannan shekara ta 2018.

Yin Amfani Da Tramadol Don Qarfin Maza Na Da Illa, Inji Masana Daga Idris Aliyu Daudawa

Wanda ake runtuva wanda kuma qwararre ne a fannin harhaxa magunguna Dokta Clever Okeke ya ja kunnen mutane da cewar su daina amfani da Tramadol saboda, domin su qara yin sha’anin kamar yadda suke so, ko kuma su xauki lokaci basu biya buqatarsu ba, yana iya samar da wata damuwa, ko kuma hali wand aba san mutum da shi ba. Okekee ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Nijeriya a Lagos ranar Litinin, cewar wasu matasa, da kuma manya suna yin amfani da Tramadol, idan

suna byuqatar masu jin daxi kamar yadda suke so. Ko kuma kada su yin biyan buqatar ne cikin sauri Kamar yadda ya bayyana ko da yake dai Tramadol ya kamata ayi amfani da shi ne ta mafanin zafin ciwon, amma kuma ana amfani da shi ne ta hanyar da bata kamata ba. Saboda na samun shifa wani hali bayan an yi amfani da shi. ‘’Shi Tramadole yana cikin magungunan da suke cikin ajin analgestic Opiod Analgesis, saboda ana mafani da sune saboda zafin ciwo ko kuma kiximewa, daga qarshe da abubuwan da suke yi da basu dace ba.

‘’Babbar allura ce anakgesic ana kuma amfani da ita ga babbar cuta da take damunwanda ya kamu da ita sosai.’’ Amma kuma abin da mutum zai lura shi ne saboda yadda take samar da matsala wani lokaci,saboda opiod da kuam euphoric, wannan kuma wani vangare ne ne yadda take samar da abubuwan da basu kama ce ba. Tana sai mai amfani da ita ya ji lamar shi ya hakicci kan shi. Okeke ya bayyyana cewar wasu daga cikin masu amfani da shi wannan magani suna iya samun sha’awa ta bayan

sun kammala amfani da shi maganin, shi yasa sai su yi sha’awar cigaba da mafani da shi. Kamar yadda wani qwararre a harkar harjaxa magunguna abin da aka yarda da a sha shi ne 50mg zuwa 100mg, ana kuma iya shan 200 mg , idan rashin lafiya ya yi qamari. Duk kuma wani abin da ya wuce 200mg na iya samar da matsala. Okeke ya ci faba da bayanin saboda ita Koken ba a iya gane ta shi yasa, shi yasa mutane ke shan maganin da ya wuce qima, domin su samarwa kansu abin da suke so. ‘’Bai kamata kawau

domin wasu na jin daxi sai a mayar da abin ya zama kamar na wasa ba, ba za a samu jinkirin rashin biyan buqata ba,. Ya qara jan hankalin mutane cewar idan aka sha maganin ya wuce qa’ida hakan yana iya zama sanadiyyar samun wasu matsalolin da suka shafi lafiyar jiki. Don haka ya yi kira ga iyaye su riqa kula da yadda ‘ya’yansu ke tafiyar da rayuwarsu, su riqa lura da wasu alamu da suka haxa da daxewa ana barci, rashin yin wani aiki na kirki, da kuma wani baqon halin da ba a saba da shi ba.


24 Talla

A Yau Alhamis 15 Ga Maris, 2018 (26 Ga Jumadal Thani, 1439)


25

A Yau Alhamis 15 Ga Maris, 2018 (26 Ga Jumada Thani, 1439)

Kimiyya

Dala Miliyan 500

ne adadin kuxi Nijeriya ke kashewa duk shekara waurin safarar xanyen man fetur da wasu sinadaran da ake amfani da su a sashen sinadarari da magunguna

Shagunan Siyayya Ta Shafin Intanet Daga Bakir Muhammad

A yanzu a duniya shagunan siyayya na shafin intanet (Online Stores) su ake yayi , sun shahahara sosai a duniya, akwai manyan shagunan siyayya da suke siyar da ko wanne irin kayan siyayya in dai ba haramtattun kaya bane, misali akwai waxanda suka fi shahara irinsu kamfanin Amazon, Ebay, Walmart, Alibaba da sauransu, kusan duk abinda kake buqata na daga kayan wuta, kayan sawa, littafai, kai harda na’urori, manyan injina da ababen hawa kamar babur, keke da mota zaka iya samu a waxannan shagunan na shafin intanet. Tsarin siyayya a shagunan intanet yana da matuqar sauki, maimakon mutum ya tafi wata qasa domin yin siyayyar kayayyaki, kawai zai duba shafin shagon intanet ya duba abinda yake sha’awar siya, ya duba yanayin qarkon abun da kyaun shi, sannan ya duba farashin in yayi mishi sai ya shiga adaxin kayan da yake buqata, sai yasa adireshin da yake buqata a aiko mishi da kayan da ya siya bayan wasu ‘yan kwanaki, wani abun sha’awa shine zaka iya biyan kuxi ta bankin ka a take ko kuma ka zavi ka biya kuxin kayan in sun iso gareka. A nan gida Nijeriya ma akwai shagunan siyayya na intanet da suke kawo kayayyaki masu qarko da rahusa, waxanda zasu iya kawo maka duk abinda ka siya har kofar dakinka, ko wajen aiki ko sana’arka, zaka iya zavar biyan kuxi a take ta hanyar banki ko ka zavi biya bayan kayan sun iso gareka, wani abun sha’awa shine zaka iya fasa siyan abu ko da bayan an maka odarshi gidanka ko wajen sana’arka, sannan babu wata matsala da zaka fuskanta a yin hakan, ko da ka biya kuxi to za’a dawo maka da kuxinka, muddin abun bai maka ba har canja maka ana iya yi. Yanzu zamu duba wasu shaguna da suka fi shahara anan gida Nijeriya, waxanda suka fi kawo kayayyaki da ake yayi a duniya, manyan wayoyin hannu ne, kayan sawa na maza da mata ko man shafawa da turare ne, ko na’urar kwamfuta ce duk dai gasunan akwai su a farashi mai rahusa, kuma mafi yawan kayan suna da inganci sosai.

1-Jumia: kusan sunfi ko wanne kantin siyayya na intanet shahara a Nijeriya da wasu qasashen makwobtan Nijeriya, suna shigo da duk wasu nau’in kaya da ake bukata a cikin qasar nan, amma sunfi shahara da shigo da kayan sawa da kuma kayan wuta waxanda suka hada da wayoyin hannu, nau’rar kwamfuta, talbijan na zamani, da sauransu, wannan kantin na Jumia yana da arahar kaya sosai sannan suna kawo wa mutum odar kayanshi cikin kwanaki biyar a duk birnin da yake a faxin Nijeriya da wasu qasashen makwobta ma, wato litinin zuwa Juma’a sannan kuxin odar bai taka kara ya karya ba, bayan haka akwai manyan shagunansu da mutum zai iya ziyarta domin karbar kayan da yayi oda. Zaka iya ziyartar shafinsu ta jumia.com.ng 2-Konga: suma kamar Jumia ne duk da shafin jumia ya ruga shafin konga fara kasuwancin intanet, amma fa suma ba tayar baya bane a harkar kasuwancin intanet, wani abun sha’awa da wannan shafin na konga shine suna da abokan kasuwanci da suke

