Page 1

12.3.18

AyAU Litinin

LEADERSHIP Don Allah Da Kishin Qasa

Jaridar hausa mai fitowa kullum ta farko a nijeriya

www.leadershipayau.com Leadership A Yau

12 Ga Maris, 2018 (23 Ga Jumadal Thani, 1439)

LeadershipAyau

No: 104

N150

An Yi Jana’izar Tsohon Gwamnan Adamawa, Saleh Michika Daga Muhammad Shafi’u Saleh, Yola

A jiya aka yi jana’izar Alhaji Saleh Abubakar Michika, tsohon gwamna na farko da jama’a suka zava a jihar Adamawa. Tsohon gwamnan ya rasu ne sakamakon wata doguwar jinya da yayi

fama da ita a babban asibitin gwamnatin tarayya (FMC) da ke Yola. An haifi tsohon gwamna, Marigayi Michika a shekarar 1941, ya riqe muqamai da dama, inda a biyu ga watan Janairun 1992 zuwa 17 ga Nuwambar 1993, ya zama gwamnan farar hula na farko a jihar, biyo bayan qirqirar jihar

Gongola, qarqashin jam’iyyar NRC. A wani bayanin da babban mai taimakawa gwamnan jihar Adamawa kan harkokin sadarwa Macaulay Hunohashi ya fitar, ya ce, tsohon gwamnan Saleh Michika, ya rasu ranar Asabar da daddare. Yace, gwamnan Umaru Bindow, ya

ziyarci tsohon gwamna Saleh Michika, a daren kafin daga bisani cikin daren aka sanar da gwamnan cewa Michika ya rasu. Da misalin qarfe biyu na ranar jiya ne aka yi Jana’izarsa. Michika dai ya rasu ne ya bar mata huxu da ’ya’ya 38; Maza 11 da Mata 27.

Qarin Kuxin Haraji:

Barasa Da Sigari Za Su Yi Tsada A Nijeriya 4

Gawar Tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Marigayi Aliyu Akwe Doma jiya yayin da ake yi mata Sallah a Garin Doma ta Jihar Nasarawa

Ba Gwamnan Da Ya Isa Ya Mutuwar Akwe Doma –Al-Makura Wa’azi Ne Garemu Yi Babakere A PDP –Wike > Shafi na 4 > Shafi na 2


2 labarai

A Yau

Litinin 12 Ga Maris, 2018 (23 Ga Jumada Thani, 1439)

Ba Wani Gwamnan Da Ya Isa Ya Yi Babakere A Jam’iyyar PDP –Wike Daga Umar A Hunkuyi

Daga Umar A. Hunkuyi Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana cewa, ba wani Gwamna da ya isa ya mamaye tsarin Jam’iyyar na su ta PDP, a matsayin kayansa, inda ya bayyana masu raxe-raxin hakan a matsayin maqaryata. Da yake magana a cikin wata tattaunawa ta musamman a gidan Talabijin na Channels, a qarshen makon nan, Wike, ya bayyana xaukacin gwamnonin Jam’iyyar ta PDP, da cewa duk matsayin su guda ne, suna kuma aiki ne domin ganin daidaiton Jam’iyyar. Ya ce, ba wani Gwamnan da yake juya akalar Jam’iyyar a wata Jihar ta daban da ba ta shi ba. Da yake mayar da martani a kan jawabin da aka ce tsohon Shugaban qasa, Olusegun Obasanjo, ya yi, Wike, ya ce, ai tsohon Shugaban ya rigaya ya bar Jam’iyyar ta PDP, har ma ya yaga katin zamansa xan Jam’iyyar, to don me kuma yake damuwa da abin da ke faruwa a Jam’iyyar ta PDP. Gwamnan, ya yi nuni da cewa, ba kuxi ne za su iya daidaita jam’iyyar ba, face dai haxin kan ‘ya’yanta. Sannan ya ce, a irin wannan yanayin, hatta ma hukumar zave ta qasa mai zaman kanta, (INEC), ta rasa qumajin iya shirya sahihin zave. Wike, ya ce, ba maganar fatan baki kaxai ba, kamata ya yi hukumar zaven ta xauki qwararan matakan da za ta nu nawa ‘yan Nijeriya cewa,a shirye take da ta gudanar da sahihin zave. Abu na farko In ji Wike, ya wajaba hukumar zaven da ta yi bincike a sarari, ko su wane ne, shugabannin jam’iyyar APC, xin da suka buga jabun takardun

hukumar zaven na jabu a Jihar ta Ribas. Sannan kuma,hukumar zaven ta INEC, ta bayyana ko ta yaya ne ‘yan sanda suka sami ingantaccen sakamakon zaven mai xauke da lamba iri xaya na zaven shiyyar Xan majalisar Dattawan Ribas ta gabas, inda har hukumar zaven ta ayyana Sanata George Sekibo, a matsayin wanda ya lashe zaven, kafin daga bisani, mutane su zo da wani sakamakon zaven na daban, wanda Kotu ta yi amfani da shi ta tabbatar da xan takarar Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaven. Kan irin ayyukan da ya yi a Jihar ta Ribas, ya nanata cewa, yanzun su sun fito da wani tsari na qin barin ayyukan da ba a kammala ba, waxanda ya gada daga wanda ya gabace shi. Ya qara da cewa, gwamnatin sa ta aiwatar da mahimman ayyuka a dukkanin Qananan hukumomi 23 na Jihar, sannan kuma duk ayyukan da ya gada daga Ameachi, ya kammala su. “Na shirya yanda zan iya kammala duk aikin da na sanya a gaba ne a cikin shekaru huxu, ba zan fara wani aikin da na san ba zan iya kammalawa ba.” Ya ce, “Gwamnati na, ta qarfafa hanyoyin da za su qara kusanto da mata cikin gwamnati, da kuma tallafa masu. Mun kuma keve sama da Naira milyan 500 domin tallafawa matan Jihar Ribas.” Ya koka da cewa, ba a bi ta hanyar da ta dace ba, wajen sanar da shi ziyarar da Shugaban qasa zai kawo a Jihar na shi ta Ribas, yana mai cewa, ai a tsakaninsa da fadar ta Shugaban qasa, ya wuce a ce sanarwa ce kawai zai ji a jaridu ta bakin Femi Adesina. “Idan an ce Shugaban qasan zai zo ne domin ya jajantawa iyalan mamatan ranar 1 ga

•Shugaban Hukumar NCC, Danbatta

watan Janairu ne, hakan yana da kyau. Domin ko a lokacin da abin ya faru a ranar 1 ga watan Janairu ba wanda ya jajantawa gwamnatin Jihar Ribas. A maimakon hakan ma, sai Shugabannin APC xin suka saka siyasa a cikin lamarin.

Gwamnan ya ce, kusan shekaru uku kenan, ba wani abin da Jihar ta Ribas ta amfanu da shi daga gwamnatin APC ta tarayya, ya ce, maganar yashe yankin Ogoni, har gobe a matsayin mafarki yake, hakanan batun aikin hanyar

Bodo zuwa Bonny, shi ma ana gab da yin watsi da shi. Ya qarfafa cewa, aikin hanyar Gabas maso kudu, da na Filin saukan Jirage na Fatakwal da sauran ayyukan gwamnatin tarayya a Jihar duk an yi watsi da su.

Hukumar Sadarwa Ta Gargaxi Kamfanonin Waya Kan Cutar Al’umma Da Suke Yi Daga Umar A Hunkuyi

Hukumar sadarwa ta qasa, (NCC), ta sake gargaxin Kamfanonin waya na qasar nan kan cutar da suke yi wa masu hulxa da su ta hanyar cajan su kuxaxen da ba su ji ba, ba su gani ba. Daraktan hulxa da jama’a na hukumar, Mista Abdullahi Maikano, ne ya yi wannan gargaxin a qarshen mako wajen taro na 92 na hukumar

da ta shirya a Qaramar Hukumar Ekpene, ta Jihar Akwa Ibom. Maikano, wanda Alhaji Ismail Adedigba, ya wakilce shi, ya nanata cewa, hukumar ta NCC, a shirye take da ta kare dukkanin haqqin al’umman da suke hulxa da kamfanonin wayan, wajen ganin an yi masu aiki mai kyau, wanda ya cancanci kuxin su. “Baya ga aikin tabbatar da kare haqqin mutanan

da ke hulxa da kamfanonin sadarwar, muna kuma qoqarin ganin ba a ci da guminsu ba, ba a kuma yi masu cuta ba. Hakanan kuma, wannan taron yana qara sanya hanyar sada masu amfani da kafofin sadarwar da kuma hukumomin da suka dace. Daraktan, ya umurci shugabannin sassan sadarwan da su yi amfani da irin wannan taron domin samun dukkanin bayanan da suka dace, ta yanda

wani ba zai yaudare su ba. Shi ma da yake magana, mataimakin daraktan, Alhaji Ismail Adedigba, cewa ya yi, taron a kan shirya shi ne a tsakanin jami’an hukumar, shugabannin kamfanonin sadarwan da kuma masu hulxa da su, domin warware wasu matsaloli da ke tsakanin su. A cewarsa, a shekarar 2017, wacce hukumar ta NCC, ta bayyana a matsayin shekarar kamfanonin sadarwan, ta yi

wani shiri na musamman da nufin qarfafawa da kuma kare masu hulxa da kamfanonin sadarwan, ta hanyar wayar masu da kai. A wata maqala mai taken, “Information and Education as a Catalyst for Consumer Protection”, an sake faxakar da kamfanonin na sadarwa cewa, masu fa hulxa da su xin ne kasuwansu, don haka kare martabarsu shi ne kare martabar kasuwarsu.


3

A Yau Alhamis 8 Ga Maris, 2018 (19 Ga Jumada Thani, 1439)

Ra’ayinmu

Yayin Da Aka Yi Bikin Ranar Mata Ta Duniya… A ranar Alhamis xin da ta gabata 8 ga watan Maris 2018, xaukacin al’ummar duniya suka gudanar da bikin ranar Mata ta duniya. Ranar 8 ga watan Maris, rana ce da aka keve musaamman domin qara sanar da duniya matsayi, qima da kuma darajar da Allah Ya yi wa Mata. Rana ce, da a kan gudanar da taruka domin yayata irin ci gaban da kuma gwagwarmayar da mata suka yi ko kuma ma suke kan yi a dukkanin sassan duniyar nan. Tun a farkon wannan qarnin ne aka keve wannan ranar ta 8 ga kowane watan Maris na kowace shekara domin nu na halin da matan ke ciki a jiya da kuma yau, rana ce da gwamnatoci, Qungiyoyin mata, Kamfanoni da ma sauran xaixaiku sukan yi taruka, shirya wasu bukukuwa na musamman, domin su tattauna halin da matan ke ciki saboda mahimmancinsu, a duk faxin duniyar nan. Ranar mata ta duniya, rana ce da a kan dakatar da komai domin a tsaya a yi dubi da kyau a kan qimar matan, a matsayin su na, Matan aure, Iyaye, manyan ‘yan kasuwa, Shugabanni, ‘yan gwagwarmaya, da makamantan hakan. Taken ranar ta wannan shekarar shi ne, “Lokaci ya yi: da ya kamata a sami canji a rayuwar mata,” a taqaice kenan, da turanci taken ranar matan ta bana shi ne, “Time is Now: Rural and Urban Activists Transforming Women’s Lives”. Bikin na bana, ya yi karo da yunquri kala-kala da matan ke yi a dukkanin sassan duniyar nan,na ganin sun fitar da kansu daga wasu al’adu ko dokokin da suke tawaye ne a cikin darajar da Allah Ya yi masu. Suke kuma gwagwarmayar tabbatar da samun ‘yanci wanda ya yi daidai da na kowane mahaluqi a bisa gaskiya da adalci ba kuma tare da nu na wani bambanci ba. A wasu qasashen kamar qasar Amurka da makamantansu, matan sukan gudanar da jerin gwano ne a bisa tituna da kuma bin gidaje a cikin birane da qauyaku, inda suke tunatar da mutane a kan wasu haqqoqinsu da aka tauye masu, musamman a wuraren da a kan bambanta albashin matan da na maza ko abin da ya shafi matsayin su wajen raba muqamai a siyasa da sauran qungiyoyi. Hakanan kuma sukan yi amfani da wannan ranar domin tunatar da al’umma haxarin da ke tattare da cin mutunci, tsagwama, qoqarin raina matsayi, Fyaxe, da duk da a kan yi wa matan. Mu a nan, muna ganin kamata ya yi Shugabanninmu da sauran masu faxa a ji, su yi amfani da wannan ranar ta wannan shekarar wajen tsayawa tsam da kuma yin dubi bisa hali da kuma yanayin da matan ke ciki musamman

ma matan karkara. Waxanda za mu iya cewa, sune kaso aqalla xaya bisa huxu na al’ummar wannan duniyar tamu. Tare da wannan ximbin yawan na su, da kuma gagarumar gudummawar da suke baiwa al’umma ta dukkanin fannoni, sai kuma sukan zama abin tausayi, domin kuma za ka taras a duk wani sashe na more rayuwar da suka taimaka wajen daxaxa ta, su ne a baya. Akwai bukatar xaukan matakai na gaggawa waxanda za su ciyar da rayuwar matan da muke kira da iyayen

al’umma gaba, tilas ne mu baiwa matan gudummawa ta kowane sashe kuma a birane da karkara da ma dukkanin qauyaku. Tilas ne mu zaqulo matan da suka yi dukkanin abin yabo a cikin al’umma domin mu yaba masu kamar yadda a kan yabawa kowa. Tilas ne mu qarfafi mata ‘yan gwagwarmayar fito da haqqi da qimar mata a duk inda suke. Sannan kuma ya zama wajibi ga gwamnatocinmu da su tabbatar da sun gusar da dukkan wani abu mai qarfafa qyama da kuma nu na bambanci ga

EDITA Sulaiman Bala Idris

MATAIMAKIN SHUGABA (NA MUSAMMAN) Christian Ochiama

MATAIMAKIN EDITA Bello Hamza

DARAKTAN SASHE Mubarak Umar

RUKUNIN KAMFANONIN LEADERSHIP SHUGABA Sam Nda-Isaiah

BABBAN MANAJAN DARAKTA Abdul Gombe BABBAN MANAJAN DARAKTAN KADARORI David Chinda MANYAN DARAKTOCIN KAMFANI Dele Fanimo Felicia Ogbonlaiye DARAKTAN KULA DA MA’AIKATA Solomon Nda-Isaiah DARAKTAN KULA DA KADARORIN KAMFANI Zipporah D. Tanko MANYAN MANAJOJI Ibrahim Halilu Femi Adekunle Ebriku John

manufarmu

LEADERSHIP A Yau jarida ce da ake bugawa a Abuja. Ta yi tsayuwar daka wajen tabbatar da shugabanci da wakilci nagari. Jaridar za ta ci gaba da kare muradun al’umma, ba kare ra’ayi da muradun mahukuntanta kaxai ba. Da waxannan qudirorin ne muke fatan jama’a za su xora mu kan Mizani. Haka kuma duk ra’ayoyin masu karatu da muke bugawa, ba manufar kamfanin LEADERSHIP ba ne, ra’ayin masu karatun ne. Sai dai, ba za mu tava mantawa da dalilin wanzuwarmu a doron qasa ba, wato: Don Allah Da Kishin Qasa!

mata. Kamar yadda ya zama wajibi ga gwamnatocin namu da su yi dukkanin abin da za su iya yi na ganin sun kyautata rayuwar matan, ta hanyar fito da shirye-shirye da kuma wasu ayyukan da za su kyautata rayuwar matan. Kamata ya yi, wannan rana ta kasance ta shekara ce sukutum, ba ranar 8 ga watan Maris ba kaxai, muna ganin lokaci ya yi da dukkanin mutane a xaixaikun su ne ko gwamnatoci, Kamfanoni, Qungiyoyi da sauran dukkanin al’umma za su yi dukkanin abin da ya dace na ganin sun fitar da haqqin matan gami da kyautata rayuwar su ta hanyar samar masu da dukkan abin da zai iya ciyar da rayuwar ta su gaba. Kowace al’umma ya kamata ta duba ta ga hanyar da ya kamata ta taimakawa rayuwar matan ta yadda za su mori rayuwar su daidai da sauran mutane. Mutane da yawa, zaton su shi ne, fifiko yana ga mawadata da kuma masu mulki ne kaxai, wanda lallai ba hakan ne ba. Wannan zamani ne wanda duniya ta kasance tamkar ta taru ne a cikin xaki guda, musamman kasantuwar hanyoyin sadarwa na zamani da ake da su yanzun, ta yadda duk abin da ya faru a nan duk duniya za ta kasance da masaniya a cikin sa. Wannan ya isa ya nu na mana cewa, ya zama tilas mu guji taka haqqin mata da ma sauran marasa qarfi, domin kuwa dukkanin abin da muka yi tabbas duk duniya tana kallonmu. Wannan aiki ne da ya hau kan kowa. Ya wajaba, mata su fito su ma su faxa domin a ji su a kuma saurare su, su kuma yi amfani da hannuwansu wajen yin nu ni da dukkanin halukan da suke ciki ta hanyar rubuce-rubuce, su kuma yi amfani da dubarbarun da Allah Ya huwace masu wajen taimakawa junansu kamar yadda suke taimakawa al’umma bakixayanta. Su kuma ci moriyar dukkanin kafafen sadarwa wajen yayatawa duniya hali da kuma yanayin da ‘yanuwansu na karkaru da qauyaku ke ciki. Ya kuma kamata al’umma da ta baiwa matan sarari domin su nu na irin bajintar da Allah Ya yi masu, a makarantu, wuraren aiki, wajen wasanni da dai sauran su. Dukkanin gwamnatoci ya kamata su samar da hanyoyin kare haqqin mata da mutuncin su, musamman mu a wannan nahiyar matan da rigingimu da yaquka suka xaixaita su, suka raba su da gidajen su da kuma iyalan su. A qarshe muna kira ga gwamnatin tarayya, da ta hanzarta sanyawa a cikin dukkanin tsare-tsaren ta, gami kuma da aiwatar da abubuwan da muka bayar da misalan su dangane da kare haqqi da mutuncin mata.


4 labarai

A Yau

Litinin 12 Ga Maris, 2018 (23 Ga Jumada Thani, 1439)

Qarin Kuxin Haraji: Barasa Da Sigari Za Su Yi Tsada A Nijeriya Daga Bello Hamza

Shugaban Qasa Muhammdu Buhari ya amince da gyaran da aka yi wa dokar haraji a kan Barasa da Taba Sigari wacce za ta fara aiki daga 4 ga watan Yuni na shekarar 2018. A sanarwar da ta bayar jiya, Ministar kuxi, Kemi Adeosun, ta ce, kuxin harajin zai xauki tsawon shekara uku ne daga 2018 zuwa 2020 domin a lura da tasirin dokar a kan kuxaxen da ake sayar da sigarin da na barasar. Ministan ta qara da cewa, wannan sabon tsarin kuxaxen harajin ya samu amincewar dukkan masu ruwa da tsaki wacce kwamitin qayyade kuxaxe na ma’aikatar kuxi ya jagoranta tare da sa hannun kanfanoni masu samar da sigarin da barasa. Ta kuma qara da cewa, wannan qarin da aka samu na kuxaxen harajin barasa da sigari an yi shi ne domin samun alfanu guda biyu, na farko, anfanin qaruwar kuxaxen shiga ga gwamnati da kuma rage cututtukar da ake xauka ta hanyar mu’amala da barasa da

taba sigari. “Kwamitin qayyade farashi ‘The Tariff Technical Committee (TCC)’ ya bayar da shawarar a xan qara kuxaxen harajin bayan an yi la’akari da tsare-tsaren gwamnati na shekara 2018 da kuma rahoton Bankin Duniya da na kwamitin qungiyar lamuni ta duniya mai bayar da tallafi a Nijeriya. “Ma’aikatar Ciniki da Zuba Jari ta yi nazarin tasirin wannan xan qarin da aka yi kafin ta miqa shawarar ta ga kwamitin qayyade farashi na TTC”. “An kuma gudanar da bincike, in da aka gano cewa qasashe takwarorin Nijeriya sun yi mana nisa wajen irin harajin da suke karva a kan barasa da sigari” Misis Adeosun ta ce, wannna amincewar da shugaban qasa Muhammadu Buhari ya yi n a sabon kuxaxen haraji ya maye tsohon tsarin da ake da shi ne na “d-valorem” an maye gurbinsa da tsari haraji qayyadadde a kan barasa da sigari. “Wannan tsarin zai yi maganin kurakuran da ake samu a tsarin da ake amfani da

• Samfurin Taba Sigari

shi a baya zai kuma tabbatar da kuxaxen harajin na shiga inda ya kamata” “Ga taba sigari zamu ci gaba da karvan kashi 20 kuxin harajin sa sai dai zamu xan qara wasu kuxaxe na gudanar wa har na tsawon shekara uku domin rage farashin sigarin a kasuwa” A wannan tsarin da aka amince da shi na kashi 20 “advalorem rate” za a qara wa

kowanne karar sigari Naira 1 (Kwalin sigari mai kara 20 zai samu qaruwar Naira 20 ke nan) a wannan shekarar 2018, za a kuma samun qarin Naira 2 a kan karan sigari xaya a cikin shekarar 2019 (Kwalin sigari mai kara 20 zai kama naira 40), sannan za a kuma samu qaruwar Naira 2.90 na haraji a kan karan sigari a shekarar 2020 (Kwalin sigari mai kara 20

zai kama Naira 58 ke nan) Ministan ta kuma yi qarin bayanin cewa, gaba xaya qarin da aka yi na harajin sigari ya kai kashi 23.2 koma bayan yadda yake kashi 38.14 a qasar Algeria da kashi 36.52 a qasar Afika ta Kudu da kuma yadda abin yak e na kashi 20 a qasar Gambia. A tsarin qarin da aka yi wa barasa ya shafi Beer da Stout da Wines da kuma Spirits na tsawon shekara uku daga 2018 zuwa 2020. Sabon tsarin ya nuna cewa, harajin beer da stout ya kai Naira 0.30k a kan kowanne centiliter (Cl) a shekarar 2018 zai Naira 0.35k a kan ko wanne Cl a shekarar 2019 da 2020. Harajin Wines zai zama Naira 1.25k a kan kowanne Cl a shekarar 2018 sannan Naira 1.50k a kan Cl a shekarar 2019 da 2020, sannan harajin spirits ya kama Naira 1.50k a kan Cl a shekara 2018 da kuma Naira 1.75k a kan kowanne Cl a shekarar 2019 sannan kuma Naira 2.00k a kan Cl a shekarar 2020. Daga qarshe ministan ta ce, wannan sabon tsarin ya yi daidai da tanade-tanaden harajin qungiyar ECOWAS.

