Page 1

11.03.18

AyAU LAHADI LEADERSHIP Don Allah Da Kishin Qasa

www.leadershipayau.com

JARIDAR HAUSA MAI FITOWA KULLUM TA FARKO A NIJERIYA Leadership A Yau

11 Ga Maris, 2018 (22 Ga Jumadal Thani, 1439)

LeadershipAyau

No: 026

N150

Kuskure Ne Nijeriya Ta Cigaba Da Zama A Matsayin Bamagujiya –Gali Na’Abba Daga Mustapha Ibrahim, Kano

Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayyar Nijeriya, Rt. Hon. Gali Umar Na’Abba, ya bayyana cewa, zaman Najeriya a matsayin qasa wacce ba ta da addini kuskure ne, domin kuwa Nijeriya qasa ce da ta ke da mabiya addinin Musulunci da na Kirista kuma kowa ya na ba da gudunmawarsa ta addu’a a kan

abinda ya yi imani da shi, domin cigaban qasar ta hanyar yin addu’ar samun zaman lafiya a wannan qasa. Don haka kuskure ne Nijeriya ta cigaba da zama a matsayin bamagujiyar qasa maras addini. Wannan bayani ya fito ne daga bakin Na’Abba a yayin wata hira da manema labarai a Kano a lokacin bikin yaye wasu xaliban makarantar Madinatul Ahbab qarqashin jagorancin

Sace Xaliban Dapchi:

Khalifa Sheik Xayyib Sheik Haruna Rashid Fagge a birnin Kano. Don haka tsohon kakakin ya yi kira ga xaukacin masu ruwa da tsaki a Nijeriya da su tsaya su yi nazari wajen samo wa Nijeriya kyakkyawar alqibbila wacce ta fi ta ’yan mulkin mallaka da su ka xora ta a kai tun shekaru aru-aru wanda da yawa abubuwan na cike da kurakurai da buqatar gyara. > Shafi na 5

’Yan Sanda Za Su Yi Abinda Ke Neman Gagarar Sojoji 5

Annobar Cutar Kwalara Budurwa Ta Babbake Kanta Saboda Soyayya A Jigawa Ta Fara Kisa A Bauchi > Shafi naa 8

> Shafi na 4

Masu martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, da Sarkin Gombe Abubakar Shehu Abubakar III, a wajen taron yaye xalibai na Jami’ar Jihar Gombe karo na da a ka gudanar a jiya Asabar


2

A Yau LAHADI 11.03.2018

leadershipayaulahadi@yahoo.com

Yadda A Ka Yi Na Assasa Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya – Fadila Kurfi FADILA H. ALIYU KURFI fitacciyar marubuciya ce mazauniyar birnin Katsina, wacce ita ce ta assasa Taron Ranar Marubuta Ta Duniya da a ke yi shirin yi duk shekara. Idan ba ku manta ba, a wata hira da mu ka tava yi da shugaban kwamitin taron na bana, Malam Rabiu Na’auwa, a bara ya shaida ma na cewa, Fadila ce silar fara wannan taro na duniya. To, saboda ganin cewa a qarshen mako mai zuwa ne za a gudanar da wannan taro na bana a birnin Katsina daga ranar 16 zuwa 18 ga Maris 2018, Editan LEADERSHIP A YAU LAHADI, NASIR S. GWANGWAZO, ya zanta da wannan zaqaqurar mace mai kamar maza, wato Fadila Kurfi, don jin yadda a ka yi ta assasa wannan taro. Ga yadda tattaunawar ta kasance: Mene ne tarihin rayuwarki? Sunana Fadila H. Aliyu Kurfi, ‘yar asalin jahar Katsina, mahaifana ’yan garin Kurfi ne, amma ni an haife ni a garin Katsina kuma mu na da zama a nan. Mu shida ne gidanmu, ni ce ta biyu a wurin Mamata da Daddy, sannan mu biyu ne mata, sauran huxu maza. Na yi aure, amma yanzu ba mu tare. Ina da yarinya ta xaya, Ibtihal Bashir Kurfi. Na yi karatuna a cikin garin Katsina, Ina da difloma a vangaren girke-girke, sannan NCE a vangaren Turanci da Hausa, kuma insha Allahu zan cigaba da karatu har sai baba ta gani, saboda Ina da sha’awar karatun. Mene ne dalilinki na sha’awar rubutu kuma ya a ka yi ki ka fara? Zan iya cewa sha’awar rubutu tashi na yi da abuna. Na fara rubutu tun Ina firamare, inda na ke amfani da littafina mai shafi 20 na qirqiri labari da kaina na rubuta. Idan na rubuta zan ba wa abokaina su karanta su kuma su ba wa nasu abokan. Haka za a yi ta yawo da shi har ya tsufa ya yage. Dalilin haka na taso da farin jini sosai cikin xalibai ‘yan uwana; duk inda na nufa a na nuna ni a kan ni ce na yi wannan littafin. Tun Ina qarama na taso cikin mutane da jama’a maza da mata. Har zuwa matakin sakandire Ina rubutuna da biro da takardar a na karantawa. Da na yi suna, da ya ke makarantar kwana na yi, sai manyan xalibai na gaba da ni su riqa kira na kwana Ina ba su labari da baki. Dalilin haka na samu sauqin wahalar makarantar kwana duk da kuwa Ina da xan qiriniya kuma na yi suna sosai. Bayan na kammala sakandire sai na fara burin na fitar da littattafi ni ma kamar yadda Nazir Adam Salihi da Rahma Abdulmajid su ke yi. Babban tashin hakalin shi ne ban san Ina a ke buga littafi ba. Ga su dai na rubuta, amma Ina zan kai a buga ma ni kuma ya zan yi duniya ta karanta su ita ce matsalata. Lokacin Ina da qananun shekaru qwarai. Kafin na samo mafita guguwar aure ta yi ciki da ni. Wanda na aura bai damu da harkar rubutu ba, ni kuma ban iya haqura da shi, bai ba ni qwarin gwiwar buga littafi ba, amma hakan na yi ta rubuta abuna Ina tarawa. Sai bayan mun rabu na tuna akwai wani da ke ba ni kyautar littafi idan na shiga kasuwa. Shamsudden Fatimiyya shi ne ya saka ni a hanyar rubutu, sannan ya matsa ma ni shiga qungiyoyi. A wacce shekara ki ka fara fitar da littafi? A shekara ta 2014 na fitar da litattafina na farko mai suna Buwayar Sadaukai (labarin Sadauki Hisham), sannan kuma na qirqiri ‘group’ na marubutan Hausa mai suna Gidan Marubutan Hausa a Watsapp. Shi ne group na farko da ya fara tattara mabambantan qungiyoyin marubuta a inuwa xaya ba tare da an samu savani ba ko rikici ba, sannan shi ne group na farko mai xauke da kotu, inda duk wasu su ka samu savani ko rikici za a sasanta.

Na sha matuqar wahala kafin na samu nasarar raya gidan. Na yi ta bin marubuta Ina nuna ma su manufata; wasu su kan amsa su ce na saka su, amma ba sa magana. Ina cikin haka na yi karo da wasu zaqwaqwuren matasan marubuta waxanda su ka taya wurin qara jawo hankalin marubuta. Marubutan kuwa su ne Abdurrahman Aliyu, Fatima Ibrahim Xanbarno, Kwamared Muhammad Zailani, Maryam Nuhu Turau, Usman Alkasim, Sa’adiya Garba Yakasai, Nura Sada Nasimat da Zainab Xahiru Wowo. Ba zan tava mantawa da gudunmawar da su ka bayar ba. A 2015 na fitar da littafina na biyu mai suna Rundunar Sadaukai. Lokacin ‘group’ xina ya yi suna ta yadda marubuta ke neman a saka su da kansu; gidan ya cika da fasihai, sai na fara tunanin wacce hanya zan bi domin mu amfanar da Hausawa, sannan mu gyara rubucerubucenmu domin duniyar fasaha a dama da mu? Abin da na fara kula da shi shi ne mutane ba su san marubuta sai dai rubutunsu su ka sa ni. Daga nan ne na fara tunanin samar da Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya. Mene ne manufar wannan taro na Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya kuma ya a ka yi nasarar qirqirar shi? Manufar taron shi ne domin marubuta su gyara rubutunsu ya zamo mai fa’ida da ma’ana, sannan su riqa rubutu wanda ya shafi al’adarmu ba ta Turawa ba, domin zaburar da matasa da yara su rinqa karatu a madadin su guje ma sa. Ta hanyar karatu matasa za su fuskanci gwagwarmayar da magabatanmu su ka sha kafin su gina qasarmu, idan su ka san wahalar da su ka sha zai taimaka masu wurin kishin qasa. Mai kishin qasarsa dole ya zama xan qasa nagari. Da taimakon alqalumanmu qasa za ta iya zama lafiya. Na qirqiri taron ne domin samar da ’yan qasa nagari, sannan yaranmu masu tasowa za su taso da sha’awar al’adunmu na gado. Wannan yawan faxacefaxacen da zubar jini ba al’adunmu ba ne. Kowacce qabila ba ta cigaba sai ta riqe martabar qasarta da al’adun gado. Wannan ita ce manufar. Wacce nasara a ka samu a taron baya kuma wacce a ke sa ran samu a na bana? Farko an samu haxin kan marubuta. Mu na yanka ma junanmu adadin kuxin da za mu bayar kafin mu nemi taimakon da za mu yi taron. Mu na yin sadaukarwa mu xauki nauyin kanmu wurin wasu zirga-zirga zuwa ga sarakunan Arewa da gwamnoni da sauransu, don su sako bakinsu cikin lamarin kuma sun tallafa da kuxi. An yi taron farko cikin nasara a garin Kano. Mun samu haxin kai daga gidan jaridu talabijin da radiyo. Nasarar da a ke son cimma a gaba kuwa, wannan taron mu na saka ran zai taimaka ma masu rubutu da masu karatu wurin farfaxo da al’adun Hausa, zai saka ma yaranmu sha’awar karatu savanin wasa da wayoyi.

• Fadila Kurfi

Wanne buri ki ke son cimma da wannan taron a nan gaba? Burina Hausa ta qara samun xaukaka a duniya, sannan Ina burin mutane su fahimci kyawawan al’adunmu. Ina da burin matasa su san irin muhimmancin gargajiyar Bahaushe. Abu mafi muhimmanci shi ne marubuta sai dai rubuce-rubucensu kan al’adun wasu su riqa yi kan al’adunmu na Hausawa. Ta haka su ma ‘yan wasan Hausa za su riqa yin abubuwa masu ma’ana. Waxanne irin matsaloli taron ke fuskanta? Ka san abu idan a ka ce na mutane da yawa ne bai rasa matsaloli. Wannan shi ne karo na biyu. Irin matsalar baya ba ita ba ce a ke fuskanta a wannan karon ba. Babban burina shi ne yiwuwar taron cikin nasara. Ina godiya ga ubangaji kasancewar na yi tunani kuma ya zama gaskiya, na saka duk qarfina, qwazona, lokacina da tunanina, domin ganin yiwuwar wannan taro. Ko da zan koma gefe na zama ‘yar kallo ba ni da nadama, saboda na yi ma marubuta abin da ba za su manta da ni ba kuma muddun Ina raye sai martabar rubutu da marubuta ta dawo a idanun al’umma, sai mun yi amfani da alqalumanmu mun tallafi yarenmu da addininmu. Duk masu tafiyar da wata manufa, don Allah su kauce, saboda mu na tufka su na ma na warwara ne. Ya za a yi a shawo kan savanin da ke tsakani, musamman ganin cewa a na ganin tsohon shugaban taron, Ado Ahmad Gidan Dabino MON, ya xan janye jikinsa daga taron bana? Ba zan iya cewa komai kan wannan gavar ba; shi ne ya kamata ya amsa wannan tambayar. Iyaka magana xaya zan yi; duk abin da mutum zai yi ya yi don Allah, idan zai bari ya bari dominSa, kuma auren baya fa shi ne sadakin na gaba. Shin ki na ganin taron zai xore kuwa bisa la’akari da yawan gunguni da a ke samu? Taro zai xore, amma sai an yi gyara sosai cikin tafiyar. Ya kamata a zaqulo masu qauna

• Fadila Kurfi

da cigaban adabi. Sai mun ajiye neman suna da wannan tafiyar. Gaskiya akwai gyara; mutanenmu na da matuqar damuwa a komai namu. Dole mu cire hassada da baqin cikin, domin cimma nasara. Mu sani mu xin tamkar madubi ne ga ‘yan baya, idan mu na saka son zuciya, ba za mu cigaba ba. Babbar matsalar da mu ke fuskanta ita ce son zuciya. Ko wanne xan adam a duniya rabonsa ya ke ci; mu taru mu haxa kai domin cimma manufa, shi ne ya fi. Wane saqo ki ke da shi a qarshe? Saqona ga mutanen qasata ne kuma Hausawa. Ya kamata mu riqa tallafar junanmu, mu riqa kamanta gaskiya, mu koyama yaranmu kishin al’adunmu na Hausa da addini, mu haxa kanmu mu samar da qasa tagari, mu cire zari da son kai. Na gode qwarai.


3

A Yau Lahadi 11 Ga Maris, 2018 (22 Ga Jumadal Thani, 1439)

ra’ayinmu

Cire Tallafin Mai: Ina Amfanin Baxi Ba Rai? Tun wajejen qarshen sherakar da ta gabata ne Nijeriya ta tsunduma cikin masifar qarancin man fetur, wanda a shekarun baya an saba ganin irin duk lokacin da bikin Kirsimeti ya kawo kai, amma a farkon shekara komai ya kan warware. Ma’ana; lamarin ba ya wuce ’yan kwanaki. Don haka abin ya zama kamar ma jiki. To, shi ma wannan qarancin man mafi yawan ’yan Nijeriya na kallon sa a matsayin irin wanda a ka saba gani a shekarun na baya. To, sai dai kuma daga dukkan alamu ba hakan abin ya ke ba a wannan karon, domin ya yi matuqar wuce na al’ada. Idan dai za a iya tunawa, wannan gwamnati a qarqashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta yanke hukuncin janye tallafin mai ne bayan da ta ce ta yi dogon nazari kan cewa, tallafin man was qalilan xin mutane ya ke arzurtawa, sannan kuma tattalin arzikin gwamnatib tarayya ba zai iya jure nauyin da tallafin man da ta ke bayarwa ya ke xora ma ta ba. Don haka ta yanke shawarar soke shi gabaxaya. Wannan dalilin da ya sanya farashin man fetur xin ya yi tashin gwauron zabo rana tsaka daga Naira 87 da gwamnatin tsohon shugaban qasa, Goodluck Ebele Jonathan, ya bar shi zuwa Naira 145 da gwamnatin Buhari ta tsayar. A shekara ta 2011 an yi mummunar zanga-zanga a dukkan faxin qasar kan yunqurin da Jonathan ya yi na cire tallafin man; lamarin da ya tilasta shi janye aniyar tasa. To, amma Shugaba Buhari bai sami irin wannan turjiya ba a lokacin da ya cire tallafin man, duk da cewa a wancan lokacin da Jonathan ya nemi cirewar shi ma bai goyi da bayansa ba, ya kuma soki lamirin manufar. Ko qungiyar qwadago ta qasa, NLC, da ta nemi ta yi tawaye kan batun, mafi yawan ’yan Nijeriya sun juya ma ta baya ne, domin hatta yajin aikin da qungiyar ta kira ma’akata da su yi, ba su yi ma ta biyayya kan hakan ba; sai kowane ma’aikaci ya fita aikinsa, idan ban da ’yan qalilan xin da ba su isa komankomai ba a wasu guraren ’yan kaxan da ba su taka kara sun karya ba. A haka a ka cigaba da tafiya har zuwa lokacin da wannan masifar ta qarancin mai ta dawo a qarshen shekarar 2017, wanda qarancin man ya yi daxewar da ba a tava

ganin makamancinsa ba. Shin mene ne matsalar? Me ya hana a shawo kan wannan annoba, wacce ta hana kowa sakat ta kuma nakasta tattalin arzikin aljihun Malam Talaka? A vangaren dillalan mai su na bayyana cewa, farashin man fetur xin ne ya tashi a kasuwar duniyar, domin a yanzu kafin mai ya iso

gidajen man da za a sayar da shi, a na kashe kimanin Naira 172, kamar yadda wasu majiyoyinsu su ka tabbatat ma na. Don haka wannan ne ya sanya ba za su iya cigaba da sayar da man fetur a farashin Naira 145 ba, domin ya zama babbar faxuwa a cikin kasuwancin kenan, wanda zai iya kai su ga rushewar

EDITA Nasir S. Gwangwazo

MATAIMAKIN SHUGABA (NA MUSAMMAN) Christian Ochiama DARAKTAN SASHE Mubarak Umar

RUKUNIN KAMFANONIN LEADERSHIP SHUGABA Sam Nda-Isaiah

BABBAN MANAJAN DARAKTA Abdul Gombe BABBAN MANAJAN DARAKTAN KADARORI David Chinda MANYAN DARAKTOCIN KAMFANI Dele Fanimo Felicia Ogbonlaiye DARAKTAN KULA DA MA’AIKATA Solomon Nda-Isaiah DARAKTAN KULA DA KADARORIN KAMFANI Zipporah D. Tanko MANYAN MANAJOJI Ibrahim Halilu Femi Adekunle Ebriku John

manufarmu

LEADERSHIP A Yau jarida ce da ake bugawa a Abuja. Ta yi tsayuwar daka wajen tabbatar da shugabanci da wakilci nagari. Jaridar za ta ci gaba da kare muradun al’umma, ba kare ra’ayi da muradun mahukuntanta kaxai ba. Da waxannan qudirorin ne muke fatan jama’a za su xora mu kan Mizani. Haka kuma duk ra’ayoyin masu karatu da muke bugawa, ba manufar kamfanin LEADERSHIP ba ne, ra’ayin masu karatun ne. Sai dai, ba za mu tava mantawa da dalilin wanzuwarmu a doron qasa ba, wato: Don Allah Da Kishin Qasa!

jarinsu. Ita kuwa a nata vangaren, gwamnati ta na ganin cewa, bai dace ta bari a sayar da farashin fiye da yadda ta yiwa ’yan qasa alqawari na Naira 145 ba, domin hakan kamar zai nuna wa talaka cewa ba shi da tabbas a wajenta kenan kuma ta karya dukkan alqawarin da ta xauka na kawo ma sa sassauci a cikin rayuwarsa. Idan ka dubi kowane vangare za ka iya cewa, ya na da gaskiya, domin xan kasuwa riba ya ke nema, ita kuma gwamnati talakawanta ta ke kallo. To, amma abin tambaya shi ne, shin idan a ka cigaba da tafiya a haka, wane ne a cikin wahala? Amsa a nan ita ce talakan qasa ne ya ke wahala idan a ka yi la’akari da irin yadda lamarin ya sanya komai ya ke cigaba da tashin gwauron zabo! Kafin Buhari ya xare kan karagar mulki ya yi alqawarin gina sababbin matatun mai da kuma gyarawa tare da tabbatar da matatun da a ke da su su na yin aikin tace mai yadda ya kamata. Haqiqa za a iya cewa, wannan ce mafita ga Nijeriya, domin qasashen da ba su da xanyen mai ma su na iya sayen shi su tace shi, don amfanin ’yan qasarsu. To, ina ga qasar da ta ke da man kuma? To, amma abin damuwar shi ne, kawo yanzu da Buhari ya shafe kusan shekaru uku a kan karagar mulki ba a gani a qasa ba. Babu wani yanayi na da ya nuna cewa, a cikinb shekara huxun nan gwamnatinsa za ta iya cika wannan alqawari. To, magana ta gaskiya ita ce, idan har gwamnati ba za ta iya samar da man fetur a farashin da talaka zai daina ji a jikinsa ba, to zai fi dacewa ta dawo da tallafin mai, in ya so ta mayar da kai ga aikin matatun mai a qasar ta yadda ba za a xauki tsawon lokaci a na yi ba, za mu fara amfani da namu tataccen man. Ka ga maganar tallafi ta yanke kenan a lokacin. Amma a halin da a ke yi yanzu, haqiqa xan Nijeriya ya na ji a jikinsa, domin cire tallafin man fetur xin bai amfane shi da komai ba, illa jefe shi cikin baqar uquba da kullum ya ke sake yi, saboda yadda hakan ya kawo qarancin mai da hauhawar farashinsa. Ina amfanin baxi ba rai? Ya wajaba a ga cewa gwamnati ta na yin komai ne, don a sami sauqin rayuwa.


4

A Yau LAHADI 5.03.2018

leadershipayaulahadi@yahoo.com

An Yi Bikin Ranar Mata Ta Duniya A Jihar Bauchi Daga Muazu Hardawa, Bauchi

Kasancewar majalisar xinkin duniya ya ware kowace ranar takwas ga watan maris na kowace shekara a matsayin ranar mata ta duniya, maaikatar mata da haxin guiwar ofishin uwargidan gwamnan Jihar Bauchi da qungiyar Oxfam me taimakawa mata daga qasar Canada, sun shirya bikin ranar matan a gidan gwamnatin jiha a ranar alhamis da ta wuce inda aka gayyaci matan daga sassa dabam dabam na Jihar Bauchi kuma aka basu kyaututtuka a matsayin tallafi. Uwargidan gwamnan Jihar Bauchi Hajiya Hadiza Mohammed Abubakar, cikin jawabinta ta yaba da irin gudummowar da mata ke bayarwa wajen cigaban alumma tare kuma da bayyana irin ci gaban da mata suka samu a cikin wannan gwamnatin musamman bayar da horo kan koyon Sana’a da ba da tallafin naira dubu biyar ga mata matasa aikin yi da sauran su. Madam Lydia Shehu darakta a maaikatar mata a jihar Bauchi cikin jawabinta ta bayyana cewa akwai matsaloli masu yawa da mata ke fiskanta a wannan lokacin, don haka ta ja hankalin mata da su himmatu wajen ganin sun kawo qarshen matsalar musamman kan batun neman ilmi. Saboda idan mace ta yi karatu ba sai an ce ta kai yaronta asibiti ba, kuma

tasan yadda zata qayyade iyalinta ba tare da yin kunika ko ta tara yara ta bar su kara zube cikin wahala ba. Don haka ta buqaci matan jihar Bauchi su gode wa gwamnati na bayar da kuxi naira milyan 190 don amfani da su wajen kare lafiyar mata daga rasuwa a lokacin da su ke da juna biyu. Harwa yau ta koka da yadda ake tsangwamar mata idan an ba su matsayi yadda mata da kan su ke illatawa ko vata sunan yan uwansu. Don haka ta buqaci su yi haquri da juna don samun ci gaba, don haka ta buqaci matan su riqa isar da kukan su ga kwamishinar mata da sauran masu riqe da muqamai matan da ke cikin gwamnati. Lydia Shehu ta nemi mata da su daina mayar da kansu baya saboda suna da qoqari wajen xaukar ciki wata tara su kwana da shi su tashi da shi har su sauke. Don haka ta buqaci su zauna da juna lafiya su ci gaba da qoqarin ganin sun ciyar da kan su da iyalen su gaba. Kasancewar qungiyar Oxfam ta shirya wannan taron ranar mata, Madam Hannatu John ta bayyana irin temakon da qungiyar oxfam ta musu wajen ilmantar da su yadda ake nomar masara mai kyau inda suke samun amfani mai yawa ta hanyar bita kan noma da ba su irin shuka na zamani me yi da wuri. Itama uwargidan mataimakin gwamnan Jihar Bauchi Hajiya Fatima Nuhu Gixaxo cikin jawabinta ta, ta godewa Allah game da sake

•Taron ranar mata ta duniya a Bauchi

ganin bikin ranar matan da ake gudanarwa a kowace shekara. Ta ja hankalin matan su tashi tsaye wajen neman abin kan su don ci gaba tare da kare martabar iyalan su. Inda ta bayyana cewa wannan ranace da aka ware domin mata su tattauna kan matsalar da ke damun su ko ina a cikin duniya. Shugabar matan jamiyyar APC a jihar Bauchi Hajiya Saadatu Mahmud cikin jawabinta ta yaba game da naxa kwamishinoni mata uku a jihar Bauchi kuma ta ja hankalin mata da su wayar da kan jamaa wajen fitowa su shiga a dama da su a harkar siyasa. Ta kira mata su fito a fafata da su a siyasa, saboda

duk Arewa maso gabas mata biyu ne a majalisun jiha mace xaya a tarayya. Don haka uwargidan shugaban qasa a zaman da suka yi a Abuja ta nuna damuwa saboda ganin mata xayace ke wakiltar matan jihohi 19 na Arewa a majalisar dattijai ta tarayya. Don haka ta buqaci su miqa saqonta ga matan Arewa da dukkan matar da ta cancanta ta fito don tsayawa takarar kowace kujerar siyasa. Mataimakin gwamnan Jihar Bauchi Injiniya Nuhu Gidado shine ya wakilci gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar, inda cikin jawabinsa ya yaba da ware wannan rana da majalisar

xinkin duniya ta yi don tuna halin da mata ke ciki a duniya. Don haka ya yaba wa matan game da irin tallafin da suke ba mazaje don ci gaba a harkokin su ta hanyar qara musu qarfin guiwa don samun nasara kan duk wata hidima da suka sa a gaba. Don haka ya bayyana cewa wannan gwamnati na ba mata muhimmanci musamman ta hanyar inganta ayyukan hukumar mata da matasa ya BACYWORDnda kuma basu fifiko a shirin xaukan aiki na Npower da kuma xaukan mata don ciyar xaliban makarantun firamare shirin da ya taimaka wajen sama wa mata ayyukan yi don tallafawa iyalan su.