iya daura kayayyaki a shafin konga ta yadda in mutum yana buqatar wani abu a konga amma basu da shi to sai kawai ya duba a shafin abokan hulxar konga, sannan akwai bambanci farashi daga shafi zuwa shafi wannan shi zai ba masu sha’awar siyan kayayyaki damar zaven shafin da ya fi burgesu. Zaka iya ziyarta konga ta nan konga.com.ng 3-Kaymu: su ma dai kamar sauran shagunan, amma dais u sun fi siyarda wayoyin hannu, na’urar kwamfuta da kayan sawa na maza da mata, wani abun sha’awa da wannan shafin na kaymu shine yadda suka samar da damar mu’amala ta kut da kut tsakanin masu siyarwa da masu siya, wato zaka iya neman shawara daga masu siyarwa akan duk nau’in kayan da kake son siya, sannan in kayan da ka siya xin yana da wata matsala ba zaka sha wahala ba wajen yin Magana da masu siyarwa. Ana iya samun shafin ta nan kaymu.com.ng 4-Slot: shima wani shafi ne da ya shahara da siyarda kayayyaki nau’i nau’i, duk sun

fi shahara a wayoyin hannu, na’urar kwamfuta da sauran irin waxannan kayayyakin wutan, shafin slot suna da alaqa mai kyau da masu siyan kayayyaki daga garesu, ta yadda kana buqatar abu to cikin qanqanin lokaci zasu yi kokarin kawo maka abunda kayi oda ba tare da wani vata lokaci ba, sannan suna arhar kayayyaki sosai, kudin tuquicin odar kayayyakin su ma bashi da wata tsada, daxin dadawa suna ba wa mutum dama ya gwada abunda ya siya in yana da wata matsala ko naqasu sai a canja mishi a take ba tare da ya qara sisin kobo ba. Ana iya samunsu a shafin na intanet wato slotlimited.com Akwai qarin wasu shagunan amma tabbas a iya waxannan shagunan guda huxu mutum zai iya samun kusan duk abinda yake buqatar siya a sauran shagunan intanet da ake da su a faxin duniya, sannan siyan kayayyaki a waxannan shafukan na cikin gida yafi sauki sosai fiye da siyansu a shagunan qasashen waje, akwai matsaloli da ba za ka rasa ba a tattare da shagunan, a qaro na gaba in Allah yaso zamu duba matsalolin.


26 TATTAUNAWa

A Yau Alhamis 15 Ga Maris, 2018 (26 Ga Jumada Thani, 1439)

‘Idan Aka Ba Al’umma Ilimi An Samar Masu Sana’a’ Ci gaba daga shafi na

18

Ganin kana da irin wannan ra’ayi na canja tunanin matasa a yankin Arewa musamman na muhimmantar da rayuwarsu akan ilimi. Shin yanzu kai me ka ke yi aka? Da farko mu dai ba gwamnati ba ne, amma a matsayina na matashi mai kishin Arewar yasa na vullo da wannan gidauniya ta AlAmin Foundition. Hanyar farko da na fara xauka ita ce waxanda ke aiki a qarqashina na bayyana masu muradina akan kowani mutum da ke tare da ni ya zama wajibi a cikin ‘yayansa koda bai da ikon xaukar xawainiyar su gaba xaya ya zamana ya ware wasu daga cikin ‘yayansa ya muhimmantar da basu ilimi tun daga matakin farko har qarshe. Kan haka da muka kafa ita wannan gidauniyar muka umurci su ba mu ‘yayansu dan kulawa da iliminsu, ta yadda nan gaba su yaran da muka bai wa kulawar zasu iya zama wani abun alfahari a rayuwa nan gaba, ta yadda tun daga karatunsu a matakin farko har zuwa jami’a sun mayar da hankali akan kulawa da su wanda fatar mu idan mun samu tsawon rayuwa har aiki zamu iya samar masu. Zuwa yanzu kana da qididdiga akan yaran da gidauniyar ke kula da iliminsu? Tau, kamar yadda na faxa ma ba mu tsaya akan yaran ma’aikatan ba, muna anfani da ma’aikatan, ta yadda su da keda damar shiga cikin unguwanni idan sun ga wata Iyali da ke buqatar kulawa sai su gabatar mana, muna da waxanda su aikinsu kuma bincike rahotannin da ake kawo mana da irin gudunmawar da zamu bayar. Akan wannan qididdigar yanzu muna da yaran da muke kulawa da karatunsu a qallan su xari da hamsin a matakin faramare da sakandare har jami’a. Mai karatu zai yi tsammanin duk waxannan xaliban suna karatu ne a makarantar ku ta Al-Amin, shin in na faxi hakan dai-dai ne? Akwai waxanda ke karatu a nan haka ne, sannan akwai wasu kuma a wasu makarantun na daban. Kamar a makarantun da muke tallafa ma wa, irin Hill-Top Secondry School da GGSS makarantar fada da ke nan minna da kuma Maryam Babangida Sceince School ka ga duk makarantu ne da ke ingantaccen tsari wanda bayan xaukar nauyin wasu xalibai su kansu

•Dakta Muhammad Babangida.

makarantun muna ba su gudunmawa. Idan ka koma a vangaren jami’a kuma muna da xalibai a jami’ar Uthman Xanfodio na sokoto da Jami’ar Bayero ta Kano haka kuma akwai wasu makarantun gaba sakandare da muke da xalibai duk wannan na daga cikin tsare-tsaren mu na inganta ilimi ‘yayan marasa qarfi. Kenan kana nufin akwai wasu kuxaxe da ku ke warewa dan yin waxannan ayyukan? Kowace shekara akwai kuxaxen da muke warewa na ayyukan fanfunan vurtsatse, taimakawa jama’a da kuma xaukar nauyin marasa qarfi. Bisa la’akari ire-iren waxannan qungiyoyin suna ta’allaqa ne da taimakon wasu qungiyoyin waje. Mene ne fatarka nan gaba akan ita wannan gidauniyar? Fatana dai itace gaba kaxan kamar shekaru biyar zuwa goma qungiyoyin da ke turai su zo su san irin ayyukan da wannan gidauniyar ke yi. Kuma babu yadda zasu san da irin ayyukan mu ba dole sai mun fito mun gayawa duniya irin ayyukan da muke yi, ta haka ne zasu samu amincewa da mu da zasu iya xauko kuxaxensu su ba mu dan cigaba da wannan aikin da muke yi, koma su qara mana wasu ayyukan da su ke son mu yi saboda mun riga mun nuna masu irin abubuwan da muke muradi ga rayuwar al’umma. Idan mun dubi irin tafiyar da ake yi yau, wace shawara za ka bai wa gwamnati musamman ta fuskar ilimi. Kullun abinda muke kula da shi a Arewa shi ne ba a mayar da hankali akan ilimi yadda ya kamata, idan ka dubi sakamakon jarabawar WAEC da NECO sai ka tarar Arewa ba sa samun cigaba, kusan