Rahoton JAMB Ya Bayyana Jihohi Huxu Da Suke Kan Gaba A Karatun Likitanci Daga Umar A. Hunkuyi

Sakamakon buxe Jami’o’i da aka yi a shekaru goma baya, kusan a dukkanin sassan qasar nan, hakanan ma yawan xaliban da suke samun damar shiga manyan makarantun domin karantar darussa na musamman, shi ma ya qaru. Amma dangane da fannin karatun aikin likita, Jihohi huxu na qasar nan sun riga sun yi wa saura fintinkau a wannan fannin, musamman a cikin shekaru Biyar xinnan da suka shuxe a jere. Jihohin kuwa su ne, Imo, Anambra, Delta da Jihar Enugu. A tsakankanin shekarar 2011 har zuwa shekarar 2015, waxannan Jihohi huxun su ke kan gaba wajen samun guraban karanta darasin aikin likita a manyan makarantun qasar nan fiye da sauran Jihohin qasar nan bakixaya, hakan, kamar yadda qididdigan hukumar shirya jarabawa ta qasa, JAMB. Ya nu na. A shekarun nan biyar da muka ambata, waxannan Jihohin huxu, in ka xebe Jihar Anambra, su ke saman sauran Jihohin a kan wannan fannin. Amma ita Jihar Anambra ta kasance ta biyu ne a cikin shekaru huxu, a

sa’ilin da ta kasance ta shida a shekarar 2015. Jihohi biyu ne kawai, suka karya qwarin shiga jerin na su kaxan. Jihar Osun ta kasance ta biyar sau biyu, ta kuma zama ta huxu sau guda. Jihar Edo kuwa ta kasance ta uku ne sau guda, ta kuma yi ta biyar sau guda shi ma. Waxannan qididdigan sun qunshi lissafin shekarun, 2011, 2012, 2013, 2014 da 2015, ne, a bisa tsarin jarabawar da hukumar ta JAMB, ke shiryawa. Binciken na mu, ya mayar da hankalin sa ne, a kan manyan darussa uku, da ake yawan takara a kansu, su ne kuwa, Karatun aikin Likita, Injiniyarin da kuma darasin Shari’a. Misali a fannin karatun aikin Likita, Jihar Imo, tana da xalibai 1,940, waxanda suka sami shiga Jami’o’in daban-daban a shekarar 2011. Jihar Anambra ke biye da ita da xalibai 1,536, Jihar Enugu ita ce ta uku, da xalibai 1,280, Delta ta yi ta huxu da xalibai 1,137, sai Jihar Abiya ta biyar da xalibai 931. A shekarar 2012, Jihohi huxun dai su ne suka kasance na a saman na biyar xin. jihar Imo, ita ce ta xaya da xalibai 1,841, Anambra ta zama ta biyu da xalibai 1,473, Delta ta uku

da xalibai 1,305, a sa’ilin da Jihar Enugu ta zama ta biyar da xalibai 1,247. A wancan shekarar, Jihar Osun ta yi ta biyar da xalibai 958, a fannin na darasin karatun aikin Likita. Jihar Imo ta ci gaba da kasancewa a kan gaba a shekarar 2013 da xalibai 2,395, Jihar Anambra ta sake take mata baya da xalibai 1,645, Delta ta zaman a uku da xalibai 1,618, Enugu kuma ta yi na huxu da xalibai 1,422, Jihar Edo ta je ta uku da xalibai 1,256. A shekarar 2014, Jihar Imo ta samar da xalibai 1,588 ne a Cikin Jami’o’in domin su karanci ilimin na aikin likita. Anambra ta kasance ta biyu da xalibai 1,511, Delta ta yi ta uku da xalibai 1,170, Enugu ta yi ta huxu da xalibai 1,161, Osun ta zo ta huxu ta yi ta biyar da xalibai 1,146. A shekarar 2015, matsayin sai ya xan canza sosai, inda Jihar Delta ta tsinci kanta a mataki na farko da xalibai, 1814, Imo ta komo ta biyu da xalibai 1,727, Jihar Edo ta yi ta uku da xalibai 1,510, Osun kuma ta huxu da xalibai 1,447, Enugu ta yi ta biyar da xalibai 1,390. Karo na farko a cikin shekaru biyar Jihar Anambra ta faxi qasa warwas a

mataki na shida. Hasssan Soweto, wani mai fafutukar kare haqqin xan adam, da kuma kare martabar Ilimi, cewa ya yi, yana jin cin jarabawar ya danganta ne da irin jarin da kowace Jiha ke zubawa a fannin na ilimi. Inda yake cewa, “Hakan yana nufin wasu Jihohin sun xarar wa saura, wasu kuma lamarin na su sam babu daxi, ta yanda ba su mayar da hankalin su sosai a fannin na ilimi ba.” Jihohin da ke can qasa a wajen samun damar shiga Jami’o’in sun haxa da, Jihohin Yobe, Zamfara, Jigawa da kuma birnin tarayya Abuja. A shekarar 2011, birnin tarayya shi ne a can qasan qarshe da xalibai 24 kacal da suka sami shiga Jami’a domin karanta fannin aikin na Likita. Ta sake komawa baya a shekarar 2012, da xalibai 20, 46 a shekarar 2013, 38 a shekara 2014 sai xalibai 40 a shekarar 2015. Su ma wasu Jihohi shida suna da sakamako marar daxi a fannin shiga Jami’o’in domin karatun aikin Likita. A shekarar 2011, Jihar Yobe tana da xalibai 64 kawai da suka sami shiga Jami’a domin karatun na aikin likita, Jihar Zamfara ta

biyo bayanta da xalibai 68, Jihar Jigawa tana gabansu da xalibai 74, a sa’ailin da Jihar Taraba ke da xalibai 82 da suka karanci Likitancin a wannan shekarar. Hakanan, a shekarar 2012, Yobe xalibanta a wannan fannin su 36 ne, sai Jihar Bauci mai xalibai 48, Adamawa tana da xalibai 56, Zamfara kuma tana da xalibai 69 ne kacal. A shekarar 2013, Jihar Zamfara tana da xalibai 117 ne, sai Jihar Adamawa da ke biye da ita da xalibai 121, Jihar Yobe tana da xalibai 124, Jihar Taraba tana da xalibai 128. A shekarar 2014, Zamfara tana da xalibai 49 ne, Kebbi kuma tana da 78, Jihar Nasarawa tana da 106, Jigawa na da 108. Hakanan a shekarar 2015, Zamfara tana da xalibai 54 ne, Kebbi kuma tana da 95, Sakkwato tana da 105, Jigawa kuma tana da 111. Mista Soweto, ya ce, mafi yawan kuxaxen da a kan ware domin tallafawa Ilimin a Jihohin da ke na kashin baya, musamman ma Jihohin Arewa, ana karkatar da su ne wasu wuraren na daban a bisa son rai. Ya ce, matsalar tana samo tushe ne daga lalacewar makarantu a yankin, da kuma rashin qwararrun malamai a makarantun.


labarai 5

A Yau Litinin 12 Ga Maris, 2018 (23 Ga Jumada Thani, 1439)

Rikicin Makiyaya: Kuskure Ne A Riqa Kiran Mahara Da Sunan Fulani —Atiku Daga Umar A Hunkuyi

Tsohon mataimakin Shugaban Qasar nan, Atiku Abubakar, ya nu na fusatan sa kan yadda ake qoqarin shafa wa wata qabila laifin kashe-kashen da ke faruwa a sassan tsakiyar Arewacin Qasar nan. Tsohon mataimakin Shugaban Qasar, ya qarfafa cewa, kamata ya yi a tuhumi mutanan da suka aikata laifi a kan kawukan su, ba tare da an mayar da laifin a kan qabilar da suka fito ba. “Sam bai da ce ba, yanda ake amfani da kalmar, ‘Makiyaya makasa, ko kuma Fulani makasa,’ Mista Atiku ya yi wannan jawabin ne a cikin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai. Manema labaran, sun tambayi Atikun ne cewa, a matsayinka na xan asalin qabilar Fulani, me za ka ce a kan matsalar tsaro da ake yawan samu a sassan qasar nan, musamman wanda makiyaya Fulani ke aikatawa?” Bayan ya bayar da amsa ne a kan dalilan da ke haddasa rikicin da suka haxar da zargin da yake yi wa shugabanni, qarin yawan al’ummu, da kuma canzawan yanayi, sai ya qarqare jawabin na shi da bayyana cewa, Fulani fa mutanan kirki ne. “Idan masu garkuwa da mutane suka kama mutane, ba ma cewa, ‘yan qabila kaza ne suka aikata hakan, mukan kira su ne kawai da sunan masu garkuwa da mutane kawai. “Ana iya samun mutanan banza, wasu za su iya kasancewa Fulani ne, wasu kuma za su iya kasancewa ba su ne ba, kamata ya yi mu riqa kiransu da ayyukan da suka aikata.”

•Alhaji Atiku Abubakar

Wannan bayanan na Atiku, suna qarfafa bayanan da gwamnatin Buhari ne ta yi, a yanayin da ake bayar da rahotannin rikicin na makiyaya. A watan Fabrairu, Kakakin Shugaban qasa, Garba Shehu, ya zargi wani sashe na manema labarai da suke cin mutuncin aikin na su na yaxa labarai, da ma karya dokokin aikin na jarida. Inda yake cewa, “Muna son mu tabbatar maku da cewa, wani sashe na masu yaxa labarai a qasar nan, suna wuce makaxi da rawa.” An yi tattaunawar ce, daidai lokacin da ake samun qaruwar tashe-tashen hankulan da ake danganta su da makiyayan, musamman a sashen tsakiyar arewacin Nijeriya. Wasu hare-hare da aka kai a

wannan shekarar kaxai, sun yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 500, a sashen. A makon da ya gabata kaxai, an kashe gomomi a harin da aka kai kan qabilar Fulani da ke zanne a yankin Gembu da kuma sauran sassan da ke yankin na Mambila, ta Jihar Taraba. Amma masu sharhi na zargin kafofin yaxa labarai da laifin qin yayata hare-haren da ake kaiwa a kan qabilar ta Fulani, ko ma a wasu lokutan suna bayar da rahoton harin da aka kaiwa Fulanin a matsayin wai su Fulanin ne ma suka kai harin. “Wasu ‘yan jaridun sun jahilci yadda tsarin qabilun arewacin qasar nan suke ne,” in ji Aliyu Tilde, wani malamin Jami’a wanda ya yi ritaya a Jihar Bauci. “Sashen

yaxa labarai na qasar nan, duk ‘yan kudu ne suka mamaye shi, sannan kuma suna da qarancin ilimi a kan yanda arewacin qasar nan take.” Ya bayyana silar rashin fahimtar da ‘yan jaridun na kudu suke da shi a kan sashen na arewacin Nijeriya, wanda ya samo asali tun lokacin bayan samun ‘yancin kan qasar nan, inda xaya daga cikin waxanda suka shirya juyin mulki na farko a qasar nan ya rubuta littafi. “Matsalar ta samo asali ne tun lokacin da Adewale Ademoyega ya rubuta littafi mai taken, ‘Dalilin da ya sa muka kai farmaki,’ ko kuma a turance, ‘Why We Struck,’ inda a littafin na shi ya yi qoqarin nu na qabilar ta Fulani a matsayin mugayen mutane tun a sashen farko na littafin

na shi. “Tun daga lokacin, littafin ya zamewa ‘yan jaridun na kudancin qasar nan wani ma’auni da suke auna Fulanin da shi, wanda kuma shi ne har zuwa yau xin nan suke amfani da shi. Tilde, wanda manomi ne shi a halin yanzun, ya ce, kamata ya yi manema labarai su fahimce sarqaqiyar da ke tattare da kashe-kashen da ake yi a arewacin qasar nan kafin su je suna yayatawa al’umma. “Aqalla akwai abubuwa uku da ke tattare da rikicin da ake yi. Na farko rikicin Manoma da Makiyaya, wanda ya samo asali kan qarancin filayen noma. “Rikici na biyu ana yinsa ne a kan qabilanci, inda ake samun wasu qabilun suke hanqoron a bar su su kaxai a sashen da suke domin su mamayi yankin na su har abada. “Na uku, rikici ne kawai na mavarnata, waxanda suke amfani da gazawar jami’an tsaro suna aiwatar da mugayen ayyukan su. A wasu lokutan, masu aikata laifin sukan kasance Fulani ne, amma ba kodayaushe ba. Tilde, ya ce, za a iya taqaita tashe-tashen hankulan, musamman waxanda suke da alamun qabilanci ko na addini, in an bayar da rahotannin su tare da nu na fasaha da kuma qwarewa. Ya bayar da misali da wani abin da ya faru a farkon watan Fabrairu, inda aka kashe wasu Fulani matafiya Takwas, a ka kuma qona gawarwakin su a Gboko, ta Jihar Benuwe, inda ya ce, da farko ma manema labaran sun qi su yayata faruwar lamarin ne, ta hanyar qin faxin ainihin ko su wane ne aka kashe.

Qungiyar RIFAN Ta Soma Rabon Bashin Da Ta Samo Wa ’Ya’yanta Daga Ibrahim Muhammad Kano

Shugaban qungiyar masu noman shinkafa a jahar reshen Kano. da akafi sani da ‘RIFAN’ Alhaji Abubakar Haruna Aliyu ya ce zuwa yanzu manoma a jahar na karvar tallafin bashin noma da qungiyar ta yi jagaban samowa daga babban bankin qasa da aka bai wa manoman shinkafar. Alhaji Abubakar ya ce an kawo daidaito a matsalar da ta kunno kai yayin qaddamar da shirin a

garin Kura, saboda rashin sanin tsarin da aka zo da shi, amma daga baya an sami fahimta an baiwa manoman kayayyakin da aka tanadar a tsarin. Ya qara da cewa ana baiwa kowane manomi abin da ya kama daga ’yan kuxi bayan an ba shi kayan noman da aka tanadar wa shirin. Alhaji Abubakar Haruna Aliyu ya ce, wannan shiri ya samo asali ne a sakamokon gazawar Gwamnatin Kano wajen wucewa manoman gaba wanda a cikin shekara ta 2016 Babban Bankin

qasa da haxin guiwar Gwamnatin Kano da Bankin manoma na qasa, ta ba da irin wannan tallafi ga manoma amma saboda jan qafa da Gwamnatin Kano ta yi manoman shinkafar ba su kai ga samun tallafin ba. sai kusan qarshen damuna, hakan ta sa yawanci suka kasa biyan bashin, ba kuma wani abu da aka yi rani da damina a bara na tallafa wa manoman. Ganin kar a sake samun matsala, qungiya ta shiga wannan shiri da Babban

bankin qasa dan ta sami damar cika manufar shugaban qasa Buhari na noma shinkafar da za ta wadatar da al’ummar qasa batare da sai an sayo shinkafa daga waje ba, wanda a baya su suka riqa kira a yi hakan. Ya ce, Babban bankin qasa ya amince zai bai wa manoma 1, 000, 000 qarkashin RIFAN, Sai qungiya ta ce, za a soma da 100, 000 dan guje wa samun mishkila aka tattaro manoma wanda aka sani tun daga mazava, qaramar

hukuma da jaha wanda shugabancin jaha ya tsaya musu. Qungiya ce ta zo da tsarinta na tantance wanda za a yi wa rijista da ba da kayan . Ya ce a shirin baya manoma 5, 540, 000 suka anfana da kuxi N164, 710 aka ba wannan bashin, saboda rashin biya Gwamnatin Kano ta ja baya, mun ba da shawarar kafa kwamitin kar-takwana dan karvo bashin nan, wanda yanzu haka an yi an soma karvo bashinn na baya.


6 labarai

A Yau Litinin 12 Ga Maris, 2018 (23 Ga Jumada Thani, 1439)

Mutuwar Akwe Doma Wa’azi Ne Garemu, Inji Al-Makura Daga Zubairu T.M.Lawal lafia

A jiya ne aka gabatar da zana’izar tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Alhaji Aliyu Akwe Doma. Marigayin ya rasu ne sakamakon rashin lafiya da ya yi fama da ita. Inda kuma ya yi jinya a qasar Isra’ila inda a can ne ya cika tun ranar Talatar da ta gabata. Wakilinmu ya samu jin ta bakin Gwamnan Jihar Nasarawa,Alhaji Umar Tanko Al-makura kan yadda ya ji da wanan rashin. Gwamnan ya bayyana alhini dangane da rashin. Gwamna ya ce; “Inna lillahi wa inna Ilahir raji’un. “Mutuwan Gwamna Ali Akwe Doma ba qaramin rashi ba ne ga al’ummar wannan Jiha. Saboda Idan aka tuna yadda Gwamna Aliyu Akwe Doma ya bauta wa Jihar Nasarawa tun tana Arewa har ta koma lardin Binuwai ta kuma koma Filato, ta dawo Nasarawa. “Mutuwar Marigayi Doma ta girgiza ni sosai. Tsohon gwamna Aliyu Akwe Doma mutum ne da tarihi ba zai tava mantawa da shi ba, saboda irin faxi tashin da yayi wajen samar da haxin kan al’ummar

• Dandazon mahalrta jana’izar Marigayi Aliyu Akwe Doma

wannan Jihar.” inji shi Ya ce; “Gwamna Aliyu Akwe Doma shi ne Gwamna na biyu cikin Gwamnatin farar hula da suka muke wanan Jihar. Gwamnan ya taka rawar gani wajen kawo ci gaba da haxa kan al’umma. Mutuwar Gwamna Doma ta zama wa’azi garemu, saboda duk mai rai wata rana mamaci ne. Gwamnan yayi addu’ar Allah ya jiqan tsohon

gwamna, Marigayi Ali Akwe Doma ya kuma gafarta masa zunubansa. Ya haxa kan ‘ya’yansa, Ya ba su haqurin wannan babban rashi da ya same su. Idan dai ba a manta ba an kawo gawar Marigayi Aliyu Akwe Doma Nijeriya ne a ranar Asabar kimanin qarfe 12 na rana. Inda jirgin da ya xauko marigayin ya sauke gawar a Babban Filin jirgin

saman Nmandi Azikwe dake Abuja. Daga nan aka wuce da shi zuwa garin Lafia, Hedikwatan Jihar Nasarawa kafin kuma a ka wuce da shi zuwa mahaifarsa, wato garin Doma. An gabatar da sallar Jana’izar marigayi Alhaji Aliyu Akwe Doma a filin makarantar Islamiyya dake garin, qarqashin jagorancin Babban Limamin garin na

Doma, Sheikh Hassan Jibril. An gudanar da sallar ne da karfe 11 na safe, wanda kuma dubban jama’a, maza da mata suka yi tururuwar halartar sallar. Bayan kammala sallar Jana’izar ne kuma aka raka gawar zuwa makwancinsa. Jama’a da dama sun koka da nuna damuwa na rashin tsohon Gwamna Aliyu Akwe Doma.

Mai Talla Shi Ke Da Riba:

LEADERSHIP A YAU Ta Shirya Tsaf! Kamar yadda kowa ya sani ne, wannan jarida mai albarka, LEADERSHIP A YAU ta kafa tarihi wajen zama jaridar Hausa da ta fara fitowa a kullum. Wannan fara fitowa a kullum yana da alfanu masu yawan gaske, gare mu Kamfanin LEADERSHIP da ku masu karatu, musamman masu sana’o’i manya da qanana. Wannan ne ya sa muke farin cikin shaida wa masu karatunmu cewa mun shirya tsaf domin tallafa wa kasuwancinku, ta hanyar tallata maku shi zuwa inda ba ku zata ba. Domin a halin yanzu mu kanmu da muke buga wannan jarida ba za mu iya bayyana iya inda ta ke shiga ba. Muna da tsare-tasare da dama don talla ku da hajojinku, inda muka fitar da tsarin ‘IYA KUXINKA IYA SHAGALINKA.’ Wato akwai cikakken shafi, akwai rabi, akwai kwata, akwai kuma daidai iyaka abin da mutum ke so a sanya masa. Wanda a wannan shafin muna so masu sana’o’i, musamman manyan dillalai su tallata hajojinsu, su qananan ’yan kasuwa akwai

nasu tsarin. A wani tsarin ma da muke da shi, akwai yanayin da mutum zai tallata hajarsa, sannan ya tallata kansa, inda za a sanya hoton shagonsa, hotonsa da kuma taqaitaccen tarihinsa, kuma wannan duk a kuxi kaxan. Maza ku kasance cikin kashi na farko na masu cin moriyar wannan shiri. Ina ’yan Canji, dillalan yaduka, masu kayan masarufi, mayan da qananan ’yan tireda, dillalan magunguna, masu kamfoni da masana’antu, dillalan hatsi, dillalan mota, masu sayar finafinai da dai sauran masu sana’o’i, ga dama ta samu. A tuntuvemu a lambarmu ta 08148507210, 07036666850, 08039216372, 07037934034, 08032875238 da 08038011382: email leadershipayau@gmail.com. Ko kuma a tuntuvi wakilanmu na jihohi don qarin bayani.


A Yau Litinin 12 Ga Maris, 2018 (23 Ga Jumada Thani, 1439)

Burinmu Shi Ne Mu Sauqaqa Muku

Ba a chaj in kuxin on ka cire d i j a h c a a B saqonnin watin waya kuxi daga ak na wasu banku

Da zaran an buxe asusu da mu, za a morewa rashin chaji idan mutum ya cire kuxi a akwatin wasu bankuna, haka kuma ba za a riqa cire kuxin saqonnin waya ba.

Domin cimma nasara a hada-hadar banki, ka yi mu’amala da bankin Sun Trust a Yau Ziyarci: www.suntrustng.com

talla 7


8 talla

A Yau

Litinin 12 Ga Maris, 2018 (23 Ga Jumada Thani, 1439)

Gaba dai! Gaba dai “Super Eagles”

Bankin Zenith na taya ‘yan qwallon Nijeriya “Super Eagles”, murna sakamakon nasarar da suka samu ta kai wa gasar Cin Kofin Duniya wanda za a gudanar a qasar Rasha.


A Yau

Litinin 12 Ga Maris, 2018 (23 Ga Jumada Thani, 1439)

TALLA 9


10 LABARAI

A Yau

Litinin 12 Ga Maris, 2018 (23 Ga Jumada Thani, 1439)

Yadda Tagwaye Suka Nemi Yin Rufa Ido A Jarabawar JAMB A Maiduguri A n c a f ke wasu tagwaye masu suna Hassan da Hussaini a garin Maiduguri a lokacin da ake tsaka da gudanar da jarabawar share fagen shiga jami’a. ’Yan biyu ne an kamasu da zargin satar amsa a yayin gudanar da jarabar samun izinin shiga manyan makarantu wato (UTME) a cibiyar zana jarabawar da ke jami’ar Maiduguri babban birnin jihar Borno, lamarin ta faru ne a ranar Asabar a ciki gaba da zana jarabawar a Nijeriya. Babban jami’in da ke kura da jarabar ta JAMB, Mr. Babagana Gutti, shi ne ya shaida hakan wa kamfanin dillancin labarai ta Nijeriya, ya bayyana cewar ‘yan biyun jami’an tsaro ne suka kamasu a ranar Asabar xin a garin na Maiduguri. Gutti ya ce, ‘yan biyun sun yi amfanin da kamanninsu inda suka so su yi wasan rainin wayo wa jami’an, a yayin hakan ne kuma jami’an tsaron suka bankaxo shirinsu, inda aka ga xaya a waje, aka shigo cikin xakin zana jarabawar ma aka sake ganin irin wannan fuskar, wannan dalilin ne ya sanya masu lura da zana jarabawar suka sanya shakku kan wanda suka tarar na zanawa, hakan ne ya janyo hankulansu bincike da Daga Khalid Idris Doya

• Shugaban Hukumar JAMB

xan gudanar da tambayoyi. “Xan ya zo cibiyar zana jaraba a madadin xan uwansa, ka san suna kammani”.

Jami’an kula da jarabawar ta JAMB ya ci gaba da bayanin cewar Hussain Abdulhammeed wanda aka kama a sakamakon shaidar shigar

da bayanai ta gwaji na na’ura mai kwakwalwa (CBT), ya qara da cewa, shi kuma xan uwansa mai suna Hassan Abdulhameed ya shiga zana jarabawar a madadin xan uwansa Hussaini ne. Ya ce, “Gaskiyar magana mu ba mu iya ganowa ko kuma zargin hakan ba, har sai da xaya daga cikin masu bibiyar jarabawa ya zo domin bincike sai yake shaida cewar sun gano xayan yana wajen hall xin zana jarabawar,” “Izowar mai binciken ya tambayesa wasu ‘yan qalilan xin tambayoyi kan jarabawar da kuma bayanai amma bai gamsu da amsoshin da ya bayar ba; don haka ne ya fito da wanda yake zana jarabawar da kuma xayan da ke kama da shi a wajen domin bincike. Abun mamaki kuma sai muka samu bincike ya nuna cewar Hassan ya zo wajen zana jarabawar a madadin xan uwansa Hussaini ne,” Shugaban da ke sanya ido kan jarabawar, wato Gutti ya bayyana cewar nan take ne kuma suka yanke hukuncin dakatar da jarabawar ‘yan biyun gami da kuma miqasu ga jami’an tsaro don ci gaba da bincike. Hassan da Hussainin dai sun xan baiwa jami’an wahalar ganewa, kasantuwarsu masu kammanin da junansu.

Hukumar Kiyaye Haxurra Ta Karrama Masari A Katsina Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

Daga Sagir Abubakar, Katsina Hukumar kare haxurra ta qasa ta miqa tambarin yabo ga Gwamna Aminu Bello Masari domin karrama shi akan gudummawar da yake badawa wajen bunqasa ayyukan hukumar a jihar nan. Kwamandan hukumar mai kula da shiyya ta xaya dake Kaduna, mataimakin Corp Marshall Bulus Darwana ya miqa ma Gwamnan lambar yabon a gidan gwamnati. Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana jindaxinsa bisa yadda hukumar ta fahimci gudummawar da gwamnatin jihar Katsina ke badawa akan al’amuran da suka shafi kula da hanyoyi. Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana cewa rage yawan afkuwar haxurra kan hanyoyi nauyi ne, da ya rataya wuyan gwamnati, xaixaikun

al’umma da kuma sauran hukumomin da abin ya shafa. Gwamnan ya bayyana cewa xaukar kayayyaki fiye da qima da kuma fasinjoji ke yi ya zama abin damuwa, ya qara da cewa ya kamata a xauki qwararrun matakai domin shawo kan matsalolin. Ya bayyana cewa tuni gwamnati ta aike da wata doka ga majalisar dokoki ta jiha akan buqatar kafa hukumar kula da dokokin hanya domin tallafama qoqarin hukumar kare haxurra ta qasa. Alh. Aminu Bello Masari ya yi kira ga hukumar da ta qara qaimi wajen duba ababen hawa, rajistar lambobi da kuma lafiyar ababen hawa a matsayin wasu matakai na kare rayuka da dukiyoyi. Haka kuma gwamnan ya buqace su da su maida hankali wajen vullo da hanyoyin wayar da kan al’umma akan muhimmancin kula da dokokin hanya.