Ta Babbake Kanta Qurmus Sanadiyyar Soyayya A Jigawa Daga Jamila Umar Tanko, Abuja

Wata matashiyar budurwa ’yar kimanin shekaru 18 mai su na Hafsat ta babbake kan ta har lahira a sanadiyar an hana ta kula sAurayin da ta ke so. A makon da ya gaba ta ne a qaramar hukumar Birnin Kudu da ke cikin jihar Jigawa Hafsat ta yi yunqurin halaka kanta bayan ta sha knanzir kuma ta kwara fetur a jikinta daga bisani ta qyartawa kanta ashana, nan take wuta ta kama ta. Mahaifiyarta da su ke zaune a gida xaya ta na daga falonta ta jiyo ihun Hafsat, ba shiri ta fito da gudu. A

cikin wannan hali ta iske ’yarta, inda azaba ta yi azaba

•Marigayiya Hafsat

Hafsat ta fita qofar gida a guje ta na neman agaji. Yaran unguwa su ka yi ta kwara ma ta ruwa, inda da qyar a ka samu wutar ta mutu bayan da jikin Hafsat ya saluve kamar jan garwashi. Yatsun hannayenta da na qafafuwanta duka sun yi qurmus. Nan take a ka garzaya da ita asibiti. Bayan kwanaki Allah Ya yi wa Hafsat cikawa a babban asibitin qashi na Dala da ke cikin Jahar kano. Kafin rasuwarta, Hafsat ta gama sakandire kuma mahaddaciyar Qur’ani ce, sai dai danginta sun tabbatar da cewa vacin rai ne ya tayar da aljanun da

ta ke fama da su, inda su ka tabbatar da cewa ba ita ta qona kanta ba, aljanu ne, domin a cewarsu, da ta na cikin hayacinta ba za ta aikata haka ba. Kamar yadda labari ya zo ma na a majiya mai qarfi, Hafsat ta na soyayya da xan uwanta wanda su ka haxa kakanni mai shekaru 22, wanda tela ne, sai ya yi xinki ya ke biyawa kansa kuxin makaranta har ya fara karatun NCE. Da magabatan Hafsat su ka tuntuvi iyayen yaro sai su ka ce bai isa aure ba. Don haka cikin fushi mahaifiyar Hafsat ta je ta gargaxi iyayen yaro da su hana xansu zuwa

hira marar amfani wajen ’yarta tunda bai shirya yin aure ba. Ko da Hafsat ta ji shiru ba ya zuwa, sai ta tuntuve shi a waya, shi kuma ya sanar ma ta saqon mahaifiyarta kuma ya ji maganarta ba zai sake zuwa ba. Hafsat ta xauki fushi na tsawon kwanaki. A safiyar da abin zai faru mahaifiyar Hafsat ta soya dankali ta xauka da kanta ta kai har gaban Hafsat ta ajiye. Bayan ta tafi Hafsat ta ci dankali ta kora da ruwan sanyi, sannan ta tashi ta shiga xaki ta yi wannan aika-aika, kamar yadda majiyarmu ta tabbatar ma na.


Babban Labari A Yau LAHADI 011.03.2018

5

Sace Xaliban Dapchi: ’Yan Sanda Za Su Yi Abinda Ke Neman Gagarar Sojoji

Daga Muhammad Maitela, Damaturu Mataimakin sufeto janar na ’yan sandan Nijeriya, Mista Joshak Habila, ya bayyana cewa, rundunar ’yan sandan Nijeriya a qarqashin jagorancin Ibrahim Idris Kpotum za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin an gano tare da dawo da ’yan matan Dapchi, waxanda a ke zargin ’yan qungiyar Boko Haram da sace su a makarantarsu ta kwana kwanakin baya kuma a ke ta faman qorafin cewa har kawo yanzu sojojin qasar ba su iya ceto ba. Babban jami’i a rundunar ’yan sandan ya bayyana cewa, jami’an tsaro su na qara

xaukar sabbin matakai da dabarun da za su kai ga nasarar yadda za a ceto xaliban makarantar Dapchi da a ka sace a jihar ta Yobe. Mista Habila ya bayyana hakan ne a sa’ilin da ya ke zanta wa tare da manema labarai a Damaturu, inda ya ce ya zo jihar Yobe domin domin haxuwa da gwamnati haxi da masu ruwa da tsaki a sha’anin ilimi a jihar. “Mun yi taron ne domin lalabo matakan bi da za su kai ga nasarar ceto ’yan matan tare da qarin wasu dabarun xauka kan lamarin daban-daban, kana da yadda za a samu cikakken tsaro a makarantu da

qoqarin kauce wa duk abinda zai kawo cikas a sha’anin karatun,” in ji Habila. Ya qara da cewa, ’yan sanda tare da haxin gwiwa da jami’an tsaron Civil Defence sun riga sun tuttura jami’an tsaro a makarantun jihar. Bugu da qari kuma ya ce, wannan taron zai qunshi kwamishinan ilimi a jihar, manyan jami’an ma’aikatar ilimin, shugabanin manyan makarantu, shugabanin makarantun sakandire da na firamare tare da malaman makarantu a jihar Yobe. Haka zalika kuma, Mataimakin Sufeto Janar xin ya buqaci jami’an ’yan sanda da

qanana da ke jihar kan su bayar da himma wajen gudanar da ayyukan da ke gabansu, domin kaiwa ga samun cikakken tsaro a jihar Yobe. Har wa yau kuma ya ankarar da ’yan sandan kan cewa su yi qoqari wajen gina kyakyyawar alaqa ta gaskiya tsakanin su da jama’a wanda hakan zai sahale mu su hanyar samun sahihan bayanan sirri da zasu basu damar daqile irin wannan ta’asa wadda ta afku. Kana kuma ya qara jaddada muhimmancin gudumawar al’umma a aikin xan sanda ta fuskar gina kyakkyawar alaqa tsakanin ‘yan sanda da jama’a wajen samun tsaro.

...Iyayen Xaliban Dapchi Sun Yi Zanga-Zanga Abuja Daga Muhammad Maitela, Damaturu

• Daga dama zuwa hagu Dan takarar Shugaban Qasa Kingsley Moghalu; Farfesa Wole Soyinka tare da Ambasada Toye Okonlawon shekaran jiya a ziyarar da Moghalu ya kai wa Farfesan a Legas

Kuskure Ne Nijeriya Ta Cigaba Da Zama A Matsayin Bamagujiya –Gali Na’Abba > Ci gaba a shafi na farko Haka kuma ya qara da cewa, abin damuwa ne sosai yadda Nijeriya ta zama qasar da a ka biya aikin Hajjin da ya gabata mafi tsada a tsakanin qasashen duniya duk da irin arziqin da Allah ya yi ma ta. A cewarsa, shi a matsayinsa na jigo a jam’iyyar APC mai mulkin qasar nan ba a yi shawara da shi ba lokacin zartar da kuxin aikin Hajji da ya gabata, haka kuma bai san wani xan APC da a ka yi shawara da shi ba. Don haka akwai buqatar

a sanya tallafi na taimakawa masu abada domin su ma su na ba da gudunmawa ta kowanne fanni, musamman wajen xorewar zaman lafiyar Nijeriya. Ya ce, “ba wani abu ne ya ke ganin shugaban qasa Muhammadu Buhari ba ya son taimakawa addini ba sai dai saboda tsorata shi da a ka yi tun farko na cewa shi mai tsattsaran ra’ayin addini ne, wanda Ina ganin shi ne ya sa ya ke jin tsoran taimakawa addini, wanda kuma hakan kuskure ne mutum ya qi taimakawa addininsa da duk wani abu da

zai amfani qasa.” Shi ma wani malami mai suna Malam Abbas Abdullahi ya ce, su a mastayinsu mabiya xariqar Tijjaniyya duk abinda a ka ga su na yi da hujja su ke yin sa. Don haka kullum qoqarinsu su ga ’ya’yansu sun yi karatu da tarbiyyar addini. Fitattun mutane da dama ne su ka samu halartar wannan taro, ciki har da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Ramalan Yaro Dallatun Zazzau, wanda ya shaidawa manema labarai cewa ya rufe magana a kan gwamnati, amma bai yi

Wasu daga cikin iyayen xalibai 110 da a ka sace a makarantar GGSTC Dapchi a jihar Yobe tare da haxin gwiwa da qungiyoyin fafutuka sun gudanar da zanga-zanga a farfajiyar majalisar dokoki ta qasa, inda su ka yi kira ga gwamnatin tarayya da ta qwato mu su ’ya’yansu. Masu zanga-zangar, waxanda mafi yawan su ke sanye da baqaqen kaya tare da gamayya da qungiyoyin fafutuka irin su ‘Coalition in Defence of Nigerian Democracy and Constitution’ da haxin gwiwa da ‘Our Mumu DonDo Movement’. Jerin gwanon ya qunshi biyar daga cikin iyayen xaliban guda biyar daga Dapchi zuwa babban birnin tarayya na Abuja. Uku daga cikin iyayen, waxanda su ka zanta da manema labarai, sun bayyana yadda bacci ya yi qaura daga idanunsu tare da rashin jin xanxano daga harshensu tun bayan sace yayan su da mayaqan Boko Haram su ka yi a sa’ilin da su ke dakon jin xuriyar ’ya’yansu. Xaya daga cikin iyayen, Yahaya Tarbutu, mai kimanin shekaru 45 a duniya, ya bayyana yadda lamarin ya rutsa da yayan sa guda biyu daga cikin ’yan matan da aka sacen. Ya ce a halin da a ke ciki yanzu, rayuwar sa ta tashi daga duniyar farin ciki zuwa wata duniya ta matsanancin damuwa, tun ranar 19 ga Faburairun da aka tafi da xaliban makarantar. ’Ya’yan nasa su ne Fatima Tarbutu mai shekaru 13 da Amina Tarbutu ’yar shekara 14, yayin da kuma ya yi sa’ar gano xayar, Maryam Ahmed, mai shekaru 15 a duniya, wadda kuma marainiya ce da ya ke riqo. Malam Tarbutu ya ce, “sam ba na jin daxi a rayuwata, tuni bacci ma qoqari ya ke ya qaurace wa idanu

na, sannan harshe na ya rasa jin xanxano. Tun a sa’ilin da na kira mataimakin shugaban makarantar kan lamarin sace yaran, tare da bani tabbacin cewa Boko Haram sun shiga xakin kwanan xaliban. Tun daga wannan rana rayuwata ta ke cikin tsanani”. “Wanda kuma a kashe gari, ni da sauran iyayen xalibai mun shiga makarantar tare da kutsa kai cikin daji ko Allah zai sa mu gano waxanda suka gudun. Wanda kuma a haka muka yi sa’ar gano wasu yan matan, inda muka rasa sauran. Alhalin waxanda muka gano xin suka tabbatar muna cewa an yi awon gaba da sauran”. Inji shi. Bugu da qari kuma, a wannan ranar saida xaya daga cikin iyayen, Malama Fatima Saleh, ta faxa rashin lafiya yayin da har aka garzaya da ita zuwa asibitin Asokoro dake Abuja. Malama A’isha Bukar, uwa ce ga xaya daga cikin xaliban da aka sacen inda kuma ta ce yarinyar wadda take gab da kammala sakandiren (Senior Secondary: Class 2A), tayi qarin hasken cewa ita kam tuni ta naxa gammo da rungumi qaddara. Ta bayyana cewa, “sun sace ‘ya ta wadda take ajin babbar sakandire na SS2A. Kuma tun daga wancan lokacin muka yi rabon makaho da kuturu da bacci. Qarawa da qarau, babu wani jami’in tsaron da ya tava tattauna lamarin damu. Muna buqatar gwamnati ta qwato muna yayan mu. Ni matar aure ce, bana aikin gwamnati, na damu matuqa da rashin ya ta”. Ta ce. “Ba mu da wata masaniya dangane da yuwuwar zuwan mayaqan Boko Haram a makarantar, kawai sun zo muna ne cikin rashin sani. Sun zo tare da harbin kan mai uwa da wabi, kuma basu bar Dapchi ba sai wajen qarfe 8:30 na dare,” in ji ta.


6 TALLA

A Yau Lahadi 11 Ga Maris, 2018 (22 Ga Jumadal Thani, 1439)


A Yau Lahadi 11 Ga Maris, 2018 (22 Ga Jumadal Thani, 1439)

Burinmu Shi Ne Mu Sauqaqa Muku

Ba a chaj in kuxin on ka cire d i j a h c a a B saqonnin watin waya kuxi daga ak na wasu banku

Da zaran an buxe asusu da mu, za a morewa rashin chaji idan mutum ya cire kuxi a akwatin wasu bankuna, haka kuma ba za a riqa cire kuxin saqonnin waya ba.

Domin cimma nasara a hada-hadar banki, ka yi mu’amala da bankin Sun Trust a Yau Ziyarci: www.suntrustng.com

TALLA 7


8 LABARAI

A Yau

Alhamis 10 Ga Disamba, 2017 (22 Ga Jumadal Thani, 1439)

Za A Aurar Da Zawarawa 100 A Qaramar Hukumar Argungu Daga M.J. Yusuf, Birnin Kebbi

Yanzu haka dai shirin aurar da zawarawa guda dari (100) a karamar hukumar mulkin ta Argungu ya iso gaba ta karshe India ta kai ga yanzu an kai ga matakin gwajin lafiya angwayen tare da amaren su. Alhaji Aminu Musa Magajin gari wanda shi ne ke wakiltar mai martaba Saukin Kabin Argungu Alhaji Samaila Muhammad Mera a harabar hedikwatar karamar hukumar mulki ta Argungu, ya bayyana gamsuwar sa bisa ga yadda marasa hali daga cikin matasa da kuma wadansu masu dan yawan shekaru suka masa wannan kira kuma suka amince da ka’idojin da duk aka shata. Ya cigaba da cewa wannan shirin fa an aiwatar d shi ne bisa ga zummar rage bata-gari musamman abin da ya shafi zinace- zinace a cikin alu’umma da tallafawa ga marasa karfi, kuma yana iya zamewa wata sila ta saukaka aure, Hasali ma yana iya zama ishara ga iyayen da ke tsawwalawa wajen aurar da yayan su, ya Allah budare ne ko zawarawa. Malam Abdullahi Haruna Tambasi

(Mai gwauraye) wanda shi ne saukin gwaurayen Kabi ya bayyana wa wakilin mu da cewa wannan abin alfahari ne da jin dadi a ce wani alheri ya sauka a cikin al’ummar da ka ke jagoranci. Wannan shirin ya dade da kafawa tun gwamnatocin da suka gabata amma sai dai romon baka abin ya zamo Kaulinbi-la-amalin sai da wannan gwamnati ta Atiku Bagudu ta zo ta aiwatar da shi. Ya cigaba da cewa yanzu haka akwai zawarawa sama da dubu biyu da suka jiran irin wannan damar saboda haka insha-Allahu da zarar aka kammala wannan a matsayin gwaji za a cigaba da wani. Ya kuma na kunnen zawarwan da su kasance masu biyayya ga mazajen su sannan kuma su yi tanadin kudin da aka ba su a matsayin jari su nemi sana’o’i kada su saka kudin a gaba su kashe. Daga qarshen ya yi farar Allah ya saka wa duk wanda ya taka wata rawa wajen ganin an sami nasarar wannan shirin. Honorabul AbdulSalam Sani, mai magana da yawun shugaban karamar hukumar mulkin ta Argungu Alhaji Musa Muhammad Tungulawa ya bayyana cewa samun nasarar wannan shirin ya samo

asali ne ta hangar hadin gwiwar karamar hukuma da masarauta da kwamitin hisba da kuma sarkin gwauraye. Ya cigaba da cewa wannan shirin ba shakka ya sani nasara duk da ya ke ba za a rasa yana matsaloli ba musamman wajen wadansu mazaje da adadin su bai kai uku bisa dari ba a lokacin da suka ji an ce sai an yi gwaji sai kuma wadanda suka zo don su karbi kudin wadanda a zaton su kudin ne za a ba su sai suka fita wanda bai hana samun nasarar shirin ba. Malama Sadiya Isah daya daga cikin zawarawan da suka kammala gwajin tantance lafiya zawarawan kuma wacce ta yi watanni takwas kacal yana zawarci ta bayyana jin dadin ta kuma ta yaba wa hukuma bisa kirkiro wannan shiri da ta yi na shirya auren kuma bayan shirya auren ga wani tallafi na jari don su tsaya da kafafuwan su. Ta yi kira ga zawarawan da ke jan kafa wajen kawo mazajen aure da kuma wadanda ke jin kunyar shiga wannan shirin da su sake tunani saboda a rayuwar ya mace ba abin da fi a wajen ta da ya kai yana gidan aure komai matsayin gidan su.

Malam Garba Usman, daga daga cikin wadanda za su angwancewa ranar 17/3/2018 ya bayyana farin cikin sa Inda ya ce shi ba ya da matsala wajen saka mata amma sai dai tsadar auren ce ta fi damun sa. Ya ce wannan ta isa ta zamo yar manuniya ga mata da kuma iyayen da ke tsawwalawa wajen aure. Ita kuwa Malama Fatima Ibrahim wace ta share shekaru sama da da goma ta na zawarci ta bayyana wannan shirin a matsayin wata rahama ga resu, ta dai ja kunnen mazajen su da su yi hakuri da su kuma su rike amana. Shugabanci majalaisar Malamai ta karamar hukumar mulki ta Argungu Dokta Abubakar Muhammad Wali ya yaba wa gwamnati bisa ga wannan shirin da bullo da shi wanda kuma dauke wani nauyi ne da shari’a ta dora wa mahukumtana na yin duk abin da ya shafin wani bangare na rayuwa. Ya kuma yi kira ga yana kwamitin da aka dorawa alhakin tantace ma’auratan da su ki tsoron Allah kada su saka siyasar a cikin.

Mutane Biyu Sun Rasu 18 Na Asibiti Sakamakon Vullar Amai Da Gudawa A Bauchi Daga Muazu Hardawa, Bauchi

Bayan samun bullar amai da gudawa a cikin garin Bauchi, mutane biyu sun rasa rayukan su yayin da mutane 18 ke kwance a asibitoci daban-daban, lamarin da ya sa hukumomin kiwon lafiya a Jihar Bauchi xaukar matakin ko ta kwana wajen yin feshin magani a rijiyoyi da kuma samar da shiri wajen ilmantar da mutane domin ganin annobar ba ta ci gaba ba ko kuma ta kai ga yankunan karkarar Jihar Bauchi ba. Pharmacist Adamu Ibrahim Gamawa shugaban hukumar lura da lafiya a matakin farko ta jihar Bauchi, shine ya bayyana haka cikin taron manema labarai da ya qira jiya, inda ya qara da cewa a qarshen makon da ya wuce an samu vullar amai da gudawa a wasu daga cikin unguwannin Bauchi musamman a tsangayoyin almajirai da kuma wurare masu cunkoso, don haka aka fara feshin magani tare da faxakar da mutane game da tsabta da wanke hannu bayan an fito daga bayan gida saboda shine hanya mafi sauqi da ke yaxa qwayoyin cuta. Ya ce a halin yanzu suke samar da magungunan amai da gudawa da na feshi a cikin rijiya, da takalman da kayan aikin feshin don ganin an dakatar da yaxuwar wannan cuta musamman a wannan lokaci da ake fama da zafi. Alhaji Adamu Gamawa ya qara da cewa sun gayyaci qungiyar likitoci ba tare da hawaye ba ta duniya wato (doctors without border) domin duba

yiwuwar shirin kafa sansanin kar ta kwana domin a keve masu fama da wannan cuta ta kwalara waje guda aci gaba da basu magunguna da kulawa ta musamman don ganin sun samu sauqi cikin lokaci ba tare da sun baza cutar zuwa ga wasu mutane ba. Inda ya ce ya zuwa wannan lokaci ana ci gaba da jinyar mutane da suka zo da wannan cuta kuma an salami wasu, amma hankali ba zai kwanta ba

sai an ga an kawo qarshen wannan matsalar.

Alhaji Adamu Ibrahim Gamawa

Pharmacist Adamu Gamawa ya qara da cewa a wajen Bauchi har yanzu ba a samu wata sanarwa ba game da vullar wannan cuta ta amai da gudawa da a halin yanzu ta bulla a yawancin unguwannin da suke cikin ganuwar Bauchi da kuma sauran wurare da suke cikin lunguna, musmman yadda ba su da wadataccen ruwan sha mai tsabta. Don haka ya ja hankalin mazauna cikin

garin na Bauchi kan su lura da tsabtar muhallin su ta hanyar share wuraren da suke zaune da magudanun ruwa da tsabtace ruwan sha ko tafasawa kafin a sha. Bayan haka kuma ya ja hankalin jama’a da su kasance masu wanke hannu bayan fita daga magewayi don tabbatar da tsabtar hannaye daga najasa, saboda shine hanya mafi sauqi da ke baza cutar kwalara a daidai wannan lokaci.

Xan Majalisar Dattawa A Kebbi Ya Raba Injinan Noma A Mazavarsa Daga MJ Yusuf, Birnin Kebbi

Xan majalisar Dattawa mai wakiltar gundumar Kebbi ta Arewa, Sanata Dokta Yahaya A. Abdullahi, ya raba injinan noma da kaftu (kafce) wanda aka fi sani da ‘Power Tiller’ har guda 20 ga manoma a mazavarsa waxanda kimanin kuxinsu zai haura Naira milliyan takwas da ya na kai. Alhaji Usman Sani, matamaki a kan siyasa ga sanata Dr. Yahaya ya bayyana cewa maigirma sanatan ya yi haka ne saboda sanin kowa ne wannan yankin ba abin da su ke alfahari da shi Wanda ya zarce noma musamman na shinkafa. Yin haka ba shakka sai karfafa wa manoman gwiwa kuma zai kara saukakawa manoma wahala wajen gudananr a cikin gona kuma zai takaita lokaci a maimakon yin aiki cikin zagi daga zai dawo kwana daya. Ya kuma cigaba da cewa wannan gwamnati ba ta da muradin wasoson dukiyar jama’a, a maimakon haka ta ci son karfafa wa kowa gwiwa ya tashi tsaye don ya tsaya da kafafuwan sa. Ya kuma bayyana cewa wannan ba shikenan ba saboda haka wadanda wannan bai kai hannun su ba da su yi hakuri

su ma wadansu abubuwa za su biyo baya a cikin shirye-shiryen maigirma Sanata na tallata ga manoma, sanao’i’ da kuma samar da ayukkan yi a wannan yankin da ya ke wakilta. Xaya daga cikin manoman da suka ci moriyar wannan shirin Uban kasar Gulma Alhaji Muhammadu Bashar Gulma ya

yaba wa Sanatan bisa ga iron wannan tunanin, ya ce “ Wannan shi ne a ke kira cigaba”. Ya cigaba da cewa rabawa mutane kudi ba taimako ba ne sai da barna ce kawai ga al’umma, a maimakon haka yana da kyau a karfafa wa mutane gwiwa ta hanyar samar da ayukan yi da kuma tallafa musu da kuma yin ayukkan da za su

amfani jama’a. Ya kuma yi kira ga manoma musamman matasa da su yunkura don ganin sun tsaya a kafafuwan su kuma su kasance masu dogaro da kai su daina harkokin shayeshaye da zaman banza wanda ta haka ne gwamnati za ta ni saukin gudanar da irin wadannan ayyuka.

Alh. Muhammad Bashar Gulma yayin da ya ke karbar makullin power tiller daga hannun A lh. Dannarba Tela mukaddashin shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar mulkin ta Argungu Alh. Aliyu Abdullahi Hard game.


9

A Yau LAHADI 11.03.2018

Yau Da Gobe Adabi/Al’ada/Zamantakewa/Nishaxi

Binciken Tarihin Hausa: Labaran Da Bishiyoyin Kuka Ke Sanar Mana Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN 08060869978 .......................................................................

Kashi na xaya. Kasancewar akwai ilimi acikin kowanne abu, ya kamaci muyi duba ga bishiyoyin kuka don fahimtar iliman da suke sanar mana anan kasar Hausa. Domin kuwa kamar yadda masana kimiyyar duwatsu ke cewa akwai tarihi a kowanne dutse, haka ma akwai labari ga mafi yawan rukunonin bishiyoyin kuka anan kasar hausa. To amma, wanne labari bishiyoyin su ke sanar mana? 1. A na gane wanzuwar birnin Hausawa daga kukoki. Haqiqa, kasancewar tun da jimawa, babu shahararrun gine-gine masu kafuwa cikin kasa a kasar hausa, muna iya cewa babu wani ma’auni dake tabbatar mana da wanzuwar tsohuwar rayuwa a kasar hausa sama da rukunin kukoki. Ko tantama babu, duk inda aka samu kukoki sun jeru reras, ko sunyi da ira, ko wani abu mai kama da haka, to akwai labarin cewa gari ya taba wanzuwa a wannan wuri. 2. A na sanin tsufan gari gami da tumbatsar sa daga kukoki. A kan haka, mun yi duba ga tarihin wasu tsoffin garuruwa anan kasar hausa masu cike da bishiyoyin kukoki, kuma ga xan abinda muka samo:I. Sabon Birni Daga tsoffin biranen dake kasar hausa, akwai wani Sabon Birni a kasar Getso mai cike da kukoki. Masana tarihin garin, sun bayyana cewar wasu fulani ne suka kafa shi, waxanda suka taso daga arewa sama da shekaru xari biyar da suka gabata. Kasancewar garin fulani irin wannan mai cike da kukoki, yasa akwai zakuwar sanin dalilan fitowar waxannan kukoki a wannan gari. A da, hasashen mu yafi tafiya akan cewar mu’amala da iskokai ke tilastawa hausawan dauri rayuwa da kukoki a muhallansu, amma samunsu a mtsugunin da tun asali fulani suka kafa, sai yazo da wani sabon abu. A bisa jin dalilin fitowar kukokin, Mazauna garin sunce acan baya babu kukoki a wannan wuri kafin ya zama gari, amma kasancewar fulanin da suka zauna a wurin suna amfani da kwalba wajen kaxa nono (‘ya’yan kuka), to idan an zubar dasu a wuri, sai kaga wata bishiyar ta sake tsirowa.