kullun baya ma muke yi. Sai ka tarar wata jihar ma yaran da zasu iya tsallakewa ba su da yawa da suke iya tsallakawa yadda ake so. Sai ka tarar a cikin yara dubu biyu waxanda zasu iya samun nasara ba su wuce mutum goma, ka ga wannan ba abu ne da za a ce muna jin daxinsa ba. Kuma abinda zai xaure ma kai, kullun sai a riqa ware kuxi ana gina makarantu, ayi wa makaranta kwalliya, amma karatun kuma ba a mayar da hankali akai. Yadda yaro zai zo yau, gobe, jibi har ya samu ya kammala karatun da yake yi, ba lallai ba, kuma iya abinda gwamnatin zasu iya yi ke nan, to mu Iyayen me muke yi. Gwamnati ya kamata su zauna da Iyayen su san muhimmancin karatu, in ba su san muhimmancin karatun ba koma me ita gwamnatin za ta yi koda sabbin makarantu za a riqa ginawa kullun ba zai yi tasiri ba, dole a zauna da Iyaye ana nuna masu illar rashin ilimi ga yaro mai tasowa shi ne abu na farko da ya kamata ita gwamnati za ta yi. Idan an samu yardar iyayen, sai a qirqiro dubaru misali kamar tsarin ilimi kyauta da ake tafiya akai, ban da hali amma na san gwamnati na nan za ta xauki nauyin yarona ba sai na biya komai ba. Ya gwamnati za ta haxa qididdigar yaran da ke son ilimin kyautar, in samu qididdiga to su tabbatar zuwansu, kayan karatunsu da su malaman da zasu koyar xin komai na tafiya yadda ya kamata. Shi me koyarwan a ba shi haqqinshi ya ji daxin zuwa koyarwar, yaran duk abinda suke buqata na abinci har yadda zasu taso daga gida zuwa wannan makarantar gwamnati ta kula da hakan. Idan mun yi la’akari da irin halin da matasa ke

ciki yau, duk yadda ake son kulawa ko basu ilimi ba zai yi tasiri ba dole sai sun samu kwava. Yau rashin kwavar nan ko kuma gurvataccen yanayin ya jefa matasa da dama cikin harkar shaye-shaye. Shin ina mafita. Shaye-shayen wani bala’i ne da yake ko ina a Arewa, yawanci ‘yan siyasa suna da laifi a nan, ana anfani da matasa ana ba su abinda bai taka kara ya karya ba don su yi shaye-shaye su quntata ma wani, ko xan adawarsu ne a siyasa da sauransu ka ga hakan bai da ce ba. Na farko ‘yan siyasa su daina anfani da yaran mu, na biyu yaranmu a nemar masu abin yi, ya zama na gwamnati ta vullo da wani abu da zai iya taimakawa matasa ta yadda zasu iya riqe kawunansu. Samar masu madogarar rayuwa zai taimaka su wajen faxawa cikin miyagun xabi’u, wanda rashin hakan ba qaramin illa zai cigaba da jawo wa ba. Gaskiya ‘yan siyasa ne kan gaba wajen gurvata matasa masu tasowa, mu kuma da iyayen mu ya kamata mu mayar da hankali, me yaran mu ke ciki, mun ji muna zuwa muna nema amma ya zama wajibi mu zauna da yaran mu, mu kusance su dan mu san irin rayuwar da suke yi in ba ma nan. Mu da iyaye mata ya zama wajibi mu samar da lokacin da nazartar halin da iyali ke ciki, ta haka na ke ganin za a iya rage waxannan abubuwan. Ko akwai wani shiri da ku ke yi na wayar da kan matasa akan shayeshaye? Zuwa yanzu ba mu fito da wani shiri akan hakan ba, amma tunda abu ne da ya shafi al’umma dole mu yi wani abu akai.


rahoto 27

A Yau Alhamis 15 Ga Maris, 2018 (26 Ga Jumada Thani, 1439)

An Bankaxo Naira Biliyan 136 Na Kuxin Shiga Da NCAA Ta Qi Ayyanawa

Daga Abubakar Abba Wani qwararren akan harkar sufurin jiragen sama kuma wakili a taron tattanuna na masu ruwa da tsaki akan harkar (ART),Kaftin John Ojikutu mai ritaya ya fasa kwai, a ya yin da ya yi kira da a gudanar da bincike akan hukumar zirga-zirgar jeragen sama ta qasa (NCAA). Ya kuma zargi hukumar akan rashin ayyana kuxin shigar da ta samu akan tikitin da aka sayarwa fasinjoji da kayan da aka yo jigilar su don sayarwa, inda ya yi iqirarin cewar, hankan ya janyo an mayar da wasu hukumomin hada-hadar jirage a qasar nan kasa amfana. John Ojikutu a cikin qasidar sa mai taken: “Gudanar da bincike akan hukumar NCAA na kashi biyar bisa xari akan tikitin fasinjoji da kayan da aka yo jigilar su a jiragen don sayarwa da ya baiwa wakilin mu” a ranar Talatar da ta gabata, ya zargi hukumar NCAA akan qin ayyana jimlar tikitin fasinjojo, inda hukumar ta ajiye kuxi a gunta ta akan harmtacciyar hanya. Ojikutu ya ci gaba da cewa, “hakan abin takaici ne akan yadda hukumar taqi ayyana waxannan kuxaxen da take ci gaba da kula dasu tare da haxin kan ‘yan kwangilar ta har tsawon shekaru goma zuwa yau. Ya ci gaba da cewa,” a taron manema labarai da a cikin watan Fabirairun 2017, hukumar NCAA ta fitar da rahoto wanda ya nuna cewar, kuxin shiga da aka samu ta hanyar sayar da tikiti kawai a cikin shekarar 2015 da shekarar 2016, sun kai yawan

naira biliyan 385 da kuma naira biliyan 330. Ya qara da cewa, “wannan adadin, ba’a kasafta su ba don tantance kuxin shigar da aka samu na hada-hadar qasa da qasa da kuma na cikin gida ba.” Ojikutu ya qara yin nuni da cewa, “har ila yau wannan adadin suna haifar da ruxani idan aka kwatanta da bayanan da hukumar ta NCAA da kuma na DATR suke dashi na kashi biyar bisa xari na kuxin tikitin da aka sayarwa da fasinjoji masu fita qasashen qetare da kuma waxanda suke yawo a cikin qasar nan kawai, musamman daga watan Janairu zuwa watan Disambar 2016, wanda ya kai yawan naira biliyan 15.1 da kuma dalar Amurka miliyan 23.5 ko kuma jimlar naira biliyan 23.3. Ya yi nuni da cewa, “idan naira biliyan 23.3 aka samu akan kasha biyar bisa xari na sayarwa da fasinjoji tiliti kawai a shekarar 2016 da hukumar NCAA da kuma DATR suka yi, a saboda haka bazai kai naira biliyan 330 kamar yadda hukumar NCAA ta sanar a cikin watan Fabirairun shekarar 2017 ba a taron manema labarai da hukumar ta gudanar, amma akwai bambancin alqalumma a tsakanin naira biliyan 466 da naira biliyan 136.” Ya qara da cewa, a dai wannan taron manema labaran da hukumar ta gudanar a shekarar 2017, hukumar NCAA ta samu kuxin shiga na fasinjoji da suka kai adadin naira miliyan 11.4 da kuma naira miliyan 11.3 a shekarar 2015 da kuma a shekarar 2016, haka wannan adadin shi ma yana da rikitar da

kai idan akayi la’akari da adadin naira miliyan 15.2 da kuma naira miliyan 14.2 duk a cikin wannan lokacin da hukumar kula da filayen jiragen sama na qasa (FAAN), mai sanya ido ta farko akan fasinjoji a xaukacin tasahar tashin jaregen sama da saukar su dake qasar nan. Ya bayyana cewar hukumar NCAA ta kuma samu kuxin shiga har 3,272,331 a cikin wannan shekara na jigilar fasinjoji zuwa qasashen waje, inda kuma adadin hukumar FAAN yake nuna an samu naira miliyan 4.30 da kuma naira miliyan 4.20.” Ya ce bugu da qari,“duk a wannan lokacin adadin kuxin jigilar fasinjojo ta cikin gida hukumar ya kai naira miliyan 8.1 da kuma naira miliyan 8.0, inda kuma hukumar FAAN, ta samu naira miliyan 10.2 da kuma naira miliyan 10.9 duk a lokaci xaya. Ya yi nuni da cewar, akwai banbanci matuqa na sama da miliyan huxu a tsakanin FAAN da kuma NCAA akan yawan adadin fasinjojin da aka yi jigilar su a cikin kowacce shekaru biyu, kuma akai qarin banbanci na sama da naira miliyan xaya na fasinjojin da aka yi jigilar su zuwa qasashen waje, kuma wannan hukumar NCAA ta bayyana cewar ta samar da kuxin shiga na jigilar fasinjo da ya kai yawan naira biliyan 385 da kuma naira biliyan 330 a cikin shekarar 2015 da shekarar 2016, inda shi ma wannan adadin, yanada rikitarwa kuma yanada alamar tambaya. Da aka nemi jin ta bakin mai magana da yawun hukumar