• Shugaban Hukumar FRSC ta Qasa

Ya bada tabbacin cewa gwamnatin jiha za ta cigaba da samar da dukkanin tallafin da ya dace ga hukumar domin cimma nasarori da ake son

cimmawa. Tun da farko, mataimakin Corp Marshall mai kula da shiyya ta xaya dake Kaduna Bulus Darwang yace miqa lambar yabon ga gwamna

Aminu Bello Masari wani vangare ne na bikin cika shekarun hukumar talatin cif-cif a inda ake karrama mutane da suka taka muhimmiyar rawa ga


LABARAI 11

A Yau Litinin 12 Ga Maris, 2018 (23 Ga Jumada Thani, 1439)

Uwar Gidan Gwamnan Sakkwato Ta Qaddamar Da Na’urar Busar Da Amfanin Gona Daga Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto

Uwargidan Gwamnan Sakkwato, Hajiya Mariya Aminu Waziri Tambuwal ta bayyana cewar muhimmancin makamashin hasken rana ya fi gaban a nanata wanda a bisa ga tasiri da alfanun da yake da shi zai iya zama babbar hanyar samar da makamashi tare da magance matsalolin wutar lantarki da a ke fuskanta a qasar nan. “Abin da qasar mu ke buqata shine jajircewa, samar da kuxaxe da aiwatar da shiraruwa wanda kuma a gabana a yau xaya ne daga cikin irin wannan hovvasa wadda Hon. Abdussamad Dasuki ya yi domin amfanin al’ummarsa.” Uwar Gidan Gwamnan ta bayyana hakan ne a yayin da take qaddamar da katafiyar Na’urar Musamman ta Busar da Amfanin Gona Mai Aiki da Hasken Rana ta miliyoyin Naira a garin Dogon-Daji da ke a qarqashin Mazavar Tarayya ta Kevve/Tambuwal a ranar Juma’a domin murnar zagayowar Ranar Mata ta Duniya tare da yaye matan da aka baiwa horo kan shirin na musamman. Na’urar ita ce irinta ta farko da aka samar a wata Mazavar

Tarayya a Sakkwato. Ta ce “A matsayina na uwar wannan taron, ina son in bayyana cewar wannan aikin abin yabawa ne. Wannan kaxai ya nuna cewar an qarfafawa matan wannan yankin domin su gudanar da abubuwan da a can da ba za su iya ba. Haqiqa alfanun da matan mu za su samu a dalilin wannan aikin ba zai misaltu ba.” In ji ta. Uwar Gidan Gwamnan wadda ta qaddamar da na’urar tare da taimakawar Uwargidan Xan Majalisar, Hajiya Jamila Dasuki -Wada ta kuma buqaci matan da suka amfana da su yi aiki da na’urar yadda ya kamata tare da kare ta daga lalacewa. Ta ce idan mata suka rungumi sana’a to ba za su fuskaci qalubalen rayuwa ba. Hon. Abdussamad Dasuki Xan Majalisar da ke Wakiltar Mazavar Kevve/Tambuwal kuma Shugaban Kwamitin Sojojin Ruwa A Majalisar Wakilai ne ya samar da na’urar ta (Solar Powered Farm Produce Dryer) domin bunqasa aikin gona da samar da aikin yi ga al’ummarsa. Qungiyoyin mata tara ne masu mutane 15 kowanne suka ci gajiyar shirin na farko a matsayin na gwaji wanda kuma za a yi a garuruwan Kevve da Tambuwal tare

•Hajiya Mariya Aminu Tambuwal

da tallafin Naira 50, 000 ga kowace qungiya domin su sayi kayan amfanin gona. Bakixaya mata 135 ne za su ci gajiyar shirin irinsa na farko. Da take gabatar da jawabin qwararru kan shirin da abin da ya qunsa, Hajiya A’isha Dasuki ta bayyana cewar an assasa shirin ne domin tafiya da zamani da samar da aikin yi tare da kaucewa qalubalen da ake fuskanta na lalacewar amfanin gona. “Wannan na’urar ta na

busar da kayan amfanin gona a cikin kwanaki biyu zuwa uku. Ta kan busar da tumatur, albasa, lawashi tarugu, tattasai, kifi da nama. Na’urar ta na da batur ta na kuma amfani da hasken rana wadda Allah ya albarkace mu da ita. Muna da matsalar adana kayayyaki amma idan aka yi amfani da wannan na’urar to ta na hana kaya lalacewa a lokacin kakar su wadanda kuma za a ci moriyar su a lokacin da suke

da wuyar samu kuma suka yi tsada.” In ji ta. A’isha Dasuki ta kuma bayyana cewar za ta jagoranci samo masu sayen amfanin gonar domin ganin waxanda suka amfana sun samu kuxaxen shiga tare da fatar nan gaba kadan yankin zai zama xaya daga cikin yankunan da ke fitar da busassun kayan amfanin gona. Haka kuma ta yi kira ga matan da su kasance masu tsafta.

Sheikh Abduljabbar Ya Buqaci Matasa Su Qaurace Wa Tsattsauran Ra’ayin Addini Daga Khalid Idris Doya

Shararren Malamin addinin Islama, wanda yake zauna a Birnin Kano, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya gargaxi matasa da su qaurace wa biye wa tsatstsauran ra’ayin da za su iya fidda su daga haqiqanin layin addinin Musulunci, haxe da jefa su cikin wani ruxani da sunan addini. Shehin Malamin ya ce, aqidun da suke tsattsaurawa su ne ke haifar da mafiya yawan ta’addanci a duniya a halin yanzu. ya kuma ce, akwai gayar buqatar a kawo qarshen wannan lamarin. Shaikh Abduljabbar ya yi wannan kira ne ne a makon da ya gabata, lokacin da yake tattaunawa da manema labarai jim kaxan bayan kammala babban taron rufe bukukuwan maulidi, wato ‘Khatama’ wanda

qungiyar ‘Qadirriyya Riyadul Jannah Movement’ suka saba shirya wa a birnin Kano. Sheikh AbdulJabar ya bayyana cewa, dukkanin kakkausar ra’ayin addini na haifar da munanan halayya na ta’addanci a duniya. Suna samo asali ne daga matasa a sakamakon rashin bin tafarkin da ya dace a sane ko rashin sani. Ya ce, “Ya kamata matasa su qauracewa wa dukkanin zunuban da suka sava wa qa’idodin da addini ya shimfixa, sannan kuma akwai gayar buqatar matasa su kauce wa munana ko kuma tsattsauran aqidun da za su kai su ga haifar da rikici ko tashin hankali. Abin takaici ne ka ga matasa suna shiga abubuwan da ka iya kawo tashin hankali a tsakanin al’umma,” inji shi. Malamin ya kuma bayyana cewa, haqqi ne da ya hau kan malamai da jagororin addini

da su farka gami da tashi tsaye wajen ilmantar da matasa haqiqanin koyarwar addinin musulunci don kauce wa haifar da matsaloli a cikin al’umma. Sheikh Kabara ya bayyana cewa, wannan maulidin na ‘Khatama’, ana gudanar da shi ne a duk shekara, ya bayyana cewar yau sama da shekaru 10 kenan ana gudanar da wannan gagarumin taron wanda ke haxa malamai, da sauran musulmai daga sassa dabandaban na duniya. Ya ce, kasantuwar yawan gayyace-gayyace da ake yi masa a sassa daban-daban na duniya domin gabatar da wa’azin maulidi da bukukuwar maulidin, ya bayyana cewar hakan bai ba shi damar halartar kowanne daga ciki, don haka ne yake shirya wannan gagarumin maulidin da aka sanya masa suna Khatama domin waxanda suke almajiransa da bai samu zuwa yankin nasu ba su samu

•Sheikh Abduljabar Kabara

zarafin halartar taron. LEADERSHIP A Yau ta fahimci cewa, wannan taron ya haxa mahalarta daga sassan jahohin Nijeriya 36 da kuma wasu yankuna a shiyyar Afirka, haka kuma wakilinmu da ya halarci taron ya bayyana

mana cewar a kowace shekara malamin na amfani da wannan damar wajen tattauna muhimman abubuwan da suka shafi rayuwar jama’an qasa da na duniya kai tsaye domin samar da gyara ko kuma mafita wa jama’a.


12

A Yau

Litinin 12 Ga Maris, 2018 (23 Ga Jumada Thani, 1439)

Hatsin Bara Tare da Huzaifa Dokaji

arabiandokaji@gmail.com 08135353532

Mene Ne Tarihi? Ra’ayin Karl Marx (1818- 1883) Shehun malami Karl Marx, mutum ne da ya tafiyar da rayuwarsa akan tafarkin wayarwa da marasa qarfi kai, akan yancin su da kuma abin da ya kamata su yi domin kwatar wannan yancin. Canjin fasalin rayuwa da Turai ta samu sakamakon bunkasar kimiyya a qarni na 17 da fasaha a qarni na 19, ya sa hanyoyin samar da ababen mora rayuwa suka sauya. Daga kirar hannu, masana’antu suka dawo kirar injina. Wannan yasa mutanen da ke neman abinci, suka koma bayi a masana’antun. Burin tara dukiya fiye da bukata da wannan sauyi ya haifar, ya kara tazarar dake tsakanin talaka da mai kudi, da kuma tsakanin masu masana’antu da ma’aikatansu. Kasancewar masana’antu na kwana suna aiki, mafi akasarin gidaje, wadanda sune ginshikin gina al’umma ta gari, suka dakushe, su ka kuma rasa alkibla irin ta manufa. Yawaitar shegu saboda cakuduwar maza da mata da kuma kwana a kamfani da aka samu, rayuwa ta kara kazanta. Albashin da ake biyan ma’aikata baya fin 1% na abin da ma’aikatan ke samarwa kamfani. Wannan ta jawo rikicerikice na neman lallai sai an sauya wannan kashin dankalin. Ko da yake an samu kafuwar kungiyoyin kwadago da suke wakiltar ra’ayi da manufar ma’aikatan, sai dai kuma masu hannu da shuni, da gwamnati na amfani da su wajen juya akalar asalin dalilin kafa su. A irin wannan hali, duniya ta fara jin amon Karl Marx. Marx ya tashi a cikin al’ummar da mai qarfi yake danne mara qarfi. Arziki ya zama mallakin wasu mutane, wanda idan ba a cikin su kake ba, ba yanda za su barka ka shiga. Wanda aka haifa a talauci, a talauci yake mutuwa, wanda kuma aka haifa a arziki, a cikin sa zai mutu. Marx ya yi kokarinya samawa rayuwa ma’ana ta fuskar nazarin tarihi da matakan da ya bi har aka zo yau. Marx ya fara kallon duniya ne da sigar makarantar tarihin Hegel, sai dai fa darasin makarantar, bai ba shi amsar wasu jiga-jigan tambayoyi da yake da su ba, wadanda kuma ya yarda su ne jigon kafuwar tarihi da kuma rushewarsa. Marx ya dabbaka cewa lallai fa mataki ne haifar da tunani, ba wai tunani ne ke haifar da mataki ba. Hikimar Marx ita ce, ko wane tsuntsu dai kukan gidan su yake. Tunanin mutum, da yanda yake kallon rayuwa, na samuwa ne daga mataki da matsayinsa a cikin al’umma. Talaka na ganin duniya ne da idon talauci, mai kudi kuma na ganinta ta fuskar wadata. Daliban Marx sun kasa al’umma zuwa uku. Akwai masu mulki (governing class), akwai masu fada aji wato filogai (ruling

class) akwai kuma talakawa. Kasancewar wanda masu fada aji suka goyawa baya ne ke samun nasarar mulki, Tarihi na faruwa ne a sanda aka samu canjin wannan aji na tsakiya. Bayan nazari na tsanaki, Marx ya ce tarihi na tafiya hannun da hannu da tattalin arziki. Dukkan matakan tarihi sun samu ne sakamon canji da aka samu a hanyar samar da dukiya. Tarihi ya fara ne daga zamanin Raba Daidai (Primitive Communalism), Bauta (Slavery Era), Sarauta (Feudal Era) kana aka gangaro zuwa zamanin Jari Hujja (Capitalist Era) wanda shine tsarin da ake ciki yanzu; sai kuma tsarin Gurguzu (Socialism/ Communism) da za a shiga a gaba. Matakin farko shine matakin da duniya ta samu janta a ciki ba tare da yunkurin wani ba. Mataki na biyu kuma, ya samu me sakamakon son kai da dan’adam ya koya a zamansa na duniya. Masu qarfi suka gane cewa babu dalilin da za su dinga wahala wajen samar da abincin da za su ci, tunda akwai masu raunin da za su iya tirsasawa su samar musu da shi kyauta. Sai dai tsananin zaluncin da ke zamanin, ya sa zamanin ya halaka kansa da kansa, sakamakon wayewa da Dan Adam ya kara samu. Zamanin sarauta kuma, a nan ne aka samar da barori da kuma iyayen daki, maimakon bawa da ubangijin kamar yamda yake a zamanin baya. Wadanan barori, suna bautar gidajen sarauta ne, maimakon bawa da ke bautar mai shi. Kasancewar wayon da Dan Adam ya kara ya fara hana shi bautar da mutane qarfi da yaji, saboda rikici na rashin dalili, sai mutane masu kwakwalwa suka kirkiri fasahar addini domin bautar da mutane. A gun Marx, a wannan zamani ne aka fara koyawa mutane cewa akwai ‘wani’ Allah a sama, wanda ya ke aiko annabawa, kuma dole a bi shi yanda yake dole su ma a bi su. Wannan ce ta sa akidar bata yarda da dukkan wani abu da ba za a ganshi, taba shi, shanshan shi ko jin sa ba (Materialism). Tunda babu wani abu da zai faru ba tare da goyon bayan masu mulki ba, sai wadannan addinai suka kirkiri wata kariya da take nuna cewa Allah ya halicci ahalin sarauta ne dama don su mulki duniya (Divine Rights of Kings). Wato cin hancinsu kenan ga masu mulki!. Wannan fahimta ta raba masu mulki aji biyu: ajin masu mulki bisa doron addini, wato annabawa da waliyai da limaman coci, wanda sune ke da iko akan lahirar mutane. Akwai kuma ajin masu mulki bisa doron sarauta, wadanda ke da iko akan duniyar mutune. Zamani na hudu shine

zamanin jari hujja, wanda dukiyar da zamani na uku ta taimaka aka haifar. A nan ma, wayon da Adam ya karu, maimakon bautar mutum ko gidan sarauta, sai aka dawo bautar kudi. Ana bautawa kudi ne ta hanyar jakadunsa, wato injina da masana’antu. Babu wanda zai tilasta wani ya zo ya masa bauta, amman kuma kusan kowa zai dinga bin mai wadata a bashi dama yazo masana’anta ya yi bauta don ya samu na tuwo. Wato kenan, maimakon aje farautar mutum, mutun ne da kansa yake kawo kansa. Sannan, ba wai masu qarfin tuwo ko na mulki ne ke jagorar duniya ba, masu qarfin arziki da wadata ne. A mahangar wannan akida ta Marx, marasa qarfin da ake dannewa (wato ma’aikatan kafofin samar da dukiya), za a je wata tukewa da za su tashi domin kifar da danniyar da masu wadatar ke yi. Wannan yunkuri kuma zai fara ne daga kasashen da suka fi ci gaba, da qarfin arziki. Sai dai, a nan, babban dalibin Marx, wanda kuma ya jagoranci juyin-juya halin farko da akai aka kafa wannan akida a aikace, wato Vladimir Lenin, ya ce akwai gyara a wannan gabar karatun da Malaminsa Marx ya bayar. Lenin ya ce, wasu masu hankali ne daga cikin mutane za su tashi su jagoranci wannan babban jihadin gyaran tattalin arziki, tunda dai ya bayyana cewa da yawan mutane basu da hakalin gane ko rabe gaskiya da karya. Wannan sauyin ra’ayi na Lenin ya faru ne sakamakon ilimin zahiri da ya samu sakamakon kafa wanna akida a Daular Rasha da ya jagoranta a shekarar 1917. Ilimin karatu daban, ilimin kuma zahiri ko aiki shi ma wani abu ne na daban. Wanda ya karanta siyasa, ba zai sa baki ba, mafi akasari, idan wadanda suke siyasa na magana. Wannan yunkuri, shine zai kai duniya ga zangon karshe na tarihi, inda za a kuma daidaita samun kowa da kowa ya zama daya. Kowa zai bada gudunmawar

samar da abin duniya daidai qarfinsa, sannan kowa za a dinga bashi daidai abin da yake bukata. Kurun kus! Tarihi ya kare! Sai dai fa wanann karatu na Marx ya fuskanci kalubale iri-iri. Da fari dai, Marx yayi wa tarihi jadawali, tare da yi masa wani karatu irin na yan duba, masu ganin gobe! Misali, zatonsa na cewa juyi-juya halin Gurguzanci zai fara ne a kasashen da suka fi kowanne kafuwar jari hujja, bai zama gaskiya ba, domin Rasha, in da aka fara, na cikin kasashe ma fi koma baya a wancan lokaci. Birtaniya da take mafi ci gaba a bangaren, har yau bata samu kafuwar akidar ta Gurguzu ba. Na biyu, addini da Mrx ya kalla a matsayin wata guba da ake danne mutane a hanasu ci gaba, an yi amfani da shi a gurare da dama an kuma kawo ci gaba. Babban misali shine juyi-juya halin Shi’a na Iran, da aka yi a shekarar 1979. Abu na uku, daga shekarar 1993 da hadaddiyar daular Rasha ta karye, babu wata alama dake nuna cewa akidar ta Gurguzu zata game duniya. Kusan ma iya cewa akidar jari hujja ta cinye wannan duniya, babu kuma alamar tana da wata kishiya in ba Musulunci ba. Wannan ya kuma sabawa da ra’ayin Marx, wanda yake ganin duniya ta wuce zamanin addini, ta shiga na tuwo da miya. Abu na hudu, wanda Marx da kansa ya gyarawa kansa,

shine ikirarinsa na farko da ya yi cewa juyi-juya halin da zai kawar da jari hujja tilas wanda za a zubar da jini ne. A wani jawabi da ya yi a shekarar 1872 a kasar Switzerland, Marx ya ce, wasu kasashen (kamar ita Switzerland din) za su juya wannan canji ta hanyar demokradiyya. Abu na biyar, dolentawa Tarihi ginshikin rikicin tattalin arziki ya sa ana kalubalance shi da dauke kai akan rawar da dabi’un dan adam

irin farin ciki, bakin ciki, kiyayya, hassada da soyayya ke takawa a tarihi.


LABARAI 13

A Yau Litinin 12 Ga Maris, 2018 (23 Ga Jumada Thani, 1439)

Al’umma Na Da Rawar Takawa Domin Bunqasa Ilimin Kimiya Da Fasaha –Dakta Suwaiba Daga Daga Mustapha Ibrahim Kano

Sashen Ilimin Kimiyya da Fasaha na Jami’ar Bayero da ke qarqashin shugabancin Dakta Ali Idris ya shirya taron qasa a karon farko domin wayar da kan jama’a akan yadda za a bunqasa ilimin kimiyya da fasaha a wannan lokaci da ake fuskantar tattalin arziqi ta yadda za ayi iya qoqari na ganin an ciyar da wannan fanni gaba duk da irin wannan yanayi da ake ciki na yau. A yayin da take jawabi, Dakta Suwaiba Sa’id Ahmad shugabar kwamitin shirya taron na qasa da sashen Ilimin Kimiyya Da Fasaha na Jami’ar Bayero ya shirya. Ta ce, al’umma na da rawar

takawa domin bunqasa ilimin musamman ilimin kimiya da fasaha a wannan qasa ta ce an shirya wannan taro ne domin a tattauna matsaloli da suka damu wannan ilimi na a ga an warware dukkanin matsaloli da suke cima wannan sashen tuwo a qwarya da nufin magancesu. Dakta Suwaiba ta ce, masana da suka gabatar da jawaban su a wannan taro sun tabbatar da cewa mayan matsalolin da ake samu na raunin ilimi a wannan fanni yana samo a saline tun daga matakin Firamare, da Sakandare da wannan matsalolin wasu Xalibai suke zuwa Jama’a dan haka ne ake samun rauni wanda kuma maqasudin wannan taro a

tattauna su dan magancesu dan haka ta ja hankalin jama’a wajen tallafawa ilimin kimiya da fasaha domin wannan bai zama a ce komai sai gwamnati ta yi ba domin abu ne da ya ke da mahimmanci wajen cigaban al’umma. Tunda farko a nasa jawabin shugaban sashen Kimiyya Da Fasaha na Bayero Dakta Ali Idris ya ce wannan sashen yayi nisa wajan horar da Xalibai Sana’oin dogaro da kai kamar harkar Gyaran Motoci, Gina gine, Injina, Sarrafa Qarafa da kuma ilimin Halittu dana harhaxa Magunguna domin ciyar da Qasa gaba kamar yadda Qasashen Duniya irin su Tunusiya, Malesiya, Indunusiya, Singafo, Japan da dai sauransu suka ci gaba. •Dakta Suwaiba

Xan Majalisa Ya Buqaci Matasa Su Daina Bari Ana Amfani Da Su Don Cin Mutuncin Wasu Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Wani Xan Majalissar Dokoki ta jihar Bauchi ya yi kira ga matasa da su daina bari ana amfani da su wajen cin mutuncin mutane a lokacin yaqin neman zave, da kuma amfani da su ta hanyoyin da basu kamata ba a fagen siyasa. Xan majalisar Hon. Umar Sale Nabayi, wanda shi ne mai wakiltar qaramar hukumar Ganjuwa ta gabas a majalisar dokoki ta jihar Bauchi shi ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake miqa qautar mota ga wata qungiyar matasa mai buri haxe da manufar wayar wa jama’a kai don ganin APC ta sake lashe zave a shekara mai zuwa wato 2019, qungiyar mai suna ‘M.A Youth Mobilization For Continuity 20019’. • Dan Majalisar A Lokacin Da Ya Baiwa Ya’yan qungiyar kyautar mota Nabayi ya bayyana cewar matasa suna da gagarumar da kullum, sai ya buqaci da su shugaban qungiyar M.A Youth rawar katawa wajen kawo sauyi sarrafa motar ta hanyar da suka Mobilization For Continuity 20019 Alhaji Mahamud Yelwa a siyasance, amma idan suka yi dace. A jawabinsa na godiya, ya bayyana cewar godiyarsu ga wasa da damarsu kuma za su kasance wasu mutanen da ba za su amfani al’ummarsu ba, don haka ne ya yi fatan matasan da za su ke gudanar da abubuwan da suka dace domin kyalliya ta biya kuxin sabulu. Daga Sagir Abubakar, Katsina tarihi na Arewa dake Kaduna. Xan majalisar ya ce, ya bai Dr. Bashir ya bayyana Babban Sakataren Shugaban wa qungiyar mota ne saboda cewa hukumar zata cigaba da hukumar kula da adana kayan ta samu damar shiga lunguna bunqasa adana kayayyakin tarihi da al’adu na Jihar Katsina da saqona a faxin jihar domin tarihi na ciki da wajen jihar Dr. Bashir Aliyu Sallau Safana wayar da jan jama’a kan aikacenana. ya yaba da goyon bayan da aka aikacen gwamnatin jihar da Dr. ya kuma bada ba hukumar wajen xaga darajar kuma jagorancin APC a jihar, tabbaci ga hukumar da dukkanin kayayyakin tarihi ya yaba musu sosai da wannan ma’aikatan gidan adana kayan dake gidan adana kayan tarihi huvvasawar tasu. tarihi na Arewa dake Kaduna na Arewa dake Kaduna. Wannan kyutar motar, tana cewar jihar Katsina zata cigaba Babba shugaban zuwa ne a sakamakon wata da bunqasa kayayyakinta domin hukumar, wanda shine Sarkin ziyarar da suka tava kai masa a ta zama abin koyi ga sauran Askan Yariman Katsina ya faxi kwanakin baya, inda ya yi musu vangarorin dake cibiyar. hakan yayin da yake duba wasu alqawarin cewar zai samar musu Babban shugaban kayayyakin tarihi mallakar jihar da motar domin su samu gudanar hukumar ya buqaci masu Katsina dake gidan adana kayan da yanayin zirga-zirgansu a yau ziyartar gidan tarihi da yawon

xan majalisar basu misaltuwa a sakamakon cewar shi ne kusan na farko day a fara bai wa qungiyar irin wannan motar, sai ya sha

alwashin cewar za su tabbatar da yin amfani da motar wajen wayar wa jama’an jihar Bauchi kan don zavar nagartaccen kuma hazaqan shuwagabanin a kowani lokaci. Ya kuma bayyana cewar za su tabbatar da nuna wa xan majalisar farin cikinsu a aikace ta hanyar wayar wa jama’an yankinsa ta Ganjuwa kai dagane da kyawawan manufarsa na siyasa, ya kuma yi bayanin cewar wannan motar za su yi amfani da ita wajen shiga lunguna da saqona na jihar Bauchi don wayar da kan jama’a kan zave. Daga qarshe ya fuwace ‘ya’yan qungiyar da su mara wa shiryeshiryen gwamnati mai ci baya gami da kuma sake bai wa gwamnan jihar Muhammad Abubakar dama ta hanyar zavensa a 2019. Haka kuma, ya buqaci gwamnan Bauchin da ya ci gaba da zage damtse domin samar wa matasa aiyukan yi a kowani lokaci.

Ma’aikatar Tarihi Da Al’adu Na Samun Goyon Baya Yadda Ya Kamata –Dakta Safana buxe ido da xalibai musamman daga jihar Katsina dasu ziyarci xakin adana kayan tarihi na Arewa mallakar jihar Katsina da sauran kayayyakin hukumar dake Katsina. Haka kuma, yayi kira ga xaukacin al’umma dasu zama a matsayin masu ruwa da tsaki wajen haxin gwuiwa da hukumar domin bunqasa kayayyakin tarihi da al’adu. Shi ma da yake jawabi, Daraktan gidan adana kayan tarihi na Arewa dake Kaduna Farfesa Sule Bello ya godewa hukumar da ma’aikatan

hukumar adana kayan tarihi da al’adu dake jihar Katsina bisa qoqarin da suke wajen xaga darajar adana kayan tarihin. Daraktan wanda yayi magana ta bakin jami’in dake kula da cibiyar adana kayan tarihin Alh. Usman Suleiman ya bayyana cewa jihar Katsina na xaya daga cikin jihohin Arewa cikin qasar nan dake xaga darajar kayayyakin adana kayan tarihi. Ya godewa Gwamna Aminu Bello Masari bisa goyon baya da qarfafa gwuiwa da yake ba hukumar a vangarorin bincike da al’adu.