Har ma sai da takai ga cewa a kowanne gida, akwai kuka acikinsa. Wani gidan ma har sama da xaya akan samu. Wanzuwar tsoffin kukoki da kuma yawaitarsu a wannan tsohon gari ke nuna cewar ada-can baya, garin ya cika da gidajen mutane. Sai dai, duk da cewar fulanin garin basu taba gina ganuwa ba kasancewar su matafiya ba mazauna ba, idan labarin yaki yazo sukan shige birnin getso ne wanda wani bamaguje mai suna Babbaka Toro ya kafa bisa neman mafaka. Daga al’adun mutanen garin kuwa, sharo ne yafi shahara, wanda suka ce ada can a duk shekara mutane mata da maza daga garuruwa makwabta na taruwa a kofar gari, kusa da wasu duwatsu ayi kwana biyu ana sharo, ana kixan kotso da gangi harma da kixan Balaye wadda ake mata rawar juya-juya. Daga wannan garin ne aka samu wani maharbi mai suna Ganjigo ya tashi har yaje ya gina garin walawa a kasar karaye, da kuma wani gari mai suna Kafin Allah Gaba a kasar zazzau. Don haka, mazauna garin sun tafi akan cewar babban labarin da kukokin garin ke bayarwa shine jimawar al’umma a cikin sa, domin kuwa saida mutane suka soma zama sannan kukokin garin suka fito. Har ma wani dattijo yace akwai wata kuka data fito a gidansu suna yara, sama da shekaru hamsin kenan bata girma ba har zuwa yau, don haka yace tabbas akwai shekaru xaruruwa ga waxannan tsofaffin kukoki na garinsu. II. Zangon Dan-Nafada Shi kuma wannan gari, wani mai suna Madugu ne aka ce ya sare shi shekaru xaruruwa da suka shuxe. Rukunin kukokin da suka zagaye garin kaxai ya isa ya bada shaidar cewa hausawa sun jima suna rayuwa a wannan gari. A ka ce wai yayin da Madugu yazo wucewa, sai ya yada zango a wannan wuri, don haka sai ake cewa da wurin zangon madugu. Daga baya sunan garin ya koma Zangon xan Nafada. A cewar wani mazaunin garin, Babbaka Toro daya sari garin getso, anan ya soma zama tare da Madugu da wasu jama’a kowanne cikin xan botonsa, daga bisani ya tashi yaje ya sari Getso. Da ya ke shi ma wannan gari cike yake da kukoki, mazauna garin sun tabbatar da cewa sai da mutane suka soma zama sannan kukokin suka

fito a dalilin zubar da kwallayensu da akeyi ko ina idan an shanye. Don haka, tsufan garin na iya zamowa wasu shekaru sama da shekarun kukokin wannan gari kenan.. A bisa tsoffin hausawa da fulani da muka tambaya, kusan xaukacin su sun tafi akan cewa duk kukar daka gani ba’a san sanda aka shukata ba. Dukkan su sun gamsu cewar manyan kukoki masu alamar shekaru, tasowa sukayi suka gansu. Haka nan, ana iya lura cewar a gonaki da dazuzzuka inda babu mutane dake rayuwa a wurin, ba kasafai bishiyar kuka ke fitowa ba. Amma kuma mafi yawan unguwannin hausa na tsoffin garuruwa na xauke da bishiyoyin kokoki. A wani sa’in ma,

akan samu bishiyar kuka a kowanne gida, ko kuma a bayan kowanne gida. Wataqila, hakan na nuna cewar sai da mutane suka fara zama a wannan wuri sannan kukokin suka fito. Idan kuwa hakan ta tabbata, to zamu iya sanin shekarun kukoki a qasar Hausa ta hanyar binciken zamani, sannan da watakila zamu iya sanin jimawar lokacin da hausawa suka fara zama a wannan wuri, tayadda daga bisani zamu gane gari mafi tsufa a kasar hausa. Idan kuma ta tabbata cewar yawan bishiyoyin kuka ke nuni da yawan mutanen da suka rayu a gari, da shima zai zamo mana ma’auni mafi sauki don gane tsoffin garuruwan da sukafi tumbatsa da mutane shekaru aru-aru da suka wuce.

Adabi A Yau

Mudassir Kassim: Gwarzonmu Na Mako Shafi na 18

Ranar Marubuta Hausa

Katsina Ta Xau Harami: Manyan Jami’o’in Arewa Sun Amshi Taron Ranar Marubuta Hausa Hannu Biyu Shafi na 16 Kaucin Kaba

Maigida Kan Gida (2) Shafi na 20


A Yau LAHADI 10.03.2018

10

Wa’azin Kirista

Tare Da Fasto Yohanna Y.D. Buru 0806 871 8181 yyohanna@gmail.com

La’ananne Ne Mai Dogara Ga Mutum

Wurin Karatu: Irimiya 17:5 “In ji Ubangiji: La’antace ne mutum wanda ke dogara ga mutum, wanda ke kalafa ransa ga jiki, wanda zuci yatasa tana rabuwa da ubangiji” (Irimiya 17:5) A cikin shika-shikan imani Kirista shi ne kaxaita Allah Ubangiji mahalici mai kowa da komai. Allah shi ne abin madogara kuma shi ne kaxai a kan dangana a gare shi a ko’ina a kuma kowane lokaci. Allah shi ne mai iko a kan komai, mai rai kuma kowane lokaci. Allah shine mai iko akan komai mai rai kuma shine kadai ke da, mallakan komai. A cikin ka daitan Allah shine ya zama dalilin da kowane cikaken Kirista ya dogara ga a kowan lokaci kuma a ko ina da in wani abu ya faru das hi. Imani Kirista ya koyar masa da ya dagana ga Allah a kowane lokaci domin Allah ne kaddi mafifici. Duk halin da Kirista ya sami kansa doles ne ya dangana ga Allah. Kiristan gaskiya doles ne ya dogara da kuma. In Kirista ya dogara da kuma dangana ga Allah, to tabbas zai zama mai nasara a kowane lokaci tare da yardan Allah. Annabi Irimiya ya tabbatar mana da cewa shi Allah

Ubangiji da kansa ya la’anci kowane irin mutum da dogara ga mutum. In ubangiji Allah da kansa ya bude bakinsa ya fada wa Bil Adama da cewa matuka mutumin day a dogara mutum la’anane ne. To doles ne san da cewa babban laifine ko kuwa babban zunubi ne. Duk mutmin day a dogara ga halite ba mhalaci ba ne, wannan shirka ne kuma sabani ne ga Allah . Makiyan Allah sun eke dogara ga mutum maimakon Allah mahalici. Dogara ga mutum kaskanci ne ga sunan Allah ubangiji da kadai tashi. Abinda ya bambanta Kirista da kowane irin mutum mai addini shine kadaita Allah da kuma dogara gareshi. Mutumin da ke dogara ga mutum ya zama masa doles ne ya kalafa ransa ga jiki ko kutum. Amma yaya a ce mutum domin rashin imani ko domin mutuntaka sai, ki dogara ga Allah? Yaya mutum da Allah ubangiji ya hallace cikin ikonsa wai sai wayi gari a yau mutum ya juya wa Allah baya? Allah ne kadai abin bautana domin da haka shine dallilin da kowane mutum ya dogara ga Allah ubangiji. Sai a wayi gari mutum sai ya juya wa Allah baya ya koma ga dogara ga halita ko mutum domin jahilci ko fandarewa

daga gaskiya. Annabi irimiya ya kara tabbatar mana da cewa; la’antace ne mutmin da ke kalafa ransa ga jiki. Dalilin da yasa Allah ya la’anci muhumin day a dogara ga mutum ko kalafa ga jiki shine. Alama ce na rashin imani ga Allah da maganarsa ko kalmarsa. Domin bai kadaita Allah Ubangijiba. Domin bai yarda da tashin alkyama ba ko ranar tashin matattu. Domin ya yi wa Allah ubangiji ma kadaica kishiya. Domin an kamanta Allah da halitan sa. Domin ya dauki girma yabo bauta daukaka da kowane irin abu day a wajaba ga Allah ubangiji ya bai wa halitan Allah. Wannan da wasu abubuwa rashin imani ne da kuma kaskanci ga Allah. Annabi irimiya ya kara tabbatar mana da cewa Allah Ubangiji bai tsaya nan ba sai ya cigaba da cewa; la’antace wanda zuciyatasa tana rabuwa da ubangiji. To wannan wata nau in rashin imani ga Allah ubangiji ne in zuciyar mutum tana rabuwa da ubangiji mahalicin zuciya. Yaya a ce wai zuciyar da Allah mahalici ya halata shine kuma tana rabuwa da mahalicinsa?

Duk zuciyar da ta rabu da mahalici to zuciyar rikicine (Irimiya 17:9-10). Zuciyar da ke a hanyan halaka shine ke rabuwa da Allah irin zuciyar da ke a hanyan halaka shine ke rabuwa da Allah ubangiji maiceto. Mutumin da ke gaba da ubangiji Allah, irin zuciyar ne ke rabuwa da Allah ubangiji. Zuciyar mugunta da halin shaidanci halin ne da ke rabuwa da ubangiji. Duk zuciyar da tana rabuwa da Allah ubangiji to zuciyar da ta rigaya ta kudur ta zata hallaka. Zuciyar da tana rabuwa da Allah ubangiji zuciyar da bata da rabon shiga mulkin Allah. Makiyar mulkin Allah, makiya gaskiya, makiyar ceton Allah da dukan abubuwan da ken a Allah Ubangiji sune zuciyarsu tana rabuwa da Allah ubangiji a kowane lokaci. Diomin da haka duk mutumin da ke ji, yana dogara ga mutum ko wand eke kalga ransa ga jiki ko kuwa mutumin da ke ji zuciyarsa tana rabuwa da ubangiji. To wannan alamar la’anane da ke kansa. Domin da haka kowane mutum da ke da imani ga Allah ya cigaba da imani ga Allah Ubangiji. Shalom! Shalom!! Shalom!!!


11

A Yau Lahadi 11 Ga Maris, 2018 (22Ga Jumadal Thani, 1439)

KA SAN JIKINKA

Tare da Mustapha Ibrahim Abdullahi 08037183735 musteeibr10@yahoo.com

Ka San Jikinka: Jikinka Duniyarka (2) Mu na magana a kan sarqaqiyar duniyar jikin mu, satin da ya wuce, inda mu ka tsaya a kan “genes” wato halittun da ke qunshe da asalin xabi’ar mutum. “Genes” ne tubalin ginin “chromosomes” kuma a jere suke, ta yanda idan ka kalle su ta na’ura mai kambama girman abu wato microscope, za ka ga kamar zare ko yawa mai tsayi sosai. Kowanne gene akwai bayanin dabi’ar da yake qunshe a cikinsa. Misali akwai ‘gene’ mai qunshe da bayanin kalar fatar ki, akwai mai xauke da bayanin tsawon ka ko gajartar ka, akwai mai xauke da bayanin halayyar ka ko halayyar ki, akwai mai qunshe da bayanin kalar. Idanun ka ko Idanun ki da sauransu. Ya na daga abu mai muhimmanci da za mu koya daga jikinmu Tsafta. Babban misalin da zan ba ku a nan shi ne hanyoyi iska ko kuma bututun iska da ya bi ta maqogwaro ya shiga cikin huhu. A cikin wannan bututu akwai halitu masu rangaji kuma masu kama da ‘yan yatsu. Suna da ta matuqar qanqanta kuma suna da yawa. Aikinsu shi ne fitar da datti daga hanyoyin iska. Idan ka yi ko ki ka yi aikin qura, bayan kin fyato majina daga hanci, ko ka khako majina daga maqowaro, me ku ke iya gani a cikin majinar? Qura ko? Eh hakane. To wannan halittun masu kama da tsintsiya su ne suka sharo wannan datti. Wata hanyar da duniyar cikin jikin mu ke da tsafta shine a baki. Kullum, a kowacce daqiqa, yawu na gudana a bakin mu. Mafi abin da muka fi sani shine yawu na taimaka mana wajen hana bushewar baki. Amma a gefe guda, yawu yana tsaftce bakunan mu daga qwayoyin cutuka musamman na ‘bacteria’. Wani Abu mai matuqar muhimmanci a game da jikin shi ne juriya. Jikin mu yana xaxewa wajen yaqar qananan cutuka

wanda ma bamu san da zaman su ba. Juriyar qwayoyin halittun mu ne ke sawa muyi ta yawo da qananan cutuka ba tare da mun San suna tare da mu ba. Idan jiki yayi iya qoqarin sa bai samu nasarar yaqi da su ba, sai kuga mutum ya kwanta rashi lafiya. Ammma kafin nan, qwayoyin farin jini, waxanda sune sojojin jiki, zasu yi ta yaqar wannan qwayar cuta. Shugabanci Duniyar jiki na da tsarin shugabanci kamar yadda Duniyar mu ta waje ta ke da shi. A cikin jikin mu, qwaqwalwa ita ce shugaba. Ita ke bada umarni na mafi yawan ayyukan dake gudana a jikinmu. Idan wani ya taka qaya, sai an sanar da qwaqwalwa domin ta bada umarnin matakin da ya kamata a dauka, a cikin xan qanqanin lokaci. In kaci abinci, sai an sanar da ita domin ta bawa jijiyoyin motsi da suke ciki, hanji, tumbi, izini su gudanar da Aikin narkar da abinci. Wannan shi ya kawo mu batu na gaba, wato biyayya. Kusan taare suke tafiya da kyakkyawan shugabanci. Kusan duk wata qwayar halitta ta jiki, Aikin ta ya

ta’allaqa da bin umarnin qwaqwalwa. Idan qwaqwalwa tace tsoka ta motsa, zata motsa da izinin Mahalicci, Idan tace a zauna, dole ne a zauna. A taqaice dai, a na bin umarnin ta ana kuma kaucewa hanin ta. Idan akwai abin da ya kamata ka kai matuqa wajen yiwa biyayya, to babu tamkar Mahalacci, wanda Shi ne ya bamu qwaqwalwar. Duniyar jikin mu nada qa’ida. Idan har wani abu yasa aka qetare wannan qa’ida, to abin da ba’a so, zai iya faruwa. Misali. Akwai iya yawan fitsarin da mafitsara ke iya riqewa. Idan ya wuce wannan iyakar, to ko kana so ko baka so, ko an shirya ko ba’a shirya ba, zai fito da kansa. Haka kuma idan mutum yaci abinci da yawa, fiye da abinda cikinsa zai iya dauka, ko dai yayi amai, ko kuma ya dinga numfashi da kyar, kaifin jin sa zai ragu a wannan lokaci, haka ma kaifin fahimtarsa. Sannan kuma qwayoyin halittar da suke shimfixe a cikin bututun abinci zasu gaji saboda an jibga mu su lodin da yafi qarfinsu. Abu na qarshe da na ke so na tava shi ne isar da saqo. Ko da yaushe, jikin mu cikin isar da

saqo ya ke. Kullum sai kun ji sauti kala kala, sai kun kalli abubuwa kala kala dabam dabam, wato duniyar cikin jikinmu ta na ta’ammali da duniyar mu ta sarari. Daga ciki, qwayoyin halittar dake kusa da juna su ma suna musayar saqo a tsakanin su, da kuma sauran qwayoyin halittu na sassa daban-daban. Misali; idan ka kalli kalar. Wani abu, nan take halitta mai fayyace hoto wato retina zata sarrafa abin da ka kalla a cikin ido. Daga nan kuma sai saqon ya bi ta jijiyar motsi ta ido da ake kira optic nerve, dag nan sai qwaqwalwa. Amma idan muka xauki ita kanta jijiyar saqo, akwai qwayoyin halittun da suka haxu suka yi ta. Saboda haka saqon sai yabi ta kowacce qwayar halittar jijiyar motsa ido, dagan nan har cikin kai. Mafi yawan abubuwan da na faxa, za mu iya xaukar darasi daga garesu, mu kwaikwaya domin mu inganta rayuwar duniyar mu ta waje, saboda ta cikin, tana da tsari mai ban sha’awa; wasu kuma sai dai kawai ku karanta dan ku qara ilimi da ganin girman Mahalicci. Mu haxu wani satin idan Mai duka Ya kai mu.


12 TALLA

A Yau Lahadi 11 Ga Maris, 2018 (22 Ga Jumadal Thani, 1439)


A Yau Lahadi 11 Ga Maris, 2018 (22 Ga Jumadal Thani, 1439)

TALLA

Gaba dai! Gaba dai “Super Eagles”

Bankin Zenith na taya ‘yan qwallon Nijeriya “Super Eagles”, murna sakamakon nasarar da suka samu ta kai wa gasar Cin Kofin Duniya wanda za a gudanar a qasar Rasha.

13


14 KANNYWOOD

A Yau Lahadi 11 Ga Maris, 2018 (22 Ga Jimadal Thani, 1439)

Ba Na Fitowa A Fim Amma Har Yanzu Ina Shiryawa –Sapna Aliyu A baya ba a cika samun jaruman fim musmaman ma mata su na yin wasu harkoki na kasuwanci ko na sana’a ba, sai dai kawai mace ta ce ita ’yar fim ce. To, amma a yanzu yanayi ya canja, ta yadda za ka ga da damansu a yanzu kowacce ta na yin harkokin kasuwancinta. SAPNA ALIYU MARU ta na xaya daga cikin jaruman fim mata da a yanzu su ke sahun manyan ’yan kasuwa, da ta ke shige da fice a cikin qasashe domin saye da sayarwa. Baya da kantin da ta buxe a Xantsoho Plaza da ke titin Abdullahi Bayero a Kano. WAKILIN LEADERSHIP A YAU LAHADI ya tattauna da jarumar a game da yadda take gudana da kaswancinta a matsayinta na jarumar finafinan Hausa. Shin ta daina aktin ne ko kuma tudu biyu take ci? Don haka sai ku biyu mu ku ji yadda hirar ta kasnace. Sapna, sunanki ba voyayye ba ne a masana’antar finafinai ta Kannywood, amma dai za a iya cewa sama da shekara xaya kenan an rabu da ganin ki. Wannan ya sa a ke ganin kamar kin bar harkar fim ne. Eh, haka ne, amma dai ni abin da zan faxa Sapna dai ba ta daina yin fim ba, don fim sana’ata ce, babu yadda za a yi na daina, sai dai idan na yi aure kuma ko da na yi aure zan ci gaba da yin furodusin kamar yadda na ke yi. Illa iyaka dai a yanzu akwai wasu abubuwa da na ke yi da su ka shaf harkar kasuwanci wanda a yanzu su na saka a gaba. Kuma a yanzu ma fim na daina fitowa a ciki ban daina furodusin ba, kawai dai ba na fitowa ne a ciki. Kamar wanne irin kasuwanci ki ke yi? To, kasuwanci ne yanzu ka ga a kantina ka zo ka same ina sayar da kayayyaki irin su atamfofi, leshi, takalma, agogo da ‘yan kunnaye da jakankuna. To kuma wannan harkar ta sa ina da qarancin lokcin da zan rinqa zuwa lokeshin, saboda shi fim yana buqatar cikakken lokaci/ to ni kuma a yanzu ba ni da shi. Don haka idan na karbi aikin mutane ban san yadda zan yi a shi ba. Saboda kula da kanti da kuma zuwa na kawo kaya. Amma dai nan gaba kaxan idan na gama saita harkokina masoyana za su ci gaba da ganina a fim. A yanzu kin kai tsawon wanne lokaci ba ki fito a fim ba? To, ina ganin dai a yanzu na fi shekara don tun fim xina mai suna Watarana, da muka yi fim xn da Adamu a Kaduna, ina ganin tun daga hsi ban qara fitowa ba. A matsayinki na jaruma, furoodusa, ko ya ya kike kallon harkar fim a wannan lokacin? To, gaskiya ana smaun ci gaba sosai don na ga ana fita aikin

fim a kodaysuhe don haka ci gaba ake smau da koia baya aka samu ba za a samu haka ba, don haka an samu ci gaba ta kasuwa da kuma kayan aiki, ni dai a yadda nake gani kenan. Me ya sa a yanzu ba a samun jarumai masu awa ake yayin dai kamar da sai ki ga mata da yawa ana yayinsu a yanzu sai dai xaya ko biyu? To, abin da ya ya sa yanzu idan ka duba a ba cika tsayawa ba fim kaxai kusan kowacce jarua tana da harkokinta na kasuwanci da take yi don haka yanzu an diana tayawa ana jiran a yi fim sai ake haxawa da kasuwanci. To irin wannan sai ka ga wata ma idan ana neman ta ta fito a fim sai ka ga ba ta a lokaci kamar a baya don haka za ka ga duk an ragu wasu kuma sun yi aure ba a samu waxanda suka maye gurbin su ba Amma ba kya ganin a matsayinki na ‘yar kasuwa nan gaba idan kika awo za ki yi fim sai a ga kuxin da za a ba ki sai furodusa ya shirya don kada ki raina? Ai ba haka ba ne shi xan fim duk wata alfarma da ya samu a duniya ta hanyar fim ce, don haka duk ina ya je ya dawo fim ne gatansa, don haka ko nawa za a bai wa mutum ba zai raina ba. Don tun kadin ya zama wani abu ya san haka ake biyan a don haka ba wani abu ne daban ba.

• Sapna Aliyu Maru

yanzu da ‘yan fim? Mu’amala ta tana nan kamar dai muna tare da su kamar tare uke yi kuma na faxa maka ina furodusin don haka koyaushe muna tare sai dai idan na afi wajen kasuwancina. Daga qarsge wace shawara kike da ita musamman ga mata ‘yan fim? To, shawarata a garesu ita ce, lokaci ya yi da za su gane harkar fim kaxai ba za ta riqe su ba. Domin kuwa suna cikin fim xin za su yi aure. Kuma idan sun yi aure ba za su ci gaba da fim ba, don haka su raba qafa su rinqa haxawa da kasuwanci ta yadda ko da sun yi aure za su ci gaba da yin kasuwancinsu. To, madalla mun gode. Ni ma na gode.

To, ya ya kike iya gudanar da kasuwancinki a matsayinki na jaruma da kowa ya san fuskarki? Ina jin daxi sosai don ka ga su ‘yan fim suna da alfarma. Sau da yawa idan na je waje ko da ana hana mutane shiga sai ka ga an bar ni na shiga. Aga an ga ni ‘yar fim ce. Do haka ina jin daxin sosai kuma wasu ma saboda sun san kai xan fim ne suna zuwa sayan kaya wajena. Dn su zo su gan ni kuma duk fim ne ya ja min wannan ce alfarma. To ya ya mu;malar ki take a

• Sapna Aliyu Maru

• Sapna Aliyu


15

A Yau Lahadi 11 Ga Maris, 2018 (22 Ga Jumadal Thani, 1439)

SHARHIN FINAFINAI

Tare Da: Saddiqa Habib Abba 09097438402 habibsaddiqa@gmail.com

Sharhin Fim Xin ‘Sabuwar Rayuwa’ Daga Saddiqa Habib Abba

Suna: Sabuwar Rayuwa Tsara labari: Malam Yusha’u Furodusa: Ali Risuni Bada umarni: MJ Big Man Kamfani: Dukawa Film’s Producition Jarumai: Abdul M Sharif, Asma’u Muh’d, Umar Y Malunfashi, Isa Bello Ja, Bashir Nayaya, Baballe Hayatu, Teema Makamashi, Saratu Gidado, Ahmad Tagge, da Muh’d Baba Hasin. Sharhi: Saddiqa Habib Abba A farkon fim xin an nuna su Alh.Wada (Bashir Na Yaya) tare da Alh. Musa Mai Qaro( Umar Malunfashi) da sauran muqarrabansu suna cikin wani kamfani wanda su costomet’s ne suna kawo wa kamfanin chemical suna saye saboda shi kamfanin suna sarrafa atamfofi da shaddodi ne. a lokacin wani mutumi ya fito ya fara karanto musu wata takarda tana qunshe da bayanin chemical xin da Alh. Musa ya kawo musu shi kamfaninsu yake so kuma shi zai saya domin sun fi ganin kyansa da aukinsa saboda ya fi na Alh.Wada kyau saboda haka shi Alh.Wada sai dai ya yi haquri don baza su sayi na sa ba, a gurin Alh. Wada ya miqe yana faxa yana nuna vacin ransa a fili da kuma nuna adawa ga Alh.Musa Mai Qaro har Alh. Wada ya yi qiqirarin sai ya ga bayan Alh. Musa suka watse suka bar wajen ran Alh. musa ya vaci sosai sakamakon abinda ya faru. Bayan Alh. Musa ya koma gida sai ya fara tunani yana ji ajikinsa wani abin zai faru sai ya xauki wata laya ya sakawa xansa guda xaya da ya mallaka qarami mai suna Mubarak a wuyansa sai matarsa ta tambayeshi menene hikimar hakan ya faxamata cewar wannan layar duk sirrikansa daya mallaka ne aciki yasan zai yi wa Mubarak amfani a gaba. bayan an yi haka a daren ranar sai Alh. Wada yazo da ‘yan iska suka kashe Alh. Musa tare da matarsa xansu Mubarak ya sha da kyar domin shi ficewa ya yi daga gidan yana ta tafiya har isa wani Qauyen Fulani Baffa ya tsinceshi (Isa Bello Ja) duk a galabaice ya kai shi gidansa gurin matarsa sakamakon basu tava haihuwa ba suka riqeshi tsakani da Allah har ya girma a gabansu, har ta kai wataran

shima Mubarak yana cikin gona yana kiwo ya jiyo sautin qarar mota an yi hatsari ya fita da gudu ya ceto ran wadda ta yi hatsarin mai suna Karima ya kawo ta rigarsu yana kulawa da ita har ta sami sauqi har ya fara bata tarihin rayuwarsa cewar shima tsintacceni garin ba garinsu ba ne. Karima ta kwaxaitu akan ya bita birni domin nemo danginsa, mariqin Mubarak Baffa ya amince Karima da Mubarak suka taho birni suka sauka a gidansu Karimar gaba ki xayansu a lokacin suka tarar mahaifin Karima yana jinyar shanyewar varin jiki ko magana ba ya yi, Mubarak yana ganinsa sai ya ga ashe Alh.Wada ne domin lokacin da ya cakawa mahaifinsa wuqa bazai tava mantawa ba tun daga lokacin Mubarak ya fara qulla qullar yanda zai ga bayan Alh.Wada ya voye sirrin acikin zuciyarsa ba tare da ya bayyanawa kowa ba har sai lokacin da ya farka layar wuyansa ya ga ashe flash ne na computer Karima ta xaukeshi suka je kafe domin suga me flash xin yake xauke da shi suna zuwa suka sami Kabiru (Baballe Hayatu) suka yi gam da katar ashe ma shine sakataran Alh.Musa kafin ya rasu kuma babban amintaccensa ne hasali ma duk abinda yake cikin flash shine ya saka shi domin flash xin yana xauke da duk takardun dukiyarda Alh. Musa ya mallaka Mubarak ya ji daxi sosai daga baya suka sake haxuwa suka fara qulla ta yanda za’ayi su fito da dukiyar da Alh.Wada ya mamaye ta mahaifin Mubarak suka haxa baki da wani lauya(Alasan kwalli) ya je gurin iyalin Alh.Wada ya shaida musu cewar duk dukiyarda Alh.Wada ya mallaka ba shin banki ne saboda haka za’a biya su Alh.Wada yana ji yana gani amma ba shida ikon magana sakamakon lalurar da ya ke ciki haka suka kwashe kaf dukiyarda ya mallaka hatta gidan da suke ciki duk aka tattara aka miqawa Mubarak hakkinsa Mubarak ya haxa da dukiyarda mahaifinsa ya bar masa ya zama babban attajiri har ya sayi gidan da su Alh. Wada suke ciki saboda ya qara quntatawa Alh.Wada kuma ya auri ‘yarsa Karima suka zauna tare acikin gidan a qarshe har baqin ciki ya hallaka Alh.Wada shi kuwa Mubarak da Karima suka buxe sabuwar rayuwa domin dama itama Karima tare da mahaifiyarta (Saratu

Gidado) haushin abinda Alh. Wada yake yi suke ji saboda suma ba daxinsa suke ji ba. A qarshe Karima da Mubarak suka koma qauyen xan tsinke domin su saka halaccin da Baffa da matarsa suka yi musu sannan su ba su labarin duk abubuwan da suka faru sannan su xaukesu su kawo su birni suma suji daxin rayuwarsu su dandali arziqi. Abubuwan Birgewa: 1- fim xin ya sami kayan aiki masu kyau musamman camera ta xaukar hoto. 2- Jaruman sun yi qoqari gurin isar da saqon sannan kowannensu ya dace a gurbin da aka saka shi. 3- Labarin fim xin ya tafi ya dire bai karye ba. Kurakurai: 1-Mubarak qaramin yaro ne mai kallo ya ga gidansu acikin birni yake kuma sai aka ga an tsince shi a wannan qauyen shin da qafa yazo ko kuma wani ne ya kawo shi? sannan menene silar ciwukan jikinsa duk ba’a bayyanawa mai kallo wannan ba. 2- An sami matsalar xaukewar sauti a wasu hotuna na fim xin. 3- Tun Mubarak yana yaro Kabiru yake a yanda ya ke kuma har ya girma tsahon shekaru ko xan yaya Kabiru bai canja ba shin shi Kabiru ba ya tsufa ne? 4- Acikin babban gari irin Kano yanda aka nuna a labarin ace har an kashe babban

mutum irin Alh.Musa Mai Qaro amma babu wani bincike da hukuma ta yi a haka abun ya tafi. 5- shin shi Alh.Musa ba shida kowa ne? sannan itama Matarsa bata da kowa ne har ayi musu irin wannan kisan ace babu wanda yazo sannan babu wanda ya nemi Mubarak ko bayan ya dawo shi kaxai yake rayuwarsa? 6-Gurin da aka nuno Mubarak da Karima suna waqa kwata-kwata bai kamata a nuno wani sashe na birni ba tunda ba’a birni suke ba. 7- Bai kamata ace daga zuwan Karima ba baffa yana tare da Mubarak tsahon shekaru amma lokaci xaya ya amince Mubarak ya bita birni tunda baisan ko ita wacece ba idan so ya ke Mubarak ya bita yakamata ace ya bisu tunda riqon tsakani da Allah yake yi wa Mubarak. 8- Mai kallo ya ga Mubarak tsahon shekarunsa a qauye sutturar fulani yake sakawa tunda ba’a birni ya ke ba amma lokacin da Karima ta zo suna sallama zasu ta fi Birni sai aka ga Mubarak ya tsuke da qananan kaya itama Karima ta saka nata shin a ina suka sami wannan sutturar tunda ita Karima ma hatsari ta yi ba ta zo da komai ba. Qarqarewa: Fim xin ya yi kyau kuma ya yi ma’ana amma akwai abubuwan da ya kamata a buxasu kuma a in gantasu ta yanda mai kallo zai gamsu sosai.