NCAA Mista Sam Adurogboye, ya yi fatali da zargin na Kaftin Ojikuti,inda ya ce, iqirarin nasa ba zai tava savuwa hukumar (NAS) ta rikita ma’adanar bayanan ta a bisa yananan dake qasa a yanzu ba. A saqon karta kwana da wakilin mu ya turawa Mista Sam Adurogboye ta wayar sa ta tafi da gidan ka ya ce, “wannan iqirarin ba haka bane kuma bazata tava savuwa hakan ta kasance ba”. Ya ci gaba da cewa, a cikin littafin ajiya na hukumar na farko, ako yaushe kwamitoci da ban-da-ban na Majalisar qasa suna tantance shi ta hanyar turo masu binciken kuxi na tarayya daga ma’aitar Sufurin jiragen sama da kuma Akawu mai binciken kuxi na tarayya.” Ya ce, “na biyu kuma, NCAA da NAMA da FAAN sunada tsayayyen kwamiti da yake yin zama a dukkan lokuta don yin dubi akan adadin akan yawan jiragen da suka yi jigilar fasinjoji.” Acewar sa, “a saboda hakan adadin mu na kuxi daidai suke babu wani canji.” Ya bayyana cewar, zirga-zirgar jirage ana yinta ne akan adadin jiragen da suka yi jigilar fasinjoji akan yawan jiragen da aka samar, a saboda haka babu wani cajin kuxi da ake tunani.” A qarshe ya bayyana cewar, yanada kyau da irin wannan zarge-zargen suke tasowa domin kuwa akwai waxanda suka nemi kwangilar da babu ita a qasa domin tuni an bayar da kwangilolin shi ne a yanzu suke bijirowa da irin wannan zargezargen don su vatawa hukumar suna.


28

Tauraruwa Mai Wutsiya

A Yau Alhamis 15.3.2018 08174743902 wutsiya2019@gmail.com

Mahaukaci Ya Kashe Xaliban Firamare Biyu A Ogun Daga Khalid Idris Doya A ranar Litinin ne wani da ake zargin yana fama da tavin hankali ya kashe wasu xaliban Firamaren Saint John’s Anglican Primary School da ke Ogodo a jihar Ogun. Su biyu mace xaya na miji xaya, xaliban dukkaninsu ‘yan qasa da shekaru huxu sun gamu da ajalinsu ne a sakamakon sharva musu adda da muhaukacin ya yi. Rahotonnin sun zo cewar mahaukacin ya shigo habarar makarantar ne daga dajin da yke kusa da makarantar xauke da sharveveyar adda a tattare shi inda ya iske xaliban a lokacin da suke yin karin kumullon samun abun jefawa a bakin salati da sauran xaliban. Muhaukacin dai ya arci na kare wajajen qarfe 11:15 na safiya bayan da ya kammala aikata mummunar ta’asar tasa. A sakamakon sararsu da wannan addar, muhakacin ya bar xaliban cikin jinni kafin kiftawa da bismilla. Wata majiya ta shaida mana cewar wannan makarantar babu kofar kullewa domin tantance mai shigowa. Kamfanin dillacin labarai ta Nijeriya ta bayyana cewar iyayen xaliban sun hanzarta yi wa makarantar kwanya domin kwashe ‘ya’yansu cikin gaggawa, inda kuma jami’an tsaro suka

fantsama gudanar da binciken su kan lamarin. A hirarsa da manema labaru a garin Abeokuta, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Mr Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da aukuwar wannan lamarin. Oyeyemi, har-wa-yau, ya kuma qara baiwa ‘yan jaridan qarin bayani kan hakan har ma da sunayen xaliban da suka mutu a sakamakon farmaqin da muhaukaci ya kai musu a makarantarsu, xaliban kamar yadda mai magana da yawun ‘yan sandan ya shaida su ne Mubarak Kalesowo da kuma Sunday Obituyi, dukkaninsu xalibai ne da basu haura wa shekaru huxu ba, kuma suna ajin qaramin aji ne na neman ilimin firamaren. Kakakin ya ce “Lamarin ta auku ne da misalin qarfe11:30 na safe, a lokacin da xaliban suke yin huxun karin kumullo na rana. Yaran suna kan yin wassaninsu,” “Mutumin wadda muke tsammanin daga cikin daji ya fito, ya cakwami xalibai biyu kuma sun mutu, nan take ya fita da xan Karen gudu,” “Wadda ya yi kisan ana tsammanin mahaukaci ne, mun nemi jin bayanin ko shi haifafen wannan wajen ne, amma har zuwa yanzu ba mu samu amsar hakan ba,” “Mun xana tarkokinmu domin mu tabbatar da kamo shi. Maganar

da mu zamu gamsu da ita shi ne, sai mun kamosa mun kaisa ga likitoci su ne kaxan za su tabbatar mana da cewar shi mahaukaci ne ko kuma ba mahaukaci ba ne,” Ya qara da cewa, “Ina tabbatar muka za mu kama shi, yanzu haka da na ke magana da ku,

aka bayyana ance xalibin yana amatsayin xalibi na ajin qarshe ne a tsangayar ilimin kimiyyar kwamfuta a jami’ar. Adams xin sun bayyanashi a matsayin haziqin xalibi ne mai sakamakon jarabawa na mataki mafi darajawa (first class) kuma sunce ganin qarshe da suka yi wa Adams shi ne na ranar alhamis inda ya miqa wani aiki da aka basu bayan ya

kammala shi. Saboda ganin ya xauki kwanaki ba’a ji xuriyarshi ba sai aka yanke shawara suka valle qofar xakinsa inda suka taras ya rataye kanshi ya mutu. Kakakin hukumar jami’ar Micheal Osasuyi ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace alokacin da mahaifin Adams xin ya kawo masa ziyarane aka lura aka gane ce

shugabanmu da ke kula da yankin da kuma DPO na Abigi dukkaninsu sun tashi tsaye zuwa wannan yankin domin ganin yadda za a yi a kamo wannan. don haka za mu tabbatar da kamo shi,” In ji Mai magana da yawun ‘yan sandan.