14 LABARAI

A Yau

Litinin 12 Ga Maris, 2018 (23 Ga Jumada Thani, 1439)

Gwamnan Gombe Ya Ba Xalibai 51 Da Suka Yi Zarra Aiki Daga Khalid Idris Doya

A shekaran jiya ne Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo ya bayar da damar xaukan aiki kai tsaye ga xaliban da suka yi zarra cikin waxanda suka kammala jami’ar jihar Gombe. Su dai xaliban sun kamala ne da sakamakon qwazo mafi qololuwa na ‘First Class’, waxanda suka samu wannan zarafin adadinsu ya kai mutum 51. Gwamnan Gombe, Dankwambo, ya sanar da qudirinsa na xaukansu aiki kaitsaye ne a yayin bikin yaye xaliban da suka kammala jami’ar na rukuni na 6, 7, 8 da na tara waxanda suka samu takardar shaidar jami’ar a matakin farko har zuwa aji huxu. Har-ila-yau, gwamnan ya kuma bayyana cewar gwamnatin jihar Gombe ta amince da xaukan su aiki

kai tsaye ga duk mai buqatar hakan a cikinsu, haxe kuma da basu tallafin naira dubu xari-xari ga kowanne xaya daga cikin xalibai 51 da suka yi zarran. Dankwambo ya bayyana cewa a qarqashin gwamnatinsa ta iya samar da cikakken amincewa wa ASUU da kuma yarjejeniya da gwamnatin tarayya, ya kuma qara da cewa tallafin karatu ma gwamatinsa ya na qoqari wajen bayarwa. A nashi jawabin, muqaddashin shugaban jami’ar jihar Gombe, Farfesa Ibrahim Musa Umar, ya ce, adadin xalibai dubu uku da xari tara da hamsin da uku 3,958 ne suka samu kammala jami’ar a wannan lokacin. Ya ce, xalibai da suka yi zarra suka kammala da lambar qwazo na xaya su 51 ne, adadin xalibai 864 ne suka fita da lambar sakamako na biyu mai

daraja, a yayin da kuma xalibai 1,945 suka fita da sakamako na biyu marar daraja ‘second class lower’, su kuma xalibai 1,038 suka kammala jami’ar da mataki na uku. Da yake jawabi a madadin NUC, Dr Bello Gidado Kumo, ya ce, hukumarsu za su amince da tsangayar ilimin lauya da wasu fannoni guda biyu a rukinin karatu na gaba na jami’ar. Wakilinmu ya labarto cewar jami’ar ta kuma karrama shugaban jami’ar kuma sarkin Gome Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III da kyautar Digirin girmamawa, sauran waxanda suka samu kyautar Digiri xin su ne Sakatariyar majalisar xinkin duniya Hajiya Amina J. Mohammed, Cif Christopher Kolade da kuma babban manajin darakto na bankin Access Bank PLC, Mr Herbert Wigwe.

• Gwamnan Jihar Gombe, Dankwambo

Mun Gamsu Da Ayyukkan Gyaran Asibitotin Mazavar Kebbi Ta Kudu, Inji Danhalima Zuru Daga Umar Faruk, Birnin-kebbi

Matasan garin Zuru sun bayyana gamsuwarsu ga ayyukkan gyara da ake yi ga manyan asibitoti gudu takwas da ke a mazavar Kebbi ta kudu a jihar Kebbi. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban matasan unguwar gidajen Shagari da ke a GRA Zuru, Malan DanHalima Zuru ya bayyana hakan ne bayan kammala wata ziyarar gani da ido kan yadda aikin gyaran asibitotin tawas ke gudana a yankin

masarautar Zuru da ke a jihar Kebbi. Shugaban matasan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya samu zantawa da jaridar LEADERSHIP A Yau a garin na Zuru a jiya. Inda yace “ mun gamsu da yadda a ke gudanar da aikin gyaran asibitotin”. Ya ci gaba da cewa asibitotin dai sun xauki lokaci suna bukatar gyara, amma sai a lokacin sanata Bala Ibn Na’Allah da ya gabatar da bukatar yin gyaran asibitotin ga majalisar dattijai domin ganin cewa mutanen da ya ke wakilta sun samu kula ta kiyon

lafiya da kuma inganta ruyuwa mutanen mazavar Kebbi ta kudu. Har ilayau shugaban yace ko bayan gyaran asibitotin tawas da ke a mazavar Kebbi ta kudu, sanatan ya yi waxanda su ayyuka da dama a mazavar Kebbi ta kudu kamar gayaran makarantun firamare da kuma kayan aiki kama daga litatafar, kayan wasanni , magungunna da kuma Samar da ruwan sha ga wasu garuruwa da kuma wasu makarantu duk a mazavar Kebbi ta kudu. Hakazalika sanata ya tallafawa mata da injimin

nika, telar xunki da kuma kuxaxen domin yin sana’o’i don su samu su dogaro da kansu. Yace matasa ko an baiwa wasunsu mashin da matoci domin suma su samu abin dogaro da Kansu, inda kuma matasa da su kayi karatu mai zurfi an samomusu aikin gwamnati a ma’aikatun daban daban na gwamnatin taraiya. Bugu da kari da cewa sanatan ya baiwa masarautar Zuru da Yauri matoti domin kungiyoyin ci gaban masarautun biyu su iya gudanar da ayyukkan ci gaban masarautun

biyu. Yace har ilayau ya bayar da tallafin jirajen ruwa da kuma matotin xaukar marasa lafiya da ke tsalaken kogin ruwa Neja a masarautar Yauri. Daga karshe yayi kira ga matasan mazavar Kebbi ta kudu da su ci gaba da ba Sanata Bala Ibn Na’Allah goyun baya da kuma amince da ya koma tsayawa takara a matsayin sanatan mazavar Kebbi ta kudu karo na biyu kan irin ayyukkan ci gaba da yayi a mazavar Kebbi ta kudu. Ya kuma ce “ amadadin matasan unguwar gidajen Shagari da ke GRA a Zuru,

Bankuna 17 Sun Sha Alwashin Tallafawa Gwamnatin Jigawa Wajen Bunqasa Aikin Noma Daga Munkaila Abdullah, Dutse

Kimanin Bankuna 17 ne suka quduri aniyar taffawa yunqurin gwamnatin jihar Jigawa na bunqasa fannin noma domin samarda ayyukan yi da kuma‎ bunqasa tattalin arziqi. Shugaban manajojin bankunan dake jihar ta Jigawa Alhaji Ibrahim Garba

ne ya bayyana haka ya yin tattaunawarsa da maneema labarai jim-kaxan bayan kammala walimar ranar ma aikatan banki wanda aka gabatar a Sansanin ‘yan bautar qasa dake Fanisau a birnin Dutse‎. Ya ce, bankuna a yunqurinsu na sauke nauyin al’ummar yankin da bankunan ke aiki, sun amince su tallafawa

shirye-shiryen gwamnatin na bunqasa aikin noma a jihar. ‎Shugaban, wanda shi ne kuma babban Manajan Bankin Sterlin reshen Dutse‎ ya ce na xaya daga tallafin bankunan marawa gwamnatin jihar baya wajen bunqasa shirin nan na Anchor Borrower. Sannan ya qara da cewa, bayan wannan kuma, akwai

shirye-shirye da dama waxanda bankunan suka shirya wanda za a gabatar nan bada daxewa ba. ‎Haka kuma ya bayyana cewa kasancewar Allah ya albarkaci jihar ta jigawa da ingantacciyar qasar noma wanda yawanta yakai kimanin hekta dubu 500, wanda masu bincike suka tabbatarda cewa hecta dubu 200 kawai ake iya

nomawa, to bakunan zasu bada gudummawarsu domin tabbatarda manoma na iya noma duk wannan qasar noma yadda jihar za ta iya ciyar da qasa baki xaya. Daga qarshe ya yi kira ga manoma da sauran al’ummar jihar da su kasance sun bude asusu da bankunan domin a cewarsa ita ce kaxai hanyar da zasu iya cin wannan ggajiya.


LABARAI 15

A Yau Litinin 12 Ga Maris, 2018 (23 Ga Jumada Thani, 1439)

PDP Ta So Ta Siye Mu Don Mu Yi Wa APC Zagon Qasa –Ma’ajin APC na qasa Daga Mustapha Ibrahim, Kano

Kishin ci gaban al’ummar qasar mu da jama’armu ne ya sa muka sadaukar da rayuwarmu gabaxaya domin mu ga jam’iyyarmu ta APC ta yi nasara tun a 2015 domin mu shugabannin wannan jam’iyya ta APC amma na ta yi biliyan kimanin 25 inda za a ba kowanne mu biliyan xaya da alqawarin gidaje gare mu da kuma muqamai ministoci idan PDP ta yi nasara amma muka qi yarda da a yi wa jam’iyyarmu ta APC zagon qasa da haxin bakin mu domin kishin qasar mu ta fita daga halin da PDP ta jefa qasar a baya. Wannan bayanin ya fito ne daga bakin ma’ajin jam’iyyar APC na qasa Honarabul Bala Muhammad Gwagwarwa a lokacin da yake tattaunawa da ‘yan jarida a gaban wasu daga cikin magoya bayan Jam’iyyar ta APC a Kano. Ya ce, don haka duk wani abu na shirme da wasu za su faxa akansu to ba zai zama gaskiya ba dominAllah ka xai ya san irin gwagwarmayar da suka yi kuma suke yi na ganin ba a wargaza jam’iyyar APC ba. Haka kuma ma’ajin jam’iyyar, Honorabul Bala Gwagwarwa ya ce, su a matsayinsu na shugabannin Jam’iyyar APC har yanzu su na ci gaba da hikimomi da nuna qwarewa a siyasance na a ga ba a samu Nasara da zata kawo wa APC matsala ba inda y ace kuma har yanzu akwai haqqoqin su da ya Kamata jam’iyya ta ba su amma ba a basu kuma hakan bai hana su su ga sun tsaya tsayin Daka domin APC ta yi Nasara ba, ga kuma irin jajircewar da su kayi na hana biyan buqatar wasu masu yiwa APC

zagon qasa musamman a lokacin da shugaban qasa Muhammadu Buhari ba yi da lafiya su kaxai su ka san wacce siyasa su ka yi don ceton Najeriya daga biyan buqatar masu son zuciya a jam’iyyar da qasa baki xaya. Danga ne da qarin lokaci da akayi wa shugabannin APC kuwa ya ce abu ne da ya ke kan qa’ida kuma wata Hikima ce babba a siyasance wacce APC ce za ta fi kowa cin amfanin wannan qarin lokaci ga shugabbanin jam’iyyar da akayi a wannan lokaci wanda kuma wannan ya samu Amincewar kasha 99 cikin 100 na shugabannin zartarwa da ake kira NEC na APC dan wasu qalilan sun so ki lamarin ai bazai yi wani tasiri ba tun da siyasa akeyi kuma siyasa kullum masu rinjaye sune ke da nasara a siyasance.

Haka kuma ya bayyana cewa shi a matsayin sa na Xan Kwankwasiyya ba wani abu da za a ba shi domin ya bar Kwankwasiyya domin su Kwankwasiyya aqida ce amana ce domin kula da haqqin al’umma musamman raunana na a ga sun sami ilimi da sauran ci gaba domin al’umma ta zama mai Daraja a ko ina kuma a ko da yaushe kuma irin jajircewa da sadaukar wa da sukayi wajen ganin ba ayi wa APC zagon qasa ba wannan aqida ta rikon amana bas a duniya a gaba ba shi ne aqidar Kwankwasiyya a cewar Honorabul Bala Muhammad Gwagwarwa Kano Ma’ajin Jam’iyyar APC na qasa inda kuma ya buqaci al’ummarmu musamman ta arewa da su tsaya wajen koyi da magabata ta hanyar riqe sana’o’i da kuma mutunta kan su kamar ya kamata.

•Honorabul Bala Gwagwarwa

Jam’iyyar KOWA Mafita Ce Ga Qasar Nan –Bobboi Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jam’iyyar kowa ta fito ne dan kawo mafita ga qasar nan saboda qangi da aka saka al’umma domin rashin adalci da shugabanni suke. Shugaban jam’iyyar na qasa Alhaji Sa’idu Bobboi ya bayyana haka a wajen zaven shugabannin jam’iyyar na jahar Kano. Ya ce, jam’iyyar tun a 2009 aka yi mata rijista a qasar nan kuma ta tsai da ’yan takara a matakai dabandaban har da shugaban qasa ba tare da jingina ko haxa kai da wata jam’iyya ba. Bobboi ya ce, Jam;iyyar ta soma da rarrafe ta yi ta-ta-ta kuma yanzu tana tafiya da qafafunta duk wanda bai gamsu da yadda abubuwa ke tafiya a qasar nan ba ya zo a haxa kai a cikin wannan jam’iyyar a sami mafita yanzu haka

akwai masu neman su tsaya wa jam’iyyar takarar shugaban qasa mutum huxu a qasar nan. Alhaji Hamisu Bobboi ya ce, jam’iyya ce da take da manufa ta ci gaban talakawa wanda za ta sa matasa a gaba dan kaiwa ga nasara duba da duk shugabanni da suka sami kai qasar nan ga nasara suna matasa ne, dan haka muka zo da manufa ta kawo ’yanci ga matasa maza da mata dan sau da dama sukan yi zave sai a tura mota a gudu a bar su da qura, sai zave ya zo a watsa musu tsaba dan su sake zava. Shugaban jam’iyyar na qasa Saidou Bobboi ya ja hankalin sabbin shugabanin jam’iyyar da aka zava yayin taron su riqe amana da aiki tuquru wajen ciyar da jam’iyyar gaba. Ya ce, saboda kula da bai wa naqasassu

muhimmanci shi ya sa suke tafiya tare da su a shugabancin jam’iyyar. Shi ma jagoran jam’iyyar kowa a jahar Kano Malam Hamisu Magaji ya nuna rashin gamsuwa da mulkin APC na kusan shekaru uku da ba wani abu da ta kawo wa talaka ya amfana a qasa. Ya qara da cewa, hasali ma koma baya aka samu, an shiga qangin talauci da rashin kwanciyar hankali, masifu ana cikinsu a qasar nan ta kowane vangare, dan haka suka kawo wannan jam’iyya domin nema wa al’umma mafita. Malam Hamisu Magaji ya ce, ko a zaven 2015 sun shiga zave sun yi na uku a Kano, kuma sun tsai da ’yar takarar shugaban qasa Farfesa Uwargida Remi Shonaya da ita aka yi muhawara ma da tsohon shugaba Jonothan

da Buhari kafin zave ta zama ta xaya a manufofin da ta kawo dan ci gaban qasa. Malam Hamisu Magaji ya ce, yanzu matasa na shiga jam’iyyar tasu wanda ita za ta zama mafita ga al’umma saboda qosawa da rashin adalci da ke wanzuwa a mulkin qasar nan. Malam Hamisu ya ce, jam’iyyar KOWA ta kowane vangare ne na al’umma da suke son kawo sauyi a qasa .Ya yi kira ga ’yan jam’iyyar su ci gaba da ba shi haxin kai bisa zaven da suka yi masa dan kai jam’iyyar ga nasara. A lokaci taron dai an sake tabbatar da Malam Hamisu Magaji a matsayin zavvavven shugaban jam’iyyar KOWA a jahar Kano, qunshin zavavvun shugabanin jam’iyyar a Kano guda 18 ne ciki har da wakilcin mutane masu buqata ta musamman.

An Yi Zaven Shugabanin Kasuwar WAPA Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Qungiyar al’amanat ta ’yan kasuwar musayar kuxi ta wapa ta gudanar da zaven sababbin shugabanin quniyar a Kano. Da yake bayyana sakamakon zaven shugaban kwamitin zaven kasuwar alhaji sani ajah ya bayyana cewa ’yan takara biyar ne suka nemi shugaban kasuwar da suka haxa da Alhaji Auwalu Maigwado ya sami quri’a 168. sai Alhaji Auwalu Nagari quri’a 114. Alhaji Kabiru Pele

60. Alhaji Sani Salisu 356. Sai Alhaji Ado Muhammad wanda shi ya yi nasarar lashe zaven da quri’a 404. Sai matsayin mataimaki shugaba da Labaran Abdullahi ya yi nasara a kan Auwalu Soja da quri’a 761. Sakatare da mataimakinsa sun ci ba hamayya inda Alhaji Mustapha Muhammad Rago ya zama ma’aji da quri’a 584. Mataimakin ma’aji da mai binciken kuxi da mataimakinsa ba hamayya. Sakataren kuxi Alhaji Yusuf Abdulhamid ne ya sami

nasara da quri’u 723 sai mataimakinsa da ya ci ba hamayya. Matsayin jami’in walwala da mataimakinsa ba hamayya, sai matsayin jami’in hulxa da jama’a da Adamu Nalalo ya sami quri’a 768. A yayinda Ibrahim Sabiu Moda ya zama mataimakinsa da quri’a 561. Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala zaven, tsohon zavavven shugaba na farko a qungiyar Alhaji Abdulhadi Rabiu Kura ya yaba wa kwamitin zaven qarqashin jagorancin Alhaji

Sani Ajah bisa nasaara gudanar da wannan zave a damakwaraxiyan ce da shi ne na biyu tun bayan kafa qungiyar. Alhaji Abdulhadi ya ce, ba a yi zaven kasuwar kwatankwacin wannan ba, tun bayan zaven da aka tava yi musu domin duk abin da ya biyo baya-bayan sun sauka riqo ne, sai yanzu ne aka sami cikakken zave a qungiyar. Alhaji Abdulhadi Kura ya yi kira ga waxanda suka yi nasara a zaven su riqe amana da aka xora musu su rungumi

kowa a kasuwar ba tare da nuna bambanci ba. Ya ja hankalin sabbin zavavvun su shiga su fita wajen samun haxin kan Gwamnati domin ci gaba da bunqasar kasuwar Wapa da harka canji a jahar Kano ta yadda za a tafi da canjin zamani. Alhaji Abdulhadi Kura ya ce qungiyar kasuwar tana da raunin samun kuxaxen shiga dan haka ’yan qungiyar su yi qoqari wajen ganin an havaka samun kuxin shiga a qungiyar.


16

Siyasa A Yau A Yau

Litinin 12.3.2018

Maqarfi Ya Tallafa Wa Al’ummar Kasuwar Magani Daga Balarabe Abdullahi, Zariya

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Alhaji Ahmed Kohammed Maqarfi ya shawarci al’ummar qaramar hukumar Kajuru, musamman na garin Kasuwar Magani da su rungumi zaman lafiya a tsakaninsu domin ci gaban wannan qaramar hukumar, da kuma jihar Kaduna baki xaya. Alhaji Ahmed Maqarfi ya bayyana haka ne a saqon tallafin kayayyakin abinci da ya aika ga al’ummomin Kasuwar Magani da wasu matsaloli suka faru a garin wanda har aka rasa rayukan al’ummomin da suke wannan qaramar hukumar. Tsohon gwamnan jihar Kaduna, wanda Shugabar mata ana jihohin arewa ma so yamma na jam’iyyar PDP Hajiya Halima Yunusa Kajuru ta wakilta ya ci gaba da cewar, babu al’ummar da za ta sami ci gaba sai al’ummar

ta rungumi zaman lafiya tare da girmama ra’ayoyin juna, san nan, in ji shi, za a sami ci gaban da ake buqata. A dai saqonsa Alhaji Ahmed Maqarfi ya yaba wa shugannin addinin musulunci da kuma na kirista, na yadda suka haxa hannu a lokaci guda, suka daqile yaxuwar wannan matsala da taso a garin Kasuwar Magani da kuma wasu qauyuka da suke maqotaka da wannan gari da aka ambata. Ya kuma shawarci shugabannin addinan musulunci da kuma na kirista da su qara tsayawa irin na maid aka, waje ci gaba da bin hanyoyin da suka dace , na ganin wannan matsala ba ta qara tasowa ba a wannan gari da kuma jihar Kaduna baki xaya. Hajiya Halima Yunusa Kajuru, a matsayinta ta ‘yar qaramar hukumar Kajuru, ta ce, dole ta yaba wa Alhaji

Ahmed Maqarfi, na yadda ya tausaya wa waxanda wannan matsala ta rutsa da su, har kuma ya ba su wannan tallafin kayayyakin abinci. A jawabansu daban-daban, shugabannin qungiyoyin Jama’atul Nasrul Isla da na Qungiyar kiristoci a Nijeriya, duk sun yaba wa Alhaji Ahmed Maqarfi, na yadda ya tallafa wa al’ummar Kasuwar Magani da wasu garuruwa da wannan matsala ta shafa. Shugabannin qungiyoyin biyu, sun kuma tabbatar wa wakiliyar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Halima Yunusa Kajuru cewar, kwamitin da ke tattara gudunmuwar zai riqe amanar da aka xora ma san a rabon kayayyakin tallafin bisa adalci a tsakanin waxanda matsalolin tashin-tashinar ta rutsa da su, kamar yadda suka sava laya a lokacin da aka qaddamar da su, jim kaxan bayan faruwar tashintashinar.

•Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Bello

Rikicin Gidan APC: Al’amarin Da Ya Qi Ci Ya Qi Cinye Wa Daga Muhammad Maitela

Rikita-rikitar cikin gidan jam’iyyar APC mai mulki a tarayyar Nijeriya, wadda ta fara kama manyan turakun da take tafiya a kai. Rikicin wadda ta fara ci bal-bal tun bayan ayyana nasarar APC a zaven 2015 rikicin da ya kama kowanne lungu da saqon ta. Matsalar da ta jawo naxa kwamitocin sulhu tare da sasanta ‘ya’yan jam’iyyar APC. Na baya bayan nan shi ne wanda fadar shugaban qasa ta kafa da damqa ragamar sa zuwa ga Asiwajo Bola Ahmed Tinubu domin sasanta rikita-rikitar da ta kanannaxe yan jam’iyyar. Haka zalika kuma, wannan kwamitin yana fuskantar babban qalubalen yadda kallon hadarin kaji ke daxa zafafa tsakanin waxannan qusoshin guda biyu. Bugu da qari kuma da rikita-rikitar da ke hauhawa a jihohi; da matakan qananan hukumomi wanda

ya dabaibaye yan jam’iyyar APC. A jihar Ondo, Borrofice ke rikici da gwamna Rotimi Akeredolu, yayin da a jihar Kogi, Hon James Faleke yake taqaddama tsakanin sa da gwamna Yahaya Bello; ga Sanata Dino Melaye haxi da shugabanin APC suna takon saqa da Yahaya Bello. Inda a Bauchi kuma Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara yana karon battar qarfe da Gwamna Mohammed Abubakar, baya ga yadda a KadunaSanata Shehu Sani tare da Suleiman Hunkuyi suka ja daga tsakanin su da Gwamna El-Rufai. Yanayin bai canja zani ba a jihar Oyo ba, wanda ake dambacewa tsakanin qaramin ministan sadarwa, Adebayo Shittu da gwamna Abiola Ajimobi. A gefe guda kuma, a jihar Ogun zaman doya da manja ake yi tsakanin Sanata AdeolaYayi da Gwamna Ibikunle Amosun. Qarawa da qarau

kuma, sai a Kano inda tattavurzar da ke ci gaba da zafafa a tsakanin Sanata Rabiu Kwankwaso da gwamna mai ci-Abdullahi Ganduje. Idan ka je jihar Zamfara qurar rikici ce ta musqe a tsakanin sanata Marafa da Gwamna Abdul’aziz Yari, sannan da wutar rikicin jihar Rivers wadda ta kama hannun rigar Rotimi Amaechi da ta sanata Magnus Abe. Har wa yau, a Imo, babu ga maciji asakanin Gwamna Rochas Okorocha da Sanata Ifeanyi Ararume, kuma da kallon hadarin kaji dake gudana a tsakanin Oyegun da Adams Oshiomhole a jihar Edo. Haka lamarin yake idan ka leqa jihar Bayelsa, inda Timipre Sylva ya shelanta shaya dagar fito-na-foto tsakanin sa da shugabanin jam’iyyar APC a jihar, sai rikicin da ya kannanaxe qafafun tsuffin hannu a jam’iyyar jihar Abia da ministan kasuwanci,

Okechukwu Enelama. A jihar Gombe kuma, Sanata Danjuma Goje ke kai ruwa rana dashi da shugabanin jam’iyar APC a jihar. Har yanzu tsugunen bata qare ba a tsakanin Segun Oni da Kayode Fayemi a Ekiti, inda wata wutar ke ci a jihar Osun, a tsakanin Gwamna Rauf Aregbesola da Mista Lasun, sannan da rikicin cikin gida a jam’iyyar wanda ya kankama a jihar Lagos, inda ake nuna wa juna yatsa a tsakanin Gwamna Akiwunmi Ambode da lauyan APC na qasa, Muiz Banire. Ita ma jihar Delta bata kuvuta daga wannan rikita-rikitar ba, yayin da Mista Erue Jones-jigo a jam’iyyar ke takon saqa da qusoshin jam’iyyar. A Adamawa kuma, Gwamna Jubrilla Bindow ne ke yartifa da tsohon gwamnan jihar- Murtala Nyako, kana da rashin jituwar da ke tsakanin Sanata Nyako da Nuhu Ribadu. Yayin da

a jihar Cross River kuma, rikici ya varke tsakanin shugabanin jam’iyya a jihar da minista mai kula da lamurran Niger Delta, Pastor Usani Nguru. Manazarta su bayyana cewa, bisa haqiqanin gaskiya Tinubu ya shiga sahun waxanda ke hana ruwa gudu a jam’iyyar APC tun bayan savanin da ya kaure tsakanin sa da Dakta Bukola Saraki da Dino Melaye- biyo bayan shatale qafar sa wajen qoqarin sa na kafa yaran sa a majalisar dattijai. Wanda kuma hakan ya jawo dangantakar sa tayi tsami da wasu qusoshin jam’iyyar a yankin kudu maso yamma, irin su gwamna Amosun da Akereduolu, tare da ministan makamashi da ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola da makamantan su. Bisa ga wannan kuma, babbar matsala ce ace mai bunu a gindi ya kai gudumawar kashe gobara.