16

17

A Yau Lahadi 11 Ga Maris, 2018 (22 Ga Jumadal Thani, 1439)

TARON RANAR MARUBUTA HAUSA TA DUNIYA

Katsina Ta Xau Harami: Manyan Jami’o’in Arewa Sun Amshi Taron Ranar Marubuta Hausa Hannu Biyu Daga Bilkisu Yusuf Ali, Kano

A yayin zagaya da kwamitin taron qungiyar ranar marubuta ta duniya da za a yi a Katsina ta yi qarqashin jagorancin shugaban taron Alhaji Rabi’u Na’auwa da Haijiya Sa’adatu Saminu Kankia da Malam Nasiru Wada Khalil da Hajiya Bilkisu Yusuf Ali tawagar ta isa Gusau, inda ta baqunci mataimakin gwamnan jihar. Daga nan ta wuce wajen shugaba kuma jigo a taron, Alhaji Ibrahim Muhammad Xan Madamin Birnin Magaji, wanda shi ne kwamishinan kasafi da tsare-tsare na jihar Zamfara, tare da zavavven shugaban Qaramar Hukumar Maru, inda su ka sanya wa taron albarka. Daga nan sai tawagar ta shiga kwalejin ilimi ta Gusau. Kwamitin ya iske shugaban sashen Hausa na wannan kwalejin kuma ya yi maraba da zuwan kwamitin ya karvi takardar gayyatar tare da yin alqawarin bayan ya yi jagorancin wasu malaman sashen zuwa wajen taron kuma shi ma ya na da abin faxa zai amayar ko ba yawa. Daga nan sai kwamitin ya wuce kai tsaye Jami’ar Jiha ta Gusau. Duk da shugaban sashen Hausa, Farfesa Aliyu Bunza, ba ya nan amma mutanen Ofis xin sun karrama tafiyar kuma sun karvi saqon da a ka kawo. Bayan tafiyar ’yan kwamiti Farfesa Bunza ya kira waya ya ce, wannan taro nasu ne, ya na nan tafe tare da muqalar da zai gabatar a wajen in Allah ya nuna ma na ranar. A hanyar kwamitin ta barin Gusau tawagar ta tsaya ta miqawa jigo a harkar adabi da wasan kwaikwayo, Alhaji Ahmad Hashim Shanu, tashi takardar ta gayyata shi da mutanensa. Daga nan kai tsaye Tawagar ta wuce Sokoto. Duk da dare ya yi wannan bai sa tawagar ta zauna ba sai da ta kai wa Alhaji Kabiru Assada ziyara da miqa godiyar kwamitin ranar marubuta bisa wasu nauye-nauye da ya xauka zai yi don ganin an yi taron cikin nasara. Washegari da safe tawagar ta ajiye kayanta a Jami’ar Usmanu Xanfodiyo na fa tawaga ta ga gata ga dukkan malaman sashen qarqashin shehun malami mai walwala da harshe Farfesa Salisu Ahmad Yakasai. Tashin farko Farfesa Yakasai a cikin ajin da ya ke koyarwa ya sa kwamiti ya yi wa xalibai bayanin maqasudin taro tare da ba wa xalibai damar su yi wa marubuta duk wata tambaya da ta shafe su. Ba a nan karamcin ya tsaya ba farfesan ya umarci a sanar a gidajen radiyo da talabijin wannan ziyara da kwamitin ya kawo tare da kafa kwamitin zuwa ranar marubuta ta bana a Katsina duk da a lokacin su na cikin jarrabawa, amma zai roqi hukumar makaranta a san abin da za a yin a gyara tsarin jarrabawar, don malamai da xaliban ilimi su halarci wannan gagarumin biki na raya adabi da al’adun Bahaushe. Shugaban sashen Hausa na jami’ar da malaman sashen sun cika a ofishin shugaban sashen inda su ka dinga gabatar da jawabai kamar kwamitin na xakin taron qarawa juna sani. Sun yi jawabai masu ximbin fasaha da gamsarwa kan yadda adabi ya taso da ina madosa. A ofishin Farfesa Yakasai nan ya yi wa kwamitin kyautar alfarma ta littattafai. Bayan kwamiti ya sha madarar illimi ya tashi bai tsaya ko’ina ba sai Jami’ar Jiha ta Sokoto. Duk da kwamitin bai sami shugaban sashin Hausa ba nan ma ya bar takardar gayyata. Kwamitin ya kai takardar gayyata ga kwalejin Shehu Shagari. Ranar 28 ga Fabrairu, 2018 kwamiti ya dawo Katsina. Daga nan na Kano su ka koma gida birnin Dabo.

Ranar 7 da Maris, 2018 kwamitin Ranar Marubuta Hausa ya kuma zagayawa, don kai ziyara inda kwamitin ya nufi birnin Zazzau. Tafiyar an yi ta ne qarqashin shugaban kwamitin ranar marubuta Alhaji Rabi’u Na’auwa da Hajiya Bilkisu Yusuf Ali da Malama Faima Garba Xanborno da Malam Isa Xanmusa. Da isar kwamitin Jami’ar ABU Zaria ya wuce inda ya tafi kai tsaye wajen shugaban Sashen Hausa na jami’ar ya gabatar da kansa ga wakilin shugaban da ya iske. Sashen ya karvi baquncin

tawagar, sannan ya kira shugaban qungiyar xaliban Hausa tare da bayar da umarnin ga fa bikin zuwa ga zanin xaurawa don haka a yi gangami a sanar a kafa kwamitin zuwa birnin Dikko don halartar taron ranar marubuta. Daga ABU Zaria sai tawagar ta wuce FCE Zaria. Nan ma kwamiti ya ajiye qwarya a muhallinta ya iske Dr Ahmad Bello, wanda sananne ne a duk inda a ke harkar adabi, to kuwa ya na nan. Ya yi wa kwamitin alqawarin halarta duk da ximbin aikin da ke gabansa.

Kwamitin bai numfasa ba wa wuce kamfanin xab’i na NNPC nan ma ya buxe hajarsa kuma hajar ta yi farin jini inda tun kwamitin bai baro ofishin daraktan kamfanin a ka sami fahimtar juna kan yadda marubuta ke kallon kamfanin da mafi son kai wajen xaga marubuta ya mayar da marubuta irin su Abubakar Imam da waxanda su ka biyo bayansu ’ya’yan mowa sannan marubutan wannan zamanin kuma ’ya’yan bora. Daraktan ya ce, rashin fahimta ne kuma za su zo bayan baje kolin littattafansu da za su a wajen za

su zauna da marubuta su nuna mu su su fa har yanzu su na nan su na hidimtawa marubuta in dai har sun bi tsarin da a ka shimfixa. Bayan kwamitin ya yi sallama zai tafi nan darakta ya yi ma sa ruwan arziqi na litattafai kaya guda, waxanda kwamiti ya karva ya na godiya. Ranar 8 ga Maris, 2018, kwamitin ranar marubuta ya cigaba da zagayawa, inda ya ya kai ziyara a birnin Kanon Dabo qarqashin Shugaba Rabi’u Na’auwa da Balannaji Zubairu da Bilkisu Yusuf Ali.

Kwamitin ya isa kwalejin Sa’adatu Rimi da ke Kano, inda ya kai takardar taro ga sashen Hausa na jami’ar. Daga nan kwamitin ya wuce kwalejin Shari’a da addinin Muslunci ta Aminu Kano. Sun iske shugabar sashen Hajiya Zainab Umar Sale, inda ta karve mu hannu bibbiyu da ita da wasu malaman sashen. Ta yi alqawarin tun 16 ga wata za ta zama a Katsina insha Allah ita da wasu malaman sashen duk da ranar za su fara jarrabawa, amma za ta duba wanda za

ta bar wa ya kula ma ta. Daga nan nan sai FCE da ke Kano nan ma kamar saura kwamitin ya iske shugaban sashen Hausa na kwalejin kuma ya yi na’am duk da ya ce lokaci ya kusan qurewa, to amma ba a makara ba taro da su za a yi don taron adabi kwalejin na tunqaho da shi. Taro na ta matsowa shirye-shirye na ta kankama za a gudanar da taro ranar 16-18 ga watan Maris, 2018 cikin birnin Katsina. Allah Ya nuna ma na, amin.

Kwamitin Taron Ranar Marubuta Hausa Ya Ziyarci Fagacin Katsina Daga Fadila H. Aliyu Kurfi, Katsina

•A ofishin shugaban sashen Hausa na jami’ar Usmanu Danfodio da ke •Tare da wakilin marubutan Jihar Zamfara Hon Ahmad Hashim Tsanu •Ziyarar taron ranar marubuta a jami’ar ABU Zaria Jihar Sokoto a Gusau

•Ziyarar taron ranar marubuta a jami’ar tarayya ta Gusau

• Ziyarar taron ranar marubuta a kamfanin xab’i na NNPC Zaria •Ziyarar taron ranar marubuta a ofishin Copyright Commission na Kano

A cigaba da shirye-shiryen da marubuta ke yi na Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya da a ke gabatarwa duk shekara, a cikin makon nan ne wakilan kwamitin kuxi su ka kai ziyarar bangirma tare da miqa takardar gayyata da neman taimako ga Mai girma Fagacin Katsina kuma hakimin Matazu, Alhaji Iro Maikano. ‘Yan majalisar sarkin kamar yadda su ka tarar sun haxa da Magatakardan Matazu Alhaji Muntari Nuhu, Lamixon Matazu Alh. Mannir Atiku, Malumman Matazu Abdulhamid M. Sani da ‘yan fadarsa da dama. Duk da ya ke sun tarar da mai girma Fagacin tare da baqi, hakan bai hana su marabci marubutan cikin mutuntawa ba. Ziyarar da Yazid Na Sudan ya jagoranta a madadin ‘activate chairman’ Kwamared Lukman Umar Kankiya ta yi armashi ainun. Sun bayyana maqasudin zuwan inda Mal Nasudan ya ce, “mun zo ne don gaisuwar bangirma tare da gayyatar ku wannan taro gagarumi da za ai yi a Katsina domin raya adabi.” Alhaji Yazid ya cigaba da cewa, “babban kwamitin kuxi ya aiko mu, mu kawo ma ku wannan ziyara, saboda cancantar ku, musamman yadda ya kula kuna tsaye kan cigaban al’ummarku ba dare ba rana.” Hajiya Fadila H. Aliyu Kurfi a nata jawabin ta yi godiya ga yadda fadar ta karvi baquncinsu, sannan a ka gabatar da ita a matsayin wacce ta assasa taron na ranar marubuta, sannan a ka ba ta damar bayani kan manufar taro. “Allah ya taimaki mai girma Fagaci manufar taron nan domin farfaxo da martabar rubutu a idanun duniya sannan raya al’adun Hausa da zaburar da matasa,” in ji Fadila Kurfi. Sai gwarzuwar BBC Hausa a gasar Hikayata, Hajiya A’isha Sabitu Mobil, ta yi ta’aliqi kan jawabin shugabar. A nasa jawabin Mai girma Fagaci ya nuna jin daxinsa ainun da wannan ziyara da gayyata da a ka yi ma sa, ya na mai cigaba da cewa, “da yardar Allah zan halarci wannan taro kuma zan yi qoqarin ba da gudunmuwata don nasarar taron” Malam Bello Hamisu Ida da Abdulhamid M. Sani (Malumman Matazu) su na cikin ‘yan tawagar marubutan da su ka ziyarci Maigirma Fagacin a fadarsa dake Garin Matazu nan jihar Katsina. Fatima S. Muhammad ba ta samu halarta ba bisa wasu abubuwa da su ka taso ma ta. Tuni dai marubutan su ka koma garuruwansu lami lafiya.

•Ziyarar taron ranar marubuta a sashen Hausa na FCE •Ziyarar taron ranar marubuta a sashen Hausa na Kwalejin •Tare da HOD Hausa Shehu Shagari college of Education •Ziyarar taron ranar marubuta a ofishin Farfesa Salisu Kano a tsakiya da Media Asistace Na Maigirma mataimakin koyon aikin shari’a ta Aminu Kano (Legal) Ahmad Yakasai na jami’ar Danfodio ta Sokoto gwamnan Zamfara Na biyu daga hannun hagu

•Mambobin kwamitin Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya tare da Fagacin Katsina kuma hakimin Matazu, Alhaji Iro Maikano


18

A Yau Lahadi 11 Ga Maris, 2018 (22 Ga Jumadal Thani, 1439) Tare Da Bilkisu Yusif Ali – 08054137080– bilkisuyusuf64@gmail.com

Daga Na Gaba...

Mudassir Kassim: Gwarzonmu Na Mako

• Mudassir Kassim

An ce ba ka iyawa ba ka gamawa kuma ba a yabawa in ka riqe wannan to gwiwarka ba za ta yi sanyi ba a kullum ka sa kare addininka da al’adarka a gaba a duk abin da ka sa a gaba to ba z aka taxe ba. Wannan shi ne makami da Malam Mudassir ya riqa don haka har yau tauraruwarsa ke haske in ha rana maganar Waqa. TARIHINSA An haife ni a Kano. Na fara neman ilimina daga gida kasancewar gidanmu gidan ilimi ne akwai makaranta don haka na fara karatuna na muhammadiyya a hannun mahaifina daga nan aka sa mu makarantar allo mun yi makarantar islamiyoyi da dama kama daga makarantar rana zuwa ta yamma da ta dare wanda Alhamdulillahi zuwa yanzu mun sami abin da muka samu a vangaren karatun islama.A kuma boko nan ma na yi makarantar firamare da sakandire a Kano . Na yi qaranar diploma a FCE Kano sannan na yi wata qaramar Diploma xin a jami’ar Bayaro a vangaren jarida. FARA WAQA Na fara waqa tun lokacin ina makarantar firamare lokacin da aji yake ba malami sai akan tashe ni

cikin yara sai a tashe ni na yi waqa a lokacin ina waqoqi ne irin su mai fitsarin kwance ko daqiqi marar qoqari yara za su ta kaxa tebur ni kuma ina waqa. Abin haka ya taso har lokacin da aka fara waqoqi irin na Madhu na yabon Annabi (SAW) Akwai qungiyoyi irin su Usshaqu da madinatul ahbab da akwai qungiyoyi irin na malam Rabi’u Usman Baba da sauransu mu ma mun kafa namu anan Kurnar asabe Madinatul Ahbab a nan muka fara ha rake kira na da xan’autan me waqe saboda qanqantata a lokacin. Amma sai na ajiye na koma karatu a lokacin. Waqar fim kuwa ban a mantawa shagona da nake yin askin baba a lokacin Shehu Hassan Kano daHusaini Sule Qoqi suna zuwa hira kusa da wajen wurin wani yayana abokinsu. Ni kuma a lokacin ni sha’awata na zama xan wasa ne sai na sami Shehu Hassan Kano n ace ina son na zama xan wasa sai y ace ba kana yin waqa ba sai n ace ey. Sai y ace to zai haxa ni da kamfanin fim na Sarauniya sai mukaje. Daga nan na fara waqar fim da waqar Sannu-sannu Halifa jinjina Mu kai ma ka In da rai da lafiya mulkinga kai za ka riqa Sai kuma

Ga mu cikin harka noma na shuka dan daminarga da albarka Daga nan sai muka tafi Iyantama Ali Baba ya yi mana kixa rana guda muka fara ni da Misbahu M Ahmad. Amma waqar da na fara yi ita ce waqar madahu da na yi a lokacin ban fi shekara 12-14 ba

Bayani na taho na ba ki kan soyayyata Cikin nutsuwa tsaf a waye ba na yin wauta Mutanen kirki da gaskiya suka shiryata Tunanuna ai da ni da ke ba savawa Uhum! Ka ji maigida a bar dai tonawa.

ME YA JA HANKALINKA KA ZAVI WAQA Sha’awa da ra’ayi shi ne abin a ya ja hankalina har na fara waqa. Sannan ni tuda na taso a cikin manya na taso ban a zama da sa’annina wannan kuwa yana bi na har yanzu. Wannan ta sa na ji ina son na bayar da guummawa. Burina na zama ginshiqi a al’umma wand azan bayar da gudummawa don haka ko da na fara waaqa ba da waqar soyayya na far aba da waqa ce ta noma da waqa ta masarauta. Waqa ce ta al’umma. Na fara harkar dirama da malam Abdullahi makarantar lungu a duniyar nan tamu da jami’ar albarkawa na yi ya kai shekara 10 ina yi harkar fim da ta shigo ta xauke min hankali na bar waccar xin.

An yi wannan waqar ne a fim xin Nagari. Amma ni wadda na fi so ita ce waqar Fim xin Rana: Rabbi ga zare nan a saqa k aba ni baiwa Baiwa ta saqa arziqi ga kowa Ey Rana ta haska baiwa… Abin da ya san a fi son ta shi ne na yi addu’a acikinta.

WACCE WAQA CE BAKANDAMIYARKA? Bakandamiyata a waqa ita ce

WAQARKA TA BAKA CE KO RUBUTACCIYA KO KA HAXA DUKA Wato zamani shi ya sauya abubuwa da yawa a da sai ya zama mu sai muka xauki salo biyu rubutacciyar waqa ba a damu a a samo mata kari ba in aka karanta ta kawai ya wadatar koayasarrafata da muryar da yake so amma mu sai ya zamana kafin ma mu xora abin rubutu sai mun sami kari sannan mu rubutata da kari sannan mu rera ta. Ni waqoqina yawanci duk sai na rubuta kuma nan a bi qa’ida

Ci gaba a shafi na

19


19

A Yau Lahadi 11 Ga Maris, 2018 (22 Ga Jumadal Thani, 1439)

Mudassir Kassim: Gwarzonmu Na Mako Ci gaba a shafi na

18

sannan wani lokacin kuma ina iya zuba ta a jere ba tare da qa’ida ba kamar waqar baka in ta hau rauji ta yi ma’ana shikenan tunda qafiya kwaninta ce kawai. SU WA YE IYAYEN GIDANKA? Iyayen gidana sune Malam Shehu Hassan Kano da Auwalu Muhammad Sabo har gobe ina girmama su a matsayin iyayen gidana tunda sune suka yi min silar shigowa . A vangaren kixa ina girmama Mukhatari Kwanzuma na zauna a wajensa lokacin ba ni da ofis a wajensa har na koyi kixa ya koya min abubuwa da dama ni da marigayiya Rabi Mustapha. Mun sha kwana muna waqa a lokacin hatta amshi sai ka tattaro ‘yan amshin ba kamar yanzu ba da mutum xaya zai yi ba. Wataqil ma da safen sai ya kunna y ace ba ta yi ba kuma baya aiki da rana sai da daddare da ranar commercial ne na mutane yake yi. Yanzu kome ya zama digital. WANNE TASIRI WAQOQIN FINAFINAI SU KA YI A YAU? Gaskiya waxannan waqoqi sun taka muhimmiyar rawa saboda sau tari ma waqoqin ke sayar da fina-finan a baya ma mun ta damuwa a raba fim da waqa mu mawaqa a bar mu mu yi ta waqoqinmu su ma ‘yan fim su je su yi fim xinsu amma su ‘yan fim xin suka qi saboda waqar tana cikin kyalakyalen fim duk da sukan yi fim xin ba waqar kuma ya karvu amma su sun fi so dai a yi da waqa. Mawaqa suna bayar da gudummawa ta kowanne vangare ko dai addini ko zamantakewa ko kuma tattalin arzqin qasa. YA ZA KA IYA WAQAR FIM A YANZU? Ai ita waqa yayi ce da mu ake yayi yanzu mun girma mun bar wa wasu mun tafi wani layin. Industry xin tana da faxi dole kana girma kana kaucewa inda ka san akwai yarinta a ciki kana komawa inda hankali da dattijantaka take AMMA A NA CEWA KUXI KUKA YI KU KA KU JI HARKAR Ko alama kawai na girmi na yi waqa ne ba wai na fi qarfi ba ne irin fina-finan a ake yi da za mu yi ma waqar ji za a yi ba daxi. Da za a yi fim irin namu to mu ba waqa za mu yi ba sound tract za mu yi a dinga rerawa yana bin abinda ake aiwatarwa a lokacin misali an biyo varawo yana gudu a sa waqa kan biyo varawon da sauransu. Mu haka muka fi so da za ayi to muna iya yin waqar. GWAGWARMAYAR DA KA YI Gaskiya an sha gwagwarmaya ba akan kaina ba kaxai har ma ita waqar kanta, in ki ka duba

• Mudassir Kassim

daga inda aka ratso ake inda ake a yau. Misali a da waqa dole sai ka iya sannan a yi recording haka aka taho aka sami wani mashin da in an yi za a iya ware kixa. Ana nan aka zo kwamfuta sannan yau abu ya qara girma mawaqi yana hulxa da internatiol media za a iya xaukarsa ya je ya yi performance a bas hi maqudan kuxi da sauransu. An kai matakin da mawaqan na da daraja da qima ba kamar da ba.A da sanda muka fara waqa kusan kyauta muke yi saboda duk a lokacin koya muke kuma harkar babu jari. Yan siyasa suna da mawaqansu kamar su Rarara da Ibrahim Ibrahim in kuwa ana maganar makaxin mata ga su gwanja da Adam Zango nan haka ma fina-finan. Haka in kika dawo vangaren tallacetallace a kwarzanta abu a ji ana sha’awar sayensa to ga mu muma a vangaren yabon Annabi SAW kuwa in ka ji waqoqin Hafiz sai ka ji kamar ka mutu yanzu ka haxu da Annabi. A KIRA WAQA DA SANA’A? Ey to a gargajiyance ba za a kira waqa da sana’a don suna ganin waqa roqo ce kawai ba amma a zamanance waqa sana’a ce amma a yanzu in ka yi waqa kai da kanka z aka tafi nema mata kasuwa ko ma ka ga wani a gefe zai ga in ya xauki waqar ya sarrafa kasuwancinta za a sani alheri shi da mawaqin. ME YA HAXA KA DA EFCC AN GA KUN YI TARO ? Yana daga gwagwarmayar rayuwa ita ke saw a ka buxe tunaninka kake shigo da wasu abubuwa. Wannan gwamnatin tana yaqi da cin hanci da rashawa. Babbar hanyar da za abi a yaqi cin hanci

ga yara masu tasowa sai muka ga mata da yara da matasa me suka fi so. Abin da suke so shi ne waqa mu kuma mn iya waqa. Sai mu ka ga mu ta ina za mu taimaka mu mu yi waqa su kuma hukumar su xau nauyi. Don haka aka yi wannan gangamin kowa ya shiga ya gani kyauta NASARA Alhamdulillahi nasara kam an samu na farko dai lokacin da muka fara waqa na sha kaiwa gidan radiyo a ce a’a wannan hark ace ta yarinta za ku vata mana yara ku vata mana tarbiyya ga mu da mawaqanmu irin su Xankwairo da su shata. Tun muna yi ba a jin mu ana korarmu har Allah ya kawo freedom Radio suka ce ina muke ga program sukutum guda an ba mu daga nan sai gidajen radiyo suka ce muna ina. A jamio’I an saka m a cikin hajarsu dumu-dumu suna turo mana xalibai. Ana nazarin waqoqinmu. Yanzu raywar sai da mu ‘yan siyasa sai da mu za a aurar da yara sai da m shago ka buxe sai da mu wannan ma babbar nasara ce. Kana hulxa da manyan mutane wanda a da ko a tv ka gansu sai ka rusuna amma kai ka zauna da su ka ci abini da su ka yi hira da su da sauransu. Ni ne wanda na kawo kalangu a tsarma a waqa na kira tambai n ace ya zo mu koya masa. A lokacin da da muka yi waqar nigari wani malami ya tare ni y ace Allah yi min albarka y ace satinsu biyu bas a Magana da matarsa amma matarsa na jin waqar nan sai suka shirya y ace abinda ya farru a waqar matsala ce tsakaninsu bai ma san ya yi mata laifin ba amma an agama waqar ta

ce laifin da ka yi min kaza da kaza shikenan suka shirya. A dalilin waqa na je wurare da dama a dalilin waqa na je Ghana Niger chadi Yawundi da sauransu. A irin wannan ziyarce-ziyarcen mun yaxa harshen Hausar waxanda kuma ke jin Hausar amma ba ta yi laushi ba a dalilin waqa sun gyara wani ma bai iya Hausar ba amma in yana saurara yana bi sai ka xauka ya kware. Hatta kira a zauna lafiya akwai wata waqa da muka yi kuma har yanzu ana amfani da ita. Ni na fara sakin album din audio na sayar nawa na kaina a cikin mawaqa amma da sai dai a ce the best of sai a faxi fim kaza. Amma ni na fara karya wannan sai na ce idan na yi wa mai fim waqa sai na ce ni ma ina son zan yi amfani da ita in an kwana biyu. Ni na fara kaxa life band a wannan masana’antar me kaxa jita da kalangun duk ga su a zaune na fi shekara goma ina gwada wannan waqoqina yaanci live nake yi ban a son miming duk da yake maming yana da tashi ranar. QALUBALE Babban qalubalen shi ne yadda al’mma suke kallonmu a wancan lokacin ana ganin mun kawo wani sabon abu maimakon wanda aka sani tun iyaye da kakanni irinsu Xandawo da Xankwairo da Shata da sauransu. A ka dinga qin mu har aka bari wasu ma suka hauro suka fara gurvata abin sannan aka yarda da mu. WANNE KIRA ZA KA YI GA MAWAQA Kira na shi ne mutum yak are addininsa da al’adarsa saboda duk abinda kake yi ka san da akwai ranar da za a tambaye ka.