Wani Xalibi Ya Kashe Kanshi A Benin Daga A. A. Masagala, Benin Hukumar gudanarwa ta jama’ar gwamnatin tarayya (Uni Ben) daka garin Benin na jihar Edo ta tabbatar da mutuwar xalibinta da akace ya kashe kansa da kansa . Kuma an tsinci gawar xalibin mai suna Adams ne axakin kwanansa dake u Ekosidi na qaramar hukumar ovia ta kudu kuma kamar yadda

wa bayanan atsawon kwanaki sai abokansa da sauran ‘yan uwa suka je suka valle qofar xakinsa inda suka ganshi arataye. Don kaucewa sake faruwar irin wannan agaba Osasuyi ya buqaci xaliban jami’ar dasu daure su dinga yin magana aduk lokacin da suka fuskanci wata matsala ko damuwa acikin harkokinsu na rayuwa a makaranta ko a gida.

Yadda Masu Gadi Suka Kashe Wata Jami’ar Soja A Edo Daga Bello Hamza

Hankali ya tashi a layin Ugiagbe da ke garin Ugbor a qaramar hukumar Oredo ta jihar Edo yayin da mai kula da lafitar wata jami’ar soja mai muqamin Manjo tare da wasu masu gadi suka kashe sannan suka qona gawar ta. Majiyarmu ya muna cewa Manjo Ajuya na aiki ne a yankin Kudu maso Kudu ta dawo ne daga wani tafiya dai-dai karfe 9;30 na dare in da mai kula da lafiyar ta bahaushe ya tarbe ta daga baya kuma ya dirar mata da duka, daga baya wasu masu gadi su 8 suka haxu suka ci gaba da duka da saranta har ta mutu. Majiyar tamu ta ci gaba bayyana mana cewa, bayan sun kashe ta ne sai suka watsa mata man fetur suka kuma banka wa gawar wuta, suka kuma sace kuxaxe da kwanputan ta da gwalagwalan ta, bayan sun gama

mugun aikin nasu ne suka sanar da jama’a cewa an samu hatsarin gobara ne ya kona shugaban masu har lahira, da jama’ar da suka taru ana qoqarin kawar da gawar zuwa asibiti an lura masu gadin nata na qoqarin kwashe abin da suka sata zuwa wani kangon gini. Daga baya ‘yansanda daga yankin Ugbor suka iso inda suka kama mai gadin ta tare da waxanda suka aikata kisan. Wata mazauniyar unguwan da bata buqatar a ambaci sunan ta, ta ce “Wata mata ce ta sanar da ni cewa matar ta qone a kan gadon ta, mun shiga muka ga gawar a qasa, daga baya wasu makwabtan ta suka gaya mani cewa, masu gadin ta ne tare da haxin bakin wasu hausawa masu gadi suka qona ta bayan sun caccaka mata wuqa” “Sun kwashe kayayyakin ta da kuxi har Naira 600,000 suka kuma kashe ta daga baya suka qona gidan gaba xaya”

“Da farko mutane na tunanin sigari ne ya kawo gobaran amma da ake fito da gawan sai wani makwabcin ta ya lura da yadda gawar ya ke ya kuma lura da xaya daga cikin masu gadin na qoqarin wurga wasu kayayyakinta ta katanga, nan take ya sanar da jama’a aka bi shi aka kuma kame shi” Lamarin ya tayar da hankalin mutanen unguwan, yayin da masu gadin da ke unguwan suka gudu bayan jin labarin mutuwar jami’ar sojan. Da majiyar namu ya ziyarci gidan ranar Litini ya lura da wani vangare ya qone, gidan kuma na kulle, an dai fahinci cewa, marigayyar na zaune ne ita kaxai yayin da yaran ta ke karatu a qasashen waje, wani makwabcin gidan ya nuna takaicinsa a kan yadda mai gadi zai kashe mai gidansa ba tare da wani hatsaniya tsakaninsu ba. “Ba zamu yarda da masu gadi hausawa ba a wannan unguwan

daga yanzu” in ji shi Kwamishinan ‘yansanda jihar Mista Johnson Kokumo ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma ce tuni aka kama su, za a kuma gabatar da su gaban kotu da tuhumar kisan kai da zaran an kammala bincike. Sai dai ya ce, ba zai iya tabbatar da ko marigayyan Manjo ce a rundunar sojojin qasar nan. Ya ce, dukkan alamu na nuna cewa, kisan kai ne, ‘Masu gadin sun kashe ta ne daga baya suka banka wa gidan wuta da nufin voye aika-aikan su. “Sai dai shugaban rundunar sojojin Nijeriya kaxai ne zai iya tabbatar da cewa ko ita Manjo ce ko a a, amma a gare ni ita ‘yar Nijeriya ce kawai” Qoqarin jin ta bakin jami’in watsa labarai na Brigade ta 4 Kaptain Mohammed Maidawa ya ci tura don kuwa ya qi amsa waya bai kuma mayar da amsan sakon kar ta kwana da aka aika masa ba.


29

A Yau Alhamis 15 Ga Maris, 2018 (26 Ga Jumada Thani, 1439)

Qasashen Waje Faransa Za Ta Gana Da Qasashen Nijar Da Algeria Kan Tsaro

Tare da Rabiu Ali Indabawa 08069824895

Qungiyar Qasashen Turai Ta Jera Wasu Qasashe Cikin Yankunan Dake Halalta Kuxaxen Haram Qungiya qasashen Turai ta sanya sunanyen Bahamas da Tsibirin Virgin Island mallakar Amurka da Saint Kitts da kuma Nevis cikin Yankinan dake taimakawa attajirai kaucewa biyan haraji. Taron ministocin kuxin kungiyar ya kuma bayyana cire sunayen Bahrain da Tsibirin Marshall da Saint Lucia daga cikin jerin

A yau jiya Laraba ne ministan cikin gidan Faransa, Gerard Collomb zai fara ziyarar aiki a qasashen Algeria da Nijar, inda zai tattauna da hukumomin kasar kan yaqi da ta’addanci da kuma matsalar baqin haure. Sanarwar ta ce, a Jamhuriyar Nijar, Ministan zai halarci taro kan yadda za’a magance matsalar safarar baqin-haure, wanda zai samu halartar wakilai daga qasashen

Chadi, Mali, Burkina Faso, Mauritania da kuma qasar Cote d’Ivoire. Sauran qasashen da zasu halarci taron sun haxa da Guinea, Senegal da Libya, tare kuma da wakilan qasashen Jamus, Italia da Spain. A baya bayan nan dai qasashe nahiyar Africa da ke yankin Sahel da suka haxa da Nijar, Mali da kuma Burkina Faso sun fuskanci hare-haren

ta’addanci, a dai dai lokacin da ayyukan rundunar dakarun haxin gwiwa na G5 Sahel suka fara kankama domin yakar ta’addanci. Xaya daga cikin hare-haren da aka kai mafi muni a bayabayan nan shi ne na birnin Ouagadugou, inda aka kai hare-haren kunar baqin wake kan hedikwatar sojin kasar da kuma ofishin jakadancin Faransa.