A Yau

SIYASA 17

Litinin 12 Ga Maris, 2018 (23 Ga Jumada Thani, 1439)

PDM Ta Shirya Karve Kujerun Qananan Hukumomi A Jihar Neja –Nasko Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

Jam’iyyar PDM ta qasa reshen jihar Neja ta qalubalanci gwamnatin kan kasa aiwatar da zaven qananan hukumomi. Ba wani dalili ga kasa rushe shugabannin qananan hukumomi saboda wa’adinsu ya cika shekaru biyu. Shugaban jam’iyyar PDM, Kwamared Musa Nasko ne ya bayyana hakan bayan kammala taron jam’iyyar na tantance ‘yan takarar shugabancin qananan hukumomi da kansuloli. Kwamared Nasko ya cigaba da cewar ba mu san ko a wata doka ne shugabannin ke cigaba da mulkin ba tunda wa’adinsu na shekaru biyu ya cika, kan haka majalisar dokokin jiha ta jawo hankalin gwamnati kan rushe majalisar shugabannin qananan hukumomi amma har zuwa yanzu ba wani bayani. Mu a matsayin jam’iyya

mun tuntuvi hukumar zave ta jiha dan jin ranar da aka ware dan yin zaven qananan hukumomin amman ita ma cewa tai ba ta sani ba, wanda hakan ya savawa dokar da aka yi zave tare da rantsar da shugabannin. Ba na kokwanto ko yanzu gwamnati ta cire tsoro indai za a gudanar da zave a dukkanin qananan hukumomi ashirin da biyar na jihar muna da ‘yan takara. Don haka muna masu jawo hankalin gwamnati akan a riqa aiki bisa dokokin da majalisa ta amince da shi amma yanzu ba mu san a wani matsayi ake akai ba. Gwamnati na jin tsoro ne saboda shugabannin qananan hukumomin ba su tare da jama’a idan an yi zave ta hango faxuwa muraran, ba wani bambamci da gwamnatin da ta gabata har yanzu ba wani zavavven shugaban qaramar hukuma da zai iya kwashe

kwanakin mako a qaramar hukumarsa, saboda ba sa aikin komai duk da irin kuxaxen da suke samu. Shugaban ya jawo hankalin shugabannin jam’iyyar a matakin qananan hukumomi da mazavu da su tashi haiqan wajen wayar da kan magoya bayansu muhimmancin mallakar katin zave, duk yadda ka ke son yin gyara muddin ba ka da katin zave ba zai yiwu ba, Don haka kowa ya jure ya tabbatar ya mallaki katin zave shi ne muhimmin abu. Taron dai ya shafi duk masu ruwa da tsaki a jam’iyyar, wanda shugabanta Kwamared Musa Nasko ya jagoranta, bisa goyon bayan sakataren jam’iyya na jiha da shugabar mata ta jiha, Hajiya Fatima Bida. Taron ya gudana a harabar sakatarinyar jam’iyyar ta jiha da ke Nateco cikin garin minna a lahadin makon nan.

• Kwamared Nasko

Majalisar Katsina Ta Jaddada Qudurin Goyon Bayan Gwamnati Daga Sagir Abubakar, Katsina

Majalisar dokoki ta jihar Katsina ta qara jaddada qudurinta na bayar da goyon baya ga manufofi da shirye-shiryen gwamnati mai ci a yanzu. Shugaban majalisar Alhaji Abubakar Yahaya Kusada ya bada tabbacin hakan ne a lokacin da ya amshi baquncin manyan jami’an qungiyar haxin kan Qafur watau Qafur Unity Forum da suka kai ma shi ziyara. Ya bayyana Gwamna Aminu Bello Masari a matsayin shugaban abin koyi wanda manufarsa ta bunqasa rayuwar al’umma ta wuce buqatunsu ta qashin kansa. Ya bayyana cewa majalisar tana alfahari da gwamna Aminu Bello Masari akan halayensa na nuna xa’a da rashin sanya iyalensa a cikin • Kakakin Majalisar Jihar Katsina harkokin gwamnati. Shugaban majalisar ya bayyana cewa tsawon lafiya lau ba har sai in akwai zaman da majalisar tayi tare ja in ja tsakanin vangaren da wannan gwamnati mai zartaswa da na majalisa. Shugaban qungiyar haxin ci a yanzu babu wani lokaci kan ta Qafur mai suna inda gwamnan ya aikata Qafur Unity Forum Alhaji ba daidai ba a kasafin kuxi Abubakar Magaji ya bayyana sai dai wurin da majalisar cewa sun je majalisar ta bada shawarwari na yin dokoki ta jiha ne domin sun gyara. jindaxin al’ummar qaramar Alhaji Yahaya Kusada hukumar ta qafur ga me da ya bayyana cewa goyon bayan da majalisar ta demokoraxiyya ba za ta tafi

da gwamnatin Gwamna Aminu Bello Masari ta ke ba muhimmanci. Shugaban qungiyar ya bayyana cewa xaga darajar manyan asibitocin Katsina, Vaure da Funtua da gwamnatin jiha mai ci a yanzu ta yi ya taimaka

wajen inganta samar da kiwon lafiya ga mutane. A jawabin shi wani Dattijo na qungiyar Alh. Abubakar Dogo ya bayyana vangaren majalisa a matsayin wanda ya ke taka muhimmiyar rawa wajen cigaban demokoraxiyya.

Tiriliyan Shida PDP Ta Ciwo Bashi A Shekaru 16, Amma APC Ta Ci Bashin Tiriliyan 11 A Shekaru 3 –Melaye Daga Khalid Idris Doya, Abuja

ke ba Gwamna Aminu Bello Masari a jihar nan. Kamar yadda yace irin wannan haxin kan tsakanin vangaren zartaswa da na majalisa ya taimaka wajen kawo cigaba mai ma’ana a jihar nan. Ya bayyana kiwon lafiya, ilimi, aikin gona da samar da kayayyakin more rayuwa a matsayin vangarorin

Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin birnin tarayya FCT Abuja, Dino Melaye (Sanata a qarqashin APC daga Kogi) a makon da ya gabata ne ya bayyana wa Majalisar Dattawan cewa, a qarqashin mulkin jam’iyyar APC ta ciwo bashin tsabar kuxi har tiriyan goma sha xaya a cikin shekaru uku kacal da suka yi a bisa karagar mulki, inda kuma PDP ta ci bashin tiriliyn shida kacal a tsawon shekaru 16 da ta yi tana mulkar qasar nan. Dino Melaye, wanda ke jawabi kan qin amincewa da kudirin wanzuwar gami da amincewar hukumar ‘Peace Corps’ wanda shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi facakali da shi. Melaye ya ce babu wani

takamaiman tsari ko shirin da wannan gwamnatin ta kawo domin samar wa matasa ayyukan yi a qasar nan. Ya bayyana cewar qorafin da shugaban qasa Muhammadu Buhari ya gabatar na cewar a sakamakon rashin kuxi ne ya sanya ba a amince da wanzuwar Peace Corps ba, da cewar wannan uzurin ba qarvavve bane, kuma bai gamsar ba. Ya ke cewa, “Wani abu makamancin wannan ya faru a lokacin da ake qoqarin amincewa da hukumar NSCDC, an samu qorafe-qorafen cewar babu kuxi, babu kuxi”. “Amma a yau, ga shi muna ganin amfanin samar da Civil Defence da yadda suke taimaka wa gwamnati wajen bayar da kariya,” A cewar Dino.


18 SHARHI/SIYASA

A Yau

Litinin 12 Ga Maris, 2018 (23 Ga Jumada Thani, 1439)

Sace ’Yan Matan Dapchi: Wai Ina Hadiza Bala Usman Ne? Daga Abdullahi Usman, Kaduna

G w a g w a r m a y a r nemo ‘yanci ko kuma gwagwarmayar ganin cewa an qwato ‘yan matan Chibok da aka sace sama da shekaru huxu da suka gabata ba zai cika ba har sai an sanya sunan cikakkiyar ‘yar gwagwarmayar kare haqqin xan Adam xin nan, wato Hajiya Hadiza Bala Usman. Hadiza Bala Usman tana daga cikin na gabagaba wajen wajen yaxin neman ganin an sako ‘yan mata sama da xari biyu da aka kama lokacin mulkin waccan gwamnati da ta gabata. Hajiyar ta yi qaurin suna wajen caccakar gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan da ta gabata, in da ta sha bayyana cewa shugaba Jonathan da sauran muqarrabansa na da hannu wajen sace waxannan matan. Hajiya Hadiza Bala Usman, wadda ‘yar jam’iyyar CPC ne a wancan lokacin, kafin a yi maja tsakanin jam’iyyun CPC, ANPP, ACN da kuma wasu ba’adin jam’iyyun APGA da PDP, in da suka koma jam’iyyar APC. Kuma ita ce ta yi wa jam’iyyar CPC takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya a mazavar Musawa/Matazu. Duk da cewa ba ta ci zave ba a wancan lokacin, amma ta taka rawar ganin sosai a wannan yanki. Wasu ma na ganin cewa dalilin da ya sanya ba ta yi nasara ba shine savanin da aka samu tsakaninta da xaya ‘yar takarar, wato Hajiya Hannatu Musa Musawa bayan an kammala zaven fidda gwani. Hakan ne ya sanya ita Hannatu ta koma jam’iyyar ACN ta yi takara a cikinta. Don haka sai jam’iyyar PDP ta ci zave a lokacin saboda raba quri’ar suka yi a tsakaninsu. Bayan siyasar 2011 ta qare a wancan, a wannan lokaci rikicin da ake fama da shi na Boko Haram ya

yi tsanani in da har ta kai ga sace ‘yan matan Chibok da aka yi a shekarar 2014. Wannan abu sai ya baiwa Hajiya Hadiza Bala Usman dabar shiga cikin qungiyoyin da ke fafutukar ganin an sako waxannan ‘yan mata da Boko Haram ta sace. Ba wai kawai shiga ciki ta yi ba. A’a ta zama wata jaruma ne a cikin waxannan ‘yan gwagwarmaya da suka xaukar wa kansu alqawarin cewa ba za su huta ba har sai an sako waxannan ‘yan mata. Cikin wata sanarwar da ta raba wa manema labarai a shekarar 2014. Hajiya Hadiza ta soki wasu jami’an gwamnati bisa zarginta da suka yi na cewa jam’iyyar APC ce ke xaukar nauyin qungiyar da ta kafa mai suna ‘Bring Back Our Girls’ wato a dawo mana da ‘yan matanmu a Hausance. Cikin takardar Hajiya Hadiza ta bayyana cewa ita ‘yar jam’iyyar APC ce amma ta kafa qungiyar ‘Bring Back Our Girls ne don tausayi da kuma matsawa Gwamnati nemo ‘yan matan Chibok da aka sace rane 14 ga watan Afrilun 2014. “Ni Hadiza Bala Usman, Jagora kuma shugabar gwagwatrmayar ‘yanto matan Chibok ta Bring Back Our Girls, ni mamba ce ta jam’iyyar APC. ban tava boye cewa ni ‘yar APC ba ce kuma ba zan tava voye hakan ba. Amma lokacin da na nemi matan Nijeriya da su fito ranar 30 ga watan Afrilu domin mu yi zanga-zangar matsawa gwamnati don nemo ‘yan matan Chibok da aka sace, ban yi hakan da sunan APC ba. Na yi hakan ne a matsayina na ‘yar Adam, Mace. Uwa, ‘yar Nijeriya kuma ‘yar Afirka. Wannan magana ba ta siyasa bace ko jam’iyyar da mutum ya fito. Abu ne da ya shafi ‘yanci da kuma jin qai a matsayina na Uwa.” In ji Hadiza Bala Usman.

•Hadiza Bala Usman tare da abokan fafutukarta a lokacin da suke tsaka da gwagwarmayar BRINGBACKOURGIRLS.

Ta ci gaba da cewa, “A matsayina na Uwa, na san raxaxin rashin sanin in da xa ko ‘ya ta shiga. Saboda haka ya zama wajibi in taya iyayen matan Chibok jajen halin da suka shiga na rashin sanin in da ‘ya’yansu suke yau sama da kwanaki 189.” In ji Hajiya Hadiza Bala Usman a shekarar 2014. Ta ce wannan qungiya da ta kafa kowa zai iya shigarta don yin gwagwarmayar ganin an saki waxannan ‘yanmatan Chibok ba tare da nuna banbancin siyasa ko qabila ba. Ta ce wannan wata dama ce don ganin an haxa kai wuri guda ba tare da nuna banbanci ba. Sai dai kuma wani abin mamaki shine yanzu haka an kwashe makwanni da sace ‘yan matan makarantar Sakandare ta garin Dapchi a jihar Yobe, amma har yanzu ba wanda ya ji motsin Hajiya Hadiza Bala Usman. Abin da kowa ya yi zato shi ne za a ga Hajiya Hadiza a filin Unity Fountain da ke Babban birnin tarayya Abuja, in da ta kafa qungiyar ‘Bring Back Our Girls’ don ci gaba

da yin gwagwarmayar ganin Gwamnati ta karvo ‘yan matan Dapchi kamar yadda ta yi lokacin gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan. Har yau xin nan Hajiya Hadiza Bala Usman ba ta fito ta yi koda Allah wadai ne da sace ‘yan matan Chibok ba. Ballantana ta sake kafa wata qungiyar don yin fafutukar ganin an sako ‘yan matan Dapchi. Tuni mutane ke zargin cewa Hajiya Hadiza Bala Usman ta tsallake ta bar sauran waxanda suke yin wannan gwagwarmaya tare tun da shugaba Muhammadu Buhari ya naxa ta shugabar hukumar kula da tashoshin ruwa na Nijeriya. Wannan hali da ko-inkula da Hajiya Hadiza ta nuna game da sace matan na Dapchi, ya sanya mutane shakku kan masu da’awar kare haqqin xan Adam a Nijeriya. Wasu na ganin cewa masu kare haqqin xan Adam na yi ne lokacin da mulki ya kuvuce musu. Da zarar suka sami wurin maqalewa a cikin gwamnati, sai su manta da duk wani hali da takala ke ciki.


A Yau

Litinin 12 Ga Maris, 2018 (23 Ga Jumada Thani, 1439)

SHARHI/SIYASA 19

Buqatar Haxin Kai Tsakanin Shugaba Buhari Da Majalisa Don Ci Gaban Qasa Daga Bello Hamza

A halin yanzu zaman doya da manjan da ake yi tsakanin ofishin Shugaban qasa Muhammadu Buhari da Majalisar Dokoki ta tarayya ba wani abu daya zama sirri bane, al’amarin ya kai qamarin da kwanakin baya shugaba Buhari a wani jawabi daya gabatar ya xora alhakin tafiyar hawainiyar da gwamnatinsa ke yi wajen aiwatar da mahimman aiyyuka a kan rashin samun haxin kai daga majalisar tarayya wajen amincewa da qudurorin da gwamnatinsa ke aikawa domin samun amincewar majalisar tarayya. Nan da nan Shugaban Majalisar Dattijai Dakta Bukola Saraki ya qaryata zargin daya fito daga fatar Shugaban qasar ya na mai cewa, a cikin shekara 3 da ake ciki na wannan zangon mulkin dimokradiyyar da shugaba Buhari ke jagoranta fadar Shugaba Buhari ta turo wa majalisa mutum 227 da aka turo daga fadar shugaban qasa domin amincewa dasu a kan muqamai daban-daban a cikin su mutum 133 kawai ne majalisar ta qi amincewa da su. Cikin waxanda aka fi cecekuce daga waxanda majalisar ta qi amincewa dasu a kwai shugaban Hukumar EFCC, duk da kundin tsarin mulkin qasar nan ya ba majalisar qarfin amincewa da qin amincewa da wanda fadar shugaban qasa ta turo domin a tabbatar da shi a kan zama wani muqami, a kan batun Ibrahim Magu sau uku fadar shugaban qasar ke miqa sunansa kuma sau uku kuma majalisar dokoki na qin amincewa da shi, cikin hujjojin da majalisar ta dogara dasu wajen qin amincewa da Magu, ya haxa da rahoton da hukumar leqen asiri ta DSS ta bayar a kan wasu badaqalar da Ibrahim Magu ke da hannu a ciki, masana na da ra’ayin cewa, rashin amincewa da Magu a matsayin shugaban na EFCC ya taka muhimmiyar rawa wajen rage qarfin aikinsa na yaqi da cin hanci da rashawa, abin da ake gani a matsayin babban alqawarin da wannan gwamnatin ta yi wa mutanen Nijeriya lokacin yaqin ta na neman zave. Rashin amincewa da majalisar ta qi yi wa wasu da fadar gwamnatin Buhari ta miqo mata har ya samu tsokaci daga wasu hukumomi na qasashen waje ciki kuwa har da Hukumar

Lamuni ta Duniya “IMF”, in da a kwanaki ta yi kira na musamman ga jagororin majalisar qasa da su gaggauta amincewa da manbobin hukumar gudanarwa na babban bankin qasa (Central Bank of Nigeria) da kuma hukumar harkar tsare-tsaren kuxi na qasa “Monetary Policy Committee, MPC”, saboda a samu qarfin fusakantar farfaxo da komatsar tattalin arziqin kasar nan da ke fitowa daga durqushewar da ta yi a ‘yan shekarun nan, su na masu lura da cewa, rashin hukumar gudanarwa a waxannan muhimman hukumomin kuxi na gwamnati ba zai haifar wa da qasar nan xa mai ido ba a hanqoronta na ci gaba da zama cikin qasashe masu samun bunqasar tatalin arziqi a duniya. A lokacin da taqadamar amincewa da Ibrahim Magu a matsayin shugaban Hukumar EFCC ya sake tasowa a farkon wannan shekara masana sun buqaci fadar shugaban qasa ta garzaya babban kotun qoli domin neman fassarar sashi na 171 na kundin tsarin mulkin shekara 1999, sashin dai ya tattauna ne a kan nau’in ma’aikatan da fadar shugaban qasa ke buqatar amincewar majalisar dattijai kafin a naxa su maimakon taqaddamar da ake ta yi a kan amincewa ko rashin amincewa da Ibrahim Magu a matsayin shugaban Hukumar EFCC, kotun qoli ne kwai za ta raba gardama a kan wanene ke a kan gaskiya, hakan kuma ne kawai zai taimaka a samu ci gaba a yaqin da ake da cin hanci da rasahawa a qasar nan. A ‘yan kwanakin nan an samu zazzafan taqaddama

tsakanin majalisa da wasu hukumomin gwamnati wannada hakan ya na kawo cikas wajen gudanar da aiyyukan yau da kullum na ci gaban alumma, shugaban majalisar Datijjai Bukola Saraki ya zargi hukumomi da ma’iakatun gwamnatin tarayya da qin bayar da haxin kai wajen miqa kundin kasafin kuxinsu na wannan shekarar duk da wa’adin yin haka da majalisar ta basu har sau biyu, a bin da ke haifar da tsakon da ake fusakanta na rashin zastar da kasafin kuxin wannan shekara har zuwa yanzu, wannan rashin haxin kan babban matsala ne ga harkar tafiyar da mulki, a nan ma ya kamata fadar shugaban qasa ta yi gaggawar shigo wa domin ganin hukumomi da ma’aikatunta sun bayar da cikkaken haxin kai domin ganin an samu zastar da kasafin kuxin wannan shekarar cikin lokacin daya kamata. Taqaddama na baya-bayan tsakanin vangaren zastarwa da vangaren majalisar tarayya shi ne na jadawalin zave da hukumar INEC ta tsara, majalisar dattijai kuma ta yi wa kwaskwarima, hakan ya tayar da jijiyar wuya tsakanin ‘yan majalisa da ake ganin masu goyon bayan fadar shugaban qasa ne da waxanda a ke ganin masu goyon bayan shugaban majalisar dattijai ne, wannan taqaddama yana iya kawo barazana da cikas ga shirye-shiryen da ake yi na gudanar da zaven shekara mai zuwa na 2019, a kwai misalai da dama na matsaloli da rashin jituwa da ake fuskanta tsakanin majalisar qasa da fadar shugaban qasa, wanda hakan babban barazana ne ga

mulkin dimokraxiyyamu. Duk lokacin da vangaren zartasawa da na dokoki suka shiga takaddama tsakaninsu harkar gudanar da gwamnati ne ke fuskantar baraza, ci gaban tattalin arziqi da gudanar da aiyyukan da zai taimaki rayuwar ximbin alummar qasar nan ya kan shiga cin matsala, abin da kan shafi romon dimokraxiyyar da alumma ke fatan samu, abin lura anan shi ne a tsarin mulkin shugaba mai cikkaken iko, ko wanne vangare na da qarfi da iko da tsarin mulki ya ba shi kuma dole kowanne vangare ya mutunta xaya vangaren, ta haka ne kawai za a samu fahintar juna, a kwai buqatar jagororin majalisar qasa da na vangaren shugaban qasa su xare teburin tataunawa domin gano bakin zaren, su kuma buxe babin fahintar juna tsakaninsu domin gudanar da aiyyukan da zai ciyar da alummar qasar gaba, duk kuma lokacin da aka samu wani rashin fahinta sai a miqa matsalar ga vangaren shari’a domin sun ne doka ta ba aikin fassara da qarin bayani a kan matsalar daya shiga duhu a wajen gudanar da tadane-tanaden da ke cikin tsarin mulkin qasar nan. Abin mamaki da takaici a wannan taqadadamar da ke faruwa tsakanin ofishin shugaban qasa da na majalisar tarayya shi ne dukkan vangarorin jam’iyya xaya wato APC ke jagorantar su, saboda haka a kwai buqatar jamiyyar ta yi gaggawar shiga cikin matsalar domin gano hanyar kawo fahintar juna tsakanin fadar shugaban qasa da vangaren majalisar dokoki domin kawo ci gaban qasa da tabbatauwar mulkin dimokraxiyya.