20

A Yau Lahadi 11 Ga Maris, 2018 (22 Ga Jumadal Thani, 1439)

Tare Da Bilkisu Yusif Ali 08054137080 bilkisuyusuf64@gmail.com

Kaucin Kaba Sha Nema Maigida Kan Gida (2)

Daga Hamza Dawaki, 08034753238 Da za ka saurari mata da kyau yayin da kuke magana, za ka ji, cikin abubuwan da suke yawan faxa, akwai “Kai ba ka fahimta.” Wasu lokutan sai ka yi watsi da maganar, kamar ba ka ji ba, amma wani lokacin kuma sai ka ji ta dame ka matuqa. Abin da ita kuma ba ta sani ba shi ne, a wurinka, ita ce ba ta fahimtar! Domin lallai da dai kana fahimtar ta to babu abin da zai hana ta fahimce ka, ita ma. Kenan kowa ne ba ya fahimtar kowa. Idan kuwa haka ne, ashe akwai aiki ja a gaban kowanne kenan. Wani muhimmin abu da ya kamata mu riqa tunawa kuma shi ne, ba maganganun juna kawai muke kasa fahimta ba. Abu mafi wahala ma dai, shi ne kasa fahimtar xabi’u da motsin junanmu. Yi nazarin wannan xabi,a ta maza. Maza Kamar Dodon Koxi Su Ke Ina fatan an san menene Dodon Koxi, wato wani xan qwaro mai tafiya a cikin qwansonsa da a turance ake kiransa “snail”. Wani abu mai matuqar wahalarwa a cikin zamantakewa shi ne mata ba su san cewa maza suna da wata al’ada irin ta Dodon Koxi ba. Wato kamar yadda haka kawai idan wannan qwaro ya ga dama sai ya fito da jikinsa daga cikin wannan qwanso ya ci gaba da harkokinsa har ka yi zaton ba zai koma ba, Amma in kuma ya ga dama haka kawai sai ya janye jiki ya koma cikin qwanson ,har sai ka yi zaton babu abu mai rai a ciki. Kuma duk yadda za ka yi don ka sa shi ya fito ba zai fito ba, haka ma maza suke a tsarin

dabi’arsu a zamantakewa. Wato dai a tsarin namiji, shi zumuxin nuna soyayyarsa yana zuwa yana kuma xaukewa ne, kamar ruwan sama. Ba zai za ki tava samunsa kullum cikin nuna soyayya da son zama kusa da ke a yi labari a yi dariya ba.Wannan xabi’a kuma galiza ce da aka gina maza a kanta. Wadda su ma ba cewa suke yi bari in janye jiki ba, kawai ji suke yi za su janye din kuma sai sun janye. Shi ya sa haka kawai mace wataran sai ta ga mijinta ya fara wani baya-baya, wataqila da suna daxewa suna hira, yanzu ya dena magana sosai. Da yana tsayawa su kalli wani film ko program tare ku wani abu makamancin wannan, lokaci guda kawai sai ta ga ya dena! A irin wannan lokaci kai tsaye sai tunaninta ya koma “Me na yi mar?” “Ko dai wasu ne suka yi min wata gulmar.” “Ko dai ya dena so na ne? Ko dai ko dai.. . “ Don haka sau da yawa sai ta nemi ta tunkare shi da irin tambayoyin can. Kai tsaye shi kuma zai ce mata babu komai. Domin duk da cewa shi kansa ya san cewa da gaske ne ya sauya, amma kai tsaye ba zai iya fadar wani abu da zai iya gamsar da ita ba cewa shi ne dalilin sauyawar. Wannan “Ba komai” da ki ka ji ya ce da gaske ne ba shi da wata amsa da ta fi ta, tare kuma da cewa ke a wurinki tabbas da komai xin. Tunda kin ga canji. Don haka ita ma sai ta fassara abin bisa irin tata fahintar, daga nan kuma wataqila sai abin ya zama silar wata rigimar. Me Ya Sa Maza Su Ke Janye Jiki?

A xabi’ar da aka halicci namiji da ita, an halicce shi mai son kasancewa mai dogaro da kansa. Komai lalacin namiji za ka taras wataran duk gatan da ake yi mar sai ya ce “Ya kamata ni ma fa in tsaya da kafata.” Ko da kuwa yana nufin wani lokaci zai dawo.. Da iyaye mata suna lura da kyau, za su iya fahimtar cewa yara maza su ne suka fi wata irin gardama. kawai wani lokaci an xauki yaro ana tafiya da shi, sai ya ce shi dole sai an ajiye shi, da qafarsa yake son tafiya. Kuma in an ajiye shin an jima kaxan wataqila ya gaji ya dawo ya ce a qara daukar sa.Muna ganin wannan kamar ba kamai ba ne, amma shi yaron ya san amfanin sa. Saboda sauke shin da aka yi ya tattaka da qafarsa a wannan lokacin. Ya ji a jikinsa cewa ya sami ‘yanci. Ya yi abu ba tare da dogara da kowa ba. To kamar haka ne katsam wani lokaci sai babba ya ji, ya kamata ya xan ja baya, ya kula da kansa a fage irin na zamantakewa. Ya kula da kansa a nan ba ya nufin ya dena yarda da duk wata hidima da ake yi mar. Amma lallai ko ana yi mar wasu ba za su burge shi lokacin ba. Kuma ya fi so kawai ya gan shi a dunuyarsa shi kaxai. Wannan kuma yana faruwa a cikin soyayya tsakanin saurayi da budurwa ma, ba sai masu aure ba. Akwai lokacin da haka kawai zai ji shi yana buqatar ya samu sarari, ya huta kawai. Ya zauna da qafarsa. Ya ji shi a matsayin mai cikakken ‘yanci. Kuma hakan ba ya nuna ya dena son ta, kawai haka ya ji ya kamata ya yi kuma yin ne samun sauqin sa , domin shi zai ba shi ainishin feeling na cewa shi namiji ne. Me Ya Kamata Mata Su Sani

Game Da Janye Jiki Da Maza Sukan Yi? Abubuwa da dama ya kamata mata su sani game da wannan: 1. Na farko shi ne, Ba rashin nuna mar soyayya ne ke sa hakan ba. A mafi yawan lokaci idan mace ta ga namiji ya yi baya-baya sai ta dauka rashin ba shi cikakkiyar kulawa ne. Kodayake sau da yawa hakan yana faruwa, amma a wannan gavar sam ba haka abin yake ba. Kai a nan ba shi kulawar ma za ta iya sa shi ya yi saurin janye jikin. Kamar dai yadda waccan yaron xaukar sa da aka yi don nuna kulawar ne ya sa shi kuma ya bijire yake ganin kawai a sauke shi, ya fi mar. Saboda haka abu na farko shi ne, idan kin ga ya janye kar ki xauka rashin qoqarinki ne. Ki fara tunanin kawai xabi’arsa ce ta son ‘yanci ta motsa. 2. Sannan yana da kyau mata su fahimta cewa yawan tambayoyi qara tunzura mutum kawai suke yi. A koda yaushe ma, a tsarin namiji, yayin da kika tambaya shi: “Wai me ya faru ne?” Ya ce miki “Ba komai” sau da yawa ba komai xin. Ko kuma koman bai shafe ki ba. Yana tunanin babu wata gudunmowa da za kin iya kawowa a kai. Idan ki ka qara tambaya ta biyu, “Wai me ya faru ne, ba zaka gaya min ba?” Ransa zai fara vaci, kuma zai maimaita “Na ce ba komai.” To fa daga kin qara tambaya ta uku, kin gama tunzura shi. To idan haka ne, ya ya kamata mace ta yi don taimakon mijinta yayin da ya shiga irin wannan hali? Mu haxu a mako na gaba, don tattauna wannan da ma wasu muhimman abubuwa da su ka shafi Maigida Kan Gida, in sha Allahu.


SHARHI

A Yau Lahadi 11 Ga Maris, 2018 (22 Ga Jumadal Thani, 1439)

21

Tsakanin Gwamna Abubakar Da Ahmed Yarima: Siyasar Cigaba Ko Akasi? Daga Muazu Hardawa, Bauchi

08062333065

Ganin yadda muhawarar siyasa ke qara tsami tsakanin gwamnan Jihar Bauchi da xan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazavar Misau da Dambam Honorabul Ahmed Yarima, a kullum matsalar sake xaukar sabon salo ta ke yi musamman ganin yadda ake yaqin cacar baki tsakanin su da magoya bayan su inda kowa ke yaqar kowa ta inda zai iya. Kasancewar Ahmed Yarima xan jarida ne da ya qware na qasa da qasa wanda da su aka yi yaqin fasa qasar rasha lokacin yana rediyon mosko ya koma gidajen rediyon amurka da BBC duk ya yi aiki ya dawo ya shiga siyasa da qafar dama ya samu zama xan majalisar wakilai lamarin da ya sa a wannan lokaci yake ganin akwai yadda ya kamata gwamna Abdullahi Abubakar ya bi don jagorancin Jihar Bauchi, amma shi gwamnan ke nuna mu su ba wanda ya isa ya nuna masa hanya ko ya masa jagora yake ganin duk abin da ya ke yi daidai ne a siyasance ko a hukumance. Wannan batu ya sa Ahmed Yarima Sarkin Malaman Misau ya himmatu wajen nemo duk inda gwamna Abdullahi Abubakar ya tafka kuskure inda shi kuma a matsayin sa na xan jaridar da duniya ta sani yake shiga kafafen watsa labarai yake bayani wajen jan hankalin gwamna da mutanensa cikin hujjoji masu gamsarwa da tambihi don gwamna ya gyara tafiyar sa ya rabu da halin ‘yan bani na’iya don a samu sauke nauyin da Allah ya xora musu na jama’a. Lamarin da su kuma ‘yan kusa da gwamna ke ganin wata dama ta samu yadda suke kai wa da komowa ba tare da nazartar me Ahmed Yarima ke faxa ko yaya za a yi a amfana da abin da ya faxa don a gyara ba, idan kuma ya yi kuskure su bayyana masa kuskurensa. Duk da cewa Ahmed Yarima na maganganunsa da hujjoji da kuma ladafi wa gwamna, amma masu kai komo suma sun mayar da wannan batu wata sabuwar hanyar neman abinci daga aljihun gwamna Barista Abdullahi Abubakar. Lamarin da ya sa a halin yanzu ake neman wuce gona da iri ta hanyar niyyar kunna wutar rigima tsakanin talakawan Jihar Bauchi a qarqashin wannan biyayya da magoya bayan gwamnan su ke yi wajen hura wutar gaba da qiyayya wacce za ta iya haifar da matsala a siyasance da zamantakewa har da niyyar haifar da rashin zaman lafiya ko asarar rai ko dukiya. Abu na baya baya shi ne wanda ya faru a garin Hardawa da ke cikin qaramar hukumar Misau in da Ahmed Yarima ke wakilci, kasancewar sun shafe kusan watanni bakwai cikin duhun rashin hasken lantarki a wasu sassa na garin saboda rashin na’urar daidai

wuta ta transformer sakamakon lalacewa da ta ta yi, lamarin ya haifar da matsala mai girma yadda mutanen wannan gari suka yi ta bin bayan gwamnatin Jihar Bauchi ta saya musu wannan na’urar amma ba su yi nasara sun samu ba. Don haka suka sake dabara suka rubutawa xan majalisar su Ahmed Yarima, don neman temako shi kuma nan take ya sayo sabuwar na’urar ya tura garin na Hardawa aka kafa wuta ta dawo suka ci gaba da sa albarka. Kwatsam alhamis da ta gabata sai kwamishinan kuxi na Jihar Bauchi Alhaji Garba Sarki Mohammed Akuyam ya zo da masu aiki wannan gari, saboda shima Hardawa ce mazavarsa kuma ya tava xan majalisar dokokin Jiha mai wakiltar Hardawan amma aka samu matsala kotu ta cire shi. Don haka ya kawo ma’aikatan yace su cire wannan transformer ba a so saboda wanda basa jituwa da gwamnati ne ya kawo, don haka gwamna zai kawo tasa a sanya. Madadin ace sun taho da transformer a mota a sauke wannan a cire a sanya waccan ta gwamna to ba haka aka yi ba, za a cire ne sannan aje neman wata daga wurin gwamna da a halin yanzu baya qasar. Ganin kar a musu salalar tsiya mutanen gari suka fito suka ce basa son wacce za a kawo a bar su da wacce suka samu, idan kuma a na nufin za a yi don cigaba ne za a kawo wacce ta fi wannan kamar yadda Garba Sarki ya bayyana to su gani a qasa kafin a cire tasu a kai inda ake so shi ne mafi sauqi. Amma sai ya ce dole sai an cire a kawo wata kuma idan basu yarda ba za a ga wanda ya fi wani iko tsakanin gwaman da xan majalisar tarayya. Hakan ya haifar da rigima inda ya tura aka kawo motar soja guda zuwa garin Hardawa don su tsaya a cire wannan na’ura sai a kawo ta gwamna. Kafin qiftawa da bismillah mutanen gari sun fi dubu sun fusata sun mamaye wurin sun ce sai ko idan duk an kashe su kafin a cire. Daga nan sojoji suka koma suka ce ba za su shiga wannan rigima ba, amma daga baya sai aka sake turo motoci uku na soja da ‘yan sanda zuwa wannan gari da nufin za su cika aiki. Mu kuma ‘yan wannan gari da ke Bauchi kowa ya fara damuwa tare da yin abin da ya ga zai iya

•Yadda jami’an tsaro ke kwantar ta tarzomar a garin hardawa ranar alhamis da ta wuce

wajen neman manyan jami’an tsaro mu ka ba su labarin abin da ke faruwa saboda gudun kada a illata mana mutane saboda son zuciya. Hakan ya temaka aka ja kunnen jami’an tsaro da cewa su daidaita wannan rigima kar ta kai ga tava kowa ko amfani da makami wanda dama buqatar mu kenan. Saboda tunda aka fara rigimar mutanen gari suke sanar da mu ta waya mu kuma muka riqa magana da manyan jami’an tsaro. Kuma Allah ya taimaka jami’an tsaron suka tara mutane su ka musu bayani da kowa ya gamsu na cewa ai wannan na’ura ci gaba ne a garin saboda mutane suna da hakki a kan xan majalisa don ya samar musu da ita alheri ne ba wani abu na vacin rai a ciki. Musamman ganin su ‘yan siyasar da suke cewa sai an cire an kawo ta gwamna dukkan su ba wanda ke da gida a wannan gari illa su zo su fice ko su wuce. Duk da yadda wuri ya yamutse matasa suka riqa nuna halin gani kashe ni amma jami’an tsaron sun yi haquri sun kuma yi aikin hankali sun daidaita komai sun ce ba wanda zai tava wannan na’urar sun zo ne don su sasanta. Kuma nan take suka shawarci Alhaji Garba Sarki Akuyam da ya fita ya bar garin saboda kada bayan sun tafi baya ta aihu ta hanyar matasa su nemi wulakanta shi ko yi masa abin da bai dace ba. Shi ma kuma haka ya yi haquri ya fita a gaggauce ya bar gari ya mance da zancen cire transformer da ya kusa haifar da wani sabon bala’i na siyasa a garin na Hardawa da ke qaramar hukumar Misau. Saboda shima Garba Sarki bayanansa na nuna za a yi ne don kawo wacce ta fi

wadda a ka sa, amma zahiri shine magana ba baxini ba. Ko me ake ciki ya kamata ‘yan siyasa su riqa kasancewa masu haquri da nuna sanin ya kamata ta yadda za a samu ci gaba a siyasance da kare rayukan jama’a. Kuma a nisanci son zuciya da nuna qiyayya saboda ita siyasa mai wucewa ne ta barka da xan uwanka. Kuma duk abin da ka tara dole a wayi gari ko ka qare ka barshi ko ya qare ya barka. Amma zunubin da ka xauka kuma yana nan babu mai kankare maka shi sai ko idan ka daidaita lamarin ka tun daga duniya shine mafita. Don haka ya kamata mutane su daraja jinin ‘yan uwansu kuma su kasance masu xorawa daga inda suka samu don a riqa samun ci gaba a harkokin siyasa a samu a gina qasa. Kuma duk a abin da xan majalisa Ahmed Yarima ke faxa a kafafen labarai yana yi ne don a gyara kuskure a samu haxin kai siyasa ta ci gaba. Don haka ya kamata gwamna Mohammed Abdullahi ya kasance mai yin abin da ya dace don haxa kan mutanen sa ya nisanci masu kai komo don haxa tsakanin sa da mutanen sa ‘yan siyasa don a samu sukunin gina qasa ta hanyar xora duk wani aikin alheri a kan wanda mutum ya zo ya taras, hakan shi ne ci gaba na zahiri. Amma idan aka ci gaba da xaukar maganar ‘yan bani na’iya to za a wayi gari ana nadama ta hanyar fasawa kowa ya rasa, saboda yanzu talakawa sun fahimci halin da ake ciki a siyasance don sanin ci gaba shi ne siyasa ba nuna soyayya ga shugaban da bai damu da gina mutanen sa ko qasar sa ba.


A Yau LAHADI 11.3.2017

22

Tare da UMAR MUHSIN CIROMA ‘Smartkid993@gmail.com Ingram: Smartkid.skd_official 08104314052

Arewa HipHop

Gadon Sana’a Na Yi A Wurin Mahaifina -Nomisgee

Shahararren mawaqin Hausa na hiphop, AMINU ABBA RINGIM wanda a ka fi sani da NOMISGEE, fitataccen mawaqi ne wanda ya yi shuhura a gabatar da shirinsa na Hiphop a gidan talabijin na Arewa24. Wakilinmu, UMAR MUHSIN CIROMA ya samu tattaunawa da shi. Ga yadda hirar tasu ta kasance:

Da farko dai masu karatun mu zasu so susan cikkaken sunanka? To, assalamu alaikum da farko dai cikkaken sunana Aminu Abba Umar Ringim, don ma haifina xan Jigawa ne a garin Ringim, maihaifiyata kuma ’yar Rano da ke jihar Kano ce. Ka ga kenan Ina Kano kuma Ina Jigawa. Ko za mu iya sanin kaxan daga cikin tarihin rayuwar ka? Toh zan ce kaxan daga cikin tarihi na dai na farko ni haifaffen Kano ne kuma girman Kano a Kano kuma na yi makarantar sakandare, daga nan na tafi jami’ar Bayero da ke Kano a nan nayi digiri a Mass Communication. Na zo na fara hidimar qasa a garin Fatakwal. Na dawo Kano, amma saboda harkoki na irin na entertainment na zo na qarasa hidimar qasar a garin Kano. Ka ga kaxan kenan da cikin tarihina. Sannan kuma Ina cikin harkoki irin na entertainment aqalla yanzu na kai shekara 17, don sanda na fara waqa Ina ga a Kano Studio xaya ne don ba zan manta ba na fara yin wasu abubuwa a Zoo Road, kuma a lokacin na kan yi waqa ne da Turanci. Kenan so ka ga yadda tafiyata ta taso kenan. Sai kuma lokacin da muka fara muna ta xan dai yawace-yawace, saboda kasan dai nomisgee mutun ne mai tafiye tafiye, saboda kasan ance tafiya mabuxin ilmi ba ma a

arewacin Najeriya ba kaxai na zauna a kudu na zauna Lagas Porthacout na zauna agaruruwa da dama, sai yasa mutane da dama suke gani kamar niba bahaushe bane, saboda suna ganin yanayin shiga na da waye wana, lallai na samu nayi yawace yawace, haka ma qasashen duniya da dama, kuma dukkansu ana zuwa dan neman na kai da qara sanin wasu abubuwa da suka shafi entertainment, wani lokutan kuma waqa ke kaini da in je in yi wasa in dawo. Sai kuma daga baya Ina gani shekara 18 da su ka wuce, da ba a arewa 24 na fara aikin tv ba, na farko dai ita kanta aikin jarida gadanta nayi saboda mahaifina dan jarida ne kuma sananne danko kaima ina ganin zaka san Abba Umar Ringim, kusan su ne mutane na farko da suka fara aiki a gidan rediyo na Kaduna kuma ya yi yawace-yawace gidajen rediyo Katsina da dai sauran garuruwa har kuma ya dawo Kano garinsa sai da aka ba Jigawa jaha sannan ya koma can, dan kaga ringim a cikin jigawa take so kaga na fara aiki ne a Dstv, dan wajen shekara takwas da suka wuce na fara H Hip Hop a dstv amma a can ana kiranshi da Africa Hip hop magic Hausa, aqalla na kai shekara xaya ina bada aikina ana kallo, sai daga baya arewa 24 tazo, suka xauke ni aiki, daga nan kuma na fara shege da fece don in zaqulo mawaqan Arewa da su ke da talent in nuna su idon duniya a san su a gan su a duniya. To, me yaja hankalinka ka tsinduma harkan waqa? Shi komai da ka gani baiwa ne dan tin ina qarami yaro nake da wannan abun kuma yayyena

dikansu na koyi wasu abubuwa daga wajensu, sanan akwai waxansu mutane dana zauna dasu sunyi nisa a harkan rediyo a Kano, na farko akwai su Muhammad Tahir MC wanda ya riqe dala fm sannan kuma akwai irinsu Muhammad Jolie, irin su Ahmed don tin ina qarami na koyi abubuwa da dama a wajensu so kaga akwai ra’ayi kenan. Kawo yanzu ka na da waqoqi kamar nawa? Gaskiya yanzu ban san yawan waqoqin da na ke da suba domin su na da yawa don akwai na Turanci zalla amma yanzu na Hausa sun fi yawa wato na Hausa hip hop, tunda mu na jan hankalin mutane su dawo shi ne, kwanan nan ma Ina da sabon aiki, amma sanannun cikin su da su ka yi fice su ka karvi ‘award’ akwai kamar su duniya ina zamu je tasamu lambar yabo da dama har da qasashen waje akwai su feeling, da su geto, akwai kuma an cukule, an cukule ta nuna cewa Nijeriya gaskiya fuskar kuwa a cukule take ba’a jindaxi, sannan akwai young Alhaji wanda bidiyon ta zai fito kwanan nan da kuma subani 2 fingers da dai sauransu. Kuma ka ce a shekarun baya ka kan yi waqa ne da Turanci kawai, ko za mu iya sanin mai ya ja hankalinka ka koma Hausa hiphop? Haka ne a shekarun baya na kanyi waqa ne kawai da Turanci, dalili kuwa kowa a lokacin yana qoqarin yaga yayi koyi ne da irinsu ingila amerika da dai sauransu, daga baya kuma munzo mun fahimci cewa yanzu ko ina a duniya kowa da yaranshi yakeyi, in kace Saudiya da Larabci su ke yi Faransawa da faranshi su ke yi dai sauransu, haka kuma ko lagos abun dayasa suma suka zama


A Yau

23

Lahadi 11 Ga Maris, 2017 (22 Ga Jumadal Thani, 1439)

Gadon Sana’a Na Yi A Wurin Mahaifina -Nomisgee akan waqar kenan, sannan in ka kalli bidiyo zaka ga al’majiri ne da wasu abu buwan ana nuna fa cewa a tashe hankalin duniya yake, da kuxin daza mu dinga kasha wa a banza mu taimaka ma almajiran nan, in ba haka sune suke girma su zama ‘yan ta’adda su futine Duniya. Kuma a dalilin duniya ina zamuje naje gurare da dama, na samu lambar yabo akan waqar aqalla kamar guda biyar kuma kwanan nan a dalilin wannan waqar aka mun PEACE Ambassador wanda akayi a yobe NGO da dama sun halarci wannan taron, YEF wani Entertainment kamfani da haxin gwiwar NGO da sauransu suka bani wani lambar yabon PEACE ambassador.

jag aba a Nijeriya saboda suma suna saka yare suna saka pingin, sai yasa mu muka dawo muka dage sai ansan Hausa hip hop, mu ta xaga matasa, yanzu gashi ta fashe ko ina maganar Hausa hip hop ake. Wasu irin darussa waqarka duniya ina za mu je ta ke koyarwa? Darussan da duniya in zamuje take koyarwa suna da dama musamman in ka lli halin da duniya take ciki a yanzu ana jubar jinni mara misali ana ta qashe qashe ta ko ina, wasu mugayan abubuwa suna ta vulluwa wa’inda bamu san ta ina suke ba, amm kuma in ka zauna da idon basira zaka ga wasu ne a can gefe suke haddasa fitinu burinsu kawai suka a zubar da jini, to abinda waqar take koyar shine sai mun ajiye maganar addini mun bar batun cewa kai musulmine koko kai kirista ne mun haxa kai to sannan ne zamu zauna lafiya, sanin kuma ina kara wayar da kan ‘yan arewa mu dai na ganin da kawo mana kowani kalan al’adu mu xauka, dan wasu zaka ga sun saka riga mai rubutu sunyi gayu dashi basu san me rubutu yake nufi ba, sai ka duba zaka ga baa bun daya dace ka dinga adune dashi ba, kaga sai yasa ita waqar duniya ina zamuje kaga har America a Washington Dc an zauna ana tattaunawa