Trump Ya Bayyana Dalilan Sauke Tillerson Daga Muqaminsa

Shugaba Donald Trump ya ce, samun banbancin ra’ayi a kan wasu muhimman al’amuran da suka shafi manufofin Amurka a qasashen ketare ne ya sashi xaukar matakin sallamar sakataren harkokin wajen qasar Rex Tillerson. Trump ya ce daidai lokacin da yake kallon shirin nukiliyar da qasashen duniya suka qulla da Iran a matsayin kuskure, shi kuwa Tillerson na kallon yarjejeniyar ce a matsayin wadda ta dace. Shugaban na Amurka ya

kori Tillerson ne yayin da ya rage kusan watanni biyu ya bayyana matsayarsa a kan yarjejeniyar ta Nukiliyar Iran da qasashen duniya. Hakan yasa manazarta ganin cewa matakin sauke sakataren wajen, na nuni da cewa Trump zai iya yin watsi da wannan yarjejeniya a ranar 12 ga watan Mayu mai zuwa, duk da goyon bayan da take samu daga sauran manyan qasashe ne duniya. A shekarar 2015, aka cimma yarjejeniya tsakanin Iran da

manyan qasashen duniya, wadda a qarqashinta kasar ta Iran, ta mika wasu kayayyakin sarrafa makamashin Uranium tare da bai wa tawagar masu bincike damar sa ido kan ayyukan da take yi na inganta makamashin Uranium, da ta dade tana ikirarin cewa manufarsa ta zaman lafiya ce. Bayan cimma yarjejeniyar ce, manyan qasashen duniya suka amince da janye da dama daga cikin takunkuman karya tattalin arzikin da aka qaqaba mata a baya.

qasashen saboda matakan da suka dauka. A watan Disambar bara ne, aka qaddamar da shirin sanya sunayen qasashen dake taimakawa masu voye dukiyar domin kaucewa haraji, ganin sun sauya dokokin su da za su tafi da na duniya, wadda ke tabbatar da cewa, ko wanne attajiri na biyan haraji a qasar da dukiyar sa take.

Stephen Hawking Ya Rasu Shahararren masanin kimiyyar duniyan nan na Burtaniya Stephen Hawking, wanda ya yi ta nazarin maudu’o’i iri-iri da su ka shafi duniyoyi - kama daga yadda su ka samu, zuwa yadda su kan shuxe su zama wani bakin rami mai zurfi, wanda ake kira black hole, ya mutu yau dinnan Laraba ya na mai shekaru 76 da haihuwa. Wani mai magana da yawun iyalinsa ya ce Hawking ya mutu salun-alun a gidansa da ke birnin Cambridge, inda ya shafe shekaru gommai ya na aiki a matsayin Sheihin Malamin Lissafi na Jami’ar

Cambridge. “Ya kasance wani mashahurin masanin kimiyya kuma wani irin mutum da ba a sama gani ba; sannan ayyukansa za su cigaba da yin tasiri zuwa shekaru masu yawa,” a cewar ‘ya’yan Hawking, Lucy da Robert da kuma Tim a wani bayanin da su ka yi. Tun ya na dan shekaru 21 da haihuwa ya kamu da wata cutar naqasa, wadda sannu a hankali ta sa ala tilas ake sa shi cikin wata kujera ta musamman kuma ya daina magana sai ta amfani da na’ura mai fassara manufar mutum.


Wasanni 30

A Yau Alhamis 15.3.2018

Tare da Abba Ibrahim Wada Leadership Ayau@yahoo.com

Real Madrid Su Na Vata Lokacinsu Akan De Gea - Mourinho Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Idan Arsenal Suka Nemi Na Zama Kociyan Qungiyar Zan Karva Daga Abba Ibrahim Wada Gwale Tsohon xan wasan tsakiyar qungiyar qwallon qafa ta Arsenal, Patrick Viera, xan qasar Faransa ya bayyana cewa idan har Arsenal ta nemeshi yazama kociyan qungiyar zai karva amma kawo yanzu bazai tava nuna cewa yanason aikin ba saboda yana ganin girman Arsene Wenger.

A kwanakin nan dai mai koyar da qungiyar Arsenal, Arsene Wenger yasha suka daga vangaren magoya bayan qungiyar bayan da qungiyar tasha kashi a hannun qungiyoyi da dama ciki har da wasanni biyu da sukayi rashin nasara a hannun Manchester City. Vierra yace, idan qungiyar ta nemeshi zai saurareta amma kawo yanzu bazai iya cewa komai ba idan ana raxe raxin

komawarsa Arsenal saboda yadda yake ganin Mista Wenger a matsayin wani babban mutum a rayuwarsa. Vierra yaci gaba da cewa ya kamata a bawa Wenger dama ya zavi lokacin da ya kamata yayi ritaya daga qungiyar idan akayi la’akari da abinda yayiwa qungiyar na mayar da ita babbar qungiya sannan kuma ya lashe kofuna da dama a qungiyar.

Sevilla Ta Karya Wa Manchester United Tarihin Shekara 60

Mai koyar da yan wasan qungiyar qwallon qafa ta Manchester United, Jose Mourinho, ya bayyana cewa Real Madrid suna vata lokacinsu ne kawai akan mai tsaron ragar qungiyar tasa, David De Gea domin xan mai tsaron ragar bana siyarwa bane. Mourinho ya bayyana hakane bayan qungiyarsa ta tashi daga wasan da suka buga da Sevilla inda yace ya kamata su nemi wani mai tsaron ragar saboda bazasu samu abinda suke so ba a Manchester United. Yaci gaba da cewa idan shine shugaban gudanarwar qungiyar ta Real madrid da tuni ya haqura da neman De Gea saboda yana neman abinda bazai samu ba kuma yana vata lokacinsa domin idan ya haqura zai iya samun wani a wata qungiyar. Real Madrid dai tana shirin yin garambawul a qungiyar bayan da qungiyar takasa abin azo agani a gasar laliga kuma tuni shugaban qungiyar ya shirya kashe kuxi domin siyan duk xan wasan da yake so. David De Gea dai shine mai tsaron ragar da Real Madrid take zawarci sai kuma mai tsaron ragar qungiyar Chelsea, Thibaut Courtoise wanda qungiyar shima take zawarci idan bata samu De Gea ba. Sai dai Mourinho ya bayyana cewa mai tsaron ragar babu inda zashi a wannan kakar domin ya shirya cigaba da buga wasa dashi har zuwa kakar wasa mai zuwa. David De Gea dai yanada ragowar watanni 16 a ragowar kwantaragin daya rage masa a qungiyar.

Neymar Ya Fara Samun Nasara A PSG, Inji Mahaifinsa

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Qungiyar qwallon qafa ta Sevilla dake qasar sipaniya ta fitar da Manchester United daga gasar zakarun nahiyar turai, bayan samun nasarar da tayi akanta daci 2-1 a wasan mataki na qungiyoyi 16, bayan da a wasan farko aka tashi canjaras-0-0. Xan wasan Sevilla Wissam ben Yedder ne ya zura duka Qwallyen biyu bayan yashigo daga baya, yayinda Romelu Lukaku ya zurawa United qwallo daya tilo da ta ci.

Karo na farko kenan da Manchester United ta gaza kai wa matakin gaf dana kusa dana qarshe (kwata Final) acikin shekaru 60. Manchester United ta bi sawun qungiyar Tottenham wadda itama qungiyar Juventus ta yi waje da ita a gasar zakarun nahiyar turan. Mai koyar day an wasan qungiyar Jose Mourinho ya bayyana cewa daman ba sabon abu bane kuma qungiyar zata mayar da hankali a ragowar wasanninta da take bugawa.