A Yau Litinin 12.3.2018

20

CINIKI

Kasuwanci MASANA’ANTU

INSHORA

HANNUN JARI

Editan Kasuwanci Mohammed Shaba Usman

KASUWAR SHINKU

Dandamalin ‘Zero Hunger’ Ya Buqaci Gwanmoni Da Su Mayar Da Hankali Ga Noma Da Kiwo Daga Abubakar Abba

Qungiya mai suna ‘ Zero Hunger Forum’ ta jaddada cewar akai buqatar gwamnatocin jihohin qasar nan su mayar da hankali wajen noma da kiwo don a havaka sana’oin biyu. Ta kuma buqaci gwamnonin jihohin dasu bada mahimmanci wajen zavar amfanin noma uku da sana’ar kiwo. Bayanin hakan yana qunshe ne a cikin takardar bayan taro da shugaban qungiyar kuma tsohon Shugaban qasa Cif Olusegun Obasanjo (PHD) da Gwamnan jihar Borno kuma shugaban qungiyar gwamnonin jihohin Arewa Kashim Shettima suka rattabawa hannu a satin da ya gabata. Taron qungiyar jaro na uku an gudanar da shi ne daga ranar takwas zuwa tara ga watan Maris na 2018 a garin Maiduguri cikin jihar Borno. A cewar sanarwar, qungiyar ta gudanar da taron karo na uku ne da nufin sanya ido wajen qaddamar akan qoqarin da jihar ta yi da kuma duba nasarorin da jihohin da aka fara qaddamar da shirin suka samar tun bayan taron qarshe da aka gudanar a jihar Ebonyi a shekarar data gabata. Wakilan jihohin biyar da aka fara qaddamar da shirin a jihohin su, suma sun harci taro. Jihohin sune; Benue da Borno da Ebonyi da Ogun d Sokoto da Bauchi da Nasarawa da kuma Oyo. Sauran waxanda suka halarci taron sun haxada; qwararru da suka yi haxaka da qungiyar da cibiyar aikin noma ta qasa da qasa (IITA) da jami’an shirin samar da abinci(WFP) qungiyar noma da samar da abinci ta (FAO) ‘yan kasuwa masu zaman kansu da qungiyoyin manoma da wakilan Masarautar Borno da kuma ma’aikatar noma da raya karkara. Gwamnonin da suka halarci taron sun haxada; na Borno Kashim Shettima da mataimakin Usman Mamman Durkwa da mataimakin gwamnan Ebonyi Kelechi Igwe da mataimakin gwamnan jihar Ogun Yetunde Onanuga. Shi kuwa gwamnan Jihar Biniwai Samueal Ortum,

kwamishinan sa na noma Mista James Abuane ne ya wakilce shi. Ko wacce jihar da aka fara gudanar da shirin, ta gabatar da qasida a wurin taron akan nasarorin da suka samu don cimma burin shirin da kuma yadda taron da qungiyar ta gudanar a jihohin Biniwai da Ebonyi suka ja hankalin su. Suma masana’antu masu zaman kansu, sun gabatar da bayanai, musamman akan noman waken Soya a jihar Biniwai kamar yadda wani Titus Agbecha ya bayyana cewar, shirin na qungiyar yaja hankalin su sosai da kuma havaka aikin su na noma. A wata ziyara da aka kai a cibiyar gona da ruvanya irin noma da kuma kai ziyara ga cibiyar (Machinery Shade),an kuma kai ziyara ga makarantar mata da jami’ar Borno domin duba yadda ayyukan noma da gwamnatin jihar Borno ke gudanarwa don cimma burin shirin na qungiyar. An kuma haska faifan Bidiyo mai tsawon mintuna ashirin dake qunshe da irin nasarorin da aka samu sakamakon rashin kai ziyara ga matsugunin ‘yan gudun hijira inda ake gudanar noman rani don samar da abinci da kiwo kaji da kifi da kuma sabon tsarin aikin noma don tallafawa matasa. A bisa bayanai da aka samu, daga masu gabatar da qasida da ziyarar gani da idon da aka kai, wakilian qungiyar sun yabawa gwamnatin jihar Borno a bisa xaukar nauyin taron bayan da kuma bayar da shawarwar. Qungiyar ta kuma yabawa akan qasidun da aka gabatar akan nasarorin da jihohin suka samar wajen cimma nasarar shirin qungiyar da kuma matakan da jihar Ebonyi ta xauka da qungiyar ta gabatar a taron ta na baya. Bugu da qari, manyan masana’antu sunada kyau wajen samar da wadataccen abincu. Qungyar ta kuma bayar da shawara da a mayar da hankali ga matsakaitan sana’oi na noma waxanda zasu zama haxaka a tsaknin qananan manoma da masana’antu. Har ila yau, qungiyar ta jinjinawa qiqarin gwamnatin tarayya ta hanyar Babban Bankin Qasa(CBN) da Bankin

Manoma don samar wa manoma matsalar kuxi da suke fuskanta. A taron, an kuma yabawa CBN akan amasa gayyatar halartar taron. Qungiyar ta kuma jinjinawa CBN akan taimakon kuxi data bayar da masana’antun dake jihar Biniwai, musamman taimakaon da aka baiwa manomi Titus Agbecha akan sarrafa waken soya tare da zuba jarin da gwamnatin jihar Borno ta yi wajen samar da kayan aikin noma na zamani. Wakilan qungiyar sun kuma yi kira ga jihar ta Borno data kafa samar da kayan noma na zamani da yafi dacewa don manoman jihar su dinga samun su a cikin sauqi. Ta kuma bayar da shawara wajen kakkafa cibiyoyin noma ta hanyar yin amfani da masana’antu masu zaman kansu. An kuma amince akan cewar akwai biqatar jihohi su horar da masu koyar da yadda ake yin amfani da kayan noma na zamani kamar Taraktoci da gyran su da kuma kula da dasu. An kuma yaba wa jihar Borno akan qirqiro da kayan na’urorin noman rani qungiyar ta kuma yi kira ga gwamnatin jihar data samar

da kasuwar fasaha ga xaukacin sauran jihohi dake qasar nan, musamman a yankin Arewa Maso Yamma. Qungiyar ta kuma yi jinjina noman rogo, inda ta ce, hanya ce yin yaqi da yunwa da da samar da ayyukan yi musamman ga mata da matasa. Ta kuma buqaci jihar ta Borno data zuba jari a noman rogo. Don qara havaka ci gaba, qungiyar ta shawarci jihar da a cikin gaggawa data samar da yanayi wajen baiwa masana’antu masu zaman kansu dammar yin haxin gwaiwa da qananan masana’antu. Shirin zuba jari a fannin ilimi na jihar shima taron ya amince dashi musamman don tabbatar ko wane yaro na jihar ya samu ingantaccen ilimin Boko kyauta tun daga matakin sakafare. Qungiyar ta kuma yabawa hukumar(IITA) akan jan jihohi a jiki wajen basu taimako don lura da aikin noma musamman noman rogo da doya da bayar da tallafin irin noma. Suma sauran masu ruwa da tsaki suma an jaba masu. An kuma yabawa qoqarin da haxaka tskanin (FAO) da qungiyar. Qungiyar ta kuma amince ta taron da za ta gudanar a watan Yuli 2018 a jihar Sokoto.


A Yau

Litinin 12 Ga Maris, 2018 (23 Ga Jumada Thani, 1439)

KASUWANCI 21

Gwamnatin Nijeriya Za Ta Samar Da Matatun Mai Biyu A Neja Delta Daga Abubakar Abba

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewar tana qoqari wajen kafa matatar mai guda biyu na zamani a yankin Neja Delta. Gwamantin ta sanar da hakan ne bayan data shigo da kayan aikin cikin qasar nan bayan hukumar hana fasa qauri ta qasa ta tantance kayan. Mataimakin Shugaban qasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan a Abuja a taron da kwamitin yankin Delta wanda Osinbajon ya jagoranta, inda ya sanar da mahalarta taron cewar, za a kafa matatun man ne a yankin na Neja Delta. Furucin na Farfesa Yemi Osinbajo yana qunshe ne a cikin sanarwar da mai taimaka masa na musamman akan harkar yaxa Labarai, Laolu Akande ya sanyawa hannu, inda sanarwar ta nuna cewar, kuma ana tsimayin sauran kayan da za su iso qasar a cikin watan Afirilu da za a kafa su a jihar Ribas. Osinbajo ya ci gaba da cewa, aikin ya haxa da samarwa da al’ummar dake kusa da matatar mai aikin yi. A cewar sa Osinbajo, al’ummar dake zaune a inda za a kafa matatun man za a tabbatar da sun samu ayyukan yi kai tsaye da kuma samarwa da matasan dake yankin ayyukan yi. Idan dai ba a manata ba, a cikin watan Disambar shekarar 2017, kwamitin ya karvi rahoto akan lasisi talatin da takwas na ‘yan kasuwa masu zaman kansu da suma suka nuna sha’awar su ta zuba jari akan qananan matatun mai a yankin. A lokacin taron, aqalla masu zuba jari goma da suka samu lasisi tuni sun yi nisa wajen shirye-shiryen kafa qananan matatun mai. Bugu da qari, rahoton hukumar NDDC, a taron ya nuna yadda aka yi nisa wajen qaddamar da aikin a yankin. Sanarwar ta qara da cewa, a shekarar 2017, jimlar ayyuka da suka haxa da aikin hanyoyi 372 da gada da samar da wutar lantarki da ruwan sha da sauran su hukumar ta kammala. Aikin ya kuma haxa da akin hanya ta Nembe-Ogbia ma tsawon kilo mita 25.7 wadda nan bada daxe wa za a qaddamar da hanyar. Akwai kuma aikin hanyoyi na Otueke dake cikin

qaramar hukumar Ogbia a cikin jihar Bayelsa data Kira Dere Mogho da aikin gada a qaramar hukumar Gokana cikin jihar Ribas. Bugu da qari, akwai kuma aikin hanyar Iselu-OkaigbenIdung-Boko-Onicha Ugbo a jihohin Edo da yankin Delta da aikin hanya na Orie Ukwu Amaoji a cikin qaramar hukumar Isiala Ngwa ta Arewa a jihar Abia da aikin hanyar AshikemUfono-Betwaswan a garin Obudu cikin jihar Koros Ribas. Hukumar tana kuma kan aiki tare da ko wanne vangare harda AMCON, don a tabbatar da an qaddar da samar da gangar mai 6,000 a kullum a qaramar matatar mai dake Amakpe da za a kafa a garin Eket cikin jihar Akwa Ibom. Hukumar NDDC ta bayyana cewar, ta kafa cibiyoyin samar da ayyukan yi da ake sa ran za a samarwa da kimanin matsa 208,000 dake yankin Neja Delta ayyukan yi. Manufar a cewar hukumar ita ce, don a rage ywan matasa masu zaman kashe wando a yankin kuma cibiyoyin za su yi daidai da samar da ayyukan da ake dasu ta hanyar koya masu sana’oin dogaro da kai a yankin. Akan nasarar da aka

samu wajen share dagwalon mai a Ogoni aikin wanda yake a qarqashin ma’aikatar muhalli ta qasa kuwa, zata fara neman qwararru don kammala share dagwalon na mai a Ogoni. In an kammala aikin, zai bai wa kamfanin dake qasashen waje za su samar da ayyukan da za su inganta rayuwar mazauna yankin. Takardar ta qarshe ta qaddamar da aikin na (SIWP), an gabatarwa da kwamitin. A wata sabuwa kuwa, jami’ar Maritime dake Okerenkoko a cikin yankin Delta, ta shirya tsafa, wajen xaukar sababbin xalibai na shakarar karatu ta 2017/2018 kuma za a fara koyar da darussa a cikin watan Afirilu. Kimanin jimlar xalibai 196 jami’ar ta samnce zata xauka,inda kuma fam 76 xin xalibai na neman gurbin karatau suke ajiye. Shugaban qasa Muhammadu Buhari tuni ya amince da qarin naira biliyan biyar daga naira biliyan biyu da a baya aka amince. Wannan kuxin an sanya su a cikin kasafin kuxi na shekarar 2018 da aka gabatarwa da majalisar qasa a cikin watan Nuwambar shekarar 2017. Haka kuma, shugaban qasa ya qara amincewa

da naira biliyan xaya don tallafawa ayyuka na musamman dana xaukar ma’aikata a jami’ar a cikin watan Nuwambar shekarar 2017 2017. Gwamnatin jihar Delta ta bai wa jami’ar gudunmwar Janareto guda biyu. A cikin watan Janairu ne hukumar jami’oi ta qasa (NUC) ta amice jami’ar, ta fara yaye xalibai da suka karanta Digiri a sassa uku na jami’ar, da suka haxada; darasin sufuri da da qereqere da kula da muhalli da za a fara sassa sha uku na jami’ar daga shekarar karatu ta 2017/2018. Wasu daga cikin jami’an gwamnati da suka halarci taron sun haxa; Ministan yankin Neja Delta Usani Usani da qaramin Ministan na muhalli Ibrahim Jubril da Manajin Darakta kuma babban jami’I na hukumar NDDC Nsima Ekere. Sauran sune, Darakta Janar na hukumar (NIMASA) Dakuku Peterside da mai bai wa shugaban qasa shawara ta musamman akan shirin afuwa na gwamnatin tarayya Paul Boroh da babban sakatare na (NUC) Adamu Rasheed da shugaban jami’ar Maritime Ongoebi Etebu da wakilan sauran hukumomin gwamnatin tarayya.


22

Kiwon Lafiya

A Yau

Litinin 12.3.2018

Jihar Abiya Ta Qara Qaimi Don Ceto Yara Daga Cutar Sanqarau Daga Idris Aliyu Daudawa

Gwamnatin jihar Abia ta kammala dukkan shirye shiryen da suka kamata na yin wayar da kan jama’a akan a ceci yara qanana daga kamuwa da cutar ‘yan rani. Wannan al’amarin wayar da kan jama’a za a far shi ne daga ranar 8 zuwa 20 ga watan Maris, wanda ana son a samu yara ne, domin saboda su ake yi, za kuma afara ne ranar 8 zuwa 20 ga watan Maris, waxanda kuma ake son abin ya shafa sune masu daga wata tara zuwa shekara biyar da haihuwa, saboda an san sune shekarun da ita cutar ke matsawa yara qanana. Jihar Abia ta haxa kai ne da Hukumar lafiya ta duniya, da kuma Hukumar kula da asusun yara ta majalisar xinkin duniya, a wajen wannan wayar da kan da zata yi. Shugabar shirin lafiya matakin farko ta jihar Abia Mrs Meg Onwu ta bayyana cewar su tawagar jami’an lafiyar, waxanda zasu yi allurer rigakafin an riga an haxa ta, an kuma basu horo a dukkan Qananan Hukumomi 17 na jihar. Ta ce ko wacce tawagar ta qunshi ma’aikatan lafiya bakwai, da suka qunshi masu allurer rigakafi su biyu, masu

rubutu biyu, mai kulawa da gidajen da za aje xaya, mai shela, da kuma mai lura da jama’a su bi umarnin da ake so. Ta qara jaddada ko wace tawaga tana da nata abin da akeson ta kula da shi,domin tabbatar da an samu nasarar ita allurar rigakan. Ta yi bayanin shi al’amarin wayar da kan jama’a da kuma allurar rigakafi dangane da cutar ‘yan rani, wanda aka yi

duk bayan shekaru biyu, ta ce kuma wanda aka yin a qarshe cikin shekarar 2016 ne, don haka akwai buqatar yin wata sabuwar allurar rigakafin saboda a kare qananan yara daga wata tara zuwa shekara biyar. ‘’Ana yin tane domin a bada tsaro na yara, ‘’ shi wani shege kuma mugun ciwo ne, wanda yake sanadiyar mutuwar yara,’’ ta qara

bayanin ita allurar rigakafin da ake yi, ba wai ana nufin a gama ta ita cutar ban gba xaya,amm kuma ana son ne a kawo cikasa akan yadda cutar take wahalar da yara sosai. Omwu ta qara yin bayanin ba kamar ita allurar rigakafi ba wadda take daga gida zuwa gida ce, ita ta ‘yan rani, ana yin tane a wani asibiti, da kuma wani wuri wanda aka gina saboda ita allurar

rigakafin. Daga qarshe ta bayyana ko wacce tawaga da zata yi allurar rigakafin an zavo sune daga wurare daban daban, daga can kuma, za a tura su zuwawurin yin aikin, domin a kaucewa sake aukuwar, abin da ya faru shekarar data wuce, a Abia lokacin da aka fara raxe raxin cewar za ayi allurar rigakafin monkey fox ne za a yi.

Likita Mai Aiki A Asibitin Gwamnatin Ya Yi Wa ’Yar Shekar 16 Ciki Inda Ta Mutu Lokacin Haihuwa Daga Abubakar Abba

Ana zargin wani qwararren Likitan kiwon lafiya dake aiki a Cibiyar lafiya ta gwamnatin tarayya dake Bida a cikin jihar Neja a bisa yiwa wata yarinya yar shekara sha shida mai suna Fatima Yusuf fyaxe har ta xauki juna biyu, inda hakan ya janyo mutuwar ta a lokacin data fara naquda. Mutuwar yarinyar ya tayar da turniqi a tsakin alummar jihar. Rahotanni sun ce, Likitan ya yi ta yiwa yarinyar fyxe a lokacin da yarinyar take jinyar mahaifiyar ta a asibitin dake fama da ciwon Sikari.

An ruwaito wata majiya kusa da dangin mariganyan Fatima tana cewa, lamarin ya fara aukuwa ne a lokacin da Likitan ya gayyaci Fatima zuwa xakin sa a lokacin mahaifiyar ta tana barci. Majiyar taci gaba da cewa, Likitan ya fake ne kan cewar yana son ya bai wa Fatima shawara, inda ya yi amfani da damar ya dinga yin lalata da Fatima. Likitan yaci gaba da cin karen sa ba babbaka har sai da bayan an sallami mahaifiyar Fatima daga asibitin. Majiyar ta kusa da dangin Fatima data buqaci kar a ambaci sunan ta saboda bata kai matsayin yin magana a

madadin dangin mariganya Fatima ba ta ce, bayan da wasu daga cikin ‘yan uwan Fatima suka gano cewar tana xauke da juna biyu sun tambaye ta gaya masu wanene ya yi mata ciki, inda ta ambaci sunan Likitan, amma Likitan ya qaryata cewar ba shi bane. Bugu da qari, maganar ta qara qamari, domin Mai Martaba Sarkin Bida, Alhaji Abubakar Yahaya, ya kawo xauki a cikin maganar. Likitan da ake zargi da aikata ta’asar bayan an gudanar a bincike a kansa a fadar Sarkin, ya amsa cewar, shi dai ya san ya dai tava rungumar Fatima da kuma haxa jikin sa da nata, amma

bai yi lalata da ita ba. Sai dai an ce Fatima ta haqiqance cewar Likitan ne ya yi mata faxe da qarfi da yaji, inda hakan ya janyo ta xauki juna biyu. Ance lamarin ya sanya Sarkin na Bida ya bayar da umarnin ga mahukuntan asibitin da Likitan yake yin aiki su gudanar da gwaji akan juna biyun na Fatima. Sai dai, asibitin yana vata lokacin wajen fitar da rahoton gwajin na juna biyu, inda hakan ya sanya aka kai Fatima wani asibitin dake wajen jihar aka gudanar da gwajin. Sai dai wani abin takaici ana cikin wannan danbarwar ne, sai Fatima ta rasu a ranar

Litinin data gabata bayan data haifo jariri a gidan su dake Bida. Mutuwar Fatima ta haifar da damuwa a hukumar kula da ‘yancin yara wadda aka ce ta shigo cikin maganar. Darakta Janar na hukumar Barista Mariam Kolo, ya tabbatar da hakan, inda ya ce hukumar zata ci gaba da bin ba’asin maganar har sai inda qarfin ta ya qare. Musamman ganin cewar mahukuntan asibin suna son su yi rufa-rufa akan maganar. Wata majiya ta bayyana cewar, ana hukumar zata maka likitan a gaban quliya sakamakon mutuwar Fatima.


KIWON LAFIYA 23

A Yau Litinin 12 Ga Maris, 2018 (23 Ga Jumada Thani, 1439)

WHO Ta Yi Kira Da A Xauki Mataki Kan Yawaitar Matsalar Kurumta

Daga Idris Aliyu Daudawa Hukumar lafiya ta duniya ta bayyaba cewar nzn da zuwa shekara ta 2050 za a samu yawan waxanda za su samu matsalar rashin ji, abin da ya kai mutane milyan 900, wannan ya fito ne daga wani sabuwar qididdigar da aka fitar ranar 3 ga watan Maris ranar da aka yi bikin ranar ji ta duniya. Akwai mutane milyan 466 a faxin duniya waxanda suke da matsalar rashin jin magana sosai, dagha ciki milyan 34 yara ne, wannan ya qaru ne daga milyan 360 shekaru biyar da suka wuce. Hukumar ta ce, babban dalilin da ya sa ake samun qaruwar haka shi ne saboda ana samun yawan mutane waxanda suka tsufa, sune kuma suka fi yawa, da kuma yawan dauwama akan abin da ba shi ne fa, wato yadda wasu suke ganiin ba dole ba ne wurinsu, kamar kulawa da kunne, sai kuma allurer rigakafin cututtuka kamarsu ‘yan rani, mumps da kuma rubella, amfani da magunguna waxanda za su iya kasancewa matsala ga saurarar magana. Kamar ire-iren waxanda suke

magungunan da ba wai suna warkar da cututtukan da suka shafi tarin fuka, da kuma zazzavin cizon sauro, sai kuma yawan kasancewa wuraren da ake ake sa wasu waqoqi ko kuma maganganu da qarfi, abin har ma ya wuce misali. Abin da ya haxa da wuraren da ake shaqatawa, sai wuraren aiki. Abubuwan da suka kasance ada da kuma hasashen da aka yi na iyyuwar qaruwar mutane da ba za su ji magana ba, kamar yadda Darakta na Hukumar lafiya ta duniya, bugu da qari kuma sashen haxa yaxuwar cututtukan da suke yaxuwa da sauri, nakasa, da kuma tashe tashen hankula, da kuma rauni kamar dai yadda Dokta Etienne Krug ya ce. ‘’Sai dai idan an xauki wani qwaqqwaran mataki ko kuma xaya daga cikin mutane goma zai haxu da matsalar rashin ji zuwa nan da shekara ta 2050, wannan al’amarin zai ita shafar rayuwar al’umma, zai kuma qara xorawa gwamnati xawainiya ta kuxaxe, gwamnatoci ya dace su yi duk yadda ya kamata, dangane da mutane masu fama da matsalar jin magana.’’

Da yake furta albarkacin bakinsa Darektan lafiya na vangaren jin magana a cibiyar Ikoyi, wanda kuma bugu da qari mamba ne ala’amarin da ya shafi ji na Hukumar lafiya ta duniya WHO, wanda shi kuma har ila yau wanin qwararre ne akan harkar jin magana Dokta Bolajoko cewa ya yi, ‘’ Wannan wata dam ace wadda za a ilmantar da al’umma akan muhimmancin jin magana abin da ke cikin tsarin kula da lafiya na Nijeriya’’. Kamar yadda ta qara jaddadawa wannan da akwai buqatar ita Hukumar kula dalafiyar kunne ta qasa, a qarqashin ma’aikatar lafiyta ta qasa, da su zage damtse domin yin ayyukan da suka kamata. Kamar yadda ita Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana, ‘’ Matsalar nakasar rashin jin magana yana shafar mutane ta hanyoyi da yawa, tana kawo ma mutum cikas wajen yin hulxa da mutane, ya koya, da, zamantakewa, da kuma jin daxin rayuwa, bada gudunmawa ga yadda za yi yaqi da fatara, da kuma yadda za. A mutane waxnda suka tsufa rashin yadda basu jin mgana

sosai ,an alaqanta wannan da rashin wani sinadari, ga kuma yioyuwar iya kamuwa da depression da kuma demantia. Rashin jin maganar da ba ayi maganin shi ba, yana sa qasashe su yi asarar dalar Amurka bilyan 750 ko wacce shekara.” Hukumar ta qara da cewar duk wasu al’amuran da suka shafi rashin jin magana, ana iya maganin hakan na yara wajen kashi 60 cikin 100. ‘’Wannan ya haxa da allurar rigakafi wadda za ayi mayara domin kare su daga kamua daga wasu cututtuka yin gwaji, da kuma gano waxanda cutar ta kamar wato yara masu fama da cutar kunne wadda take masifaffiya, sai kuma a guje ma amfani da maganin da aka ce yana da wani nakasu, a kuma riqa guje duk wuraren da ake amfani da qarar mai yawa, wuraren shaqatawa, da kuma ilmantar da al’umma akan hadari, ilmantar da al’umma da su riqa bin sassa da kuma sauran wurin da mutane ke samu, a kuma wayar da kan al’umma da su bar zama a ire iren wuraren da ake amfani da abubuwan


24 TALLA

A Yau Litinin 12 Ga Maris, 2018 (23 Ga Jumada Thani, 1439)


25

A Yau Litinin 12 Ga Maris, 2018 (23 Ga Jumada Thani, 1439)

Kimiyya

Dala Miliyan 500

ne adadin kuxi Nijeriya ke kashewa duk shekara waurin safarar xanyen man fetur da wasu sinadaran da ake amfani da su a sashen sinadarari da magunguna

Sashin Kimiyya Da Fasaha Zai Samu Tallafin Naira Biliyan 12.2 Daga Bello Hamza

Da zaran kanfanin MDXi ta bayar da Naira Biliyan 2.5 da ta sanar kwanan nan ga sashin sadarwar kimiyya da fasaha na Intanet a qasar nan, kuxaxen da ke a sahsen zai kai Naira Biliyan 12.2 ke nan. Kanfanin na MDXi ya dai sanar da shirin ta na zuba jarin Naira Biliyan 2.5 domin qarfafa harkokin ta a Nijeriya abin daya kai jarinta a wannan shashin daga Naira Biliyan 10.7 a zango na farko zuwa Naira Biliyan 12.2 a wannan zangon na biyu. Wannan jarin ta aka zuba zai qarfafa aikin kanfanin na samar da guraben intanet a qasar nan daga 300 zuwa 600. Shugaban kanfanin MDXi, Mista Gbenga Adegbiji, ne ya bayyana haka, ya kuma qara da cewa, “Buqatar masu hurxa damu ne yake qara mana qaimin faxaxa aikin da muke yi, a halin yanzu an mallake gurabe 300 da muka samar a shekara 2015 a cibiyar mu ta Lekki a Legas” Adegbiji ya ce, tun da aka buxe kanfanin MDXi a shekarar 2015 an kashe Dala Miliyan 35 kwatankwacin Naira Biliyan N10.7 wajen samar da kayan aiki na zamani a cikin shekara 5 da ya gabata. Adegbiji ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya in da ya ce, “Lokaci ya yi da gwamnatin tarayya za ta samar da tsare-tsare da zai tilastawa kanfanoni masu zaman kansu da hukumomin gwamnati su kafa kafafen urabe sadarwa na intanet a ma’aikatunsu domin bunqasar tatalin arziqi da dalilai na samar da tsaro” “Dole gwamnatin tarayya ta sani cewa, samar da cibiyoyin sadarwa daga cikin qasa yana da mahimmancin gaske saboda in har daga qasashen waje ake kafa wa kanfanoni da hukumomin mu cibiyar intanet, haka na nuna kenan sai kasashen waje sun ga abin da aka aiko kafin mu a nan gida mu iya gani ke nan, abin kuma da zai iya sa harkar tsaron qasa cikin hatsari.” “Fiye da kashi 70 na bankuna a Nijeriya na amfani da intanet da MDXi ke samar wa 21 daga cikin su suna da

wani hurxa intanet ko xan ya ya da MDXi, faxaxawar da muka samu daga gurbi 300 zuwa gurbi 600 ya farunne saboda tsananin buqatar da ke fitowa daga abokan hurxanmu”inji shi. “A watan Maris za a qarar da tanadin da muke da shi hakan ya sa muke ta qoqarin samar da qarin gurabe 300, a halin yanzu ma wasu kanfanoni sun riga sun nuna buqatar sun a gurabe intanet da zamu samar a zango na gaba” Ya kuma amince da maganar da ke yi na cewa, harkar samar da guraben intanet yana da tsananin buqatar kuxaxe masu xinbin yawa saboda haka ya buqaci gwamnatin tarayya ta kawo wa harkar samar da intanet agaji don bunqasa harkar a Nijeriya” “A kwai buqatar sa ido a tafiyar da harkokin samar da intanet a qasar nan, ya kamata gwamnatin tarayya ta aiyana cibiyoyin samar da intanet a matsayin cibiyoyi masu mahimmanci ga qasa saboda gudumawarsu ga tattalin arziqin kowanne qasa” Da yake qara haske a kan aiyukan MDXi a Nijeriya, Mista Adegbiji ya ce, “Kanfanin MDXi ne ya fi kownne girma a yankin Afrika ta yamma da ke gabatar da cikkaken harkokin da suka shafi samar wa da

rarraba intanet da sauran harkokin da suka shafi intanet a yankin Afrika ta Yamma” Kanfanin MDXi ne kan gaba da ke gabatar da aiyukansa a Legas da Sagamu da Accra da qasar Code D’Ivoire da kuma Senegal” Adegbiji ya qara da cewa, kanfanin MDXi na da tsari da gogewa irin na takwarorinsa a ko’ina a duniya, an yi mata gini mai tsarin TIA 942 tare da mataki na “Tier III Standards” da kuma “West Africa’s Tier III” tare da shaidawar PCI DSS da ISO 27001da kuma 9001. Masu hurxa da kanfanin MDXi na iya hurxa kai tsaye da masu irin wannan hurxar a yanki Afrika ta Yamma, za kuma su iya musayan bayanai da takwarorinsu a qasashen Ghana da Amsterdam da kuma Landan. Da yake jaddada buqatar da ake da shi na gwanatin tarayya ta kawo wa sashin agajin gaggawa, ya ce, “Kashi 60 na abubuwan da ake buqata a sahashin shi ne wutan lantarki, saboda tsananin buqatarmu na wutar lantarki da kuma matsalar wutan lantarki a qasar nan, hakan yana kuma qara kuxin harkar samar da intanet a qasar nan” Ya kuma qara da cewa, “Ya kamata gwamnatin tarayyar Nijeriya ta tilasata

wa kanfanoni da hukumomin gwamnati dasu rinqa hurxa da kanfanin samar da intanet a cikin gida saboda samar da intanet a cikin gida zai saukar da tsadar kuxin da ake samu a wajen kafa intanet a qasar nan” ya kuma qara da cewa, lallai wasu hukumomin gwamnati na hurxa da kanfanin MDXi amma ana da buqatar qarin hukumomin gwamanti su rinqa hurxa da MDXi saboda har yanzu wasu hukumomin na hurxa da kanfanonin samar da intanet na qasashen waje. Ya ce, Nijeriya na tsananin buqatar masu zuba jari mai yawa a fagen samar da intanet saboda faxaxa yawan masu amfani da intanet a qasar nan. “Yawan masu hurxa da intanet da ake dasu zai qara qwarewar kanfanonin mu hakan kuma zai qara rage tsadar da ake fama da shi a qasar nan” Daga nan ya kuma qara da cewa, kanfanin MDXi ita ce kaxai a qasar nan ke samar da tsarin sadarwa na OTTs a Nijeriya, ita ce kuma kaxai da ke da hanyar sadarwa a cikin ruwa har na tsawon kilomita 10 a cikin teku mai nau’in ACE da WACS da Glo 1 da kuma MainOne. Cibiyar samar da intanet xin na kuma da zurfin Kilomita 20 na “Primary and secondary data centre” domin isar da saqo ga ko ina a duniya.