Ko za ka iya gaya ma na wasu daga cikin lambobin yabon da ka samu daga lokacin da ka fara waqa zuwa yanzu? Lambar yabo da na samu su na da yawa gaskiya da kusan ko wata shekara za ka ga na samu best Hip Hop artist a arewacin Nijieriya wanda Kamfanin MTN suke shiryawa AMMA kannywood Award na kuma ci best rapper Album of the Year, haka kuma zalika na qarvi kyautar lambar yabo a nijar na amsa Best program Of Year wanda ni nake gabatarwa na biciken masu fasaha a duniya, na kuma zo na karvi Talent Hunter, Alhamdulillah na karvi kyaututtuka da dama, ko a qarshen shekaran da muka fita na qarvi best rapper of the wanda Sarauniya Beauty Pergent ta kaddamar a Kaduna. Waqarka da kayi a Ghetto Area waqace da ta samu karvuwa soasai a idon duniya, musamman a nan yankin area. ko itama zaka iya gaya mana darussan da take koyarwa? Darussan da waqar Ghetto Area take koyarwa, kasan ghetto unguwa ne da talakawa suke zaune da yare da mutane iri iri ba aiki ga dai sunan, rayuwar ta fita daban, amma fa cikin wannan unguwar ta ghetto akwai masu basira akwai masu ilmi suna buqatar gudun mawa ne kawai suma su daga su zama wani abu a duniya, so abun da ita waqar ghetto star take nuna wa kenan

a taimaki ‘yan ghetto sai yasa zaka ji ina cewa a kwai masu zaman baqinciki, a ghetto mata suke ta bamu loving a ghetto police suke ta bamu hating, sai dai in ka saurarin waqar zaka gane gaskiya gayu suna jin jiki, gashi suna da ilmi ga kwakwalwa amma basu samun taimako. Sananne ne kai a harkar waqa kuma ka na aiki a gidan talabijin na Arewa 24. Ya ka ke iya haxa aikinka da harkar waqa? Kowanne aikinsa daban lokacin da ake aikin gidan tv daban lokacin da ake waqa daban, amma kuma waqar ita ke qara haskaka gidan tvn asanshi a duniya saboda haka dik inda ka sani mutun yana da baiwar waqa kuma yana aikin gida tv riqeshi ake hannu biyu saboda yan bawa gidan tvn gudunmawa ta wannan hanyoyin inda yake saida gidan tv da sauransu da hakan lokacin kowanne daban in naje weekend ina samun hutu, ko kuma dik garin dana je aiki kamar legas da jos in inaso nayi waqana naqanje studio ko da daddare in waqana shi yasa kaga lokacina qanqani ne. Wani irin qalubale ka fuskanta daga lokacin da ka fara waqa? Toh gaskiya ni ban samu wani qalubale ba, saboda qalubale babba shine in kana yin abun da iyayenka basa so da haka kaga wannan akwai damuwa, toni ban samu ba a wannan bangaren saboda haka ina qalubalen kawai da na samuina makaranta ina waqa wannan kaga qalubale ne, sai kuma vangaren kuxi saboda ni tun farko ina aiki, don a wannan lokacin nayi aiki da AA Rano a gidan manshi na farko, don xan uwane a guna, na zauna a matsayin mataimakin manaja nike kula da fannin kuxin, to kaga tun alokacin ina da kuxi ina zuwa makaranta. Wane irin qoqari ka ke yi don ganin ka faranta ma masoyanka rai? Ta inda nake faranta ma magoya baya rai irin su facebook instagram twiiter da dai sauransu akwai fans Page xina na duba musamman da daddare in amsa masu

tambayoyin da zan iya amsawa masu bukata in biya wanda zan iya wanda ban iya ban a basu haquri,wani lokutan in kabi ta irin masoya ma sai ranka ya vaci kalan tambayan da zai ma sai ya vata ma rai, amma haka muke lallava a rabu lafiya, amma ina iya bakin qoqarina na faran ta ma masoya rai a hanyar zada zumunta. Tin kaga masoya a fain duniya sub a wai kano ba nijeriya tin inda kasani, gasu nandai indiya ne amerika jamani da dai sauransu, haka kuma a tv ina miqa godiyana ga masoyan da suke nuna mun qauna. Daga yanzu zuwa nan da shekara biyar wane hidima ka ke shirin yima Arewa Hiphop? Daga zuwa nan da shekara ashirin kana tinanin wani irin hidima zamu ba hip hop, toh zan iya cewa ko yazu ma Alhamdulillah, dan bana jin jama’a sun san da Hausa hip hop sai da nomisgee ya fara haska Hausa hip hop a idon duniya baki xaya san nan aka santa, kuma anan ne muke qoqarin a san bahaushe da Hausa ita kanta aduniya, akwai qalubale dana samu da dama Alhamdulillah saboda in kana da stardom sai ka zama wani abu ake maganarka amma in baka wani wa baza ayi maganarka ba, amma qalubalen da na samu musamman a gurin malamai sun cewa nomisgee yana canja al’umma, amma ni a tinanina basu da sani ne akan wannan abun shine yasa, kuma in ana haka a hankula zaka ga sun gane fa’idar wannan abun, amma fa daga nan zuwa nan da shekara biyar inaso in sa kana gida kana wurin sana’ar ka a matsayin mawaqi kana samun kuxi a account xinka da ta online, san kuma a ta hanyar waqa ne muke so muwayar da kan al’umma a samu zama lafiya matasa su samu aikin yi to kaga abun da muke so mu samar ma hip hop nan da shekara biyar. Zamu Cigaba A Mako Mai Zuwa..


24

A Yau

Lahadi 11 Ga Maris, 2018 (22 Ga Jumadal Thani, 1439)

Ba Don Kannywood Tawagar Gwamnati Ta Tafi Qasar Morocco Ba –Bincike

Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja

Bincike ya nuna cewa, tafiyar da ta haxa da wasu ’yan fim na Kannywood zuwa qasar Morocco a ranar Litinin 5 ga Maris, 2018 ba an yi ta ne musamman domin masu sana’ar shirin fim xin Hausa ba, illa sai don wani dalili na daban. Wani bincike da LEADERSHIP A YAU LAHADI ta gudanar ya nuna cewa, maqasudin tafiyar ba zai rasa nasaba da buqatar da kwamishinan kuxi na jihar Kano, Alhaji Aminu Muktar Xan’amu, ya ke da ita ba ta samun damar gabatar da qasida a taron DEMO Africa da za a fara gudanarwa nan gaba a ranar 27 ga Satumba, 2018 a qasar ta Morocco. Bayanan da LEADERSHIP A YAU LAHADI ta samu ya nuna cewa, masu gudanar da taron ba su cika aminta da tsoma hannun gwamnati a Nijeriya kai-tsaye ba, amma sun fi yarda da haxa alaqa da qungiyoyi ko masu sana’ar irin ta qwararru, kamar masu shirin fim, injiniyiyi da makamantansu. Wannan ziyara ta tawagar kwamishina ta sharar fage ce ga wannan taro da za a gudanar, inda an saba yin ganawar sharar fagen duk shekara musamman ’yan watanni gabanin gudanar da babban taron. Wata majiya ta qara da cewa, a wannan taron ne za a iya tabbatar wa da kwamishinan yiwuwar ko zai samu damar gabatar da qasidar ko akasin hakan. To, amma da yawan ’yan fim ba su san da wannan tsari ba, inda majiyar ta ce, hatta wasu daga cikin waxanda a ka yi tafiyar da su ba su da masaniya kan haqiqanin dalilin janyo su cikinta. Ita dai tawagar da ta tafi

Morocco ta qunshi wasu daga cikin ’yan fim na Kannywood, kamar Jarumi Nura Hussein, Mawaqi Ibrahim Ibrahim, Jaruma Hadiza Aliyu Gabon, tsohon shugaban MOPPAN Alhaji Abdulkarim Muhammad da Isma’il Na’abba Afakallah, wanda shi ne babban sakataren hukumar tace finafinai da xab’i na jihar Kano. Binciken ya cigaba da nuna cewa, ba a tuntuvi shugabannin qungiyoyin Kannywood ko sanar da su maqasudin tafiyar ba, inda a lokacin da wakilinmu ya nemi jin ta bakin qungiyoyin ’yan fim, kamar qungiyar masu shirya finafinai (wato furodusoshi) a qaqashin jagorancin Malam Abba Miko Yakasai da qungiyar daraktoci a qarqashin jagorancin Malam Aminu Saira da ma haxaxxiyar uwar qungiyar masu shirya fim xin gabaxaya, wato MOPPAN, babu wata shaida da ta nuna cewa an tuntuve su kan batun wannan tafiya. Bugu da qari, hatta shugaban kwamitin zamanantar da kasuwancin finafanan Kannywood, Alhaji Hamisu Lamixo Iyantama, ba a saka shi cikin tafiyar ba, wanda hakan ke qarqafa zargin da a ke yi na cewa, tafiyar ba ta da nasaba da bunqasa sana’ar shirin fim kai-tsaye, saboda kasancewar a kwanakin baya an damqa ragamar harkar kasuwancin fim ga wannan kwamiti na Iyantama. Binciken ya cigaba da nuna cewa, LIONS@FRICA ya fara qirqiri taron DEMO Africa tun a shekara ta 2012, domin tallata ’yan qasashen Afrika da su yi fice wajen qirqirar fasaha ga qasashen duniya, inda kawo

Tawagar ‘yan fim tare da kwamishinan kuxi na Kano

yanzu kamfanoni 180 ne su ka ci moriyar taron. Duk shekara a wajen taron a ke gabatar da kayayyakin qirqira da qasidu a wajen taron, wanda hakan ke bai wa waxanda su ka sami damar gabatar da qasidun samun vullewa zuwa ga haxuwa da masu ruwa da tsaki na qasashen duniya kan sana’o’i, wanda an ce hakan ba ta samuwa sai mai gabatar da qasidar ya danganta kansa da wasu masu sana’a ta qwararru, kamar ’yan fim da makamantansu. A nan ne Kwamishina Xan’amu a ke ganin zai ci moriyar alaqanta kansa da ’yan fim, kamar yadda wata majiya ta shaida ma na. Ita wannan tafiya ta Morocco sharar fage ce ga taron da za a gudanar cikin watan Satumba mai zuwa. Amma kowa ya na da damar neman halartar wannan taro, ba sai xan fim ba, matuqar ya cika qa’idojin da masu shirin su ka bayyana ta hanyar yanarsu ta gizo, inda a bana za a rufe cike

nema ranar 15 ga Juni, 2018. An gudanar da taron bara ne a ranakun 21 zuwa 24 ga Nuwamba, 2017 a cibiyar Birchwood Convention Center da ke birnin Johannesburg na qasar Afrika ta Kudu, inda kamfanoni 30 su ka samu shiga daga cikin kamfanoni 956 da su ke nemi shiga taron daga qasashen Afrika guda 28. A cikin kamfanoni 30 xin, kamfanoni bakwai ne su ka tsallake siratsin daga Nijeriya, takwas daga Afrika ta Kudu, shida daga Kenya, bib-biyu daga qasashen Ghana da Zimbabwe, yayin da guda xai-xai daga qasashen Kamaru, Uganda, Morocco, Tanzania da Senegal. Waxanda su ka xauki nauyin taron na bara su ne sashen bunqasa qananan sana’o’i na Afrika ta Kudu, Birnin Ekurhuleni da kamfanin Microsoft. A 2017 qwararru sun zavi kamfanoni biyar daga qasashe huxu na Afrika a taron, waxanda

su ne za a kai su taron Lions@ frica Innovation Tour a Silicon Valley ta jihar Califonia, inda a can ne za su bajekolin fasaharsu tare da saduwa da masu ruwa da tsaki kan sana’a a mataki na qasashen duniya. Waxannan kamfanoni guda biyar da su ka tsallake sun haxa da SOS Sante daga Morocco, ZOA Tech da M-Post daga Kenya, Rooster daga Afrika ta Kudu da Versecom daga Nijeriya. A karon farko za a gudanar da taron a yankin Afrika ta Arewa a birnin Casablanca na qasar Morocco. Duk qoqarin da mu ka yi na jin ta bakin kwamishinan kuxin jihar, Xan’amu, ya ci tura. Hatta babban sakataren hukumar tace finafinai, Afakallah, da ke tare da shi a Moroccon mun tuntuve shi, domin ya haxa mu da kwamishinan, don yi ma sa tambayoyi kan jin gaskiyar wancan zargi, amma Afakallah bai amsa ba.

Gwamna Bagudu Ya Bayyana Vacin Rai Kan Rashin Ba Wa ‘Yan Makaranta Abinci Kan Lokaci Daga Umar Faruk, Birnin-kebbi

Gwamnan jihar Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya bayyana vacin raansa kan rashin baiwa dalibai kwalejin ‘yan mata da ke garin Birninkebbi a jiya. Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai wata ziyarar bazata da safen jiya a kwalejin ‘yan matan, inda ya ce, “na lura da cewa yanzu karfe goma da rabi na safe sannan dalibai ke karvar abincin safe”. Saboda haka gwamnatin jihar kebbi a karkashin jagoranci na zata amince wannan ba. Sanata Bagudu ya ci gaba da cewa ya zama wajibi ga

shuwagabanin kwalijin makarantar ‘yan matan da su canza tsarin bayar da abinci ga daliban. Ya ce “ ya zama wajibi a basu abinci a cikin lokaci “. Hakazalika Gwamna Bagudu ya ce ya saurari shugabar dalibai ta makarantar ‘yan matan Malama Amina Hussaini Yakubu irin matsalolin da suke furkanta a makarantar kamar rashin layin sadarwa na xakin karatu na zamani, rashin isasun kayan kimiya ga xakunan gwajegwaje da ya shafi harakar kimiya na zamani. Har ilayau yace da kuma Karin wuraren wanka da ruwan sha da kuma sauran su. Inda ya

tabbatar wa dalibai da kuma taraiya da ta jihar Kebbi a shirye Daga karshe yaja kunnen hukumar makarantar gyara da ta ke na ganin ta Samar da ilimi dalibai da su maida hankalinsu kuma Samar da abubuwan da mai inganci ga daliban qasar ga karatu domin samun ilimi daliban ke bukata a makarantar nan. mai inganci. da su dalibai suka gabatar ga Gwamnan Bagudu. Bugu da kari Gwamna Bagudu ya yi kira ga shuwagabanin makarantar da kuma dalibai da su kara maida hankalinsu ga harakar tsaro a makarantar, domin a kwanan an samu rashin tsaro a makarantar Dapchi a jihar Yobe inda ya zama sanadiyar sace ‘yan matan makarantar su Dari da goma a Dapchi. Saboda haka su kula sosai. Kazalika yace gwamnatin Gwamna Bagudu yayin ziyara a makarantar


LABARAI

A Yau Lahadi 11 Ga Maris, 2018 (22 Ga Jumadal Thani, 1439)

WASIQAR MALAM AKU (Gyara Kayan Ka…)

Tunda safiyar Larabar yau wannan takardar ke hannuna wadda ta fito ne daga wani xan’uwa mai son a yi gyara a cikin qasar ta mu da kuma tsakaninmu al’ummar qasar ya fara da cewa, “Salamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu, na yi matuqar farin ciki da takarda ta ta iso hannunka wannan xan Tahaliki da wannan zaure na WASIQAR MALAM AKU ke hannunsa. Zan so duk mutane su yi mata duba na tsaki ko sa samu su tsinci wani abu daga cikin rubutuna. Duk sanda nake yawona tsakanin al’umma ko kuma a maqalun sadarwa na intanet nakan dinga cin karo da mutane ‘yan zafin kai da zafin zuciya waxanda a kullum zan rinqa gani suna janyo masifu ko kuma faxin ra’ayinsu dangane da wata matsala tasu musamman ma daga vangaren ‘yan siyasa, wani yakan yi zagi ko cin mutunci ko yin addu’ar rashin dacewa ga wannan abin da yake qi xin; kai a wasu lokutan ma masu maida musu martanin har ka ji suna raba su da Rahmar Allah. Qwarai abin na damuna fiye da yadda tunani ke kawo wa mai yin shi amma rashin sanin hanyar da zan isar da wannan abin da ke damuna ya sa na yi qoqarin haxuwa da mai riqe da akalar wannan fanni na Wasiqar Malam Aku don in fexe masa Biri har wutsiyarsa duk da dai abin yakan xumama min kai ya kuma xugunzuma hankalina a duk sanda na yi arba da irin wancan kalami.

Haka tunanikan wasunmu kan vaci wajen neman hanyar da zamu daqile wannan xabi’a ta janyo bala’i kawaunanmu, wasu kan ce har abadan ba za a tava sauya al’ummar qasar nan ba sai idan dukka rayukansu aka xauke kana aka sake halittar wasu al’ummar tukun za a iya samun ci gaban hakan. Shin ina mu ka baro hankulanmu ne da zamu mance da Allah shi ne ya qagemu ya kuma sanya gani a idanunmu kana ya sanya zuciya a qirazanmu shin ba zai iya warkar da mu waccan cutar da mu ka xaora ta ga kawunanmu ba ne? Ka da mu kuma mu mance muna cin abinci yayin da yunwa ta addabe mu har mu yi qoqarin neman duk hanyar da zamu ciyar da kanmu ko da kuwa da yin roqo ne, haka zalika mukan yi barci a lokacin da mu ka yi aiki tuquru da mun gaji sai mu nemi wurin da zamu huta da gajiyar da ke jikinmu. Sannan mukan nuna vacin ranmu a duk sanda wani ya yi yunqurin kawo mana raini har ga ji muna shan alwashin xaukar mataki. A tunanina idan har zamu iya nuna fushi a tsakaninmu, mai zai hana hakan mu rinqa nuna shi ga duk wanda ke mulkarmu babu bambanci hasken fata ko kuma disashewar ta ko kuma bambanci harshe yayin furta magana amma ba ya zam wani na ci mana duduniya daga baya ba, mu kuma muna neman cin zarafin makusantmu ko da ta halin qaqa ne kuwa. Ba manufata ke nan mu xauki makami don nuna qin

amincewar abin da ake yi garemu ba, muna da hanyoyin da zamu iya isar da dukkan fushinmu walau ta hanyar rubutu ko ko dai xaukar matakin daina dangwalen quri’a ga duk wanda mu ka zava da niyyar ya yi qoqarin kawo mana ci gaba amma kuma hakan bai samu ba ke nan a sanda ya yi qoqarin sake dawowa garemu da zummar son mu taimake shi da quri’unmu a nan ne zamu nuna masa kullum tunanikanmu a jikkunanmu suke ba sa tava yin qaura. Da zamu yi karatun ta nutsu mu kuma yi dawayya na abin da ke aukuwa a baya da kuma yanzun ba su zam iri guda ba, a da duk wanda bai martaba na sama da shi dole zai zamo marar kyakkyawar xabi’a an fi ganin shi ma a matsayin wanda yake yin shaye-shaye ko kuwa mai wata muguwar halayya! Amma a wannan zamanin babu wani mai yin duba irin na da mutum ne ya yi jika da da kai amma ba za ka iya shanye duk wani abu da zai gaya ma ka ba, duk abin da ya zo bakinka sai ka fito da shi fili daga zuciyarka ka faxa masa kamar yadda ake cewa bin na gaba bin Allah haka zancen yake da ace zamu yi duban tsanaki sai mu ga cewar tuntuni an bar Allah ke nan tunda dai ba a bin abin da ya zo a cikin Qur’ani da sauran Hadisai na Annabin Tsira, muddin Allah ya ware wani daga cikinmu ya ce shi ne shugaba, biyayya gareshi ta zamo mana dolenmu ko kuwa yankar naman jikinmu yake yi a kowacce rana.

25

Tare Da: Abdulyassar Aminu Abubakar, 08093924782 abdulyassaraminu782@gmail.com A wannan zamani na mu kowa ganin shi yake yi wanda ya fi qarfin doka musamman wadda aka ce an yi ta ne bisa sahalewar gwamnati walau ta Tarayya ko ta Jiha, shugaba dai ko kafuri ne biyayya aka ce mu yi masa. Jama’a, tuni fa mun rigada mun makaro lokaci ya yi gaugawar qure mana. Ga mai karanta wannan rubutaccen saqo na wa zan so da ka tsaya da duban tsanaki ka fahimci wani abu a cikinta ko da kuwa daidai da saxara guda ne ka da ya zamo sai dai kullum ka sanya kuxi ka saya amma duba rubutun da ke ciki shi ne na ka babu wani abu da kake fahimta ka da kuma qwaqwalwarka ta zamo a daqile kai ba ga neman hanyar da za a magance duk wata matsala ba, ya zamo kullum kana tunani irin wannan: Ta wacce hanya za a iya daqile harkar shaye-shaye ga xaukacin matasan da ke cikin garinka? Kana ta wacce hanya za a rage marasa aikin yi a cikin unguwarka? Wanne tunani ka yi da har zai zamo silar warakarmu daga faxawa hannun miyagun mutane a dangane da mulkin zalunci da ake yin sa garemu?. Nan nake qoqarin na sanya aya sai kuma a haxuwa ta gaba. Ba zan tava gajiyawa da godiya ga wannan xan Tahaliki na zauren WASIQAR MALAM AKU da ke iya bakin qoqarinsa wajen ganin dukka al’umma sun yi tunin hanyar nema wa kawunansu hanyar tsira a nan duniya da kuma can lahira idan mun je.”

Zaven 2019: Sardaunan Badarawa Ne Zavinmu – Al’ummar Kaduna Ta Tsakiya Daga Ibrahim Ibrahim, Kaduna

An bayyana Honarabul Usman Ibrahim, Sardaunan Badarawa, a matsayin Mutumin da yafi dacewa da kujerar Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattawa a qarqashin inuwar jam’iyyar APC a zaven shekara ta 2019, idan Allah ya kaimu. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban Qungiyar ci gaban Gundumar Al’ummar Kaduna ta tsakiya, wanda a turance ake kira da Concerned Cizitens of Kaduna Central, Alhaji Bello Adamu Wakili, a yayin da yake jawabi wajen gangamin nuna cikakken goyon bayansu ga Sardaunan Badarawa, Honarabul Usman Ibrahim, domin ya amince ya amsa kiran da ilahirin xaukacin Al’ummar kaduna ta tsakiya ke yi masa na ya yarda domin ya tsaya takarar neman kujerar Xan Majalisar Dattawa mai wakiltar kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa dake Abuja. Alhaji Bello Adamu Wakili, ya qara da bayyana cewa, basu

manta da irin Namijin qoqarin da Matashin Xan siyasar, Sardaunan Badarawa ya yi masu ba, a lokacin da yake riqe da kujerar Shugabancin Qaramar hukumar kaduna ta Arewa ba, domin a lokacinsa Al’ummar Qaramar hukumar kaduna ta Arewa suka shaida cewa lalle suna da shugaba mai adalci da taimakon al’ummarsa. Ya qara da cewa, “ lokacin da bawan Allah nan ke Shugabancin Qaramar hukumar kaduna ta Arewa, ya yi matuqar inganta rayuwar ma’aikatan Qaramar hukumar kaduna ta Arewa, sannan ya biya xaukacin bashin da ma’aikatan Qaramar hukumar ke bi a baya. Sannan ya raba ma xaukacin Masallatai da Coci Coci dake Qaramar hukumar kaduna ta Arewa ta Janareta da kuma Lasifika, da Kafet domin gudanar da ibada kyauta.” Alhaji Bello Adamu Wakili, ya ci gaba da cewa, “a ci gaba da inganta rayuwar Al’umma da ya saba yi, Sardaunan na Badarawa, ya raba Motoci da

Babura kyauta ga xaukacin qungiyoyi 35 dake Jihar kaduna, domin inganta rayuwar Mata da Matasa. Sannan a vangare xaya kuma, ga Gidauniyarsa, wanda a kullum yana kan sahun gaba wajen taimakon Marayu da Marasa Galihu, musamman

wajen xaukar nauyin karatun Marayu da Marasa Galihu, da kuma baiwa Mata masu Qananan sana’oi jari domin dogaro da kai.” Itama a nata jawabin, Shugaban Mata na qungiyar, Hajiya Ramatu Abdulaziz, ta bayyana roqonsu a

madadin daukacin Mata dake yankin kaduna ta tsakiya, da Sardaunan Badarawan ya amince ya yarda domin ya tsaya takarar kujerar Sanata mai wakiltar kaduna ta tsakiya, saboda ya ci gaba da aikin alkhairin da ya saba yi a ko da yaushe.


A Yau

Lahadi 11 Ga Maris, 2017 (22 Ga Jumadal Thani, 1439)

TATTAUNAWA 26

Qur’ani Da Hadisi Ne Dogarona (2) – Sheikh Abduljabbar Daga Rabiu Ali Indabawa

Cigaba daga mako biyu Idan masu karatu ba su manta ba mun tsaya a inda Shehi ya yi bayani kan tarihin Cibiyar Ashabulkahfi a da sunan da hadafin, a vangaren ilimi, yanzu kuma Malam zai faxi kaxan daga cikin tarihinta a vangaren ayyuka. Akramakallahu ya zuwa yanzu As’habulkahfi tana da zawiyya da rawiyya kamar nawa? To akwai xan banbanci, in kai maganar Zawiyya da Rawiyyah, to yanzu ka koma kana tambaya ta Qadiriyyah ken an, da a nan ina amfani da sunan Qadiriyyah, wannan a gabatarwarka ban ji ka yi wannan tsokacin ba. kuma tun da ka faxo maganar Zawiyya da Rawiyya, to ka bar maganar As’habulkahfi ka faxo maganar Xariqa, ita idan za ka yi maganar As’habulkahfi sai dai ka yi maganar Makarantu, da Mu’assasa, Laburare, da Littattafanmu, waxannan duk a qarqashin As’habulkahfi suke, kuma abu ne magami na duk Musulmi. Rawiyyoyi kuwa, wannan su ne suka qunshi zikirai, ko da yake Rawiyya za ta oya shiga qarqashin As’habulkahfi, tun da maganar Riwayyah ake yi, Zawiyyah ce abinda ya shafi zikirai. A gaskiyar zance su ma zikirai in da za a kale su da idon da ya kamata, ai na duk Musulmi ne, amma yanzu ko wane an sauya shi, cewa a yanzu idan ma Xariqar kake, za ka ga Qadiriyyah da ban take Tijjaniyya daban take Arusiyya daban take, wanda wannan kuma abin takaici ne, wanda bai dace ace La’ilaha illallahu ta zama daban ba, ace Astagfirullah ta zama daban ba, bai dace Salati ya zama daban ba, ko Tasbihi, ko sauran azkaaru, abu xaya ne. To amma dai tunda ka ce Rawaiyyah da Zawiyyah, to ina son in ce maka muna da Zawiyyoyi a qarqashin Qadiriyyah amma Riyaadhuljannah, a yanzu dai muna da Rawiyyoyi sai dai mu ce xaruruwa, tsakanin ginannu da Tamfurare, wato na wucin gadi waxanda ba a kamala ba xaruruwa ne. Domin ba maganar Kano ake ba a yanzu, wannan al’amari ya faxaxa ya shiga cikin jihohin Arewa duka, kai yanzu ma har jihohin kudu, na Yarbawa da na Inyamurai.