Mahaifin xan wasa mafi tsada a duniya na PSG, Neymar, ya ce xan sa yana da damar kai wa ga nasarar da yake nema a qungiyar tasa ta PSG, kuma tuni ma ya fara samun nasarorin da yake buqata. Neymar Santos, mahaifin xan wasan, ya bayyana haka ne yayin zantawa da manema labarai a gidansu da ke jihar Sao Paulo, a Brazil, a lokacin da shugaban qungiyar PSG Nasser Al-Khelaifi ya kai masa ziyara don duba lafiyar xan sa Neymar da ke murmurewa daga raunin da ya samu a qafa, a ranar 25 ga watan Fabarairu da ya wuce. Kalaman na Mahaifin Neymar sun zo ne a dai dai lokacin da ake ci gaba da tofa albarkacin baki akan labaran da suke nuni da cewa, xan wasan ya fara qoqarin yi wa tsohuwar qungiyarsa ta Barcelona kome, idan kuma hakan ya gagara, tuni mahaifin nasa ya fara tuntuvar Real Madrid, dangane da sauyin sheqar dan wasan. A halin da ake ciki, likitoci sun tabbatar da cewa sai neymar ya shafe akalla watanni biyu da rabi zuwa uku, kafin ya warke sarai ya kuma dawo filin wasa domin cigaba da buga qwallo.

Neymar dai yasamu rauni ne a watan daya gabata a wasan da qungiyar ta buga da Marseille a wasan rukunirukuni na qasar Faransa wanda hakan yasa bai samu dammar buga wasa na biyu ban a zakarun turai da suka sha kashi a hannun Real Madrid. Neymar dai yakoma PSG ne daga qungiyar Barcelona kan kuxi fam miliyan 200 kuma tuni ya zura qwallaye 19 cikin wasanni 20 daya buga agasar qasar Faransa.


wasanni 31

A Yau Alhamis 15 Ga Maris, 2018 (26 Ga Jumada Thani, 1439)

Ya Kamata Southampton Ta Xauki Hughes A Matsayin Sabon Mai Koyar Wa Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Tsohon xan wasan qungiyar qwallon qafa ta Blackburn Rovers, Robbie Savage, xan qasar Wales, ya ce kamata ya yi qungiyar qwallon qafa ta Southampton ta xauki mai koyarwa Mark Hughes a matsayin sabon kociyanta har zuwa qarshen kakar nan. A ranar Litinin qungiyar ta kori kociyanta Mauricio Pellegrino bayan ta ci wasa xaya daga cikin 17, abin da ya sa ta zama maki xaya kawai a saman matakin faxuwa daga gasar firimiya. A wata hira da ya yi da manema labarai, tsohon xan wasan wanda ke sharhi kan qwallon qafa a yanzu ya ce, za a iya xauka shi mahaukaci ne. Amma idan aka duba cewa saura wasa takwas a gama gasar ta firimiya, kuma idan aka duba kociyoyin da ba su da aiki Mark Hughes ne ya fi dacewa. Savage wanda ya yi wasa a tawagar Wales da kuma kungiyar Blackburn qarqashin Hughes yana ganin mai koyarwar shi ne ya fi cancanta da aikin duk da cewa Stoke City ta kore shi a watan Janairu. Hughes ya jagoranci kusan wasa 450 na firimiya a qungiyoyin Blackburn da Manchester City da Fulham da QPR da kuma Stoke. Haka kuma ya buga wa Southampton wasa na xan wani takaitaccen lokaci a qarshen wasansa na qwallon qafa. Savage ya ce kociyan ya yi wa Southampton, wasa a baya kuma zai so ya nuna wa Stoke cewa sun yi kuskure, saboda yana da qwarewa sosai. Southampton na fatan naxa sabon kociyanta kafin karawar da za ta yi da Wigan ranar Lahadi na neman zuwa wasan dab da na qarshe na cin kofin FA. Duk wanda aka naxa zai kasance kociya na biyar na qungiyar tun lokacin da Mauricio Pochettino ya maye gurbin Nigel Adkins.

Ina Son Mu Haxu Da Real Madrid Ko Liverpool, In Ji Edin Dzeko Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Xan wasan gaba na qungiyar qwallon qafa ta AS.Roma, Edin Dzeko ya bayyana cewa yanzu burinsa shine su haxu da qungiyar Real Madrid ko Liverpool a wasan zakarun turai da suka kai wasanmatakin kusa dana kusa dana qarshe a ranar Talata bayan sun doke Shakhtar Donesk. Qungiyar qwallon qafa ta Roma ta samu kai wa ga matakin gaf da kusa

dana qarshe, bayan samun nasara akan Shaktar Donetsk ta qasar Ukraine daci 1-0. Xan wasan gaba na Roma Edin Dzeko, xan qasar Bosnia Herzgovinia ne ya ci wa qungiyar tasa qwallon a mintuna na 52 da fara wasan bayan yayi arangama da mai tsaron ragar Shakhtar. A zagayen farko na wasan da suka buga a Ukraine, Roma ta yi rashin nasara a hannun Shaktar Donetsk da qwallaye 2-1.

Karo na farko kenan da AS Roma ta samu kai wa ga zagayen gaf da kusa dana qarshe a gasar ta zakarun nahiyar turai cikin shekaru 10. Zalika rabon da wasu qungiyoyin qwallon qafa da suka fito daga kasar Italiya su kai matakin na gaf da kusa da qarshe, kamar wannan karon a lokaci guda, tun bayan kakar wasa ta 2006/2007, a lokacin da kungiyar ta Roma, da AC Milan suka samu nasarar kai wa zagayen.

Dole Sai Mourinho Ya Ajiye Sanchez A Benci Idan Yanson Ya Ga Dai-Dai, Inji Paul Scholes Daga: Abba Ibrahim Wada Gwale Tsohon xan wasan tsakiyar qungiyar qwallon qafa ta Manchester United, Paul Scholes ya bayyana cewa dole sai Mourinho ya ajiye sabon xan wasan qungiyar, Alexis Sanches idan har yanason yaga dai-dai a qungiyar. Scholes ya bayyana hakane a hirar dayayi da manema labarai bayan da Manchester United tabuga wasa 2-1 da qungiyar Sevilla a filin wasa na Old Trafford wanda hakan yasa qungiyar tafita daga gasar ta zakarun turai. Tsohon xan wasan yaci gaba da cewa qwallo tana yawan mutuwa a qafar Sanches saboda haka ya kamata Mourinho yagane kuma ya ajiyeshi a benci domin yabawa wasu dama su bayyana kansu a wasannin qungiyar. Yaci gaba da cewa dole Mourinho ya fahimci irin abinda Sanches yake bugawa cikin wasanni goma daya buga a qungiyar saboda shi ba makaho

bane kuma yana ganin abinda yake bugawa amma yake cigaba da sakashi a wasanni. Yanzu dai Manchester United dole ta mayar da hankali wajen kammala gasar firimiya a matsayi na biyu sannan kuma ta sake mayar da hankali a gasar cin qalubale na FA wanda zata buga da Brighton Albiona ranar Asabar.