26 Tattaunawa

A Yau

Litinin 12 Ga Maris, 2018 (22 Ga Jumada Thani, 1439)

Rashin Biyan Harajin Kwastan Na Rage Wa Motoci Farashi A Idon Masu Saye –Alhaji Xan Asabe ALHAJI XAN’ASABA NE IBNU USMAN Motors Shi ne mai riqon muqamin shugaban qungiyar masu sayar da motoci na jihar Bauci. A hirarsa da Leadershp A Yau, ya yi bayanin halin da sana’ar mota take ciki a wannan marrar, ya kuma yi bayanin muhimman matsalolin da suke addabar su a halin yanzu. Shugaban, ya bayyana cewa da akwai gayar buqatar hukumar hana fasa qwairi ta qasa wato Kwastan ta sake bai wa jama’an qasa zarafin biyan haraji. A cewarsa, akwai muhimman matsaloli da jama’a suke fuskanta kan sha’anin motoci, har ma dai ya yi bayanin yadda sana’ar take a jiya da kuma yau, wadda ya bayyana cewa, akwai banbanci sosai. A taqaici dai ya bayyana kasuwarsu tana tangal-tangal a wannan lokacin. Wakilinmu KHALID IDRIS DOYA ne ya tattauna da shi kamar haka: Da Wa Muke Tare? Suna na Alhaji Xan Asabe Ibunu Usman Motor’s, ni ne shugaban sashin amintattu na qungiyar masu sai da motoci na jihar Bauci, har ila yau kuma, ni ne mai riqon muqamin shugaban qungiyar masu sana’ar sai da motoci na jihar Bauci. Me za ka iya cewa kan wannan sa’ar taku a halin yanzu? Babu abin da za mu ce sai dai godiya wa Allah, amma maganar da ke a gaskiya yadda harkar nan yadda take tafiya a da a yanzu babu ita, sana’armu ta sai da motoci ba ta tafiya kamar yadda take a da. A da maganar gaskiya a lokutan baya, ana samun kasuwa sosai kamar yanda ya dace ya kuma kamata. Amma a yanzu a halin da muke ciki mun shiga wani irin hali a Nijeriya wanda yake tattalin arziki ya samu matsala, duk inda ka je za ka ji babu-babun ya yi yawa, daga gwamnatin jihohi zuwa ita kanta gwamnatin tarayya, kukan babun ya fi qarfin kukan akwai xin, wanda a yanzu yawancin masu sayen motocin gwamnatoci ne. Amma daga ciki a da, idan ka kasa masu sayen motoci ko masu canza mota kashi 30 yanzu babu kashi biyar, saboda kowa yana fama ne ya zai yi da kansa. ‘Yan kasuwa da suna sayen motoci, amma a yanzu daga cikin masu sayen motar nan wasu jarinsu ya lalace, wasu xin kuma bashin gwamnati ko na bankuna ya hau kansu, don haka a kullum abin da ake fama da shi ne ya za a yi na ciyar da kaina, ba ya za a yi na shiga mota ba. Wannan shi ne dai halin da muke ciki, gaskiya kasuwarmu ta ja baya sosai,

jama’a ba su sayen motoci a halin yanzu. Me kake ganin ya jawo irin wannan rashin sayen motoci sosai xin? Maganar gaskiya abun da ya janyo wannan shi ne a yanzu mutanen da suke sayen motocin nan da yawa ma’aikatan gwamnati ba su saya, saboda yau idan ka canza mota, matuqar wannan motar mai tsada ce za a ga kamar kana xibar kuxin gwamnati, kai kanka mai sayen motar nan kana jin tsoro, su kuma kansu waxanda ake sayen motocin nan a wajensu su ma motocin sun yi tsada sosai, domin wannan dokar sanya shigo da motocin nan shi ma ya janyo koma bayan tafiyar sana’ar, wannan dalilin ne shi ma ya sanya motoci suka qara kuxi, su kuma masu sayen motar nan babu kuxi saboda an shiga wani irin hali a Nijeriyar, tattalin arzikin ana maganar ya yi qasa sosai a Nijeriya. Kamar wasu dokokin da gwamnati ta kafa, kana ganin abun bai shafe ku ba ne? A’a ya shafe mu mana, sosai ma kuwa, a da maganar gaskiya gwamnati ta bari ana shigo da motocin nan daga Kwatano, in ka shigo akwai gurare kusan biyar zuwa shida da ake yin haraji, ka ga a Babanna da ana yin haraji, Same ana yi da, Ude, Seneboda da sauran wuraren da ake yin haraji a wajen. Amma yanzu an hana shigowa da motar balle ma a barka ka yi harajin kwastan, yanzu an koma Legas, Legas xin nan a wajen ne aka mai da ta wajen da muke zuwa mu sayo motoci. Matsalar ita ce, mafiya yawan motocin Legas a kan canza motocin daga wata zuwa wata,

• Alhaji Xan Asabe. haxe da canza wasu abubuwan da suke jikin mota, don haka ne ake samun rigima da waxanda suka sayi motar, domin in an saya za ka ga ana samun rigima ta wajen sayen mota, idan an canza wani abun wani abun ba a canzawa, shi kuma mutum in ya saya zai je ya ga an canza wani abu wannan sai ya dawo rigima. Me za ka ce kan wa’adin da hukumar hana fasa qwauri ta tava fitarwa na kowa ya je ya yi biya harajin motarsa? Muna kira ga gwamnati da ta duba, a da can lokacin da gwamnati ta ba mu xan qanqanin lokaci kan cewa, motocin da suke gida a je a biya harajinsu, to waxanda suka sayo motocin nan a wannan lokacin wallahi wani jarinsa xin ma babu shi! Babu shi a yanzu, motocin ne kawai ga su nan a qasa, abun da ke hanunsa ya rigaya ya cinye. Saboda haka, Kwastam ta yi kiran a je a biya haraji wasu an yi musu wasu kuma muna tsammanin cewa gwamnati za ta ce to motocin da suke hanun jama’a waxanda ba a yi musu haraji ba an ba su dama su je su yi wannan haraji xin, har yau ba a sake bayar da wannan damar ba. A saboda haka ne muke roqon gwamnati sauran motocin da suke hanun jama’a masu saidawa ta sake sanya musu lokaci ta bayar da dama a sake zuwa domin biyan kuxin haraji na motocin nan, a xan wannan kuxin harajin da za a biya gwamnati za ta samu kuxin shiga fiye da yadda ba ka tsammani, kuma a yanzu a misali aka sanya mota ta kama, idan motar nan abun da za a biya haraji ne, misali kamar dubu xari biyu ko uku, idan aka kame wannan motar a hanya a

ce za a zo a yi gwanjonta sai a je a yi gwanjonta ma wata a dubu talatin ko dubu hamsin ko ma dubu xari. An raba mai mota da motarsa, shi ba a ba shi damar da zai je ya biya wannan haraji xin ba, an je an sai da ma wani kuma da sunan an kame motar. Da a ce Kwastan za su bayar da damar da kowa zai iya motocin da suke hanu suke cikin qasar nan yanzu waxanda aka shigo da su tuntuni suna da dama ai, idan gwamnati ta bayar da dama za a samu kuxin shiga kuma jama’a da dama za su ji daxin hakan. Kamar yadda a lokutan baya aka tava yin wani alfarma jama’a suka je suka yi yanzu xin ma muna son a sake ba da wannan damar motocin da suka rage su je su biya wannan haraji xin. Yanzu haka a hanunku masu sai da motoci akwai waxanda ba a biya harajinsu ba ne da dama? Sosai ma kuwa, wasu suna nan a kasuwa ana neman masu saye, wasu kuma an ma sai da su, wasu za su iya ta kiranmu suna tambayar mu shin an sake maganar haraji ne? Sai mu ce a’a, ina son zan biya harajin kwastan ne don na kare dukiyata, shi wannan da ya sayi motar shekara biyu zuwa uku ko ma fiye, yana son ya biya harajin, a lokacin da aka ce a je a biya xin qila bai da hali, yanzu kuma ya samu halin yi, ka ga ya kamata a ce gwamnati ta bai wa mutum dama tun da xan qasa ne. muna neman gwamnati ta sake buxe yadda za a yi wannan haraji, kuma in za a yi ma a sassauta wa xan Nijeriya don ya samu ya biya wannan haraji xin domin bin doka. Gwamnati ya kamata ta kalli jama’arta da idon rahama. Na san idan gwamnati ta karvi kuxin nan,

Ci gaba a shafi na

27


A Yau

Litinin 12 Ga Maris, 2018 (22 Ga Jumada Thani, 1439)

Tattaunawa 27

‘Rashin Biyan Harajin Kwastan Na Rage Wa Motoci Farashi A Idon Masu Saye’ Ci gaba daga shafi na

26

yana zama kuxin shiga ne da ake amfani da shi wajen ci gaban qasa. Yanzu idan hukumar Kwastom ba su bayar da izinin biyan wannan haraji xin ba mene ne zai faru da motocin da suke shawagi a cikin qasa da kuma waxanda suke kasuwa a hanunku? Ka san kullum akwai fargabar komai zai iya faruwa, domin idan ka hau kan hanya za ka iya tarar da kwastan suna aiki, waxansu idan suka binciki takardunka in suka samu takardun sun daxe ko suka kalleka suka ga kai kanka Nijeriyar ma ta shiga jikinka sai su tausaya maka su ce maka wuce, wanda kuma ya ci rashin sa’a suna iya kame motar. Yanzu bayan shi wannan haraji xin, shin akwai wani tsarin harajin akan motoci ne da kuke biya? Maganar gaskiya babu wani haraji a kan motoci illa wannan haraji na kwaston xin, wanda in ka biya shi ne haqqin qasa, wannan biyan an amince maka ka biya domin motarka ta samu izinin shawagi a cikin qasa. A da ana maganar idan mota ta rigaya ta shigo cikin qasa to ta sha, to fa amma a cikin halin da ake ciki qasar ta durqushe, ta samu kanta a halin qaqani-ka-yi, amma a da ba a tsawwalawa sosai kan wannan harajin da zarar mota ta kutsa ta shigo to ta sha, amma yanzu a sakamakon karyewar kamfanoni, matsalar man fetur da sauransu sai ya zama yanzu abu biyu manyan kuxaxen shiga wa qasar nan. Manyan hanyoyi biyu xin nan su ne kawai ta fuskacin harajin da kwastan suke kawowa sai kuma sha’anin man fetur. Man fetur xin nan ma akwai barazana a kansa, shi kuma kwastan ta kowace fuska ba za a rasa samun kuxin shiga ba. Don haka ne muke kiran a duba, shi kansa shugaban hukumar ya duba ya kuma yi adalci a kan adalci kamar yadda ya tava yi wanda ya yi aiki da basirarsa. In Kwastam sun buxe biyan harajin nan dukkanin ‘yan qasa kowa zai biya? Eh, ko an sake buxewa tabbas ba kowa ba ne zai biya domin idan wasu sun samu sarari wasu kuma wallahi suna cikin wani halin matsatsi, da dama a Nijeriya yanzu ana fama da rashin babu, dole ne dai a duba a kuma sassauta, duk yadda za a yi dai a Nijeriya ake kuma mu ‘yan Nijeriya ne. amma tabbas idan aka bayar da damar nan mutane da daman gaske za su biya wannan haraji na kwastan xin. Ya kuke hada-hadar motocin da ba su da wannan haraji xin, ma’ana yadda kuke saidawa shin kasuwarsu na tafiya sosai? Ai mutum na zuwa zai ce

•Alhaji Xan Asabe. maka akwai harajin kwastan? In ka ce babu, zai ce maka ya za ka yi? Mu kuma dai muna ce musu muna ta qoqarin yadda gwamnati za ta sake yin harajin xin sai mu biya, mutum zai sake tambayar cewa, zai kai yaushe? Sai mu ce muna dai ci gaba da roqo. A taqaice dai motocin da ba su da harajin kwastan ba a sayen su a kasuwa. Harajin ya kai nawa ne? Ai ya danganta ne da yanayin mota qirar wace shekara ce, daraja-daraja ne, ya danganta ne. Idan muka juya wani babin na daban kuma, a lokacin da wannan gwamnatin ta Bauchi ta zo kan mulki, kun gudanar da wani aikin kwashe kwatami da shara a faxin jihar a matsayinku na qungiya mene ne ya jawo hankalinku kan yin hakan? Na farko dai waxanda muka yi wannan aikin kwashe sharan dai mu ‘yan cikin garin Bauci ne ko kuma na ce ’ya’yan jihar Bauci. a lokacin da gwamnatin nan ta hau mulki an yi ta bayanin cewa, ta kama shugabancin jihar babu xin ya yi yawa a gwamnatin, a wannan lokacin kuma duk wanda ya zo jihar zai fita sai ransa yavaci a sakamakon sharar da suka mamaye kan hanyoyi. Wannan abun a lokacin na damunmu, dukkanin wani mutum zai ce maka ya aka bari Bauci tana neman zama shara. sai muka ce to a matsayinmu na qungiya kuma ‘yan jaha tunda gwamnati ta zo babu kuxi ya za a yi mu, mu magance wannan matsalar, a lokacin muka sanya wa kawukanmu haraji, mun kasa lamarin gida uku, ya

danganta da girman kamfanin sai da mota, abun gida uku muka tsaga, A, B da C, manyan kamfanoni suna A, su sun bayar da dubu 100 kowanni wanda ya shiga gidan A, masu gidan B kuma suka kawo dubu 70, masu gidan C kuma muka har-haxa dubu 30 zuwa 20, da waxannan kuxaxen ne muka yi aikin kwashe sharan nan a wancan lokacin. Don haka ne muka tattara ababuwa a tsakaninmu, mun xauki motoci tifofi guda 80 da xori, a kowace tifa idan ta yi sawu xaya dubu biyar, adadi yawan zirga-zirgar tifa adadin kuxin da muka kashe a wancan lokacin. Muka yi kuxi-kuxi a tsakaninmu; shi kuma Alhaji Mai Shano Shafa ya ba mu gudunmawar babbar mota ‘Fen-loada’ don a gudanar da wannan aikin. Muka bi garin nan gaba xaya muka share domin tabbatar da cewa, Bauci ta yi tsafta tsaf. Kwana biyu muka yi wannan aikin. Ya batun sayen motoci a wajenku daga wannan gwamantin, shin ana wannan harkar da ku? Gaskiya kamar yadda aka saba misali a gwamnatin Isa Yuguda ana zuwa a qungiyance a ce mana ana son motoci guda kaza, mu kakkasa a tsakaninmu mu ce kamfani kaza ta kawo guda kaza, kai ma ka kawo guda kaza, a wannan gwamnatin a qungiyance ba a tava sayan mota a hanunmu ba. Sai dai a xaixaku wannan kuma ba zan ce ga adadinsa ba. gwamnatin Bauci a qungiyance ba ta tava ce mana kawo muta ba; amma ban ce ba ta saya ba, a hanun xaixaiku take wani aiki makamancin wancan sharar ba, don haka ne yanzu

mambobinmu ba za su so a sake haxa kuxi don yin wani abu ba, sakamakon su xin ma ba wai wani jarin a zo a gani ba ne yanzu kamar da xin. A qalla qungiyoyin da suke qarqashinku masu sai da mota za su kai nawa? A da can za a samu kamfanoni a cikin gari da wajen gari za a samu sama da kamfanoni xari, da suke qarqashin wannan qungiyar tamu. Mambobinmu kuma muna da mambobin da ba su yi qasa da miliyan xaya da suke ci suke sha a da sana’ar sai da mota a nan jihar Bauci ba. idan ka je kamfanin sai da mota za ka samu mai wajen, yaran da suke sai da motocin, masu yanka rasixi, masu gadi kowane kamfani mutanen da suke ci a qasanta suna da yawa. Akwai wasu qalubale ne da kuke fuskata a wannan sana’ar ta safarar motoci da saidawa? Babu wasu manyan qalubale da muke fuskanta, in ka ga mutum ya samu qalubale to sai dai mutum ya shigar da rashin gaskiya a cikin sana’arsa ne, amma gaskiya sana’ar nan idan kana yinta da lura da kiyayewa za ka ci abinci hankalinka kwance. Ya kuke fama da masu sayen motar sata? Eh, ana iya samun hakan, amma mu a qungiyance idan ka kawo mota za ka sayar mukan xan yi wani dabara muna da sunayen kowani mai saida mota a Nijeriya idan ba mu gamsu ba za mu iya bincika ko ta wayar tarho. Idan kuma duk da hakan ba mu gane ba, za mu ce wa wanda ya kamo motar mu je wajen ‘yan sanda a rubuta ‘yarjejeniya gabanin mu sayi motar nan, saboda gudun matsala, idan motar ba ta matsala ba ce mutum zai yarda, in kuma ta rashin gaskiya ce zai kawo wasu matsalolinsa ya yi gaba. Haka kuma akwai wata dabarar da muke amfani da ita wacce ita kuma ba muhallin na bayyana a wannan waje ba ne, sirrice a gare mu. Za a ka iya qiyasce mana kes-kes xin mota nawa kuka samu a shekarar da ta gabata? Ai kes-kes xin mota bai tava qarewa, yana da yawan da ba zan iya riqewa a kaina ba. Ya kuke yi wajen baiwa ‘yan sanda haxin kai, kamar wajen binciken gano varayin mota? Tabbas muna hakan, ai idan ka ce ba za ka haxa kai da ‘yan sanda wajen kama varayi ba, wata rana kai ma za ka shiga zargi, domin za a iya kawo maka mota ta sata ‘yan sanda su zo neman bayanai in ka voye za su ce kana daga cikin masu xaure wa varayin baya, don haka muna da wasu hanyoyin da muke alaqa da ‘yan sanda wanda shi ma sirri ne, amma a taqaice muna tafiya tare wajen magance varagurbi.


28

Tauraruwa Mai Wutsiya

A Yau

Litinin 15.3.2018 08174743902 wutsiya2019@gmail.com

Yadda Mai Juna Biyu Ta Arce Daga Sansanin Matsafan Da Suka Sace Ta A Ogun Daga Abubakar Abba

Masu iya magana sun ce mai rabon ganin baxi ko ana ha maza ha mata sai ya gani. Wannan karin maganar ya yi daidai da labarin wata mata mai suna Janet Oyewole, wadda aka yi zargin cewar, wasu matsafa ne suka sace ta daga jihar Osun suka kaita mavuyarsu dake yankin Ado Odo a cikin jihar Ogun. Rahotanni sunce matsafan sun asirce, Janet suka kaita mavoyar su. Da qyar Janet ta iya samun sukunin yin bayani bayan ta samu ta arce daga hannun matsafan. Wasu mutane da suka tausayawa Janet, sun sun tara mata kuxi da kuma bata suttura sun kuma yi qoqarin gano ‘yan uwanta. Wani mazaunin yankin mai suna Wale Hammed ya ce, ”munga matar ne tana ragaita akan titi, inda ta kuma tsaya a wata mahaxa

Matar da ta tsero

har tsawon awowi kafin mutane su matsa kusa da ita su da ita su tambaye ko ina take nema.” Ya ce, ”matar ta bayyana mana cewar, wasu da bata san su bane suka sato ta daga garin Oshogbo lokacin

tana kan hayar ta zuwa gida, inda suka rufe mata ido da tsumma suka kuma kaita inda bata sani ba.” Ya ci gaba da cewa, matar gaya mana Allah ne ya kuvutar da ita daga mafakar matsafan bayan sun fita

daga mavoyar su. A qarshe ya ce, ”za mu yi iya qoqarin mu don mu taimaka mata wajen kai ta wurin ‘yan uwanta ko mijinta da kuma sanar da ‘yan sanda don su miqa ta ga ‘yan uwanta.

“Yadda Aka Tilasta Mana Kwana Da Maza Ko Da Muna Cikin Yin Al’ada” Daga Abubakar Abba

Xaya daga cikin ‘yan matan da aka yi safarar su daga jihar su ta haihuwa Edo zuwa qasar Rasha aka kuma tilasta masu yin karuwanci har tsawon shekara biyu, ta bayyana yadda aka riqa kwana dasu har a yayin da suke yin jinin al’ada. Yarinyar wadda aka tafi dasu a lokacin tanada shekaru sha tara, ta bayyana hakan ne a gaban wasu manyan jami’an gwamnati har da Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki, a lokacin Majalisar Dattawa ta shirya taron tattaunawa da ‘yan matan a garin Benin cikin jihar Edo. Bayanan yarinyar wadda aka sakaya sunanta, yana qunshe ne a cikin faifan bidiyo da kafar zumunta ta facebook na na Malisar data taxa. Yarinyar wadda a yanzu ta yi aure har da juna biyu, taci gaba da cewa, “sun ce min zan je yin karuwanci ne har na tsawon wata shida zan samo kuxi don in zurfafa neman ilimi na”. “Mun kwana da maza iri-iri har a kan hanya muna tsayawa a kan tituna.” inji ta

Ta qara da cewa, “ ‘mafi yawanci ‘yan matan suna barin gida ne da qarfe uku na dare su tsaya a titi neman abokan hulxa kuma uwar xakin mu tana tilasta mana mu kwana da maza koda muna al’adan. Tana ce mana ba ta yadda aikin ta ya tsaya ba. “Akwai wata adugar mata da take bamu tace mu tare jinin bata barin mu mu zauna a gida ciyar da ita da tufatar da ita da kuxin hayar ta duk mu muke biya. “Mu muke sayawa kan mu kororon Roba wani lokacin maza daga shida zuwa bakwai suna zuwa gu na suna ko wannen sai ya biya ni kuxin Rasha 1,000 kafin su kwanta dani a kullum wani lokacin indan kasuwa ta buxe har 10,000 zuwa 15,000. “1,000 na kuxin Rashnin ya kai kima bout dalar Amurka 17,inda kuama ya kai daidai da naira 6,120”. Ta kuma bayyana yadda wataran wasu maza suka sukayi mata taron dangi suka yi mata fyaxe da wani lokaci da ‘yan sanda suka cafke ta suka kulle ta a office xinsu har tsawon kwanaki suka kuma yi mata duka da fyaxe.

Wasu daga cikin ‘yan matan.