Hasali ma ranar Asabar xin nan mai zuwa ma zan je Ibandan, kuma gun Zawiyyar ce, ga kuma kafin in je Ibadan xin nan sun yi shiri za su tare mu, na Abekuta sun yi magana, to dun muna da irin waxannan Rawiyyoyi da Zawiyyoyi a waxannan jihohi duka. To, tunda an yi maganar xariqa, menene banbanci tsakanin Qadiriyya Riyaadhul Jannah da kuma wadda ba Riyaadhul Jannah ba? Ai banbancin a rabe yake, al’amura ne, tafiya ce take hukunta kanta, kuma ta hukunta dole a yi wannan rabewa, sakamakon ana kwana ana tashi manufofi suka dinga banbanta, kuma aka yi-aka yi su haxu suka qi, har muka ga an kai matsayin da xariqar tana neman ta rushe, wasu aqidu sun shigo sababbi, wataqila wasu suna da labarin an samu har a cikin quryar gidan Qadiriyyar, wasu aqidu sun shiga na kallon wanda ya assasa gidan ma ba Musulmi bane qarara, ba Muwahhidi bane, ana yi masa kallon Mushiriki, ana kuma faxa qarara. Ana kallon cewa abubuwan da ya assasa ba addini bane. to wannan wutar fitinar ta daxe tana ci qasa-qasa muna ta qoqarin a xau matakan da suka kamata, amma ba mu samu yadda muke so ba, to dole ga muka cewa wannan abu in muka bari ya game, to za a wayi gari wata rana babu Xariqar duka, ya sa muka ga idan ba za ka iya gyarawa duka ba, to gyara kayanka, in duka ya yi yawa kare na kanaka. muna da mabiya, muna da Halqoqi, mun da Masallatai, waxanda a qarqashinmu suke, mu muka kai su qarqashin xan uwanmu, xan uwammu kuma ya kasa saisaita tafiya ta tafi yadda ya kamata, har ta kai ga an samu ‘ya’yansa suna fita daga cikin Da’irar tafiyar ta mu suna xebo mana aqidun magauta, sai muka ga to gara mu tsira da bakinmu. Sai na ce to iya duk Da’irorin da ya zamana ni na assasa su, da garuruwan da ni na kai masu Xariqa, ko kuma ma ba ni na kai ba, amma a yanzu haka da ni suka jingina, na ba da sanarwar cewa, a yanzu na janye maganar zamana qarqashin xan uwana, ina qarqashin Ubangiji (SWT) qarqashin Manzon Allah

Sheikh Abduljabar

Sallallahu alaihi wasallama, qarqashin Shehu Abdulqadir (RA) qarashin mahaifina, Rahimahullahu Ta’alah, kuma ina tsaye da qafata, wanda duk zai bini ya bini a haka, wanda bai gamsu ba ya tafi, kuma jama’a suka yi min adalci suka gamsu suka fahimce ni, kuma kowa shaida ne lallai akwai waxanda suka amsa min daga cikin waxanda suka fahimce ni, don sun san ina gaskiya a wannan lamarin, ban zo da son rai, ko qyashi ko raini a wani vangare ba, to wannan shi ya jawo, ma ana na yi maka tarihin rabuwar Xariqar, wannan shi ya kawo rabuwar Xariqar. Sunan Riyadhul Jannah kuma abin da ya kawo shi, gyara ne wanda ba Qadiriyya ba, ya kamata ace duk Xariqu sun yi shi, na kula a iya binciken da na yi a littattafan Xariqu dukkansu, sun fifita Zikiran Manzon Allah akan nasu da Allah ya yi masu buxi da su, kuma za ka ga duk littattafan in ka duba ta kan waxannan zikiran na Manzon Allah suka kai hasken da su kansu aka yi masu ilhama

da nasu zikiran qari akan waxancan. To amma a kwana a tashi himmar ta dishe, sai ya zamana yau an daina Manzon Allah duka, an koma iya na Shehunan, har yau ne zaka zo kana zikiran Manzon Allah, Subhanallahi wal hamdu lillahi wa la ilaha illallahu wallahu akbar, Astagfirullahal azeemallazi la ilaha illa huwal hayyul qayyum wa a tuubu ilaihi, Allahumma anta Rabbi La’ilaha illa anta Khalaqtani wa ana Abduka wa ana ala ahdika wa wa a dika mastaxa’a tu, a uzu bika min sharri ma sana ayu, a buu’u laka bi ni’imatika alayya, wa a buu’u bi zambee fagfirli fa’innahuu La yag firuzzunuuba illa anta. to irin waxan nan zikirai na manzon Allah da wanda suke da lokaci da waxanda ba su da lokaci, da waxanda suke da adadi da waxanda ba su da adadi, ya faxi girmansu da falalarsu ya rayu a kai, yana rantsuwa yana cewa, Allah bai tava yin zikirai masu ladansu da falalarsu ba. Da yawa wasu ‘yan xariqa ba su ma san suba, al’amarin da ya san a fara nasiha da cewa

Ci gaba daga shafi na

27


27

A Yau

Lahadi 11 Ga Maris, 2017 (22 Ga Jumadal Thani, 1439)

“Qur’ani Da Hadisi Ne Dogarona” Ci gaba daga shafi na

26

ya kamata mu koma tsarin asali, ba sakin Shehunai na yi ba, amma a xauko waxann nan na Ma ‘aikin a tsara su kuma su zama a farko. To na ma sai aka samu tirjiya, sai wasu suke ganin kamar ni na zo da su tun dad a ba a yi ya yanzu ni zan ce a yi? Sai ya zama wasu suka tsani zikiran, to ni kuma ganin haka shi ya sa na ga tafiyar, dama ba ni na sa sunan ba shi ya sa, kuma manzon Allah duk wata Halqazzikiri shi ya kira ta da Riyadhul Jannah, koma ta wacce Xariqa ce, ko ma ta wacce ba ya Xariqa. Annabi cewa ya yi duk inda aka zauna aka yi zikiri sunan wurin Riyaadhul Jannah, domin Hadisi ya zo Hasani, da hanyoyi ma banbanta, maruwaita duk sun kawo shi, Malam Hadisi sun babuka don girmansa, Manzon Allah yana cewa Izaa maradhtum bi Riyaadhul Jannah Farta’u, qaalu wama Riyaadhul Jannah? shi “Riyaadhu” Jam’i ne mufradinda “Radhu” wato Dausayi. Dausayi shi ne Lambu mai yawa Furanni da ‘ya’yan itatuwa, da ni’imar ruwa da laima. wuri dai da yake maia qayatarwa da ban sha’awa, shi ne Dausayi. “Idan kuka tarar da Dausayai kada ku wuce sai kun shiga kun yi kalaci a cikinsa,” Sahabbai suka ce ya Rasulallahi me kake nufi da Dausayi? ya ce “Halqoqin zikiri.” Ma’ana duk Halqazzikiri in ji Manzon Allah ya ce Dausayi ne na aljannah, kar a wuce sai shiga an mai da yawu, ma’ana sai an shiga an yi zikirin. to ka ga ke nan Annabi ne ya kira duk wata Halqazzikiri da wannan sunan. Sai na ga tunda wasu suna gudun sunan ni kuma bari in xauke shi in yi wa Annabi biyayya. tun da ya ce Halqoqin zikiri Riyadhul Jannah bari mu sawa namu sunan, ba suna ne da ya shafe ni ba, Ta’assubanci ne ya sa wasu suka bar min shi ni kuma ina murna sosai, don haka sai na sawa Qadiriyyar Riyaadhul Jannah, na yi Iqtibasi daga Hadisi. domin me, mun je za mu kai sanarwa gidan rediyon Kano farkon da na yi sanarwar da na yi ta cewa tafiyata tana zaune da qafarta ne, sai xan uwana ya tura ya ce a gaya masu sun shiga haqqinsa ba su da haqqin kiran wani Shugaban Qadiriyyah, tunda shi shi ne Shugaban Qadiriyyah. Sai muka sami shawara daga qwararru, suka ce to ai a iya ravawa, a iya rava sunan kada ya zama Qadiriyyah kawai, a qara da wani abu, sai muka

ce to a rubuta Qadiriyya Riyadhul Jannah, shi ke nan kuwa aka kai wa ‘yan jarida gidan rediyon Jihar Kano ne suka ci gaba da sawa. Sai ya tura ya ce don me suka ci gaba da sawa, sai suka ce ai an raba sunan, kai ba mu tava ji ana kiran vangarenka Riyadhul Jannah ba. To shike nan kuwa, da Lauyoyi da komai ya tura, da suka zauna su ma da Lauyoyinsu aka tattauna da Lauyoyina aka buga sosai aka tattauna a bisa doka da Oda, aka ce lallai babu ‘yancin hana ci gaba da sanarwa tunda suna ya banbanta. abu na biyu ke nan saboda kauce wa fitina, na farko tabarruki da Hadisin Manzon Allah na biyu doka da Oda tun da aka sani da Qadiriyya, to kuma aka ce ga wani sunan Qadiriyyah, duk da ba Rijista, ba na doka rubutacce, amma dai don zama lafiya muka ga cewa shi ke nan, kuma mu Alhamdulillahi mun fi son wannan ma sunan, za ka ji duk sanda za a yi sanarwa rediyo in aka ce Qadiriyyah za ka ji an ce Riyaadhul Jannah, to ni ake nufi, ai a nan wurinma aka tunanin akwai Qadiriyya Arusiyyah kuma Sheikh Abduljabar su ma suna da shugabanci, to a nan suka fahimci babu wata ya xau makullin motata ga shi. Ga shekarar ta dawo fitina a tare da ni. yanzu har yau babu wanda ya Akwai waxanda suka kawo. Kuma ka san mutane kuskure fahimtarka da da abin duniya, kuma ga shi suke ganin a karatunka suna ganina a cikinta kullum kamar kana tava ina yawo, a wurin na da sun martabar sahabbai, kawo da sun xauki motar. Meye zagin Sahabban akwai buqatar yin nan ne da suke faxa, mutum bayan ga jama’a. ne duk wanda ka qure shi To, shi mutum ba a hana a wata magana da kuka yi shi faxar abinda ya ga dama, da shi a can sai ya xauko Allah ma suna faxa kansa, wannan zance. Saboda wasu sun ce yana xa, wasu na rubuta wani littafi mai sun ce yana da mata, yana suna Muqaddimatul azifa, da abokin tarayya, yana dayana da, zuwa qarshe. Sun Muqaddimatul’azifan nan ta ce talaka ne shi ya ce a ba shi shiga hannun duk Malaman Zakkah, sun ce mabuqaci ne, qasar na sun ganshi, wani sun ce Yadullahi Maglula. To ya saya ya mallaka wani ya ka ga ba xaya gaskiya kuma. ara, wani ma kwafar masa Amma gas hi yau Annabi aka yi, kar ka zaci da wani dubu 100, da dubu 20, da Malami a qasar nan da ya ke dubu 4, suna faxa da aqidar iya karanta Larabci bai duba na har yanzu bata mutu ba, littafin ba, da littafin nan ana gaya wa Allah maganar yadda ake yaxa wa cewa zagin nan cewa lallai su a wurinsu Sahabbai ne, da tuntuni an yi haka yake, amma ka ga bah masa raddi. Ka tambaye su me ya sa aka yake ba. suka yi shiru, duk wanda Ba a hana xan Adam ya yi ya karanta littafin sai ya yi magana a kan ra’ayinsa, sai shiru? Ruwa bay a tsami dai ba dole ya zama gaskiya banza, maganganu ne na ba. Na’am suna faxa Shi’a gaskiya na kawo su, da suka nake, sai dai in ka ce ina jingina da ayoyi Muhkamai da hujja, a nan gizo yake saqa. Hadisai sahihai na Manzon Yana zagin Sahabbai, ina zagin ba mai kawo maka. Allah. Wanda siyasar duniya Bara a gun Mauludina wajen ta jujjuya aka samu juyin juya mutum dubu 50 ne a wurin, hali aka tattake su, har ya na kama abin magana na yi zamana ma take su xin shi shela na ce duk wanda yaw ne addini sakamakon abin o min inda na zagi Sahabbai ya daxe, wannan juyin-juya

hali an same shi tun Hijirar Manzon Allah na da shekara 30, ko kuwa in ce Wafatinsa, Hijirarsa shekara 40 lokacin. Tun daga lokacin nan aka samu sauye-sauyen sunnonin nan aka sauya su, wannan Daula da ta kama sai ta shekara 100 tana sauya Sunnonin nan, tana kashe Malamai akan faxar su, tana biyan kuxi ana qirqirar wasu, ana nata Malamai alqalai a yi ma mufti, a yi maka limamin gari, ana ta samun dai tsari sosai a sakamakon yaqar Sunnonin nan, kuma ana mutuwa a sakamakon qin binsu. Wannan ya ja Malamai suka tsorata, irin su Nasa’i duk a irin haka suka mutu, akan sun qi yarda da wannan sauye-sauye, irinsu Xabari, duk waxannan ba ‘yan Shi’a bane, su ne manyan Malaman Sunnah amma duk an kashe akan haka, wasu kuma aka xaure su a kurkuku, irinsu Abu Hanifa, irinsu Imamu Maliku ma nan da aka yi masa duka sai da varin jikinsa ya mutu, kowa yana da labarin haka, sai dai ana voye me ya sa aka yi masa hakan. Me ya sa gwamnan Madina ya yi masa duka ba a faxa, saboda cikin abin faxar akwai tpnuwar abin da ba za su a sani ba. Jama’a, za mu cigaba mako zuwa idan Allah ya kai mu.


28

A Yau Lahadi 11 Ga Maris, 2018 (22 Ga Jumadal Thani, 1439)

SIYASA

Tare da Mu’azu Harxawa 08062333065 hardawamuazu@mail.com

Rikicin Zub Da Jini A Jihohin Nijeriya: Ina Mafita? Daga Muazu Hardawa, Bauchi 08062333065

Ganin yadda fitintinu suka yawaita a tsakanin mutnen qasar nan game da abin da ya shafi rikicin qabilanci ko na addini ko rikici kan filin kiwo ko noma da makamantan su, wannan batu yana da kyau a tattauna a kansa tsakanin jama’a da gwamnatin tarayya da qungiyoyin addini da gwamnatocin jihohi ganin yadda a kullum son zuciya ke yin xauki xai xai wa rayukan bayin Allah ta hanyar hawa dokin zuciya a kan abin da bai taka kara ya karya ba, lamarin da a kullum idan mutane sun tambayi kan su shin me ke faruwa, duk inda aka kai aka dawo sai a taras son zuciya ne ko hassada game da yadda wani ya mallaki abin duniya wani kuma bai mallaka ba. Ganin irin abin da ke faruwa a qasar nan ya kamata a ce gwamnatin tarayya ta sa dokar ta vaci a wasu Jihohi musamman Binuwai da Taraba waxanda da gangan ana kallo suka bayyana cewa sun haramta kiwon dabbobi a Jihohin su, ba tare da sun yi wani tanadi na yadda masu dabbobin za su alkinta •Gwamna Bauchi kan su da dabbobin su wuri guda don gudanar da bincike kan tashin rigimar, ci gaba da hidimomin su na neman da haka za a gano wanda suke haifar da arziqi ba, musamman ganin yadda tun fitina suke samun abin duniya, kuma lokacin turawa aka ware dazuzzuka na duk gwamnan da ya san idan mutane musamman don kiwo da kuma gandun sun mutu kujerar sa za ta yi rawa ba zai daji babu farauta saboda an xauki kiwo tava bari rikici ya qi qarewa a jihar sa ba. a matsayin hanyar arziqin bunqasa Kamar dokar da gwamnonin Taraba Nijeriya tun wancan lokacin. da Benue suka kafa game da filin Amma daga baya son zuciya ya shigo kiwo kowa ya san cewa za ta haifar da kowane mutum ya taka matsayi sai ya ce matsala kuma masana sun ja hankalin a bashi daji zai yi gidan gona ko otel a gwamnatin tarayya ta tsawata musu yanka a bashi takarda kan kuxi qalilan. da cewa idan an samu matsala laifin Wannan ya haifar da duk manyan gwamnonin ne amma aka yi biris da su qasar nan sun saye gandun dajin da har rayuka da dukiyoyin mutane suka yi ke mambilla da bakin kogin Binuwai ta salwanta kuma har wannan lokaci ana da Nija da manyan koguna da sauran ci gaba da samun barazana kan wannan wurare masu dausayi da ke qasar nan. matsala ba a kwana uku sai wasu sun kai Wannan batu ya haifar da duk filayen wa wasu hari tsakanin qabilu manoma da ake hadahadar noma da kiwo sun da Fulani makiyaya, kuma har yau ba koma hannun masu ido da kwalli wasu wanda a ka ce an hukunta duk da cewa sun mayar da su gonakin alfarma wasu an san waxanda suka haifar da kowace kuma an mai da su gine-gine na alfarma, fitina a dukkan jihohin. wasu kuma ba abin da suke yi da su illa Bayan haka duk mutumin da aka iyaka suna zaman kadara don a barwa san ya taka rawa wajen hura wutar yara gado. rigimar kar a kusanto da shi jikin Ya kamata gwamnatin tarayya ta gwamnati ko kwamitin a sa masa ido samar da doka mai qarfe kan gwamnoni, kuma a kira shi cikin kwamitin amma don nuna misali game da duk gwamnan dole ya zo a bayyana masa zargin da da Jihar sa ta kasance ana yawan rikici ake masa. Kwamitin ya shirya zama ya kamata a dakatar da shi tare da don jin bahasin mutane rukuni rukuni dukkan kwamishinoninsa da masu misali daga kan matasa da qungiyoyi da bashi shawara a naxa gwamnatin riqon sarakuna da jami’an tsaro da mutanen qwarya kamar yadda Obasanjo ya yi a jihar da ake ganin kimar su, a gayyato Jihar Filato da rikici ya qi ci ya qi cinyewa wakilan waxanda ake rigima na zahiri lokacin gwamna Joshua Dariya. a fiskanci gaskiya kwamitin ya zauna Bayan an dakatar da gwamnan ya da su a tattauna sosai da duk wani da kasance kuma an kafa wani kwamiti mai ake ganin zai yi tasiri cikin shirin kawo qarfi da zai samu wakilcin qungiyoyin qarshen duk wata fitina da ake fiskanta musulmi da na Kirista da na matasa da a kowa ce jiha, ba a shirya kwamiti a sha qungiyoyi masu zaman kansu da na kare shayi a ci kuxi a watse ba. haqqin bil’adama kuma a sanya mutane Idan an gano masu haxa wannan masu kima a ciki a sahun gaba don wuta a sanar da su laifukan da ake

•Hon Ahmad Yarima

tuhumar su jama’a su sani cewa sune suka hura wuta kan rigima iri kaza idan na hukunci ne a tura su kotu, idan na sasantawa ne a taru a yi magana ba juna haquri a sani ba wanda ya isa ya kori wani daga wannan qasa. Allah shi ne ya haxa zaman kuma shi ne ya san ranar da zai raba, idan sun gamsu shikenan idan ba su gamsu ba sai a fito fili a gayawa masu haxa rigimar irin shaidun da ake da su a hannu game da lamarin su idan an ga mutum zai yi wasa da hankalin gwamnati a tona masa asiri a kawo hujjoji a kama shi a tafi da shi sama a tsare a tura kotu ko shi waye, hakan shine zai zama darasi. Idan ba haka ba aka bar mutane kara zube kowa na yin abin da ya ke so wasu qalilan na samun amfani daga jinin bayin Allah to da sannu kowa sai ya ji a jikin sa domin Allah zai sakawa duk wanda aka cutar ko aka zubar da jininsa, kuma idan aka zuba ido wa masu ci da rigima sai qasar nan ta gagari kowa zama cikin kwanciyar hankali kamar yadda ake fama a wasu sassan duniya. Idan an gama wannan aiki an gano masu laifi sai gwamnati ta sauya dukkan jami’an tsaron da ke Jihar da ake fama da rigima kamar yadda a ka tava yi lokacin Obasanjo a wasu Jihohin qasar nan da rigima ta qi qarewa. Bayan haka a yawaita jami’an tsaro na farin kaya a cikin qauyuka da yankunan karkara,a ja kunnen shugabanni idan wani abu ya sake tashi a tsige mai unguwa ko sarki ko mai riqe da mulki ko matsayi, idan ya sake tashi a karamar hukuma ko yanki a tsige sarki ko kansila ko shugaban karamar hukuma kai tsaye daga gwamnatin tarayya, idan sun ga suna ta rasa rawunnan su ina gani za a

samu maslaha daga irin fitintinun da suke aukuwa a wasu jihohin qasar nan. A qara qaimi wajen jan hankalin kirista da musulmi su ci gaba da addu’ah tare da xaukar nauyin malamai da fastoci domin zuwa qasa mai tsarki su riqa yiwa Nijeriya addu’ah kamar yadda aka saba a gwamnatocin baya. Haka kuma a yi amfani da kafafen watsa labarai wajen wayar da kan mutane game da illar tashin hankali da ke aukuwa a qasashen duniya da suka lalace irin su Somaliya da Congo da Libya da Syria da makamantansu kamar yadda wasu qungiyoyi ke yi. Babban abu kuma shine gwamnati ta riqa xaukar matasa aiki don cike guraban da ake da su a qananan hukumomi da gwamnatocin Jihohi harma da tarayya, hakan zai taimaka wajen ganin gwamnoni sun daina lalata dukiyar qasa da sunan kwangiloli da tafiye tafiye suna sace kuxaxe. Misali idan an ba gwamna naira bilyan shida daga gwamnatin tarayya albashinsa bilyan uku to a tilasta masa ya xauki ma’aikata ya zamo yana biyan bilyan huxu idan ya so bilyan biyu sai ya yi abin da ya ke so na ayyuka. Domin biyan albashi ya zamo dole idan ba ma’aikata kuma haka za a yi ta sace kuxin a bar ma’aikatu suna lalacewa matasa sun lalace idan sun sauka kuma a bar su da rigima da EFCC da sauransu duk a banza haka za a sake su daga qarshe sun ci banza sai lahira. Amma yawancin rigingimun da ake fama da su ba wanda ke haifar da su kamar amfani da matasa masu zaman kashe wando domin neman abin da za su ce ko da tsiya ko da arziki da fatar Allah ya mana jagora, Allah ya wuce mana gaba ya kawo qarshen matsalolin Nijeriya.


Wasanni

29

A Yau Lahadi 11 Ga Maris, 2018 (22 Ga Jumadal Thani, 1439)

Tare da Abba Ibrahim Wada Leadership Ayau@yahoo.com

Waxanne ’Yan Wasa Real Madrid Za Ta Siya A Kakar Wasa Mai Zuwa? Daga Abba Ibrahim Wada Gwale Duk da cewa Real Madrid har yanzu tana fafatawa a gasar zakarun turai ta bana amma zamu iya cewa kakar wasa ta bana bata yiwa qungiyar daxi ba saboda yadda tasha kashi a wasanninta na laliga sannan kuma qungiyar Barcelona tana gabanta da maki goma sha shida a gasar laliga wanda ba qaramin qalubale bane a qungiyar. Real Madrid tana buqatar lashe kofin zakarun turai idan har tanason ta gama kakar bana cikin nasara amma rashin lashe kofin na zakarun turai na nufin qungiyar zata qare kakar bana a tutar babu bayan da akayi waje da ita a gasar Copa Del Rey. Wasu suna ganin qungiyar tana buqatar yin garambawul a cikin yan wasanta yayinda kuma wasu suke ganin kamar qungiyar tana buqatar sabon mai koyarwa ne domin akwai manya kuma shahararrun yan wasa a qungiyar duk da haka. A shekarar data gabata ne qungiyar qwallon qafa ta Real Madrid ta lashe kofin zakarun turai kuma duk da yan wasan qungiyar da suke fafatawa a yanzu haka a qungiyar. Bayan da aka bayyana cewa akwai yan wasa da yawa waxanda suke qungiyar kawo yanzu kuma suke buqatar barin qungiyar domin kawo sababbin jini a qungiyar domin cigaba da tallafawa qungiyar. Real Madrid dai qungiya ce wadda take yawan jan hankalin manyan yan wasa a duniya idan har ta bayyana sha’awarta ta neman xan wasan kuma yan wasa da yawa suna nuna sha’warsu ta komawa qungiyar koda kuwa ace bata nemesu ba. Qungiyar tana buqatar siyan yan wasa kalakala domin dai qara qarfi inda tuni qungiyar a baya ta nuna sha’awarta na siyan mai tsaron raga da yan wasan tsakiya da kuma yan wasan gaba masu zura qwallo a raga. Sai dai ko dawa-dawa qungiyar ake tunanin qungiyar zata nema idan an buxe kasuwar siye da siyar da yan wasa? De Gea Ko Thibaut Coutoise A shekara ta 2015 ne dai qungiyar qwallon qafa ta Real Madrid ta kusa siyan mai tsaron ragar Manchester United, David De Gea, xan asalin qasar sipaniya sai dai cinikin bai kammalu ba sakamakon tangarxar na’ura da aka samu wajen tura takardun mai tsaron ragar zuwa ga hukumar qwallon qafa ta duniya , FIFA, domin tabbatar da cinikin. Lalacewar wannan ciniki yaja cecekuce tsakanin qungiyoyin biyu inda shugaban gudanarwar qungiyar Real Madrid ya bayyana cewa Manchester United bata nuna qwarewa ba wajen cinikin kuma suna sane sukaqi tura takardun xan wasan akan lokaci. Tun bayan lalacewar wannan ciniki Real Madrid ta cigaba da neman mai tsaron ragar inda kamar yadda rahotanni suka dinga bayyanawa Real Madrid tana son yin musaya da Manchester United da David De Gea da kuma Gareth Bale. Shima Thibaut Coutoise wanda ya tava zama a qungiyar qwallon qafa ta Atletico Madrid yana xaya daga cikin yan wasan da qungiyar ta Real Madrid take zawarci bayan da mai tsaron ragar ya bayyana aniyarsa ta komawa qasar sipaniya domin cigaba da buga wasanninsa. “Inason zaman birnin Madrid saboda garine mai xaxi kuma matata da yayana duk suna can a

Neymar Jr. zaune saboda haka ina fatan nan gaba zan koma birnin domin cigaba dabuga wasana” wannan shine kalaman mai tsaron ragar wanda shima yana cikin masu tsaron ragar da qungiyar ta Madrid take nema. Sai dai abune mai wahala qungiyar ta samu xaya daga cikin waxannan masu tsaron raga sakamakon kowanne daga cikinsu yana bugawa ne a babbar qungiyar kuma yana xaukar albashi mai kyau wanda zaisa sai qungiyar ta Real Madrid ta dage domin jan hankalin xaya daga cikinsu ya amince ya koma qasar sipaniya da buga wasa. Emery Can Da Verati Da De Bruyn Duk da cewa za’a iya cewa Real Madrid tana da yan wasan tsakiya waxanda za’a iya cewa suna daga cikin fitattun yan wasan tsakiya na duniya amma qungiyar tana neman siyan yan wasan tsakiya waxanda zasu maye mata gurbin waxanda take dasu a yanzu wato Toni Kroos da Luca Modric waxanda shekarun sun fara cimmusu. Xan wasan qungiyar qwallon qafa ta Liverpool, Emery Can, xan qasar Jamus wanda kwantaraginsa zai qare a qungiyar a qarshen kakar da ake ciki shima yashiga cikin yan wasan tsakiyar da qungiyar Sai Verati, xan qasar italiya wanda kuma yake buga wasansa a qungiyar qwallon qafa ta PSG wanda shima qungiyar ta xaxe tana zawarcinsa domin ya buga mata wasa sai dai abune mai wahala PSG ta iya siyar da xan wasan nata sakamakon itama yanzu tana ganin qarfinta ya kawo kuma tana son lashe gasar zakarun turai. A kwanakin baya ma an dan ganta qungiyar Real Madrid da neman xan wasa Kevin De Bruyn, xan qungiyar Manchester City wanda kawo yanzu za’a iya cewa tauraruwarsa tana haskawa a duniya amma kuma shima abune mai wahala Manchester City ta iya siyar da babban xan wasan nata wanda ake tunanin zai iya lashe kyautar gwarzon xan wasa na gasar firimiya gaba xaya a bana. Shi ma xan wasan qungiyar qwallon qafa ta Bayern Munchen, David Alaba, xan qasar Austria yana cikin yan wasan da qungiyar take nema domin yin amfani dashi a tsakiyar fili duk da cewa yafi buga wasa a tsakiyar baya ko kuma gefen hagu na baya amma shima Madrid xin zata iya tuntuvar qungiyarsa ko zata siyar mata.