LEADERSHIP 15.3.18

AyAU Alhamis

Don Allah Da Kishin Qasa

www.leadershipayau.com Leadership A Yau

Jaridar hausa mai fitowa kullum ta farko a nijeriya

LeadershipAyau

No: 107

N150

qasashen waje

Trump Ya Bayyana Dalilan Sauke Tillerson Daga Muqaminsa > Shafi na 29

Tsakanin Zuwa Xaurin Aure Da Zuwa Garin Dapchi A Wajen Buhari Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@gmail.com

T

un bayan da aka bayar da sanarwar sace ‘yan matan makarantar Sakandiren Gwamnati dake Dapchi a jihar Yobe, mutane da yawa musamman a shafukan sada zumunta na intent suka riqa kira ga Gwamnatin tarayya da ta yi wani abu akan wannan batu, amma aka yi shakulatun bangaro, shugaban kasa ya kasa nuna damuwarsa a fili akan abin da ya faru na sace waxannan ‘yan mata. Mutane sun yi ta kira ga Shugaban kasa a shafukan Twitter da Facebook da ya daure ya je garin na Dapchi domin jajantawa iyayen da aka sace musu ‘ya ‘ya a hannun Gwamnatin da suka baiwa amanar yaran nasu, amma Shugaban kasa ya nuna ko in kula, ya nuna sam wannan batu ba a gabansa yake ba. Ana tsaka da waxancan kiraye kiraye na ya daure yaje garin na Dapchi domin jajantawa iyayan yaran da aka sace ‘ya ‘yansu a hannun Gwamnati, kwatsama sai aka wayi gari da jin cewar Shugaban da kansa zai halarci xaurin auren ‘yar gidan Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da kuma dan gidan Gwamnan Oyo Abiolla Ajimobi. Da farko da naji sanarwar cewar Shugaban zai halarci wannan aure ban yarda ba, domin nasan duk Shugaban da ya damu da al’amarin al’ummarsa ba zai kyale ‘yan matan Dapchi ya tafi Kano xaurin aure ba. Ashe ban sani ba tunani na ba gaskiya bane, domin kuwa Shugaba Buhari ya amsa wannan gayyata ya kuma halarci wannan xaurin aure da aka yi asabar din da ta gabata. Zance na gaskiya abin ya xaure min kai qwarai da gaske, ta yadda Shugaba Buhari yayi fatali da talakawan da sune silar zuwansa kan karagar mulki amma ya kama masu hannu da shuni ya rike a matsayin sune mutanansa da yake ji da su. Na zata Shugaba Buhari zai fi damuwa da al’amarin talakawa kan abin da ya shafi sharholiya irin na masu hannu da shuni, ashe shima yana tare da irin masu sharholiyar mune bamu sani ba. Wannan halartar xaurin aure

Muqalar Alhamis

da Buhari yayi ta sanya mutane da yawa daga cikin massoyansa na gaskiya sun nuna damuwa da wannana abin da Shugaban yayi, domin Farfesa Salisu Shehu wanda Malami ne a jami’ar Bayero dake Kano, kuma masoyin Shugaba Buhari, ya wallafa a shafinsa na Facebook irin damuwarsa kan halartar wannan xaurin aure da Shugaban yayi, yayin da yayi fatali da ‘yan matan Dapchi da aka sace. Amma maimakon mutane su yiwa Farfesa Salisu Shehu kyakkyawar fahimta, sai aka samu irin ‘yan gani kashenin nan wanda basu iya bambance soyayya da kiyayya, suka hau Farfesan malamin da zagi da cin mutunci, sabida kawai ya bayyana ra’ayinsa na rashin gamsuwa da zuwa xaurin auren da Shugaba Buharin yayi yabar ayyuka masu muhimmanci da suka shafi talakawa. Akwai abubuwan da suke faruwa kuma suke da bukatar hanzarin Shugaban kasa,amma sai yayi kunnen uwar shegu ya nuna sam bai damu ba, misali a Mambila an kai hare hare yafi a kirga,an kashe mutane daruruwa, amma Shugaban bai damu ba, bai kuma yi tunanin zuwa ya jajantawa mutanen da abin ya faru da su ba. Daga nan aka yi kashe-kashe a jihar Binuwai, nan ma ya nuna halin ko in kula, akai yi ta yi da shugaban ana cewar bai damu da al’ummarsa ba,amma yayi kamar

bai ji me mutane suke cewa ba. Yaki zuwa Binuwai don jajantawa mutanan jihar abin da ya faru da su. Aka zo aka kashe mutane da yawan gaske a kauyen Birani dake yankin karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara, amma Shugaban kasa ko jajaje bai aika ba, sai daga baya. Duk irin waxannan da ma wasu sun faru amma babu ruwan Shugaban kasa da nuna damuwarsa kan halin da al’umma suke ciki. Amma da yake masu arziki ya damu da su sai gashi shi ne yake zuwa xaurin auren ‘ya ‘yan su, wannan abin takaici ne mai sosa rai qwarai da gaske. Bayan zuwa wannan xaurin aure da Shugaban yayi a jihar Kano, mutane da yawa suka nuna damuwa, matsin lamba tayi yawa, sannan ne Shugaban kasa ya bayar da sanarwar wai zai je jihohin da suke fama da kashe-kashe da suka hada da Zamfara da Adamawa da Yobe da Taraba da kuma Binuwa da Ribas. A dacan baai yi tunanin haka ba, sai da caccaka da matsin lamba suka yi yawa. Irin wannan nuna halin rashin damuwa da Shugaba Buhari yake nunawa, ya nuna sam shi a irin mutumiin da talakawa suke tsammani bane, domin ya nuna talakawa ba a gabansa suke ba, yafi damuwa da abin da ya shafi masu hannu da shuni da masu arziki sama da abin da ya shafi talakawa.

+23408099272908

Yana da kyau Shugaban kasa ya sani talakawa da sauran al’ummar Najeriya duk sun zabe shi a bisa doron adalci. Wannan ta sanya aka zabe shi, amma yazo yana nuna sabanin abin da ake masa tsammani. Lallai ya kamata Shugaban kasa yaji tsoron Allah, kuma ya sani cewar, Allah sai ya tambayeshi akan dukkan mutanan da suka rasa rayukansu a qarqashin mulkinsa, abubuwa da yawa suna faruwa a qasar nan bisa sakacinsa. Wasu abubuwan inda yana yin abin da ya dace da basu sake faruwa ba. Misali kashe-kashe da ake yi a Zamfara, inda ya nuna damuwa da kuma xaukar matakin da ya dace, da wannan abu bai cigaba ba, haka nan jihar Taraba da Binuwai. Amma babu ruwansa da mutanen da ake kashewa, to ya sani idan shi babu ruwansa, Allah da ya haliccesu yana da ruwa game da duk mutanen da aka kashe ba bisa hakki ba. Lallai muna kira ga Shugaban kasa yaji tsoron Allah, yayi abin da ya dace, kada yaga abin da bai dace ba a inda babu kudi sai ayyukan alheri da munanan ayyuka. Muna masa fatan Allah ya bashi ikon sauke nauyin al’umma da yake kansa,amma kuma muna jiye masa tsoron gamuwarsa da Allah akan sakaci da nuna halin ko in kula akan abin da ya shafi al’ummar da yake Shugabanta.

Babba Da Jaka Tsaro: ’Yan Sanda za su yi haxin gwiwa da Mafarauta –Labarai

Tabxi! kar dai a ba su Bindiga...

Ana shiryawa da buga LEADERSHIP A Yau a kamfanin LEADERSHIP GROUP LIMITED, lamba 27, kan Titin Ibrahim Tahir, a Gundumar Utako, Abuja. Tarho: 07036666850; Fax: 09-2345360. P. O. Box 9514, Garki II, Abuja. Ofishin mu a Legas: 34/36 Titin Adegbola, Anifowose, daidai Oba Akran, Ikeja. Tarho: 01-8963459. E-mel: leadershipayau@gmail.com, Leadershipayau@yahoo.com

LEADERSHIP A Yau E-paper 15 Ga Maris, 2018  
LEADERSHIP A Yau E-paper 15 Ga Maris, 2018  

LEADERSHIP A Yau E-paper 15 Ga Maris, 2018