Ta qara da cewa, “har fitsari suke yi akai na in kuma nace su biya ni kuxi na sai suce min in kai qarar su ga mahukuntan qasar in kuma faxa cewar sun yi mini faxe, ba zan iya kai qarar ba domin bami da wata shedar d azan gabatar kuma na san hukumar bazata saurare nib a tunda ni karuwa ce. “A hankali na yanke shawarar

daina yin karuwanci na samu na gudo na dawo Nijeriya ba tare da Fasgo, wani xan Nijeriya da ake kira Mista Ken”. A qarshe ta ce, “kafin na gudu ina biyan uwar xaki na dalar Amurka 15,000 daga cikin dalar Amurka 50,000 da take sa ran zan riqa bata don ta ;yanta ni na yi matuqar dana sanin tafiya ta Rusha”.


29

A Yau Litinin 12 Ga Maris, 2018 (23 Ga Jumada Thani, 1439)

Qasashen Waje

Tare da Rabiu Ali Indabawa 08069824895

Shugaban Faransa Da Ministan Indiya Sun Sanya Wa Yarjejeniya 50 Hannu Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Fira Ministan Indiya Narendra Modi, a Birnin New Delhi a shekaran jiya. Aqalla yarjejeniyoyi 50 shugaban Faransa Emmanuel Macron da Fira Ministan Indiya Narendra Modi suka sanya wa hannu, bayan ganawarsu ta farko a ziyarar kwanaki hudu da shugaban na Faransa ke yi a qasar ta Indiya.

Daga cikin yajejeniyoyin akwai sa hannu wajen karfafa alakar samar da tsaro a mashigin tekun Indiya, da kuma fannonin kasuwanci da zuba hannun jari da jimmilar kudinsu ya kai euro biliyan 13. Macron ya ce babban makasudin ziyararsa shi ne daukar Indiya a matsayin babbar kawa Faransa a kudancin nahiyar Asiya, da kuma aiki tare akan

batutuwan da suka shafi tsaro, canjin yanayi da kasuwanci. Shugabannin sun kuma amince da hadin gwiwa wajen bunqasa samarwa da kuma sarrafa makamashi daga fannonin hasken rana da gina cibiyoyin makamashin nukiliya. Zuwa yanzu an shafe akalla shekaru 20 Faransa da Indiya na rike da kyakkyawar alaka ta Dilomasiyya.

Haraji Kan Qarafa: Turai Da Japan Sun Nuna Damuwarsu Kan Matakin Amurka Tawagar cinikayya ta qasar Japan da ta Tarayyar Turai sun gana da takwararsu ta Amurka a jiya Asabar, a wani kokarin kawar da yakin cinikayya a kan niyar shugaban Amurka Donald Trump na dora kudin fito a kan tama da farin karfe. A ganawar tasu, wakilin Amurka Robert Lightizer da kwamishinan cinikayya ta Tarayyar Turai Cecilia Malmstrom da takwararsu na

Xi Jinpin Na Sharar Fagen Zama Shugaban Chana Na Din-din-din Majalisar qasar Chana mai manbobi 2, 924, zata kada kuri’ar amincewa da soke tsarin wa’adi a shugabancin qasar, abin da zai bai wa Xi Jinping zama shugaban qasar ta Chana na din-din-din. Daga shekarar 1990 Chana ta fara amfani da tsarin wa’adi biyu bisa shugabancin qasar. Amma a karshen watan fabarairu da ya gabata, jam’iyyar qasar mai ra’ayin gurguzu da ke muki ta gabatar da bukatar soke bin tsarin wa’adin, abin da zai baiwa Xi Jin Ping damar cigaba da shugabanci bayan karewar wa’adinsa a 2023. Duk dacewa ana kyautata zaton majalisar mai manbobi dubu 2, 924 zata amince da bukatar cikin sauki, akwai yiwuwar wasu da dama su

kauracewa jefawa bukatar kuri’a. Shugaban Amurka Donald Trump ya fara fuskantar suka bisa kalaman da ya yin a baya bayan nan, na goyon

bayan yunkurin na bai wa Xi Jinpin damar zama shugaban Chana na dindin-din, inda ya ce babu mamaki suma Amurkawa su gwada yunkurin a nan gaba.

qasar Japan Hiroshige Seko sun tattauna a kan yanda bangarorin zasu yiwa juna adalci a huskar kasuwanci. Tarayyar Turai ta fada a wata sanarwa cewa ita da Japan suna da matukar damuwa a kan wannan kudin fito na Amurka. Manyan qasashen masu tasiri, kuma manyan abokan kasuwancin Amurka sun bukaci a fiddasu daga wannan kudin fiton. Jim kadan bayan tattauanawar, Malmstrom, ta

dora a kan shafinta na Tweeter cewar babu alama ko Amurka zata fiddasu a cikin batun harajin, don haka tattaunawa zata ci gaba a mako mai zuwa. Shiko Seko mai wakiltan Japan, ya fada a wani taron manema labara bayan ganawar, yace yayi tsayin daka kuma ya bayyana matsayinsa cewa wannan batu abin takaici ne, ya kuma ce wannan abu zai yi mummunar tasiri a kan bakin dayan tsarin huldan cinikayya.

Sakataren Amurka Rex Tillerson Ya Warke Daga Cutar Dake Damunsa Sakatare Rex Tillerson na Amurka ya murmure daga rashin lafiyar da ya yi fama da ita, bayan da ya soke wasu taruka da ya kamata ya je a qasar Kenya yayin wata ziyarar qasashe biyar da yake yi a nahiyar Afirka. Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson, ya koma bakin aiki a ziyarar da yake yi a Kenya, bayan da ya soke halartar tarukan da aka tsara zai je a jiya Asabar, sanadiyar rashin lafiya da ya yi fama da ita. A yau Lahadi, Tillerson ya ajiye kunshin furanni a ofishin jakadancin Amurka da ke Birnin Nairobi, a wani biki da aka yi domin karrama wadanda suka jikkata da kuma wadanda suka mutu a harin bam din da aka kai wa ofishin shekaru 20 da suka gabata. Bayan da ya gana da shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta a ranar Juma’a a

Birnin na Nairobi, Tillerson ya yaba shirin sasanta rikicin siyasar qasar da shugaba Kenyatta da abokin hamayyarsa Raila Odinga suka fara. Ya kuma kwatanta shirin a matsayin “gagarumin ci gaba da aka samu a fannin sasanta rikicin kabilanci da na siyasa da ya haifar da rarrabuwar kawuna,” kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Amurkan ta sanarwa.


Wasanni 30

A Yau

Litinin 12.3.2018

Tare da Abba Ibrahim Wada Leadership Ayau@yahoo.com

Na Gama Da Liverpool Saura Sevilla, Inji Mourinho Daga Abba Ibrahim Wada Gwale koyar da yan wasan qungiyar qwallon qafa ta manchester United, Jose Mourinho, ya bayyana cewa yanzu kuma hankalinsa zai koma wasan zakarun turai da zasu fafata da qungiyar Sevilla a ranar Talata bayan kammala wasan Liverpool. Marcus Rashford ne ya zura qwallaye biyun da Manchester United ta doke Liverpool sannan ta qarfafa matsayinta na kasancewa ta biyu a saman tebirin gasar firimiya ta Ingila. Wannan nasarar na nufin qungiyar, wacce Jose Mourinho ke jagoranta, na ci gaba da cike givin da ke tsakaninta da Manchester City wadda ke matsayi na xaya a tebirin da tsiran maki 13 - aqalla dai har sai lokacin wasan da Manchester City za ta yi da Stoke City ranar Litinin - kuma tana da tazarar maki biyar da Liverpool wacce ke matsayi na uku. Rashford, wanda ya buga wasansa na farko tun bayan wanda ya buga ranar 26 ga watan Disamba, zai zama xan wasan da manema labarai za su fi tattaunawa a kansa, ko da yake ya ci dukkan qwallayen ne da taimakon Romelu Lukaku. Qwallon da Lukaku xan qasar ta Belgium ya doka da ka ce ta isa wurin Rashford wanda nan da nan ya zura ta a raga bayan yayi wani wayo yadawo da ita da baya lokacin da xan wasan Liverpool yake binsa a baya. Qwallo ta biyu da United ta ci kuwa, Lukaku ne ya riqe wallon sannan ya miqa ta ga Juan Mata, wanda bai samu damar buga ta ba ta faxa hannun Rashford wanda ya sake zura ta a ragar ta Liverpool bayan qwallon ta daki xan wasan Liverpool ta canja hanya Dawowar da Sanchez ya yi zuwa Manchester United daga Arsenal a watan Janairu ta yi tasiri sosai kan ‘yan wasan United, ciki har da Rashford, wanda bai buga wasan da ya wuce na minti 100 ba kuma ana sanya shi ne domin maye gurbin wani dan wasan wato bayan hutun rabin lokaci Sai da Rashford ya yi ta jira domin damarsa ta zo, kuma bai yi watsi da ita ba da ta zo xin a lokacin da kocin Ingila Gareth Southgate ke kallon wasansu. Manchester United za ta bi sahun Liverpool da makwabciyarta Manchester City domin buga wasan ‘yan-takwas na gasar cin Kofin Zakarun Turai zagaye na biyu, inda za su fafata da Sevilla ranar Laraba, bayan yin 0-0 a Sipaniya. Mourinho ya bayyana cewa wasan da zasu fafata da Sevilla shine mafi mahimmanci a wannan makon kuma yace zasuyi iya qoqarinsu domin ganin sun doke Sevilla sun kai zuwa mataki na gaba.

Za Mu Ba Duniya Mamaki Akan Barcelona, Inji Willian

Matar Messi Ta Haihu An Sa Wa Xan Suna Ciro

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale Xan wasan gaba na qungiyar qwallon qafa ta Chelsea, Willian, ya bayyana cewa zasu bawa duniya mamaki a wasan da zasu fafata da qungiyar qwallon qafa ta Barcelona idan sun kai ziyara filin wasa na Nou Camp a ranar Laraba. Willian, mai shekara 28 a duniya wanda kuma shine ya zurawa Chelsea qwallonta a wasan da qungiyoyin biyu suka buga xaya da xaya a wasan farko da suka buga a filin wasa na Stamford Bridge yace sun gama shiryawa tsaf domin tun karar Barcelona. Ya ci gaba da cewa duk da abune mai wahala buga wasa a filin wasan Barcelona amma zasu dage kuma zasu

nunawa duniya cewa qarfinsu yakai buga wasa da Barcelona a gidansu kuma su dokesu. Ya qara da cewa wasan da suka buga na farko basu da nasara ne kawai amma sun buga wasan daya kamata ace sunci Barcelona qwallaye uku amma kuma duk da haka sakamakon yayi kyau tunda basuyi rashin nasara ba. Sannan kuma yace yanzu abinda yake gabansu shine doke Barcelona sannan kuma su kasance cikin qungiyoyi huxu na farko a gasar firimiya ta ingila domin samun gurbin zuwa gasar cin kofin zakarun turai a shekara mai zuwa. A wasanni 8 da qungiyoyin suka buga a baya dai Barcelona bata samu nasara akan Chelsea ba a gasanni daba-daban.

Xan wasan gaba na qungiyar qwallon qafa ta Barcelona, Leonel Messi ya bayyana a shafinsa na sada zumunta cewa matarsa, “Antonella” ta haihu kuma tuni aka sakawa yaron suna “Ciro” sannan kuma duka yaron da uwar suna cikin qoshin lafiya. Messi, bai buga wasan da Barcelona ta buga ba a ranar Asabar da qungiyar Malaga sakamakon haihuwar ya bayyana cewa yana farin ciki sosai kuma yana yiwa magoya bayansa dake faxin duniya godiya bisa kulawar da suke bashi. Tun farko dai daman Messi yanada ‘ya’ya guda biyu Matteo da Thiago waxanda matar tasa ta Haifa masa a shekarun baya, ya kuma bayyana cewa barinsa shine yaga iyalinsa suna cikin farin ciki da walwala kamar kowanne iyali. Barcelona dai a yammacin ranar Asabar ta bayyana cewa Messi bazai buga wasan da tabuga da Malaga ba saboda wasu dalilai ta taya xan wasan nata murnar samun qaruwa inda ta bayyana cewa wannan ba qaramin abin farin ciki bane kuma duka qungiyar tana tayashi murna. A ranar Laraba ne dai Barcelona zata karvi baquncin qungiyar qwallon qafa ta Chelsea a filin wasa na Nou Camp a wasan qungiyoyi 16 na gasar zakarun turai bayan 1-1 da suka buga a wasan

farko makonni biyu da suka gabata. Kawo yanzu dai Barcelona tana kan gaba akan teburin laliga inda tabawa wadda take mataki na biyu, Atletico Madrid maki 8 yayinda Real Madrid take mataki na uku. Messi ya zura qwallaye 32 cikin wasanni 41 daya buga kawo yanzu a dukkan wasannin daya bugawa qungiyar.


wasanni 31

A Yau Litinin 12 Ga Maris, 2018 (23 Ga Jumada Thani, 1439)

Barcelona Ta Amince Da Siyan Arthur Daga Gremio Daga Abba Ibrahim Wada Gwale Qungiyar qwallon qafa ta Barcelona ta tabbatar da cewa ta amince da siyan xan wasan tsakiyar qungiyar qwallon qafa ta Gremio, Arthur Henrique Ramos mai shekara 26 wanda zai koma qungiyar a watan Yulin shekara mai zuwa. Itama qungiyar qwallon qafar ta Gremio ta tabbatar da cinikin inda tace ta amince da siyar da xan wasan zuwa Barcelona akan fam miliyan 26 sannan kuma zata karvi qarin fam miliyan 8 idan har Barcelona zata biya kuxin a watan na Yuli. Qungiyoyin Manchester United da Tottenham da Inte Millan dai sun daxe suna zawarcin xan wasan wanda akewa laqabi da sabon Rivaldo. Xan wasan zai kasance xan wasan qasar Brazil na uku a qungiyar Barcelona kawo yanzu bayan Philliph Coutinho da Paulinho waxanda suke bugawa qungiyar wasanni a yanzu. Qungiyar Barcelona dai tana neman yan wasan tsakiya domin fara tanadin yan wasan da zasu maye mata gurbin Sergio Basquet da kuma Andries Iniesta waxanda duka shekaru suka fara cimmusu kuma qoqarinsu yana raguwa. Barcelona dai kuma har ila yau tana zawarcin xan wasan gaba na Atletico Madrid, Antonio Griezman, xan wasan qasar Faransa wanda ake tunanin zai kai kuxi kusan fam miliyan 80 a qarshen kaka idan har Barcelona ta amince zata biya kuxin.

Na Shirya Zama Mai Koyar Da Arsenal -ALLEGRI Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Mai koyar da yan wasan qungiyar qwallon qafa ta Juventus, Maximiliano Allegri ya bayyana cewa yagama shiryawa domin karvar aikin koyar da qungiyar qwallon qafa ta Arsenal a qarshen kaka. Allegri, mai shekara 52 ya bayyana hakane inda yace tuni yafara koyan yaren turanci kuma yafara tunanin rayuwa a birnin Landan a shekara mai kamawa. Qungiyar qwallon qafa ta Arsenal dai ana tunanin zata nemi sabon mai koyarwa domin cigaba da koyar

da qungiyar bayan da ake tunanin mai koyar da qungiyar, Mista Arsene Wenger zai ajiye aikin koyar da qungiyar sakamakon matsin lamba dayake fuskanta. A kwanakin baya ma dai an danganta mai koyarwar, xan qasar Italiya, da karvar aikin koyar da qungiyar qwallon qafa ta Chelsea inda zai karvi koyarwar a hannun xan uwansa xan qasar italiya, Antonio Conte. Arsene Wenger dai yana fuskantar matsin lamba daga vangaren magoya bayan qungiyar sakamakon qungiyar tasha kashi sau 4 jere a wasan firimiya dana Europa da kuma rashin nasara

a hannun Manchester City a wasan qarshe na cin kofin Karabawo. Wenger dai ya shafe shekara 22 yana koyar da Arsenal bayan daya jagorancin qungiyar ta lashe kofuna daba-daban ciki har da kofin firimiya guda uku sannan kuma yakawowa qungiyar shahararrun yan wasa a lokutan baya. Har yanzu dai mahukuntan qungiyar basu ce komai ba game da makomar Wenger sai dai kamar yadda rahotanni suke fitowa abune mai wahala ya ci gaba da zama a qungiyar indai bai lashe kofin Europa ba da qungiyar take fafatawa a yanzu.

Ina Son Barin Real Madrid Har Abada, Inji Contrao Xan wasan qungiyar qwallon qafa ta Real Madrid, Fabio Contrao wanda yake zaman aro a qungiyar qwallonj qafa ta Sporting Lisbon ya bayyana cewa yanason yabar qungiyar qwallon qafa ta Real Madrid gaba xaya a qarshen kaka. Contrao, wanda yakoma Real Madrid a shekara ta 2011 daga qungiyar qwallon qafa ta Benfica wadda itama take qasar Portugal yace abune mai wahala barin qungiya kamar Real Madrid saboda irin girmanta da tarihinta. Ya ci gaba da cewa lokacin da yakoma qungiyar yayi farin ciki a rayuwarsa domin yasan cewa yaje maqura a wasan qwallon qafa saboda haka baya buqatar komai sai dagewa domin samun buga wasanni. Sai dai yace daga baya abubuwa suka dinga tafiya ba dai-dai ba na jin ciwo da kuma abubuwan da suka saka yasamu matsala dayawa ta rashin buga wasa a qungiyar. Ya qara da cewa yana farin ciki a qungiyar dayake a yanzu ta Sporting Lisbon kuma baya fatan barin qungiyar sai dai bazai tava nuna farin cikinsa ba idan Real Madrid tayi rashin nasara a kowanne wasa saboda qungiyar tayi masa komai kuma bazai tava mantawa da ita a rayuwarsa ba. Contrao dai yabuga wasanni 43 ne a qungiyar tun bayan komawarsa qungiyar a shekara ta 2011 sannan kuma ya wakilci qasarsa ta Portugal a wasanni daba-daban da suka gayyace shi.


AyAU LEADERSHIP 12.3.18

Litinin

Don Allah Da Kishin Qasa

www.leadershipayau.com Leadership A Yau

Jaridar hausa mai fitowa kullum ta farko a nijeriya

LeadershipAyau

No: 066

Muqalar Litinin

N150

wasanni

Matar Messi Ta Haihu An Sa Wa Xan Suna Ciro > shafi na 30

Kashe Buharin Daji: Wane Ne Dogo Gide, Kuma Ina Yake?

Sulaiman Bala Idris

A makon da ya gabata dai, cikin ikon Allah da nufinsa, an kawo qarshen shafin hatsabibin makashin nan, wanda aka fi sani da Buharin Daji. Buharin Daji, asalin sunan da aka fi saninsa da shi, kafin ya gawurta, ya fara keta mutuncin al’umma, an fi kiransa da Buhari Tsoho. Da yawan waxanda suka yi mishi farin sani, har yanzun Buhari Tsoho suke kiranshi da shi. Wasu ma ba su sanya ‘Buharin’ a sunan, sai dai su ce Tsoho kawai. Hatsabibi ne na gaske, wanda ke ji da kansa a harkar rashin mutunci. tsagera na wanda kansa ke hayaqi. Irin mutanen nan ne masu mugun ji da kansu, waxanda kuma ji – ji da kai xin ke kai su ga ajali. Tsoho – Buharin Daji a wani faife da na saurara, kafin ya haxu da ajalinsa, cikin Gadara ya ke magana, yana cewa ‘Sai Zamfara ta koma tamkar Maiduguri’. Wai kuma fa a wurin Buharin Daji, gaskiya yake faxi, domin ya ce, ba barazana yake yi ba. Tsabar raina gwamnatin Jihar Zamfara da Buharin Daji yayi ne, ya sa yake jin kansa kamar wani Sarki, •Gawar Buharin Daji yayin da Sojoji suka xauko ta a makon da ya gabata wanda ya fi Fir’auna iko da qarfi. Kuma ba wai hasashe ko ga dukkan na Tsoho, ya biyo bayan sace Shanu neme shi an rasa, saboda ya raina alamu ba, a’a, a qashin gaskiya yana da yi wa mata fyaxe da yayi a gidan tukuicin da gwamnatin ta bashi. Kuma Majiyar ta ci gaba da bayyana da nashi dalilan na raina Mahukuntan surukan Dogo Gide. Dogo Gide yayi iyaka iyawarsa cewa; Dogo Gide ne ya sanar da Jihar Zamfara. Banda Zamfara, a ina ne za a wurin ganin Buharin Daji ya sako Jami’an tsaro wurin da za su je su sakarwa Makashi kamar Buharin Daji Shanu da matan da ya sace musu, xauki gawar Buharin Daji tare da mara yayi ta tsula tsiyarsa? Kuma wai amma hakan ta ci tura. Wannan makusantansa shida waxanda ya irin waxannan maganganun ne idan lamari ne ya hargitsa Dogo (wanda kashe. Ko da Sojoji suka shiga Dajin tare aka faxi ko aka tanka a kai, sai ciwo wata majiyar ke nuni da cewa ya tuba, har ma yana taimakon jam’ian da taimakon ‘yan sa kai, sun tarad da ya zama qari. Saboda tsabar rainin hankali irin tsaro wurin daqile varayin Shanu a gawarwakin kamar yadda Dogo Gide ya sanar da su, sai dai bisa umurnin na Buharin Daji, ba Zamfara ba ce yankin). Daga qarshe, sai Buharin Daji ya da suka samu, gawar Buharin Daji kawai iyakarsa, yak an tsallaka zuwa wasu sassan Katsina da Kaduna a aminta da su haxu da Dogo Gide a kawai za su xauko, kuma ita xin suka inda yake aikata ayyukan ta’addanci Dajin Nabango a gundumar Goron xauko suka kai ta Gidan Gwamnatin da keta haddi. Mafakarsa dai ita ce, Dutse ta Qaramar Hukumar Birnin Jihar Zamfara. Akwai wasu tambayoyi da Gwari dake Jihar Kaduna, domin a yi Jihar Zamfara. gwamnatin Jihar Zamfara ya kamata Tsoho ya haxu da ajalisansa ne a zaman sulhu kan batun. Ko da lokacin haxuwarsu yayi a ta amsa su. Na farko dai, wane ne ranar Larabar makon da ya gabata, an kuma tsinto gawarsa a ranar Juma’ar ranar Larabar da ta gabata, yayin da Dogo Gide? na biyu, shin tuntuni Buharin Daji suka iso wurin shi da me ya hana shi ya xirkawa Buharin da ta gabata. Rahotanni daga Jihar Zamfara sun ‘yan tawagarsa, sai Dogo Gide ya buxe Daji harsasai har sai bayan da ya sace tabbatar da cewa, wannan hatsabibin musu wuta. Inda a wata ruwayar aka Shanu da matan Surukansa? Kafin mu je ga tambayoyi na gaba. makashi, Buharin Daji xan asalin ce, a take ya kashe Buharin Daji da Garin Dangulbi ne, wani qauye dake kwamandoji Shida daga cikin manyan Na fara wani tunani, kuma ya kamata kowa ma yayi wannan tunanin. Daga Maqwabtaka da garin Dansadau dake hatsabiban yaransa varayin Shanu. Wata Majiya mai tushe ta naqalto labaran da suka fito na yadda Dogo Qaramar hukumar Maru, a Jihar cewa, Gwamnatin Jihar Zamfara ta Gide ya samu nasarar kashe Buharin Zamfara. Yaronsa, wanda a wani rahoton xauki nauyin Dogo Gide domin ya Daji, za mu iya fahimtar wani abu ake nuni da cewa, yana daga cikin na halarci qasa mai tsarki don yin aikin xaya; wannan abin kuwa shi ne; Dogo hannun daman Buharin Dajin, wato Hajji a wannan shekara mai zuwa. fa ya fi Buhari wayo, dabara da zafin Dogo Gide shi ne ya samu nasarar Amma kuma, inji majiyar, sai Dogo nama. Kuma ga dukkan alamu ba halaka shugaban ‘yan ta’addan. Kisan Gide ya yi tutsu, zuwa yanzu ma an don Allah Dogo ya kashe Buhari ba,

0703 666 6850

tunda har ya raina tukuicin kujarar Makka! Idan Dogo Gide ya rikixe, labarin zai canza. Don haka tun da wuri, tun kafin a yi latti, ana buqatar a nemo Dogo Gide a duk inda yake. Ba kawai ido za a sa mishi ba, domin shi ma barazana ne ga rayukan al’umma da zaman lafiya. Wane ne Dogo, kuma ina yake? Gwamnatin Jihar Zamfara ce za ta bamu amsa.

Babba Da Jaka Za a samu hauhawar Farashin Giya da Taba a Nijeriya

Shinkafa dai za ta sauko koh?

Ana shiryawa da buga LEADERSHIP A Yau a kamfanin LEADERSHIP GROUP LIMITED, lamba 27, kan Titin Ibrahim Tahir, a Gundumar Utako, Abuja. Tarho: 09-2345055; Fax: 09-2345360. P. O. Box 9514, Garki II, Abuja. Ofishin mu a Legas: 34/36 Titin Adegbola, Anifowose, daidai Oba Akran, Ikeja. Tarho: 01-8963459. E-mel: leadershipayau@yahoo.com

LEADERSHIP A Yau E-paper 12 Ga Maris 2018  

LEADERSHIP A Yau E-paper 12 Ga Maris 2018

LEADERSHIP A Yau E-paper 12 Ga Maris 2018  

LEADERSHIP A Yau E-paper 12 Ga Maris 2018

Advertisement