Edin Hazard Salah, Lewandowski Da Hazard Sakamakon qarancin qwallaye da qungiyar tasha fama da ita wannan kakar musamman a farkon kakar bana inda yan wasanta na gaba da suka haxa da Cristiano Ronaldo da Karim Benzema da Gareth Bale basu zura qwallaye da farkon kaka ba kuma hakanne yasa qungiyar bata fara wasannin da qafar dama bat a dinga samun tuntuve. Qungiyar qwallon qafa ta Real Madrid ta shirya kashe kuxi domin siyan manyan yan wasan gaba waxanda zasu dawo da martabar qungiyar wajen zura qwallo a raga kuma tuni qungiyar ta shirya tuntuvar qungiyar Liverpool domin siyan Muhammad Salah wanda kuma kamar abune mai wahala wannan ciniki ya kasance. Salah dai yakoma Liverpool a shekarar data gabata daga qungiyar qwallon qafa ta Roma akan kuxi fam miliyan 34 sai dai kuma abune mai mutuqar wahala Liverpool xin ta yarda da wannan cinikin sakamakon xan wasan yafara buga gasar da qafar dama. A kwanakin baya ma mai koyar da tawagar yan wasan qasar Egypt (Masar) ya bayyana cewa Salah zai iya komawa Real Madrid saboda yadda ya iya buga qwallo kuma shima xan wasan yana son buga qungiya kamar Real Madrid. Tabbas a qarshen kaka Real Madrid zata tuntuvi Liverpool akan xan wasa Salah duk da cewa abune mai wahala Liverpool ta yarda da cinikin sakamakon bata daxe da siyar da xan wasanta Philliph Coutinho zuwa qungiyar Barcelona ba. Shi ma Robert Lewandowski yana cikin yan wasan da Real Madrid take nema kawo yanzu sakamakon Karim Benzema baya buga abinda qungiyar take buqata kuma tuni xan wasan ya nuna sha’awarsa na barin Bayern Munchen domin buga wasa a wasu qungiyoyin kuma hakanne ma yasa tuni xan wasan ya canja wakilin yan wasa inda tuni ya xauki Zahavi, wanda ya shafe shekara 30 yana wakilcin siyar da yan wasa. Harry Kane Kusan shi ne xan wasan da za a ce yana kan gaba a cikin yan wasan da qungiyar take zawarci bayan da tuni qungiyar ta shirya tsaf domin taya xan wasan wanda zai kai sama da fam miliyan 100 kamar yadda rahotanni suka bayyana. Kane kawo yanzu yanada qwallaye 24 a

Harry Kane gasar firimiya yayinda yafi kowanne xan wasa zura qwallo a raga kuma shekaru biyu da suka gaba ma shine yake lashe kyautar xan wasan dayafi zura qwallo a raga a gasar firimiya ta qasar ingla. Edin Hazard Xan wasa ne wanda shima za’a iya cewa Real Madrid ta xauki tsawon lokaci tana zawarcinsa sai dai zamu iya cewa haqanta yakusa cimma ruwa sakamakon rahotannin da suka bayyana cewa tattaunawar xan wasan da qungiyarsa ta Chelsea tana samun cikas sakamakon xan wasan bai gamsu da tsarin tafiyar da qungiyar ba musamman wajen siyan sababbin yan wasa da kuma yanayin yadda qungiyar take buga wasanninta na wannan shekarar. Tuni dai Real Madrid tayiwa Chelsea tayin xan wasa Gareth Bale domin ta xauki Hazard sannan kuma ta cikawa Chelsea kuxi sai dai Chelsea har yanzu tana ganin zata iya shawo kan xan wasan domin yaci gaba da zama a qungiyar. Hazard dai ya daxe yana sha’awar komawa Real Madrid kuma kusan kamar lokacin yayi na yin wannan ciniki bayan da qungiyar t agama shiryawa domin siyan xan wasan. Neymar Jr. Shi ne xan wasa na kwana kwanan nan da qungiyar Real Madrid take zawarci tun bayan da rahotanni suka bayyana cewa yafara samun rashin jituwa da wasu daga cikin yan wasan qungiyar wanda hakan yasa akace yafara danasanin barin Barcelona domin zuwa qungiyar ta PSG. Tuni Real Madrid ta nuna sha’awarta qarara na xaukar xan wasan a kakar wasa mai zuwa sai dai abune mai wahala qungiyar ta iya samun xan wasan a qarshen kaka saboda PSG bazata siyar da xan wasan ba bayan yayi shekara xaya kacal a qungiyar. Shi ma xan wasan yanason bugawa Real Madrid wasa bayan da wasu daga cikin yan wasan qungiyar ta Real Madrid musamman yan qasar sa ta Brazil suka bayyana fatansu na ganin xan wasan yakoma Real Madrid Sai dai duk wannan canji da qungiyar take buqata ya ta’allaqa ne ga mai koyar da yan wasan qungiyar yayinda wasu suna ganin kamar qungiyar zata raga gari da mai koyarwa Zidane domin xaukar sabon mai koyarwa.


30

WASANNI

Pogba Ya Ji Rauni A Ranar Juma’a, In Ji Mourinho Mai koyar da yan wasan qungiyar qwallon qafa ta Manchester United, Jose Mourinho ya bayyana cewa xan wasan qungiyar, Paul Pogba yaji rauni a lokacin da yan wasan qungiyar suke xaukar horo a ranar Juma’a wanda hakan yasa bai buga wasan da qungiyar ta lallasa Liverpool ba da ci 2-1. Mourinho yace xan wasan yaji rauni kuma likitocin qungiyar sun bayyana cewa bazai iya buga wasan da quniyar ta buga da Liverpool ba saboda haka yana jiran rahoto akan ciwon nasa a gobe Litinin. Ya cigaba da cewa Pogba bashi da sa’a wajen jin ciwo kuma kamar Pogba, shima baiji daxin ciwon da xan wasan yatafi ba saboda haka yana baqin ciki da faruwar wannan lamari mara daxi. Sai dai an tambayi Mourinho cewa ko Pogba zai iya buga wasan da qungiyar zata buga da Sevilla a gasar zakarun turai? Sai Mourinho yace shima bai sani ba saboda haka yana jiran bahasi daga wajen likitocin qungiyar. Manchester United dai ta lallasa Liverpool daci 2-1 a filin wasa na Old Trafford ta hannun xan wasa Marcos Rashford wanda duk shine ya zura qwallayen guda biyu a dai-dai minti na 14 da 24 da fara wasa sai dai xan wasan baya na qungiyar, Eric Bailly yaci gida bayan andawo daga hutun rabin lokaci. A ranar Talata ne Manchester United zata karvi baquncin Sevilla wadda zata zo daga qasar sipaniya a wasa na biyu na gasar zakarun turai bayan da aka buga 0-0 a wasan farko da suka buga a qasar sipaniya.

A Yau

Lahadi 11 Ga Maris, 2017 (22 Ga Jumadal Thani, 1439)

Kante Ya Warke Kuma Zai Buga Wasan Barcelona, In Ji Conte Mai koyar da qungiyar qwallon qafa ta Chelsea, Antonio Conte, ya bayyana cewa xan wasan tsakiyar qungiyar, N’Golo Kante ya warke kuma zai fuskanci wasan da qungiyar zata fafata da Barcelona a wasan zakarun turai na wannan makon. Kante, xan asalin qasar Faransa ya faxi ne ana tsaka da xaukar horo a qungiyar sakamakon muku mukun sanyi da akeyi a birnin Landan a yan kwanakin nan wanda hakan yasa likitocin qungiyar suka duqufa wajen ganin xan wasan ya murmure. Antonio Conte yace zuwa yanzu komai yayi dai-dai kuma xan wasan yasamu qwarin jiki tun a satin daya gabata sai dai sun yanke shawarar qin amfani dashi ne a wasan da suka sha kashi a hannun Manchester

City domin ya sake murmurewa. Ya cigaba da cewa amma yanzu xan wasan ya halarci filin xaukar horon qungiyar gaba xaya a wannan satin kuma tuni ya shirya domin buga wasan wannan satin da Barcelona bayan da likitoci suka bayyana cewa babu matsala. Kante dai yabuga wasannin firimiya 29 a Chelsea kawo yanzu kuma ya buga wasanni 9 a ragowar gasanni inda Chelsea xin take mataki na 5 akan teburin firimiya. A ranar Laraba ne Chelsea zata kai ziyara qungiyar qwallon qafa ta Barcelona domin buga wasa na biyu na gasar zakarun turai bayan da qungiyoyin suka haxu sati biyu daya gabata a filin wasa na Stamford Bridge dake Landan kuma suka buga 1-1.

Haihuwar Da Matar Messi Za Ta Yi Ya Hana Shi Buga Wasan Barca da Malaga Xan wasan qungiyar qwallon qafa ta Barcelona, Lionel Messi, ya janye daga buga fafatawar da Barcelona za ta yi da Malaga a jiya Asabar saboda dalilai na “kashin kansa” Barcelona ta sanar a shafinta na sada zumunta cewa xan wasan ba zai shiga a karawar ba tana mai cewa ta maye gurbinsa da Yerry Mina, sabon xan wasan da qungiyar ta siyo Rahotanni sun bayyana cewa ana sa ran mai xakinsa ce za ta haifi xansu na uku kowanne lokaci daga yanzu wanda hakan yasa ya buqaci abashi dama ya kula da halin da take ciki Barcelona ce ke kan gaba a saman teburin La Liga kuma za ta fafata da Chelsea a wasa na biyu a wasan ‘yan qungiyoyi 16 na gasar cin Kofin Zakarun Turai ranar Laraba. Mai koyar day an wasan qungiyar, Enersto Valverde, ya bayyana cewa ba matsalar ciwo bace tasa xan wasan bazai buga wasan ba kuma zai buga wasan da zasu karvi baquncin Chelsea a filin wasa na Nou Camp. Barcelona ce dai akan gaba akan teburin laliga inda tabawa Atletico Madrid wadda take maraki na biyu maki 8 bayan ta dokesu a satin daya gabata.

Anceloti Ya Na Son Amsar Aikin Wenger Rahotanni daga qasar italiya sun bayyana cewa tsohon mai koyar da qungiyar qwallon qafa ta Real Madrid da Chelsea, Carlo Anceloti, xan qasar italiya yana son aikin koyar da qungiyar Arsenal idan har mai koyar da yan wasan qungiyar, Arsene Wenger ya ajiye aikin nasa. Anceloti. Wanda yakoyar da qungiyar qwallon qafa ta AC Millan da Juventus da PSG da Real Madrid bashi da aiki tun bayan da qungiyar qwallon qafa ta Bayern Munchen ta sallameshi a farkon kakar nan da ake ciki. Mai koyar da yan wasan qungiyar Arsenal, Mista Wenger dai yana fuskantar matsin lamba daga wajen magoya bayan qungiyar dake faxin duniya inda suke kira daya ajiye aikin koyar da qungiyar bayan daya shafe

shekara sama da 20 yana aikin koyar da qungiyar. Arsenal dai tana matsayi na shida a kan teburin firimiya kuma maki 13 tsakaninta da mataki na 4 wanda shine mataki na qarshe na samun gurbin gasar zakarun turai. Qungiyar qwallon qafa ta PSG ma dai tana zawarcin tsohon mai koyar da qungiyar yayinda itama Chelsea, wadda ya tava koyar da qungiyar a shekarun baya tana son yadawo domin cigaba da koyar da qungiyar. A kwanakin baya dai an danganta mai koyarwar da karvar aikin koyar da tawagar yan wasan qasar Italiya domin maye gurbin wanda qasar ta kora sai dai an bayyana cewa mai koyar da yan wasan Chelsea, Antonio Conte, shine akan gaba a waxanda ake tunanin zasu

karvi aikin horar da yan wasan tawagar ta Italiya.


A Yau

Lahadi 11 Ga Maris, 2017 (22 Ga Jumadal Thani, 1439)

Madrid Da Barcelona Na Zawarcin Blind Na Manchester United

Daga Gwale

Abba

Ibrahim

Wada

Rahotanni daga qasar Holland suna bayyana cewa manyan qungiyoyin gasar laliga guda biyu wato Real Madrid da Barcelona suna zawarcin xan wasan baya na qungiyar Manchester United, Danley Blind. Blind dai yakoma Manchester United daga qungiyar qwallon qafa ta Ajax Amsterdam dake qasar Holland a lokacin tsohon mai koyarwa Luis Van Gaal yana iki da qungiyar. Xan wasan dai baya samun buga wasa a qungiyar a daidai wannan

lokaci inda gaba xaya a wannan kakar sau uku aka fara wasa dashi a cikin yan wasa sha xaya na farko duk kuwa da yanayin yadda ya iya taka qwallo Sai dai qungiyar qwallon qafa ta Real Madrid tana neman xan wasa wanda zai iya bugawa a baya da kuma tsakiyar fili wanda shi kuma Blind din duk zai iya wannan abu yayinda itama Barcelona take neman kalar irin wannan xan wasa. A kwanakin baya Luis Van Gaal, tsohon mai koyar da Manchester United wanda qungiyar ta kora ya bayyana cewa yakamata xan wasan yakoma Barcelona domin sune suka

dace da yanayin wasansa da kuma yanayin yadda ake buga qwallo a qasar ta sipaniya zata yiwa xan wasan daidai. Ana tunanin xan wasan zai bar Manchester United a qarshen kaka idan har mai koyar da yan wasan qungiyar ya amince idan kuma ba haka ba Blind zai bar qungiyar a qarshen kakar nan ba tare da qungiyar ta siyar dashi ba sakamakon kwantaragin xan wasan da zai qare. Itama tsohuwar qungiyarsa ta Ajax tana zawarcin xan wasan xan asalin qasar Holland mai shekaru 27 a duniya.

WASANNI

31

Klitschko Ya Siyar Da Riga Domin Tallafawa Marasa Qarfi A watan Afrilu, Wladimir Klitschko ya sayar da rigar da ya shiga fage da ita wadda ke xauke da ‘yar ma’adanar bayanan kwamfuta ta tafi da gidanka (USB stick), mai qunshe da hasashen yadda dambensa zai kasance da Anthony Joshua, wanda ya doke shi, a kan fam dubu 160. Klitschko tsohon zakaran damben boksin na mafiya nauyi na duniya mai shekara 41, ya sanya doguwar rigar ne ya zo dandalin, kafin damben nasa na qarshe a filin wasa na Wembley, da zakaran na duniya na yanzu Anthony Joshua. An xinke ‘yar na’urar ne a jikin rigar wadda ke xauke da hasashensa na yadda yake ganin damben zai kaya, wanda ya ce mutumin kawai da zai ji wannan hasashe shi ne wanda ya sayi rigar. A turmi na goma sha xaya Joshua ya doke Klitschko qan qasar Ukraine, wanda tuni ya yi ritaya daga damben boksin din. Kuxin da aka samu na sayar da rigar a wurin wani taron samar da tallafi a Landan ranar Laraba, za a yi amfani da shi ne a ayyukan da Gidauniyar Klitschko ke taimaka wa.

Siyan Neymar A PSG Ba Zai Sa Ta Zama Babban Qungiya Ba Wataqila A Yi Wa Eric Bailly Tiyata A Qafarsa Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta AC Milan Arigo Sacchi, ya ce sayan Neymar da PSG ta yi, bai isa bai wa kungiyar damar yin kafada da kafada da sauran manyan kungiyoyin kwallon kafa na duniya ba. Sacchi wanda ya jagoranci kungiyar AC Milan wajen lashe kofunan gasar zakarun turai biyu a

jere cikin shekarun 1989 da 1990, ya ce bai gamsu da irin salo ko matakan da kungiyar PSG ke dauka ba domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu, a kokarin da ta ken a yin fice a fagen kwallon kafa. Idan za’a iya tuna wa PSG ta kashe kudi euro miliyan 400 wajen sayen dan wasan gaba na kungiyar Barcelona neymar akan euro

miliyan 222 mafi tsada a duniya, da kuma matashin dan wasan gaba na kungiyar Monaco Kylian Mbappe akan euro miliyan 180, bayaga sauran cinikayyar ‘yan wasan da ta yi. Sai dai duk da haka ta gaza kai wa matakin gaf da kusa da karshe a gasar zakarun turai, fafutukar da ta ke yi tun daga shekarar 2011.

Wataqila a yi wa xan wasan baya na Manchester United Eric Bailly aiki a qafarsa sakamakon tsananin raunin da ya ji in ji mai koyar da yan wasan qungiyar Jose Mourinho a jiya Asabar. Xan wasan mai shekara 23 wanda Mourinho ya ce ya ji rauni a idon sawu lokacin da ya je buga wata qwallo bai taka wa Manchester United wasanni ba tun kusan watan Janairu Mourinho ya ce a yanzu suna jarraba wasu hanyoyi na maganin raunin kamar yadda aka saba amma idan ya ci tura to dole sai an yi masa aiki wanda kuma basa fatan hakan. A rashin xan wasan yanzu kociyan ya ce yana amfani da Chris Smalling da Victor Lindelop kamar yadda ya sa su a wasannin qungiyar na baya Bailly shi ne xan wasan farko da Manchester United ta siyo daga Villareal a bazarar 2016 a kan fam miliyan 30, bayan da Mourinho ya zama mai koyar da yan wasan qungiyar. Sai dai a na tunanin xan wasan zai buga wasan da qungiyar zata buga da Sevilla a gasar zakarun turai a ranar Talata a filin wasa na Old Trafford


11.03.18

AyAU LAHADI LEADERSHIP Don Allah Da Kishin Qasa

www.leadershipayau.com Leadership A Yau

11 Ga Maris, 2018 (22 Ga Jumadal Thani, 1439)

WASANNI

Waxanne ’Yan Wasa Real Madrid Za Ta Siya A Kakar Wasa Mai Zuwa? > Shafi na 29

JARIDAR HAUSA MAI FITOWA KULLUM TA FARKO A NIJERIYA

LeadershipAyau

No: 026

N150

Mahanga Gudunmawar Qungiyar UFUK Wajen Samar tare da

Musa Muhammad

Da Fahimtar Juna A Tsakanin Jama’a 08148507210 mahawayi2013@gmail.com

A wasu rubuce-rubuce da na yi a baya na yi bayani game da muhimmancin zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin jama’a. Wannan ya zama wani abu ne da ya wajaba a ce jama’a sun mayar da hankali a kansa, musamman bias la’akari da irin muhimmancin da zaman lafiya da fahimtar juna ke da shi a tsakanin jama’a, musamman a wuraren da ake cuxanye da addinai daban-daban ko kuma qabilu daban-daban. Xaixaikun jama’a da qungiyoyi ma a bar su a baya ba wajen fitowa don yin yekuwa game da muhimmancin wannan muhimmin abu, ta yadda ake ta yin kirayekiraye ga jama’a su rungumin aqidar zaman lafiya da fahimtar juna a duk inda suke. A irin wannan ne wata qungiya da wasu mutanen qasar Turkiyya, waxanda suke gudanar da ayyukan kasuwanci da taimakon al’umma da yawa a wannan qasa, wato UFUK DIALOGUE ta duqufa wajen gudanar da ayyukan da take ganin za ta wayar wa da jama’ar qasar nan kai wajen samar da zaman lafiya da fahimtar juna. UFUK DIALOGUE ta kasance tana gudanar da tarukan wayar da kan jama’a a wurare da dama domin a nuna yadda wannan abu na fahimtar juna ke da muhimancin ga duk al’ummar da zaman tare da ta kama, ba tare da la’akari da addini, qabila ko yankin da mutum ya fito ba. An kafa qungiyar UFUK DIALOGUE ne a Abuja domin ta shiga gaba don bayar da tata guduamawar wajen samar da fahimtar juna da zaman lafiya a tsakanin al’ummar Nijeriya, ta hanyar shirya tarurrukan da za a tattauna, a yi musayar ra’ayi a duk hanyoyin da ake jin za su taimaka wajen cimma wannan manufa ta samar da fahimtar juna. Yana da muhimmanci a san cewa a rayuwa babu wani abu mai muhimmanci kamar samar da fahimtar juna a tsakanin jama’a, domin ta hanyar haka ne ake samun duk wani ci gaba mai amfani ga duk wani mahaluki zai tunai a kansa.

•Sultan Sa’ad AbubakarIII

Babu yadda za a a samu wani ci gaba mai ma’ana ba tare da an samu fahmtar juna a tsakanin jama’a ba. Domin da fahmtar juna ne ake samun zaman lafiya, da zaman lafiya ne ake damun duk wani ci gaba mai amfani ga al’umma da duk wani mai rai. A yawancin lokuta rashi kusantar juna ne babban jigon kawo duk wani savani da rashin jituwa. A irin wannan ne ya sa ita wannan qungiya ta UFUK DIALOGUE ta fi mayar da hankalinta wajen abubuwan da za su kusanto da jama’a kusa domin a ji daga juna, a fahimci juna, a magance duk wani savani da ka-iya kawo ruxani a tsakanin jama’a. Na kasance cikin waxanda wannan qungiya ta UFUK DIALOGUE ta gayyata wajen wani babban taro da ta kira a Abuja cikin watan da ya gabata, bisa haxin qwiwa da wasu Hukumomi domin shirya wani babban taro na qasa da qasa don tattauna muhimman batutuwan da suka shafi wannan maudu’i namu na samar da fahimtar juna a tsakanin jama’a.

•Archibishop Onaiyekan

A taron na bana, wanda yake shi ne karo na huxu, ya gudana ne a babban xakin taro na IPCR da ke babban birnin tarayyar qasar nan, Abuja a ranar 15 ga watan Faburairun da ya gabata, kuma an sa masa taken ‘COUNTERING VIOLENT EXTREMISM.’Kuma ya gudana ne bisa jagorancin ita UFUK DIALOGUE , tare da haxin qwiwar IPCR, ECOWAS, NDA, NCWS, Ma’aikatar yaxa labarai da al’adu, ma’aikatar matasa da wasanni da jaridar DAILY TRUST. An tattauna batutuwa da daman gaske game da wannan batu, inda duk waxanda suka haxa qwiwa a wannan taro sun turo da wakilansu, kuma aka gudanar da qasidu masu muhimmancin gaske, musamman a wannan yanayi da muke ciki. Ga duk wanda ya halarci wannan taro, lallai ya tafi da tunanin cewa babu wani abu a rayuwa wanda ya fi al’umma su fahimci muhimmancin zaman lafiya, ta hanyar fahimtar juna, zaman tare da duu masu ra’ayi kowne iri, da kuma duk masu kowace irin fahimta ce. Domina an

tattauna batutuwan da suka shafi wannan harka, ta yadda za a iya shiga gaba a jagorancin duk wani nau’i na wannan abu. Ba zan tsunduma a batutuwan da aka tattauna a wannan muhimman taro ba, amma a hankalin, da yardar Allah zan kawo su a wannan shafi mai mai albarka.

Babba Da Jaka A karon farko sanatocin Zamfara sun haxu a inuwa xaya -Labarai

Uwar Bari!

Ana shiryawa da buga LEADERSHIP A Yau a kamfanin LEADERSHIP GROUP LIMITED, lamba 27, kan Titin Ibrahim Tahir, a Gundumar Utako, Abuja. Tarho: 09-2345055; Fax: 09-2345360. P. O. Box 9514, Garki II, Abuja. Ofishin mu a Legas: 34/36 Titin Adegbola, Anifowose, daidai Oba Akran, Ikeja. Tarho: 01-8963459. Shafinmu: leadershipayau.ng, E-mel: leadershipayaulahadi@yahoo.com

LEADERSHIP A Yau 11 Ga Maris 2018  

LEADERSHIP A Yau 11 Ga Maris 2018

LEADERSHIP A Yau 11 Ga Maris 2018  

LEADERSHIP A Yau 11 Ga Maris 2018

Advertisement